manta. Ta koma cikin motarta
inda babanta ya kira ta.
"Yana ciki bai gan ki ba yanzu ya kira ni
kina ina ne?"
"Father ina mota ina jiran sa in ya fito kace
masa ya same ni gaban mota, ba zan iya jira
waje ba na gaji"
a
Bata rufe baki ba sai ta ji an dan
kwankwasa motarta. Ta juyo ta dube shi. Babu
tababa shine bakonta. Yana rataye da jaka a
77 Mafivan Masova Rahma AbdulMajid
kafadarsa duk da yana sanye da kayan gida.
Wato zabbuni mai nauyi da yayi masa kyau.
Fuskarsa tayi kama da masu saukin fahimta. Та
tattaro murmushi ta fora a fuskarta a yayinda ta
fito daga motar ta fuskance shi.
"Kai nc....
"Abdul Azeez, na san kin manta sunan".
Suka yi musayar hannu a yayinda tayi
murmushi ta yi fari.
99 "Kayi hakuri kan nawa ne...
Ya gyada kai.
"Na san haka kuma zan taimaki kan naki a
dan zamana:.
Ta wuce ta bude masa but ya jefa jakarsa
sannan sannan ya dawo kujerar gaba ya zauna ta
ja mota.
"Ina zan kai ka masauki don na san ka
gaji?"
Ta yanke hirar gabatar da junan da suke a
yayinda ta kama hanyar titin shiga gari. Ya dan
dubeta kamar yadda ya jima yana satar kallon ta
a tafiyar nan.
"Ban gaji ba muddin baki gaji ba, na zo ne
don na dan zauna dake mu yi hira, amma in kin
gaji zan je ni ma na huta".
Ta sha kwana cikin cin taya.
"Na fi so ka huta don gobe kamar muna da
dokaci in ba sauri kake ba, zamu zauna mu shiga
gari"
Rahma Abdul Majid 78 Mafiyan Masoya
"Yadda kika ce, sai ki sauke ni a otel din da
yayi miki, amma bana son Stars, sun fan cika
hayaniya *
Jifar ta yi da Jakarta ne ya janyo hankalinsa
na cewa ta dawo har ta shigo falon ya zaburo da
alamar ya jima yana jiran ta. Ya yi gumi
kashirfan kamar ba sanyi ake ba duk kuwa da
babu na`urar zafafa gida a kunne. Daga shi sai
gajeren wando.
"Kin dawo"
ya ambata da sauri yana shirin tahowa gare
ta. Ita kuwa hankalinta na kan yanayinsa da ya
fadar mata da gaba ko wani abu ya faru.
"Baby lafiya? Me ya sa ka yi wurjanjan
haka.. gumi fa kake...Gaya min lafiya?"
Ita ma tuni ta rike shi tana duba jikinsa
Yayi ajiyar zuciya ya lumshe ido.
"Bar ni kawai, babu abin da ya faru sai
kewar ki da...da gaskiya bari in gaya miki da
kishi... ina so in yi miki magana bana so in 6ata
mana tsari, na rasa yadda zan yi ban san a
halinda kike ba, duk na damu"
Ya ruko ta da kyau idanunsa cikin nata
ayayinda take dariyar keta.
"Na san kina tare da wani na Farida... na
damu ba ni da mafita, na san yadda kowane na
miji yake iya ji in har Farida na tare da shi"
Ta toshe bakinsa sannan ta yi magana.
"Ina tare da wani amma ba waninka ba.
Belly baka da wani a wurina kai kaďai ne. kada
7 Mafiyan Masoy a Rahma AbdulMajid
ka bari kishi ya kashe ka kan abin da ka kago
gobe ma zai sake faruwa don kishiyarka na son
yin doguwar hira da ni
Ta fashe da dariya a yayinda ta ji cikin
mamakinta ya fada jikinta ya kankame ta ya
sunne kansa cikin kirjinta yana fadin. 'Na yi
kewarki Farida...rayuwa na kara tabbatar min
bata da dandano in ba ki cikinta'. Ta fahimce
shi. Tunda suka yi aure basu taba rabuwa na
awa daya ba sai yau, dole ya ji wani iri.
"Kuma dole rayuwa ta ci gaba da yin dadi
domin ba inda zani na bar ka”.
*
A wata 'yar haraba da ke otel din da aka
kebe saboda irinsu masu hirar kadaita Farida се
zaune gaban AbdulAzeez dukansu sun yi
matukar suturar sanyi saboda maido da jiki da
yayi tun a daren jiya. Dukan su suna shan kayan
zafi a yayinda suke hirar.
"Farida bisa alada irin wadda muka tashi da
ita masoya kan jinkirta lokacin fadin soyayya
gatsau har sai sun sami lokaci mai daman a
fahimtar juna da tsara yadda wannan ranar fadin
albarkacin baki zata fi dacewa, wasu kan ja
lokaci suna wannan shirin har sai lokacin da
Kalmar tayi amai ta fito da kanta ba bisa lokacin
da aka tanada ba a sabili da gajiyar 6oye ta ko
kuma wani dalili ya tilasta hakan. Duk na san
hakan kuma nayi duk wannan tanadi, don haka
kada ki ji ina gaya maki sirrin zuciyata ki zaci
kamar rana tsaka ne, kayya! Farida na dade ina
80 Mafiyan Masoyaа Rahma AbdulMajid
son ki so irin wanda ban taba jinsa ba a
rayuwata ballantana in taba yi wa wani. Sai dai
ko kadan ban taba tunanin cewa dole ne na sami
dacewa da soyayyarki ba, na san zuciya, tana
dauke da 'yanci ne ko da kuwa mutum bai ba ta
shi ba. Ni dai ina fita hakkin zuciya ta ne, kuma
ina shirye da fita naki hakkin"
Ya dan kura mata ido kamar yadda take
kallon sa tun dazu.
"Farida ina son ki ban san yadda zan yi da
kaina ba, amma tuni jiki na ya fara gaya min
cewa kina da inda kika sanya zuciyarki... ban
ga so na a idonki ba, amma kuma gaskiyar
lamari daya shine ba zan iya rabuwa dake ba,
ina son ki ne muddin rayuwa, zabina daya shine
na sanya kai na a hidimarki muddin zan dinga
samin sanyin zuciya a ganin ki da jin ki, koda
ba zaki iya so na ba Farida kiyi min wata
alfarma ita ce ta kada ki yanke da ni, kada ki
sake yi min nisa, zan yi manejin koda ganinki
ne da murmushin ki da nuna min sanayya a
matsayin goron da rayuwata zata iya samu...
Ya dauke murya ya dan fara kallon wasu
wuraren daban yana wasa da yatsunsa cikin
junansu, kamar yana jin kunyar kansa da
maganganun dake fitowa ta bakinsa cikin tilas.
"Ki yi hakuri kamar na cika ki da surutu ko?
In kina da abin da za ki gaya min kowane iri ne
ban damu ba"
Farida wadda ta jima tana kallon sa da karantarsa ta kidime cikin sanyin jiki ta rasa
81 Mafiyan Masoya Rahma Abdul Majid
abin da zata ce. Lallai bata ji wani zauki a
wannan dingimemiyar soyayya da bata da gurbi
a zuciyarta ba, hasali ma hirar ta dan ginshe ta
saboda kewar masoyinta, ji take tamkar yana
misalta mata soyayyarsu ne ita da Ibrahim,
amma gaskiyar da ba zata iya kaucewa ba ita се
yana matukar son ta. Ba a bakinsa kawai ba, ta
karanci matukar soyayya a idonsa, da
yanayinsa. Yayi kama da maza masu fadawa
tarkon soyayya mai tsanani kuma su yi shahada
a gare ta.
Ta fan kawar da kai gefe tana kada kafarta.
"Kayi hakuri AbdulAzeez, na ji duk
maganar ka, kuma duk wani hasashe da kayi
akaina haka yake, ina...ina son wani, amma ina
da matsala da su Father kan hakan. Ina cikin
wannan tukuna, amma...ba zan yi maka
alkawarin wani abu ba duk da ba zan hana ka
abin da kake neman alfarma ba"
Ta dawo da idanunta gare shi inda ta samu
yana kallon ta cikin neman dauriya a karaya, ya
sake sunkuyar da ido yana matsa yatsunsa.
"It's ok, zan yi hakuri zan yi godiya ga duk
yadda kika tare ni, sai dai ki sani, zan ji dadi
idan kika sanya ni a duk wani service din ki da
zan iya... ina son hakan tun daga karkashin
zuciyata"
Da wannan suka kawo karshen zancen su
suka tashi daga wannan wuri da kamar yanzu
sun gane bai kamace su ba suka koma cikin
yama.
82 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Farida ta is0 gida a gajiye bata manne jikin
mijinta kamar Yadda ta saba ba, bayan da suka
sunbaci juna kawai sai ta hau kujera ta zauna ta
rike kanta na gajiya, shi kuwa ya doshi
ma`ajiyar kayan sha ya soma hado mata mai
zafi.
"Yaya ganawar taku ta kasance?"
"Mun yi mun gama kuma mun fahimci
yadda zamu fahimta"
Yayi dariya.
"Yaya kika ga candidate din na Father?"
Ta dan lumshe ido na gajiya.
"Man! He is in love.... Yana cikin soyayya
da gaske, kuma abin da tausayi, abin sha`awar
shine yana da irin saukin kan da ba zan sami
matsala da yana so na ba koda kuwa bai dena so
na ba, ba shi da irin zukatan `ya'yan manyan
Africa da suke jin duk abin da suka so sai sun
samu, jininsa da rainonsa na farar fata yana
masa aiki.... Banbancinku shine in da shine kai,
da tuni an yi abin da na so mu yi don mu gama
da su baba...bai da zafin ra'ayi da akida irin
taka, bambanci na biyu shine ba ni da takin son
sa kamar yadda ba ni da takin kin ka”
Bata san ya bar falon ba sai da ta ji karar
sakin ruwa nesa da su. Ta bude ido ta ga baya
nan. Ta san kwanar zancen a guje ta mike ta
zubar da gajiya ta fada neman sa tana kiran
'Belly...ina kake baby'
A gidan wanka ta same shi ya saki shayar
zafi kansa ba tare da ya cire singileti da gajeren
83 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
wando ba. Ta fada ciki itama ba tare da ta cire
kaya ba. Ibrahim wanda yake jingine ruwa na
zuba akansa kamar yadda hawaye ke zuba a
idonsa bai kalle ta ba. Ta iso gare shi a tsorace
ta ja kafaďunsa ta girgiza.
"Ibrahim me ya faru?"
Ya dan dube ta.
"Na zaci haka zata faru, na zaci rana irinta
yau zata zo... Farida zan rasa ki a lokacinda na
fi bukatarki a rayuwata, yaya aka yi na kasa
daurewa shi ne takaicina”
A rikice take don bata san abin da ya faru ba
da ba don haka ba ita ma da ta fashe da kuka.
"Me ya faru da zai sanya ka rasa ni?"
"Har zaki tambaye ni? Me kike ji a zuciyar
ki kan saurayin da kika je kiką hadu da shi...
kin fara hangen dacewarsa fiye da ni... yana son
ki ya fi ni saukin kai, ya fi ni mika miki
wuya...Farida akwai mika wuyar da ya wuce
rabuwa da iyayenmu da dukiyoyinmu domin mu
yi hijira da soyayyar mu?"
Tunda ya fara magana kada kai take na nuna
rashin fahimta, amma da ta ga ta kasa samin
hankalinsa sai zuba yake yana kara kuka ita ma
sai ta shige jikinsa tana kukan.
"Ban nufi haka ba, ban taba nufin haka ba...
ka yi hakuri, kai ne rayuwata kai ne dadina kai
ne dacina yaya zan yi na hada ka da wani, ina yi
maka bayanin abin da na karanta ne ban san zai
yi maka ciwo ba. Am so sorry. I love you...i
love you"
84 Mafiyan Masoyа Rahma AbdulMajid
Suka rike juna kam suna kuka ruwan zafi na
dimarsu a baya
*
Mahdi ya shigo falon inda Farid ke zaune
yana sauraron bugun sauti a rukodar falon da ya
tilasta mata juya baitukan tsohon mawaki
Micheal Bolton wanda yake fadin halinda na
miji ke shiga yayinda yake soyayya a cikin
wakarsa ta 'When a man loves a woman'. Ya
jefe shi da wata jaka mai tambarin Zain yayi
sauri ya cafe bai ce masa wani abu kan jakar
nan ba ya ajiye ta gefe.
"Oboy! Ina nan karban gaskiyar lamari daga
hannun Boltin"
Ya ja tsaki ya sami kujerar bangaren cin
abinci ya zauna ya dauki wata tuffaha dake
cikin wani tangaran na ajiyar kayan lambu dake
kan teburin ya gatsa.
"Kai ya dama.. baka damu ka duba me na
kawo maka ba ballantana ka gode"
Da sauri ya dauko jakar ya bude yana fadin
'oh yi hakuri na tafi ne'
"Za ma ka dawo"
Ya bude jakar mai dauke da kan waya
samfurin Blackberry. Ya taso da sauri ya nufo
shi.
"Wa ka kawo wa wannan?"
"Idan baka so ajiye min, kai kace kana son
sayen blackberry baka da lokaci, shine na ga
yau a na promo a kamfanin mu na ma`aikata na
karbo maka tun da ni ina da ita"
85 Mafiyan Masoyа Rahma AbdulMajid
Ya rungumo shi ta baya yana duba wayar.
"Bold 2 fa! Kai Allah na gode da irin
wannan shegen aboki da ka ba ni... saura na
kawai na sami Farida na kara shi kenan kun ishe
ni zaman duniya"
Mahdi bai da zabi ban da fashewa da dariya.
"Yanzu me nene na Farida a wannan
lamarin?"
Farid ya koma kujerarsa da sauri domin ya
ba shi labari.
"Yau na samu nayi magana da mutuniyar
wallAhi don murna barin ofis nayi na kasa aiki.
Mad nayi magana da ita! Ka san way a hada
mu? Chairman da kansa. Ina zaune a ofis ya kira
ni muna wasu tattaunawa kawai sai ga wayarta.
Bayan sun gama magana sai yace mata ga
na'ibinta nan su yi magana. WallAhi tayi min
kalmomi masu dadi...ban da sakewa da na ji a
muryarta sai kuma kalmomin yaba min cewa ta
ji an ce ina aiki kamar agogo, na dauke duk
hankalin ofishin, ta gode min da ban bata kunya
ba kuma tayi alkawarin zuwa min da
tsaraba....Kai Mad ina cikin sunan ka yau mad,
amma na jin dadi"
Mahdi wanda yake masa kallon haushi ya
kasa tanka shi har ya gama.
"Toh yanzu me nene na dadi a ciki, na zaci
cewa tayi tana son ka ko tana kewar ka...kawai
don me gidanka ta ce ka kyauta a aikin da ta
sanya ka sai mc? Farid ban san ka da son
mutane don dukiyarsu ba, amma gaskiyar
86 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
lamari dukiyar Chairman din ka ta ruda
ka...dukiya ce kawai zaka so ka mallaka da zai
sanya ka haukace haka ba wata mace ba. Haba
Farid kada ka fadi ba nauyi mana"
Ya ja tsaki ya dora kafarsa daya bisa
hannun kujerar.
"Matsala ta daya da kai wauta irin ta
asalinku `yan fari... Yanzu Farida ita kadai ba
Material bace da za a haukacewa sai an hada da
wani kudi? Baka fa taba ganin Faridar da nake
fadi ba duk ka bi ka ishe ni. Macen da ta ishi
kanta da bata bukatar agazawar komai hali ko jiki kafin a so ta ita ce Farida. Idan da za a
kwace duk abin da na mallaka da wanda zan
mallaka a musanya min shi da Farida na yarda
na wanye rayuwata daga ni sai wando sai
singilet sai abin da zan faranta mata rai"
Mahdi ya tashi a gajiye yana dariya.
"Ai baka hadu ba tunda kace a bar ka da
wando da cewa zaka yi daga kai sai Farida..."
Suka kwashe da dariya inda Mahdi ya shige
da ragowar tasa ya bar Farid nan ya koma fagen
tunani.
*
Abdul Aziz ba kamar kullun ba yana ta
asarar kwallon da ya saba ci a duk lokacinda
suke wasa da mahaifinsa na kwallon sanda. Har
dai mahaifin ya ankara sannan ya tsaida sandar
ya dogara da ita sannan ya kalli dan nasa.
87 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Yaya kuka yi da Farida? Sai ce min kake
komai daidai amma ban san me nene dai dai ba,
ban ga daidai a dabi'arka ba"
Ya kalli sama kamar me neman daukin
mala`iku kafin yayi magana.
"babu komai kawai dai tana soyayya da
wani, ke nan ba zata so ni ba"
"To me nene sabo. Dama ba mahaifinta yace
tana son wani kuma yana kokarin raba su ba?"
Ya juyo ga mahaifinsa cikin murmushin
takaici.
"Ba da wannan saukin ake raba so ba
Abbana... da a na dena so cikin sauki ka san da
ni na fara rabuwa da Farida tun kafin na san ta
don kada na ji kunya a ce ina son yariya a
jarida.Na ga matukar soyayya tattare da Farida
wadda ita da kanta tana shan wuya kafin ta sami
dadinta. Farida bata rabu da wanda take so ba
don ba tace min ba bata kuma nuna hakan na da
sauki ba..."
"Kana jin akwai bukatar ka daure ka manta
da ita ke nan?"
"Abin da nake da tabbacin ba zan iya ba
kenan...ba kawai yadda mace ke shiga zuciyar
namiji Farida ta shiga zuciyata ba, kamar ma ba
hanyar ta bi ba ma dungum... na dai tabbatar da
cewa ba zan same ta ba, ba rayuwar kauye
muke ba ballantana a yi maganar auren dole.
Farida ta riga ta so wanina, amma fa duk da
haka zan kasance ne tare da ita koda ba don
zaton wata rana zata so ni ba, amma don tsoron
88 Mafiyan
kada na sake maimaita ranakun da nayi bana
ganin ta bana jin ta na rungumi kaddara na
ganin ta koda daga nesa ne"
"Kada ka zame min shahsa Abdulaziz! Idan
na dauki ciwon son ka kafin ka san Farida
yanzu kuma ba zan gane son ta da yi mata bauta
tana son waninka ba, haba sai kace ba na miji
ba, wane galahangar ne a duniya zai yi haka ban
da kai. Ka shigo gidan nan ka gaya min ka
manta da yarinyar nan shine wajibinka kuma
cikin gaugawa"
Ya saki sandar ya shige ciki da sauri cikin
haushi inda ya bar Abdulaziz na yi masa kallon
jahili al`amarin da yake magana.
Ibrahim na kwance yana baccinsa, hanunsa
kan filon da Farida ta dora bayan da ta zare
jikinta daga shi. Tana tsaye a bayangidan tana
jiran dakikun gwajin fitsarin da take ya cika
cikin zumudi da doki. Ta cire tsinken daga 'yar
robar fitsarin bayan da lokacin yin hakan yayi ta
duba da zarwar ido. Alama ta fito mai nuna
cewa lallai ciki ya shiga jikinta. Bata tsaya 6ata
lokaci ba ta saki wata kururuwa wadda sai da ta
wuntsilar da Ibrahim daga kan gadon zuwa
Kasa. Ya fado bayan gidan ya rike ta a tsorace.
"Belly mun yi nasara! Yes we made it!"
Ya san kwanan zancen don haka kawai
kwace dan tsinken gwajin yayi duk da bai san
ina alamar cikin take ba.
"Ina alama kin tabbatar?"
89 Mafiyan Masoya Rahma Abdul.Majid
Tuni fuskarsa ta fara bayyana murmushi da
ta nuna masa sai kawai yayi wo cikin daki da
tsinken tamkar a cikin tsinken cikin yake. Ya na
dubawa yana hajijiya. Can sai ya tsinci kansa ya
kai wa Allah sujjada yana fadin 'na gode
ubangijina' Ta iso gare shi ita ma ta durkusa ta
kai sujjadar tana dawowa ya ruko ta yana duba
ta sama da kasa har ya kai ga cikinta inda ya
tsaya yana raba ido akai.
'Farida? akwai dana a cikin nan?"
Ya rungume ta yana zubar da hawaye
"Yanzu lokacin komawa mu fuskanci gida
yayi ke nan?"
*
Salma wadda take cikin shiga irinta kasar su
Eritirya wato laffaya koriya mai zanen fari babu
abin da ya raba ta da Farida baya da tsawo da
Faridar ta fita sai `yar alamar dake bambance
tsufa da kuruciya. Ta iso falon kunshe a kafadar
mijinta Na'ibi Mansur sannan ta wuce wata
kujera ta jefar da Jakarta sannan ta bi ta a
yayinda shi kuma ya wuce kantar tattara ababen
sha ya tsiyayo mata wani maganin gajiya ya iso
gabanta yana mika mata.
"Welcome home sweetie"
Ta dan yi ajiyar zuciya sannan fari da ido
kana ta janyo hannunsa ya fado kujerar shi ma.
"Na yi kewar ka da duk gidan nan na
mu...Na yi kewar 'ya' ya na"
Ya kwashe da dariyar da bai saba yin irinta
ba.
90 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Salma ke nan, ba ki yi kewar kowa ba don
zuciyarki bata kewa, ki bar dai zancen a sannu
da zuwan da na yi miki"
Ta dan bata rai.
"Me yasa kullun kake yawan tuhuma ta da
ban damu da ku ba ne? bana son haka Mansur"
Ya dan kashingida can kusa da kafadarta.
"Ba karya nake yi miki ba. Salma in har kin
yi kewar mu me nene zai hana ki zuwa ki gan
mu? Wane aiki kike da ya zamo wajibi sai kin
nisanci iyalinki ban da dai haka kika zaba.
Farida tayi fama da matsalolin zuciya kan
soyayyarta da dan Hadi, na kuma gaya miki,
amma ko wannan bai isa ya sanya ki zo ki ga
`yarki ko ki je can Germany tun da kuna kusa ki
duba ta ba? Ko kadan aikin kula da yara da
bukatunsu nawa ne, to na dauka, yanzu ma na
san akwai abin da ya kawo ki kasar nan, amma
ba don kewar mu ba, don haka ina yi miki sannu
da zuwa”
"Ka ba ni nan da shekara daya na kulla
muradina, na zamo shugabar kungiyar mata
masu tattali da tsafta ta duniya, ina tabbatar
maka da cewa daga lokacin sai kun gaji da ni,
duk aikin da kayi zan biya ka zan baka lokacina
fiye da duk ilahirin zaman mu"
Ya kalli ilahirin fuskarta sannan ya sa hanna
ya kamo wani yanki na dogon gashinta dake
sauka gadon baya ya shinshina sannan ya rike.
"Yaushe? Sai wannan ya zamo audiga ya
kade ya tsufa, fuskokin mu sun tamuje kafin na
91 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
sami lokacin ki? Me kike so yanzu da wannan
zuwan?"
Ta kwanto jikinsa.
"So nake mu kwana biyu ni da kai muna
morewa sannan rana ta uku sai ka raka ni mu je
kasar Moroco inda muke da taron tsayar da dan
takara, kowa zai zo da nasa mijin ko abokin
zama
Yayi dariya sannan ya ce 'uhum..'
"Wato idan dai na gane zaki ba ni cin hanci
na kwana biyu sai mu je na biya ki aikin ki ko a
zuwa taro"
"Ba fa haka na ce ba. Zamu je taro amma
kuma na zo na zauna da kai mana"
"ko ma yaya kika sanya ba zai sake yi min
zafi ba, sai dai kada ki manta Farida zata dawo a
ranar da kike so mu je taro, don haka sai ta
sauka mun gan ta kafin a wuce in yayi miki to
in bai yi miki ba sai ki je ke kadai"
"Yayi min mana, ai ni ma ina son ganin
yata, idan ta zo da wuri sai mu tashi daddare
ko?"
Ya mike tsaye ya ciccibe ta.
"Mu je ki fara biyan zama da ni tunda kin
amince. Ba zancen gajiyar tafiya don ba a jaki
kika zo ba"
*
Ibrahim na kamala ajiye jakarsa ya zauna
kujerarsa ya zaro waya, Farida ya kira suke ta
hira har zuwa lokacinda jirgi ya soma ninkayan
tashi sannan suka yi sallama cikin kewa.
92 Mafiyan Masoya Rahma Abdul Majid
"Kada ka damu ina tare da kai. Ka gama
sasantawa da shi sannan jibi mu sake haduwa
ko?"
Kalmar karshe da ta karanto masa ke nan da
ta fahimci dimbin damuwa a muryarsa, sannan
ta sumabci wayar ya mayar mata sannan ya
kashe tasa. Jirgi ya tashi ya bar Ibrahim cikin
tunani mai dagula kwakwalwa, zaton Farida na
cewa damuwarsa ita ce rabuwarsu da kuma
yadda zai fuskanci babansa ya samo asali ne kan
yadda suka kulla yarjejeniyar shi zai fara zuwa
ya shawo kan mahaifinsa don da ta isa ta wuce
wurinsa su tafi tare dukansu uku ga mahaifinta a
sasanta. Amma ainahin damuwarsa ta karkata
ne kan wani sirri da ita Farida bata san da shi ba
kuma tsoron yadda zata kaile shi ne ya hana shi
gaya mata. Wannan sirri ba na komai ba ne sai
na zuwansa ya auri Faridar a 6oye. Ibrahim
wanda mahaifinsa ke zaton ya ta`allaka ne da
sha`awar Farida ba son ta ba yayi masa tayin
daukan nauyin tafiyarsa a boye zuwa ga Faridar
wadda leken asirinsu ya tabbatar masa ta doshi
hanyar Jamus, inda suka kulla yarjejeniyar zai
dauki nauyi ya kuma kawar da kai daga yaudara
da more rayuwa da Ibrahim zai yi da Farida ba
tare da aure ba ko da kuwa hakan zata nuna
cewa ya gudo ne babu yardar mahaifin nasa,
kuma in so samu ne yayi mata ciki su yi hotuna
na samar da tabbacin hakan sannan in ya koshi
ya baro ta ya dawo ya bar wa mahaifinsa sauran
aikin da ya ke ganin yayi wannan sadaukarwa
93 Mafiyan Masoyà Rahma AbdulMajid
dominsa wato karya lagon Na ibi da wannan
wulakanci a kan 'yarsa da tanyara ta a duniya a
matsayin karyar su shi da dansa. Duk da
lokacinda baban Ibrahim ke ba shi wannan
shawara ya kufula matuka ya kuma ga wallen
uban nasa, ya daure ya amince da wannan tayi
bayan kwana daya tak ba don komai ba sai don
ya isa ga Faridar dake shirin kubuce wa
rayuwarsa, a yayinda mahaifin nasa ya
kanjamar da asusun sa na kudi don kada ya iya
yin wani motsi na radin kansa, sai dai a
zuciyarsa ya kudiri niyar auren Farida da niyar
zama da ita har iya rayuwarsa, kuma in suka
sami karuwa zai zo ya gaya wa mahaifin nasa
cewa bai yi aikinsa ba. Yanzu dai abin da ya
kama hanyar zuwa Najeriya yi ke nan, kuma ba
wani abu ne ke damun sa ba illa yadda zasu kai
ruwa rana shi da mahaifinsa kafin su yarda da
kaddara, watakila ma su rabu, amma in so samu
ne yana son su gama wannan abu gaba daya
Farida bata san wancan sirrin ba koda kuwa sun
rabu da mahaifinsa ko suna tare. Wannan lamari
ne ya zame masa abokin hira har ya iso Najeriya
ya kuma shiga motar da mahaifin nasa ke
tukawa zuwa gida suna hirar jin dadi suna
tafawa.
A tsakiyar babban falon nan dai da babu
komai sai shinfidun darduma da jefi-jefin
kujeru, AbdulHadi ya zubo wa dansa lemo shi
ma ya zuba nasa sannan suka soma kai komo
suna sha.
94 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Na ga kana cikin damuwa, na san za a y
haka, rabuwa da kyakkyawar yarinya irin Farida
wadda aka zauna da ita fiyc da wata biyu ba
Karamin lamari bane. Amma ka yi hakuri tunda
ka yi min aiki na yadda ya kamata na yi
alkawarin zan yi amfani da ko da duk dukiya ta
ne na samar maka wadda ta fi ta"
Ya fadı yana dafe da kafadar Ibrahim yana
dariya bayan da suka kurbi lemon tare.
"Daga yau tsalle-tsallen da Na'ibi ke min ya
kare, zan tozarta shi da `yarsa...Haaaahaaa!
Sauri nake gobe tayi mu fara aiki....Dana ka
haifu kuma ka goge min bakin cikin rashin
yawanku"
Ibrahim ya sunkuyar da kai sannan ya fara
magana.
"Dady ka yi hakuri ban yi aikin nan yadda
ka sanya ni ba.."
Ya dago ido suka kalli juna shi da
mahaifinsa wanda ya dauke wuta, sannan ya ci
gaba da magana.
"Na je Jamus yadda muka tsara kuma na ji
dadın zamana da Farida, sai dai a matsayin miji
da mata ba wai kawai wata mistress ba. Na auri
Farida bisa sunna ne da kuma shaidar Kotu.
Sannan a halin yanzu tana da ciki na dan da
nake son ya soma zama dana na fari a
rayuwata...sabanin yadda ka ce Dady ka yafe
min. Farida son ta nake ba sha'awarta ba, don
haka baba in akwai abin da zaka yi wa Baban
Farida ya ji haushi shine ka karbi 'yarsa a
95 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
matsayin matar danka, ka rungume mu, Farida
shirye take ta amshe ka a matsayin uba muddin
mahaifinta ya ki ba mu hadin kai kuma..."
"Ya isa bari na ji magana"
Ya ko yi tsit a yayinda AbdulHadi ke nuna
shi da yatsa cikin mamaki.
"Ka auri Farida ka се?"
"Eh baba! Kuma tana dauke da jikanka na
fari"
"Ke nan ba yadda na ce