a
duk fadin duniya haushin da kamar ya fi
dalilansa na jin haushi yawa. Dansandan ya
kawar da wannan yanayi da tambayar wannana
baiwar Allah mai tsaye tana wasa da mukullin
mota kusa da makalalliyar Jakarta dake kusa da
hammata.
"Ke ce kika kade Mr Gebriel da mota?"
"Ni ce na kade shi'
Ta amsa da karfin gwiwa har yanzu bata
kalli mai satar kallon ta cikin rudani ba wato
Farid.
"Wace ce ke malama?"
"Suna na Farida Na`ibi Bici"
Sunan ya girgiza duk wanda yake wurin ban
da Farid wanda ya san kowacece, abin mamakin
da yake jira shine makircin da ya kawo Farida.
Amma dansanda mai rubutu da mai sauraro duk
sun bar aikinsu sun nuna nitsuwa.
"Amma ranki ya dade yaya a kayi da kika
buge shi baki tsaya ba?"
38 Mafiyen Mosoye Rahma AbdulMajid
A yanzu ta dora idanunta kur kan Farid, duk
da bata kalle shi sama da kasa ba, amma
yanayin kallon na nuna raina shi tayi.
"Ina da wasu matsaloli ne da suka sha kai na
shiyasa har na bige shi ban sani ba, bayan na
bige shi na ji tsoron tsayawa saboda rashin
hankalin `yan-zauna gari-banza da zasu iya
daukan hukumci a hannunsu basa barin wa
Allah ballantana hukuma"
Da alamar da irinsa take shiyasa ta sanya ido
kansa tamkar da shi take magana.
"Shin ranki ya dade kin san ma'anar bige
mutum da laifin hakan a idon hukuma
musamman bayan ka gudu?"
"Na sani koma yaya ne laifi ne, amma kun
san zan iya kaucewa ba tare da wani hukumci
ba, amma na kawo kaina a yi min hukumcin da
ya dace da laifina, muddin hakan zai iya bai wa
mai raunin lafiya, domin ban san yana jin jiki ba
sai a jarida na gani. Na shirya daukan nauyin
duk abin da zai kawo masa lafiya, don haka ne
na kawo kai na gare ku don a sada ni da
lafiyarsa"
Dansanda mai rubutu ya kalli Farid.
"kai kuma aikin ka ya kare sai ka bar wurin
nan"
Farid cikin rikita, raunin jiki da sanyin
gwiwa ya juya ya bar wurin inda a cikin
zuciyarsa ya ji yace da Farida na bar ki lafiya
amma Kalmar bata fito ba.
A
2
39 Maliyan Masoya Rahma AbdulMajid A kofar dakin Gabriel babu kowa sai wasu
kabilun sa da basu jin turanci da karamar 'yarsa
wadda take jin turanci amma bata da isasshen
bayanai. Ya tambaya ko yaya me jiki yarinyar ta
amsa masa da cewa an ce su fito ana yi masa
wasu gwaje-gwaje, sannan ta ji ana cewa za a
wuce da shi asibitin kashi idan kudi ya zo. Ya
tsaya yana nuna tausayawarsa sannan ya ke
cewa yana sauri zai koma. Basu yi aune ba sai
ga wadda ya gudo biye da shi. Farida ce cikin
rakiyar `yansanda sai dai da alamar ba kamata
sukayi ba tsaron lafiyarta suke. Ta iso ga kofar
dakin har zata tambaya ko nan ne amma da ta
ga Farid sai ta ji babu bukatar tambaya. Duka
mutanen suka dan dare na tsoro suna gaishe ta,
bata bata lokaci ba ta wuce ga yarinyar cikinsu
wadda da alamar ita ta fi damuwa don har yanzu
shasshakar kuka take. Farida ta sunkuyo gare ta.
"Yarinya wace ce ke?"
Ta amsa cikin kallon idon Farida.
"ni ce 'yar Gabriel da mota ta kade min
babana"
Sai da Farida tayi ajiyar zuciya ta kada kai
sannan ta daure ta dan yi fari da ido.
"Ki yi hakuri da ni nice na kade baba da
"mota יי
Bata rufe baki ba sai ta ji mari daga hannun
yarinyar nan wadda bata tsaya nan ba ta kai
mata cakuma tana ihun fadin 'ke ce zaki kashe
min baba?' wani dansanda ya zakudo don
kwace ta daga hannun yarinyar amma da sauri
a1
40 Mofiyan Masoyа Rahma Abdul Majid
Farida ta kada masa kai ya tsaya, hakan ya
sanya yarinyar wadda da alamar makwabinta
daya tilo baya wurin tana abin da ta ga dama
don haka babu wanda yace mata kanzil sai da ta
tsaya da kanta tana Kara shasshaka. Da
tsayawarta Farida ta yi kasa ta durkusa a
gabanta ta ruko hannayenta tana kallon ta cikin
ido sannan ta soma magana cikin nuna tausayi
da taushin murya cikin turancinta na bakin
kasar waje.
"ki yi hakuri ba so na ne na taba kade dan
adam ba, tsautsayi ne ya faru, babban kuskure
na shine kasa samin kwarin gwiwar tsayawa da
nayi domin na fuskanci kuskurena, amma ki
yarda da ni duk yadda kuke jin zafi haka na ke
ji, zuciyata bata huta ba cikin kwanakin nan
biyu har sai da na miko kai na ga hukuma. Ki
sani na shirya yin duk abin da zan iya na ganin
mahaifinki ya sami lafiya, koda hakan na nufin
duka karfina ya kare, zan kula da shi zan kula
dake kin ji ki yafe min"
Yarinyar ta kura mata ido cikin sanyin jiki
har zuwa lokacinda Farida ta shafi kanta sannan
ta sake ware ido ta tambaye ta 'kin yafe min
kawata?' bata da zabi baya da samin kanta yana
gyadawa na nuna yarda. Mikewar Farida ya zo
daidai da lokacînda wata mata ta bayyana tana
ambaton ina muguwar take, ku nuna min ita
cikin lankwasasshen turanci.daure take da zani
biyu kan wata rigar leshi fari maras isashen
hannu, ta ci dauri da gwaggwaro kalar zaninta
C
2
41 Mallyan Masoya Rahma AbdulMajid
bulu mai kyalli-kyalli, ta rame ta koke, ban da
fata da jijiya babu komai da ya rage mata sai
tsawo. Ramar ta hana a tantance halin da
fuskarta ke ciki na muni ko kyau, watakila haka
take watakila kuma rashin isar abinci ce. Da
sauri ta shigo ta sha gaban Farida wadda take
tsaye a yanzu da niyar shiga dakin me jinya.
amma ta tsaya da ta ji hayaniya. Matar nan ta
dubi saura da suke tsaye tana tsalle da jikinta
kamar mai shirin shiga filin kokuwa.
"Me kuke jira kallon ta kuke? Ba itace ta ke
son kashe dan uwana ba? Don kina da kudi? To
yau zan nuna miki cewa talaka ma ba a bar shi a
baya ba. Abin da kika yi wa kani na sai an yi
miki a yau. Duka mu je ba lafiya. Ki sa hukuma
ta kashe mu
Sauran suka yi wo kan Farida wadda ke
kallon abin mamaki, amma kafin jami'an tsaro
su yi aikinsu, tuni Farid ya yiwo gaba ya kare ta
sannan ya daka tsawa.
"Ya isa!"
Duka suka tsaya kamar masu bin umarnin
Allah. Shi kuwa yana ta hucin fushi yana kallon
su daidai ko akwai mai shirin bijirewa.
"Na dana sani yi da jin kunyar kai na na
zamowa na daya daga cikinku. Cikinku
talakawan da sau tari masu kudi na zargin cewa
kuna jin haushin su ba don wani dalili ba sai
don baiwar da Allah Yayi musu. Lallai yau kun
tabbatar haka muke. Na san da talaka ne yayi
abin da wannan baiwar Allah tayi muddin ya zo
42 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
mana da uziri zamu tsaya mu saurare shi, amma
dubi abin da kuke shirin yi wa wata mace don
kawai tana da kudi. Don ta kawo kanta gare ku
da neman gafara da shirin daukan nauyin
laifinta, kun manta da cewa tana da karfin cewa
itace kuma ba zata yi komai ba ta kwana lafiya.
Tana da hujjar cewa ba ita bace kuma babu me
hujjar cewa lallai itace. Amma duk da haka ta
kaskantar da kanta ta zo muku daga ita sai ita ta
hana shigar jami`an tsaro tsakanin ku da ita, ta
baku hakuri, wannan bai ishe ku girmamawa ku
yafe mata ba? Idan bai ishe ku ba ku sani zan
janye daga duk wani kokari da kuka san ni
kadai nake muku zan juya baya don na zo
tabbatar da an yi gaskiya ne ga wanda ya
cancanta, amma idan kuka nuna min baku
cancanta ba zan nuna muku tawa iyawar, nine
shaidar da zata samo muku hakkinku ko ku rasa
to zaku rasa din kuwa"
Duka suka sunkuyar da kai kamar wadanda
ruwa ya ci, wani da ya iso gaban kofar dakin
mai jinya don hana ta shiga ya kauce a hankali,
a yayinda Farid ya juyo ga Farida cikin sanyin
murya ya nuna mata kofar dakin domin ta shiga
, ta gyada kai tana murmushin mamaki sannan
ta shiga.
Kafar Gebriel wadda ta cakude ita ta fara
sanya ta tashin tsigar jiki har da hawaye, dakyar
ta karasa kusa da shi, sannan cikin kada kai
tace.
5
43 Maflyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Haka nayi da kai? Wai ni nayi haka da
kai?"
Ya dan lumshe ido.
"Yata na yafe miki,ba zaki taba yin hakan
da saninki ba, na kuma ji duk abin da mutane na
suke yi miki a waje, na ji kokarin da dan uwana
dan Najeriya yayi domin ya kare ki ya sanar da
su gaskiya. Ki yi hakuri da su fishi ne na ganin
halinda jininsu yake ciki, ki yafe wa 'yata mai
marin ki, tsoro ya sanya ta, don bata da kowa sai
ni...ni kuma na yafe miki Allah Ya kiyaye mu
duka a gaba"
Babu abin da take nanatawa ban da Kalmar
'Am so sorry'
Mutanen na waje cirko-cirko har ta fito ita
da Farid a lokacin da alamar wani kakkarfan
direbanta da aikinsa na iya fin na direba zuwa
na mai tsaron lafiya ya karu a ketaren, ta kalli
mutanen daya bayan daya a yanzu bata ce da su
komai ba baya da yarinyar da ta sunkuya ta
sunbata a goshi sannan ta ce mata 'sai na sake
zuwa ko?' 'bye aunty' ita ma ta mayar mata. Та
dubi Farid sannan tace masa 'walk with me'
wato biyo ni. Farid ya ji nauyi kamar ba shi ne
mai jin haushin Farida ba ya ji ba shi da dalilin
kasa bin umarninta.
Ta karbi mukullin motar daga hannun katon
nan tayi masa umarnin shige wa kujerar baya,
sannan ta yi wa Farid umarnin shiga gaba da kai
a yayinda ita kuma ta shiga wurin tuki. Tuni
motar ta dumama kanta iyaka Farida ta ja
25 Mefiyon Masoya Rahma AbdulMajid
zungureriyar motar da in banda kallon wuce
gine-gine baka sanin tana tafiya. Komai a motar
fari ne kamar akwatin gawa, akwai kofa a
cikinta da ta raba matuki da mai gidansa na
baya, kenan wanda Farida ta tura baya ba
ruwansa da su sai an neme shi.
tuki.
"Me sunanka?"
Ta tambayi Farid ba tare da ta kalle shi ba.
"Farid Akil"
Sai yanzu ta dube shi sannan ta koma ga
"Waw! Sunan mu kusan daya"
Ta yi wani murmushi da gefen kumatu daya
da ya lotsa kwalamar kumatun nata da yayi
matukar sanyaya wa Farid koda bai tantance
dalili ba.
"Dama ka san ni na kade shi ne?"
"Na sani kuma har na gaya wa babanki cewa
yayi wani abu don na sani
Da alamar yana maganar ne yanzu da jin a
na son a yi masa `yansandan ciki
"Oh! Kai ne wanda baba yace ya san ni na
yi wannan aikin?"
Tayi dariya sannan ta sha kwana.
"Believe me, ba don gargadin ka ne na fito
ba, na jima abin yana damuna, amma duk
wadanda na turo su yi wani abu ba su yi ba shi
yasa na zo da kaina, amma da yadda na tafi in
na so tafiya na tafi kenan"
"Na sani ai"
Shi ma ya amsa daga kokon zuciyarsa.
45 Mallyan Masoya
"Wane aiki kake?"
Rahma AbdulMajid
"Ban sami aiki ba tukuna"
Ta dube shi da mamaki.
"Me ka karanta ne da baka sami aiki ba?"
"Na karanta Computer science ne"
"Da kyau! amma me ya hana ka samun aiki
da wannan karatu me tsada?"
"Na ci jarabawa ne da yawa shi ne
ma'aikata suke jin na yi musu tsada"
Ta sake yin dariya da kyau. Basu dade ba
suka iso ofishin nan da ya zo satin da ya shige.
A babban falon yau ba kamar ranar
shigowarsa ta farko ba domin kowa ya mike ya
bayar da hankalinsa ga Farida. Ta isa ga wata
doguwa kamar ta wadda ke cikin shigar sut da
siket bakake kalar karin gashin da ta zuba wa
kitso a kanta.
"Akwai wani ofis da babu ma`aikaci?"
Ta kada kai.
"No ma'm"
Ta kada kai ta wuce da sauri sashin gabas
inda take cewa 'sai nawa ofis din ne babu
kowa'
Ta tura kofa, faffadan ofishin ya bude mai
matukar haske komai fari da ruwan milki.
Akwai sashin karban baki akwai na aikin ofis, a
teburinta akwai sunan ta da aka adana da ruwan
gwal a wasu abubuwan aikinta kamar su gidan
biro da akwatin takardu. Ta nuna masa kujera
ya zauna sannan ta doshi teburinta. Ga
mamakinsa sai ya ga ta kwashe duk wani abu da
46 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
aka rubuta sunanta ta doshi wata `yar kwaba ta
watsa su ta rufe sannan ta dawo gare shi bayan
ta danna wata lamba a waya.
"Za ka rike min wannan ofishin daga sati
me kamawa har na dawo, kafin nan na samo
maka wurin aikin da ya dace"
Ya ji ya rikice yana kallon fadin wurin babu
kakkaftawa, wai da gaske ne ko a mafarki,
ofishin Farida...ko ma dai wasa take? Bai taba
raya wa kansa aiki a irin wannan wuri ba
"Farida me kike nufin..."
Mahaifinta wanda ya bankado kofa ya fado
ofishin cikin yanayinsa na sirara masu haiba.
Yau kuma da wata T shirt mai sunan
kamfaninsa fara da malafa irin T. shirt din, da
alamar wani abu zasu yi da ya shafi sanya
wannan kaya. A masifance yake don haka har
tunanin Farid ya tsayar wanda in ban da dauriya
wannan mutum na ba shi tsoro. Har yanzu bai
kalli inda Farid din yake ba ba kuma don bayа
son kallon ba sai don abin da ya kawo shi ya
shafe masa ido.
"Wata matsala ce Father?"
"Da kin je wadan nan mutanen dajin sun
miki wani abu zaki gane me nake nufi...ba sai
da nace kada ki yi komai kan mutumin nan ba ni
zan dauki mataki nace ki je Burge, ina zaton
kina can ashe ke kina can wurin shashanci"
Ta dan yi murmushi sannan ta zagayo zuwa
gabansa.
Rahma AbdulMa jid 47 Matiyan Masoya
"To ai ga shi na hutashshe ka Father. Na je
na karar da komai da kaina, kuma gobe zan yi
tafiyar, yanzu ba sai ka yi komai ba. Mutumin
na karkashin kulawarmu na wakilta masu yin
komai a kan lafiyarsa..."
Rawar dari zuciyar Farid take yayinda kafin
Farida ta gama magana idanun mahaifinta sun
hau kan sa kuma sun tsaya a can.
"Me wannan yake a wurinki, kada shi ya kai
ki ga yin wannan wautar?"
"Sam! Shi na kawo shi ne a matsayin sabon
networker din ku kafin na dawo daga tafiya ta"
"What! You must be out of your mind!"
Ya nuna Farid da hannu.
"Baki san yaro ba kawai ki kawo shi ki cе
yayi min aikin ofishin dake daf da ofishina?
Wannan yaron da yake jin bai da kunya kuma
ina daf da koya masa ita.. shi ya aiko da
takardar cewa ya san ke kika bige wani da mota
kuma zai ja da ni"
Ta ruko hannun mahaifin nata tana
murmushi tana magana cikin sanyi.
"Zai yi kunya Father, zan gargade shi, lallai
na san shi, na san yana da Kwarewar da zai iya
rike ofishin kafin na dawo zaka ji dadin aiki da
shi ba...."
Har yanzu idanunsa na kan Farid ya umarce
shi da ya fice daga ofishin. Nan ne Farida tayi
abin da ta saba, ta sanya ihu ta kira mahaifinta.
"Father! Kada ka yi min haka...Idan bai
kware ba ka sanya idanu kansa mana kana yin
48 Motiren Maseys Rahma AbdulMa jid
hakan... na yi maka alkawarin Farid zai zamo
irin yaran da kake so, kada ka manta digiri na na
farko kafin Networking na karanta ilmin sanin
dabi`ar dan adam ne. na karanta irin wadanda
kake so kuma Farid na cikinsu. Abin da yayi
min ba don wata gaba ce ba koda kuwa irin
wadda ke tsakanin mu da talakawa ba, yayi ne
don irin yanayin kekashewarsa akan gaskiya, in
ba haka ba bai san ni ba bai san kaba, ji yayi ya
kamata a biya hakki kuma na biya ba sai
magana ta wuce ku amfani juna a abin da na san
zaka bukace shi ba...."
Ta yi ajiyar zuciya sannan fari da idanu.
Father! Kai ne ka ce babu abin da zan nema
a wurinka baka yi min ba ban da auren
Ibrahim...yanzu ina neman alfarmar ka bai wa
Farid dama yayi aiki da kai a nan, wannan ba
wai alfarma kawai nake nema ba, yana cikin
dabaruna na rabuwa da wanda kace na rabu da
shi, domin idan Farid na rike da ofis dina zan yi
tafiya mai nisa hankalina kwance har na manta
abin da kake son na manta. Idan kana tuhumar
rashin iya aikinsa sanya shi karkashin
idanunka"
Ta dan mannu da kirjin mahaifinta wanda
da alamar ya soma saukowa.
"Please father"
Yana ta kikkifta ido na karaya, sannan ya
dubi Farid ya nuna yatsunsa biyu ga idanunsa
sannan ya mai da ga idanunsa, wato alamar ina
kallon ka.
1
2
49 Matiyan Masoya Rahma AbdulMa jid
"Congrat! Ka ci albarkacin 'yata, amma ka
sani akwai matsanancin ido a kanka"
Farida ta sunbace shi a goshi cikin godiya
sannan ta dubi Farid ta yi masa barka, а
lokacinda babanta ya tsala kira ga Wilson.Ya
shigo cikin shiga irin wadda Farid ya tafa
ganinsa da ita. Shine dogon mutumin nan mai
kyan kamanni da alamar tsadar rayuwa da ya
tare shi a farkon shigarsa wannan ofishi.
"Sa idanunka a kansa,sabon ma`aikaci ne"
Ya amsa sannan yayi hannu da Farid. Na'ibi
tuni ya bar ofis din ya koma nasa. Wilson ya
dan mammatsa hannunsa, sannan ya dubi Farida
cikin fuskarsa din nan mai yawan murmushi.
"To ranki ya dade ko za ki bar ni da shi mu
dan yi musayar wasu tambayoyi"
Farida ta dauki Jakarta.
"Sure is all yours, ka dai bar shi ya fara aiki
sati me kamawa, ni zan fita sai kuma na dawo".
Ta daga masu yatsu, irin yadda turawa suke
sallama, cikin murmushi ta fita.
*
Mahdi na zaune gefen katifa ban da kamo
hannun Farid da yake yana tafawa da shi babu
abin da yake sai karawa da kykyata dariya.
"Abokina yanzu ka haye kenan"
Ya dan yi rausaya na murna.
"Mad! Wai nine nake da gida babu abin da
yake bukata sai jakar kaya na. ina da mota ta
gani a fada, zan dinga mallakar kudi naira dubu
dari hudu a wata! Na kasa gaskatawa"
50 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ya fadi da baya zuwa cikin katifar sannan
ya dawo ya sami idanun Mahdi akansa yana
dariya.
"Gobe Mad ka fara tattara mana `yan abin
da zamu yi amfani da su kafin na dawo, gobe za
a bani mukulli, kawai sai mu koma jibi da safe
tun da zan karbi hutun zuwa tattara daga gida"
"Ni kuma a wane matsayi zan koma gidanka
matar ka nake ko danka?"
"A matsayin mai dafa min abinci mana ka
gane ai, ko dubu hamsin nake baka da abinci ai
ba laifi, mu da har aikin dubu talatin a wata mun
nema mu ci gaba da dambe kan wannan katifar"
Suka sake tintsirewa da dariya har da
faduwa duka kan katifa.
Har Mahdi ya gama ya tsaya yana kallon
Farid wanda dariyarsa ta ki karewa ne saboda
cakuduwarta da murna. Sai da ya lafa bayan da
jikinsa ya ba shi a na kallon sa.
"Me kake ji a zuciyarka kan Farida yanzu?"
Farid ya dube shi da kyau sannan ya tofar da
wani nunfashi.
"Me kake nufi? Kada dai kana son taso da
maganar soyayyar da kullun kake tuhuma ta da
ita? Idan ita ce ka kwantar da hankalinka, ina
murnar samin aiki ne amma ba ni da wani abu
har yau kan Farida"
"Ba nufi na kenan ba, watakila don hakan ce
a zuciyarka shiyasa ka fassara ni. Nufina shine
sanina da kai a wancan satin, Farida itace mace
da ka fi tsana a duniyarka kake kyararta da yi
51 Maryan Masoya Rahma AbdulMajid
mata munanan zato. Yanzu da ka ga wadan nan
halaye tattare da ita yaya ka koma jin ta?"
Ya tafa hannu.
"Gaskiya kallo na ga Farida ya sauya,
maimakon haushin ta sai na ji ina jin haushin
kai na ne zalla da nayi azarbabi wurin yanke
mata hukumci cikin al`adata, kamar har yau
kauyancin da nake zaton ya fita dga kaina na
nan daram. Farida bata da girman kai bata da
munanan halayen da na zata, tana da matukar
ilmi, tausayi, da saurin fahimta. Abu daya da ya
ta hankalina a wancan lokaci bai wuce yadda
take da mahaifinta ba da bangaje ni da ta yi. Sai
dai daga baya na fahimci cewa Farida rainon
turai ce zuryan da suke da wani irin `yanci kan
mahaifansu da basu daukan ladabi ko rashinsa a
tsakaninsu da iyayensu, haka nan fishinsu na
mawadata wanda kan hada da fashe-fashe a
gida watakila shi yasa ta bangaje ni ba tare da ta
waiwayo ba. A yanzu wanda nake da sauran jin
haushi ko tuhuma bai wuce mahaifin Farida ba.
Bama haduwa tun bayan kawuwar Farida, wasu
ma'aikatan sun tabbatar min da cewa baya zama
dama a kasar nan sama da sati biyu a shekara,
tun bayan dawowar Farida, dama ya zauna ne a
Kokarinsa na shirin mayar da ita waje da yake,
kuma in zata sama masa matsala ya kan zauna
ya kwan biyu. Yanzu ya hana ni ofosihin da ta
ba ni da cewa sai ya ga aikina na wata shida zan
kuma nuna masa ko ofishinsa zan iya rikewa...
amma yanzu damuwata ita ce ina Farida ta
52 Mafyan Masoya Rahma AbdulMajiр
shiga? Ban sake sanya ta a ido ba tun
washegarin da ta ba ni aiki, na tambaye ta
lambar wayarta sai murmushi tayi ta ce min
babu bukata, ina gudun kada kawai ta dauke ni
aiki ne ba ta dauke ni wani na daban ba. Ban
san dalili ba ina jin kamar ina son kulla
amintaka da ita, amma ko ina take a halin
yanzu?"
53 Mafiyan Masoya Rahma AbduiMajid
Biyu
Girgijen da kamar baya tafiye shine ya maye
gurbin talabijin din da Farida ta mayar abin
kallon ta a cikin jirgin saman da ke dauke da ita
zuwa kasar Jamus maimakon Afrika ta kudu.
Sai dai koda idanunta na kallon girgijen
zuciyarta na cikin kuna da kadaici. J take
kamar ita kadai ce a duniya cikin wannan hali
da ta jima tana gudun shigarsa, kuma ga shi ya
tirnike ta a cikin wannan tafiya. Dun yawon da
tayi da shiga wasu lamurra da basu shafe ta ba a
farkon wannan satin zuwa karshensa tayi ne don
ta katse damar da zuciyarta ke da ita na tsananta
tunanin Ibrahim. Ya dai sha kiran lambarta tare
da yi mata sakwanni masu motsa zuciya, amma
tayi nasarar kin karaya ta tanka shi har sai a
yanzu da ta shiga jirgi ita kadai a kujerun da aka
yi jefi-jefi domin jin dadin Bussiness class a
cikin jirgin. A yanzu ta karaya matuka duk wata
soyayya da ta san tana yi wa Ibrahim din da ta
taba lafawa yanzu ta tashi, tana kallon
kyawawan rayuwar da suka taba yi da Ibrahim
din tun daga makaranta zuwa sauran sassa.
"Idan muka yi aure miyar katantanwa zan
dinga yi miki?"
Ta kalle shi da zare ido.
"Saboda me?"
54 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMalid
"Saboda na lura duk wani abu da ke da
alaka da ruwa kin fi son katantanwa"
Ta karkata kai tana kallon sa kallon so da
shauki.
"Baby zamu yi aure kuwa?"
"Idan bamu auri juna ba wa zamu aura
Farida? Ban san ke ba in zaki iya auren wani na,
amma ni dai Farida ba zan iya rayuwar aure ba
sai da ke...Baby na ina son ki fiye da yadda na
san soyayya...
Hawaye suka ci karfin idanunta ayayinda
take wannan tunani.
"I love you Bally... I love you so much"
a Haka take gaya wa hotonsa dake bayyane
fuskarta a yayinda zuciyarta ke tafasa mai
saduwa da kwakwalwa. Ta tashi ta bar wurin
don kada wani ya hange ta ta koma toilet.
A filin jirgin saman motar masaukinta ta iso
aka dauke ta kasancewar tuni a intanet tayi
hayan masauki da gida irin wanda ya dace da
ita. Direban bai bar ta ba sai da ya damka ta ga
masu aiki a wannan faffadan gidan na kasa.
Suka dauke mata kewa ta hanyar nuna mata ko
ina a gidan suka sanya mata kayanta a inda ya
dace sannan suka tafi suka bar ta.
Wai yanzu ita kadai ce zata rayu a nan duk
da halin da zuciyarta ke ciki, zata yi rayuwar da
bata san ranar da zata kare ba muddin bata san
ranar da zata manta da Ibrahim ba. Ta dubi
agogo, karfe tara agogon jamus ta buga har da
55 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
mintuna biyu, ta fada bayan gidanta ta face
wanka da ruwa mai matukar zafi sannan tayi
shigar sanyi mai matukar armashi tunda bata da
zabi ban da zagaye birnin Berlin. Ta je wuraren
wasanni da dama irin wadanda ta iya amma sun
kasa yi mata tasiri, don haka bata da zabi illa
mika wuya ga bakin ciki ta dawo gida don tayi
ya ishe ta tun kafin goma da rabi ta kulla kanta.
Ta sauka daga tasi ta kara rufe kanta da
hular rigarta tana shirin fylfyalawa don shiga
cikin gidanta kafin kankarar sanyin ta sauka a
fatar kwanyarta sai ta ji an rike hannunta. Da
fargaba ta dago kai ba tare da shayin kankara ba
don taga wane mai karfin halin ne. suka hada
ido da Ibrahim wanda yake cikin shigar sanyi
amma babu kwakkwarar hula a kansa. Suka yi
wa juna kur kowanne zuciyarsa na duka na
dalilai mabanbanta. Farida dai dalilanta na da
yawa cikin su har da wata 'yar rahusa da
zuciyarta ke samu don ganin Ibrahim sannan
fargabar ganin ba zata a lokaci guda sai
rikicewa, yayinda shi Ibrahim din dalilinsa
bayan samun sa'idar ganinta tausayi da tsoron
lokacinda zai bata kafin ya samo hankalinta su
ne suka addabi zuciyarsa
"Am sorry"
Ya ambata cikin kwallar da ta karya shirun
da zuciyarsu ke ciki.
"Me ya kawo ka nan?"
Ta tambaya cikin sanyin murya.
56 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMalid
"Na biyo ki ne... na sami labarin kin taho
nan shine na zo na zauna tare da ke"
Ta dan sanya karfi ta kwace hannunta daga
nasa a yayinda kuka ke yi mata barazana.
"Excuse me?"
Ta ce masa sannan ta kama hanyar gidanta.
Ya sassarfa ya sha gabanta.
"Farida ki yi hakuri ki saurare ni... Na san
kin yi fishi da ni saboda karya zaton ki a kaina,
ina baki hakuri,amma ki sani ba yi na bane,
tuggun mahaifina ne domin ya raba mu,. Na yi
duk abin da kika so, amma ya koma da baya ya
6ata.Farida kin san dalilinsa nayin hakan don ya
99 raba mu ne...
Ta kalle shi cikin nuna alamar gamsuwa
amma ba da zancensa ba da fishinta. Ta saki
ajiyar zuciya.
"Idan ka gama bayaninka sai ka kama
hanya, domin mahaifin ka yayi nasara, na rabu
da kai kuma mun rabu"
Ta shige harabar gidanta a yayinda ya sake
sharowa a guje ya tokare kofar da ta so rufewa
da kafa.
"Farida ki yi hakuri kin san ina son ki ba
zan iya rabuwa dake ba....babu mai yin nasarar
raba mu... Na san zaki zo nan, amma ban biyo
jirgi daya dake bane don na