zai sanya
Ibrahim ya rabu đa babansa duk abin da zai yi
masa muddin bai nemi ransa ko na Farida ba me
zai sanya Farida ta yi watsi da Ibrahim mijinta
muddin ba ta ga zasu raba ta da ranta ba. Biyu
sau biyu fa hudu ce me gida na"
Naibi ya dinga gyada kai na samin
gamsuwa.
"Na ji kamshin hakan, amma ban sami
hujjojin dafa wa ba sai a wurinka... an so kashe
Farida yayinda aka sami damar gaya mata
Ibrahim baya son ta da gaskiya".
Wilson yayi dariya a hankali.
"Amma kuwa Ibrahim na matukar son ta.
Ga shi har ya ba mu kansa"
"Me zamu yi da shi?"
"Me gida na kana abu kamar ba kai ka koya
min ba, ka san dai ba zamu kai Me gida Hadi
wurin `yansanda ba, mu zamu yi masa hukumci.
Ranar soyayyar Ibrahim da kayutarsa ke nan"
Na`ibi ya sanya masa ido don mika wuya ga
dabarar me dabara
"A gayyaci Ibrahim, ka ba shi gida ka yi
masa daurin talala da sunan zaka sasanta shi da
Farida in ta warke ka ga duk sun zama na mu,
amma fa zaku yi tozali da tsohon abokinka
134 Manyan Masoya Rahma AbdulMajid
bana, Oga Hadi. Kai dama ina nan zaku hadu na
ga kewa".
"Sai kuma me?"
"Sai ka hadu da Hadi ka sanar da shi duk
abind a aka gano da kuma hujjojin kayar da shi,
babba ma shine dan cikinsa na shirin tona masa
asiri a idon duniya don ya bayar da hadin kai....
Ka ga yana da zabi ko ya fita ya bar mana
takarar kwangilar 96 Column ya sanya hannu a
masu goyon bayanmu ko kuma daga nan
sunansa ya tafi kwandon shara ka ga...
Na`ibi ya saki hannu ya ja tsaki.
"Kai kullun batun kudi da gasa ne a gabanka
in2 maganar iyali na kana maganar a bar mana
kwangila... ya taba kasa mu ne a neman
kwangila?"
Duk maganar da me gidansa yake yana kada
kai cikin murmushin ruwan sanyi watakila ma
shi yasa ya ba shi damar ci gaba da magana
bayan ya yi tambaya.
"ko kadan yau ba kudi ne a gabana ba ranka
ya dade saukake maka abu na ke son yi. Hadi
bai taba kasa mu ba, amma bamu taba cin riba
kansa cikin ruwan sanyi, ba, wannan karon ina
son hakan ta faru cikin ruwan sanyi kamar
yadda kai shi kotu daga baya zai zo mana cikin
ruwan sanyi....Haba yanzu in muka ce mu wuce
da shi wurin `yansanda kai tsaye ka san kashe
kudi gida biyu ke nan, shi ma ka san fa me kan
sarki ne fa zai kashe za a kashe masa masu
hanya zasu yi masa kara. Koda na san zamu yi
135 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
galaba amma dakyar, amma in har mun kasa shi
a wannan kasuwar bayan kudin da ya kashe a
kanta, darajarsa za ta kara zubewa a idon masu
iya son goyon baya a duk lokacin da rigima za
ta hafa ku, sannan fa in ya tsaya ja da kai a kotu
shi yana kashe uwar kudi ne kana kashe
riba...."
"Na ji na gane... shi kuma dan yaya zan yi
da shi in yi ta rikon sa?"
"Da sunan Farida na kara murmurewa kuma
kana shawo kanta ba. In an gama shari'a, zamu
yi masa hukumci da sunan ubansa ne yayi masa
don haushin ya kalubalance shi...kai me gidana
in wannan tsari ya tabbata Hadi ya fita daga
littafin mu na masu yi mana ta`addanci"
Shi ma sai da yayi dariyar saboda gamsuwa,
sannan ya koma gefe daya yana danna wayarsa.
"Bari na kira yaron"
Wilson ya dauke wuta dif.
"Hello Ibrahim? Ina gajiya... a ina kake a
halin yanzu?... to na dan yi tunani kan
maganarka kuma ina son ganin ka gobe zan
sanya a zo a dauke ka a kawo ka inda zamu
gana
Ya kashe wayar ya dubi Wilson.
"A otel yake, gobe zan gana da shi a gidan
Merry, ka yi hanyar yadda zai zo can zuwa sha
biyu na rana zan isa wurin sha daya da rabi".
"An gama ranka ya dade"
Ya juya ya bar dakin ganawar kafin Wilson
*
136 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ibrahim ya dan nisa ya karkata kai gefen
hagunsa ba inda Farid yake ba.
"Me nene hadin ka da Farida?"
Ya tambayi Farid wanda ke kallon sa cikin
kokarin boye duk wani zafi.
"Kamar na fi ka bukatar jin wannan amsar,
ko ba komai na san mene ne"
In ji Farid wanda ke kokarin yin ta maza
don ya kwaci hakkinsa na mazakuta, ko ba
komai ya samu ya janyo hankalin wanda ya
tambaya din da jin girmar tuhumar da yake har
ma ya kalle shi cikin ido.
"Ni? Wa nene ga Farida?"
Ya dan mike daga jinginar da yayi da
teburin.
"Ni ne mijin Farida da ta aura cikin tsananin
so duk da ni da ne ga babban abokin hamayyar
mahaifinta AbdulHadi. In kana da labarin tana
da ciki to ni ne uba ga abin da yake cikinta..."
Ya dan sarara sannan ya sunkuyar da kai.
"Tana fishi da ni da zaton cewa ina da
masaniya kan cutuwar da tayi...ba ta ba ni
damar da nake bukata ba na wanke kai na,
amma nayi mata uziri don sanin kaunarta gare
ni da cewa tana ganin ban kamaci na yi mata
haka ba, ta ji zafin abin matuka, sai dai ba zan
dena jira ba, wata rana soyayya za ta ba ni dama
a wurinta na wanke kai na tsaf"
Ya dago ya kalle shi da kyau.
"Amma fa mata ta ce da ba zamu taba
rabuwa ba"
Σ
Rahma AbdulMajid 131 Mafiyan Masoya
Kwatsam sai Farid ya sami kansa yana mai
rage jin haushi da zafi, kai! Kamar ya ma saba
da yanayin nan take. Farida ta auri wani ke nan
ba shi ba kuma tayi haka ne don tana son sa har
shi yasa ta 6oye wa mahaifanta, akwai alamar
har yau tana son sa duk kuwa da tana zarginsa
da cutar da ita, amma ta kasa bayyana hakan ga
mahaifanta don kauna. Haka ma wanda take so
yana yi mata matukar so wanda in bai fi shi ba
zai yarda su yi tangangan. Can wani bege na
dama a ce shine da Farida cikin wannan yanayi
ya kama shi har ya sanya shi tsanananta kallon
da yake yi wa Ibrahim ba tare da ya san yana yi
ba.
"Zaka iya gaya min kai kuma me ke hada ka
da Farida bayan da na gaya maka ko ni wa
nene?"
Yayi murmushi ya sunkuyar da kansa cikin
jin nauyin rashin sanin takamaiman lokacinda
ya 6ata yana kallon Ibrahim.
"Ni?.. Ni abokinta ne kuma me yi mata fatan
alheri, amma ban san tayi aure ba in gaya maka
gaskiya. saibayan faruwar wannan
lamarin...wafi abu ne da nake fatan in har ta ba
ni dama na ji karin bayani abakinta...sai daị in
ya tabbata kai ne mijinta kun yi auren, zan so ka
san ka sami mata, jaruma ce kuma mai halin
kwarai...ka rike ta kuma ka faranta mata rai. Kа
san cewa wata alheri ce a rayuwarka da wasu ke
fatan samu ba su samu ba, kuma kai kanka zai
yi wuya ka maimaita samun irinsa.
138 Moyan Masoya Rahma AbdulMajid
*
Merry ta dan waigo ta dubi bayanta ba don
bata gan shi ta madubin gabanta ba sai don
mamakin zuwansa a wannan lokaci. Ta ko
tabbatar shi ne yake tsaye a kofar katon dakin
yana murmushi, ta mai da kanta ga madubin
inda ta ci gaba da gyaran gashinta.
"Me ciyamanan ke yi a gidan Sa-daka yau a
lokacin da matarsa take gari?"
Ya zubo hannayensa na al'ada cikin aljihu
sannan ya karaso cikin dakin.
"Duk wani abu naki da yake gidan nan na
sanya an kwashe miki shi zuwa sabon gida da
ke kan wannan adireshin"
Ya ja linzamin maganar har ya a jiye mata
adireshin a kan karbun miron dake gabanta.
"Abin da ya saura naki sune wannan kayan
gyaran gashin naki sai ki kwashe abinki da
kanki. Nan da mintuna arba`in wasu zasu
bakunci gidan nan, amma ke zaki iya komawa
sabon gidanki da ya fi nan kyau da girma"
Ta dube shi da sauri cikin zallar mamakin da
bai cakudu da komai ba duk da fishi na son
maye gurbinsa.
"Mene ne ya zo kuma? Me yasa kake min
haka? Kullun cikin canjin gida ba zan taba cewa
ga muhalli na ba. Ko dansanda ko soja ba su kai
ni sauya muhalli ba tun da na fara zama tare da
kai ciyaman wai...
Ya shafi kumatunta yana murmushin kashita
har zuwa hafarta sannan ya rike.
139 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Sauyi Plan ne na ciyaman din ki gara ki karba da hakuri.
Ya sake ta inda ya doshi kwabarta ta kayan
bacci ya soma tattara mata yana magana.
"Nan da mintocin da na ambata ina jin zan
yi ajiya da ba zamu so ta san dake ba...Ibrahim
din Farida kuma dan abokin mu Hadi zai
bakunci gidan nan na mika wuya gare ni...kin
san ba zan so ko ke ki so saurayin kawarki ya
gan ki a turakar sirikinsa ba..."
Da sauri ta dafa shi.
י
"wane Ibrahim?Balalan Farida? Me zai
kawo shi kusa da rayuwarka?"
Ya sake ruko hannayen ta.
"Kwantar da hankalinki sallamawa ce yayi
ga masoyinki kuma zai mika wuya ga duk
makircina na kai karshen Hadi mu huta a karo
na karshe. Wannan mintoci na da muhimmanci
don haka ki bar nan kafin su cika"
Ya sunbace ta sannan ya fita ya bar ta tana murmushi
"Ciyaman dinki ya kusa dawowa don uwar
gida ta kusa tafiya"
Ta rankwafa ta soma kwashe kayanta da
sauri tana fadin bukatarmu zata biya. Har sai da
yayi nisa sannan ta dakata ta duba ta tabbatar ya
fita sannan ta yi watsi da kayan ta fashe da
dariya.
"Dubunki yana ta,cika Farida. Ramuwata
gare ki tana ta kara fin gayya zaffi, yau
140 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
saurayinki zai zo har inda na sani, zai zauna
inda watakila ni kadai na sani bayan ubanki
Ta fashe da dariya sannan ta sake karantowa
kanta wani zancen.
"Wannan kumatun kika mara kika watso wa
wannan kayan jikin kayansa waje daga gidanki
wai don ina kawo masoyina gidanki kika kira ni
karuwa ina kawo miki maza gida. Yanzu
sakayyata gare ki shine har ubanki nake kai wa
London din da kike jin don kin kai ni zaki mare
ni. To yau kin ji karin wani dadi kan dadi...za a
kawo min masoyinki...ina da hotuna da babanki
zan yi da masoyinki ki san lallai ni karuwa се
Farida".
Kau! Ta ji zafin marin ya dawo mata har ta
tuna ranar da abin ya faru. Wata rana ce da suka
cika kwana uku a tsakiyar birnin Landan inda
tayi rakiya ga kawarta Farida wadda ta je buikin
wata kawarta da aka yi a can. Sun dawo gida ne
daga biki ta sami Merry kawarta a cikin uwar
dakinta suna saduwa ita da wani katon mutum
da alamun dan Najeriya ne, amma bata san shi
ba, abin yayi mata ciwo matuka yadda da ta taso
ta sha gaban Farida zata yi mata magiya Faridar
ta kife ta da mari ta nuna mata kofar fita, har ta
biyo ta da kayanta da fasfo da tikitinta cewa
kada ta sake zuwa gidanta tunda ita 'yar iska ce
kuma tana bata mata gida. Wannan kunyata da
tayi gaban saurayinta wanda ya gayyace ta zuwa
nasa gidan don su karasa abin da suka fara ya
hana ta iya more z manta a dakinsa inda shi ma
141 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
ya kore ta don ba zata biya masa bukata ba. Ba
shiri ta dawo Najeriya inda ta fara shirin daukan
fansa kan Farida ta ko halin kaka. Da fari ta so
matuka ta yi ramuwarta kan Farida ta hanyar
anfani da Ibrahim amma kasancewar ita ba wata
ba ce bayan da wadda ta daga ta ta yar da ita sai
ya zamo ganinsa ma bai samu gare ta ba don
bata da matsayin da zata isa inda yake. Ko da
yake tana da kyauwunda zai iya kai ta ga
kowace turbar maza masu son kyawawa da
alamun shi Ibrahim tunda ya dora idanunsa kan
Farida ya kulle irin wannan dama,, amma kuma
kamar akwai wata damar wadda bata kullu ba in
ta biyo ta wurin mahaifin Farida. Mutum ne da
yake rayuwa shi kadai shi da aikinsa a da
ya'yansa tunda matarsa ta ki zama wuri daya,
sai dai hakan bai hana shi ajiye wuri musamman
da ya kan leka wasu matan idan bukatar hakan
ta taso, duk kuwa da ba shi kan zabar wa kansa
ba saboda yawan aiyuka, idon=garinsa wato
Wilson shi ne kan yi haka. Kuma ta hanyar
Wilson din wanda ta nema ta samu ya biya ta
da sada ta da me gidan shi wanda yayi
marhabun da zama da ita muddin zata amshi
bukatarsa ta tsugunar da ita a nesa da jamaà
yana biya mata duk wata bukata ta duniya da
zata so, amma da sharadin zata yi kamar ba a
halicce ta ba a rayuwar iyalinsa musamman ma
in matarsa ta zo gari yana son tayi kamar bata
taba ganinsa ba. Ta amince da haka a zahiri,
amma a badini zata yi hakan ne da niya biyu, na
MenaR Masoya Rahma AbdulMajid
Sarko tara abin duniyar da ta gani
ta na biyu
sai shaidun cin zarafin wadda ta kira ta
Karuwa don ta ga yadda tayi da jinin da ta ke jin
fito daga ciki har take ganin tsarkin kanta da najasar Merry.
ta
Ta katse tunaninta a nan ta shiga kwashe
kayanta inda take fadin'Bally na Farida sai na
zo tunda Allah Ya kawo wa angulu garin
dadinta kusa wato masa
*
Bai gama sabawa ko natsuwa da inda aka ce
an kawo shi a matsayin mazauninsa na wucin
gadi ba sai dai ya mika wuya ga zaman falon
yadda ya mika wuya ga duk wani abu da zai
dawo masa da Farida. Ya na zaune a kujera
daya duk iya zaman sa a falon duk kuwa da an
gabatar masa da abubuwan ci da sha na alfarma
a wurare da dama, kama daga gabansa har zuwa
falon abinci, amma babu wanda ya tanka. Abin
da zai iya tankawa shi ne zuwan Na`ibi wanda
yace masa nan da awa daya za su sadu.
Awa daya da mintuna biyu kacal da ga yin
maganarsu da sirikinsa sai ko ga shi ya iso
falon. Shi kadai kuma cikin shiga mai sauki
kamar yadda aka san shi da kamannin saukin
kai. Da sauri ya isa gaban kujerar Ibrahim
wanda ya tashi tsaye da sauri ya na yi masa
maraba. Ya mika masa hannu suka gaisa sannan
ya girgiza hannun ya saki ya doshi wata kwaba
ta kayan sha maras sanyi.
143 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
"Baka ci komai ko ka sha komai ba
Ibrahim?"
Ya nufo shi da kofi guda biyu ya rike naasa
sannan ya mika masa nasa ya koma kujera mai
kallon ta Ibrahim ya zauna sannan ya umarce
shi da ya zauna.
"Ka dinga jin ka a gida, domin wannan
gidanka ne, ni na yi maka masauki da shi don
ban ji dadin cewa kana zaune a otel ba"
Ibrahim ya kurbi abin shansa sannan ya sake
yin zaman ladabi da jiran abin da ya kawo shi.
Shi kuwa alkali ya dora kafa daya bisa daya
cikin sakewa.
"Ibrahim na juya maganarka kuma na yi
bincike a kanta, na sami tabbacin cewa Farida
na da ciki kuma naka ne. ba abu ne da zan ji
dadin sa ba da fari domin kuwa ba boyayyen
abu ne gare ku kiyayyarmu ga kasancewarku
tare ba, amma sanin kanka ne zan iya amincewa
da abubuwa guda biyu a duk lokacin da suka zo
gaba na. Daya duk inda aka ce jinin Farida zan
so shi domin kasancewarsa jinina ko da kuwa da
na kare aka cakuda shi,na biyu ba karamin
kyauta ka zamo min ba muddin da gaske ne ka
fahimci inda mahaifinka ya sanya gaba ka kuma
kyale shi don kasancewa tare da ni. Ibrahim zan
iya amincewa in ba ka Farida kuma in gyara
tsakaninku in fauki nauyin auren ku in har abin
da ka zo min da shi haka yake..."
44 Mayan Masoya Rahma AbdulMajid
"Da gaske ne Father. Na hakure wa zama da
babana na wani lokaci don zan so rama wasu
abubuwa da ya yi min"
"Da gaske kuwa ni ma zan agaza. Sai dai
samin tabbacina zai danganta da yadda ka bi
dokoki na ne kawai. Zan so ka zauna a gidan
nan ba ruwanka da kowa har zuwa lokacin da
Farida za ta sami lafiya ku sami ganawa, а
wannan bangare ni kuma zan yi kokari in ga na
ci gaba da shigar mata da kai tun kafin ku
fuskanci juna, zan yi iya yi na in kubutar da
sunanka daga zarginta. A takaice dai nan da
mikewar Farida zan gama amincewa da sadar
da aurenku ga shari`ata muddin za ka yi min ni
ma nawa aikin...Aikina ba shi da zagon kasa ko
makirci illa kawai tsayar da gaskiya. Na san
mahaifinka ne ya so kashe Farida, amma ko
kadan in har zan hada zuri`a da kai ba zan ja da
wannan zance ba, domin kuwa ba abin da zan so
ya fito jika ta ko jika na ya sani ya kuka da shi
ba ne. Sai dai fa ba zan sake amincewa da
Alhadi ba don ya shiga inda ba za a iya shigar
min ba. Abin da kawai zaka yi min shi ne ka
shiga yakinda nake da shi kan sabuwar
kwangilarmu don ka dauki fansar da kake son
dauka ba wai don ba zan iya ba sai don baka
naka fagen, zamu bata masa rai a haka kuma
wannan ya ishe ni fansar abin da ya so yi wa
yata kurna matarka. Ina so duk dabarar da na
fito maka da ita don nuna haka ka biye min.
alkawarine ba zan cutar da kai ko saba maka
A
145 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
alkawari ba, domin ba ni da riba kan haka in na
yi a wannan karon. Farida ta riga ta aure ka
kuma ba zan kashe ta ba, haka nan mahaifinka
da yayi amfani da dabarar kisa ya riga ya tsiraita
ta ta inda babu wanda zai amfanu da ita, ke nan
muddin kuna raye to kai da Farida miji da mata
ne da babu yadda zamu yi da su, amma goron
amfanuwa da nawa aikin shi ne ka yi min
wannan alfarmar ka ga ni kuma yadda zan saka"
ba.'
Ya juya ya nisa ba don ya fita daga tsoro
"Zan yi haka father, kuma na ji dadin da ya
zamanto baka nuna za ka amfanu da zargin da
kake yi wa mahaifina na neman hallaka Farida
ba, domin wannan kusan shi ne abin da zai iya
karar da kusancin mu da iyalin mu a ruwan
sanyi. Fata na Allah Ya taba zuciyarsa ya san
kuskuren da ya so yi wa rayuwarsa ta wannan
hanya, wannan ne zai sanya na mika wuya ga
duk wani shiri da zai girgiza shi ya san lallai
abin da ya so tabawa babban laifi ne taba shi"
A nan Ibrahimi ya gama nasa kaulin ya sake
kasa kunne ga hirar Na`ibi wanda a yanzu ya
sake ne yana hira da shi kan dalilai biyu, kara
ba shi tabbacin sakewa da shi da kuma bugun
ciki na hikima don samin abin da zai dafa nan
gaba a tuggunsa, duka dai sun a ginuwa kan
alkawarin da yake nanata ya daukar wa Ibrahim
din don karin neman yardarsa.
*
146 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Tabar bata kare ba ya cire ta ya taka ya
mutsittsike ta saboda fitar da wani sashi na
takaicinsa, amma ba a hada minti uku ba ya ji
yana bukatar ya sake kunna wata duk dai kan
dalili daya wato rage takaici. Ya sakala ta a
bakinsa zai nemo abin kunnawa amma sai ya ji
an kunno masa wuta. Ya dubi me kunna-masa
tabar ba don bai gane shi ba sai don baya son
dauke idonsa har sai ya rage fargabar da ta ke
kalubalantarsa. Na`ibi yayi murmushi sannan ya
jingina da makarar tafkin da ke bayansa ya
kawar da ka.
"ka yi mamakin ganin mutumin da ka jima
yana matsayin wanda zuciyarka ke yawaita
tunawa a rayuwarka. Ni ma haka, sai dai
mamakin ganinka bai kai min mamakin yadda
abu ya kai ka ga yunkurin kashe Farida ba don
kawai tana son danka...Huf! Na fi ka samin irin
wannan dama a lokacin da Ibrahim yayi ta
zarwa a gida na yana son na ba shi Faridar,
amma sai na ga kisa ba dabara ce ta isassu ba
kamar ka. Matsalata da kai saurin sikewa
Hadi...
Shi ma ya kunna tasa tabar a yayinda
AbdulHadi ya nisa yace 'me kake so da ni
yanzu?"
"me ko nake so da kai ma?.. oh na tuna, so
nake in gaya maka fansar da zan dauka kan abin
da ka yi min babu yawa, na san ka so kashe min
yata, kuma ina da shaidun da zan tona asirinka
ciki har da Faridar da ka so kashewa da danka
147 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ibrahim wanda ya bar ka ya koma hannuna da
zama don jin ciwon abin da ka yi. Sai dai duk
bana son wannan ina so ne ka janye kawai daga
sabuwar ja-in jar mu ni ma na kashe maganar.
Ba wani abu bane illa kawai ina so in ga ka
nuna wa duniya kasawarka a gabana. In kana ga
ba zaka iya wannan ba nan da kwana uku sai ka
sanar da ni domin na sami gabatar da karar da
za ta tozarta ka fiye da hakan a gaban duniya
musamman in aka ce danka na goyon bayan
makiyanka da yin shaidar da za ta kayar da kai.
Kuma ka san wani abu?"
Ya zo kusa da kunnen AbdulHadi yayi
masa rada.
"Duk zai yi haka ne wai don na ba shi
Farida aure... zan kuma nuna masa zan yi hakan
har sai ya sake sannan na dawo maka da abin ka
yadda kake so ba tare da ya aure ta ba. to yaya
ma za a yi na bai wa wanda ya so kashe Farida
Kimar surukuta?"
Ya juya zai bar wurin yana fadin. ‘Sai na ji
ka' Hadi ya janyo shi da karfi cikin fishi ya ko
dawo yana kallon kafadarsa.
"Ka san ba zan taba yin abin da kake so ba"
Ya yi murmushi.
"Babu dadi ka mika wuya nan da nan shi
yasa na baka har kwanaki uku ka tunana. Kada
ka damu zuwa lokacin zan sani ko za ka yi ko
ba za ka yi ba"
Ya juya ya bar AbdulHadi na yin wani nishi
da bai san iyakar inda kirjinsa ke kaiwa ba.
148 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
*
Farid ya sami lokacin Farida a wani zango
mara amfani gare shi a yanzu watakila ma sai
cutarwa. Farida na asibiti ta takura da cewa
shine zai zamo mata abokin hira a kusan duk
lokacinda take zaune ido biyu a lokacinda shi ya
soma yakin da bai yi imanin zai ci nasara ba
wato yakin raba zuciyarsa da son Faridar wanda
ke karuwa a duk lokacinda ya zauna da ita har
ya ji kamar sake kara ninkaya yake.
Tana shan shayi daga jingine a bango
hannuwanta biyu rike da kofin kamar wanda
yayi mata nauyi, ta kan kale shi a duk lokacinda
ya fadi wani abu da ya bata mamaki ko dariya
sannan ta tanka shi. Tana jin ta sami sauki kuma
tana da karfin fita daga 'asibiti. Ciwonta shi ne
kewar Ibrahim da tunanin me za ta yi musu da
son yardar wa kanta da kanta cewa za ta iya yin
wani abu in ta fito daga asibiti da zai sanya ta
iya ci gaba da rayuwarta ko da kuwa ta gama da
Ibrahim mijinta ta duk hanyar da ta so.
"Idan zan iya tambaya Hajiya, me yasa kika
nisanta kanki da rayuwar Ibrahim mijin ki da
lafiyarki"
Ta kalle shi shiru har sai da ta hadiye shayin
da take ta tsiminsa a bakinta.
"kamar kana da wani karin bayani....Ka yi
min mana don na ga ka san lamarin sosai"
Ya mommotsa yatsunsa na hannu sannan
yayi murmushin rudewa.
a
に
シ
149 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
"Kawai dai gani na yi bai kamata ba, yana
matukar son ki muddin har zai iya mika wuya
ga mahaifinki kan yayi duk abin da zai yi da shi
ko da zai cutar da babansa....Ban sani ba in har
ya kamata in gaya miki ko bai kamata ba, amma
abin da na san su Chairman na shiryawa na
amfanuwa da shi kuma su yar da shi a nan gaba
ba zai zamo adalci ga dan cikinki ba....Oh! ban
san me ya sanya nake gaya miki ba, amma ina
jin kamar bai kamata ba, mutumin yayi duk abin
da zai yin a daukar fansa kan abin da yake
zargin mahaifinsa da yi. Ya rabu da shi ya koma
cikin tawagar Chairman, amma kuma kamar ba
wai sun karbe shi ne da....
Ta jima tana rike kanta don kada ta yanke
masa magana amma a yanzu ta kasa.
"Ibrahim na tare da father? Kuma suna
shirya wani abu? Ya rabu da mahaifinsa? Kan
me... Yaya?"
Ya mika wuya ga in ma katobara çe to ya
riga yayi ta.
"Ina ga dalilinsa shi ne na yá nuna wa
mahaifinsa bakin ciki kan yadda yake son raba
ku, amma kamar Chairman zai amfana da haka,
kuma yadda na ji yana fadi shi'ne ba zai sasanta
ku ba in ya gama amfanuwa da Ibrahim abin ba
zai yi dadi ba gare shi. Farida ina ga ki yafe wa
mijinki ku sasanta daga yadda abin ke son
kasancewa, yana matukar kaunarki, ba zai yi
wani abu da zai cutar da ke ba, in ba shiri aka yi
masa ba, in ba haka ba me zai sanya ya rabu da
15 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
mahaifinsa ya koma ga naki har ya mika wuya
ga duk abin da za a yi wa nasa mahaifin"
*
Ya yi matukar mamaki da firgita na ganin
wani mahaluki da ba Na`ibi ba a wannan falon,
kafin ya tantance ko wa cece sai ya ji ya fara jin
sanyi domin kamar tana da alaka da Farida. Ya
sauko matattakalar a hankali, sannan ya mai da
murmushi bayan ya iya tuno ta cif-cif.
"Ah! Merry? Yaya aka yi kika san ina nan?"
Yayi tambayar ne don ya sami amsar cewa
Farida ce ta turo ta, duk kuwa da ya san
hargitsinsu da Faridar, amma bai ga ta yadda
zata san yana gidan nan ba in ba ta wurin Farida
ba. A tsaye yake a gabanta abin da ya sanya
itama ta mike tsaye ba don kara girmamawa
gare shi ba sai don ta nuna masa kwalliyarta
daga sama har kasa. Ya ko kare mata kallo har
ta tuna masa da Faridar da baya mantawa don
sukan kwashi kama ta siffar jiki da irin
kwalliyarsu da ta zamo daya.
"Kana lafiya? Yaya masu jiki?"
Ta kawar da tambayarsa. Hakan ya dan ba
shi mamaki, amma ya dawo da tambayar ta
wani salo babu karaya.
"Mai jiki na wurin jinya, ba tare kuke ba?"
Ta koma ta zauna cikin