tsaya in yi shirin da
in mun hadu ba zamu sake rabuwa ba"
Ta dan tsaya da jin wannan kalma, sannan ta
juyo ta dube shi.
57 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Wane shiri zaka iya yi da ba zai sake raba
mu ba, matsoraci?"
Ibrahim ya dauko wani tsiraitaccen zobe
daga aljihun damar kwibinsa sannan ya durkusa
irin al'adar turawa a gaban Farida sannan ya
mika mata.
"Na gama shirina na karasa sauran rayuwata
dake...Farida zaki aure ni?"
Kumallon son sa da fargabar kada rayuwar
dake faruwa a gabanta mafarki ne ya lullube ta.
Ibrahim da gaske ya shirya. Ta tsinci kanta tana
dariya kamar ta gatse.
"Ibrahim kai kuwa wannan na mijin ne? ka
shirya mu yi aure? Ibrahim ban san ko lokacin
wa an ka kenan yanzu ba, amma ni ba nawa
lokacin ba kenan"
Bai daga daga durkusonsa ba haka nan bai
rage tsayin hannunsa ba.
"Idan har kin yarda zaki aure ni to yau ba
zamu kwana ba sai da auren mu. Na shirya
mana duk wani abu na aure, daga madauran
aure irin na addinin mu har dan karamin biki na
masoya masu gudun hijira domin tsira da
soyayyarsu. Kina so na Farida ki yarda ki hada
zuciyarki da 'yar uwarta. Na yarda da ba
hakarkarina kawai aka diba aka yi ki ba, kai har
6arin rabin zuciyata da na rasa shine 6arin da ke
cikin kirjinki, Farida ki bawa zuciyar nan dama
ta hade ta zamo guda kamar sauran
takwarorinta. Duka abin da nake gaya miki babu
د
58 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
tsari ko shiri in kin kalli idanuna zaki gansu a
cikinsu da gaskiya"
Ta gama narkewa da yarda, amma saura taki
daya ta mika wuya.
"Menene ya baka shawarar irin wannan
yanke hukumci Ibrahim?"
Ya kada kai.
"Sati guda da nayi cikin takunkumin da kika
kakaba wa alakarmu, na karu da abubuwa da
dama kan martabar soyayyarmu. Farida tunda
uwata ta mutu na rayu na san zan iya rayuwa
babu mahaifiyata. Rashin 'yan uwa daga wurin
iyayena baya sanya ni in ji ko gezau, haka nan
zaman makaranta na nuna min cewa zan iya
rayuwa babu mahaifina, amma zaman sati daya
babu alakar ko magana dake ya nuna min cewa
ba zan iya rayuwa babu ke cikin rayuwar ba.
Farida ni na san abin da na ji kuma na gani...
Na san yadda nake jin an daba min wuka a duk
lokacinda na kira ki baki dauka ba, ba ni da
sukuni. Farida ina son ki fiye da komai na, ki
bai wa wannan soyayya dama ta nuna miki
kanta ta hanyar yarda da aurena. Farida idan
zama da iyayena na nufin dole rabuwa dake to
na gama zama da babana, ban san ke na ki
bangaren ba...Zaki aure ni masoyiyata?"
Tuni kalmomin suka fi karfin kafar Farida
inda ta sami kanta durkushe a gabansa tana
kuka yadda yake yi a lokaci guda tana kokarin
murmushi don fayyace dadin da take ji. Tana
wani gyada kai da sauri-sauri na zaukin shauki
59 Mafiyan Masoyа Rahma AbdulMajid
ta mika masa hannunta inda ya sanya mata
zoben tana fadin.
"Ina son ka zan aure ka Baby... Ina son ka
da yawa"
Ibrahim wanda ya kara gyara gashin kansa
ya rage shi matuka, yana sanye da farar kwat da
farin wando da bakar shet da aka dora wa farin
tai ya soke hannun amaryarsa a kafada wadda
ita ma ke sanye da farin kayan auren turai jim
kadan bayan fitowarsu daga masallacin
malamin da ya daura musu aure a sunnance,
babu kowa baya da su biyu da suke shan bikinsu
na zagaye gari. Bakinsu ya ki rufuwa, suna tafe
suna rera wakokin amarci su biyu ko dai
Ibrahim na amshi Farida na bayarwa ko kuma
shi yana yi tana amshi ko suna yi tare, suna ta
samin gaisuwa da taya murna daga daidaikun
jama`an da kan wuce su gamu da su kuma su
san me suke ciki, wasu na ganin honeymoon ne,
wasu kan tausaya musu a matsayin amare
marasa jama'a masu matukar son juna. Wata
mata mai alamar tsufa musamman ta wuce ta
basu fulawa suka yi ta godiya, suka kara kan
wanda suke rike da ita.
Bayan Ibrahim ya fuskanci gajiya da bacci
tattare da amaryarsa a lokacinda suka kusanto
gida sai ya sanya hannayensa ya kwashe ta
musamman ma da kankarar dake zuba tace
bisimilla ya zura a guje da ita suka shige gidan
nan da kamar wadda Farida ta san zata yi
60 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
amarci a ciki ta zabi mai kyawu da tsada na kin
Karawa.
*
Farida wadda ta bar mijinta dunkule cikin
farin bargo yana bacci tana ta wake-wake da
muryarta mai zaki cikin gidan wanka wanda
gilasine zalla da wanda ke dakin ka iya hango
zuban ruwa da dodon mai wanka a ciki. Kamar
yadda mai wanka ke hasashen dakin.
Ta fito daure da farin tawul da wani kato
irinsa da tayi gwaggwaro wa gashin kanta, bata
ga Ibrahim a kan gado ba, babu kuma duriyarsa
a dakin. Tayi murmushin jin dadi da walwala
sannan ta soma kiransa da "Baby where are
you?" bai amsa ba amma tana jin kamshin soyesensa a kicin don haka kicin din ta dosa.
Ko ina akwai na`urar zafafa wuri, watakila
hakan ce ta bashi damar fitowa daga shi sai
gajeren wando da farar singilet. Ta yi sanda ta
je ta rungume shi ta baya a yayinda ya mai da
hankali yana soya wasu abubuwa, ta kwantar da
kanta cikin tsakiyar bayansa.
"Bally me kake yi da sassafen nan
maimakon ka kwanta ka kara hutawa?"
Ya dan jingino kansa bisa nata yana dan
murmushi da lumshe ido.
"Me kika san ina dafa miki? In kin fadi
daidai zan baki kyautar kiss guda uku"
Ta lumshe ido.
"Kana yi min jajjagen dodon kodi ne da
'ya'yan basil"
ご
61 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ya juyo ya rungume ta da sauri.
"Kin ci wallahi, ashe kina tune?"
Ta lunshe idanunta.
"Biya ni goro na kawai".
Ya sanya bakinsa a nata shima bayan ya
lumshe idanunsa ya sunbace ta na tsayin lokaci
inda nunfashinta ne kawai ya ke musu jagora.
Ya janye bakinsa a hankali kamar ba don yana
so ba, ya tsayar da idanunsa kan nata yana
kiftawa da sauri irin na mai karaya.
"Farida daren mu na jiya tare shine dare
mara takwara da na taba yi a rayuwata kuma ina
jin ba zan sake kamarsa ba"
Ta rike tsinin karshe na hancinsa.
"Zamu maimaita shi duk iya tsayin
rayuwarmu Bally"
"rayuwa dake Farida iyakar aljannata kenan,
ina ciki wani yanayi da bana jin wani ma'auraci
ya san da shi..Farida ina jin dadi, kin san me
haka ke nufi, makwanci na dake daya, jikinmu
daya, kicin din mu daya, toilet din mu daya
komai namu daya, a yayin da a da ina zaton ko
muryarki na ji a waya karshen dadin duniya
kenan"
Ta manna kanta a kirjinsa.
"Na dade da hango hakan shi yasa ka ji na
sallama zan rabu da kowa da komai don na
kasancc tare da kai"
Ya ciro kanta ya sake tura bakinsa cikin nata
ta amsa masa na zirin lokaci, sannan a wannan
lokaci ita ce ta zare bakinta ta zura masa ido.
Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"Kayi alkawari duk rintsi duk tsanani zaka
rayu da ni ba zaka rabu da ni ba?"
Ya ruko fuskarta cikin manyan tafukan
hannayensa.
"Farida ina son ki ina son ki da matukar
yawa, ina son ki fiye da dukkan rayuwa, ba wai
alkawari kawai nake ba, ba zan iya rabuwa dake
ba ne muddin ba zan iya rabuwa da raina ba. Kc
ce ya rage ki yi min alkawari, amma ni na gama
yanke wa kai na hukumci. Dake zan rayu iya
rayuwarmu Farida"
"Baby ba zan rabu da kai ba, ba zan taba iya
rabuwa da kai ba, kai ne rayuwar da nake jin
zan iya yi zan iya bayar da duk wani abina
domin na same ta"
Ya sake matso da bakinsa zuwa nata amma
ta tare shi da yatsa.
"Ban da dodonkodi na kada ya kone"
A guje ya juya da yake ya ji kamshin ya
soma sauyawa. Ya jujjuya sannan ya dauko abin
kwashewa. Farida ta soma kokarin taya shi,
amma ya ruko hannayenta biyu ya tura su
kirjinta.
"A`a! ni a doka ta amarya ta bata aiki har sai
ta ce na gaji da hutawa bayan a kalla kwana uku
sai mu zo mu fara tare, amma yanzu har gado
abinci zai dinga bin ta"
Ya sure ta a guje ya mayar da ita daki ya
ajiye ta kan gado.
"kada warin abinci ya bata min wankan ki,
zauna ki caba min kwalliya, kin ji?"
A
R
D
こ
63 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ya surħbaci goshinta sannan ya fice da sauri
daga dakin.
Ta nutse cikin bargon tana more wani dadi
da zuciyarta ke ciki, dama ashe haka aure yake,
auren ma na masoyi? Bata taba jin abin da take
ji ba kamar yau, duk wani nauyi dake kanta da
damuwa ji take sayau ta sauke shi, ga
mamakinta sai ta ji bata tuna matsalolinta na
cikin gida, hasalima ta mance da barazanar
mahaifinta.
*
Cikin wata daya Farid ya sauya ya zamo
babban mutum. Tunanin sa ya sauya daga na
daki daya zuwa na tunanin gina kansa. Yana
zaune yanzu a gidan kasa mai daki biyu
kowanne da bayan gida, da falo mai dauke da
wani loko da ya ketara zuwa kicin da wani
karamin falo na cin abinci, sai toilet na bakin
falo da cikinsa babu abin da ya wuce wurin
wanke hannu da kaskon tsuguno da ma`ajiyar
sabulu. Dukan gidan babu inda ba a yi masa
shirin da ya dace da shi ba. Tun daga falonsa da
aka yi wa haden fari da bulu, dimadiman
kujerunsa masu matasan tada kai bulalene masu
ratsin fari kamar labulen da aka sanya a falon.
Haka dardumar falon ita ma fari da bulune aka
zana katon gida a jikinta da shi, akwai kayan
kallo isassu duka a jikin bango a rataye kama
daga talabijin din har manyan sifikun yada
sauti, sai iya kwandishan katuwa dake zaune da
Kafarta, haka dakuna suke da kicin kowanne
64 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
gyaransa mai tsada da kyau da tsari. A waje
kuwa akwai inda yake ajiye motoci guda biyu,
wato Honda Accord 2008 model wadda take
tasa da Toyota Camry ta Mahdi wanda shi ma
yana tare da Farid a wannan gida bayan da shi
ma ya sami aiki da kamfanin sadarwa na Zain.
Suna zaune a gidansu cikin kwanciyar hankali
har sun fara aiwatar da abubuwanda da suke son
yi a rayuwa. Domin a yayinda Mahdi ya gabatar
da shirin aurensa har aka sanya shekara mai
kamawa, shi kuwa Farid ya kasa nuna ko da
kulawa ga kowace irin mace, ba kuwa domin
komai ba sai don yadda ya fara fayyace
matsayin Farida a zuciyarsa. Babu yadda za a yi
ya ci gaba da cewa ba son Farida yake ba, ya
damu da ita ta inda baya iya mantawa da ita a
duk tsayin kowace rana, ya damu da rashin
ganin ta da rashin jin ta. Ya dai dade da fahimta
ko a ofishinsu babu wanda yake da hurumin
tambayar ina Farida take don haka ya dena
tambaya koda kuwa ba wai ya san inda take ba.
Tun washegarin mika masa aiki da ya gan ta.
Ya damu matuka yana kewar Farida komai yake
yi kokari kawai yake, amma bisa gaskiya yana
son ganin Faridar a gabansa, baya ganin ko
wace mace ta kai ya Faridar ballantana ta fi ta,
bai san lokacinda ya dena ganin bambancin
asali da dukiya tsakaninsu da Faridar ba domin
ba kokwanto yake ko soyayya tsakaninsu zai yi
wu fata yake ta yiwu. Ya dauki Kalmar da
Faridar ta taba fadi gaban babanta na cewa ba
L
R
=
65 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
shi aiki zai taimaka ta manta da Ibrahim a
matsayin ruwan dafa kansa, domin a tafsirinsa
karara wannan kalma na nufin soyayyar Faridar
ne gare shi, sannan a sharhinsa mutane irin
Faridar masu jin tausayi da fahimtar dan adam
da kololuwar wayewa basa iya daukan
bambancin arziki a matsayin hujjar çancanta
kamar yadda suke girmama kwakwalwa mai
nunfashi wadda baya shakkar yana da ita, don
haka ne ya zage damtse yake aiki da jini da
tsokar kwakwalwarsa don ya ga albarkacinta
kamfanin Na`ibi ya sami wata ciccibą da bai
taba samu ba. Kuma lallai ya kai ga nasara
domin taswirar da ya gabatar a kan yadda za a
inganta samar da wutar lantarkin kasar Liberia
wadda yaki yayi wa ninkaya ita ce ta sanya
kamfaninsu ya doke na mutane irinsu
AbdulHadi wurin samun dillancin samar da
kamfanin wutan da zai ja ragamar aikin na kasar
China, abin da ba a taba samun kamarsa wurin
daga farincikin Na`ibi Bici duk fadin shekarar
nan ba, domin ba kawai nasarar samun wannan
kwangilar dillanci ba, samun kayar da Abdul
Hadi wanda yake gadajjen abokin gasarsa
wanda shi ma yayi ta barin kudi don samun
wannan kwangila don ko ba komai ya doke
abokin hamayyarsa amma suka samu suka kayar
da shi cikin ruwan sanyi. Hakan ta sanya Na` ibi
cikin farin ciki ya zaro mukullin sabuwar jeep
din Highlanda ya mika wa Farid tare da kyautar
kudi Naira milyan biyu. Kyautar da ta dada
66 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
shigo da Farid din taro wanda tuni ya kusa
hattama gidansa da yake son ya sanya
mahaifinsa ya zauna ciki kafin yayi aure. A
yanzu yana jinsa matashin mai kudi da tsari da
ilmi da babu wadda ta fi karfinsa muddin ajin su
Farida ce. Abin da ya hana shi iya zamowa na
hannun daman Na`ibi fiye da Wilson kamar
yadda yake fata shine kekashe kasar da yayi na
cewa shi fa ba zai yi wasu aiyuka da suka
haramta a dokar neman kasuwa wai kawai don
ya kasa wanı a kasuwa ba, don haka iyakarsa ga
Na'ibi shine aikin da kwalkwalwarsa ke iya yi
wa kamfani musamman da kamfanin
AbdulHadi suka soma zawarcinsa ta hanyar
kara masa albashi domin su same shi.
こ
67 Mafiyan Masoya Rahma Abdul Majid
Uku
Na'ibi Bici wanda ke sanye da irin shigar da
aka san shi da ita, wato riga shet da wando ya
dora kafa daya bisa daya yana shan lemo a daya
daga kujerun ganawa da baki na gidan ministan
makamashi wanda suke 'yan asalin kauye daya
sai tafawa suke suna dariya a duk hirar da suka
yi don jin dadin nasara. Wannan ziyara ta zo ne
a dalilin kawo kason ministan da Na`ibi yayi
kan ruwa da tsakin da yayi na sama musu
wannan kwangila. Ministan wanda yake sanye
da doguwar riga fara sol mara hannu ta shan
iska ya zauna rike da wani dan littafi yana
dubawa yayi magana kafin ya dago kai.
"Haba Munir! Ai ba sai ka yi wani abu na a
zo- a gani ba ni ma ina da irin tawa bukatar"
Sannan ya dago ya dube shi.
"Da me zaka fi Hadi da zan damu in
taimake ka in bar shi? Dukan mu fa abokai ne
kuma 'yan kauye daya kai ma ka san dole ni ma
akwai tawa alfarmar"
Na`ibi ya ajiye kofinsa sannan ya daga kai
sama.
"Месе се bukatar Honarabul minister?"
Bai amsa masa ba a lokacinda wani saurayi
ya fito. Yana sanyc da rigar bulun yadin dinkin
shan iska wando iya gwiwa haka rigar ma mai
68 Mafiyan Masoy я Rahma AbdulMajid
hannu iya gwiwa. Duk da wankan tarwada ne
amma gashin kansa kwance yake duk da ya aske
mafi yawa, fuskarsa na da matukar kyau da
alamar hutawa kamar sauran sassan jikinsa.
Yana da yanayi na masu satkin kai musamman
yadda ya rusuna ya gaida Na`ibi sannan ya dubi
mahaifinsa ‘na`am baba?"
"Ka san ko wanene wannan?"
In ji minister wanda ya nuna Na`ibi.
Yaron yayi murmushi sannan ya kada kai.
"Ban san shi ba popsie"
"Wannan shi ne ya haifi Farida"
Kallon razana sannan fuskar farin ciki ta
bayyana da fararen hakora sannan ya sake
rusunawa ya kara gaida Na`ibi wanda shi dai
nasa amsawa. Minister ya dawo ga Na`ibi bayan
da ya dafa dansa wanda a yanzu ya karaso kusa
da shi.
"Na`ibi wannan shi ne dana Abdul Azeez.
Dan daa haifa daya kenan da matata
marigayiya Daliya 'yar kasar Moroco wadda ta
rasa ranta a fashewar jirgi a Locarbie. Ni na
raini abi na don Allah ya jarrabe ni da son sa
yadda Ya jarrabe shi da son `yarka Farida. Вa
don son kai ba da gaske ina gaya maka ya fi
kowace zuri`ata nutsuwa, ya tsaya yayi karatu
don likita ne, duk wata hatsaniyar duniya bata
dame shi ba, mata ko shaye-shaye ko rashin
da a duk kuwa da shagwaßa shi da nayi. Bana
so ya taba rasa abin da yake so domin bai tabа
son abin banza ba, cikin abubuwa masu nagarta
4
2
69 Mafiyan Masoy a Rahma AbdulMajid
da ya taba so a duniya har da 'yarka Farida. Bai
san ka ba bai san ta ba. Jaridar Ovation ne ya ga
hoton ta ranar bikin fitarsu daga jami'a shi
kenan ya kasa sukuni ban da na Farida. Da yak
baya boye min komai sai ya gaya min abin a
ke damun sa kuma nayi alkawarin ya sa ransa a
inuwa zan nemo masa ita. Gaskiyar lamari
saboda shine na neme ka har muka yi abokanta
kuma nake damuwa da faranta maka rai. Fatana
kuma fatansa ka hada shi da Farida"
Na'ibi ya mike cikin mamaki inda ya fadi
wata kalma cikin turanci wato 'this is material!'
"wannan yaron danka ne?Abdul Azeez kana
son 'yata Farida?"
Ya sunkuyar da kai cikin kunya yayi dariya.
"kai ne irin sinadaran da nake so 'yata ta so
1 kuma na samu"
Ya kamo hannunsa don su fita.
Zo nan fana, zo nan...wannan
kyakkyawan saurayi. Zo mu je mu yi magana
irin na maza"
A filin kwallon Kwando da ke gidan suka
tsaya suna fuskantar juna inda Na`ibi ya soke
hannaye a wando ya ke tambaya.
"Gaya min gaskiya wane irin so kake yi wa
Farida Abdul Azecz?"
Ya karkata kai irin na me matukar jin abin
da yake fada.
"I love her dearly! Idan har zan hadu da ita
ta so ni mu fahimci juna tuni zan soma tunanin
20 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Karashe sauran ranakun rayuwata da ita. Ina son
ta shine gaskiyar lamari baba"
Cikin wata annishuwa da ba ko yaushe
Na`ibi yake yi ba, ya sake dora hannu a kan
kafadarsa suka fara tafiya.
"ina mai tabbatar maka Farida zata so ka
domin irinku take so... zan baka wata satar amsa
da zata isar da kai ga Farida har cikin zuciyarta.
A yanzu tana Berlin kuma tana fama da kadaici
bayan rabuwarta da wanda ta so kuma suke son
su yi amfani da ita wurin karya ni. A yanzu
zuciyar Farida ta koma budurwa babu kowa
ciki, zaka iya hanzartawa ka shiga ciki"
"Ta yaya zan shiga ciki? Na je Berlin na
same ta... zan iya zuwa yaushe?"
Ya Ambato zantukan cikin zumudi irin na
wanda ciwon so ke gararamba a zuciyarsa.
Na`ibi ya kama hannunsa ya tafa da shi.
"that's my boy. Haka nake so... ka isa
Berlin ko gobe ne, zan fara shigar da kai in mun
yi magana yau. Ka yi ta maza ka shige ta ku
saba zata so ka na san `yata"
Suka sake tafawa yace 'mu koma wurin
mahaifinka mu ba shi albishir'. Suka koma ciki
hannun Na`ibi na kafadar yaron nan wanda ya
kasa sakewa da ka gan shi ka ga rainon bature
amma mai ladabi.
Farida zaune kan gado Ibrahim na kwance
kansa bisa cinyoyinta tana wasa da yatsun
hannunsa na dama suna hira cikin raďa kamar
71 Mafiyan Masoya Rahma Abdul Majid
akwai wani a gidan bayansu. Wayar ta tayi kara
ta duba lambar sannan ta yi masa alama da ya
toshe baki wato babanta ne. ya toshe baki. Haka
suke yi wa junansu duk lokacinda mahaifin
daya ya bugo.
"yaya Farida yau tun safe ba ki neme ni ba
ko teďt?"
Ta dan bata rai.
"ina dan ciwon kai ne Father"
"Ina ga ya kamata na zo na gan ki ko....?"
Ta katse shi da sauri.
"No father, ina so na zauna da kai na ni
kadai har sai na huce
"Sai kin huce me?"
Ta dora hannunta kan fuskar Ibrahim tana
dariya.
"har sai na huce na mance da Ibrahim"
Ko a muryarsa zaka iya jin sa'ida a yayinda suke tintsira masa dariya.
"Haka ne `yata kina da gaskiya ko ni zan so
kada ki shigo sai zuciyarki ta zamo ko haduwa
tayi da Ibrahim ba zata ji komai ba, amma ina
kewar ki, ina son ganinki, mamanki ma haka
tace tana so mu zo nan mu hadu tare"
"Father ka bari duk zan gaya muku
lokacinda nake son mu hadu, ina kewar ka
father, but na fi so na daure na gama wannan
zaman ina samin nasara a haka"
"Shi kenan ba komai. Amma akwai wani
yaro da zan so ku hadu, wannan bana so kiyi
min musu, dole zaki iya haduwa da shi matashi
72 Mafiyan Masoy a Rahma AbdulMajid
ne kamar ki da zaki iya raba bakin cikin ki da
shi, ku zauna ku yi hira ku fita tare....In gaya
miki gaskiya, yana son ki son da bana jin wani
ya taba yi miki. Sunan shi abdulAzcez dan
ministan makamashin Najeriya Lukman Nura.
Yana da duk siffar da `yar Na'ibi zata iya son
shi, sai dai ba zan miki dole ba, kina bukatar ki
gan shi tukuna ku daidaita... in kin so shi zan yi
farin ciki, amma ki gan shi tukuna, gobe ina so
ki je ki taro shi da yamma"
"Amma father..."
"ban ce kiyi min musu ba, kawai ganinsa
zaki yi in bai yi miki ba ai ba dole ko?"
"To father"
Suka Karasa hira jikinta a sanyaye har ta
ajiye wayar. Ibrahim ya taso ya rike ta
"Lafiya na ga kin sauya? Yana zuwa ne?"
Ta kada kai.
"Father ba zai kyale ni nayi rayuwata ba...
Wai wani Abdul Azeez dan ministan
makamashi yana so na, ina ga shi yace da gayen
ya zo nan ya takura min, don yace yana zuwa na
je na dauko shi a airport, mu fita tare, mu zauna
tare har na ji ko zan iya son sa mu fahimci juna"
Ibrahim yayi shiru yana kallon kasa har na
wani lokaci zuciyarsa na so tayi abin da ta saba
na neman yin abin da ya dace.
"Yaushe kika ce zai zo?"
"Gobe zai zo
Ya mike tsaye.
A
ا
73 Mafiyan Masova Rahma AbdulMajid
"Kenan ya kamata na dan bace daga gidan
nan muna magana a waya har ya tafi don kada
ya gan ni"
Da kanta na wani gefe ne, amma yadda take
juyo da shi don ta kalli Ibrahim na nuna wata
fusata da bata taba yi ba tunda suka yi aure,
wani tiriri na so ya kona zuciyarta.
"Me na ji ka cc?"
Ya dada kwantar da murya
"Wai da ina so ne na dan boye har ya tafi
don kada.."
"Ibrahim! Har yau kana shirin 6oye aure na
da kai kamar wadda kake kyara
Ta mike tsaye a kan gadon
"Me kake nufi? Kana nufin ko yaushe ba
zaka taba zamowa na miji ba. Har a fagen daga
ba zaka yarda ni matarka bace. Ibrahim kana so
na kuwa? Wane irin..."
Kuka ya kwace mata ta fice daga dakin da
gudu. Ibrahim yayi jifa da bargon da yaké kan
sa ya tashi yana kiran ta amma bata amsa shi ba.
Ya iso kicin inda ta juya ta jingina kanta da
bango tana girgiza. Bai karaso kusa da ita ba ya
tsaya a rikice a galabaice.
"baby please, ba ina nufin abin da kika zata
bane... na san bakya shakkar ina son ki fishi ne
kawai amma...
Ta juyo a fusace.
"Ka rabu da ni kawai Bally. Ka rika ka nuna
min ko wancne kai, nayi kuskure, ina son auren
na miji ne mai tunani irin na maza ba mace
74yan Wasoya Rahma AbdulMajid
kamata ba... tsoro ne ya sanya har yau
iyayenmu ke zaton zasu iya raba soyayyarmu
duk da goyon `yancin da suka yi mana".
Duk abin da take cewa Ibrahim kara kusanto
ta yake yana kada kai.
"Bana jin tsoron kowa sai na Allah sai na
Gacin ran masoyiyata. Farida bana son nayi abin
da zai tayar da hankalin mu a wannan lokacinda
ya fi kowane lokaci dadi cikin rayuwarmu.
Farida mahaifinki ko mahaifina ina jin zasu iya
jin sassaucin kiyayyarsu'ga auren mu da za a се
muna da iyali, yau in Allah Ya azurta mu da
haihuwa ko don saboda wannan jika nasu zasu ji
suna kaunar mu da kaunar abin da muka basu.ki
tuna basu da yawan 'ya'ya duk da suna so. Shi
yasa ni a so na mu hakura mu boye auren mu
har sai mun sami arzikin haihuwa sannan mu
fito musu da gaskiya, amma in fitowata yanzu
zata faranta miki rai ki kara yarda da ina shirin
sadaukar da rayuwata kan soyayyarki zan fito
ko yanzun nan"
Ta juyo kamar da alamar ta sami sassauci a
zuciyarta idanunta kan Ibrahim.
"Kana shirin zama Daddy Bally?"
Shi ma idanunsa a kanta cikin tausayawa.
"Ina shirin zamowa Daddy na 'ya'ya ko
nawa ne muddin zasu zamo 'ya'yan Farida ta"
Ya kamo hannunta ya zuba kan kirjinsa.
"Farida ina son 'ya'yana ina son mu sami zuri'a, ina son in zamo Daddy cikin gaggawa,
ko ba don su Father da popsie ba ina son na ga
75 Mafiyan Masoya Rahma Abdul.Majid
abin da Allah zai bamu a matsayin arzikin
soyayyata ni da Farida. Please Farida let me
have a child with you"
Ta fada jikinsa ta rungume shi kamar zata
cakuda namansu wuri guda.
"Mu je mu samo guda ne?"
Ta gyada kai. Ya ciro ta daga jikinsa yana
duban ta.
"Kin shirya?"
"Ina shirye kuma ina kan layin masu iya
samu a yau"
Ya sure ta da sauri.
"Bari mu gani"
Ta rataye hannayenta a wuyansatna dariya
suka koma daki.
Da yammacin washe gari Farida ta sanya
wandon jeanse bulu shar sannan ta sanya wata
farar shimi mai kauri ta dora shet ja mai dogon
hannu sannan ta sanya wani takalmi shoe mai
fari wata `yar jaka kamar ta sanya waya fara
wadda ta rataya ta tun daga kafadar hagu zuwa
kugun dama. Ta bayyana a matattakalar da ke
hada gilasin da falon su inda lbrahim ke tsaye
yana kokarin kunna talabijin.
"Na shirya".
Tace a yayinda ta fan jingina da bangon
tana hango shi. Ya juyo ya kale ta sama da kasa
sannan yayi dariya.
"Kin yi kyau amaryata"
76 Mafivan Masoya Rahma AbdulMajid
Ta juya zata koma daki a fusace kamar
yadda ta fito a fusacе.
"Ina kuma za-ki?"
Ya tambaya a rikice don ya san halin
futsuwar amaryar tasa.
"Zan je na sauya, don ba cewa na yi ma
in yi kyau ya gani ba
Ya kamo ta da sauri ya dawo da ita.
SO
"sam! Ba nufi na kènan ba. Ko wane lokaci
kyau kike min, gara ki je ki yi musu ya kwala
mana.Farida bana shakkar ki ba zaki taba yin
shirin da ba zai miki kyau ba ko da ganye zaki
daura, ni kawai Allah Yayi min sa`a ne kike so
na amma da aure sai kin yi shela kafin ki zaбa.
Zo ki je ki dauke shi, ki kai shi masauki, sannan
ki dawowa masoyin ki mai jiran ki"
Ta sunbace shi na al`ada ba don ana cikin
farin ciki ba domin bata son fitar narr da ba don
ya matsa ta ba.
A wajen harabar filin jirgi take tsaye bata
san kamanninsa ba bata kuma san koda sunansa
ba domin har ta