domin
manufarsu ta soyayya ta fi tamu ta kiyayya...
Farida ta kubuce min kamar yadda Ibrahim ya
kubuce maka, sun gane duk makircin da muka
shirya musu kuma a halin yanzu suna tare da
junansu a matsayin ma`aura babu abin da nake jin
zamu sake iyawa in ba zamu kai lamarin ga abin
da be kai ba wato tsine musu da cire su daga
sunayenmu. Kafin mu kai haka nake son mu dawo
bic. Mun yi nisa da yawa ya isa haka ya kamata
mu dawo..."
Ya sake mikewa tsaye ya fuskance shi da
natsuwa amma babu murmushi.
"Na yarda wukata....... ina so kai ma ka yar
da taka mu bar wannan gaba mu sake kulla zaman
lafiya a karo na biyu kuma a matsayin surikan
juna ko ba don farin cikinmu ba don farin cikin
'ya'yanmu. Ga hannuna"
.........ya kura masa ido cikin tafasa bai kalli
ko inda ya miko hannunsa ba ballantana ya mika
nasa.
"Kana tune da cewa ka kai matsayin neman
ran 'yata Farida"
"Ka yafe min an sami babban kuskure a
nan...Farida ta yafe min"
Ya kada kai..
"Ba zan sake sanya hannu a hannunka ba
Andul Hadi ka janye duk makircinka"
170 Mafiyan Mas ya Rahma AbdulMajid
"Comon! Daurewa za ka yi...ni ma ba wai
don bana jin haushin ka ba ne, amma na daure don
hakan ya fi alheri..."
Ya jima da hannunsa tsaye, amma da ya ga
babu niya daga Na'ibi na sanya hannu sai ya janye
yayi murmushi.
"Farida ta auri Ibrahim cikin sunnar ma`aiki
har suna shirin samun karuwa. Ina sake rokon
dama a wurinka na ka yardar mana da ita a
matsayin matar dana, kuma zan yi kokari na ga
mun zo wurin ka ni da shi don yin baiko a
al'adance....zan ba ka lokaci kayi tunani idan har
ka huce sai ka gaya min waya na zo na same
ka"
"Ka san ina Farida take?""
Naibi ya kawar da amsar wancan dogon
zance.
"Tana tare da mijinta ai...kana son ganin ta
ne?"
"Ka ce ta zo ta gan ni ina da magana da ita ta
Karshe kafin na ba ka amsar bukatarka"
"Za a yi haka na gode.... Amma ka daure ka
yi tunani, na biya wajibi na na sauke
nauyina...mu ne yau ba mu ne gobe
ba.... ya`yanmu ba na`urori ne da za mu ci gaba
da tsara su ba... na bar ka lafiya"
Yana ficewa daga falon ya dauko wayarsa ya
latsa lambobin Wilson.
"Hello Wilson meet me at home now'"
i
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
AbdulHadi na bayan motarsa yana murmushi
yana kada kai ya ciro wayarsa ya latsa lambobin
Farida.
"Na`ibi ba zai sauya ba"
Ya ambata kafin ya kara wayar a kunnensa.
Can ta dauka.
"Farida mahaifinki na son ganin ki...Eh...to
ya ce ba shi da magana da ni har sai ya gan ki...ki
daure ki je yau don na san mutumina yana da
taurin kai wani lokaci wani lokacin kuma yana da
saurin sallamawa. Watakila idan ya gan ki ku
sasanta in kun gama na ji yadda kuka yi, amma ki
daure ki je ki same shi yanzu...shike nan, ba ni
mijin naki...Bala...to yaya kuke?...ka lallashi
matarka ta je ta ga mahaifinta, na san ba zai iya
sauya ta ba idan ya yi magana da ita karshe zai
sallana, amma a halin yanzu bai bar kofar wata
tattaunawa tsakanin mu ba..: to shi ke nan""
*
Wilson ya karkata kai yayi murmushi ya sosa
kasumbar da ta dame shi da kaikayi.
"Ranka ya dade za ni in yi aski....idan ita Anti
Farida ta zo ta kuma dage a kan tana son ka
amince da auren, ka amince mata ka kuma a
gayyaci angwayen. Za mu koya musu darasi na
har abada tunda in an bar su zasu yi taurin kai ne
suma har abada"
Na'ibi ya kashe tabarsa ya juya kujera.
"Je ka yi askinka, amma ka sani bana son
kuskure domin ba zan taba amincewa har ga
zuciyata da auren kasada ga dukiyata da sunana da
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Farida ke so ba, tunda kuwa Hadi ya shigo wasan
gadan-gadan ina son mu yi bugun karshe"
"Ka taba kama kuskure a kowane kudirina
ranka ya dade? Ballantana a damar karshe?""
Shigowar Farida da karfi ya karar da maganar
inda duk suka zuba mata idanu. Tana rike da
hannun kofar yayinda babu walwala ko gaisuwa ta
ce 'ga ni Dady'
Wilson ya yi tari ya rusuna ya gaishe ta babu
murya sannan ya juya ya fita a kaikace
kasancewar bata bar jikin kofar ba sai da ya bar
falon sannan ta karaso ciki ta mayar da kofar
Ta sunkuyar da kai tana tsaye a gaban sa gab
da gab yanzu
"Ga ni Father"
"Sannu da zuwa, sami kujera ki zauna
maganar mu ta karshe се"
Ta ko amsa umarninsa ta zauna, sannan ta
dago idanu don sauraro. Ya nisa ya miko hannu
ya dauki wata 'yar takarda don kawai yayi wasa
da ita lokacin magana, sannan ya fara.
"Kin gudu Farida zuwa wurin wasu wanda
kika san ban so duk kuwa da barazanar da suka yi
wa rayuwar ki baki daddara ba kika bar ni ni me
fafutukar kare lafiyar ki a matsayin uba.... Sai dai
ba wannan ne ya dame ni ba, hasalima ina son in
sanar dake cewa lallai ina mai ba ki hakurin
abubuwan da na sakaye miki lokacin da ba ki da
lafiya. Wannan ya biyo bayan dabaru na kare
lafiyar taki ne ba cutar dake ba, amma ir baki ji
dadi ba ina mai baki hakuri kan
hakan....tambayoyina ba su da yawa guda ne uku
173 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
kuma ina so ki ba ni amsa tunda ga kwalkolin
zuciyarki kuma a sanin cewa karo na karshe
ne tambaya ta farko ita ce kina da masaniya
cewa A. Hadi ya zo nan kuma ya nemi in ba ki
damar auren dansa. Kuma kina jin dadin haka?"
Ta dago tana ci gaba da wasa da yatsunta.
"Yes father"
"Fine! Tambaya ta biyu....duk da neman
salwantar da ranki da alaka da iyalin A.Hdi suka
kusan yi wanda ya nuna miki manufarsu akan
komai kin sake amincewa da auren Ibrahim a karo
na biyu kuma zaki zauna da wannan barazana?""
A nan ma ta sake dagowa.
"Father Bally ba shi da hannu kan abin da ya
faru kuma ka sani har rabuwa yayi da mahaifinsa
kacokam domin wannan lamari.... kamar yadda
kace kai ka boye min gaskiyar hakan bayan na so
in sani.... Ke nan ba shi da wata barazana gare ni
muna son juna zamu zauna da juna'""
"Tambaya ta karshe..."
Yanzu cike fuskarsa take da karin walwala da
murmushi.
"Kun san cewa ni da A. Hadi ba za mu taбa
zamowa surukan arziki ba haka nan ba za mu
zamo kakannin arziki ba ga zuriyar ku amma kuke
shirin dauko wannan alaka don kanku ba kwa
duba zuriyarku?""
"Father... kun taba zamo wa abokan arziki kai
da A. Hadi kuma bai bawa duniya mamaki
zamowar ku makiya ba... ke nan sake zamowar
ku masoya nan gaba saboda mu abu ne me
yiwuwa ba kuma wani mamaki ko haramci ga
174 Monyan Masoya Rahma AbdulMajid
bakan.... zamu yi iya kokarin mu don ganin
hakan ta sake faruwa a dalilin aurenmu.... wani
Karin haske akan ko mun so kanmu ina jin ba ka
nufin wannan magana da kyau.. domin a saboda Kiyayya kun taba mantawa kuma da bukarun
ya`yanku na soyayya kuka je ko wane nisa wajen
neman rabuwarmu... ina jin don mun fauwala
rayuwar soyayya kan kiyayyarku kuma mun koya
wa 'ya`yanmu baya nufin son kai in har na ku bai
nufi son kai ba.... ka duba father in dai ga zuri`ar
da zamu samar ne, ku kakanni ne baku son juna,
mu ko iyaye ne muna son juna. Duk da tambayoyi
uku ka ce zaka yi min ke nan kamar ka gama
father, ina so in tabbatar maka da cewa mun
shirya rungumar koamai ba ma tambaya kawai ba
don mu zauna da junan mu cikin soyayya ni da
Bally...please I want you to bless that father"
Ya nisa sannan ya katange dawowar
nunfashinsa da murmushi ya kuma kra mata ido.
"That's my girl... ki cewa A.Hadi da Ibrahim
ina son ganinsu tare gobe da misalin karfe bakwai
na yamma don su nemi aurenki a wurina... zan
kuma shirya musu liyafa irin wadda ta dace da
surukai na"
Ta zaburo ta kuma zaro ido amma ya tare ta
da tagumi cikin yalwar murmushi.
"Kada ki damu in har sun iya zuwa gidana me
zai hana in ba su 'yata zan bayar dake Farida"
Ta rungume shi da murna har da hawaye ya
amshe ta yana dariya 'kada ki damu `yata ki je ki
gayyato su kada ki yi latti, ok?"
A
i
175 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Da zumudi ta sake shi za ta zaro waya amma
ya katse ta
"Um-um! Not on phone... ki je har inda
masoyi kuma mijinki yake ki yi bikin wannan
farin cikrda shi kin ji?""
"Haka ne father sai na dawo..."
Ta sumbace shi sannan ta ya yi Jakarta ta fice
daga wannan majalisa.
Ta dauki kamar mintuna uku da fita kafin ya
dawo da yanayinsa na bacin rai kan fuskarsa a
yayinda ya latsa lambar Wilson.
"Yaya aka yi me gidana?"
"Ta amince da daukan duk tsautsayin da auren
ta zai janyo...ke nan za ta amince da daukan
tsautsayin abin da zan yi...bayar da karatun
karshe""
"An gama oga na karfe nawa?""
"Karfe bakwai na yamma'""
"Allah Ya ba ka sa`a me gidana"
*
Har ya shigo ba ta sauke kafarta daya dake
kan daya ba, tana ci gaba yiwa faracen hannunta
gyara, ko dagawa ta kalle shi ba ta yi ba.
"Kai na zo a sa`a...wannnaan kwalliyar tawa
ce ko ta me gidana ko ta aikin da na zo miki da
shi?""
Har yanzu ba ta dago ta kalle shi ba.
"Na taбa kwalliya saboda kai ne Wilson?
Kada ka dinga bata min kasuwa mana"
"Amma da kin san kasuwar da na kawo miki
bana zaki yi kwalliya saboda ni
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ta dan kalle shi bayan ta tsayar da wukar feke
farcen kan babban yatsarta.
"Bana kuma me kake tafe da shi"
"Bonanza! Yes it's a Bonanza....kudi Cash
zunzuruyun dala dubu dari daya. Hutu na wata
shida a Hawaii da duk wani jakuzziy da kike so.
Uwa uba saurayin da kike so ki karba da duk
dukiyarki ga shi kyauta manne da kafadar ki wato
Ibrahim A. Hadi"
Ta fashe da dariya sannan ta koma gyaran
akaifarta.
"Wa zan kashe bana wa zan raya da zan sami
irin wannan gàrabasar?""
Ya matso kusa da ita yana rada cikin zakuwa
da neman amincewa
"Shi yasa nace miki garabasa... domin babu
wanda zaki kashe illa gobe da yamma bayan
Ibrahi ya farfado ki nemi ganinsa a asibiti ki tsara
masa cewa abin da ya same shi shi da mahaifinsa
shirine na Farida bayan ta gana da mahaifinta ya
gamsar da ita. Ke sai ki zare da saurayinki ki bar
mu da yakin mu da Farida"
A firgice ta tambe shi tambayar da ta dame ta.
"Ibrahim ba shi da lafiya ne?"
"Aa! Lafiyarsa kalau yanzu, zai dai sami
rashin lafiyar ne yau kafin bakwai na yamma"
"Zaku kashe dan mutane? Wilson kada ma ka
gwada haka"
"Idan zan kashe shi ne ina za ki same shi gobe
ku tattauna Allah Ya raba mu da kisa, kawai dai
so muke mu ba ki Bally na Farida mu mu samu
sa'ida. Ke ce dai in ba ki amshi aikin mu ba kin yi
N
177 Mafiyan Masaya Rahma AbdulMajid
shi a kan kari kuma a tsare irin tsarin da aka san
ki da shi ba zan iya kare ranki daga tsautsayin
hakan ba. Domin wannan ogana ke kira aikin
karshe... kin kuma san duk aikin karshe kan sami
ة tsautsayi
Ta sauke kafar ta janyo hannunsa zuwa kan
cinyoyinta dake bude tun da dadewa.
"Bai kamata in musa ka ba don ba ka taba
kawo min kasuwar da babu riba ba. Zo na fara ba
ka Alakoro kafin na cika maka aiki...ko na ce mu
yi sallama da kai don inna sami Bally ko me
gidanka bana jin zan šsake sani"
Wando baki da shet mai ruwan toka da farin
tai ya gama sanyyawa sanman ya tsaya shafe shafe
a gbana madubi cikin zumudi da wake-wake.
Mahaifinsa wanda ke sanye da shadda da wando
farare masu dibar ido kuma da alamar ya gama
kintsawa ya zo ta bayansa dauke da kwat din
wadon jikinsa ya mika masa.
"Ya isa kwalliyar Ballin Farida ai ka ishe ta
haka ka sanya rigarkau tafi kada mu yi latti.
"Ka tabbatar na kdu a ango Pop?""
Suna fuskant juna a yanzu cikin murmushi
da kallon Kauna.
"Ka hadu na A. Hadi da Farida mu je kada
mu yi latti".
Ya karbi kwat din ya sanya sannan suka baro
dakin.
Har zasu sanya kafa wajen babban falen
amma sai mahaifinsa ya tsayar da shi da hannu.
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMalid
"Ba ka yi rokonka na karshe ba... za mu fita
neman babban sa`a ka san yaya za mu dawo?"
Ya daga hannu sama cikin dariya.
"Allah ina rokon shigo wa gidan nan da
Farida babu shamaki a wannan karon ya zamo in
zan dawo kafata kafar matata"
Abdul Hadi yayi dariya.
"Ba dai nan gidan ba...Farida ta fi karfin
gidan nan...kai dai mu je a baka ita tukuna.Farida
ta fi karfin gidan tsoho muddin tana sirikar
A.Hadi. mu je ango kada mu yi latti"
A waje direba ya rusuna ya mika mukulli ga
AbdulHadi wanda ya wuce ga muhallin tuki.
Ibrahim ya kalle shi cikin yalwar farinciki
"Pop kai ne direbanmu yau?"
Ya nuna shi da kwayar mukulli.
"Me gida yace mu biyu yake son gani. In na
dauki direba ya zamo bamu cika sharadi ba yaya
ke nan? Shiga mota mu je muna da sauran
mintuna ashirin kuma a gabansa nake so su cika
mana in so samu ne"
*
Ta dauki wani dogon kofin tangaran mai
bulun filawa ta na goge shi da farin kyallen cikin
murmushin tsanananin farin ciki wanda bata
ankara tana yi ba har sai da ta hada ido da Farid
wanda ya kawo kansa don taya wannan aikin sa
kai da ta tsira. Shi ma wani tangaran yake gogewa
amma idanunsa na kanta yana murmushi da irin
nasa manufar ta bambanta da tata. Cike yake da
sanin ba fagen Farida ba ne aikin kicin da gogegoge ba, amma ta rasa abin da zai cike mata
179 Mafiyan Masoya Hahma AbdulMajid
mintocin zumudin da suka addabe ta ne na jiran
masoyinta don shimfida sabuwar rayuwa cikin
yanci da walwala. Yanzu da a ce shi ne ya sami
zuciyar wannan abin kauna tasa da irin wannan
tafkin soyayya haka za ta zake ta shigo fagen da
ba na ta ba don saboda harshensa da tumbinsa? Ya
rasa Farida, ta yi aure, tana da ciki, kuma kamar
ita da Ibrahim Balala babu abin da zai taba raba su
saboda yadda suka so juna ko suke kan son
junansu. Amma fa ya kasa kau da kai zuciyarsa na
gaya masa karyar cewa takwarar tasa fa na iya son
sa, kuma duk inda tayi murmushi ta cancanci a
taya ta.
"Kana kallon farin ciki ya sa ni shisshigi ko
shi yasa ka ke min dariya?"
Ta fassara murmushinsa don katse kallon da
yake mata sannan ta mai da idanunta kan jera
wasu tangaraye da take gani kamar ba su zauna
kan muhallansu ba sannan ta ci gaba da magana
kafin ya ce komai duk da yana shirin cewa.
"Ba zumudine ya sa n a kwace aikin nan ba
Farid kamar yadda ka za ta illa yau rana ce gare ni
da zan tuna wasu farin cikina na baya don na hada
da na yau da na gaba in tabbatar da dorewarsu.
Na taba tsintar kaina ina irin wannan aiki lokacin
da nake wani kwas a Brassels kuma farkon ziyarar
Bally a gidana. Ni na yi masa girki yana tsaye a
inda kake yana taya ni jera kwananika a
muhallinsu ni ina kicin. Bamu sake kwatanta
wannan kwanaki ba sai bayan auren mu inda a
karamin gidan daga ni sai shi babu ko mai shara.
Don haka yana shara ina kade tebur, ina dahuwa
18 Mahyan Masoya Ralma AbdulMalid
1
Ι
:
yana wanke-wanke muna hirar soyayya da
wasanni. Duk wancan a baya sun faru ne
lokacinda babu `yanci amma yanzu ga su nan zasu
soma faruwar dindindin daga yau....
Ta tsaya ta dube shi dą kyau.
"Kuma kai ne sila na faruwar yau. Da baka
ankarar da ni ba da yau din da rayuwar gaban ba
su faru ba. Ba ni da abin gode maka Farid""
Yayi fari da ido sannan murmushi. Duk ta
zubar masa da abin da ya so fada duk da bai samu
abin dadi a maganarta ba, tun da kuwa ba samun
ta zai yi ba.
"Babu godiya tsakanina da ke Farida"
Ta tsira masa ido tana murmushi.
"Farid ka taba soyayya kuwa?'
Ta ji tambayar ta kußuce daga bakinta a karo
na farko tun tsayin lokacin da jikinta ke ba ta
cewa shi ma fa yana son ta yana sadaukarwa ne
kawai ga abin da take so, ba ta taba son tayi
tambayar ba duk da tambayar ta sha matsa kanta
domin ta fito. Ba ta so ta san gaskiyar lamarin da
zai iya watsa abokantarta da mutumin da take
ganin shi ne kashin bayanta a yanzu. Shi ma
kamar ya fahimci tambayar kubucewa tayi domin
kuwa fuskarta ta kawu daga tsammanin amsa. Ko
shi ba zai so ainahin amsår ta fita ba a lokacin da
yake ganin amfaninta ragagge ne.
"Na taba jin so, amma ban yi sa'a ba don son
maso wani nayi"
Ya bayar da amsar ba tare da ya dago fuskarsa
ya kalle ta ba, haka ita ma sai cewa tayi.
'Oh! Am so sorry'
181 Mafiyan Masoya
*
hdidMaiid
Rahma AbdulMajid
AbdulHadi ya yi tagumi yana kallon gabansa,
motar na sharara gudu, hannunsa na ajiye kan sitiyarin ba don yana juya shi ba. "Allah Ya sa wannan lamari na ku ya kawo
Karshe ta hanyoyi da dama..."
Ibrahim ya dube shi.
"Ban gane karshe ba"
Yayi murmushi sannan ya cire taguminsa
domin ya karya kwana.
"Ni da Na'ibi ba mu yarda da juna ba, komai
zai fito daga hannun junan mu mu kan sanya
shakku da zaton akwai makirci, wannan ne ya
sanya muka kasa shiryawa tun tsawon lokaci duk
kuwa da kowa ya wadata da sharrin kowa, kuma
da ba haka muke ba. Abokai ne na gaske masu
kishin kauyensu. Gaskiyar lamari itace ni na
haddasa matsalar, amma Na'ibi ya fi ni zakewa
bayan da ya sami amintattun kwararru a bayansa
kamar Wilson, da Adamu, da Farida `yarga da ma
wani sabon yaro Farid... tun a da ya fi ni iya
zaben ma'aikata da kashe kudi a kansu.... Sai dai
Alhamdulillahi gani a hanya zan je karar da abin i
da na fara. Fata na Allah Ya, sanya Na'ibi da
gaske ya shirya ya kare"
"Amin"
In ji wanda ya koma murmushi cike da
yakinin karewar ce ta zo da fara sabon shafi na
aminci ta hanyar soyayya. Farida ce a ransa da
tunaninsa da idonsa, me za ta shirya masa? Yaya
za su ga juna? Kamar yau a ka daura aurensu,
yana jin za su yi haduwar amarya da ango. Amma
1
1
a
a
n
a
ם
ar
182 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
kwatsam karan juya sitiyari da taka burki ya kawo
karshen wannan hotuna don kallon ainahin abin
da ke gabansu. Duhu ya fara gani saboda girman
Daf din wadda ta karkato kan titi za ta shiga
dayan hannun ba tare da la`akari da ko babu mota
a kan hannun da ba nata ba. Abdul Hadi yayi
yunkurin kaucewa ta hanyar dauke kan tasa motar
zuwa filin baya da daf din ta bari, amma kamar a
tsorace mai daf din ya dawo da baya, abin da ya
sake ba shi damar hankida su cikin daji don su
tintsira babu iyaka cikin motar da bata dena gudu
ba.
Na`ibi wanda ke cikin shigar doguwar riga
mara hannu ta shan iska kuma yana zaune a daya
daga kujerun dogon falon na kusa da mashigar
gidan yana raba idanunsa tsakanin jarida da
agogo, baya kallon Farida wadda take ta zarwa
tana duba agogon tana kiran wayar da ba a dauka.
Can sai ya mike yana kallon agogo.
"Farida ni ina da abin yi in ba ki da shi. Awa
daya da mintuna arba`in na kara na jiran
angwayenki. Ba ni kara ko sakan daya....in sun
zo sai ku ci marabarku, kuma ku sake shirya wani
lokacin da zamu hadu, idan basu zo ba sai ki
fahimci gaskiyar cewa AlHadi ya tabbatar miki da
cewa babu abin da zai canja tsakanin ni da shi...."
Ya jefar da jaridar ya juya ya kama hanyar
matattakala. Ita dai sakate tana kallon sa, a-rikice
take ba ta jin dadi, ba ta san dalili ba, me zai hana
su Ibrahim zuwa baya da sun yi sallama yace mata
sun bar gida? Yanzu kuma ta kasa samun sa a
183 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
waya ba don babu layi ba sai don ya ki daga
wayar. Me haka ke nufi? Ta sake komawa gwada
lambar...
*
Karfe goma sha daya kamar wadda ta buga a
tsakiyar kunnensa ya ji ya farka a irin duniyar da
bai taba jin nauyinta ba. Kansa na ciwo kuma
yana dauke da nauyi, sannan kamar wuyansa a
kangare yake cikin wata roba. Ya so sanya
hannunsa na dama ya shafa amma sai ya ji hannun
ma na wani karajin ciwo duk da daurin jikinsa bai
hana shi motsawa ba a guje ya mayar yana nishi,
sannan ya dan mika wuya ga kwanciyar. Nan take
ya ji yana waro wa kansa abin da ya faru. A hanya
suke shi da mahaifinsa zasu gidan sirikansa
gaisuwa suka yi mummunan hatsari mai kama da
shiri. Ya dubi dakin baki daya babu mahaifinsa.
To ina yake kuma a wane hali yake? Tambayar a
cikin zuciyarsa ta zo daidai da bayyanar wata me
aikin jinya wadda ta ambata Kalmar 'ka farka?"
"Ina Baba na?"
Ya bukata yana hadiyar yawun fargaba. Та
soma neman kubucewa.
"Yana nan kwance yana bacci...yana samun
sauki...yaya naka jikin? Bari na kirawo likita"
Ta juya za ta fice a yayinda ya daure ciwo ya
sanya hannun ya janyo ta. Suka hada ido da nasa
idanun maras rahma sannan yace mata
a
"Ina son ganin Babana ko ki kai ni ko ki saura
nan tare da ni"
Yana kwance rigingine, babu riga a jikinsa sai
koren kyalle da aka rufa masa zuwa kirji, kamar
184 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
babu wata tawaya. a jikin nasa sai dai yana madaddewa ta jin jiki. Ibrahim dake dingisawa dakyar ya iso inda fuskarsa take ya dan zura masa
ido kamar ya zubda hawaye. Ya dena jin nasa
ciwon domin kuwa da alamar radadin da
mahaifinsa ke ciki ya dame nasa ya shanye. Can
dai ya ambata 'Sannu Daddy'lokacin ne mahaifin
ya tsai da wani kakarin numfashi da yake sannan
ya dan bude ido ya kalle shi.
"....Ibbbraaahhim kai ne?"
Ya dafa kan mahaifin nasa da hannunsa na
hagu mai sauran lafiya
"Ni ne yaya kake ji?"
Ya dan dubi mai jinyar.
"Ko za ki ba mu wuri na dan yi magana da. dana?"
Ta gyada kai sannan ta fita ta tsaya a kofa. Ya
dawo da idanunsa kan Ibrahim bayan ya tsawaita
nishinsa sannan yayi murmushi.
"Ban gaya maka cewa ban yarda da Na'ibi
ba?.... Ga shaida ta samu...Na`ibi ya so ganawa
da `yarsa kafin ya gayyace mu sannan bayan sun
gana din Farida ta kaurace mana sai a waya har
aka tabbatar mun fada rami....hum!... ban sani ba
ko za ka iya yarda da ni... idan na ce ban yarda da
Na'ibi ba har da Farida domin na san ko me
Farida tayi min a lokacin da baka rayuwarta da
lokacinda ka shigo rayuwarta.... Koma dai yaya
ne ka sani Na`ibi yayi nasararsa ta karshe a kaina,
ya raba ni da dukiyata da sa`ata amma ban
daddara ba ina motsi...yau ya kawo karshen
motsin nawa ya raba ni da raina kuma ta hanyar
185 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
amfani da ſana....Ibrahim ka sani wannan abu ya
faru ne da hannun Na`ibi, ban kullace ka ba don
an yi amfani da kai don na san ba ka sani ba,
amma a yanzu ka sani, kai ne zaka saura musu kai
ne halifa na kai ne a gaban Na'ibi ko ka yarda ka
zama bawa ko kuma ka rike kanka ka ja da su.
idan da zabi na za ka bi da nace in kai dana ne da
ya haifu to ka daukar wa ubanka fansar ransa da
aka raba shi da shi... kada ka bar Na'ibi ya shara
ko ya sarara kamar yadda ya kai ni karshe, amma
ka kare kanka daga sharrinsu, musamman ta
hanyar Farida.
Tun da yake maganar Ibrahim baya son katse
shi ko da da sannu don wahalar da yake sha wajen
hada kalmomi don tsananin ciwo, a waje daya
tausayi da yarda sun sanya yana tasirantuwa da
hangen abin da ma mahaiufin nasa bai gaya masa
ba a cikin matafiyarsa. Amma a yanzu ya soma yi
masa sannu da yi masa alkawarin tashi
musamman da ya ga mahaifin nasa zai kame zuwa
wani halin sharafa, mai jinyar ta shigo a guje ya daka mata tsawar ta nemo likita, fitarta da minti
kasa da daya likitoci da dimbin masu taimako
suka afko cikin dakin yayinda wasun su suka
tilasta wa Ibrahim barin dakin domin kwantar da
shi a nasa dakin.
A kofar dakinsa... ta bayyana rataye da jaka
fuskarta cike da tausayi. Cikin hanzari ta miko
hannun taimako inda ita ma ta rike kafadarsa tana
'sannu' don hakan ya ba ta damar shigewa
dakinsa.
186 Малyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ita kadai ta ragu a dakin bayan an sassarkafe
shi da kayan magunguna tana rera masa sannu. Ya
dago da rurin kuka ya kalle ta, a yanzu babu zafin
Kiyayya da tuhumar da ya saba nuna mata a
idonsa.
"Baba na zai mutu"
Kwalla ta kubuto daga idanunta ta dafa shi.
"Allah ba zai sanya haka ta faru ba. Likitoci
zasu cece shi.... Sai dai bana ka daure ka yarda da
abin da nake gaya maka. Idan a ce ka ba ni dama
tun a wancan lokaci na kwance maka wannan
yaudara da haka ba ta kai ga faruwa ba. Farida
kawata ce kuma makusartiya amma na san me za
ta iya na san yaddaa gaji ubanta wajen hada
makirci da iya daure soyayya. Ban ce Farida ba ta
son ka ba, amma za ta iya daure wannan domin ci
gabansu. Farida da babanta sun shirya kashe
babanka ta hanyar zuwa baiko sai ka saura a
duniya ku yi aure, sannan su mallake ka ta hanyar
dan da ke cikin Farida bayan kai ma sun kashe ka.
Na`ibi Group zasu huta da ku da kuka zame musu
karfen kafa"
Tunda take babatun kallon ta kawai yake baya
ko kiftawa duk da yana hawaye. Sai dai ba ta gaza
ba domin kuwa wannan karon ko ba komai ya
saurare ta sabanin wancan kora da ta sha kaye....
*
Wilson ya fado ofíshin mai gidansa cikin farin
ciki yana bayyana murmushi.
"Me gidana ka kira ni ina daf da shigowa
wurin ka....Karshen tika-tika-tik! Allah Ya'yanke
mana jayayya da hasuma da gasa. Allah Ya karbi
Rahma AbduMajid
187 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Malam Abdul Hadi zuwa wurinSa. Na san