ka yi
rashi babu abin da zamu ce sai Allah Ya jikan sa
da rahma. Gobe jana'iza da misalin karfe goma na
safe, sai mu shirya ka isa wurin ka....
Ya dakatar da shi da yatsa daya domin ya gaji
da sambatu, ji kake dif
ji
"Wilson a cikin Kalmar koyar da darasi ina kа
an ce kisa? Yaushe na ce ka kashe wani?
Wannan aikin naka ban so ba don ban sanya ka
ba יי
Ya sake yin murmushi.
"Ranka ya dade ai damuwarka ita ta sanya ni,
domin na ga kamar a na son cin maka a bango
abin da kuma ba zan taba bari ba. Dole na motsa
ta yadda zan karar da wannan wasa har karshe. Ni
dai kawai ka huce fishinka mu dan jira sararawar
komai ka ga yadda za mu ci moriyar wannan
yanayi"
"Na ji, fita ka ba bani wuri ban son ganin ka
yanzu יי
"Yadda ka so haka za a yi ranka ya dade"
ya juya da sanda ya fice. Sama da mintuna hudu
Na`ibi Bici tunani kawai yake shararawa da ganin
abin da ya faru bai dace ba har må da jin tausayi,
amma fa da nasa kuskuren, shi ne yace a koya
darasin da bai ce ga bakaken ba, sannan sau tari
Wilson kan yi amfani da wannan kalma ta
mummuniyar hanya, yaya za a yi yayi
haka?Amma kuma shi ma Wilson ya kamata ya
san cewa babu yadda za a yi hukumcin AlHadi ya
zamo daya da hukumcin kananan arna. Farida da
ta bangazo kofa ta shigo ta bangaje tunanin sa
189Man Masoya Rahma AbdulMajid
inda ya kalli fuskarta a tsanake don ya san me
yake tafe da ita.
"Thanks father! Na ji kuma na ga shirinka. Ка
so ka kashe mijina shi da ubansa, baka yi nasarar
kashe dan ba, amna ka yi nasarar kashe uba.
Amma fa ka sani....
"Shut up!"
Ya daka tsawar da ta jima ba ta ji ya taba yi
wa kowa ba koma tace bai ta6a yi mata ba, don
haka ta girgiza ta tsaya kallon sa tana jan
nunfashin fishi har ya taso.
"A me kika san ni? Me kisa ko me sana`a?
gaya min.... kin taba ji na yi kisa?"
Ba ta tanka ba ta yi inasa kur da ido domin
amsar ba ta dace da yanzu ba, fishinta ba zai bari
ta ce masa baya kisa ba đuk da ta san a harkar
kasuwancinsa kamar babu jini. yayi ajiyar zuciya
sannan ya girgiza kai ya karaso inda take ya dafa
kafadarta yana son yin maganar hankali kuma
hankali.
a
"Farida. Mutuwar AbdulHadi zan iya tabbatar
miki cewa mutuwa ce irin kowace mutuwa mai
dauke da kaddara, kuma ni ma da nake zaune a
nan ina jin zafinta domin ko ba komai ya taбa
zama abokina. A yanzu zan rayuwar babu aboki
babu kishiya. Kin san manufar haka gare ni?
Farida na taba yi miki karya kuwa tunda kika
wayi gari da ni?"
Ya gyara tambayar bayan ta Kura masa ido.
"Yes, na san kan batunku ke da Ibrahim na
boye miki wani abu, amma sai dai 6oyewar ba
wai in yi miki karya ba. Farida ki yarda da ni ba
Gath
189 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
zan miki karya ba, ina duban cikin kwayar idonki
ina gaya miki cewa ban kashe kuma ban yi
yunkurin kashe AlHadi da dansa ba"
Ya dan jima suna kallon juna cikin kwayar
ido sannan ya juya ya bar mata filin.
*
Ta sami isowa har kofar dakin da Ibrahim ke
kwance cikin sassarfa sauranta budewa, amma sai
wata mai aikin jinya ta tare ta.
"Ina za ki?"
"Nan aka kwantar da Bally... sorry Ibrahim
Hadi?"
"Eh nan ne, sai dai ya ce a dinga sanar da shi
ko waye ya zo kafin ya shiga masa daki"
"Ok. Ki ce masa matarsa ce Farida"
Ta ambata cikin zumudi a yayin da
ma`aikaciyar ta mai da kai cikin dakin da Faridar
ke kokarin lekawa don zumudin ta ga Ibrahim.
Bayan 'yan sakwanni kofar ta bayyana, maimakon
ma`aikaciyar ta fito sai wata me ban mamakj/ta
bayyana. Kawarta Merry ta fito tana takí da
yanga.
"Farida ce kuwa! Ki yi hakuri majinyacin
yace ba ya son ganin ki"
Tuni ta daure faduwar gaba da mamaki ta ari
karfin zuciya mai famar kubucewa.
"Me ya kawo ki nan?"
Tayi dariya sannan tayi rausaya.
"Me ya kawo ni nan? Nice nake jinyar saurayina Bally, ko yaya kika gani? Ba dai kin
zarge ni da karuwanci ba, shi ne nake nuna miki
Mayran Masoya Rahma AbdulMajid
zan iya shigar ki ta ko ina ba ki ga ma komai
ba
Farida ta daga hannu domin ta mare ta amma
ta rike tana kada kai daidai lokacin da mai aikin
jinyar ma ta fito.
"A'a! Kada ki jawo masoyina ya nuna miki
fishinsa don kin mari mafificin wurin da ya fiso a
jikina. Kumatu fa kusa da baki yake kada ki
manta"
Mai aikin jinyar ta dan tsaya kallon su cikin
mamaki har suka sarara sannan ta waiwayi Farida.
"Malama mai jinyar yace ki yi hakuri ba ya
son ganin ki"
Farida ta kura wa mai maganar ido duk da
idanunta na yi mata nisa da ita. Ta so bude baki
tayi mata tambayar da ta dame ta, amma bakin
yaki buduwa. Tana son cewa Bally ne yace baya
son ganin Farida, amma wani sa` in bakinta rawa
kawai yake. Me aikin jinyar ta bar wurin da sauri
a yayinda ita ko Merry ta sake buga rausaya da
dariya, ta juya don komawa cikin uwar dakin.
"To kin ji a bakin da baya karya, tunda ba za
ki yarda da nawa ba. Yanzu sai a koma ko?"
Ta shige ta bar Farida tsaye kan gwiwoyin da
ke shirin kasa daukarta.
An yi jana`izar AbdulHadi cikin yanayi na
ban tausayi musamman ga wanda zasu kalla daga
nesa. Akwai dimbin 'yan uwansa amma babu
wanda ya fi daukar ido kamar dansa daya tilo
dake tsaye bisa sandar guragu biyu yana sharar
kuka babu kafkaftawa har ya kasa rike kansa.
191 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ministoci da manyan jami'an gwamnati sun
halarta sai dai Na'ibi Bici bai sami zuwa sahun
gaba a masu sallar gawar ba, wannan kuwa ta biyo
bayan umarnin da Ibrahim ya bayar na kada a bar
shi ya zo kan gawar mahaifinsa bayan ya sami
labarin isowarsa mukabirar. Sai dai a lokacin da
yan jarida suka yi masa tambaya kan hakan, shi
Na'ibi ya ambata cewa latti yayi sanadiyyar ruwa
da ake a hanya wanda ya haddasa gosilo, ya kuma
kara da cewa shi ne na biyu a rashi in aka yi
la`akari da yadda zai kare rayuwarsa babu aboki
babu kishiya a harkar sana`a sakamakon kawuwar
AbdulHadi. Ko da aka tambaye shi kan sabaninsu
ya bayyana cewa ya ji dadi da ya zamnto ta kawu
kafin barin dayan su duniya, domin kuwa ko
kwana uku da suka wuce yana tare da AbdulHadi
suna tattauna wasu muhimman abubuwa da suka
shafi rayuwarsu ko da bai bayyana wannan abu
ba. Sai dai ya fadi cewa marigayin ya ambaci su
kawo karshen adawarsu kasancewar in sune yau
ba sune gobe ba, kamar wanda ya hangi karatowar
lokacinsa. Yayi fatan Allah Ya jikan abokinsa ya
silale daga hannun 'yan jaridar.
Duk wannan lamari ya faru kan idon Farida
wadda ke kulle a dakinta tun jiya da ta je wurin
mijinta ta kasa samun shiga. Duk da hoton yadda
yake tsaye kan sanda da kukan da yake ya makale
a zuciyarta kamar yadda ya sanya ta zubar da
hawaye maras iyaka, hakan bai kau da hoton
yadda ya kasa mika wa mahaifinta hannu yayi
kamar bai gan shi ba a yayinda suke ficewa daga
makabarta. Ta san ma'anar haka kuma nauyi ne
192 Maflyan Masoya Rahma AbdulMajid
ke karuwa a kanta. Hakan na nuna wata sabuwar
rugujewar alakar aurensu da ba ta san ta inda za ta
gyara-ba. Sai dai ko ma me nene a yanzu tana jin
matukar bukatar kasancewa da shi ganin halin da
yake ciki. Babu yadda za a yi ta bar shi haka. Ta
mike ta dauki Jakarta tana share idonta da hankici
a yayin da ya zo daf da shigowar mahaifinta
falonta suka ci karo. Ya kalle ta cikin ido da nuna
tausayi. Yana dauke da labari mai dadi ga
zuciyarsa shi ne na yadda Ibrahim ya kulla da shi
wanda hakan na nufin samun nasara mai sauki
kan alakarsu da `yarsa.
"Zan je wurin Bally. Babu dama na bar shi shi
kadai a wannan yanayi...yana bukatar
kasancewata tare da shi"
Ta furta da sauri cikin kuka don kada
mahaifinta ya sami damar tare ta. Shi ma bai yi
niyar haka ba duk da yana yi mata kallon tausayi.
Ya dai bar mata magana kamar haka.
'Watakila ke ya tanka ki, amma ni ko hannu
ya ki yi da ni...Ibrahim na tuhuma ta da abin da
ba zan taba yi ba, amma ki je yana bukatar ki"
Ta dafa kafadarsa tana shirin fita da sauri.
"Zan wayar masa da kansa ko ta yaya"
*
Ya kaurace wa zaman makokin don ya
kasance a falon mahaifinsa shi kadai. Ya shigo
babban falon wanda babu yawan kujeru da kayan
ado sai jifa-jifa masu dan karen tsada da satar ido. Yana dubansu ba wai don suna dibarsa ba sai don
wannan falon ne yayi fitar karshe da mahaifin a
193 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
nasa wanda a yanzu yake jin kamar shi ya kai shi
ga mahalakarsa
"...baka yi rokonka na karshe ba ... zamu
fita neman babbar sa`a, ka san yaya zamu dawo?"
"...Ni da Na'ibi ba mu yarda da juna ba,
komai zai fito daga hannun junan mu mu kan
sanya shakku da zaton akwai makirci, wannan ne
ya sanya muka kasa shiryawa tun tsawon lokaci
duk kuwa da kowa ya wadata da sharrin kowa,
kuma da ba haka muke ba. Abokai ne na gaske
masu kishin kauyensu. Gaskiyar lamari ita ce ni
na haddasa matsalar, amma Na'ibi ya fi ni zakewa
bayan da ya sami amintattun kwararru a bayansa
kamar Wilson, da Adamu, da Farida 'yarsa da ma
wani sabon yaro Farid... tun a da ya fi ni iya
zaben ma`aikata da kashe kudi a kansu....Sai dai
Alhamdulillahi ga ni a hanya zan je karar da abin
da na fara. Fatana Allah Ya sanya Na'ibi da gaske
ya shirya ya kare... Allah Ya sa wannan lamari na
ku ya kawo karshe ta hanyoyi da dama...
Kalmomin mahaifinsa da zai iya tunawá na
Karshe ke nan da suke amo a kunnensa kowacce
na ba shi fassara da aibata shi da wauta na rashin
samun fassarar tun a farko. Yayi jifa da duka
sandunan hannunsa ya tsaya kan kafafunsa yana
girgiza da rurin ciwo, amma bai jin na ciwon sai
na duk abubuwanda ke nuna masa cewa Na`ibi
kungiya ne da babu rahama ko kauna a cikinta.
Babansa ya nusantar da shi amma ya kasa ganewa
saboda kaunar Farida. Yanzu ke nan ya janyo wa
mahaifinsa asarar rayuwarsa. Alamunta ya gani
194 Mayan Masoya Rahma AbdulMalid
kamar tana yi masa gizo, amma fa da gaske ta
shigo falon kuma shi take kallo kur da ido.
"Me kika zo yi min kuma Farida?"
Ya ambata Kalmar cikin murmushin zafi. Ba
ta daina kallon sa ba duk da zafin tambayar gare
ta. Ko dai da tayi ajiyar zuciya a yayinda za ta ce.
"Kana bukata ta a wannan lokacin domin babu
dalilin da zai sanya ka kasance kai kadai cikin
wannan yanayi da muka samu kanmu"
Ya yi karin mumushi sannan ya dubi gefen
damarsa.
"Ina bukatar ki Farida? A wane matsayi za ki
yi min wannan aiki ke nan?"
"A matsayina na matarka masoyiyarka kai da
zuri`arka. Ji nan Bally na san kana cikin matukar
zafi da rashi, amma haka baya nufin mu zubar da
hankalinmu mu fara abin da ba zai yi mana dadi
ba. Na san ka yarda da ni da abin da zan
iya...Bally ba zan cutar da kai ba ba zan taba
goyon bayan mai cutar da kai ba. Bally ina son ka
ina dauke da danka yaya za a yi in yi tunanin
hallaka ka ko mahaifinka?"
"Ba za ki goyi bayan mai cutar da ni ba...har
ubanki da kuka gina sana'ar hallaka abokan gasar
ku har lahira?"
"Har ubana Bally ba zan yi tarayya da shi in
zai cutar da kai ba, kuma ka san haka. Ina tare da
mahaifina ne har yanzu domin na sani kuma na
tabbatar bai da hannu a abin da ya same ku.... Bai
tabe yi min karya ba kuma na san abin da zai iya
babu kisa a ciki, mun dade muna aiki da shi....na
san ba lokacin wannan maganar bane yanzu,
195 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
amma ka daure ka saki ranka ka bar ni na yi
aikina na kasancewa da kai a matsayin matarka
kuma....
Tunda take magana murnushi yake yana
laluben wani abu a aljihunsa, can kuwa sai ga shi
ya samo wata takarda a dunkule ya kwance ta
sannan ya nufo ta da murmushi ya muna mata.
Katin shaidar aurensu ne
"ina jin wannan ce ta hada ni da ke da kike
kiran kanki mata ta ko?"
Bata iya cewa komai ba don fargabar abin da
yake shirin yi. Ya keta ta gida hudu sannan ya
watsa mata a fuska.
"Yanzu sai ki huta da cewa na kawo karshen
auren. Dama ba mu da shaidu a nan sai ita, a
musulunce ina gaya miki cewa ke Farida na sake
ki saki uku.... Sannan abin da ke cikinki na ba ki
ki kashe shi ko ki raya shi....Abin da nake so ya
hada mu ni dake yanzu shi ne kiyayya! Mafiyanci
kika iya ko? Ina so mu san juna a MAFIYAN
MASOYA. Ba dai mafiyanci kuka iya ke da
Na'ibi ba? To ina so ku gwada da ni.... kun yi da
babana kun kashe shi ina so mu gwada ni da ku it
ga waye me nasara. Farida ina neman alfarmar mu
yi wasan MAFIYAN MASOYA ni dake"
Ya kura mata ido kamar yadda ta kura masa
tana kada kai.
"Ni Ibrahim?"
"Ke Farida"
Ta kwashi yankakkun kwalayen a hankali ta
dube su sannan ta dube shi. Har yanzu idanunsa
babu walwala kamar yana jiran me za ta yi. Dа
MARASMBOUNAK
sauri ba sauri ta juya za ta fita a yayin da zuciyarta Re Zaizay 9yNC
"Şai mun hadu a fagen daga. Gara ki yi sauri fkafin Ki kathi MRcin Garawo a gidan
nan
ongaca uyd Bf har tafalon zuwa cikin hotarti wadda ta taka da gadu kada ta rasa mai
kai ta gida
n abuEUEU m
st aids redagial mob sd ismol swo avi a
EY REMISE busbig & EION BY inde
morered ows st swas sb sud it ise nE Y
sti is a subisd sb um 6d கா
sase sa abriel sil swas ilim sysy sri mel
il sd sa iknikic ek sb nids nku i
λα 20 U9KE q9 2μ 19λς Xι κо 2μ! κπάμε 1
tonsyits !SVYEVINON ide usrisy ors in m
KAYTAM s επυ πε2 um or En! Sod sgi u
sb 3x svi sud ioπsvilem isb s AYO2AM
sb iy nuk..in sb sbewg ux or en oT Yed idi
ni ud sb in sbswg um oг aл ide edesk uuk snadad
பாமா bre STERN ON SVEW
"edsb in AYOZAM WAYAM ПЕКЕ
seem swal 61 sbbsy ismed obi sent Erua
KI பான்வு
"midaidliv
tenibs" .KG
ε μελακό 8 πsslw πυλλελον ideεwd
senunsbi SASY TH ide dub BI NERGET do
50. அj Gasy isrisa Biew a
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
MAFIYAN MASOYA
Tana ta tirje-tirje da mutsttsuka har Allah Ya
ba ta damar abin da take so wato farkawa daga
wannan bacci ko dogon suma, ta kalli dakin da
sauri. Karo na biyu ke nan a rayuwarta da ta kan
farka ta sami kanta a asibiti. Sai dai wannan karon
da alamar ba a gida Najeriya take ba. Ta san
wannan asibitin in za ta iya tunawa tayi jinyar
mahaifiyarta wadda asibitin suka yi bikin
zamowarta mace ta farko da tayi nasarar warkewa
daga barazanar kyansa ba tare da an yanke mata
nono ba. Kusan a wannan dakin suka yi hoton
tuna wannan rana. A birnin Moskow ta kasar
Rasha ne. to yaya aka yi ta zo har Rasha ba ta sani
ba? Daga gidan Ibrahim ta fara tuna ta iso gidansu
amma da alamar bata shiga ba don ba ta iya tuna
inda ta shiga illa zamanta a mota tana jinyar zafin
kirjinta.
"Sannu da farkawa"
Muryar babanta ce ta gefen hannunta na dama.
Ta juyo gare shi, ashe ma yana rike da hannunta
ba ta sani ba. Yayi mata murmushi.
"me nake yi a Rasha?"
Ta bukata. Ya dan kau da kai.
"Kin suma ne a kofar gida kamar kina
dawowa daga wurin Ibrahim. Likitoci sun nuna
cewa bai yi miki wani abu ba sai dai kin sami
fargaba wadda ta so taba zuciyarki"
Ta kura masa ido tana jin abin da yake fada
tana tuna yadda komai ya faru. Lallai Ibrahim bai
yi mata komai da likita zai iya gani ba, amma ta
198 Mayan Masoya Rahma AbdulMajid
gwammacece abin da likita zai iya gani yayi
mata. Ta tuno cikinta da ta san yanzu ya zama
mallakinta kuma kamar Ibrahim zai so yin amfani
da shi nan gaba wajen takura rayuwarta. Sai ta ji
kamar bata dauke da wani nauyi. Kuma marar
tana masifar ciwo. Ta taba cikin nata zuwa kan
mararta.
"Am sorry Parida We lost your Baby"
Ta kura masa ido, cikin wani cakudadden
yanayi take.
"Ko dai ka sanya an kashe shi ne Father?"
Ya sunkuyar da kai
"Ba zan yi miki karya ba Farida, na sami
labarin yadda kuka yi ke da Ibrahim don kina ta
maimaita yace ya bar miki dan nan a cikin
magagin sumanki. Hakan ya sanya na sanya
hannu kan a cire cikin nan daga Ibrahim ya bar
miki wani abu da zai dinga damun rayuwarki da
shi. Ba sona ne in rasa jikana ba kuma ba sona ba
ne in hana uwa samin danta ba, amma wannan za
mu cuce shi ne in ya zo duniya, zai zamo cikin
duniyar kiyayya da gasar da ba za ta bar shi ya iya
tasiri ba ban da bakin ciki. Zai zargi dalilin kawo
shi duniya da kika yi nan gaba. Gara baya nan ku
yi rayuwa irin wadda kuka shirya ke da Ibrahim
nan gaba"
Kallonsa kawai take yanzu ba ta da sauran
tunani da za ta iya illa mika wuya ga duk abin da
ya zo don ba za ta iya kare kanta ba. Ta yarda za
ta iya ci gaba da rayuwa, amma ba ta san ta ina za
ta fara ba.
199 Mafiyan Masoya Rahma AbduMajid
"mun kashe me rai ke nan Father? Ya fara
samun rai yana motsi a cikina"
Ta furta haka tana shafar cikin a cikin karaya
da kewa.
Ba mu kashe me rai ba mun zabar masa
rayuwar da ta fi wadda zai yi ne a nan duniya.
Farida ba ki da wani laifi kan abin da ya faru illa
tsarin rayuwa, kuma haka za ki ci gaba ba tare da
ta sami tangarda ba. Duk abin da Ibrahim ke shiri
zan iya masa in kin bar ni da shi..."
"Father ko za ka ba ni wuri ina son yin
magana a waya"
"Sure"
Ya mike ya fita.
*
Ibrahim na zaune gefen matattakalar falonsa
yana yin abin da bai saba ba wato zukar taba sai
ya ji waya. Ya duba lambar Farida ce ba ta wani
ba. Ya jima yana kallon ta, amma sai ya ji yana
bukatar dauka, domin bai ga abin da ya saura da
zai hana shi daukan wayar Farida ba. Babu tsoro
babu tausayi tsakaninsu. Ya daga yace hello
"Ibrahim Ni ce Farida. Ina son gaya maka abu
biyu ne kawai. Daya shi ne, kyautar da ka bar min
ni ma na mayar wa Allah abinsa. Ke nan babu
wata igiya da ta hada mu babu wannan da da zai
zo da bakin cikin iyayensa ya dame shi don haka
muna da damar cin karenmu babu babbaka. Na
biyu shi ne ina tabbatar maka cewa na karbi tayin
ka na zamowarmu MAFIYAN MASOYA. Kana
so ayi wasa ni da kai, na amince da mu yi wannan
Game da kyau. Ba iyayenmu ne zasu gwada sa`ar
Mafiyan Masoya Rahma AbdulMalid
su ba ni da kai ne zamu gwada. Hakan bai hana
mu zama masoya ba, amma mu nuna wa juna
cewa ba masoya ne irin zallar sauran masoya ba.
Don haka duk wasan da ka shirya Farida ta shirya,
bana gari yanzu,amma zan dawo don ba ka damar
bude fage nan ba ba da jimawa ba
HUM! TAFDIJAN! Yanzu za a soma
mafiyanci a soyayya, duk na baya wasa ne domin
ba masoyan ke yi ba iyayen su ne suke yi, amina
yanzu sun janye iyayensu gefe, sune zasu yi, mu
hadu a littafi na gaba makaranta. Ku yi hakuri
nayi alkawari in dai da rai da lafiya ba zai dade ba
zai fito
Rahma A.Majid
Maman Ahlaam Fatima
Prints
MACE MUTUN
Rahma A. Majid
Mafiy
MASO
MACE MUTUM
BOOKSHOP
Block .No 121 lay uku Bayan Gadar Yan Kur
Kasuwa Sabon Gar Kano
08063800300. 0806453357, www.mamuwa.com
978-978-081-870-3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels