An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MAFIYAN MASOYA
1
RAHMA A. MAJID
HAUSABOOK.COM
Rahma A. Majid
Mafiyan
MASOYA
2 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Copy right ©
Hakkin Mallaka (M)
Rahma Abdul Majid
An fara bugaawa: 2011
Gargadi:
Ba a yarda a sarrafa ko a kwafa ko a juyi
wani angare na wannan littafi ba tare da
rubutaccen izinin mai hakkin mallaka ba.
Kazalika wannan littafi ba labarin wani ko wata
ba ne illa kagen nishadi daga basirar mai shi.
3 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Gabatarwa
Hanyoyi da musabbabai na rubuta labara sun
bambanta kuma sun yawaita da ba za a iya kirgawa ba,
akwai masu rubutu don fadakarwa ko nashadantarwa ko
rikitarwa ko tsoratarwa ko ban tausayi ko ban dariya,
kana akwai masu bayar da labari don habaici ko zagi ko
yabo ko fallasa ko girgiza sha`awa ko kashe ta. Har ma da
masu rubutu don daukaka wani addini ko wata akida kо
wani imani. Gasu nan babu iyaka. Sai dai Rahma Abdul
Majid a wannan karo ta zo ne ba da daya daga cikin
wannan dalilai ko wasunsu ba, dalilina daya shine taya
makarantana hira wadanda sau tari sukan yi kewar
rubutuna saboda dadewa da akan yi ba a ji duriya ta ba.
don haka mai karanta littafin MAFIYAN MASOYA ya
shirya yin hira ne da Rahma AbdulMajid a majalisar
hirarta ta alkalami da takarda.
A bangare guda kuma ina son yin amfani da damar
nan in bai wa masu jiran DA HANNUN MAZA 2 hakuri
na rashin ganinsa. Hakika labarin yadda hannun mazan
yake yana cikin na biyu kuma shine ma ginshikin littafin.
Sai dai wasu dalilai sun sanya ba zan ci gaba da labarin
kamar yadda na so ba, maimakon haka na bar masu
karatu su zana yadda suka so karshen littafin ya kasance
wa zukatansu. Ina mai bayar da hakuri bisa faruwar hakan
kamar yadda nake bayar da hakurin kan rashin jin filin
masoya a wannan karon, wannan ya biyo bayan yawan da
shafukan littafin ke da shi wanda ba zan so na Kara muku
nauyi bisa kudin sayar shi ba. Ga masu jiran jerin labaran
DUHU kuwa kada a karaya. inshaAllah in da raid a lafiya
zasu ga guzirinsu bayan wannan hira ta kare. Da fatan
zamu yi hira lafiya mu kare lafiya.
-Rahma AbdulMajid
4 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Daya
Ya sauka daga kan babur din cikin nawa
sannan ya mika masa dunkulalliyar Naira
hamsin din bai tsaya ba ya wuce ya bar dan
acaban ya na kwance kudin don ya tabbatar da
lafiyar su.
Dakin da yake kusa da kofar fitar ya tura ya
shiga a gajiye, sai da ya fara jifa da takardun
hannunsa kan katifar ba tare da ya dubi wurin
ba sannan ya soma kwance igiyar tai din
wuyansa.
"Yaya ka zo kana watsa min takardunka
kana tashi na?"
Inji wanda yake dunkule cikin wani
kodadden zanin rufa. Bai ko kalle shi ba ya ci
gaba da cire kayan jikinsa.
"Mene ne a gidan nan na abinci ne, yunwa
nake ji"
Ya bukata, Mahdi ya gyara kwanciya ya
juya kansa dayan barin kafin ya amsa.
"Indomie ce na rage maka in zaka ci, babu
ashana ne na jika na ci nawa. Da dadi ka ci ka
ci ka ji"
Tuni ya bude kafin ya gama jin bayanin ya
kalle ta a wulakance. Bata fi loma hudu ba.
Kamar ya fasa kuka, yunwa yake ji, tun safe
5 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
bai karya ba, ga shi abin da zai ci ba zai ishe shi
sunan kari ba.
"Mene ne haka Mad? Me zan yi da
wannan?"
Sai da ya dauki lokaci sannan ya dago a
fusace.
"ji nan, ba aiki ka je nema ba? Da ka samo
ba sai ka nemi abinci ba, ni zan ci da kai? Idan
bai ishe ka ba ajiye ka siyo wani ka ci, dama
ban koshi ba"
A lokacin da yake wannan sambatu lomar
da ta rage a kwanon bata wuce daya ba, don
haka Farid bai ga amfanin tanka wannan
maganar ba.
"Kai mene labari ka dawo gida sai bacci
kake da nauyi a ka? Kai ka samo aikin ne?"
a
A yanzu ya sallama ba zai koma bacci ba,
tuni ma baccin ya kare a idonsa. Kuma yana son
ya ji tsaigumin fitar abokinsa. Ya tashi zaune
tsakiyar katifar sannan ya dauki filon ya
rungume kafin ya dubi takardun da Farid ya
watsar sannan ya fashe da dariya.
"farin mutum kenan...baka samo aiki ba "
Ya sake rikicewa da dariya har da kwanciya.
"Na gaya maka baka yi serious da neman
aikin nan ba...Dubi takardun da ka fita da
su...Fotokwafe? hahaha! Na gaya maka ni jiya
da original na fita da na ga kallon da a ke yi wa
fotokwafe na wulakanci, amma ka ki yarda. Ka
zo kana watsar da su. Ji malam ka ma tattara su
wuri guda don baka da kudin sake bugo wasu"
6 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Ya ture kwanon abincin gefe guda sannan
yayi ajiyar zuciya ya jingina da wata likakkiyar
kalandar mawaka da ke bayansa.
"Oh boy! Na dena neman zabi a aiki, ko
wanne zan yi... kai! Mad a na neman aiki fa. Ka
san tun safe nan muna layi a ofishin INEC wai
an ce suna neman graduates da za su yi musu
aikin zabe, shine na ce bari na je na gwada sa'ar
wucin gadi, wallahi har karfe shida layi bai zo
kan mu ba, ba ci ba sha, ta maza kawai muke yi.
Baka isa fa ka motsa ka bar wurin ba sai a yi ba
ka. Amma Mad duk wannan wahalar saura
mutum hudu a gaba na aka ce wai mu dawo
gobe an tashi aiki. Kai ni zan koma kuwa
gobe?"
Ya saki filon da ya rungume sannan ya ja
tsaki.
"Ba za ka koma ba? Gara ma ka koma fa,
don wannan watan me gida zai zo. Kai ne ko
zaka biya wannan sabon hayan. Tun yaushe na
ke gaya maka mutane na murna in sun yi na
daya ko na biyiu a jami'a wai su sun tabbatar
sun sami aiki sun gama. Now ni matsala ta yin
na dayan ne. Duk inda na je neman aiki sai a cе
zan yi tsada basu da kudin biyan albashina, yau
ni roko nake ma a dauke ni daidai da wadanda
suka fadi a jarabawa ko ba komai ai a na biyan
su wani abu da bana samu yanzu da kwali na
amma na kasa samu. Shine kai da kayi na daya
kake neman ba zaka neman..."
1
7 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
"ban ce ba zan je neman aiki ba... cewa nayi
ba zani layin INEC ba, kenan zani wani wurin"
Ya tashi ya dauko wandonsa ya soma
sanyawa.
"Ka je fa ba ruwana. Ka je ba mu da kudi"
Ya gama sanya kayansa ya fita ba tare da
Farid ya ce masa kanzil ba, sai da ya rufe kofa
sannan ya maye gurbin da Mahdi ya bari kan
katifar domin yayi baccі.
本
Tuni kamar jiya Farid ya shirya Mahdi na
bacci, ya mayar da kayansa na jiya ya hada
takardunsa, sannan ya dada wa Mahdi duka.
"ka tashi, ai ba ni kawai aka ce na yi ta
neman aiki ba. Tashi kai ma ka fita"
Ya nannade kansa a zanin rufa ya kawo
matashi ya kara.
"Kyale ni mana Farid wai me na tsare maka
ne?""
Ya fita yana dariya.
"Ni zani neman aiki, kai kuma sai ka nema
mana na karyawa yau ba zan dade ba"
*
Kamar yadda Farid ya zata bai dade a gaban
ofishin hukumar zabe ba ya baro wurin ba don
ya sami aiki ba sai don kafin ya iso tuni an riga
an hattama jera sunayen wadanda za a dauka
kuma sun cika. Don haka ko da aka duba
takardunsa, jami'in dariya yayi ya gaya masa
cewa ai abin da ake neman ma`aikatan a kansa
baya da alaka da wata kwarewa mai nasaba da
8 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
cin jarrabawa, don haka shaidar yin na daya
bata da wata rana a nan. Jan kafa yake a kan
titin don gajiya har ya iso gaban wani dogon
gini da ya kawatu nesa da katangarsa. Bai zo
wurin don komai ba sai don ya huta kafin ya сi
gaba da tafiya, amma sai ya ga sunan dake
manne gaban wata hasumiya ta ginin ta ja
hankalinsa. Ya taba karanta tallan neman
ma`aikata na wannan ofishin a jarida da cewa
suna neman jami'ìn tattara bayanai da na
sadarwa da ma`aji, amma a wancan lokacin yayi
yawon neman wannan wuri ya kasa samu,
saboda irin wannan manyan ofisoshi ba a cika
lika sunayensu da manyan baki a babban allo
don son a sani ba, kasancewar irin wadanda ake
gayyata basa son zuwa kowane wurin yakamalam. Ya kara mikewa ya fasa zama a yayinda r
bai musa wa zuciyarsa da ta so ya shiga kai
tsaye ba. Bai sa ran zai sami aiki ba kamart
yadda ya sa ran za a koro shi ganin yadda sama
da wata daya bai taba dacewa da sa'a ba. Ya
shiga kofar mai duba ilahirin mutum cikin
mamaki, sannan ta bude masa zuwa wata
faffadar kofa wadda da ka iso gabanta take
bude kanta. Ya shigo wani faffadan falo mai
kujeru da tebura jifa-jifa. Shiru kake ji kamar
babu kowa mutane hudun da suka dukufa suna
aiki kan kwamfuta kamar kurame ko makafi,
babu wanda ya kalle shi a yayinda a rude yake
zaben wanda zai je ya tunkara cikinsu. Wata
kofar ta bude irin wadda ya shigo, wani dogon
9 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
mutum kyakkyawa kakkaura fari ya doso shi
tun daga ido har kafa, shi ma ya danne
zuciyarsa mai bugawa ya fuskance shi.
"A kwai wani taimako da žan yi maka?"
"Na zo neman aiki ne, domin tun satin da ya
wuce na ga tallan daukan ma'aikata da kuka
buga a jarida shine na ce bari na zo na gwada
sa'a ta"
Yayi murmushi da kada kai.
"Aiya! Abokina kamar kayi latti. Tuni mun
cike gurbin ma'aikatan da muke son dauka tun a
wannan satin don....
Wata kofa da ta bude da karfi kamar
fashewar gilasi ta ja hankalin dukansu suka yi
shiru na razana. Wata yarinya ce ta fito. doguwa
ce har karshe, fara ce tas. Babu abin da ba shi
da kyau a iya jikinta har tafiyarta. Kanta dauke
da kitso kanana sun haura dari biyu, tsayinsu ya
doshi gadon bayanta, amma babu ko kyalle na
rufewa, gajeren siket baki da rigarsa mai
yankakken hannu da matse jiki dukansu, sun ji
zif kamar mai ajiyar kudin adashi. Takalminta
an daddaure shi har kusan gwiwa. Tana tafiya
duk da sauri take kamar tafiyar masu tallan
kayan sawa. Fuskarta babu walwala. Ba tare da
tana kallon gabanta ba ta bangaje Farid, bata
juyo tace sannu ba ta fice a yayinda wata murya
ke ihun kiran ta da nuna isa.
Farida! Farida...Dawo nan na ce. In kika bar
wurin nan..."
10 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMajid
Farid ya bi ta da kallo na mamaki, ya manta
da wadanda ke bayansa, bai san dalilin kallon
ba, shin don tunkude shi da tayi ne ko don
kyawunta da sunanta Farida, ko kuwa don fishin
da take ciki.
Mutumin da ke yi masa magana ya dawo da
hankalinsa cikin murmushi.
"Da Allah ka yi hakuri, tana cikin fishi ne
yar shugaban mu ce. Kamar yadda na ce maka
sai dai wani lokaci, amma yanzu muna da ma
`aikata"
Ya juya ya bar wurin Farid zuwa ga wani
ma àikaci da ya bukaci da ya ba shi hankalinsa.
Farid ya dan jima a tsaye, amma bai san mai zai
ce ba, bai ji daban ba da bai sami aiki ba. Amma
ya ji daban a ganin Farida. Wacece Farida kuma
me ta ke nufi da zuciyarsa. Ya juya a hankali ya
fita. Bai tsira ba domin a wajen ofishin ya sake
cin karo da wulakancin yarinyar wadda ta busa
masa yashi da motarta mai cin taya.
Ya sake kalmashe idanuwansa bayan da ya
ture abincin wuri guda ya mike kafa, abokin
tafiyarsa bai dena kai tasa lomar ba har ma kada
cokali yake a kwanon saboda sanin amininsa ba
zai so ya cinye ya bar shi bai koshi ba, amma a
yanzu kamar bai damu ba, bai yi loma ta fi uku
ba a abincin amma ya ji duk ya ishe shi, ya dan
yi ajiyar zuciya sannan ya kada kai zai yi
magana amma kwatsam sai ya ga ya bude idanu
rai a bace.
11 Matiyan Masoya Rahma Abdull.la jid
"Ba ka ga fa yadda take tafiyar jin kai ba, ba
ka ji yadda ta cika ofishin da kara ba wai duk da
ubanta mahaifi take, wannan wane irin raino
ne?'
Mahdi ya ci gaba da gyada kai yayinda zai
yi magana.
"Farid duk na ji ka ba ni labarin nan daga
shigowar ka, sau uku ke nan har na haddace,
yanzu mene ne naka a ciki har da yin lomar
abinci uku. rumbu kamar ka..Farid kada ka
sanya kanka a uku, kada fa ka ce min son
yarinyar nan kake ?"
Da gaske Farid ya ji an rikita masa zuciya,
shi ya so wannan mara kunyar? Bai taßa zaton
kiyayya tana sanya wa mutum ya shiga ranka
tamkar soyayya ba sai yau, baya da tababa ya
san kin jinin yarinyar nan yayi.
"Ni...So?"
"Zaka iya ji kana son ta ka tsaya tsaginagini
mana, to ni tunasarwa ce tawa, Farid ko yar
tallan gyada aka kawo maka baka isa soyayya
da ita ba ballantana wannan mahalukiyar, kada
ka sanya mu a uku, bukatar mu a nan bata wuce
ta neman aiki ba"
"Ban gane me kake son cewa ba, Ni zan so
irin wannan futsararriyar? Ai talauci ba rashin
ka`ida ne a rayuwa ba"
Ya sake kai loma a abincin.
"Zaka tashi mu ci gaba da ci ko sai na
cinye?"
Ya mike da sauri ya kalli kwanon.
12 Mafiyan Masoya Rahma AbdulMa jid
“Ai ka ma cinye me ka rage, gafara"
Ya dauke kwanon a yayinda ya bar Mahdi
da cokali yana dariya
*
Ya taho da yar guntuwar zazzafar citta
dafaffiya da aka hada da sikari a wasu siraran
kofina da ake rike su a tsakanin yatsu. Har ya
iso inda take bai dena kallon ta ba yayinda ita
babu abin da take baya da yamutsa yatsunta
cikin gashin kanta idanuwanta lumshe tana
hucin takaici.
"soma kora wannan sannan mu yi magana"
Ya ankarar da ita da zuwansa a yayinda ta
bude idon ta kalle shi sannan kofinan hannunsa
""Me kake cewa?"
"Ki sha nace ki dan gasa cikinki mu yi
magana
Ta ture hannunsa cikin kada kan takaici
sannan ta mike ta bar kujerar ta fuskanci inda
wasu masu rawa ke ta cashew can nesa da su.
"Kamar fa ni nake cikin wannan matsalar ni
kadai ban da kai Ibrahim"
Ya sake biyo ta inda ya tsaya a bayanta
yanzu, ya dai kware cikin kallon ta,
"Ban gane ke kadai ce a ciki ba?"
Ta juyo bayan ta galla wani fari.
"ka ji abin da nake cewa?...Baba ubana
mahaifi ya ba ni kwana uku cewa in shirya barin
kasar nan saboda kai... kuma ka ji inda yake
nufin in je...London inda dan chairman yake
mu je mu fahimci juna... kuma ka ji yace idan
13 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
na kasa yin haka zuwea jibi, in tabbatar na ajiye
duk abin da ya mallaka min, in yi yawo ko da da
tsumma ne...1
ko?"
"Duka kin gaya min"
"kuma shine kake ba ni ruwan citta in sha
"To me zan yi kashe ki zan yi Farida?"
"Zan rabu da kai fa nace... ka san abin da
hakan take nufi?"
kai.
Ya ajiye kofinansa a gefe sannan ya karkata
"To Farida na san wannan ba zai sanya ki
rabu da ni ba ko na rabu dake... to me nene zaki
kara wa kanki damuwa?"
Ta kura masa ido a yanzu ta rasa na cewa.
"Farida... babu abin da ya saura su Baba
zasu yi a duniyar nan da zai raba mu na riga na
gama tabbatar da haka...Farida jiki na na ba ni
cewa a jinin ki akwai jini na, karewar aure ina
da da da zamu haifa tare dake, ban taba samin
kokwanto a cikin zuciyata ba, ni ne
mijinki...Tun kafin na san me nene so nake
mafarki masoyiyata me zanen rayuwarki tun
ban san ki ba...to me zai dame ni a yayinda
wani mahaluki ya kawo wa zuciyarsa tunanin
99 raba mafarkina da gaskiyar rayuwata ina...."
Ta daga zara-zaran yatsunta duka guda
goma tana nuna masa sallamawa don ya bata
dama ta fadi wani abin da ya dame ta.
"Na ji kana da aure na har ma da danka a
jiki na yaya za a yi hakan ta faru?"
14 Matiyan Masoya Rahma AbdulMa jid
Ya turo nunfashi ta bakinsa.
"aure zamu yi na sunna...aure in har kin
yarda da tsarina"
"Wane tsarin? Na mu zauna kamar wawaye
muna jira har ranar da su Baba zasu gama gabar
da kullun karuwa take? Balala baka so na ka
gaya min and I promise that you will never
find me in your life again"
Ya kara zuwa taki daya gabanta.
"Farida idan bamu bi wannan tsarin ba me
zamu yi? Farida na bi duk abin da zan iya bi, na
tura mutane da baba na ya ki zuwa, na je da
kaina na cewa mahaifinki idan yana so in bar
nawa uban zan bar shi muddin zai hada ni da ke
aure duka ya ki.. to me zan yi bau da jiran ikon
Allah? Wani abu daya da na sani shine ba zan
taba rabuwa dake ba... duk abin da zai faru sai
dai ya faru tunanin rabuwa dake ba zai taba
zuwa min ba...kuma da fadan su ba za su tabа
יי bari mu yi aure ba to...
"Sai mu fita daga rayuwarsu mu nisance su
mu bar rayuwar su mu tayar da ta mu, idan har
muna son juna”
"Farida abin da nake goyon baya kin san shi
kin san wanda bana goyon baya, na san ba zaki
zarge ni da rashin kaunar ki ba a kai idan na
sake tunasar dake...Farida ku biyu mahaifinki
ya haifa, ni kuma ni kadai. Duka duniya sun san
su da 'ya'yansu kamar yadda duka aka san su da
gabarsu, suna da suna da duk abin da ya faru
kan su sai duniya ta dauka caa duk kankantarsa,
15 Matiyan Masoya Rahma AbdulMajid
idan har su basu da niyar fahimtar hakkin kare
zukatanmu, mu mu san hakkin kare sunan
su...
Daf da ya gama ta wawuri Jakarta daga kan
dan siririn dogon teburin ta rataya sannan ta
kalle shi a yayinda yake mata kallon rikita.
"zaka jira ko? Ka jira Ibrahim... ni kuma
zan yi abin da ya dace a nawa bangaren kafin
jibin tayi"
Ta juya zata tafi, amma yayi mata burki da
karfi bayanda ya ruko kafadarta, ta juyo ta dubi
kafadarta sannan fuskarsa.
"Me nene haka Bally?"
Ya kada kai ba tare da ko kiftawa yayi ba.
"Ki yi komai, amma kada kiyi abin da zan
rasa ki...In kika yi haka ba zan yafe miki ba ba
zan yafe wa kai na ba haka ma su Baba...Kuma
kin san me zan iya yi in ban yafe ba, bana son
rayuwar da baki a cikinta Farida kuma kin san
ba zata same ni ba, domin na sanya rai a
יי tarayyar mu"
Sai da ta kare masa kallo sannan ta ja tsaki
ta fizge kafadarta ta yi gaba, bai kira ta ba ya bi
ta da ido har ta bata, sannan yayi ajiyar zuciya
ya dubi sama da kasa gabas da yamma kudu da
arewa, babu inda yayi masa sanyi a duniya ya
yamutsa hannayen sa cikin gashin kansa na
wani tsayin lokaci yana fadin.
"Ki yi hakuri Farida nine mijinki don ina
son ki...Ahh! Allah Ka san ina son yarinyar
16 Mofiyan Masoya Rahma AbdulMa jid
nan, Allah Ka da ka sanya ta yi min mummunar fahimta"
A haka yake har ya ba66alla maballan
gaban rigarsa bai sani ba bai kuma bar wurin ba
*
Ibrahim Balala da Farida ya'yan wasu
mutane ne da ba masu arziki bane kawai ba, a
tarihinsu basu taba jin labarin rashi ko karanci
ba tun daga kaka da kakanni, tun daga iyayensu
a ke musu rainon turawa kasancewar duka
iyayen na da shaidar zama 'yan kasar Birtaniya
har kan `ya'yan duk abin da ke hada su da
Najeriya itace tijara da kasashe masu tasowa da
yawancin turawa kan wakilta su saboda samin
riba mai yawa. Duk da da fari mahaifin Ibrahim
wato Zakari Abdul Hadi Bici da mahaifin
Farida Muniru Na'ibi Bici aboakaine na
samartaka kuma masu takamar'sun zo daga
asalin kauye daya bacci ne kawai yake raba su,
sai dai babu dadewa da aurensu da ma fara
wakiltar dukiyar iyayensu sai gasar kasuwa ta
fara hada su husuma, koda yake þasu fara fitona-fito da cin dunduniyar jupa ba sai a
lokacinda shugaban kasa ya so sanya Na'ibi
Bici ministan makamashi a matsayinsa na
injiniya, inda Abdul Hadi ya dauki nauyin `yan
adawa masu zagon kasa wa hakan da cewa
Na'ibi Bici ba shi da kwarewa da kishin kasa
kasancewar shi da iyalinsa basu taba zaman
kasar sama da na wata daya ba. Tun bayan rasa
wannan makami ne Na'ibi Bici ya dawo gida
17 Matiyan Masaya Rahma Abdul Majid
don kafa kansa inda ya kafa masana antar samar
da wutan rańa mai zaman kanta da gwamnoni
ke haya daga wurinsa bayan da gwamnatin
tarayya ta gaza karade kasar da wutan lantarki.
Wannan sana'a ta zo masa da tagomashi matuka
fiye da na zamansa a turai, abin da ya ja
hankalin abokin hamayyarsa da shi ma ya dawo
ya kafa kamfanin sadarwa wanda babu irinsa a
kasar ta hanyar sarkafa yanar gizo mai sauri da
saukin kudi, amma a nan ne Na'ibi yace ga
ranar sakayya da wa Allah Ya hada shi, yayi
alkawarin yin amfani da dadewarsa a kasar fiye
da Abdul Hadi da sanin manyan kasa har ma da
shugaban kasar wanda ya na cikin wasu tsaffin
gwamnoni da jiharsu ta taßa cin moriyar wutan
lantarkin hayan da ya basu a fitilun kan hanya
inda yake tabbatar da duk wata kwangilar da
zata zo ga kamfanin Dot Connect na Abdul
Hadi Bici sai ya janyo mata hasara ko rashin
karbuwa ko ma ta kubuce baki daya. Duk wani
kokari da Abdul Hadi zai yi ba tare da ya bayar
da gari ba yana yi amma ya kasa kubuta
yayinda tuni na`ibi ke ta kokarin fadada nasa
kamfanin na High System zuwa wanda zai
maye har da aikin AbdulHadi inda ya fa fitar da
tsangayar connection Matrimony, a wannan
lokaci dukan su basu tsaya amfani da hanyoyin
gasar kwarewar aiki kawai ba, tuni wannan
gasar ta haifar da amfani da manyan kudaden
cin hanci, amfani da dogayen kafa, da hanyoyin
leken asiri masu hatsari kan juna. Sai dai a duk
18 Motiyon Meroya Rahma Abdul Majid
lokacinda suke wannan basu da labarin
ya`yansu sun fara soyayya da juna bayan
haduwarsu a karshen shekarar karatu a wata
jami`a dake Kasar Canada. Hakan ta faru ne
sakamakon barin yaran da suka yi a turai
yayinda suka zo bude harkokin kudi a Afurka
domin yayan su kara samin kwarewa,.Shi dai
Na`ibi Bici ya baro `ya yansa biyu Farida da
shafik a birtaniya tare da mahaifiyarsu Salma
`yar asalin kasar Eritirya wadda ke shugabantar
wata kungiyar mata makiyaya na zamani,
yayinda shi Abdul Hadi Bici ya baro dansaa can
Kasar Canada tare da kakarsa ta wurin uwa dake
da asalin Kasar Ghana har zuwa rasuwarta a
yayinda ya isa shiga jami`a kamar yadda itama
Farida mahaifiyarta ta tura ta kasar Canadan
domin ta sauya yanayi bayan wanda tuni ta saba
da shi a kasar Birtaniya inda kaninta ya saura
tare da mahaifiyar tasu. Bayan soyayya tayi nisa
tsakanin wannan 'yan makaranta kusa da
ləkacin fitarsu ne suka fahimci ko su 'ya'yan su
wanene kuma sun san menene tsakanin iyayen
nasu, abin yayi matukar damunsu ta inda sai da
ya so shafar karatunsu, amma daga bisani bayan
kowane fangare ya tabbatar wa zuciyarsa da ba
zata iya rabuwa da masoyinsa ba sai suka kulla
yarjejeniyar kokarin shawo kan kan mahaifan
nasu kuma koda hakan ya gagara ba zasu tabа
rabuwa da junansu ba,Farida tayi aiki karkashin
mahaifinta na dan lokaci a yanayin da ya ji
matukar dadinsa, kasancewar ta yi amfani da
19 Matlyan Masoya Rahma AbdulMa