Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi masa banza, ya sake cewa, "Ni ban ga abin fushin nan ba, in ma fushin ne n zan yı tunda ni ki ka yi wa laifi, mun yi da ke za ki biyo ta nan in kin tashi schoo!? Juya masa baya ta yi tana turo baki tamkar a kan Raya ta ke jinta, ta kagara su isa ta fitar masa daga mota. Ya kalle ta da kyau, ya ce, "Da ke fa nake Mabaruka, kin juya min baya, kin kyauta kenan ki taho kanki tsaye kamar ke ki ke auren kanki, duk da kin san ba hana ki zan yi ba, amma ya kamata ki sanar min". Duk ya ishe ta da maganganunsa, sai kufula ta ke, ba ta jin za ta iya amsa masa. Ya gaji ya yi shiru. A wannan lokacin ya ji zafi sosai, kan me zai ta mata magana ta yi masa banza, ta maida shi mahaukaci kenan in ya gaji ya yi shiru kenan? Ba shi da zuciya ne da zai ta bin wannan yarinyar ta raina shi? Zuciyata ta taso masa, ya dinga kiran, “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Don ya fi karfin zuciyarsa. Idanunsa suka kada jajir saboda Gacin rai. Bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da tukinsa har suka iso. Da wani irin gudu ya shigo farfajiyar gidan saboda Gacin rai, tun kafin ya gana tsayawa ta bude kofa za ta fita, bai kalle ta ba, ya ce, "Kar ki fita". Tsaki ta ja kawai ta saka kafa ta ficen. Ai ko iskan mota ya debe ta, kafafunta suka lankwashe, juwa ta kamata saboda yanda motar ta ke tafiya. Sai dai ta ji ta tana kundumbala saboda motar na janta. Tuni ta kai kasa tare da fasa ihu. WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Cak! Ya tsaya da motar, a guje ya fito tun kan ya kashe, ya yo kanta. Ta rike Kafafuwa tana matsa su tare da kuka, wanda ba ta yi shiri ba. ne? Ya rike kafafuwan a rude yana cewa, "Kin ji ciwo Sai kuka ta ke ba baki, Kafafuwan sun rike ne gam. Ya ce, "Sannu, taso mu je". Ta ce tana kukan, "Ba zan iya ba, ba zan iya taka su ba wallahi". Ya dan ja kafar, ta fasa ihu tare da kankame hannunsa, ya ce, "Subhanallah har abin ya kai haka?" Cak! Ya dauke ta tamkar jaririya, ya shige da ita da gudu. Sai dai maigadi ya kashe motar ya rufe, tare da biyo shi da keyn. A falo ya sauke ta kan kujera, sai yarfa hannuwa ta ke tana cije-cijen lebe, fuska ta jike da hawayc. Ya daga siket din duk ta kurje a gwiwa, har saman santala-santalan cinyoyinta sun fashe sai jini kasancewar yanayin jikinta ta faye laushi, tabbas da gani za ta yi jini, haka jinin ke zubowa kamar an yi yanka mai kyau da gani lafiyayye ne. Ya kara dage siket din yana cewa, "Kin ji ciwo fa sosai". Ikon Allah, sam ta kasa hana shi, wata azabar mantuwa ma ta ke da kai wane ne, ba abin da ta ke sai kuka. Ya dade da saninta tun tana yarinya ba ta son jini tamkar ma tsoronshi ta ke, musamman ta ganshi jikinta in ta dinga ihu har sai an wanke mata, gani ta ke kamar wani babban ciwo ne. Yanzu haka ma yana lura da ita da ta dubi jinin sai ta sake fashewa da kuka tana kauda kai. 132 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Mikewa ya yi da gudu zuwa dakinsa yana circ hula ya wurgar, dan akwatinshi ya dauko na taimakon gaggawa ya tsugunna gabanta. Idan ya tabo ta sai ta yanka ihu ta rike shi a haka har ya gama treating din wurin. Sai sannan ya dubi saman kafarta ta hau kan babban yatsa kafar ta kumbura suntunı, nan da nan ya zaro ido yana kallonta, ya ce, "Kafarki ta samu matsala ko targade, ko gocewa". Fadin hakan sai ta sake fasa kuka tana kallon kafar tana cewa, "Ina, ina ne?" Abin kamar ya yi dariya, amma ya cije ganin yanzu-yanzu ta ke harararsa, ita wai ta hade fuska, amma yanzu ga ta a hannunsa ta ma manta waye a gabanta. Ta saki jiki tana masa shagwaba. Ya ce, "Idan har kafar na ta kwana ba a gyara ba za ta miki tsami, har fitsari sai kin yi. Sai kallon kafar ta ke tana ajiyar zuciya, ya ce, "Za ki yarda in ja miki?" Ta kalle shi a shagwabe ta ce, "Ka iya ne?" Ya daga mata kai yana mata murmushinsa mai kwantar da hankali. Ya matso kusa da kafar tare da jan yatsan, wani irin ihu da ta saki tare da kankame shi tana rokonsa ya kyale ta. Bai saurare ta ba ya ci gaba cike da dauriya yana jin kamar a jikinsa ne, dauriya kawai ya yi don gwanda ta yi kukan na yau a kan ta yi na gobe. Kukanta na taba masa rai, ya ci gaba da ja yana addu'a. Ita da ke kan kujera sai ga ta a kasan tayil tana ihu ta makalkale shi gam, ya sake ta ta hakura ba ta so. Sam bai saurare ta ba ya ci gaba, har sai da ya tabbatar ya fita 133 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna sannan ya kyale ta yana mata sannų. Ta kwantar da kai saman kujera tana maida numfashi. Ya shafa mata magunguna tare da mata sannu. Ba ta iya amsawa ba, ta yi shiru tana jin saukım Kafarta, yana gefenta yana mata sannu duk da ba amsawa ta ke ba har baect ya dauke ta, cak! Ya dauke ta ya shigar da ita dakınia ya kwantar. Ya yi mata addu'oli sosai bayan ya cire mata siket din gabadaya, har riga ya sa mata wacce ya ga tana sa wa. Ya dan rufe ta da bargon yana kallonia har da sakin ajiyar zuciya, duk da a bacci ta ke. Ya yi tsayс yana kallonta, ya jinjina kai tare da yin murmushi yana jin sonta na kara shigarsa komai ta yi burge shi ta ke, wannan rigar da ta ke sa wa yana sonta, tana daukar hankalinsa ya rasa nutsuwarsa yanzu yanda ta ke baccin nan zai iya komai har ya samu nutsuwa ba tare da ta iya kwatar kanta tra. Ya ce a fili, "Ba zan iya ba Mabaruka, sai idonki bude". Ya tuno maganar da suka yi da Ibrahim yau da ya same shi a ofis bayan ya zauna yake cewa, "Ina rigimammiya, mai kama da jaririya?" Ya yi dariya yana shaia kai, ya ce, "Wa? Mabaruka tana nan lafiya lau, ko in ce maka tana school, yau suka koma. Amma ba ta sánar min ba kokarin tafiya ta ke ba tare da na sani ba. Ya yi dariya ya ce, "Wallahi sha'aninku na ban dariya abokina, Mabaruka sai kai haka ita ma sai kai, ta kasa gane haka. Amma ina hango muku alkhairi a gaba, za ka ba ni labari" WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Ya ji dadin maganarsa, amma yai jim! Can ya ee, "Ta ya ya kenan alhalin kullum dodonta ne ni ba ta da wanda ta tsana sai ni, yaushe ne za mu zama daya?" Ya ce yana kallonsa sosai, "Kada ka ce min har yau ba abin da ya faru tsakaninku?" Ya girgiza kai tare da ccwa, "A'a sam". Ya ce, "Amma ya haka my friend, kana tsoro ne, ko ba ka sonta?" Tambayar dariya ta ba shi, ya yi murmushin takaici, ya ce, "Ba haka ba ne Ibrahim, kai ka san ni, ka san wane ne ni, ka san ya Mabaruka ta ke a raina da matsayinta, ba zan iya misalta maka ba, kawai ni na san ina sonta sosai. Tsoro kuma ba ta taso ba, duk da ranar farkо rotse ta min don ma ina da tsawon rai". Ya ce, "Amma serious my friend ya kamata ka yi wani abu, wannan nisancin ba zai kawo muku mafita ba, kusancin da za ku yi shi zai yi silar daidaita komai a hankali". Ya yi jim yana tunanin maganarsa, can ya te, "Tabbas haka ne maganarka, ni na san ta wannan hanyar zan jawo hankalinta. Sai dai wani alkawari da na yi wa kaina, ba zan kusance ta ba ar sai da son ranta, sai ta amince da ni..." Ya katse shi, "Yaushe kenan, ta ya kuma ba ka da wata mafita face aikata abin da Allah ya halatta maka, ba ka san alkhairin da ke cikin hakan ba, ta haka ma sai ka ga ciki ya billo. To wallahi ta sanadin dan nan ko cikin za ka sha mamakinta ko da ba ta so cikin ba, amma sanadin dan sai ta so uban dan". 135 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Ya kalli Ibrahim da sauri ganin shawarar da ya kawo, kai amma zai so dan da Mabaruka ta haifa masa ko 'ya fiye da a ce wata ce. Tabbas farin cikinsa ba zai misaltu ba a ce dansa ko 'yarsa ya fito daga jikinta har abada ba zai daina farin ciki ba. Ya ce, "Ban taba jin magana mai sa farin ciki irin wannan ba Ibrahim, ka sa min kwadayin hakan, zan so hakan". Ya yi murmushin ganin cin nasara, ya ce, "Sosai sai ma ka ga abin ya tabbata, kuma son da za ta maka wallahi sai ka yi mamaki sanadin fan nan dai". Sosai ya gamsu da hakan, yana jin ba zai yi sake ba, sai dai wani gefe na zuciyarsa na hana shi ya dube shi ya ce, "Shi kenan ka taya ni addu'a, zan yi iya kokarina". Ya ja doguwar ajiyar zuciya, ya dube ta. Yanda ta ke baccin ya dan rankwafa daidai kanta, ya shaf kumatunta tare da sumbatarta, ya ce a fili, "I love you". Ya ja mata kofar ya wucė zuwa dakinsa, ya dade zaune a saman darduma yana fada wa Allah matsalolinsa Yai masa maganinsu, Shi ne kadai mai iyawa. *** *** *** A kwana a tashi, duk lokacin da aka sa sai ya zo ya wuce, yau satinta tara a gidan Imran, abin da ya rage mata na lissafinsu saura sati uku ya sallame ta, kullum sai ta yi mark. Yau lahadi ne, duk suna gida ita da shi, tun jiya da yamma da ya shiga dakinsa ba ta sake jin motsinshi ba ko da zuwa masallaci, musamman da yanzu ta kan zauna falo. Sam ba ta yi yunkurin ta shiga ta duba ko lafiya yake ba, 136 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna musamman kasancewarsa in dai weekend ne ba inda yake zuwa, yana gida, gidan ma yana makale a dakinta duk da yanda ta ke masa in ya gaji ya fito falo ya zauna yana kallo. A haka yake cinye weck din, amma ta share tai zamanta. Sun yi da man da Rafi'atu za ta zo, tana nan zaune har a iso, kullum in sun zauna labari kamar sun dade ba su hadu ba, sai karatunsu suna sake nazari daya ta layar da daya inda ba ta gane ba. Sun dade, can suka ga wani ya shigo, suka gaisa ya cc, "Sunana Dr. Faruk mun yi waya da Imran zan zo yanzu in duba shi, please ko yana ciki?" Suka kalli juna ita da Rafi'a, nan da nan ta hade rai ta nuna masa dakin ba ta ko kallo, ba ta ee komai ba. Ya gamsu ya kalle ta, ya wuce tare da cewa, "Thanks". Ba ta ce komai ba, sai ma fushi da ta kc. Rafi'atu ta dube ta da mamaki, ta ce, "Ban gane ba Mabaruka, da man Imran din ba shi da lafiya amma ba ki fada min ba tunda na shigo na shiga na duba shi, ke kanki ban ga kina ziyartarshi ba a kai-akai, kin barni muna ta shewa ashe yana ciki kwance, na sha ma ba shi gidan? Ta ja dogon tsaki tare da dauke kanta daga ita, ba ta ce komai ba. Tsam Rafi'a tamike a fusace ta wuce dakinsa. Yana kwance kan gadonsa, ya sa hannuwa..iyu ya danne kansa, likita na tsaye kansa. Ta shigo da sauri tana cewa, "Subhanallah, sannu Ya Imran. Bai iya daga kai ya. kalle ta ba, sai dai ya ce. "Yauwa Rafi'atu, kin zo ne?" Ta ce, "Eh Ya Imran, da ma ba ka da lafiya?" 137 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Ya ce cikin ciccijewa, "Wallahi kaina ke ciwo, ba na ko iya đaga kan". Ta lausaya masa sosai, ta ce, "Sannu, Allah ya sauwake, wallahi ban sani ba?. Ya cc, "Ina Mabaruka?" Та сс, "ТTana falo ba ta sanar min ba". Ya dan juya kamar ana sara masa guduma a kan yake ji. Ya yi masa matukar nauyi, ya ce da kyar, "Ba ta sani ba ita ma, tunda na shigo ban fita ba, kuma kin santa ba shigowa dakina ta ke ba". Ta cc, "Sannu Ya Imran, Allah ba ka lafiya, Mabaruka ba ta ji. Amma insha Allahu za ta bari, ka yi hakuri" A sanyaye ya ce, "Allah ya sa Rafi'a, na gode. Kin gani dai ina bukatar kulawarta, amma ta share ni tun jiya nake juyi a nan ina kuka, cikina na ciwo na sha ma mutuwa zan yi, amma ba ta leko zi ba haka na kwana ba bacci ina juyi, ban samu bacci ba sai kuma ciwon kai na samu cikin ya yi sauki. Sai dai kan Lana ko iya daga ido tamkar zai sarc Ta ce, "Sanna". Cikin tausayawa kamar ta masa kuka. Likitan ya yi aune-aunenshi har da ma zazzabi da rashin bacei, gefe kuma akwai damuwa a ransa. Ya ba shi shawarwari da kwantar da hankali, sannan ya sa masa drip ya bada magunguna ya sha. Rafi'atun ta fita ta dafo masa lipton a cup ta kawo masa. Da kyar ya tashi zaune, sai da suka taimaka masa ya kasa sakin hannun yana dafe da shi ko ido a rufe. Likitan 138 WAVE ANGON?-3 Maryam Jatar Kaduna ya ba shi ya sha sosat sannan suka ba shi maganin ya konia vaa kwanta. Sun dade tare da sia suna masa sannu da sannu bacci ya fara kama idonsa, ya ce wa Rali'atu, "Mabaruka tana nan lafiya dai ko, ba abin da ke damunta?" Cikin tausaya masa ta ce, "Eh lafiyarta lau". Ya ce, "Don Allah ki kular min da ita Rafi'a, kar ki yarda ta bata ranta in tana son abu ki mata, kar ki sa ta fushi kafin na ji sauki na tashi, don Allah Rafi'a". Wasu kwalla suka fara yunkurin zubo mata ganin yanda yana kwance ba shi da lafiya, amma yana sambatunta, matar da ba ta sonshi ta gwammace mutuwarsa a kan rayuwarsa, tana ransa. Ta ce, "Insha Allah zan kula, Allah ba ka lafiya". Ya ce, "Amin, na gode Rafi'a". A haka dai har bacci ya dauke shi dafe dai da kan, likitan ya cire masa hannun a hankali ya ci gaba da baccinsa, suka mo ita da hikitan suna tafe suna 'yan maganganu. Dr. Faruk din ya dube ta, ya ce, "Amma ya ku ke da shi, ko ke ce Sharifa Kanwarsa?" Та сe, "A'a, ka ga na yi kama da Larabawa ne jinsinsu?" Ya yi dariya yana kaloonta ya ce, "Sosai ma, kamar daga can ki ke". Ta yı dariya jin tsokanarsa, tana baka amma yana kiranta Balarabiya, ta ce, "To shi kenan na gode, amma ba Sharifa ba ce, ni ma dai kanwarsa ce". Ya ce, "Da kyau kanwarmu ce kenan?" Ta jinjina kai alamae eh tana dariya. 139 Π WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna a Ya ce, "Kina nan kenan har anjima in dawo in ya tashi?" Π Ta yi jim tana tunani, ya katse ta, "Please say yes, kina nan". U Ta yi dariyar da ba ta yi niyya ba, ta ce, “Shi kenan 2 na ji. Ya yi dariya shi ma, ya ce, "Yauwa na gode. To amma ni ba ki faďa min sunanki ba alhalin kin san nawa?" Ta ce tana kallonsa, "Ana ce min Rafi'atu". Ya jinjina kai, "Da kyau ya yi dadi". Har suka iso inda Mabarukar ta ke zaune, ta yi kicinkicin da fuska tana harararsu. Ya ce, "Sai na dawo kenan, ko za ki ba ni lambarki?" kenan?" Ta ce, "Lamba kuna'?" Ya ce, "Sosai, ko za ki hana ni?" Ta yi dariya, ta ce, "A'a". Ya ce, "In kin hana ni za ki iya hana yayanki Тa сe, "A'a in ka dawo ka karba". Ya ce yana kallonta, "Promise?" Ta daga kai alamar ei.. Ya ce, "Shi kenan sai na dawo din, ina ganin zai dade yana baccin nan, zan dawo lokacin da zai ashi din insha Allah". Ta ce, "Aliah ya sa". Ya ce, "Amin". Ya dubi Mabaruka, ya ce, "Sai anjima Madam, Allah kara sauki" Ya wuce, ci kanka ba ta ce ba, ta raka shi da hararга. 140 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Rafi'ar ta zauna tana kallonsa har ya fita. Ta yi murmushi kawai, ta juyo ta kalli Mabarukar ta ce, "Amma dai Mabaruka ba ki kyauta ba, ban san me zan kira abin da ki ka yi ba. Sam ba ki da tausayi wallahi, mutun darajarsa ta wuce duk yanda ki ke tunani, a hakan da ki ka tsane shi ba kya sonsa a haka Allah yake sonsa, mai yiwuwa ma ya fi ki kusanci gurin Allah, haka zalika iyaye da 'yan uwa abokai da aminan arziki ke sonsa fiye ma da yanda naki ke sonki. Ya fi ki komai, ya fi ki ilimi, asali, dukiya, kyau. Ban ga abin da za ki nuna masa ba sai mugun hali da kafiya. Imran mutum ne cikakke har da rabi ma, ya fi karfin wulakanci idan ba ki sonshi dubunki na sonshi, suna kaunarsa, don ba ki damu da shi ba akwai wadanda suka damu da shi fiye da yanda aka damu da ke. Kiyayyarsa da ki ke ba abin da za ta rage masa ko ta kara masa, kimarki ce da darajarki ta ke raguwa a idonsa, ga shi can kwance ba lafiya cikin tsananin bukatar kulawa, kin banzatar kin share shi ya mutu ma ba damuwarki ba ne, in ya mutu gaba za ki yi ki je ki auri wanda ki ke so. To wallahi ki sani, ki ka yarda ya kufce miki ya miki nisa, wata ta kama ta rike gam. Wallahi ba ki isa ki kamo shi ba. Shi kanshi kallo ba ki ishe shi ba, tun wuri ki yi amfani da damarki kafin ta kufce miki, wata tana can tana neman irinsa ta rasa me saukin hali da hakuri, hankali da nutsuwa, sanin darajar mutum ko a ya yake. Amma ke kin banzatar, wallahi ki nutsu ki wa kanki fada, ki rungumi mijinki adadin soyayyarsa da za ki samu idan kin amince da shi za ki sha mamaki, ba zai misaltu ba. Ki ya da duk wani abu da 141 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna zuciyarki ke so, ta ke wasafta miki ki karbi kvautar Allah, ki bar wa Allah sai komai ya zo miki da sauki yanda ki ke so. Ni dai na fada miki". Tana yin shiru ta ja dogon tsaki tare da harararta, tanke ba ta ce komai ba. Ta jawo carphone ta sa a kunne, jinjina kai ta yi tare da cewa, "Allah ya shirya ki". Wannan baccin ya dade yana yinshi kamar ba zai tashi ba, abin ya ba Rafi'a tsoro, ta dinga zarya dakinshi ko ya tashi? Duk sanda ta ga yana dai baccin sai tsoro ya kamata, ita dai Gimbiyar tana daki nad tana game hankalinta kwancс. Daidai shigowar Dr. Faruk da motarsa, daidai tashinshi, wasai ya ji kansa, zazzabin ma babu sai ma zufa da ta keto masa. Ya farka ya ji shi sharkaf, ya yi mika tare da salati, abin ya ba shi mamaki yanda ya ji shi garau, ya cire karin ruwan ya shiga bandaki. Tare suka shigo dakin da Rafi'a suna yan labarinsu, abin ya ba su mamaki ganinsa ya fito daga bandaki, jikinsa da ruwa, likitan ya shigo yana cewa, "Me zan gani patient dina ne da wanka?" Ya yi dariya ya vece gurin drower cikin rashin karfin jiki yana cewa, "Wanka ma rahma ne, na tashi tamkar an zuba min ruwa shi ya sa na yi wankan tare da alwala, rabona da sallah tun jiya". Rafi'atu ta zauna tana farin cikin ganin tashinshi, ta ce, "Ah lailai jiki ya yi kyau, ga shi ka tashi garau ba ciwon kai. Ya zaro jallabiya daga kayansa yana cewa, "Kamar ma ban yi ba, ina rigimammiya ta?" 142 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Ta yi murmushi, "Tana can dakinta". Ya ce, "Ba damuwa dai ko?" Ta daga kai alamar eh tana kallonsa, ya ce, "Da kyau kina da tukwici da ki ka kular min da ita Dr. Faruk ya ce, "Anya ba ni zan ba da wannan tukwicin ba, don tsayuwar kamar tawa ce, ni na roka". Ya juyo yana kallonsu daidai yana son yin dariya, ya ce, "Ban gane ba, me ku ke nufi?" ku". Likita ya yi dariya, ya çe, "Me ka fahimta?" Ya ce, "Kai kar fa ku ce ciwo na alkhairi ne gare Ya ce, "Haka ne ma, ni zan ce gwanda da ka yi ciwon". Ya fada yana kallon Rafi'ar. Ta yi dariya tare da sunkuyar da kai, ya ce, "Ah iallai na ga alama, dukkanku sako daya ne a zuciyoyinku, ku gwanda ma. ko Rafi'a?" Ya fada yana kallonta. Dariya ta yi ta tashi ta fita da gudu cikin jin kunya, likitan ya bi ta da kallo cikin sha'awa yana kara jin nutsuwar hakan a ransa, tabbas ya yaba. Ya kalle shi се, "Ya dai mutumin. Maganarka fa haka ne, ko ya gani akwai matsala?" Ya ce, "A ina, gurinta?" Ya ce, "Eh". Ya ce, "Ai mutumin kwantar da hankalinka tsumma a randa, ba ka da matsala na fada maka, komai ya yi daidai". Ya ce, "Allah mutumin?" 143 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Ya ce, "Sosai, ka yarda da ni, na santa fa amıniyar matata ce 100 percent na goya maka baya, wallahi ba na shakku, Rafi`atu yarinya ce mai hankali da nutsuwa lanı da tarbiyya, iyayenta dattijai ne masu kirki, tana da ilimi masha Allat". Ya ji dadin bayaninsa sosai, ya kara nutsuwa ya ce, "Sai dai bangarenta ban sani ba ko na samu kutsawa". Ya ce yana sa jallabiyar, "Au kai ba ka gani ba, ba ka fa da sauran wahala, ka jefa ka cafke ba ka ga yanda ta yi ba? Ai alamar ta karba kenan". Ya yi sowa suka tafa, ya ce, "Godiya nake mutumin, Allah kara lafiya, ka kara danna ni gurinta har in shige". Ya ce, "Kar ka damu, ka shiga na santa fa zan muku jagora, bangarenta ni na san ba ta da matsala, haka Gangarenka zan shaide ka. Tafiyar daya ce kai da ita, na yaba wallahi sosai". Ya jinjina kai alamar gamsuwa tare da cewa, "Na huta da fadan su Hajiya yau zan je musu da zance mai dadi". Ya sa dadduma yana cewa, "Ni zan yi wannan bayanin, kar ka damu. Ni ne waliyinka, ni ne waliyyinta". Suka yi dariya tare, ya kabbara sallar. Lokacin da ta fita ita kanta haka nan ta ji ta cikin nishadi, fuskarsa ta kasa bacewa a idonta, musamman dariyarsa ta shiga fakin ta zauna tana cewa, "Dr. Faruk?" 144 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna Ta bi ta da kallo bayan ta sa purse a game din, ta ce, "Ban gane ba, na fa lura tunda ya zo ki ke wani rawar kai, haka da ya dawo kina jin maganarsa ki ka wani mike". Ta tashi zaune tana murmushi, ta ce, "Ikon Allah mana Mabaruka, sanadin ciwon mijinki na kama nawa. Lekaci daya na ji na nutsu da shi, wani abu ya daki zuciyata farad daya, har kagara na yi ya dawo". Ta ja tsaki tare da harararta ta koma ta kwanta tana cewa, "To dan iska dai ne ba na kirki ba". Gabnta ya yanke ya fadi, nan da nan yanayinta ya sauya. Ta dube ta da kyau, ta ce, "Ban gane ba Mabaruka?" Ta ce, "Dan iska dai ne na fada miki, duk abokan Imran baka suke. Shi kanshi ba ki ga dan iskan ba ne? Abokin barawo ai barawo ne". Sai yanzu ta gane inda ta nufa, ta ja tsaki ita ma, ta ce, "Na ji fin ya fi zama dan iskan ma ina sonshi, ni ma in zama ‘yar iskar, wato Imran ya ja masa tunda ba ki sonsa kowa ma ba kya so? To wallahi sai ki ta yi, yanzu muka fara. Ina sonsi:i ke ki je ki ta kin mijinki". Ta harare ta sam ba za ta so wani abu ya shiga tsakanin kawarta da abokin Imran din ba, gabadaya abin da ya shafe shi ba ta so. Idan ta bar gidanshi dole ne suna tare da Rafi'a, ba za ta iya rabuwa da ita ba ta san haka za su dinga sintiri tsakaninsu, ba za ta so a ce ga abin da ke hada ta da Imran din ba in ta barshi ta barshi ke nan, kar watarana su hadu a gidan Rafi'ar din, 145 WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna wannan ne dalilin da ta so ta lika musu mugun abu don kar Rafi`ar ta sa wa ranta. Ta ce, "Ke ba ki ganewa Rafi'a, ni kadai na san mugun halin Imran, kuma duk abokansu haka suke matansu suna shan wuyarsu kowa da tabonsu. Ina tare da matansu. Ta ja tsaki ta ce, "Na ji, a haka nake so, kullum ma ya dinga dukana idan na aure shi kin ji ko?" Haushi ya hana sai harara ta sa kafa ta magana, ta ture ta tare da cewa, "Ni tashi ki ban wuri tunda ba ki jin magana" Dariya ta yi ta mike tana cewa, "Gidan ma zan bar miki in taſi namu gidan, kuma dan iskan zai maida ni. Ta ficewarta abinta. Haka ko aka yi, bayan ya gama kara duba shi da ba shi magungunan suka yi sallama, Rafi'a ma ta masa sallama da fatan samun sauki suka fice a motarsa. Har kofar gidan su Rafi'a, sun yi musayan lambobi bayan sun taba hira ta fahimtar junansu, kowannensu ya gamsu ya nutsu da dan uwansa. Ta fito suna daga hannuwa ta shige gida cike da farin cikin yau ta yi miji. Bangaren Imran kuwa bayan ya raka su sun tafi, kai tsaye dakinta ya nufo ya shigo tare da sallama, idonsa na kanta. Ta dago ta kalle shi sau daya ta dauke kai tana amsawa a ciki-ciki. Sosai ya fada, idanunsa sun zurma da gani ya sha ciwo kamar wanda ya shekara а kwance. Ba ta damu ba ta ci gaba da game dinta. 146 WAYE ANGON? 3 Maryam Jafar Kaduna Yana daga tsayen ya zura hannuwa cikin aljihu yana kallonta, ya ce, "Ya ki ke? Da fatan ba abin da ke damunki?" Ta yi masa banza, sai ma turo baki da ta ke. Bai damu ba, ya ce, "Shi kenan, da ma na leko na gaishe ki, kuma na ga lafiya ki ke? Bari in koma

Chapter 9 of 11