ya rufe ya tsaya yana kallon
lafiyarsa. Su ma haka sauran ma'aikatan ba dai waya
yake ba kuma. Can ya tada motar ya fice, suna masa a
dawo lafiya.
Tana jin fitarsa ta ja tsaki, tare da cewa, "Aiiah
kar ya dawo da kai, dan iska jarababbe".
SULAIMAN
17
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Sai da va kwana da kwanaki a stafion din sannan
aka sake shi bayan shan duka da azaba da ya yi an masa
horo mai tsanani aka kuma sa masa sharadi da doka, aka
masa iyaka da Imran da iyalinsa. Ya sa hannu Daddyn
Imran ma ya sa hannu, sai D.P.O da sauran masu shaida,
sannan aka sake shi ya dawo gida a tangade yake tafiya,
ya yi baki ya rame, ga jarababbiyar yunwar da ke
damunsa.
Inna na zaune tsakar gida ta kasa ta tsare, Nafisa
da ke fama da itacen tuwo tana kallonta kamar yand: ta
saba ya shigo, ta bi shi da kallo galala.
Ya sulale ya zauna jiki duk ciwuka, ta ce,
"Sulaimanu?"
he?"
Ya ce, "Na'am lana?"
Ta ce, "Sun kyaie ka, sun sako ka ko ko ka gudo
Ya dube ta da kyau, ya kawar da kai, ya ce, "Sun
dai sake ni, ta ya ya ki ke tunanin zan iya gudowa?"
Ta tafe baki, ta ce, "To yanzu dai ya rage naka,
in ka nutsu su ma su kyale ka ka sha ruwa. Yanzu dai
me ka ci riba? S. biyu kenan suna sakaya ka duk kan
ka taba musu da. Wallahi idan ba ka kiyayc su ba na
rantse idan suka kama ka ba za su sake ka ba, na ce ka
hakura ka bar musu mata ba taka ba ce, amma ka ki ji,
yarinya tana can gidan mijinta hankalinta kwance, kai
kana nan kana hakilo ka ki ci bare ka maro, sai wahala
da man ba jikin kirki ba, duk talauci ya rairaye ka, sai
shegiyar zuciyar tsiyar ba ka da kwandala".
18
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ya ce, "Don Allah ki kyale ni na huta, na dawe
maimakon ki tare ni da magana mai dadi sai ma Karа
min zafi da ki ke, laifi ne don na yi fada da azzalumai
wadanda suka kwace min mata, don ni sakarai ne sai in
sa musu ido?"
Тa сe, "A'a jarumi, ci gaba har ka kwato ta. Na
rantse ka yarda aka kara kama ka da laifi har aka kuile
ka ba zan taba kai maka ziyara ba bare a kai ma abinci,
sai dai ka mutu don ubanka. Ba wai binka zan dinga yi
ba".
matata
Ya ce, "Na gwammace haka a kan na bar mishi
Та се, "Мatarka ta ina, wa ya ba ka? In ma ka
kwato din to ba a nan gidan ba, na gaya maka Allah”.
ta Nafisa ta debo masa ruwa a kofi mai sanyi
kawo masa. Zai karba ke nan ta sa hannu ta kwaбе
ruwan, ya zube. Ta dubi Nafisar ta ce, "Kin raina ni ko,
ba kya jin magana yanzu har ke za ki ba shi ruwa ina
zaune, ke ki ka haifar min shi bare ki fi ni sonsa da
tausayinsa fi'ilalliya?"
Ta sunkuya cikin ladabi ta ce, "A'a ki yi akuri,
zan kiyaye".
Daga haka ta mike, ta bi ta da harara tana cewa,
"Yar banzar yarinya sai munafunci, kinibabba".
Ita dai ba ta ce komai ba ta koma bakin aikinta
tana jin takaici.
Ya dube ta cikin fushi, ya ce, "Ke dai inna ta
ko'ina matsala ce, yarinya ba ta takura miki ba kin
19
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna takura ta, ba ta matsa miki ba kin matsa mata, duk don
Ta ce, "Wallahi zan kwade maka baki, sakarai
mara wasau, so ka ke in sake mata ta raina ni, ta samu damar gallaza min, har kai ba za ta kyale ba wallahi"
Mikewa ya vi ya gaịi da jin maganganun nan, so
yake ya huta, ya san ba za ta barshi ya shiga dakin
matarsa ba ya kwanta yanzu da rana tsaka, don haka ya
dubi Nalisar ya ce, Dan samo min tabarma da filo in kwanta zaure (soro) ko ya fi iska-iska".
Karaf Inna ta mike tana cewa, "Ta ki ta dauko
wani sabon kicihi ne, zo ka karbi wannan bar nata, ba ka
san me aka barbada ba”.
Ta shige daki don ta dauko. Wani abun in ya kai
intaha ba ya magantuwa, shiru ma ya fi shi, don haka ya
ja ya yi tsaye kawai.
Ta miko masa tana cewa, "Je ka shimfida abinka
ka huta, kaſin ka tashi na dafa maka ruwan wanka".
Amsa ya yi ba tare da ya ce komai ba, ta wuce.
Daidai shigowar Samira, ana tafe ana wakam
cinga. na iska ana kwai. Ya dube ta, ya ce, "K dai ba
za ki iya zama ba, kina can shegen yawonki ba kya nan,
ba kya can ki shiga nan ki fita nan, ba za ki taba zama
gidanku ba?"
Taturo baki ta shige ciki tana gunguni, ya ce,
"Allah ya shirya ki". Ya shimfida ya kwanta.
*** *** ***
10
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
imran kuwa ko da ya lita din kai tsaye gióan su
Mommy ya wuce don gaishe su kamar yanda за
alkawarta wa kansa duk saliya zai dinga zuwa yana
gaishe su, sannan ya wuce ofis. A kan dinning table ya
tarar da su suna breakfast. Nau'ikan abinci a jere kala da
kala, sai kamshi ke bankadowa. Ya zauna a daya daga
kujerun tsohuwar yunwarsa tana tasowa, ya gaggaishe su
cikin ladabinsa da girmamawa.
Daddy ya се, "То уа rigimammiyar Mabarukar,
lafiya muka baro ku ko?"
Ya yi murmushi ya ce, "Sosai. lafiya kamar ba
ita ba".
Momy ta ce, "Haba?" Cikin jin dadi.
Ya dube ta ganin yanda ta ke jin dadi, уа се,
"Sosai ma, ni ma na yi mamakinta".
Farin ciki ya saukar musu, suka ce, "Ah da kyau,
Allah Kara daidaita ku".
Mommy ta ce, "Da man na ce muku za ta saki
jikinta in dai akai auren, wuyarshi ba a yi ba
Daddy ya ce, "Sosai
lta dai Sharifa jinsu ta ke, tabbas tana jin ya fada
ne, amma ba haka ba ne, a idonsa ta ke gane damuwar
dan uwanta. Ba ta ce komai ba ta ci gaba da cin
abincinta.
Matuka yawunsa ya dinga tsinkewa a abincin
uau, sai hadiyar yawu yake, musamıman da ya dade da
sania zakin hannun Mommy, abincinta yana juya masa
kunue.
21
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Mikewa ya yi yana duban agogo, ya ce,Bari in
wuee ofis
Mommy ta kalle shi cikin tsokana ta ce, "Ba za
ka cı abincinmu ba yau don an yi aure, sai na amarya
ko?
Ya yi dariya iyakarsa fuska, ya ce, "Sosai, komai
sabo Mommy ai ya fi dadi
Daddy ya сe, "Пaka ne fa, mu cin tsohon hannu
ya ganmu, a gaya wa amaryar sai mun zo shan gara a
tanadar mana da abinci mai dadi".
Ya dan sosa keya, ya ce, "To Daddy sai kun zo
din, za ta ji
Ransa na son abincin nan, amma cinsa shi zai
fallasa komai, ba ya son tun yanzu ya fara tona asirin
gidansa, musamman da ya fahimci yanzu hankalinsu ya
kwanta, sun nutsu suna nishadinsu, duka yaushe akai
auren har za su fara shiga wani tashin hankalin? Don
haka dole ne ya hade yawunsa da yunwa ya hakura da
cin abincin, ya ya iya da Mabarukarsa?
Suka yi sallama ya fito, Sharifa ta biyo shi har
bakin motarsa. Ya dube ta, ya ce, "Ka: rata lafiya dai na
ga fuskarki wani iri, me ya faru?"
Ta yatsine fuska kamar za ta yi kuka, ta ce, "Ва
na jin dadi bigbro, damuwa ta cika min rai".
Ya dube ta da kyau, уа се, "Тa me? Mene ne
matsalarki?"
Ta ce, "Kai ne damuwata Yaya, koda yaushe ina
tunaninka Bigbro, a wane hali ka ke, na dadi ko na bakin
cıki? Me Mabaruka ta maka? Na kan rasa amsoshin nan,
22
WAYF ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
annia zaciyata tana fada min da akwai matsala da kyar
na yi bacei jiya
Ya yı shiru, tabbas haka ne, to amma ba zai iya
gasgata Kanwar tasa ba, dole ne ya karyata tunaninta don
samun nutsuwarta, ya ce cikin kulawa, "Ba komai
kanwata, ina cikin farin ciki, ke kin san Mabaruka, kin
san ya muke da ita a da, ha za ta taba cutar da ni ba.
Lafiya lau muke".
Ba ta yarda ba ta ji ne kawai, amma ta ce, "To ná
jı yau da safe me ta girka maka, ka ci ka fito?"
Ya yi shiru, sai can ya ce, "Wai Sharifa me ke
damünki? Kina son kure ni ne? zan miki karya ne, ba ki
yarda da yayanki ba?"
Kwalla ta ciko idonis, ta ce, "Ina sonka Bigbro,
bana son damuwarka, anjima zan wuce jirgin karfe hudu
zan bi, ina da test gobe, idan na barka a wannan halin
Bigbro ba zan iya karatu ba, zan tafi ina tunaninka, bana
son damuwarka Ya Imran, don Allah ka fada min
gaskiya".
Ya dafa kafadarta cikin son kanwar tasa, ya ce,
Da gaske kanwata ki yarda da Yayarki, lafiya lau nake,
ba rnai takura wa yayanki. Ki sa haka a ranki, ki nutsu ki
tafi, ba abia da ke damunki don ki yi karatu mai kyau".
Ta yi shiru tana kallonsa, shi ma haka tsawon
dakiku ta ce, "Shi kenan Yaya, na bar wa Allah komai,
Shi zai tsare min kai, Ya kular min da kai. Na barka a
hannunSa, kai ma ka kular min da kanka, F'il miss you
ligbro because Ilove you".
23
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Hawaye suka zubo mata, ta fada jikinsa. Shi ma
ya ji taasayin kansa da na kanwar tasa. Ya ruagume ta
sosai tsawon dakiku, sannan ya dago ta yana share mata
hawayen, ya ce, "Yayanki shi ma yana sonki, yana tare
da ke kowane lokaci kina ransa".
Ta ji dadi sosai, har sai da kyawawan hakoranta
suka ljo, ya kara cewa, "Kuma ina nan lafiya ba abin da
zai dame ni, idan ki ka dawo za ki mamakin yanda za ki
gan ni na zama kato, tulele".
Ta yi dariya sosai, ta ce, "Shi kenan Bigbro,
Allah tsare min kai, Ya kare min kai”.
Ya ce yana dariya shi ma, "Amin kanwata, ki je
ki yi karatu sosai, zan billo, ki fada wa Baffa zan zo
musu da amarya, za mu kwana biyu".
Ta ce, "Allah ya sa Bigbro, zan yi karatu sosai,
promise.
Ya ce, "Cood, za ki ji aleri.
Ta ce, "No, am ok.
Ya ce, "A'a ban yarda ba, student sai da
kwandala
Ta ce, "Shi kenan Bigbro, za. eka anjima gurin
Antin nawa kafin na wuce".
Ya yi shiru inda son samu ne kar ta je, amma ta
ya zai hana ta? Ya ce, "Well, amna in kin ga lokacin zai
miki kadan kafin ku tashi sai ki wuce kawai, got it.
Ta kada kai tana murmushi da jin dadiu ga ta ga
dan uwanta, ba ta sod rabuwa da shi.
Ya shiga ya zauna yana kokarin sa key, ta leko ta
window, ya ce, "Ya aka yi kuma?"
24
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
A shagwaбe ta ce, "Shi kenan, ka tafi ba zan
sake ganinka ba?"
Ya ce, "Sharifa rigima ko?"
Ta turo baki.
Ya ce, "Is ok, kada ki damu, ni zan raka ki har
sai kin shirya ki kira ni".
Ta ce, "Ok Bigbro, a dawo lafiya, Allah isare".
Ya ce, "Amin". Ya wuce, har ya fita tana dago
masa kannu. Ta juya ta shige cike da farin ciki.
***: *** ***
Tunda ya fita yunwa ta dame ta ainun, da ta jure
ba za ta taßa cin abinci ba har ta bar gidan, anma da ta ji
ta gagara jurewa rabonta da abinci tun jiya da safe don
haka ba shiri ta fito don nema wa kanta wani abu.
Karfe sha biyu na rana gidan fes yake an share an
goge, sai tashin kamshi. Sai da ta tambaya ina ne kicin
aka nuna mata.
In da gidan Sulaiman ne da ta yabi kicin din
matuka, haduwarsa ta kai, shin anya ma kicin ne?
dukiyar da aka narka masa, na'uror da abubuwa na
kwalliya. Ta jinjina kai ta wuce store, har ta fara tunanin
dafa wani abu sai ta tuna, ai kayan duk nasa ne, shi ya
siyo su da geminsa. In ma na gararta ne da sunanshi aka
kawo su, don haka ta sauke tukunyar da ta daura iana
cewa, "AHah ya sauwake na ci abincin nan. Ta dawo
falon ta zauna tana kumburi, wai ta yi fushi, ita dai
yunwa ba yar gidansu ba ce, sannan ba a mata fushi, tun
25
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
tana daurewa har ta kasa. Mikewa ta yi ta wuce daki ta
vafe gyalenta, ta dauko furse ta fito.
Ba wanda tai wa magana daga ma'aikatan,
direban da aka aje ya taso yana cewa, "Hajiya za ki fita me?
Ta yi masa banza tana tafiya. Ya sake biyo ta
yana cewa, "Ga mota can Hajiya".
Ta ja ta tsaya tana harararsa, tsawon dakiku sai
kuma ta wuce. Ya tare gabanta yana cewa, "Ki taimaka
min Hajiya. Aikina ne, ni zan kai ki duk inda za ki, kada
ki ja min ki zo mu je ga mota can. Wallahi na iya tuki
duk ya ki ke sonsa ko a hankali, ko da gudu".
Ta tsaya cikin fushi ta ce, "Ka san idan ka sake
tsayawa gabana ka tare min hanya zai na ci mutuncinka,
dan rainin wayau kawai, motar banza? An ki a shiga".
Ta wuce fuu tana huci.
Ya bi ta da kallo, ya rike baki yana cewa, "Tabdi!"
Mai adaidaita sahu ta samu har store din da za ta
je ta jido kayan abinci, tamkar mai bude shago duk abin
da ta san za ta bukata ta siyo, hai da stove, ta ciko
adaidaitan dam ta shigo suka dawo, har cikin gidan aka
shigo bakin falen.
Ba ta jima da fita ba Sharifa ta iso a cikin
dalieliyar motarta, ta shiga falon tana sallama, "Anti!
Anti!! Matar Yayana"
Daya daga cikin masu kula da falon ta tito ta dan
rankwafa tana gaishe ta, ta ce, "Ba ta nan, vanzu ta fita".
25
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta fada da mamaki, "Ta fila kurа?
Ta ce, "Eh",
Shar fa ta ce, "Ita kadai kuma?"
Nan ma ta ce, "Eh".
Ta jinjina kai ta dube ta, ta ce, "Ok, shi kenan je
יי ki abicki”.
Ta wuce ta koma bakin aikinta.
Zama ia yi cike da mamaki, ina za ta je to duka
kwananta nawa? Da ma ya san za ta fita kuma ta cе
masa za ta z amma bai ce ba ta nan ba, ke ko ma ta fita
bai sani ba? Ta kasa ba wa kanta amsa, abin da ya faure
mata kai, ina za ta je? Gurin wa? Duk dai dangınsu ta
san ba a nan suke ba, inda wajen da za ia je gidansu ne
gurin Mommy, amma ba ta je ba. Kanta fa ya daure
sosai.
Ta zauna dai shiru-shiru tana jiranta (a ga ina ta
je? Amma har tsawon awa biyu ba ta dawo ba, ga shi
saura awa daya jirginsu ya tashi, ya kamata ta je kafin
lokacin. Imran din ta kira.
A lokacin yana ofis, aiki ma ya gagara yinsa
saboda damuwarsa da yunwarsa, abokai kuma na ta
shigowa yi masa murna da jajen 'yan fashin da suka zo
masa. Wayarta ta shigo, ya dauka yana cewa. "Ya dai
sister?
Ta ce, "Wai Yaya da ma Mabaruka za ta je
unguwa na ce maka zan zo amma ba ka fada min ba?"
Ya dafe kai yana salati, ya yi jim har sai da ta ce,
"iHello Bigbro, kana jina?"
Ya ce, "Eh, ina jinki, kina ina yanzu?
2
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Ga oi nan a gidan naka
Ya ce, "Ok, dan jira ni ina zuwa".
Ta ce, "Shi kenan, sai ka zo”. Suka kashe.
Ya ce, "Oh ni Imran, wai wace irin yarinya ce na
aura? Ina za ta je kuma?"
Ganin efis din ba zai ba shi amsa ba ya sa ya
mike da sauri ya dauki key ya fice.
A motar yake kiranta, amma ta ki dauka. Ya kira
ta ya fi a kirga, ransa ya baci sosai, don haka ya kyale ta
dai ya iso, bai karasa kashe motar ba ya fito ya shiga
falon. Sharifar ya gani ita ba ta dawo ba, ya dube ia, ya
ce, "Tun yaushe ki ke nan?"
Ta ce, "Na fi awa biyu wallahi"
Ya cc, "Awa biyu?"
Ta ce, "Sosai, amma ka san ta fita ne?"
Kafin ya ba ta arsa suka ji shigowarta, duk suka
fito ganin adaidaiia sahu suka yi dankare da kaya. Ya
gama sauke mata kayan tas! Ta biya shi, ya ja motarsa
ya yi gaba.
스
Ma'aikatan gidan suka taho za su shigar mata da
kayan daya ya ce, "Sannu da da owa Hajiya, bari mu
shigar da su".
Suka suakuya za su fauka, ta daka musu tsawa
ranta face tamkar 'ya'yanta, suka yi cak!
Ta ce, "Kiranku na yi ku zo ku daukar min, ba
zan iya ba? Ko ko turo ku aka yi?"
Suka yi tseru-tsuru, can suka ce, "A'a duk dai
yana cikin aikinmu”.
28
WAYE ANGON?-3 Maryam jafar Kaduna
Ta ce, "Ni ke biyanku bare ku miw askis da na sa
ku?
Suka ce, "A'a, maigidanki ne ya umarce mn
Та се, "Вan sanski ba, kar ku sake danganta ni da
shi, bara son taimakonku har shi, zan shiga da kayana,
in ba zan iya ba, zan nemo almajirai su shigar min da
دو
su
Mamakinsu ya kasa karewa a kanta ganin za ta
tone masa asiri ya sa Imran ya fito da sauri, yana cewa,
"Ku je Rufa'i na gode".
Suka wucc suna waiwayenta da son yia gulma.
Ya dube ta, zai yi magana ke nan ta yi saurin
daukar kwali ta wuce abinta tamkar babu kowa a
gabanta. Ya juyo yana kallonta har ta shige. Kada kai
kurum ya yi ya sunkuya zai daukar mata wasu, ta fito
kenan ta karaso da sauri tana dakatar da shi, "Wallahi
kada ka taba min kaya, bana so, in ko har ka taba
haramiya ta, on wallahi ba zan iya cinsa ba. Ba na so"
Ta durkusa ta dauka ta wuce bakia falcn. Sharifa
ta kare tsaf ta gama karantarta, bar yanzu ba ta son dan
uwanta, hakan ya sa Sincinsa ma ba za ta iya ci ba, shi
a sa ta fita ta siyo nata saboa muguwar tsanar da ta
masa, don haka ta tare kofar taga inda za ta kai su
Ta dube ta fuska hade cikin 6aciu rai, ta ce, "Ba
ni wuri in vuce".
Ta ce ita ma cikin fushiu, “An ki a ba ki warin".
Ta sake cewa, "Ki maisa aa wuce".
Та се, "Вa zan matsan ba, ki ture ni ki wuce in
kin isa. Tunda kia tsani maigidan ai gidan ma sai ki
29
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
tsane shi, ba za kriya cin abiacinsa ba kin je kin siyo
naki. To sar ki nemi gidan da za ki sa kar gidan ya goga
miki datti a abincin, tanda har kin ji ba za ki iya cin nasa
ba, shi ma gidaa sai ki nemi nakin ki aje, sai mu ga
Karshen tsana".
Ta dube ta da rinannun idanunta na Sacin rai na
gargadinta. Ya taho ya tsaya bayan Mabaruka yana
cewa, "Mene ne haka Sharifa ki matsa ki ba ta guri ta
wuce mana
Та се, "Кyale ni da ita Bigbro in koya mata
hankali tuada sakarya ce, ba ta da wayau kar..."
Kan ta gama rufe bakin ta ji saukar wani mari
mai shiga kwakwałwa. Ta dago ta ga cikinsu wa ya yi
mata wannan marin? Mabaruka ta gani har tana huci
ranta bace, idanunta sun yi jajir tana kallonta. Ta yi
mamaki sosai, ta ce, "Ni ki ka mara?"
Ta se, "An mare ki din, ko za ki rama?"
Za ta yi magana ya ce, "Ya isa, ba na son
magana, ba ta wuri kawai".
T1 ce, "Amıa Yaya kana ganin fa ta mare ni?"
Ya ce, "Ai ba 'ifi ta yi ba, ni ına za ki iya zagina
tunda har ki ka iya zaginta, kuma hukuncin da zan miki
ke nan, don haka wannan ya zamo darasi gare ki. Bana
son rashin kunya".
Ta saki baki tana kallonsa cikin mamaki, a
ganinta ya goyi bayan matarsa a kanta.
Mabarukar ta sake cewa, "7a ki matsa ki ban
guri ko kuwa sai na nemar wa kaina hanyar da kaina?"
30
こ
WAYE ANGON?-3 Maryanı jafar Kaduna
Cikia zafin ya goyi bayan matarsa, ga ra marın
da ta mata ya sa ta ba ta aresar cikin izgili, "Ek din, ba
zan matsa ba, tunda ba gidanki ba ne, ki nemi na...
Kan ta gama rufe bakin, sai dai ta ji ta gefe kasa
a yashe, ta ture ta wuce abinta, ko kallon indá ta ke ba 1a
yi ba bare ta kalli na bayanta.
Bai ji dadin hakan ba sam, ya shigo ya nufi
gurinta, ya tsugunna yana kallonta ya ce, "Me ya sa haka
Sharifa? Rashin kunya ko?"
Tа сe, "Amma fa Yaya kana ganin abin da tai
min?"
Ya ce, "Ke ba ki ga me ki ka yi ba har ta miki
hakan? Rashin kunya fa kanwata ba halinki ba ne.
mabaruka fa matata ce, ina sonta a yau ba gobe ba, muna
iya daidaitawa tsakaninmu: Ya ki ke so ta kalle ki idan
haka ta kasance, ya za ki kalle ta? Matsayinmu daya da
ita a gurinki, abin da ki ka mata ni ma za ki iya min
Ta ce a marairaice, "Ba zan iya ba, wallahi ba
zan iya ba Yaya".
Ya ce, "To me ya sa ba ki darajta min ita ba,
lunda yayaki ce, Antinki ce mai auren Yayanki?"
Тa сe, "Sony Bigbro". Tare da kama kunnuwa,
"Ba zan sake ba"
Ya yi siiru yana kallonta ganin nadamaria da
wuri ba taurin kai, ya ce, "Ok, na ji ya wuce". Ya dago
ta suka mike tare, va zaunar da ita, ya ce, "Jira ni ina
zúwa".
Та се, "То".
Ta bi shi da kallo cike da tausayinsa.
31
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Dakin Mabarekar ya shiga, ta gama kwashe
kayan. Tarar da isa ya yi tana jera su cikin wardrobe duk
da duk na kwali ne sai dan Karamin buhun shinkafa,
kasancewar babbar wardrobe ce duk suka dauke daf, gа
kuma sarari sosai duk yana kallonta har ta gama ya dube
ta, ya ce, "Me ye haka Mabaruka, me ki ke nufi?
Ta yi masa banza tana kokarin hada gas dinta
wanda yake zuwa tare hade da silandar. ya sake
nanatawa. Ta dago tana kallonsa cikin gajiya, ta ce, "TG
idonka ya nuna maka, ba ka gani ba haba?"
Ta ja tsaki ta ci gaba da abin da ta ke.
Ya ce, "Shi ya sa kenan ki ka fita ba tare da
izinina ba tamkar ba aurenki nake ba?"
Ta dago, ta ce, "Aure ka ke, aurena? Allah ya
sauwake, wallahi ni ba auranka nake ba”.
Ya ce, "To me ki ke yi a nan in ba auran ba?
Та се, "Ва kanka amsa ban da lokaci".
Ta mike, shi ma ya miken ya ce, "Mabaruka ki ji
tsoron Allah ki san me ki ke, kar ki mutu a wannan
halin, kina gaya wa mijinki magana son ranki bayan kin
danne maa hakkokinsa, wallahi ki nutsu tun kan /Vah
ya kama ki ba haka musulunci ya ce mata tai wa mijinta
bain dai musulmar kirki ce"
Та се, "Тo kafirta ni shi kenan sai ka san kafira
ce.
Ya yi shiru dai, ya numfasa ya ce, "Ba za ki iya
cin abincin can na store ba shi ya sa ki ka je ki ka siyo
naki ko?
Kai tsaye ta ce, "Eh". Cikin ko in kula.
32
き
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Tsawon lokaci dai suna haka, ko ya vi mata
magana za ta ba shi amsa cikin gadara in ta ga dama
kenan, in ba ta ga damar ba ta share shi ta ci gaba da
aikinta.
Ganin ransa ne zai ta baci ba nata ba ya sa ya
mike ya ce, "Ok, shi ke nan na ji ba kya sona, ba za ki ci
abincina bs, ina rokonki kar ki yi girki a dakin aan,
akwai maisala musamman da gas ne, ga kicin can ki je
ki dinga yi a can don Allah na ce, ba don : ba
Mabaruka".
Ta ja tsaki, ta ce, "Wallahi sai kai ta yi a nau zan
yi ba wanda kuma zai hana ni har in gama kwanakina na
tafi".
Ba yande bai yi da ita ba, amma ta nace, ya ce,
"Shi kenan na bar wa Allah, Shi zai kare ki. Na gode".
Daga haka ya juya ya fice ransa ba ya masa dadi.
Ya samu Sharifa zaune ta rafka tagumi, bai kalle
ta ba ya ce, "Zo mu je.
Ya ficc ba tare da ya saurare ta ba. Ta dauko
furse dinta ta biyo shi, ya gyara motar ta shiga, ya ja
suka fice a barta a nan.
A mota kamar za ta yi masa kuka, duk
damuwarta halin da za ta barshi. Ya dube ta da rinannun
idanunsa.na bacin rai, ya ce, "Na fada miki ba wani abu,
ni namiji ne, ba zan takuru ba, na bar wa Allah komai.
Komai da ki ka gani za ta bari akwai ranar da za ki vi
mamakinta. Yanzun ma lafiya muke zaune".
Ta rausayar da kai, sam ba ta nutsu ba bar suka
iso gidan Mommy, ba su fata lokaci ba ta dauki kayanta
33
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
ta yi bankwana da Mommy don Daddy ba ya nan, suka
koma motar. Suka wuce airpert. Ba dadewa ba da
zuwansu aka kira ta, har sai da ya ga tashinsu sannan ya
juyo, yunwa ta dinga damunsa cikin ya dinga juyawa
yana tuki, yana matse ciki. A hanya, ya gamu da mai
rake a baro yana saidawa manya-manya, kaurin
kannunsa. Ya tsaya da tnotar ya sai masu zaki, ya sai
ruwa ya wanke kayansa tas! Ya zauna inuwa ya ci gaba
da shan kayansa. Piyun nan tas sai da ya shanye su, ya
kora da ruwa. Nan da nan ya ji ya koshi har da gyasa.
Shi kanshi rake abinci ne, ya ji farin ciki sosai, ya samu
karfi a jikinsa, ya shiga mota ya ba ta wuta, sai ofis. Ba
jimawa ya yi ba da man lokacin tafiyarsa gida ne, ya
dauki abin da zai dauka ya fito. Ibrahim ya kira, ya ce,
"Kana ina ne?"
Ya ce, "Ga ni nan a hanya, zan je gida".
Ya ce, "Ok, ga ni nan zuwa". Suka kashe.
Kamar hadin baki tare suka isa, suka shiga da
motocin a harabar gidan. Ibrahim ya fito yana
tsokanarsa, уa сe, "To kai ya na ganka ka yo nan kai da
za ka wt gurin amarya?"
Ya fito daga