An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
5
Ina godiya ga Allah (S.W.T) wanda Ya ba ni damar kirkirar wannan littafi mai suna WAYE ANGON? Tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da dukkan mabiyansa.
Typesetting:-
NURA SADA NASIMAT KT
08131994808
BUGAWA DA YADAWA
DANEJI PUBLISHERS
08037968900/08029035187 АЧАС МАYRAM
2
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
WAYE ANGON?-3
anin jikin nasa ya yi sauki ya sa likita ya G
sallame su, a harabar asibitin suna zuba
kayansu a mota Sharifa ta dubi Daddy ta
ce, "Kawai Daddy mu wuce gida da Big Bro, kada mu
tafi gidansa".
Ya dube ta da kyau, ya ce, "Saboda mene ne?"
Ta dan gyara tsayuwa cikin gajiyawa, ta ce,
"Kawai ni dai na san zai fi samun kulawa a hannunmu, a
gidansa sam-ba zai samu wata kulawa ba".
Ya ce, "Kada na sake jin maganar nan, akwar ma
inda zai fi jin dadi irin gidansa hannun matarsa? Mu me
- za mu iya masa ballantana ya samu sauki sosai, ba na
tunanin zai bukaci ai masa wani abun da ba zai iya ba da
kansa. Kin gane ko?"
Ita dai ba haka ta so ba, ta dai ji shi kawai ne,
tana ganin Mabaruka ba za ta kular mata da dan uwa ba
kamar yadda ita za ta yi masa. Za ta yi magana ya tsayar
da ita ta hanyar cewa, "Ya isa, ba na son jin wata
magana. Ki wuce ki ja waccan motar ke da su
Mabarukar, mu mun tafi a wannan".
Ta turo baki, ta ce, "Su shiga nan kawai Daddy,
ai za ta dauke ku, ni sai mu tafi da Ya Imran din".
Ya dube ta da kyau, lokacin da yake kokarin
shiga motar ya ce, "Saboda ki samu damar yi masa
ganganci da rayuwa ko?"
Ta yi shiru dai tana kallonsa. Ya shige yana
cewa, "Ki wuce suna jiranki".
3
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta wuce fuu! Ta shige motar tana ba ta wuta. Sun dade a gidan nasa suna hira, har da Daddy daga baya suka tafi duka, har da Rafi'a. ya rage gidan daga ita sai shi, bayan ta raka su ta dawo shi da man
yana falo ya kishingida hannunsa rike da remotc. Ta shigo falon can ciki ta yi sallama, kamar dole. Ta wuce
dakinta kai tsaye fuskarta ba annuri.
Ya bi ta da kallo, a tunaninsa za ta dawo falon ta
zauna, amma ya ga ta wuce ta share shi, don haka ya
daga murya ya kira ta, "Mabaruka?"
Tai tsaye cak! Ita ba ta juyo ba, ita ba ta tafi ba.
Ya sake cewa, "Zo mana”.
Ba tare da ta juyo ba ta ce, "Mene ne?"
Ya yi murmushi, ya ce, "Kí zo mana, sai ki ga ko
mene ne din".
Та се, "Ка yi hakuri, ba zan iya zuwa ba". Tа
wuce.
Ya ce, "Don Allah ki zo ko minti goma ne mu
dan yi hira, ina bukatarki kusa da ni".
Tana tafiyar ta ce, "Ba zan iya ba". Ta shige
dakin tare da turo kofai har da sa mata key.
Ya lumshe idanuwa yana jin zafin rashin
zuwanta, ko fuskarta ne yana so ya kalla don ya dan ji
dadi a ransa, amma ta hana masa kanta.
Ta zauna saman gadon har da jingina kanta
saman gadon, ta yi shiru. A hankali hawaye suka fara
zubowa masu dumi da dazi, bakin cikinta ya dawo sabo,
zamansu asibiti sati biyu ya fi mata dadi. Ta fi samun
nutsuwa da sanyi a ranta kadan, amma tunda suka
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduan
tunkaro gidan ta ji ranta ya baci, zuciyarta ta ji kueki
duk bakin cikinta ya dawo sabo dal! Ta dinga tuno gidan
wa za ta je? Makiyinta, wanda ta tsana a raywwarta bare
ta ganshi, sam gidan jinta ta ke a kuntace ba ahin da ke
i mata dadi.
Ta tambayi kanta, "yanzu a haka zan zauna cikin
wannan kuncin? A haka a ke son rayuwata ta kare a
lalace, a rashin walwala? Ta ya ya zan yi farin ciki a
gidan nan? Ta ya ya zan yi jumurin zama cikin kunci ina
ganin takaici? Wallahi an cuce ni matukar cutarwa da
aka hada ni da Imran, ba na sonsa ko kadan, zuciyata ba
ta sonsa, ba na son ko jin muryarsa, hankalina ya kan
tashi na rasa sukuni da walwala”.
Hawayen suka ci gaba da zuba har da 'yar
shessheka. Ta kife saman gadon tana cewa, "Oh ni
Mabaruka, na shiga uku na san lokacina ya yi, mutuwa
zan yi, ba zan iya kai tsawon lokacin nan ba a cikin
gidan nan, ko dai na mutu, ko kuma ya sauwake min tun
yanzu na kama gabana".
Dukkansu haka suka kasance zuciyoyinsu a
cunkushe, ba abin da ke musu dadi tsakaninta da shi.
Har aka fara kiran sallah ya mike cikin muluwar
jiki da jan kafa, ya shige dakinsa ya yo alwala ya rage
kayan jikinsa, ya sa jallabiya marar nauyi, ya fito.
Bakin kofarta ya tsaya yana kwankwasa mata.
DDaidai fitowarta daga bandaki ta yo alwala ita ma, ta ce,
"Waye?"
Ya ce, "Ni ne, ki tashi ki alwala zan je masallaci
kin ji ko?"
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
matata ki ke, ke ya kamata ki dafa min abinci na ci don
kyautatawa tun kafin na bukata
Ta juyo ta harare shi son ranta, sannan ta ce,
"Zancen banza ke nan, ka nemi matarka tun wuri, matar
wani ce ni, na rantse ba zan taba girka maka wani abu ba
don ka ci, ba zan yi aikinka ba".
Daga haka ta shigewarta da sauri. Kasa cewa
komai ya yi, ya saki baki yana kallonta cikin mamakinta,
da gaske ta ke ko ko dai wasa ta ke masa?
Komawaya yi ya zauna kan kujera a
tsammaninsa ta fito ta same shi. Shiru-shiru ba ita ba
labarinta, ga yunwa na kara azalzalarsa, musamman da
bai saba da zama da yunwar ba.
Ita kuwa tunda ta idar da sallar ta haye gadonta ta
kwanta, bayan ta sa wa kofarta key, duk da rabonta da
abinci tun safe, shi ma don Momy ce ta tilasta mata ta
dan ci wani abu. Ba ta jin za ta iya cin wani abu,
musamman wani abin ma nasa daga guminsa, aljihunsa,
ba ta jin za ta iya ci. Ta juya tare da jan tsaki, ta ce,
"Wallahi da na ci gwanda na mutu da na sa kwayar
acincinsa a bakina, tir!" Ta tsartar da yawu.
Imran mutum ne mai tsananin kyankyami tamkar
bature, ba kowane abinci yake ci ba, yana kyankyamin
masu aiki hakan ya sa ko a gida saboda shi Momy ke
girkinta ba ruwanta da masu aiki. Sai dai su gyara gidan.
Amma don Imran din ya ci za ta tashi ta girka da kanta,
in Mabaruka na gidan ta kama mata.
Haka zalika ba ya iya cin abincin waje komai
haduwar gidan cin abincin da tsaftarsu sai ya dinga
7
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
tambayar kansa ya akai abincin, su waye suka girka, don
haka sai ya dinga jin tashin zuciya.
Haka duk kayan bakery hatta biredi ba ya ci tun
watarana da yana ci ya tsinci kwayar shinkafa a ciki, duk
wanda ya ci sai da ya amayar da shi tun daga wannan
lokacin ya ke tarar cin kowane abinci. Ya fi yarda
Momy ta yi masa zai ci hankalinsa kwance, a nutse.
Hakan ya sa ba wata mai aiki da ya nema don yi musu
abinci masu share-share ne kawai da goge-goge, hatta
wanki ba ya yarda a masa da kanshi yake wanke kayansa
in ya dawo office kullum sai ya yi wanki da dare kafin
ya kwanta, wadanda ya sa a ranar kenan.
Washegari ya goge kayansa tsaf-tsaf ya jere a
dirowarsa, har da lullube kayan. Komai nashi mai tsari
ne da tsafta, don yana cewa idan ya yi aure, dole zai rage
wani abun ko matar ta masa, ko su hadu su yi don ya san
ya yarda da tsaftar matarsa ko ya ta ke kuwa. Da ya gane
wa kansa Mabaruka ce matar, sai nutsuwarsa ta karu a
kanta ko da ba ta da tsafta, yana jin zai so duk wani abin
da ta yi na dangane da abinci yanda yake sonta ba ya jin
zai iya ba ta wankinsa. Sai dai ya ci gaba da yi da kansa,
don ta huta ta ji dadi. Nata kųma zai dauki masu wanke
mata. Hakan ya sa ba wani ma'aikaci da ke kwana
gidan, daga mazan har matan da magriba ta yi za su
wucewarsu, maigadi ne kawai ke kwana Don haka
gidan yake kasancewa shiru, sai kukan tsuntsaye da
karnuka musamman idan dare ya tsala.
Ya yi mika tare da doguwar hamma, ya dafe
cikinsa da ke masa kuwwa, sam ba zai iya jurewa ba don
睡
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
bai saba ba. Mikewa ya yi daf ya nufi dakinta ya hau
buga mata kofa. Tana jinsa sarai ta share, ta ja tsaki tare
da hararar kofar ta canza kafada tana turo baki.
Ya hau kiran sunanta, "Don Allah Mabaruka ki
fito ko indomi ce ki dan dafa min, wallahi yunwa nake
ji, ba zan iya kwanciya haka ba, please".
Ta tashi a zuciye ta zauna, takaici ya turnuke ta,
ji ta ke kamar ta fasa ihu, hawaye na son zubowa tana jin
an cuce ta matuka, don me zai takura mata? Ta cije yatsa
ta koma ta kwanta tana cewa, "A!lah ya isa idan ka sake
takura min, mugu, natacce".
Yana dai jikin kofar yana ta rokon, amma sam ta
ki sauraronsa har ya gaji kafafunsa suka masa nauyi ga
yunwa, ga gajiya hade da bashin baccin da ke idonsa
wanda majinyata suka hana shi yi, a daddafe ya koma ya
zauna matse da ciki, idanunsa suka kaďa ja! Da ta ji ya
bar gurin ta ja tsaki tare da cewa, "Dan iska kawai, ba ka
ga komai ba wallahi sai ka mutu a hannuna".
Ta yi kwanciyarta, duk da yanda ita ma cikin
nata ya fara kuka don a agaje shi da abin zuba masa ta
smare.
Mikewa ya yi ya shiga kitchen ya ja ya yi tsaye,
ya rasa ma shin me zai yi, ta ya zai iya girka wa kansa
wani abun? Ya shiga store yana bude-bude a dubansa ba
abin da zai iya sarrafawa ya fito jiki a mace, ya dawo.
kitchen din ya dafe kai tare da dora kai saman freezer
yana jinyar kansa da cikinsa.
Ruwan lipton ya fado masa a rai, ko ba komai
shi ma wani abun ne. ya jona ruwan zafi ya tsiyaya a cup
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
ya masa hade-hafe, ya fita yana ajiyar dabino don haka
ya dauko ya ci sosai, yana yi yana kurbar tea dinsa har
sai da ya ji dama-dama sannan ya ajiyc.
Idanunsa suka yi nauyi saboda bacci, musamman
da ya zuba wa cikin wani abu. Mikewa ya yi ya shige
dakinsa ba da jimawa ba bacci ya dauke shi. Ita ma tana
nan da 'yan fadace-fadacenta, tana yi tana jan tsaki har bacci ya kwashe ta ba ta sani ba. Bacci ne mai matukar
nauyi, karfe daya har ta wuce na dare ta farka ta ji tsit
garin, sai kukan karnuka, ga ta ita kadai a daki. Ta tashi
zaune a tsorace jikinta ya hau rawa, zufa ta keto mata,
idanuwanta suka fito, masifaffen tsoronta ya taso,
karnuka kuwa suka dinga kuka, duk in suka ji haushi sai
ta zabura tamkar a dakintá suke.
Kamar yanda ku ka sani matsoraciya ce, sam ba
ta kwana a daki ita kadai saboda tsoro, don haka ta
dinga rawar jiki duk ta bi ta takure kanta har da runtse
idanuwa gam.
Wani haushi da suka yo, ba ta san sanda ta diro
ba, ta hau juye-juye sai kuka, jiki na rawa kamar mazari,
ba shiri da gudu ta fito dakin. Tsakiyar falo ta hau juyсjuye tsoronta ya karu, musamman da ta ga an kashe
fankar falon. Fitsari ya matse ta tamkar zai zubo, ta hau
lalube-lalube don neman wani daki, inda ke da mutum
tamkar makauniya cikin duhu, har Allah ya ba ta ansara
ta fado dakin Imran tsulum! Sai dai ta ganta tsakiyar dakin tana wuri-wuri da idanuwa yana kwance tsakiyar
gadonsa yana baccinsa mai dadi da kwanciyar hankali.
Ta tambayi kanta, me ya kawo ta dakinsa? Ta ji wani
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
irin kuka, ita dai ta san ba na karnukan ba ne, hade da
yan surutai na mutum da yake a tsorace ta ke, sai ta i
tamkar da ita a ke an ce, "Ke Mabaruka". Habawa tunı
ta yi wani tsalle ta fafo kan gadon a jikinsa, ji ka ke tim!
Yayin da fitsarin yake kokarin zubowa don kada ta fasa
kuka mai karfi, jikinta na rawa ta runtse idanuwa gam!
Tare da makalkale shi kamar za ta shiga cikinsa.
Kamar a mafarki ya ji abu ya fado jikinsa ya
bude idanu da sauri, kukanta ya ji. Ya mike da sauri cike
da mamaki, kalin ya yi magana ya ji ta makaikale shi
kamar zai gudu, jikinta na rawa duk ya jike.
Fahimtar da ya yi a tsorace ta ke, ya sa rungume
ta tsaf a kirjinsa, a hankali yana shafa bayanta yana hura
mata iskan bakinshi, kasancewar jinta da ya ji sharkaf
duk da A.Cn da ke aiki.
Ta lafe jikinsa tsaf tana jin wata nutsuwa na
zuwar mata. Ya yi magana a hankali cikin taushin
murya, a kunnenta ya ce, "Lafiya Mabaruka? Mene ne?
kin yi mafarki ne?"
Ta kara rungume shi, ta ce, "A'a ina jin tsoro ne,
karnuka na ta kuka a ďakina".
Ya yi murmushi ya kara matse ta jikinsa, ya ci
gaba da shafa mata baya yana dariyar tsoronta, wai kare?
Tsawon dakika suna haka jin ta yi shiru, jikinta
ya bar rawa, ta nutsu amma dai tana manne da shi, ya ce
yana dariya, "Fitsari fa ki ka yi?"
Ta yi shiru tana sauraronsa.
Ya ce, "To taso mų je ki wanke jikinki sai mu
dawo mu kwanta”.
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta dage kafada alamar a'a, ya ce, "Sorry
karnukan sun tafi, ba zan bari su yi miki wani abu ba,
kina tare da ni promise?"
Ta yi shiru, ya ce, "Kada ki damu ina tare da ke,
ba za ki ji dadin bacci ba ne".
z0"
Ya mike ya kamota yana cewa, "Ba wani abu,
Suka mike tare har a lokacin tsoron bai sake ta
ba.
Ta cire sket din ta yi fitsari, duk yana tsaye ta
gama. Bayan ya mika mata ruwan suka fito.
Tana kokarin kwanciya da jikakken siket G ya
ce, "A'a tashi ki cire shi, zai dame ki".
Ta mike kuwa tana cirewa, ganin a tsoracen ta ke
ya sa bai iya fita ya dauko mata wanda za ta canja a
dakinta ba, boksa dinsa ya miko mata ya ce ta saka. Ba
musu kuwa ta sanya duk gabansa yana kallonta,
zuciyarsa ta cika dam da mamakinta. Ta koma kan
gadon ta kwanta tare da jan bargo ta kudundune, shi ma
va hayo gadon ta matso tare da kankame shi. Shi ma ya
rike ta sosai, har sai da bacci ya dauke ta. Tambayoyi
makil a ransa da mamakinta, haka ta ke da ma, tana
tsoron kare ke nan har ba ta iya kwanciya dakinta ita
kadai? Ya jinjina kai tare da yin dariya cikin gamsuwa
ya ce, "lallai in dai har zai sa ki dinga biyo ni muna
kwana tare irin haka, zan nemo karnuka ma kuwa ba
kare daya ba, su zo su yi ta ba ki tsoron kina gudowa
wajena, me yiwawa hakan ya daidaita mu saboda
kusantata da za ki dinga yi. Tabbas hakan mafita ce,
12
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
gobe ba yau ba zan nemo su, Allah dai ya tashe mu
lafiya".
Ya ci gaba da shafa ta yana jin farin ciki da
nishadi a ransa kasancewarta tare da shi.
Ya ce, "Allah ka tabbatar min Mabaruka ta zama
tawa, zuciyarta ta zama tawa ce, Ya Allah".
Da haka daddadan bacci ya dauke shi mai
cakude da walwala, suka ci gaba da baccinsu mai dadi.
Sai mu ce a kwana lafiya angon Mabaruka.
Tunda ta kwanta din ba ta ko juya ba saboda
dadin baccin. Da asuba ya tashi ya yo alwala ya wuce
masallaci da niyyar sai ya dawo ya tada ta ta yi sallah.
Ta yi mika tare da salati don jin ana sallah, ta
mike zaune tana dan gyangyadi babu haske sosai, ta
mike ta nufi bayi tana dan tangadin nan da hamma irin
na wadanda suka tashi daga bacci. Ta shiga haske fayau
a bayin, ta yi saurin ja da baya cikin tsoro ganin an canja
mata bayi. Ta hau wurge-wurgen idanuwa, idanunta ya
sauka kan wasu singilet din Imran a rataye. Ta kara
dubawa gefe wajen madubi, ta ga cumb ne na maza da
sauran tarkacensa. Cikin masifa da bala! ta ce, "Kan
bala'in nan, a nan dakin na kwana?"
Ba wanda ya amsa mata, ta fito a zuciye ta kunna
hasken dakin fayau, ta bi gadon da kallo. Tabbas a nan
ta kwana, filo biyu ta gani a hade, kuma shimfidar ya
nuna mutum biyu suka kwanta, siket dinta da ta san ta
kwanta da shi ta ganshi a yashe kasa. Idanunta suka fito,
hankalinta ya tashi, tsoro ya bayyana a idanunta, ta yi
saurin duban jikinta don ganin to me ye ta saka?
13
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Idanunta ya sauka kan wandonsa tamkar ta ga macizi ta
fasa ihu, tare da yin tsalle kamar wandon ne zai fado.
Kawai sai ta fasa kuka tana, "Allah ya isa mugu, dan
iska. Wallahi sai Allah ya saka min, macuci
Ta hau kiciniyar cire wandon da yatsa cikin
takaicin ta sa wandonsa, ga wani kyankyami da ta ke ji
tana yi tana kuka. Shi kuma wandon ya ki ciruwa saboda
ta dage da yatsa za ta cire, ba za ta iya sa hannunta duka
ba ta tabа.
A haka ya same ta, tun daga falo ya jiyó kukanta,
ya shigo da sauri. Idanunsa a kanta, sai dai ta ga mutum
gabanta. Ta yi saurin daukar siket din tana rufe
cinyoyinta, ta ci gaba da harararsa tamkar sun fado,
kamar ta kai masa duka ta ke ji.
Ya karaso kusa da ita yana cewa, "Mabaruka,
lafiya?"
Cikin masifa ta ce, "Ba a sani ba fan rainin
wayau, mugu, dan iska. Allah ya isa tsakanina da kai, sai
na kai Kararka ga mahaliccina a kan keta min haddi da
ka yi.
Ya ce, "Ke ba fa abin da ya faru sakaninmu, me
دو
zan miki? Kawai dai mun kwanta tare a nan..."
Ta katse shi cikin fada, "To me ya sa na kwana a
nan din?"
Ya ce, "Tambayi kanki, wannan me zai sa ki
kwana a nan fa in ba kawo kanki da ki ka yi ba".
Ta mike cikin masifa, ta manta yanda jikinta
vake, siket din va fadi. Ta yi saurin komawa ta zauna
tare da jan siker din ta lullube jikinta, tana cewa, "Ni ma
14
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
zan kawo kaina nan, har kana tunanin zan yarda da
yaudararka na kawo kaina nan? Nasan me ka ke nuli,
kar ka raina min wayau, wallahi ba zan taba kawo kaina
gurinka ba, sai dar kai ka je ka dauko ni. Kuma Allah ya
isa tsakanina da kai".
Ya dube ta a nutse yana mamakin canzawar
tarbiyyarta, ya numfasa ya ce, "Shi kenan na ji ni na
kawo ki, amma tunda kin fahimci a nan ki ke me ya sa
tun tuni ba ki bar min daki ba tun kan na dawo na kota
miki mugancina, sai dai na dawo na tarar da ke a kan
gadona zaune, me ya sa?"
Fadin hakan ne ya sa ta yi saurin tashi tsaye tana
kare jikinta da siket din, ta dube shi, ta dubi jikinta ta ya
kenan za ta cire wandon ta aje masa tsiyarsa alhalin yana
tsaye yana kallonta? Ta yi shiru tana tunani. Can ta dago
ta dube shi, ta ce, "Ai sai ka ba ni guri ko?"
Ya yi murmushi ya kada kai, ya wuce bayi yana
cewa, "Za ki sani yarinya".
Ta bi shi da harara, ta ja tsaki.
Da sauri-sauri ta cire ta mayar da siket diata, ta
fice har da buga masa kofa cike da takaicin
kasancewarta a dakin. Ta dade a tsugunne a bayi tana
duba kanta, ko abin da ta ke zargi ya tabbata? Ba ta ga
alamar komai-ba, ta yo alwala ta fito. Ta idar da sallah,
abin da ya faru jiya ya dinga dawo mata, da kanta ta kai
kanta dakinsa saboda tsoro. Ta san ba ta iya kwana daki
ita kaďai, ga karnuka kuma da suka Kara tsoratata, ga
gidan tsit kamar ba mutane a cikinsa.
15
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta cije yatsa saboda takaicin zuwanta gurinsa, ta
runtse ido tana jin wani haushi, amma duk wa ya ja mata
in ba shi ba da ya kawo ta gidan nan? Ta ja tsaki ia ce,
"Na dai ji kunya wallahi, wannan kuma shi ne karshe.
Allah ya sauwake dai".
Ta tashi ta haye gadonta ta kwanta.
Ko da ta tashi bayan ta yi wanka, kwalliya sosai
ta yi, ta yi kyau, atamfa ta sa riga da siket, sun mata
kyau matuka. Ta samu biro da takarda ta rubuta ranaku
da kwanakinsu, tsawon wata uku. Sannan ta fara jin layi
ga duk ranar da ta wuce tun zuwanta gidan, ta yi
merking har ya cika wata uku iya kwanan da za ta yi a
gidansa kenan.
A ranar zai fara fita ofis, a tunaninsa da sai ya yi
wata uku yana hutun angwanci, amma tunda ba hadin
kan amarya yaushe zai Gata lokacinsa a gidan? Shi ba ga
more angwancia ba, shi ba ga aikinsa ba, don haka ya yi
shirinsa tsaf ya fito don ya karya. Kamas! Ya tarar ba
alamar an yi girkin wani abu. Dakinta ya nufa kai tsaye,
ya shigo tana kwance kan gadon ta yi kwalliya shar!
Hannunta rike da waya da alama game ta ke, ta yi masa
kyau sosai, ya ce yana kallonta, "Kin yi kyau fa".
Ta dago ta kalle shi sama da kasa ta watsar, ta ci
gaba da abin da ta ke. Ya sake cewa, "Amman kin shirya
mana abin kari ko?"
Ta yi masa banza, ya sake nanatawa. Ta kalle
shi, "Kar fa ka dame ni, sau nawa zan fada maka wallahi
ba ail.ina ba ne, na rantse ba zan taba maka abinci ba.
16
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduua
Ya ce, "A haba dai wasa ki ke
Ta ce, "Wallahi ba wasa nake ba, tunda ka san
ban saba maka wasan ba ka sani
Ya ce, "To me za ki yi kenan in ba za ki wa
mijinki abinci ba, bayan kuma kin hana masa hakkinsa
na aure? To me ki ka zo yi?"
Та сс, "Za ka gano amsar hakan nan ba da
jimawa ba".
Sun dade suna nanata abu daya, amma sam! Ta
ki saurarensa, ta rantse ta kuma rantsewa ba za ta yi ba,
ba aikinta ba ne, sai dai ya mutu a kan ta girka masa ya
ci. Ya rausayar da kai a sanyaye, ya ce, "Well ba komai
za ki yi watarana, insha Allah ba zan taba kara ce miki
ki min abinci ba Mabaruka, na hakura ki kwanta ki huta
kin ji ko?"
Tsaki ta ja, bai ce komai ba ya juya ya fice, ya
dauki briefcase dinsa da makullın motar ya fice
zuciyarsa ba ta masa dadi, komai ba ya jin dadinsa.
Har an wanke masa motar, an goge tana kyalli,
shi kawai ta ke jira. Ya shiga ya zauna, ya dade bai tada
ta ba, shi kuwa malgadi tuni ya bude gate din, ganin bai
tada motar ba ya sa'