inda firij yake yana dariya, ya
dauko ruwa ya tittila a kofi, sannan ya dawo falo ya zauna
yana ccwa, "Abubuwan ne da yawa, Momy sai yanzu na
fito daga gidan".
Ta yi dariya ita ma tana zama, ta ce, "Ah lallai
masha Allah, komai ya yi daidai tunda ana kai kamar
yanzu ba a fito ba".
Ya ce sanda yake aje kofin, "Bako muka yi yau tun
safe shi ya sa.
Та се, "Вako kuma, wane bakon?"
Ya cc, "Babanmu mana".
Daf! Wuta ta dauke mata, sarai ta fahimci wa yake
aufi. ta dube shi da kyau, ta cc, "Lallai kun sha baki,
wannan bakon ba na kunya ba ne, na san ka ga abubuwa,
ita dai da man ta sani".
Dariya ya yi kawai tare da daukar remote yana
cewa, "ke kadai Mommy, Daddy fa?"
lafiya".
Ta ce, "Yau ya bar kasar da yammacin nan".
Ya jinjina kai alamar gaisuwa, "Allah dawo da shi
Ta се, "Amin, bari na duba abu a kan wuta". Ta
mike la wuce.
Labari shi da Mommy ba sauki, ba sa ganin wai su
surukai ne, kailon mahaifiya yake mata, haka zalika kallon
102
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
da ta ke masa ko irin kunyar nan tsakani babu, don tun
yana yaronsa kan ya san waye shi ta ke tare da shi, har
girmansa, to ko me ye abin kunyarsa? Haka shi ma ita yake
gani matsayin mahaifiyarsa mai ba shi shawara a kan duk
abin da zai yi, sai ta amince wani lokacin ita za ta sani kan
Daddy, sai dai ya ce ta sanar mishi.
Ana magriba ya baro gidan ya yi alwala ya wuce
masallaci, sai da ya kammala sallolinsa na ranar sannan ya
dawo gida.
Zulluminta dare yau a ya za ta kwana? Tuni ta ke a
daki har ta kwanta, amma ba bacci ba waya na hannunta
tana buga game, in ta gaji ta tabo wannan kawar ta kashe,
ta nemi wannan aikin kenan. Duk da ba wai cikin fara'a ta
ke ba. Ko da ya dawo bai neme ta ba, ya shige dakinsa ya
rage kayan jikinsa ya fito da boksa a jikinsa. A kasan kafet
ya mike falo ya dauko sauran abincinsa na rana ya jawo
remote yana kallon news.
Ya dade yana kallo har sha daya na dare, sai da ya
fara jin bacci sannan ya mike dakinta ya nufa. Ya tura
kofar, da iyakarsa bakin kofa zai tsaya ya mata bankwana,
amma abin da ya gani ne ya sa shi sakin kofar ya shigo.
Kwance ta ke ta yi faidai a tsakiyar gadon ba wata
rigar kirki ba ce jikinta, ta bacci mai laushi da santsi, fara
sol duk ta yaye ta koma sama saboda dadin bacci ne.
fararen cinyoyinta santala-santala sun bayyana ba ko
alamar tabo a jikinsu tamkar budurwar Turawa. Ta yi
d'aidai da su har pant dinta a waje. Ya bi samanta da kallo,
kanta ba fankwali mai yiwuwa ya cire ne, gashin ya bazu
saman filon.
103
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Wuyanta shamfal har saman kirjinta, ta yi wani
fresh, tuskarta har wani sheki ta ke masa ba kurji ko
kadan, bacci ta ke sosai ba ta san waye saman kanta ba.
Gwiwoyinsa suka yi sanyi, ya kasa dauke kansa
daga kallonta. Ta yi masa kyau matuka, bukatar matarsa ya
taso masa, ya rasa sukuni da kuzari, kafarsa ta yi nauyi
bare ya daga ya bar dakin ko zuciyarsa ta huta da ingiza
shi da ta ke. Ya dade a haka yana kallonta, da kyar cikin
mutuwar jiki ya ja jikin ya bar dfakin, hotonta da
Kwakwalwarsa ta dauka tana kara nuno masa surarta mai
ban sha'awa da dadin kallo, ya zauna dabas! Kan gadon
yana tambayar kansa, "Sai yaushe ne to zai kasance da
matarsa? A haka za su ci gaba da zama yana kallonta ba
wani abu da zai shiga tsakaninsu alhalin yana son matarsa,
yana bukatarta? Ta ya ma za su samu fahimtar juna alhalin
suna nesa da juna, anya bai sakaci ba, kar fa damarsa ta
wuce ta wannan hanyar ne za su daidaita da juna, ba wai
suna nesa-nesa ba.
Ya tuno da alkawarin da ya yi wa kansa, a kan ba
zai neme ta ba idan bai manta rotsa da ta yi masa ba. Anya
ba zuciya ba ce da shaidan ta debe shi ba ya yi wannan
alkawarin ba? Ai ibada ce ta ya ya zairana wa kansa abin
da Allah ya halatta masa, yake so ba sunnar Annabi kuma
to in ba yau ba sai yaushe? Sannan haka za su ci gaba da
zama cikin kunci?
Kansa ya dau zafi, ya rasa me zai ji ya fisshe shi,
matuka ya kai kololuwa kan bukatar matarsa kar fa ya
kwari kansa. Ya dade kan gadon yana juye-juye da tilasta
wa kansa lallai sai ya hakura, daren nan. Karshe dai
mikewa ya yi ya yo alwala ya zo ya yi sallah, yana kara
104
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
gaya wa Ubangiji damuwarsa. Tun kan ya idar ya ji ya
samu nutsuwa, don haka yana idarwa ya fada gado, nan da
nan bacci ya dauke shi.
Yau kam ba laifi, don ta yi bacci a dakinta, sam ba
ta farka ba tunda ta kwantan, haka ma katnukan ba su
haushin kullum ba, sai gab da asuba uku da rabi an fara
kiran sallah sannan ta farka, ta yi tsuru ta ja bargo ta
kudundune, har da fuska ta runtse ido gam, ta alkawarta
wa kanta yau ba inda za ta je, ba zai sake raina ta ba, tana
nan har wani baccin ya sake faukarta. Sai dai ta farka ta ji
ana sallah.
Shi kanshi ya yi mamakin rashin zuwanta, yai ta sa
ido amma bai ganta ba, don haka ko da asuba da zai tafi
masallaci ya buga mata kofa, ta tashi ta yi salla. Ba ta ji ba,
saboda baccin da ta yi, ta ji dadi sosai yanda ta kwanta ita
kadai ba ta je gurinsa ba, don haka tunda ba abin da ya
same ta, to insha Allah kullum ma ba abin da zai same ta,
za ta dinga kwanciyarta har ta bar gidan.
Yau ma lahadi ba aiki, ya yi kw anciyarsa yana
bacci, musamman da bai kwanta da wuri ba.
ita ko tuni ta tashi ta yi wank-nta da kwalliyarta,
kamar kullum har abinci ta ci, ta loma gado ta harde.
Kamar daga sama ta dinga jiyo salamar Rafi'a a falo, ta
daka tsalle ta yo waje tana murnar zuwanta, ta fada jikinta
suka rungume juna suna dariya.
Rafi'ar ta ce, "Na shiga uku Mabaruka, sai kin
karya ni wannan tsalle da ki ka yi kaina?"
105
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Suka zauna tana cewa, "Dole ne na yi murnar
ganinki Rali'a, kwanana nawa ban ganki ba? Ina kewarki
wallahi
Ta ce, "Ni ma Mabaruka haka kawai ina tashi yau
na ji ke nake son gani, ko ya ki ke duk da duka kwana uku
ne ina ga ko hudu rabona da ke, ga shi nan na yo sauko
goma da rabi fa?
Та се, "Тo mene ne? Kin san tun yaushe na tashi
ai? Tun bakwai fa, ba abin da nake sai dai buga game"
Ta kalle ta da kyau, ta ce, "Ban gane ba sai buga
grame, ba ki nemar muku abin kari ba?"
Ta tabe baki, ta ce, "na karya mana, kin san ni sai
in dafa lipton in ci ragowar abincin jiya".
Ta ce, "Ban gane ba, shi fa imran din me zai сi?"
Ta ja tsaki tare da harararta ta ce, "Ina ruwana?
Can shi ya sani, me zai ci ni dai bana ci ba?"
Ta juyo sosai tana kallonta, ta ce, "Mabaruka kina
son ki ce min har yanzu kina nan kan ra'ayinki?"
Ta ce, "Sosai ba abin da ya sauya, ina nan kuma ba
zan sauya ba har sai sanda na bar gidan”.
Ta ce, "Kina tunanin barin gidan ke nan?"
Ta ce, "Sosai akwai iyaka, kwanan nan kuwa".
Tsaki ta ja tare da cewa, "Ina ganin ba ki da
hankaii. An Caura miki aure ba don rabuwa ba, Imran
mijinki ne na har abada, kin shigo kenan cikinsa, daga nan
sai kabari..."
Ta katse ta, "Allah sauwake, wallahi rayuwata ba
za ta kare a kunci ba da rashin walwala, dole ne in sakc in
ji dadin rayuwa kamar kowa".
106
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Та се, "Mabaruka, ki nutsu ki san me ki ke. Aure
fa ba abin wasa ba ne ki karbi hukuncin Ubangiji, ki
rungumi mijinki ku zauna lafiya. Wallahi na san za ki ji
dadin zama da shi, Imran mutum ne mai hankali da tunani,
yana da ilimi, ya san hakkokin aure, zai ba ki hakkinki, ya
kiyaye damuwarki wallahi ba zai taba muzguna miki ba.
Sannan yana sonki so mai tsanani, a rayuwata ban taba
ganin wacce mijinta ke so irinki ba".
вні Та ce, "Ni kuma bana sonsa, duk abinsa ba ya
burge ni, ba zan taba farin ciki da auransa ba. Ina jina
kamar a kabari nake, a kuntace, na takura sosai ba abin da
ke min dadi a gidansa, kawai so nake na rabu da shi ko ba
don na auri Sulaiman ba, ko don zuciyata ta yi sanyi in yi
walwala, in bar kuncin da nake ciki".
Та се, "Тo in ba ki labari, matukar ki ka bar gidan
nan ba za ki taba farin ciki ba, kunci, nadama su za su
baibaye ki. A yanzu ba komai ki ke ba, wallahi kin faye
naci da kafiya Mabaruka, ba kowa yake sa'ar samun miji
irinki ba, amma kin runtse ido kin ki karbarsa, ina guje
miki ranar da na sani, ranar da za ki kuka idan ki ka bari ya
kubce miki, hankalinsa ya bar kanki ya koma kan wata
wallahi.
sbigCikin ko'in kula ta ce, "Da hakan ya fi min farin
ciki da walwala, zan so a ce ga ranar da ya daina sona
wailahi, can wata ta kwasa".
sb edrg Ta jinjina kai, ba ta san ta ya za ta gane ba tun ba
yau ba ta ke nuna mata, amma ta kasa fahimta. Ta nisa tare
da cewa, "To na ji, yanzu dai ni me zan samu, ban ci komai
ba, ina gama wa Mama aikinta na fito na ce inina zo nan na
karya".
107
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta cc, "Ki shiga ki duba abin da ki ke son ci.
Ta mike tana cewa, "Zo mu je ga masu shara can
ina jin sun zo, zo mu je ciki".
Ta ja ta zuwa bedroom dinta.
Ta yi tsaye sake da baki ganin yanda ta cika dakin
da kayan girki tamkar kicin, ta cc, "Me zan gani haka, ba
dai a nan ki ke girki ba? Wanc irin hauka ne ya same ki
Mabaruka?"
Ta zauna tana cewa, "Za ki ga abin da ya fi hauka,
in dai na ci gaba da zama gidan nan".
Ta karaso tana cewa, "Amma me ya sa ki ke girki
daki bayan ga kicin can?"
Ta ce, "Kawai bana son shiga kicin din ne".
a
Ta ce, "Wallahi ba ki nema wa kanki mafita ba,
ban ga dalilin girki a daki ba ga kicin".
a Ta fara bude-bude, ta ga himilin kayan abinci
cikin wardrobe, jinjina kai kurum ta yi har ta gaji da
maganar ko ta fada ba jinta za ta yi ba ta bari, to ba ma
amfanin maganar gwanda kawai ta yi shiru ta nema wa
kanta abin da za ta ci, suka hau zuba labari.
Tun daga dakinshi yake jiyo maganganu lokacin da
ya tashi, matuka ya yi mamakin jiyo harshenta ko ita da
waye ne haka? Abin da bai taba ji ba tun sanda ta zo gidan,
da alama tana murna da bakon ko bakuwar.
Sai da ya shiga wanka ne ta bayi ya gane Rafi'ati
ce, saboda maganarta. Ya jinjina kai kurum ya ci gaba da
wankansa. Sai da ya shirya tsaf cikin dogayen kaya, farare
sol ya dan sa tabaransa mai kyau, kamshi ko ta ina fitowa
yake, ya yi kyau sosai ya dauko wayoyinsa ya fito.
108
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Kai tsaye dakin ya nufo tun kan ya iso kamshinsa
ya sanar musu. Ita da ji ta gane shi ne, amma Rafi'a ta yi
luf har da lumshe idanuwa tana shakar kamshin, ta dube ta
ta ce, "Wayyo Mabaruka kin ji wani irin kamshi mai dadi
ya buga? Wannan da ji na mutanen boye ne, ina mutum zai
samu wannan turaren kamar ba a duniya ba? Wallahi ya
hadu".
Tsaki ta ja tare da dauke kai tana jin haushin
Rafi'ar, sam kamshinsa bai taba burge ta ba, da dama yana
sa ta tashin zuciya tamkar z ta yi amai. Kan ta ce komai ya
fara buga kofar, Rafi'atun ta ce, "Waye?"
Ya turo kofar yana murmushi, "Ni ne da kaina".
Ta yi dariya tana kallonsa, ta ce, "Ashe kana gidan
muna nan muna ta zuba surutu?"
Ya ce, "Ina ciki ina jiyo ku, na ce ke ce kadai za ki
zo in dinga jiyo harshenta sama har da dariya".
Ta yi dariya sosai tana kallon Mabarukar, ganin
yanda ta turbune fuska.
Ya sake cewa, "Rafi'atu manyan mata, ke ce dai ga
ki ga aminiyar?"
Ta yi dariya, ta ce, "A'a ko dai kai, kai da ka ke
tashi yanzu karfe sha biyu, ni kwa tunakwas idona biyu".
Ya yi murmushi, ya ce, "To sa zan yi, wa ya hana
ni bacci jiya in ba kawarki ba?"
Ta kalle shi da sauri, "Kawaia kuma?"
Ya daga kai aiamar eh, yana kallon Mabarukar ya
ji ko za ta ce wani abu, idonta ba kanst vakeba. Ta juya
can gefe tana kumburi, Rafi'ar ta juya lanr larnbayarta,
"Wai haka Mabaruka?"
109
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Juyowa ta yi tana harararta tamkar za ta kai mata
duka, ba shiri ta kyale ta. Za ta yi magana ya tare ta yana
cewa Mabarukar, "Barka da safiya my princess".
Ta yi masa banza tana kara jin tsanarsa. Ya jinjina
kai yana dariya, ya cc, "Sarautar ce ta-motsa kenan?"
Ba ta dai ce komai ba.
Ya dubi Rafi'a yana cewa, "Bari in dan fita, zan
dawo yanzu".
Та се, "То a dawo lafiya".
Ya ce, "Amin". Tare da juyawa, fitarsa juyowarta
tana harararta tare da cewa, "ke dai wallahi yar wulakanci
ce, kina jin yana miki magana kin masa banza, anya
Mabaruka daidai ki ke? Mijinki ne fa karkashinshi za ki
shiga aljanna".
Ta juyo cikin bala'I, "Eh din, na yi, sai me? Kar ya
daga din an gaya mishi ina nema gurinsa ne? Bana so ya
take, kar ya daga, mugu kawai".
Ta zaro idanu tana kallonta a tsorace, abin nata
gaba yako. Wannan wace irin tsana ce? Ta ce, "Kina ba ni
mamaki Mabaruka, idonki gabadaya ya rufe, kin manta
Imran da matsayinsa, kin manta alkhairansa gare ki kawai
saboda an miki gatan aura miki shi, sai iskanci ki ke kalakala kina bijire wa kyautar da Allah ya miki, wallahi ki ji
tsoron Allah ki nutsu ki san me ki ke, ki tallafi mijinki da
auranki ku zauna lafiya ya fiye miki abin da ki ke son
banza za ki je ki halaka kanki".
Ta dube ta da rinannun idanunta da suka fara
canzawa na kuka, ta ce, "Har yanzu kin kasa ganewa
Rafi'a, tsana, kiyayya babbar ciwo ce da kunci, in ba ka
son mutum ba zai taba yin abin da zai burge ka ba ko da
110
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
sau daya. IHaka nan ba ka san sanda za ka dinga kuntata
masa ba, saboda zafin da zuciyarki ta ke miki. Ban ga
amfanin a nace lallai sai na zauna da wanda bana so ba,
duk ko abin da na yi kar a ga laifina saboda ba daga ni ba
ne, zuciyata ce ba ta sonsa, ba ta iya zama da shi, mafi
a'ala a sauwake min auransa sai kowa ya huta, ni ma na
samu saukin radadi da zafi da zuciyata ta ke min".
Та се, "Кarya ki ke wallahi, ke ki ka sa wa kanki
tsanarsa. Imran bai zamo makiyinki ba, masoyinki ne idan
har za ki tuna baya zuciyarki kuma ta fi karfinki, ba ki iya
sarrafa ta sai dai ita ta sarrafa ki, amma wallahi babu
kiyayyarsa a ranki wallahi Mabaruka".
Zuwa yanzu ta fara kai wa bango a kan Rafi'a,
maganganunta suna mata kaushi a ranta, don me ba za ta
fahimce ta ba, sai ta dage a kan lallai ita ce mai gaskiya
tana goyon bayansa, akwai abin da zai iya sa wa kansa
tsana ne haka kurum ba tare da an jarabce shi da hakan ba?
Ba ta sonsa ta fada ta sake fada, dole ne sai ta so shi?
Ta ce, "Ya isa Rafi'a, mu bar maganar nan ranki da
nawa duk za su baci, ba za mu taba fahimtar juna ba, ke ki
tsaya a kan naki ra'ayin, ni ma in tsaya a nawa kafin
lokacin barina gidan nan ya yi, ni ma in zama mai 'yanci
kamar kowa".
Ta numfasa ta ce, "Shi kenan na kyale ki,
maganganuna ba su ne za su fahimtar da ke ba na lura
babban abin da zan miki addu'a, ke ma ina shawartarki ki
ringa addu'a kina gaya wa Allah, sai Ya kawo miki sauki a
lamuranki. Sannan zan shiga kasuwa in duba miki wasu
littattafai na marubutanmu wadanda aka rubuta a kan irin
matsalarki, ki karanta ki ji yanda matan suka yi har suka
111
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
samu riba, ko kuma wadanda suka Ki karshe suka dawo
suna kuka da nadama. Ina ganin abin da zan miki kenan in
Allah ya taimaka sai ki ga kin yi maganin matsalarki ta
nan, sannan ga addu'a da man kina yi, sosai za ki rage
Kunci da damuwa da kadaici don ina da tabbacin za ki
nishadantu da ilimantuwa inshaAllah, a hankali
damuwarki za ta ragu har ki neme ta ki rasa".
Ta nisa cikin gamsuwa da zancenta, ta ce, "Shi
kenan ina jiranki".
Ta ce, "Zan duba miki insha Allah, sannan gobe fa
school kuma lecture ta farko test ce, har da haka na zo tuna
miki".
Ta zaro ido tare da mikewa zaune, ta ce, "Da gaskeе
Rafi'a, "Har mun cinye hutun?"
Ta ce, "Wallahi ni ma na ga saurinshi".
Ta ce, "Tabbas haka ne, daman ya ce ranar da aka
dawo da test za mu fara. Ki ce yau in kwna karatu?"
Ta ce, "Sosai, tun jiya na fara wallahi".
Ta yi farin ciki sosai da komawa school, ko ba
komai ta fita ta huta da zaman gidan, ta yo karatu watarana
ma a school ta ke wuni, sai yamma lis sosai za ta ji dadi
dogon hutu ne tun kafin auran.
Rafi'atu ta dubi agogon hannunta, ta ce, "Ke ni fa
yunwa nake ji, kin san ni indomi ba ta rike min ciki, mu
tashi mu girka wani abu".
Cikin farin cikinta ta mike suka hau kiciniyar
girkin.
Dawowar da zai yi ya tarar da gida ya turnuke da
kamshin girki, miyansa ya tsinke sosai yunwa ta taso masa
a falo ya tarar da Rafi'atu, ya ce, "Ina Mabarukar?"
112
WAYE ANGON?-3
Б 362 69 nawa
Maryam Jafar Kaduna
Та сс, "Тana ciki, wanka ta ke"!
Ya cc, "In dai ita tai girkin nan?"
Ta ce, "Sosai ma6
Ya kada kai cikin farin ciki, Da kyau, zubo min
Ya wuce dakinsa da sauri
Ita kanta ta yi dariya, ta mike ya sani idan zai cе
wa Mabarukar ta zubo masa ba za ta zubo ba, sai ranshi ya
baci dơn haka dama ce ta same shi Raff'a ta zubó din.
SHBY YG7 'Ta yi yanda ya ce, ta jere masa a falo, ya fito daga
dakinsa ya karaso da gudu-gudu yana cewa "Ba ni nan, ai
daki zan je da shi, ba ta dai saní ba ko?i
Ta kalle shi da mamaki, sai da ya sake nanata mata,
Bb d Yce, To Karki sanär mata kin ji ko sgb Ya
wuhn SLO Daga kai kurum ta yi, ya wkashe kayansa ya shige
dakinsa da gudu cike da murnar yau ma zai sake cin
girkinta mai dadi.
Ta juya ta shige dakin daidai fitowar Mabarukar ashio daga wanka, tana cewa."Ke'da waye ki ke magana?g
BAs TuSVa
5
co! Imran ana"d siek tnisi si iRD
133 ta ce komar ba, sai ma jai tsaki da ta yi ta wuce
ta dauko darduma ta shimfida da sallah. RafFa ta dube ta
kurum, ta co"Allah ya shirya kionuх влиа
ок яa ma ba ta ce komar ba,a. ta kabbara sallartasdes
Inna Binto ko tun safe ta ke ta sauri taa gama saida
alalarta ta tafi ko ita ma ta samo nata rabön Ga shi dai jiya
sun sha dage-dage, yara sai santi ake an kwan biyu ba a
lasa ba, Bare shi margidan yana ci yana sa wa Mabaruka da
ved ib syilst sums moyog olas ST
13
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
mijinta albarka, ba abin da yake cewa, sai, "Haihuwa ta yi
rana.
Sai daa ta saida alalarta tas! Sannan ta fito, tana
tafe tana lissafin kasafin kudin, kowanne ga abin da za ta
yi da su. Ta iso bakin gate, leke ta hau yi tsoronta kar a
kuma hana ta. Ta yi sa'a kam ba kowa, a guje ta shigo
tallafe da goyo ta hau wuri-wuri da idanu, ina ne kofa ko
ina kallon kanta ta ke ta madubi, ba ta ga alamar kofa ba,
da wacce ta sani sai ta yi nan ta yi can, ta rasa inda za ta bi
ta sadu da masu gidan. Tun tana ganin abin wasa har yana
kokarin zama gaske. Ta birkice ainun, cewa ta ke, "Ina
nake, nan ina ne? ina na shigo? Ko dai gidan yankan kai na
kawo kaina, gidan ne kuwa?"
Ta hau zagayen gidan duk girmansa har ta kai inda
ta daga kai, wani dogon gini mai tsini ta gani ba shi da
iyaka, karshe katanga ta tsorata sosai a guje ya baro wurin
goyo na shirin sullubea cewa ta ke, "Na shiga uku, ina
nake jama'a? Ku taimaka min".
Ba abin da ta ke gani sai kanta kurum ta jikin
gilassan. Wata kofa ta gani a tunaninta za ta fita daga gidan
ne, sai dai ta tsinci kanta tsakiyar falon tamkar wacce aka
jeho, ta yi wuri-wuri sai waige-warge ta ke da ka gani ka
san a tsorace ta ke, tak! Za ka ce ta arce da gudu.
Suna zaune falo da fara'a, tsulum suka ganta
gabansu, Mabaruka ta mike da hanzari tana cewa, "Inna ke
ce? Lafiya dai ko?"
Muryar Mabarukar ne ya dawo da ita hayyacinta,
don ko gani ba ta yi daidai, saboda firgita da ta yi.
Mabarukan ta lura da ita ta taho inda ta ke tsayc ta bayanta,
lana cewa, "Kwanto goyon, amma lafiya dai ko?"
114
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta kwanto tana cewa, "Bar ni in dawo hayyacina
Mabaruka, ban maheci in fifita duk na jike da zufa kamar
an watsa min bokitin ruwa, ke ina ma makewayi in zaga,
don marata dam ta ke saboda firgita".
Ta yi mata jagora zuwa bandakin, a can ma a rude
ta ke, ta hau lalube ta rasa inda za ta tsugunna sam gurin
bai mata kama da makewayi ba, ko ina tartar kal! Anya
akwai gurin fitsari gurin nan? Ga madubi nan da kayan
kwalliya kila dai daki ne? Ba shiri ta fito tana cewa, "Kina
ina? Ni fa ban ga makewayin ba, yana ina?"
Ta ce, "Ga shi nan inda ki ka fito Inna".
'Ta juya tana waige, "Nan shi ne makewayin?"
Ta ce, "Eh mana",
Та се, "Тo amma zo gwada min inda zan tsugunna
in yi fitsarin, kar na muku barna".
Ta wuto tana dariya, "Inna ho! Mu je ki gani".
Suka wuce ta nuna mata inda za ta zauna ta yi
fitsarin, ta ce, "A kan wannan tukunya-tukunyar?"
Ta yi dariya tana kallonta, ta ce, "Eh”.
Ta wuce tana kunna mata famfo, "Ga famfo nan in
kina da bukatar ruwa ga buta nan".
Ta jinjina kai kurum, Mabaruka ta ce tana
murmushi, "Hakan ya yi, ko akwai wani abun?"
Ta сe, "A'a je ki ya yi”.
Ta fice tana mata dariya.
Sai da ta yi fitsarin har da wanke kafafuwa da suka
yi kura, sun kwaso jar kasa aka wanke fuska, ta fito tana
cewa, "Wannan gida Mabaruka a cikinshi ki ke rayuwa?"
Ta yi dariya tana kallonta, "Eh mana Inna".
115
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta zauna tana jinjina kai, "IHodijam! Na ga
kokarinki ni kam ba zan iya ba, a kullum na san sai na
bace, wannan gida da ya yi kama da na masu satar
mutane?"
Suka yi dariya gabadaya, Rafi'a ta ce, "To Inna,
ina ki ka san yanda gidan masu satar mutanen yake?"
Та сс, "Кe bar ni Rafi'a, yau na tsorata ban taba
irin na yau ba. Gabadaya fa na rude. Cewa nake ina nake a
taimake ni, duk na firgice duk inda na juya kaina nake
gani, ko'ina ya zama madubi na rasa kofa".
Dariya ita da Rafi'a har suna fadowa daga kujera,
ita ko fade ta ke ba ta ko dariya.
Aka kawo mata abubuwan sha da na tauna zuwa
abinci, ta mike kafa ta dinga aikwa tana yi tana zuba hira,
tun abin yana ba Mabaruka dariya, har ya koma ba ta
haushi, tsoronta kar Imran ya dawo ya tarar da ita a gidan,
jiya Babanta ya zo ya matarshi ta zo? Ai abin zai yi yawa
ba hauka ake ba, da ganinsu ka ga makwadaita ita kam
kowa ya kalle ta zai ce kwadayi ya kawo ta, don ta ga jiya
abin arzikin da ya koma da shi shi ne yau ita ma ta zo ta
karbi nata.
Ta dade fa ba alamar tafiya har yamma. Ganin har
lokacin bai dawo ba ya sa ta сe, "Ke Mabaruka mijinki ba
ya dawowa da wuri ne?"
Ta hade rai, ta ce, "Lafiya, wa ke nemansa?"
Ta yi dariya tare da sosa kai, "Ah daman ni ce wai
ya zo mu gaisa, sai in tafi. Kin ga ba dadi har in zo in tafi
ba mu gaisa ba".
Ta ce, "Sosai kam, sai dai kin taki rashin sa'a, don
yau ya yi tafiya tun safe".
116
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta zaro ido tamkar wacce aka gaya wa mugun abu,
ta ce, "Ke 'yar nan sai yaushe zai dawo ke nan?"
Ta сe, "Cabdi! Ni kaina ban sani ba, don ya ce zai
kwana biyu, sai an ganshi".
Ta yi shiru tana jin takaici a ranta, me ya sa ba ta
zo tun safe ba ta riske shi kan ya tafi? Ta ja tsaki ta ce, "To
ki dan kira min shi ko ta waya ne mu gaisa ya san dai na
zo, ina gidan".
Suka haďa ido ita