sa maka gyaran biyu ka ji
ko?"
Ya ce, "To". Yana murna ya juya.
Ya tsayar da shi,"Ка се а wanke kwanon
sannan.
Ya ce, "To". Ya shige yana tsalle.
dafe Shigarsa kenan ya Keya ya ranta a na kate.
yaro ya shiga ya dinga kwarara sallama, daga kicin ta
Eite tana amsawa.
WAYEANGON?-3 Maryam jatar Kaduna
Shi kuwa tafe yake yana surulai, ya zama dole in
fita in nemo jari ko omo ne in dinga kasawa Kofar gida,
na gaji da gorin matar nan, gwanda in yi arziki ko na
huta da surutunta, kuma alkur'an idan na yi kudi sakinta
zaa yi, har uku ta bar min gida in auro zuka-zukan mata
vammata ma vanda za ia raina kanta
Kun ji fa? Gidan Mabaruka yake hankoron zuwa,
ya san ko dubu biyu ne ya samu gurinta, a da ma ya
samu haka ina ga yanzu ta yi aure, ai sai abin da ya fi
haka. Yana da naira hamsin a aljihuns, ya tsaya inda a ke
aida kati dan goma ya saya, aka sa masa.
GIDAN IMRAN
Tun kafin ta yi wanka ta nemar wa kanta abin da
za ta ci, daga bisani ta yi wanka ta shirya cikin atamfarta
mai kyau fes. Ta gyara dakinta, ta koma ta kwanta kan
gado tana buga gamc.
Lokacin da Imran ya tashi ya fito daga dakinsa
bayan yz dora jallabiya jikinsa, dakinta ya nufa ya
kwankwasa, a tunaninsa rufe ta ke kofar, amma ga
mamakinsa ya anta bude. Ya tura ya shiga da
sallamarsa, idonsa a kania.
Ta dago tana kallonsa fuskarta babu walwala,
hannunta dauke da waya. Yai tsai yana kallonta, ya kasa
dauke kansa. Sosai ta yi inasa kyau, kwalliyarta ta kara
daukar hankalinsa, a kullum Mabaruka tana masa kyau
fiye da jiva, haka zalika kullum akè kara masa sonta.
50
WAYE ANGON?.3 Maryam Jafar Kadona
can, ina ga bakan zai fi, amme wallabi ba zan kawo miki
mai aiki ba. ina fatan kin faliia?"
Ta kalic shi cikin bacin rai, "Wallahi ka san
hanya salo-salo la mugunta duk don ka kuntata min, me
na maka ka ke soa zaluntata? Idan kuwa har ka yi ajalina
wallahi ba za a kyale ka ba, ka kunshe ni a bakin
gidanka ka hana ni sukuni, ka hana ni jin dadin rayuwata
ka san ba na iya kwanciya daki ni daya ka nemo mai
taya ni, ka mmin bakin ciki. Wallahi Allah ba zai kyale ka
ba, sai Ya bi min hakkina". Ta fada daidai zubowar
hawayc.
liankalinshi ya tashi, ya dawo a dan rikice ya
tsugunna gabanta cikin lallashi da kulawa, ya ce, "To me
ye na kuka don na ce haka, sai kuka kina jin dadinsa
ko?"
'Ta yi masa banza tana kara zubo da hawayen.
Ya ce, "Is ok, is ok, sorry laifina ne, amma don
Allah ki fahince ni, ba na fada ba ne don ranki ya бaci
ke na sa ki kuka, wailahi na fada ne don haka nake
iyawa, don kuma jawo shakuwa da fahimtar jana
tsak...inınu. Mabaruka ba ki san gobe ba, a ki san
komai na rya canzawa a yanda ki ke jin tsanata wallahi
watarana za ki iya sona fiye da yanda pake sonki. Tsann
tawa za ta juye ta koma soyayya wallahi hakan na iva
faruwa, ikon Allah, tunda har Ya zaba miki ni, Ya aura
miki ni wallahi ba abin mamaki ba ne Ya sa miki
soyayyata fiye da tunaninki da nawa ki min soyayya mai
tsanani da dadi, dak sanadin muna tare ko muna kwall
tare hakan zai iya faruwa. Amma idan muna ncsanta da
53
WAYE ANGON/-3 Maryam Jafar Kaduna
juna kafia mu fahimci juna za mu dade, za mu shha wüya
ke zaman ba dadi, i ba dadi don AlDah ki duba
maganata
Ta kalle shi da jajayen idanunta, ta ce, "Ilar ma
kana tunanin zan so ka, akwai ranar da zan so ka, kana
min mugun fatz bayan ga alkawarin da muka aje a
tsakaninmu?"
Ya gyara tsugunninsa ya ce, "Na sani, ina fatan
kafin wata ukun ya cika mun daidaita, idan kuma ya cika
ba zan saba miki ba Mabaruka, zan cika miki
alkawarinki, in kuma ma na bar miki duniyar kin ga shi
kenan sai ki huta, amma don Allah ki bar maganar mai
taya ki kwana, ki zo dakina mu dinga kwanciya tare ki
daure na san da wuya za ki iya Mabaruka, ba don ni ba
sai don Allab".
Ta dauke kania zuwa gefe, ta ce, "Ba zan iya ba
wallahi ba zan iya ba, ina jin kunci idan na kasance tare
da kai. Ka tausaya min
Ya yi jim yana kallonta, can ya nisa ya ce, "Shi
kenan ba zan takura ki ba”.
Daga haka ya mike yana cewa, "Ni.n tafi in
dan yi wanka, zan je gidan Ibrahim in karya yau
weckend, ba zan je oflis ba sai yamma zan fita"
Ci kanka ba ta ce ba, sai dai ya gaji ya fice zuwa
dakinsa, ya vi wanka abinsa ya fito fes, ya yi kyau sosai
ya sha kananan kaya, rigar baka ce wandon kuma light
green haskensa va fito da kyansa na jinin Larabawa,
sumarsa la vi kwance lui-luf, kamshi yana tasowa mai sa
의
34
WAYE ANGON?-3 Maryam jafar Kaduna
nuisuwa. Ya dauko wayovinsa da key Io daca
dakinsa ya nufo gurinta.
Shi kuwa Baban nata ya laiubo lambaria ya kai
kunne yana cewa, "Dadin na baila ma kenan ga inda za
a share min hawaye".
Bugu biyu ta dauka ba laifi tana fara'a ta dauki
wayar Baban nata, ta kai kunne lare da sallama tana
cewa, "Baba".
Daidai shigowar Imran din. Ganin tana waya ne
ya sa ya ha ya tsaya yana kallonta, ko don yanda ya ga
tana fara'a da dariya da alama tana jin dadi, zai iyа сea
rabon da ya ga tana ko da murmushi ne tun kafin a fara
د maganar auransa da ita. Ta yi masa kyau sosai kamar ba
ita ba, 'yan kananan hakoranta jere reras suka bayyana,
farare kal tana dariya har da harde kafa. Ya jingina ga
bango yana kalionta yana murmushi, shi kanshi yana
ganin kamar ba Mabarukarsa ba. Sai yaushe ne za ta fara
masa irin wannan murmushin da zakwadin da ta ke
yanzu zuciyarsa ta kwadaitu da haka, ina ma tunaninsa
ya tabbata? Yayin da ita kuma ba. san yana tsaye ba
duk dokin jin Babanta, ta ce, "Baba ya su înna!"
Ya ce, "Ke rabu da wannan mahaukaciyar tana
can na baro ta da yara tana zage-zagenia da ki ka sani
Та сe, "Kai Babah har yanzu dai kuna a
ku ke ba ku fasa ba, yara na kallonku suna danyaila
ba ta girmamaka ba kai ka dinga rike girmaaka ne!
dai duk kan kudi ne sai ka daina di mata bashin k
ko alzlarta".
55
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Zai yi magana kenan 'yar hamsin din ta kare,
don haka ta kira shi, ya ce, "Kudin ne suka kare, da ma
hamsin ne".
Та се, "Луya bari zan turo maka".
Ya ce, "A'a gwanda ki ba ni na zahiri, wadannan
ai gaibu ne".
Ta ce, "To ni Baba ina zan ganka in ba ka, na san
ba barina za ai ba na zo tun yanzu ba, duka kwanana
nawa?
Ya'ce, "Abu mai sauki? Ga ni nan zuwa, sai na
zo na karба".
Ta yi saurin katse shi, "Haba wane irin ka zo ka
bari dai duk sanda zan zo sai na ba ka, yaushe za ka fara
min sintiri nan kan kudi, har ya raina ka? Ni ban farа
zuwa ba sai kai ka zo, kuma na sanka sarai Baba idan ka
gane hanya shi kenan kullum sai ka zo ka ce na ba ka
kana ba ni kunya".
Ya ce, "Ke dai 'yar banza ce wallahi wa ya ki
kudi ke kanki ba kudin ba ne ya sa uwarki ta guje min
ba, ke ma ta guje aura miki talaka ta ba ki mai kudi,
kuma don na zo gidanki sai ki hana ai, me ye laifin na zo
ganin lafiyarki?"
Ta rikice ainun, don ta san kwadayinsa, ta ce,
"A'a Baba kai dai ka bari duk sanda zan zo zan kawo
maka, bana son wallahi ka san hanya, zan tambaya cikin
satin nan na zo ka ji Baba?"
Gabadaya hankalin Irnran ya koma kan
maganganunta, ya fakimci da wa ta ke magana da
56
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
manofar hana shi, shi ko Baban ya dage lallai sai ta ha
shi adireshinia ya zo ya karba.
Ta ce, "Gaskiya Baba ba zan ba ka ba, ka bari na
zo din, yanzu zan turo maka dubu daya ka kai a cire a
siya ko dari bakwai ne ka samu kafin na zo".
s Ji, ta yi an wafce wayar daga hannunta, ta yi
saurin dagowa la ga wace ce, ko wane ne? tsoronta kar
dai a ce Imran ne. Ai ko shi ne suka hada ide, ya yi mata
sigual yana murmushi tare da kai wayar kunne yana
cewa, "Assalamu alaikum Baba".
iankalinta ya tashi ainun, ta rikice ta mike tsaye,
idanunta waje, me ya sa ya yi mata haka? Tabbas da
Baban ya ji maganar lmran zai roke shi kai tsaye, ya
gama ba ta kunya. Ta yi tsalle wai za ta kwace, gam! Ya
rike ta da hannu daya ya matse ta jikinsa, yanda ba za ta
iya kwacewa ba. Ta hau kiciniyar kwace kanta, amma ta
kasa. Shi kuwa yana maganaısa ya ce, "Kana ina yanzu
Baba in zo in tafi da kai?"
OTsd Daga can ya washe baki, shi shar abinshı ya jefa
ya caike tunda mijinta ma na gida ai yau sai ya cika
aljihu Karshen gorin Binto ya zo-yaus sai ta gane kurenta,
ya ce, "Allah sarki yaro, kai ne da kanka, kana gidan
kenan?d
mse Na dan raukwafa cikin girmamawa kamar yana
gabansa ya cc, "Eh Baba".
Ya ce, "Ka ga ita ko ba ta son na zo wai don kar
na ga hanya, kullum in dinga zuwar mata gida. Shi dai
talaka an raina shi ko zumunci ba a son ya yi sai a ce ya
57
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
20 Kwakwa, don Allah đan nan ko za ka kyamaci talaka
ka Kvamacı Babanka?"
Ya ce, "A'a Baba".
Ya ce, Te ka ga dai ita ta kyamaci zuwana
kamar yanda uwarta ta kyamace ni don su sun auri masu
kudi sun bar ni cikin talauci, ko tausayina ba su yi, ni ma
su jawo ni jikinsu in dan warware da bakin talaucina
wanda ya zama gado, vun kakana har Babana haka suka
taso cikin talauci da tsiya, suka mutu ba abin da suka bar
mana gado sai gadoa tsiyarsu. Yanzu haka na baro gidan
ko na koko ban ba su ba ta gagare ni da wazobia na
kwan, ita ma bashinta na ci jiya don in kira Mabarukas,
to ashe ma ba ta murna da zuwana?"
Maganganu fa ya dinga zubawa ba maida
numfashi, shi ko Imran din yana sauraronsa bai katse shi
ba, yayin da ita tana rike gam a hannunsa duk tana jin
me yake cewa, saboda loudspeaker. Takaici da bakin
ciki suka cika ranta na abin kunya da Babanta yake ja
mata gurin mijinta, ga shi ta gagara kwace kanta bare
wayar ba ta yi aure ba ta dinga jin hawaye na zubowa.
Bayan ya dan tsagaita ya , "To kana ina Baba
in zo in tafi da kai?"
Ya fada masa inda yake, bar tsaya nan ba ya ci
gaba, "Da ma tunanina fa ko 'yar dubu biyu ce na samu
gurinta kan ta zo din, shi ne ta ke son hana ni, ashe kana
nan
Ya ce, "Ih ga ni nan zuwa ka jira ni".
Ya ce, "To ina nan ba, inda zan je ko da zan kai
vamına ina nan har sai ka zo
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ya ce, "To shi kenan yanzu ma zan zo ya kashe
wayar".
Ya kalle ta yana son yin dariya, ya miko mata
wayar ya ce, "Ga wayarki zan je in taho da shi".
Ta dago tana kallonshi takaici ya cika mata rai,
ta rasa me za ta yi ta hude, kawai ta samu daidai Jantsen
hannunsa ta cije iya karfinta ya fasa ihu, ya kwaci kansa
ya mike yana dariya, yana murza wajen yana kallonta,
dariya na cinsa, ya ce, "Lallai yarinyar nan kina son ki
illata ni ko? Ni na ce ki kira shi?"
Ya ci gaba da dariya yana kallonta, yanda ta ke
harararsa kamar idanunta za su fado saboda takaicin
kwafsin da Babanta ya mata, ga shi nan har ya samu
abin dariya. Ta kasa daina harararsa, ganin ta ki janye
hararar ya sa ya dan rankwafo daidai ita yana dariya, ya
ce, "Sorty ba zan kuma ba, na yi karamba ni amma ki
daina hararata kin ji?"
Ya mike ya wuce yana cewa, "In tafi ko?"
Ta hau juye-juye, me za ta jefe shi da shi ko ta
huce? Ta rasa komai, sai dai ta mike tana gyara zani a
wayonta ta jawo wata kwalba same. mirrow ta jefe shi.
Ya gane sarai, ya fice yana cewa, "Sai na dawo yan/!-
yanzu, bye”.
Ya fice yana dariya. A mota ya dinga jin
haanunsa na radadi, gurin har ya fasa ga jerin hakoranta
nan. Ya shati wurin yana murmushi, ya ce, "I love you
Mabaruka, watarana cizonki zai zama kiss. Ina farin ciki
59
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
da cizon da ki ka min, kasancewar bakinki da miyanki
ya taba jikina, am happier
Da wannan nishadin ya isa inda Baban yake, ya
tsaya da dalleliyar motarsa, ya fito. Shi ko gogan da
ganinsa ya taho da sauri, jikinsa har yana rawa.
GIDAN INNA
Hawayen suka ci gaba da sintiri, ta rasa yanke
wa kanta hukunci. Shin barin gidan ko ko tsinuwar Inna
da wulakancinta gare ta da iyayenta? Daga can wajen
Inna ta ce, "Na rantse idan har ba ki bude ba yau ba za
ki kwana gidan nan ba, saki uku zai miki kin bar gidan
har abada, ba ke ba shi. 'Yar iska, makwakwaciya, yar
matsiyata".
Kai zagin nan ya ishe ta, ba za ta iya jura ba, don
haka ta bar wa Allah komai, ta kama kofar za ta bude,
ya dago ya ce, "Kin yarda ki bar gidan nan ko?"
Та се, "Кo na bude, ko ban bude ba zan barshi,
tunda ta rantse sai ka min saki uku a yau. Yi mata
biyayya ya fi rashin yinta, ka yi hakuri".
Daidai bugun kofar da aka yi tamkar za a karya
kofar. Ba shiri ta cire sakatar kofa ta bude wayam! Та
shigo tana cewa har tana tuntube, "Kina ina munafuka?"
Ta fito daga bayan kyauren tana sunkuyar da kai
cikin ladabinta, ta ce, "Ga ni..."
Jawo gashinta ta yi tamkar za ta cira sbi, ba shıri
ta biyo ta saboda zafin da ta ji, ta rike kanta har da
rantse idanu, ta sunkuyar da ita gabanta.
60
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
"Ni sa'arki ce ko uwarki, ina miki magana kin
raina ni, haihuwarki na yi, ko ko kishiyarki ce ni?"
Ta girgiza kai, "A'a".
Ta kai mata dundu iya karfinta, har tana cije
lebe, zatin dundun ya shige ta har tana yunkurin amai, ta
bankare kirii saboda yanda bayan ya rike, ta ce, "Ki yi
hakuri".
Ta sake kai wani dundun, wanda ya kai ta kasa
gabadaya, daidai dirowar Sulaiman daga gadon ya rike
hannun Innar ransa bасе, уа се, "kada ki sake dukanta,
tunda ke da kanki kin ce ba ke ki ka haife ta ba, don
haka ba dalilin dukar musu 'ya, laifin nawa ne".
Ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki, "Lah!
Ni ka dakatar Sulaiman, laifina ka ke gani ba na matarka
ba? Matarka ta fi ni ko Sulaiman? Ka goya mata baya?"
Ya ce, "Ba haka nake nufi ba, amma takurarki ta
yi yawa Inua, kin zamar mana matsala a gida ba mu da
ikon sakewa, gidan ubana haka matata ba ta da sukuni
da walwala duk matar da na aura kin korar min ita, sai
wannan ta iya zama da ni saboda hakurinta. To wallahi
ba zan yarda ki korar min ita ba, ba mai iya zama da ke
sai ita. Ya zama dole yau na kawo karshen takurarki, ba
wanda ya takura miki ke lokacinki, har zuwa yau sai ni
kin bana ni walawa, haba!" Ya fada cikin gajiyawa.
Ai fa ta yi kwalkwa! da idanuwa tana shirin
kuka, "Yanzu Sulaiman ni ka ke zagi saboda matarka?
Matarka ta fi ni ko Sulaimán? Ni na sha wuya a kanka,
na yi cikinka, na rene shi, na baife ka, na shayar da kai
61
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
gar girmanka, ubanka bai taba biyana ba shi ne yau rana
daya ka fifita matarka a kaina?"
Ta fashe da kuka, ta fice tana cewa, "Shi kenan
tunda ba ka sona, ka fi son matarka har kana min gorin
gida, to zan bar maka gidanku ka zauna da wacce ka ke
so"
Ta fada dakinta tana koke-koke har tana bugebuge tamkar wacce aka aiko wa da mutuwa da safiyar
fari.
Shi kuwa bayan fitarta ya ce, "Ki je ki yi duk
abin da za ki yi, Allah ya san zuciyata".
Ya sunkuya yana wa Nafisa sannu. Ya dago ta, ta
zauna a sandare bayanta ya rike, ta kwanta ruf-da-ciki
yana mammatsa mata bayan, yana cewa, "Ki yi hakuri
Nafee an gama musguna miki a gidan nan ina gani in
kyale, gobe ba za ta sake ba, sai da ma na ce kar ki bude
na san hakan za ta faru, amma ki yi hakuri".
Ta share hawaye ta ce, "Na yi laifi Sulaiman,
dole ranta ya baci, tun yaushe ta ke tsaye nan tana cewa
a bude kofar amma muka share ta? Ka ga dole ne ranta
ya baci, ka je ka ba ta hakuri ga tana kuka kar ta yi kur fushi da mu.
Ya ce, "Ki kyale ta in ta gaji za ta bari"
Wannan koke-koken da Innar da buge-bugenta
ya tada Samira ba shiri, ta fito ta nufi dakin tana cewa,
"Lafiya Inna, me ya faru?"
Ta ce, "Bar ni Samira, kyale ni in yi kuka kar
takaici da bakin ciki ya kashe ni, an shiga tsakanina da
dana za a raba mu, Samira kar ki yarda ta raba mu'.
이
62
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta tsugunna cikin rashin fahimta ta ce, "Yi min
bayani, me ya faru?"
Ta ci gaba, "Sulaiman ya fifita matarsa a kaina,
ya wulakanta ni har yana zagina ya zabi matarsa a kaina,
yau asirinta ya ci, malaminta ya ci kudinsa har yau
Sulaiman yana min gorin gida, ai gidanshi ne ba nawa
ba, in je in nemi namu gidan ga ta can yana lallashinta.
Na shiga uku na bani, shi kenan ta raba mu".
Daf! Saniran ta mike tana bala'i, "Kam bala'in
nan, har ta isa? Ita din banza? Wallahi sai dai ita ta nemi
gidan nata uban, wannan namu ne, ita za ta bar gidan
dole kuna ta kyale min dan uwa, ba ta isa ta raba mu da
shi ba. Karya ta ke".
Ta fice a fusace zuwa dakinsa.
GIDAN BABAN MABARUKA
Inna Binto ta fito daga daki hannunta wanke da
miyar kuka kore shar! Ta cika baki da tuwo, ia сe, "Ya
aka.yi Auwal?"
Kafin ya ce wani abu, ta ga kwanan wayam! Ba
komai cikinsa. Ta doka zagi, "Kan uban can, kar dai ka
ce min ka zubar?"
Ya buda baki zai yi magana, ta katse shi,
"Alkur' an ba zan sake zuba maka ba, ai ba ni na zubar
ba, a kudinka. Na rantse ka je a ba ka wasu". Ta hafe rai
sosai.
Ya yi dariya, ya ce, "Kai Inna ki tsaya ki ji yanda
aka yi, kin hau bala'i".
63
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "To ina jinka maganar ne da katon
bakinka yaro da kai sai fi'ili, ya aka yi ne?"
Ya ce, "Ai Baban Mabaruka ya karba ya ci a
zaure, ya ce in kawo miki ki zuba min tasa yana sauri
har ma ya ce ki kara min guda biyu". Ya karasa yana
washe baki shi zai ci alala.
Ta zaro ido tare da cewa, "Kanbu! Yau ga
makiri, wace alala tashi da ya ba ni kudi?"
Ya ce, "Ni dai haka ya ce min, ki zuba a tashi”.
Та се, "Кai kalle ni nan, kama gabanka ka ban
guri, ni na ce ka ba shi?"
Ya ce, "A`a.
Та се, "To ba ruwana, ka je gurinsa ya biya ka,
ban san da wannan zancen ba, maza bi shi ya ba ka
kudinka, na rantse ba zan zuba ba tunda bai ba ni kudi
ba, na koko ma bai ba ni ba bare wta alala, maza fita"
Yaro ya ja ya tsaya, ya ce, "Ni dai ya ce ki zuba
min tasa, ki sa gyara guda biyu".
Та се, "Тo ko ta kudinka ba za ka samu ba bare
gyara, kawai ya ci zalunka, ka tafi ka gaya wa Innarka
sai a bi maka hakkinka".
Yaro fa ya kafe shi sai ta zuba nasa wata, har da
gyaransa. Ta zaro masa ido, ta ce, "To ko zan ci ubanka
idan ba ka ba ni wuri ba, ni na cinye maka bare ka tsare
ni?"
Ya turo baki, "Ni dai ya ce ki zuba min wata"
Ta taso, "An ki a zuba wata din, dan rainin
wayau, fitar min daga gida".
64
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta jawo shi kii! Shi kuwa yana turjewa har
zaure, ta tura shi can kofar gida tana bala'i.
"Haka kawai ban ci nanin ba nanin ba za ta ci ni
ba, tunda ba ni na cinye maka ba don me za ka nace
lallai sai na biya? Can ka je ka nemi wanda ya cinye
Inaka"
Ya ce, "Wallahi sai na íuro Innata ta zo ia
Kwata".
Та се, "Кa turo Kaka ba Inna ba ka dade, zan ga
mai amsar alalar nan".
Ya wuce da sauri har ya bace ba ta daina bulbula
fada ba, duk wanda ya wuce yana kallonta.
Yaro ko da shiga gidansu ya fasa kuka, Innarsa
Ladi ta taso, "Kai lafiya? Ina alalan, ta zube ne?"
Ya ce, "A'a, Baban Mabaruka ne ya cinye ya ce
in shiga cikin gidan a zuba min tasa yana sauri, shi ne da
na kai mai alalan ta ce ba za ta zuba ba, ta koro ni".
Abu ya tarar da gida, ai ko ita ma ta hau sama,
bala'i kan bala'i kowa na ji da nasa, ta ce, "Karya suke
wallahi, daga ita har makwakwacin mijinta, da ma ya
saba yi wa yara haka abun ya zo kaina kenan? To
wallabi ba su isa ba, ko amanta sai ya yo in ba a biya ni
ba naira hamsin dina ba ta tafi a iska ba, in kwana uku
ina sana'a sannan na same ta, haka kawai wani katon
banza, gardin kauye ya tarc yaro ya cinye in kuma kyale
gumina bai tsane ba? Don haka alkur'an sai an biya ni
ko hamsin dita ko alale ta, mu je".
65
WAYE ANGON?-3 Maryam Jjafar Kaduna
Ta yayumo mayafi ta saba, yan gidansu suka
taso, "laba Ladi, ina amfanin rigima kan hamsin? Ki
Kyale su da Allah, tashin hankali ba shi da dafi".
Ta yo kansu, "Idan da mai biyana cikinku in ji,
hamsin din kawai?
Suka yi tsuru-tsuru ba mai iya biya, ta ce, "Tо
tunda ba mai iya biyana ku kyale ni in je in bi hakkina,
ai halaliyata ce, wahalata ba an kyale katon banza ba".
Suka ce, "To Allah taimaka".
Та се, "Вa amin ba". Da harararsu ta hankada
yaron tana fadin, "Mu je munafuncin banza da na wofi,
duk sai na yi maganin kowane dan iska".
Kamar an jeho su ta ga sun fado, ba ko sallama.
Tana zaune tsakar gida a wurwurce ta gansu. Ta mike ita
ma cikin nata bala'in, "Lafiya, me ya shigo da ke haka
gidana?"
Га се, "Мe zai kawo ni wajenki da man idan ba
da dalili ba? Ina marar zuciyar mijinki?"
Ta ce, "Duba ki gani mana in za ki ganshi".
Iya wurge-wurgenta ba ta ganshi ba, ta cе, "То
ya ci zalin yaro, wa zai biya masa?"
Та се, "Ki bari ya zo sai ki masa wannan
tambayar"
Ta cire gyalen ta daure a kugu, ta ce, "Ke dakata
ba wai na zo bata lokacina ba ne gurinki, kawai ki shiga
ki debə min alalata, shi kenan in kama gabana".
Fa vi shewa tare da tafa hannuwa, ta се, "Псуe,
ah lallai ma za kuwa ki bushe gurin nan in har sai ni zan
66
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
biya ki, ban ci ba a ce na biya? Ki bari wanda ya ci ya zo
ya biya".
Ta ce, "An ki a bari din, na rantse sai kin biya ni
alalata ba katon da zai cinye min kudina in kyale, samun
lafiyarki wallahi ki biya ni kawai abin da ya yi shi shi ya
yi ki, can in ya dawo shi ya biya ki, ni dai alkur'an ba
inda zan je sai kin biya ni".
Ta matso daidai inda ta ke, bar suna jin hucin
junansu, "An ki a biya din, na råntse kwandala ta ba za
ta yi ciwon kai ba". Ta nuna ta da yatsa, har tana
dunguri.
Ladi ta ce, "Kar ki sake nuna ni da yatsa na gaya
."rmiki יי
Ta kara nuna ta din, ta ce, "An nuna din, ki abin
da za ki y!".
Kan ka ce me? Fada ya kaure tsakaninsu, ji ka ke
tim! A kada wannan ta tashi, ita ma ta kadar, fadan dai
har ya kai su inda sauran alalan ta ke, Ladi ta dauko
bokitin za ta zuba na kudinta, ta yo kanta za ta kwace.
Karshe dai aka watsar da alalar gabadaya a kasa.
Inna Bintoa saki baki galala tana kailon saurau
alalanta da ta rage ta dari biyu da hamsin, ta ce, "Kan
uban can! Ki ka watsar min da alala? Alkur'an sai kin
biya ni na rantse".
Sai kuma ta cakume ta, ita tana bala'in sai ta biya
ta dari biyu da hamsin, ita kuma sai ta biya ta naira
hamsin duk dai a nan saka tattake alalar har ba za la civu
ba. Fadan fa ya ki karewa ga yaran sun yi tsaitsaye ba
mai iya rabawa, har dai ta kai su ga fitowa kofar gida
7
WAYE ANGON?-3 Maryam jafar Kaduna
ana kade-kade, mutane suka yi iururuwa ana kallo an
kasa raba su, kowa yana isoron kar ya je daga rabo a
naushe shi a barshi da jinya, sai dai daga nesa-nesa suke
cowa, "Ku yi hakuri, ku yi hakuri
GIDAN IMRAN
Tun sanda ya fita ya barta ta ke cikin takaici da
cizon yatsa, me ya sa ma ta bar wayarta a kunne har
Baban ya kara ta, yanzu haka Allah kadai ya san me zai
faru, shi da ma mai nema? Don haka ta san