motar yana cewa, "Kai dai bar ni
kawai, mu je kawai ciki"
Suka wuce suna dariya.
Suka baje a falo, Amina matar Ibrahim din ta
shigo tana cewa, "A'a ango, ango na Mabaruka daga
ofis ko daga gurinta?"
Ya ce, "Ofis dai".
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
kokwanto kamar na Mommy, don haka suka zauna suka
kwashi gara, suka yi hani'an. Daga nan suka koma hira.
Ssi ana magriba ya baro gidan suka je masallaci,
bar aka yi isha sannan suka fito. Daga nan ya shiga
motarsa ya yo wajen Gimbiya Mabaruka.
Da buda gate din ya shigo, karnukan da ya sa a
kawo masa suka dinga haushi, bakake har guda biyu. Ya
yi dariya ya fito daga motar, daga cikin ma'aikatansa ne
ana ce masa Lawal ya nufo shi cikin girmamawa suka
gaisa.
Ya ce, "Sun iso kenan Lawal?"
Ya ce yana sosa keya kasa-kasa, "Eh Yallabai,
ga su nan ina fatan sun yi ko?"
Ya wuce wajensu yana dariya, ya ce, "Ai ba zan
iya ganewa ba Lawal, wannan sai ku. Ni dai in dai suna
haushi sun min kawai".
Ya yi dariya shi ma, ya ce, "Yallabai, ai ba karen
da ba ya haushi, ga su nan da lafiyarsu".
kenan"
Ya ce, "Da kyau, ka yi kokari, na godę".
Ya ce, "Ba komai Yallabai ni ke da godiya".
Ya ce, "To madalla, bari in shiga -sai da safe
Ya ce, "Allah tashe mu lafiya, a fito lafiya".
Ya ce, "Amin". Tare da wucewa ransa na nmasa
fari kwal yake jinsa na makota ma sun hana ta bacci sun
koro ta gurinsa, ina ga na cikin gidan?
Bai yi tunanin zai same ta a falo ba, amma ya
tarar da ita zaune, hannunta rike da remote tana kallo, ya
san shi ma don kayanta ne har ta zauna ta ke kallo.
36
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ya yi sallama ya shigo yana kailon bakinta ta
amsa, tamkar rada. Ya tabbata motsa bakin kawai ia yi
ba wai amsawa ta yi ba. Zama ya yi yana kallonta, ya сe,
"Sannu da gida, ya hutu?"
Tamkar ba ta gurin, idonta ko kiftawa ba ya yi,
duk da yana shigowa ta ji ranta ya bace, kallon ma ta bar
jin dadinsa. Ya yi murmushi ya ce a ransa, "Za ki sani
yarinya
Bai damu ya sake mata maganar ba, dan
kishingidawa ya yi a kujerar yana fuskantarta, ya се,
"To bari in taya ki kailon".
Minti biyar bai yi ba da zamansa ta mike, ba ta
kalle shi ba bare ta tanka, ta wuce dakinta ta rufo har da
sa mata key, ta fada gado ta yi lamo tana jin kunci a
ranta.
Tun daren jiya kuma hankalinta ya tashi, tana
tsoron kar a kuma na jiya, zullumi ya cika ranta.
Shi kuwa yana nan zaune bai damu ya biyo ta ba,
yai zamansa yana kallon sai da dare ya yi sosai, ya fara
jin bacci, sannan ya tashi ya shige dakinsa, duk abin da
ya zai. masa al'adarsa kafin ya kwanta sai d ya yi,
wanki, wanka da brush. ya yo alwala sannan ya hau
gado ya kwanta, ya yi addu'o'insa.
Ha kuwa tana nan ta kasa ta tsare wai ba za ta yi
bacci ba, ko ya ta ji motsi sai ta zabura ia kudundune,
har da runtse idanuwa gam! Tana nan dai har bacci ya
dauke ta ba ta sani ba. A yau karnukan sai wajen biyu
sannan suka fara baushin ma har ya baci, ya yi yawa, ga
37
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
na makota ga na cikin gida, har da kukan jaki! Amma ita
ba ta san Jaki ba ne sai ta ke jinsa kamar na Zaki-Zaki,
Kura-Kura, ta iashi zaune a firgice, idanuwa sun yo waje
jikinta ya hau rawa.
Tun tana iya jurewa har ta gagara, ta diro daga
gadon tana juye-juye, ta ga dakin duk ya yi mata girma,
ya kara ba ta tsoro ta fito a gigice, falo ta zauna tana
waige-waige. Tsit! Ka ke ji, ba motsin kowa sai ma ta ji
gwanda dakinta a kan falon, saboda girmansu ba daya
ba. Da suka yi wani haushin da sauran kukan halittun sai
dai ta tsinci kanta ta tunkari dakin Imran din. Ya san za
ta zo da ma idonsa biyu, yana saurarenta. Ko da ta shigo
din ma ya yi lamoo, ta zo ta tsugunna kasan gadon ta
makurę ko ya tamotsi sai ta zabura.
Ba laifi kam tunda tana jin motsin mutum ta san
ba ita kadai ba ce a dakin, in ma wani abu zai same ta ba
ita kadai zai sama ba, don haka ta dan nutsu har dai
kukan nasu ya lafa bacci barawo a nan ta fingire tana
bacci. Da ya yi niyyar dauko ta daf! Ta dawo kan gadon,
amma tuna rashin kunyarta ya sa ya hakura ya kyale ta,
ko b. komai dai a daki daya suke, yana jii. saukar
numfashinta hakan farin ciki ya sa shi, don haka ya yi
baccinsa hankalinsa kwance. Gaf da asuba ne ya farka
saboda sanyin lokacin.
Ita kanta ya ga duk ta makure tana jin sanyin,
amma a haka ta ke baccin, ya lullube ta da lallausan
bargonsa, yana jinta har da sauke dogon numfashi ta ci
gaba da baccinta, ya koma gadonsa abinsa.
38
WAYE ANGON?-3 A Maryam afar Kaduna
ли Кo da asuba ta yi har ya tafi masallaci, ba ta tashı
ba sai da ya dawo. Yana sane ya ki tada ta don kar ta
fara masa na tun asuba, ya kwanta abinsa
аз одлаB bưde ido tana kalton dakin Caidai, a ga inda
ta ke kwance, kasan tayil jikin gado tá tasbi da sauri a
sörace ta yi saurin cire bargon cikin jin haushi, don me
zai rufa mata bargonsa ta roke shi ne? ta ja tsaki tare da
nikewa tana daura dankwali fuskarta murtuke. Kallonsa
ba ta yi ba bare ta tanka masa ta wuce abinta cike da jin
haushin kanta. Sim-sim ta fice zuwa dakinta, 12 yi
"alwala ta yi sallah, daga baya ta koma ta kwanta bayan
ta gama rokon Allah ya raba ta da wannan mugun gidan.
ansl sd agia o sl sont'sisd ah ost sl si
nIDAN INNS
Bayan ta taso shi da sanyin safryar nan kamar
Vanda suka saba, ya dawo dakinta ya kwanta a
jemammiyar labarmar da ya saba kwanciya. kai ba ko
shimfida bare filo tata zauna lare da mikE Kaata dauko
bokitin sigarinta kamar kullum tana kullawa daun-daur:
don bala in inna ko na goma ba ta kulla wa sai na ashirin
faIsingul-tsingul. Ita da kanta ke kulla shi,aa ta yarda
a kulla mata ba, wai don kar a dambaza shr da yawa. Kо
da Samira ce kuwa in lasa da yawaa yanzu za ki ji tana
balanKefafa yar banzar yarinya ce, ba ki san darajar
abin duniya ba, ki dinga cika leda kamar ubanki ya ba ni
afitn is ay onida sy asbi sw sds1 oA isb asmiκ!ς
ce, "Ke Imna ki dinga jin tsoron Allah, ina na
cika dedar ashirin fa, ya ki ke so a zuba shi, ke komai
naki bala i ne, in ban da ma kamar kin tsafe masu sıyen
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
kullum suma makale da kayanki, wa zai sai wannan
tsiyar taki?"
Ta taso da bala'i, "Ke fa ja'ira ce, sam ba ki da
hankali. Nan idan auren naki ya taso zuba min ido za ki
sai na sai miki kwanuka, wa ke gare ki da zai miki?
Dangin ubanku dai ga su nan ba zuciyanc da su ba, dole
ni din zan yi dai".
Ta tabe baki ta ce, Haka ki k cewa, yanzun
Sulaiman da ya tashi nashi auren wace tsiyar ki ka yi
masa? Ba abin da ki ka masa sai dai surutun. To haka
idan nawa ya tashi ba abin da za ki sai dai ki sa masa
ido".
Ai fa ta taso da bala'i, inda ta ke shiga ba ta nan
ta ke fiia ba, "Zagar ni na ce, kada ki rangwanta min kin
ji ko. Nan lokacin da ubanku na nan me ye ba na masa?
Ni nake ciyar da mu da shi gabadaya, ba ya wani
katabus don malalaci ne, mai mutuwar zuciya komai ni
nake muku, ba abin da yake har ya bar duniyar, shi
kanshi gidan nan ta ya aka same shi in ba..."
Ta yi saurin katse ta, "Kar dai ki ce naki ne, don
1a ardu sun yi bayani, sun nuna maigida ba 2 vandalarki
a nan, gidansa ne halilinsa ya mallake shi".
To in dai ta sa ta haka za su kasance tamkar ba
'ya da uwa ba, ita uwar girma ya fadi, ita kuma 'yar
marar kunya wacce ba ta samu tarbiyya ba sam,
Sulaiman dai ke raba wa idan ya shigo ya ci mutuncin
Samirar, bayan ya mata fada sosai, ita kuma Innar ya
dinga nuna mata abin da ta ke ba ya dacewa, ita babba
ce uwa, kuma bai kamata tana haka ba, ta rike girmanta.
WAYE ANGON?-3
Ta
Maryam jalar Kaduna
kan dawo kansa, An ki a rike girman do
uhanka, ni za ka koyawa yanda zan tafi da raynwata?
Kai ka haife ni ko ni na liaife ka eус?
Ya kan ce, "Ke сe".
Та се, "То Kyale ni in yi yanda nake so, ba ma:
takura wa rayuwala".
To hakan ya sa ta gwammace ta Kulla kayania la
yi tsadarta son ranta.
Ta jawo radiye ta kunna tana saurarer BRC,
gabadaya ba ya jin dadin baccin, ga shi a lakure yana
jinsa kwance saman sumunti don tabarmar ba ta da
maraba da ta simintin, duk ta lashe ta ciccire, ba ko
shimfida bare filo. Haka nan ta baro shi daga kan gadon
matarsa yana bacei mai dadi ia kawo shi nan, inda sanyi
zai kama shi, ga kadagaggiyar radiyo yar kullum ta
kunna ta kure sauti.
Ya juya, ya sake juyawa sam ba dadi, ya tashi
zaune ya dube ta, ya ce, "Don Allak ki kache radiyon
nan, ban ga me ki ke sauraro da ita ba tun asuba
Ta dago tana harararsa, ta ce, "Na Ki na kash
die dan bakin ciki, kar na ji abin da Lamya ta ke ciki
ko?"
Ya ce, "Da man ba ki daina ji gabadaya ba,
yanzu tanda safiya ce sai ki dinga ragewa daidai
kunnanki kar ki shiga hakkin mutane, kin kawe ni aan
kin kwaniar a saman siminti ba shimfida, seanan kin
Kure sauti a saman kaina, ta ya ya ki ke son aa vi bacei
ko na kuta kan na tashi na fita nema?"
4
از
1
WAVE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta ee. "Kai aa ki din, don Aliah in ka dau
koma zaure ka kwanta, haba".
Yana kallonta ya ce, "To me ye amfanin na
kwanta zauren alhalin ina da daki?"
Ta yi masa banza tana kirga sigarin da ta kulla.
Ganin ba za ta ba shi amsa ba, ya sa ya koma ya kwanta
cikin tausayin kansa.
Ilai dai radiyon na aiki har ta makota ana jiya
Kararta, haushi da takaici suka cika masa rai. Mikea ya
yi ya fice fuu! Ta bi shi da kira, "Ina za ka kai?"
Sam bai saurare ta ba, shigewa dakinsa ya yi da
sauri, har da sa ma kofar sakata. Ta mike da sauri har
zani na faduwa, tana zagi, "Kwabrin babanks, yau ga
dan iskan yaro, kana ina?
Ta fita ta tsaya bakin kofar tana buga masa, ranta
bace, "Sulaimanu! Sulaimanu!!"
Ya yi shiru yana jinta. Daidai farkawar Nafisa ta
ganshi kwaace, ga Inna na Kwala masa kira. Ranta bасе
ta ce, "Lafiya, me ya faru?"
Ya sa yatsansa a bakinta, "Shisssh!" Alamar ta yi
shiru.
Ta yi shirun tana kallonsa, tana kallon kofar Ya
rada mata, "Ta bana ni bacci ne shi ya sa na gudo"
Ta yi jim, sanman ta ce, "Me ya sa haka pon
Allah ka fi son ta dinga zaginka da na Babanka? Ina
n hakan, ba gwanda ka mata abin da ta ke se ba
Yace, "Na yaji Nafisa, bakurina ya kare wallahí,
e za ta bar ni na huts, na sake da matata?
42
WAYE ANGON?-3 Maryam jafar Kaduna
Kullem ina takure duk fa don ta ga ina mizia biyayya iie.
amma ke kin san ana shiga hakfi, a lauye mana
rayuwarmu".
shiri.
Za ta yi magana zagin Iena ya dakatar da ita ba
"Wallahi Sulaimana ida ba ka fito ba in na
shigo sai na karya maka Kala, dan iskan yaro. Ni
abokiyar wasarka ce har ina zaene ka fito in zo ina
niaka magana ka share ni, dan abanka za ka fito ke sai
na karya kofar na shigo?"
Suka yi tsuru suna sauraronta, ta ci gaba,
"Sulaimanu kana ina, za ka fito ko kuwa?"
Ya yi dai shiru.
"Na rantse da Allah ko ka fito ko in tsine maka,
kuma sai ka biya ni nonon da na ba ka tunda ubanka ba
biyana ya yi ba, in tsine maka gabadaya ka shiga duniya
a lalatacce".
Idanuwan Nafisa suka fito, ta tsorata ainun,
kwalla ta ciko idonta, ta ce, "Sulaiman ka rufa mana
asiri don Allah ka fita din ka mata abin da ta ke so, na
san inna wallahi za ta iya fiy. ma da abin da ta fada
Ya juya kafadarsa yana cewa, "Ta dade ba ta yi
ba, ba za ta kama ni ba don ban da laifi ko a wajen
Ailah
Ita kuwa tana tsaye tana kara kuluwa, "Kina a
ke shegiya, mayatacciya duk ke ce makircinki nе. 1о
wallahi karyarki ki raba ni da ſana, müghn abinki kanki
zai koma ki fada wa bokanki aass wasa ne aikinss, he
zai ci ba in dai a kaiua ne ba ieda zai je, sai na keryа
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
asınasa. Kuna ki taso ki bude kofar nan, ko kuwa
yanzu-yanzu ki bar gidan nan har abada, haramiyarki,
yar banza diyar mayatattu kin nace a gidan dana za ki
taso ki bude ko sai na tarasshe ki, iye?"
Ranta ya gama baci da maganganunta, hawaye
suka fara zubowa, tausayin kanta ya kamata, wai me ya
sa ba za ta yi zuciya da gidan nan ba da kuillum sai an
goranta mata a'halin ba ta da kwai daya a cikinsa, me ye
abin nacewar? Wahalar gidansu ba za ta fi ta nan gidan
ba kuwa?
Ta dago murya, "Kina ina ne munafuka, tsafiatta
duk zannuwanki a kode, kafa duk kaushi saboda bin
bokaye, za ki bude ko sai na bude da kaina?"
Ta dubi tafin kafarta da aka kira da kaushi fes ta
ke, har sulbi ta ke saboda rashin kaushi, amma ana
goranta mata duk don ta wulakantata, ina ta ke zuwa,
wane bokan ta taba ma zuwa gurinsa a rayuwarta? Ta
share hawayen tare da mikewa ta nufi kofar, tabbas
budewar ita ce mafi alkhairi gare ta ko, ta huta da
maganganunta. Tana shirin budewa ya ce, "Kar ki bude
Kofar nan".
Ta ja ta yi tsaye cak! Ta ce, "A'a Sulaiman, Inna
fa ta hau sama, ba ka jin irin zagin da ta ke mana? Mene
ne fa'idar zamanmu tare alhalin tana waje tana tsine
inana?
Ya ce, "Wallahi idan ki ka bude maia, to ki yi
gaha zuwa gidanku har sai na neme ki".
Taga haka ya koma ya kwanta abinsa. Ta ja
sas tare da date kai, jikinta ya yi sanyi, la rasa me za ta
44
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
yi. Daga can waje Inna kuma ta fa dage ia kasa ta tsare.
har tana rantse-ranise, "Wallahi, wallahi idan har ba ki
bude kefar pan ba sai na tsine wa mijin naki da ki ke
zamansa, kona in sa ya miki saki uku, shegiyи,
makwakwaciya, mara zuciya, 'yar matsiyata, kin bude
ko kuwa?"
Wasu hawaye masu dumi suka zubo a kumatunta
ta jingina ga bango ta dube shi, ta ce, "Kana jiu fa abin
da ta ke cewa Sulaiman, don me za ka hana ni??"
Ya tashi-zaune ya fuskance ta, ya ce, "Ni fa ban
hana ki ba, ni kuma ba zan bude ba. Na gaji da takurarta,
ya zama dole in yi maganinta yau, ke ma ina shiga
hakkinki idan na ci gaba da mata biyayya ba za ta bari
ba za mu danwama cikin takurarta da rashin more
rayuwamou daga yau ba za ia kuma ba, in kin taimaka
min kenan idan kuma ba za ki iya ba ga kofar nan bude,
amma ki yi gaba zuwa gidanku, don ke da ma na dage,
don haka zabi ya rage naki".
Daga haka ya koma ya yi kwanciyarsa
Ta ce, "Oh ai Nafce, me zan yi? Wacce za ta
fisshe ni?"
GIDAN BABAN MABARUKA
Tun lokacin da Inna Binto ta dawo gidan ba adin
da ya sauya daga zamansu, suna nan dai kullum cikin
fadansu na sabo, yaransu na kallonsu na dariya ba s2
45
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
awa uku suna a shirye, ke an daidaita yanzu an Sabe,
musamman kan son kudinsa, aikin kenan kullum.
Tana tsakar gida tana hidimar alalarta ta safe,
tana yi !ana cizgar fada duk a kansa dai ne.
Ya fito daga faki yana doguwar namma da mika,
ya dube ta, ya ce, "Dan kai min ruwa bandaki in yi
wanka ko na samu karfin jikina, ban jin dadinsa".
Ta dago ta kalle shi ta watsar, tare da jan tsaki ta
ci gaba da wanke gwangwanayen alalen, har ya juya jin
ba ta amsa ba ne ya sa ya juyo ya ce, "Da ke fa nake ko
ba ki ji ba ne?"
Ta dago tana kallonsa, "Ka ji ka da wata magana,
ai na ji abin wani banbarakwai wai namiji da suna
Hajara. Sai ka ee sabonka ne yin wankan har kana wani
fafa cikin iko sai ka ce inn cikakken namijin nan,
wankan da ba kuilunı ka ke yinsa ba sai ka ga dama, to
an ki a kai ruwan, ka je ka yi da kanka, in ka matsu ni
dai ka ga aiki nake wanda ya fi min wannan?. Ta ci gaba
da abin da ta ke cikin ko'inkula.
Ya ja ya tsaya tare da rike kugu ya ce, "Wai ke
Binto in tambaye ki, ke ki ke aurena ko ni nake aurenki?
Ban isa ba na sa ki aiki ki tnin ba?"
Ta ce, "Ai ba irin namijin da a ke a ba ne kai,
masu kwandala cike da aljihu kai ko nan ashirin na
koken yaran nan gagararka yake, bare a zo maganar
kosai, haka ka ke fankan fayau! Ba ka iya tsinana nin
komai, don haka wallaki ba zan Kare a hidimta maka ba,
tunda ba tsiyar da zan karu da ita a jikinka".
46
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kadna
Yai tsai yana kallonta, abin nata ma cı gaba yake.
Ya nisa ya ce. "Allah shrya ki, ki dawo hanya
madaidaiciya tun kan ki mutu a haka, hukuncin Aliah da
azabarSa ta hau kanki, don wallahi in ki ka mutu kina
saba min na rantse ba żan yafe miki ba ko da karshenki
wuta ne tunda ba ki rangwaeta min ba, aradu ni ma ba
zan rangwanta miki ba, sai dai na daga za ki shiga, to na
ga yanda za a yi".
Tamkar ya fesa mata wuta, ta mike jikinta na
barin masifa, "Don Allah ka dauke ni tun yanzu ka jefa
wuta, kada ka jira na mutu din, kar ka sake ka rangwanta
min don Allah, yo akwai ma wanda zai fara shiga wutar
in ba kai ba? Kai ne gaba, kai za ka mana jagora wane
hakki nawa ka sauke min? Akwai inda aka ce miji kar
va ba iyalinsa abinci?"
Ya ce, "Babu inda a ka ce, amma Aliah ma ya
sani ba ni da shi ne".
Ta dauka, "Ba ka da hujja, rashin zuciyar nema
ne da lalaci, in dai ka fita ai ka samu ko kwasar kashi ka
yi mana".
Ya ce, "Na ki na yi kwasar kashin, ai kina sana'a
in kin yi kuma ba ni da shi". Ya wuce.
Ta dago murya, "Wallahi ba ka isa ba, sai ka ba
mu na koko, ai ba ni kadai na haifi 'ya'yan ba".
Ya juyo, "Na ce ba ni da shi, dole ne ko zan
saida kaina ne in ba ku ku ci, yar gidan mayunwata?"
Ta ce, "in har za a siye ka da bakin talauciaka ie
ka saida kan naka, kudin san fiye min kai da na kutz
wallahi".
47
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ya ce, "Hutu bai ganki ba, inda ki ke takamar
zuwa ba masauki za a ba ki ba, ke tsiyar taki ko gidanku
ba ki da wajen zama, ni ne dai dole, sai ni din".
Abu fa ya ki karewa, da ta yanko masa zai yanko
mata. Dukkansu ba hakuri shi ba girma da rike
mutuncinsa, haka ita kuma ga raini da shegen kwadayi.
Dole dai sai shi ya dibi ruwan ya kai, ya yi wankan duk
tana kallonsa tana 'yan maganganu, tana hadawa da
zage-zage duk dai fadanta a kan naira ne.
Ya fito abinsa fes, har yana goge takalma da suka
fara sidewa. Ta bi shi da kallo, ta ce, "Wai me ka ke nufi
ban gane ba wankan nan na safe, sannan haka za ka fita
ba za ka sallami yara ba, ga su nan tsuru kowa na
kallonka ba su sa wa cikinsu komai ba?"
Ya juyo yana kallonsu daidai, duk sun kwalalo
masa ido. Ya ja tsaki tare da rike kugu ya dauke kai,
"Wai ina ma amfanin tara yara da yawa har haka na
abincinsu ma ya gagara, mace ta zauna ta dinga yo
kashin 'ya'ya kamar akuya, ina amfanin hakan?c
Sarai ta gano da ita yake, ta maido masa, "Oho
dai, da man ai-42 taba samun wata macen da ta hailu itä
kadai ba tare da taimakon mijin ba".
Ya san amsa ta ba shi, baj ce komai ba ya dubi
yaran ya ce, "Kai a ba ku alale ta sha biyar-biyar kan na
dawo, kuna na ga wacce za ta kara min baihuwa a
gida".Ya wuce.
Ta dago murya, "To ai ba ka ba da kudin ba, wa
ka ajiye ya ba su. Akuya ko wa?"
48
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ganin ya kafe ta da idanunsa ya sa ta dauke
kanta tana cewa can makoshi, "Ya aka yi ne ka shigo
min daki?"
Ya yi murmushi yana kokarin zama kan drower,
ya cc, "Kada ki yi zargin wani abu ya kawo ni dakinki,
kawai na zo ne in gaishe ki, in ji ya ki ka kwana?"
Ta yi shiru tana ci gaba da buga game dinta, har
yanzu fuskarta ba fara'a, ba ta jin za ta iya ba shi amsar
tambayarsa. Ya sosa kai yana kallonta, ya ce, "Na sani
da man ba za ki ban amsa ba, saboda yanda nake jiya
haka nake yau, ban canza ba, ban san kuma gobe ba
wane matsayi nake, ko zan canza ne na koma masoyi, ko
ko ina nan a makiyin?" Ya yi shiru yana kallonta ko za
ta ba shi amsa.
Cikin nauyin baki da gajiya da shi, ta ce, "Don
Allah ka kyale ni na huta, bana son yawan magana, ban
ga amfanin ai ta nanata magana daya ba, kar ka san
matsayinka gurina. To me ye na son nanatawa, na fada
maka ya fi a kirga, ban sonka! Wallahi ban sonka, kuma
har abada ba zan taba sonka ba na rantse da Allah, ka
shafa min lafi,a, ka kyale ni da ji da takzicin zamana a
gidanka katin wa'adin kwanikan da muka yi da kai su
cika in kama gabana".
A zuciyarsa maganarta ta masa zafi matuka, da
radadi duk da ba yau ta fara furta masa ba, amma a
kullum sabbi ne gurinsa, duk sanda za ta fada yana jin
dacinsu. A fuska ya yi murnmushi, idanunsa suka dan
canza, ya dube ta a sanyaye, ya ce, "Shi kenan, ki yi
hakuri ina damunki, amma ki taya ni addu'a Allah ya
51
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
cire min sonki a raina ko don na kyale ki ki huta,
vuciyarki ta bar miki zafi zamanki da ki ke a gidana.
Idan ki ka yi baka kin taimake ni, kin taimaki kanki don
Allah Mabaruka?"
Ta kalle shi tsawon sakwanni ta watsar, ta maida
יי
kanta awayar, ta ce a dakile, "Na ji shi kenan
Ya yi murmushi yana sake kallonta, musamman
yanayin da ta amsa sai ya burge shi, ya cc, "Na gode".
Tare da mikewa, har ya yi gaba ya dan dawo ya ce,
"idan zaman ke kadai ya ishe ki kina iya nemana ta
waya ko da ina ofis zan zo in dan fita da ke ki sha iska.
Ina fatan hakan zai sa ki ji dadi ko?
Kai tsaye ta ce, "A'a ba na bukata, ka yi
zamanka". Ba tare da tana kallonsa ba.
Bai ce komai ba ya wuce yana cewa, "Any way
in kina bukatar wani abu let me know'.
Ya buda kofar. Kafin ya fita ta ce, "Ka nemo
min mai aiki wacce za ta dinga taya ni kwana, ba zan iya
kwanciya ni kadai ba”.
Ya juya yana kallonta tsaf, har-tana tunanin zai
kawo mai taza ta kwana kenan alhalin ga shi yana
bukatarta kusa da shi. Ya yi murmushi tare da cewa,
"Mabaruka kenan, a kullum ke yarinya ce, kuruciya na
tare da ke har yanzu, hakan ya sa wani lokaci bana jin
zafin wani abu in ki ka min, don na san akwai ranar da
za ki bari. A tsarina bana son mai aiki ko da da girki ne
bare wacce za ku dinga kwana tare, ina gani aikina ne
wannan, idan ba za ki iya ba ban miki iyaka ba, ga
dakina can in dare ya yi ki dinga shiga kina kwanciya a
52
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduns
Ya ce, "Oho, ni dai na san na aje sarai a gidan
Ya wuce abinsa.
Yana jiyota tana la bambamin baia'i, ya share ta,
shi kanshi yunwar da ke azalzalarsa ba za ta barshi ya je
inda yake da niyya ba, zai ta halamniya ne gwanda ko
alalen Allah ya isa ne ya ci, ta liye masa. Don haka ya
Isaya zauren har wani yaro ya fito da alala hannunsa, уa
siye wa Innarsa. Ya kira shi, "Kai Auwalu ne ko Musa
Yaron ya ce, "A'a Auwalu nc, Musa ya ta!
makarantar allo".
Ya washe baki, duk don yai wa yaron waya
"Allah sarki haka ne, Babanku Haruna ai yana kokari
kam, ka ga sauri nake ba na son bata lokaci in na shiga
gida dan ban alalarka in ci ko guda biyu ne, allabasshi
sai ka koma a zubo maka wata, ka ce in ji ni a sa maka
tawa יי
Yaro yana rawar jiki ya miko masa, alalan shida
ce, sai da ya cinye ta tas ya lasbe hannu, ya gaje a suma
ya miko masa, kwanon ya ce, "Yauwa Auwalili, ga shi
ka ce a zubo maka tawa a