"Sai Innarmu, wannan baka ne
."kam יי
Ta yo wankanta fes bayan ta yi sallah. kamar
yanda ta ke ita dai tana son gayu ko ba inda za ta je za ta
yi kwalliya ta dauko kayan da ta fi so ta sa, ta yi
kwalliya sosai, don haka ko a nan ma haka ne, ta fsto
abinta fes.
85
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Abin da ta gani ne ya sa ta ja ta yi tsaye idonta a
waje ta rike kugu ta lada daidai yanda ita za ta ji, "Kan
bala'in nan, wa ya ce ka ci min abinci?"
Ta karaso inda suke shi da Baba,. Sun baje
saman kafet da Baban da Imran suna kwasar girki,
kowannensu na santi a cikinsu ban san wanda ya fi wani
ba, shi kam Imran tunda yake bai taba cin irin watuan
girkin ba sai kada kai yake yana jinjina mata, ashe ya
bar gara na tafiya?
Cikin tsananin fushi ta zauna tana hararsa tamkar
za ta shake shi, takaici da bakin cikin ci mata abinci ta
ke kamar ta fasa kuka. Kai ta gagara daurewa, ta tura
masa sako ta wayar da ke kusa da shi.
“Allah ya isa abincina da ka ci".
Ta tura ta ci gaba da satar iddon Baban ta dalla
masa harаrа.
Ko da ya karania murmushi ya yi, da yake shi ma
da hannun yake ci ya biye wa Baban ya cika hannu da
abincin bar yana nuna mata ya sa baki, har da lumshe
idanuwa yana motsa kunne, ya ce, "Umm..."
Takaici ya turnuke ta, ta kauda kaina sake jin
tsanarsa, don me zai ci mata abinci? Ya maido mata da
amsa, "Ba tarbiyyarki ba ce Mabaruka, bau sanki haka
ba. Kada ki sauya kanki, abinci kuma na ci sai dai ki
kwana kina min Allah ya isa".
Ko da ta karanta ta yi wurgi da wayar tana
harararsa. Yana kallonta ya'yi dariya tare da sunkuyar da
kai, shi ko Baba bai san me ake ba, gabadaya ya ba da
baakalinsa kan abincin yana ci tare da lumshe ido.
86
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Tana nan zaune har suka gama cikinsu ta rasa wa
ya fi ba ta haushi, Baban ko ko Imran din? Sam ta ji
abincin ya fita ranta, ba ya ba ta sha'awa duk da yunwar
da ta ke ji ba don komai ba sai don ya ci abincin da
kuwa ta ci abincin da ya ci gwanda ta kwana da yunwa.
Zai tafi? Zai tafi? Shiru! Sam ba ta ga alama ba,
shi ko lmran ya mike kafa yana biye wa Baban yana
canja masa channel, duk fadin duniya duk inda aka nuna
da Turawa yanzu zai cafko maagana, musamman in ya
gansu tsirara. Takaici da haushi suka cika maata rai,
tamkar yana zaune a gidansa. Sam bai yi kama da ya zo
gidan suruki ba.
Sai yamma lis! Sannan yai shirin tafiya bayan ya
sa Mabarukan ta kawo masa dan soyen da ya ci ya tafar
wa da yara. Kamar ta fasa ihun takaici, musamman duk
a gaban Imran din a ke. Haka nan dai ta zubo masa a
leda ta kawo masa, hade da dubu uku tana cewa, "Ga shi
Baba ka dan rike kwana biyu kafin na zo".
Ya hau washe baki yana kirga kudin ya ce, "Kai
Allah miki albarka rabon da na rike irin wadannan tun
ki... nan sai yau, lallai yau akwai cin balangu a nono".
Ta kauda kanta gefe, tana kumburin haushinsa.
Imran ya yi dariya tare da ciro keyn motar, ya
wuce gaba yana cewa, "Ina waje Baba".
Bayan fitarsa ta dube shi tamkar za ta yi kuka, ta
ce, "Me ya sa haka Baba? Me ya sa ka ba ni kunya, ka
riga ka gama zubar min da mutunci aa gabansa Baba,
surukinka fa ne?"
87
VAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
out
SV
Ya kalle ta da kyau yana gyara tsayuwa, уa сe,
To to lyar masu bakin ciki an sha nono. Me na yi da
ki ke Kokarin mın sharci? Gaishe ku fa na zo yi'
Ta ce, "Ba wata gaisuwa, nan ba ita ta kawo ka
ba, taka ta kawo ka. Ni ba za ka bari na zo na gaishe ka
ha sai kawai ka wanko kafa ka taho, ka zo ma din kana
da kunyata ni ka zubar da girmanka a idonsa? Wallahi na
san ya riga ya gama raina ka
Ya ciro kudin cikin fushi yana mik mata, hade
da ledar, "Ke amshi kayanki uwar 'yan tsogumi, tun kan
ki tara min jama'a. da ma 'yan kudin da ki ka ba ni ki ke
wa, to amshi ban so
Ta dube shi cikin kunar rai, ta
KSMO
ce, "Amma ka san KULsRI
a yau na saba ba ka ba ko? In su naake wa tuni me ya
sa ban maka ba tun ina gida? Ina son ka fahimce ni, ni
kaa kiyaye gaba kar ka sake, masa fuska, sama-sama
kana nuna kai ba ka damu da shi ba bare abin aljihunsa,
HASWK on nsDds don kar ya raina mu
Ya ce, "Na ki, na, yi din ba ni da kwandala ki
ZIL RD E BOST xim delШA sani fadin rai talaka ina ya ga ji da kai?"
Ganin ba zai fahimce ta ba sam, ya sa ta ce,Shi 023
ke nan ka je to in da matsala ka dinga kirana ba LG AIAR VB
ba
!uISE
sai ka vo
ba, zan zo ni ka ji Baba?"
Ya kalle ta tsawon dakiku ya ja tsaki kawar tare
da wucewa yana cewa, "Gabadaya kin kwaso mugun
halin uwarki na bakin ciki da hassada. Sam ba ta son ta
ga na ci gaba, ke ma haka ne. Allah shirya ku
Ta bivo shi da sauri tana ba shi haku kr ya
karasa gurin Imran din da yake jiransa yana surutan. Bai
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
saurare ta ba ya wuce abinsa, har bakin motar. Da zuwa
ya kama washe masa baki, yana cewa, "Sannu dan nan,
kana ta jira ko?"
Ya yi murmushi kawai, ya ce, "Ba komai Baba,
shiga mu je.
Ya kama motar ya shiga yana cewa, "Ta tsayar
da ni tana gaya min maganganu na bakin ciki. Sam ba ta
son in dan ci arziki halin uwarta ta gado".
Ta dafe kai tare da dade kunnuwa ta wuce ciki da
sauri, har tana runtse ido duk don takaicin Bbanta, ta gaji
da surutansa na dattijon banza. Allah kadai ya san inda
surutansa za su tsaya kan su sauka.
Imran yana kallonta, sam ya ji ba dadi a ransa
ganin damuwarta karara. Ya yi shiru, sam ya daina jin
me Baban yake cewa. A haka ya ja motar suka fice cikin
mutuwar jiki da tunanin Mabarukansa.
Tun kan su isa yake cewa, ya tsaya da shi ta
kasuwa ya shiga ya yo cefane, tunda ya samu kudi kar
ya shiga gidan haka nan ta kusan cinye shi saboda bala'i.
Bai musa ba ya biya ta kasuwar ya sauke shi, ya sa
hanad inda yake ajiyar kudi a motar ya ciro adi, 'yan
dubu sabbi kar! Ba ko lankwasa har guda goma ya mika
wa Baban yana cewa, "Ga shi Baba ba yawa saboda yau
weekend, kuma ba na aje kudi da yawa gida, ka dan rike
tukunna".
Ku zo ku ga buda baki wajen fara'a, ya dưbi
kudin ya dube shi, ya ce, "Duk haka yaro, ba su yi yawa
ba?"
Ya ce, "Ba komai Bab ka rike dai",
89
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Yana Kirgawa ya ce, "To madallah, Allah yai
maka albarka dan nan, wannan ai sai jari, yau ba sai
gobe ba".
Ya cc, "A'a Baba, ba da haka na ba ka ba, na ba
ka ne don ka yi cefane, zan san me zan yi na sana'ar
naka, kar ka sai komai".
Har yana feso ruwan goro, "To... to... to shi
kenan, Allah sa albarka, na gode ka ji ko?"
Ya ce, "Ba komai".
Ya murza key, shi kuma ya fita yana kara
lankwashe kudi aljihu yana washe baki, ya shiga cikin
kasuwa, shi kuma ya ja motarsa ya koma gida, dole ne
va je ya lallashi 'yar matarsa, sam bai ji dadin ganinta
cikin damuwa ba tamkar za ta yi kuka. Duk jikinsa ya yi
sanyi, da kyar ya isa gidan, hankalinsa na kanta.
NAFEESA FA?
Tunda ta shiga adaidaita sahun ta ke share
hawaye ba sauti, tana gogewa da hijabinta babban bakin
cikinta da za ta koma gidansu gurin matar Babanta, ko
kan ba ta jin dadinta, dama-dama ma id Babanta
yana gida.
A haka dai har ta isa, ta yi sa'a kam Baban na
gari ya ga tsayuwarta ta fito bayan ta biya mai motan
kudinsa, ta dauko bakaken kaya ta tsugunna kanta kasa
cikin ladabinta da kunyarta tana boye idonta ta gaishe
shi.
Dattijon kirki mai kyawun zuciya da fahinta ya
dube ta da kyau, bayan ya amsa gaisuwar ya се, "Mai
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
sunan Inna lafiya dai ko? (kasancewar sunan mamansa
ne da ita)"
Ta dan dago tare da kakalo murmushin dole iya
fuska ta ce, "Alhamdu lillah Baba".
Ya ci gaba da kallonta yana son fahimtarta, ya
santa sarai, ya san halinta ba za ta taba fadin sharri ba,
ko inasifa a bakinta ko da ita ce tare da ita ta kan saya
cikin ladabi ba tare da ta fade ta ba yanda hankalin
wanda ta ke fada masa ya tashi ba. Cikin hikima ta ke
fada, ya ce, "To shi kenan, shiga ciki ga ni nan zuwa kin
ji ko?"
Ta сe, "To Baba sai ka shigo".
Ta mike a sanyaye ta shige da sallama ta shiga.
Baba matar Babanta tana zaune tsakar gida ciki rumfa
tana kasawa yara kayan miya, ta bi ta da kallo har ta
karaso ta samu 'yar kujerar tsugunno ta zauna tana
gaishe ta.
Kan ta amsa ta ce, "Ashe kwa ke ce din, yara ke
ce miu sun ganki kwar gida ashe kwa, lafiya dai ko?"
Ta dan yi murmushi ta ce, "Lafiya lau Baba, na
zo gidan ne dai".
Та се, "То kin zo gaishe mu ke nan, yau an tuno
mu?"
Ta yi murmushi kawai.
Sai can Baban ya shigo hankalinsa tuni na kanta,
ya shiga dakinsa yana cewa, "Zo mai sunan Inna".
Ta nike cikin nutsuwa tana cewa, "Baba ina
zuwa".
91
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta shige dakin Baban, ta zauna a kan buzun da
yake shimfide tsakar dakin kamar kullum. Ya dube ta
shi ma yana daga zaunen, ya ce, "Fada min Innata, na
san-akwai abin da ya faru haka nan ba ki zuwa sai kin
sanar da ni za ki zo, kuma da ganinki na san akwai
damuwa. Fada min mene ne, zan fahimce ki kamar
yanda na saba miki"
Kalaman mahaifinta sun sa ta dan ji sanyi, da
man ta sani za ta samu sauki daga gurinsa, in kowa ya
tsane ta shi yana sonta, a kullum yana yabawa da ita,
kullum alkhairi yake fada gare ta da sa mata albarka.
Wasu 'yan siraran hawaye suka zubo, ta goge
cikin nutsuwa da kwantar da hankali ta ce, "Komai yana
da iyaka Baba, komai yana da lokaci duk abin da ya
samu bawa da sanin Ubangiji, shi ne ya sa shi ciki kuma
Shi zai masa magani duk ya jarabta ta zo min Baba na
dauke ta ba na fushi da yin Allah, gurinShi zan jira
sakamako”.
Ya jinjina kai alamar gamsuwa ya се, "Hаka ne,
amma me ya faru?"
Ta ce, "Aurena da Sulaiman ne ya-zo karshe. Iya
inda Allah ya dibar mana kenan ya cika, ya sauwake
min auransa".
Baban ya yi shiru yana tunani, can ya nisa ya
dube ta, ya ce, "Masha Allah, na gamsu hakan da ma
Allah ya rubuta, Ubangiji Allah yai muku zabin da ya fi
alkhairi da ke da shi, Ya sa hakan shi ne mafi alkhairi
gare ku".
Ta ce, "Amin Baba".
2
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ya ce, "To amma nawa ya miki, ko gabadaya
ne?"
Та се, "А;a daya ne dai".
Ya ce, "To idan akwai ci gaban zama tsakaninku
in alkhairi ne Allah ya daidaita ku, ku ci gaba da
auranku".
Ta ce, "Amin".
Ya ce, "Allah zaba abin da ya fi alkhairi, amma
me ye sanadin kin masa wani abu ne?"
Тa сe, "A'a Baba, lafiya muka rabu da shi ba
fada bare wulakanci, kawai dai matsalar Innarsa ne, ita
ce ta tilasta masa har dai ya yi sakin ba da son ransa
ba..."
Ta ba shi labarin duk abin da ya faru. Ya gamsu
sosai, ya ce, "To Allah ya sauwake, Allah ya shirya mu
da ita gabadaya".
Ta ce, "Amin".
Sun dan taba hira yana kwantar mata da hankali
da mata nasihohi, har ta ji sanyi a ranta sosai ta bar wa
Allah komai. Ya ba ta shawarar ta gaya wa Allah ya
zaSa mata mafi alkhairi. Ta dauki shawarwausa.
Ya kara da cewa, "Ga daki can wanda yake kulle
sai shirgin kaya, kina iya ciro kayan ki share ki zo ga
katifa nan ki dauka kafin mu ga abin da Allah zai yi, har
ki gama idda".
Та се, "Тo Baba, amma ka bar katifarka zan dai
dauki tabarma".
Ya ce, "A'a, katifuna biyu, ga wata can a jingine
shekaran jiya Aminu ya kawo min ita sabuwa dal! Har
93
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
da bargo wai ya ga ina kwanciya waje kan tabarma, da
yake in dakin ya yi zafi na kan sa tabarma da filo in dan
kwanta tsakar gida, sai na bar katifar a daki".
Ta сe, "To ka ga sai ka yi amfani da ita a wajen
zan dai dauki bargon".
Ya ce, "A'a, bana son musu, na ce dai ki dauka
duk kuma abin da ki ke bukata ki sanar min, insha
Allahu ba zai gagara ba, ga babarku nan a dai ci gaba da
hakuri da ita kamar yanda aka saba zama da ita, sai
hakuri na san kia san ta kanta, ki lallabata har ku rabu
2b lafiya".
Tа сe, "To Baba, na gode, zan kiyayeс".
Ya ce, "Masha Allah, Allah miki albarkaa
rayuwarki, Allah ya yi miki zabi mafi alkhairi gare ki"
Ta ji dadi sosai, ta ce, "Amin Baba, Allah kara
lafiya".
Ya ce, "Amin, amin. Je ki abinki ki huta kada ki
damu, ki yi ta addu'a in rabon za ki koma dakinki yau
ko gobe sai ki ga kin koma abinki, ki bar wa Allah dai"
Та се, "Тo Baba". Tare da mikewa.
GIDAN INNA
Tun bayan fitarta Sameerar da Innar suka shiga
dakin suka hau mata bincike, wai su karya asirin da ta
aje. Duk suka birkice mata faki ba su ga wani abu da ya
yi kama da sibiri ba. Hakazalika kwandala ba su ci karo
da ita ba, ina ma ta bari ya ba ta 'yan kudi idonta na
kansu duk ya suka motsa.
94
WAYE ANGON?-3 Maryam jafar Kaduna
A haka ya cimmasu a dakin, da ma ya shi raisd d
bace ya dawo, kuma ya tarar da wani bacin rai. Ya yi
tsayc yana kallónsu cikin kunar rai, duk ba su san yana
kallonsu ba, can Samirar ta fago. Ganin kallon da yake
mata ya sa ta tsorata ainun, duk ta kama kanta ta dan
yafito Inna da ke durkushe tana lalubo.
Suka dago suka yi ido biyu da shi, Innar ta dube
shi ta ce, "Dukanmu ża ka yi ne da ka ke harararmu?"
Ya ce, "Me zai sa in dake ku tunda abin da ku ke
daidai ne? Ya dace ku shigo mata daki kuna todid
bincike".
Ta harare shi son ranta, ta ce, "Ni na kwafde ka,
ni za ka gaya wa magana an shigo din".
Ya ce, "Ni ma ban hana ku ba, ku ci gaba in kun
gama na shigo in dauki abin da ya kawo ni.
Ya ja baya tare da samun turmi da ke gefe ya
zauna tare da harde hannuwa saman kirji yana jin wani
Kuna da radadi a ransa.
Ta kalli Samirar ta ce, "Ke zo mu bar masa daki
tun kan mu ji saukar duka".
Suka fito ta dube shi, ta ce, "Kumaa yanda za a
yi da gidana a bar min tarkacen can in na shiga a ga
laifina, don haka ina bukatar filin dakina, maza ka sa a
kwashe tarkacan can na tsafi, duk an bi an tsafe mana
gida da mugun abu".
"To". Kawai ya ce ba tare da ya musa ba. A
ganinshi doguwar maganar ba ta da amfani, har abada ba
za ta taba sauraransa ba. Ta hana masa farin ciki da
walwala, duk ta bi ta takura wa rayuwarsa. A yau yanda
95
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
yake ji da ba uwarsa ba ce, da ya rabu da ita har abada.
Ba ya jin zai kara wani auren a rayuwarsa, gwanda ya
mutu a haka, Allah ya ga zuciyarsa.
Ta wuce tana kara cizgar fadanta na ba gaira ba
dalili, ya mike ya shige dakin ya kwantar da katifar da
suka dage suna duba karkashin gadon. Ya kwanta bayan
ya datso kofar.
A kasuwar nan ya yi siyayya sosai, tun daga
shinkafa, taliya, wake, masara, maggi, mangyada har da
dan kwala-dankwalan kajinshi guda uku da cefane ya
ciko ledoji dam da kaya. Adaidaita sayu ya yo shata har
kofar gida, aka gama sauke masa ya biya ya dauko ya
fara shigowa da su jikinsa na rawa, ya rangado sallama.
Tana daki ta jiyo muryarsa, tun kan ta fiio ta hau
bala'i, "Wallahi yau ba mai raba ni da kai sai Allah,
kudina sai ka biya ni kwada..."
Abin da ta gani ne ya hana ta magana, ta yi cak!
Kalmar ta makale. Ledoji ta gani hannunsa ya tsugunna
ya aje, kajin suka leko bankararru, ya juya yana cewa,
Maza zo aiki ya same ki": Ya fice.
Ta karaso da sauri tana dubawa jiki ya yi sanyi,
ya sake shigowa da himilin doya a daure ya dire, ya sake
fita ya kinkimo karamin buhun shinkafa ya aje, duk tana
tsugunne rungume da hannuwa baki sake da kyar ta iya
cewa, "Baban Mabaruka daga ina wadannan garar, ka
samu kudi ne?"
Ya yi dariya ya fice yana cewa, "Tukunna dai,
bari in karasa shigowa da su". Ya fice.
96
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ya shigo da wasu ledojin ya aje, ta bi shi da
kallo, ta ce, "Au har yanzu ba su kare ba?"
Ya cc, "Ina?" Yana juyawa.
Sai da ya kwaso su gabadaya tas, sannan ya tsaya
rike da kugu yana zaro idanuwa, idonsa kan kayan ya
ce, "Ho kadi da wuyar samu, amma ba wuyar kashewa.
in na gaya nuki kudin kayan nan za ki sha mamaki".
Ta buda baki cikin mamaki, "Haba dai?"
Ya se, "Sosai, dan samo min ruwa in sha na ci
maski yau, sai kora ruwa nake".
Ta mike da azana har tana tuntube tana cewa,
"Ina ka je ne ka ciyo har ka samo kudi?"
Ya ce, "Kawo min dai ruwan".
Ta debo a tukunya (randa) ta kawe tana cewa,
"Kuma ba sanyi, amma bari in leka in samo yaro ya
amso maka ko na leiar nan mai sanyi, ga biyar nan a
zanina.
Ya yi dariya ya ce, "Ho su Binto manya, an ga
ledoji an san bayaniu kwandala ne yau ni ake siyo wa
ruwan leda, na randa ma watarana da ya ake ba ni?"
Ta wuce tana cewa, "Ba haka b ne Baban
Mabaruka, na ga ka shawo rana, duk ka gaji".
Ya ce, "Yau ba, sau nawa na shawo ranar ba a ba
ni ruwan ba in na ce ki kawo sai ki ce ban san hanya ba
ne, ko ban da hannu?"
Ta fice tana cewa, "Ina dai zuwa".
Karara haka ta siyo ruwan ba tama jira yaro ya
siyo ba, ya amsa yana cewa, "Ai ni yau na roba na sha
karara mai tsafta"
97
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta zauna kasan siminti gabar ledojin, ta се,
"Wai ina ka je haka ne?"
Ya ce, "Hum ke dai bari, haihuwa mai rana.
Gidan Mabaruka mana, ai can na wuni kin ga gida? Gida
duk tangaram kana kallon kanka a jiki".
Ta rike baki, "Allah Baban Mabaru?"
Ya ce, "Abinci kuwa hum uhum ba a magana,
nama zako-zako har suna dago hannu ka raba ina sha".
Ta ce, "Wai, lallai yau ka shana, in ce su suka ba
ka kudi ka yo mana cefane?"
Ya ce, "Kudade kai in kin ji kudi 'yan kadan ne,
dubu goma mijin ya ba ni, ita kuma dubu uku har da
nama ma na ye guzuri, kin ga ledarshi can".
Ta hau lalube tana cewa, "Wai wa wai wai lallai
yau za mu ci dadi, 'yar Mabaruka daman ba dai kyauta
ba. Na san a rina kam, har dubu goma Malam?"
Ya ce, "Somin tabi ne ma ya ce zai ba ni abin
sana'a, wannan na cefane ne ya ba ni kawai".
Ta ce, "Allah Baban Mabaru?”
Ya ce, "Wallahi, don haka yau dage-dage za ki
ana mu sha ga shinkafa nan da kaji aye su, rabi
kuma a yi farfesu, saura a yi miya".
Ta ce, "Ai kwa yanzu da ma ba mu ci komai ba".
Ya ce, "Ai sai ki tashi yanzu ki yi murhu biyu,
ina ma za ki iya irin wanda na ciyo da shi za ki yi, kai
yarinyar nan 'yar albarka ce, har mamakin yanda ta iya
wannan abincin nake kamar ba hannu yake ba. Shi dai
kam ya more, shi ya sa na san kullum yake gida, ga gida
duk kamshi ko'ina sanyi-sanyi, dumi-dumi. Ga wata
98
WAYE ANGON?-3 Maryam jafar Kaduna
katuwar talabijin a bango, kai! Yau na ga fitsara, mata a
zindir ba kaya jikinsu, ka ga mutane kala-kala, kasashekashe hankalinka kwance abinka. Yarinyar nan ta more
ta bar ni cikin talauci".
Та се, "НHo Malam, ai yau na san za mu sha
labari, don kai ba ka iya gano abin labari ba ka yi shiri,
dadi dai ka sba, mu ma za mu ci shi yanzu Mabaruka
kuma ai ka manta ne, duk randa ta zo in dai tana son cin
tuwo za ta ce in barshi ita za ta yi, ta yo cefanenta duk
makota sai an jiyo kamshi. Ina lura da kai yanda ka ke
sude kwano kana gyada kai, yara ko a hau dambe, ai
zakin hannu ne da ita, ina zan iya wannan girki nata?"
Ya ce, "To ga shi nan dai ki yi dai iya bakin
kokarinki, yau dai na huta da gorinki, kullum bana ba da
kudin cefane bayan kin san ba ni da shi in har ina da shi
zan yi ko da aljihuna kenan, amma sam ba ki hakuri".
Та се, "Нaka ne kuma Baban Mabaruka, in dai
kana da shi kana yi tun kan a roke ka. Ka san mu mata sai
hakuri da mu'.
Ya mike yana cewa, "To ga shi nan dai 'yata ta
fitar da ni kunya yau, tun kan mijinta ya ba ni sana'a. ina
ma zai ba ni daki, wallahi da na tare a gidan kullum in
dinga shan rabar nan, ina asuwaki da cinyar kaza"
Та се, "Кai Malam rage dai, kai yanzu sai ka tare
din?"
Ya juyo yana cewa, "Alkur'an sai na tare".
Га се, "Тab! To ba da ni ba wannan abin kunyar,
Allah kyauta".
Ya wuce yana cewa, "Ba amin ba, sau nawa aka
yi?"
99
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Ban taba ji ba, wallahi kai dai ka tsaya a ba ka sana'ar".
Ya wuce yana ćewa, "Sai ki ta yi, ni na fita"
Та се, "То a dawo lafiya, Allah ba da sa'a"
Ya ce, "Eh tunda kin ga ledoji ba, har dago murya
ki ke".
Ta tsura wa kayan ido, ta ce, "Tabdijan, ai alkur'an
gobe ni ma sai na je, in je in samo nawa rabon. Yaushe zan
zauna? Ai mu Allah ya sauwake mana tunda ya kai
Mabaruka gidan mai naira, don haka kullum ina can,
adashe ma zan shiga".
Da wadannan soki-burutsun nata ta tashi ta
gangama itace.
GIDAN IMRAN
A dakinta ya tarar da ita, gidan ya game da
Kamshin girkinta. Yar Karaınar tukunyarta akai tana
girkawa kanta sabon abinci a kan ta ci wanda ya ci.
Ya shaki kamshin tare da cewa, "Hummm dadi".
Ta dago ta dalla masa harara, ba ta ce komai ba ta
ci gaba da girkinta cike da haushi daa takaici, matar iyaka.
Ya tsuguna gabanta cikin kulawa, ya cc, "viy Angel mene
ne fushin ne har yanzu? Shi fa Baba ya riga ya tafi tuni ma
yana gida".
Ta dago tana kallonsa da idanunta da ke nuna
tsansarsa karara, ta ce, "Wai ina ruwanka da ni ne ka ke
Gamuna? Matsalata ce fa don son Allah ka kyale ni na
huta, wailahi na gaji da ganinka kusa da ni, don Allah".
Ya yı murmushi, ya ce, "Mabaruka kenan, ke tawa
ce haka ni naki ne, don haka mu abu daya ne damuwarki
Σ
100
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
tawa ce, za ta dame ni ba zan so na ganki cikin fushi ba,
zzan damu ni maa kin ga dai matsala duk tamu ce ni da ke,
zama kuma kusa da ke dole ne Mabaruka, saboda kс
matata ce, ni kum mijinki ne. ki yi hakuri da haakan"
Ta kashe wutar taa mike daf, calander laa dauko
masa ta nuna masa, "Ka ga ni yau kwanana nawa gidanka,
ga kuma abin da ya rage min na yarjejeniyar da, muka yi da
kai, don haka ka daina shige min da yawa, don zan barka
ka kuma daina kirana da sunan matarka".
Ya yi jim yana kallonta, can ya nisa ya ce, "Well
haka ne yanda ki ka fada. Amma a tissafinki idan kin duba
ko wataďaya ba ki yi a gidan nan bà bare ki ce kin kusa
barinshi, don haka baa yanu bane ya kamata na fara
ncsanta da ke ba sai lokacin ya у
Ya mike yana kallonta tare da ecwa, "Kin gane?"
Ba ia iya juran kallonsa ba ta, dauke kanta zuwa
gefe, ya ce, "Bari in tafi in ba ki wuri ko kin samu damar
karasa girkinki ki ci zan yi farin ciki da hakar, ba zn so
zamanki da yunwa ba".
Ba ta jin za ta iya amsa masa, a kagare ta Le ya bar
mata daki, ya yi dariya kawai tare da cewa, "Mabaruka
manta.
Ya budc kofar ya fice gabadaya ma ya bar gidan.
mota ya dauka ya nufi gidan Momy.
Maigadi ya bude masa get ya shiga da hancin
motar tare da mata matsugunni a wurin da ake tanada don
haka ya fito, maigadin ya taho baki bude yana masa sannu
da zuwa".
101
WAYE ANGON?-3 Maryam Jafar Kaduna
Suka gaisa a mutunce kamar yanda suka saba tun
yana gidan, ya shige yana cewa, "Zan ganka in na fito"
Har da tsalle, ya ce, "To... to... to a fito lafiya, yau
na san aljihuna dam".
Momy ta fito daga kicin tana fara'a jin sallamarsa,
ta ce, "Kai ne da yamma lis?"
Ya wuce dinning