fi samun hakan ta hanyar
shiga tuxi, gaskiya sai idan tu yi masifar kure mini ne zan
h.uu ko kuma idan mu din muna da yawa, in ba haka ba sai
62
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
dai na hau bus, máshin ko Adaidaita Sahu.
Yawancin lokuta kana gudun kaddarar ka guzuri
kake yi na taratta, kai ba ka sani ba. Rannan na fito daga
makaranta na tsaida bus wata kwararrабабвіда, па cc musu
asibitia'ciki da maza hiyu da kuma wata 'yar dattijuwa, don
haka hankali kwance na s higa, ina ta kallc-kallen waje, don
hankalina baya cikin motar tun da ni a gindin taga nakc, ní
ban aunc ba sai ji na yi wani abu ya daki kaina kafin in
tantance kome ye ke faruwa, ni dai sai bude ido na yi na
ganni a nan a yashe da yarinyata a gefe." Ta share
hawayenta. Na ce, 'Oh! Mu mun shiga uku bayin Allah, a
rayuwar yau ina mutun zai fakc ne ya ce ya tsira? A da can
san 6arayin mota kalia ce da su kila da ka gani ka gane,
amma yanzun abun ya canza salo, duk inda kuke tunanin za
su bullo muku to suma sun ganc sai su kauce inda kuma
duk kuke tunanin kun kubuce nan ne nkuma matattararsu.
Ya Allah ka kubutar da wadanda ba su ji ba, ba su gani ba,
Allah ka bankade asirin tsinannu, irin wannan bala'i haka
kawai śaboda neman duniya. To bayan an samu kuma sai
me? Mutane ba sa tsoron Mahaliccinsu?
To haka muka kasance da matar nan muna
bayyanawa juna abin da ke da akwai. Goshin Asuba barci
ya yi gaba da mu a zaunen nan, na yi mafarki da Baba da
Amma suna gaya mın in ta karanta La'ila ha'illa anta
subhanaka innikuntu minazzalinin. Allah ya yi gaskiya. Na
ko farka firgigit hasken rana ya fara hudowa. A raina na ce,
ta ina mutum zai y sallah, ba ruwa, ba kyakkyawan
muhalli, amma wanna ba uzirı ba ne. Kawai sai na kintaci
gabas na ringa shafar bango ina sallah. Matar nan ta ce,
"Kin ko kawo dabara n ai da na hakura ne." Na ce wannan
ba uzuri ba ne, tun da Allah ya ce bai dauke sallah ba a
6.3
"Haske Maganin Duhu" _Hauwu G. Lawan
lokacin da ake tsananin gwabza yaki, cowa ya yi rabi su
sallah raka'a daya, rabi su yi gadinsu, sai su kuma rabin su
koma su sallaci ta su sallah, saboda kar su dunguma su
duka ana yin sallah abokan gaba su far musu. To mutumin
Ja ke cikin wannan sammatsin ba a ke masa silak ba.
To wayc kuma za a daukewa? Don haka sallarmu kawai za
mu yi. Ta ce to. Har yaran duk mun yi sallah da su, mu kai
da'ira muna ta addu'a, La'ilaha illa'anta ce mukc ba adadi.
Mun yi Falaki da Nasi, sun yi dubu. Haka Ayatul Kursiyyu,
muna neman tsarin Allah daga sharrinsu, muna masu mika
wuya kuma muna masu kwadayin rahamar Allah ta sauka
gare mu. Mun yi tsaka da addu'a matar ta kallan ta cc,
"Zuwanki ya kawo cigaba da yawa, tun da na zo nan cikin
tsananin tsoro nake da rufani, amıma yanzun zuciya ta dake
fata nake idan zan gamu da Allah na gamu da shi ina Musulma, mai tsananin tsoransa da kwadayin rahamarsa.
Na ce haka Allah ya sa mu cika da imani, amin.
An sami misalin goman sate, sai ji kake kiririf, ana
shirin bufe kofa. Cikina ya bada wani irin sauti na tsananin
fargaba, to ta mu ta kare daga ni har su muka kalli kofar
cikin tsananin tashin hankali, Wani gabjejen kato ne ya
shigo, hannunsa rike da wa ya kallemu kallon
wulakancin da rashin imani, ya xe. "Me yс wani ku kа
zuran ido? Idan lokasin yanka ku yi za ku hana ni ne?"
Sai kawai na ji zucayata ta dake, na wurga idona cikin nasa
na kafe shi da su tadi nak
'Allahumma inna najaluka ti nuhuri him, wana
uzubika min shururiksimi" Ya yi ta kallona ina kallonsa
kaw sal ya dangwarar d samira ya juya bai kuına cewa
komai ba. Kawa sar yaran in matso jikinsu na ta
rawa za su bude. a san sanda ma daka musu tsawa ba.
64
"Haske Maganin Duhu" _Hauwa G. Lawan
Matar mai suna Fatima ta kallan ta yi murmushi ta ce, "Ki
kyale su, abinci ne ake kawo mana shi." Na ce sai ku ci?
"To ya za mu yi tun da da sauran kwananmu ai dole
muna nda bukata." Na jawo abincin na bude taliya ce jalof,
cikin samirar. Na sata gaba ina ta mata tofi duk abin da ya
samu na ıya dangane da addu'ar neman tsari, suma na ce
musu kowa ya karanta Kulhuwa, Falaki, Nasi, Li'ilafi da
Ayatul Kursiyyu, sannan ai Basmala kafin a ci, su kai kuwa
suka sa abincin gaba suka fara ci. Fatima ta ce, "Ba za ki ci
ba?" Na gyada kai. Ta yi murmushin yake ta ce, "Ki yi
hakuri ki daure, don ke din ai ba sani ki kai ba na ranar da
za ki bar gurin, kuma abincin dole ne inda kana rayuwa
lafiya da numfashi. Na ce, "Haka ne, ku dai ku ci kawai, ke
din ai ko dan bukatar yarinyarki mai shan nono." Ta juya ta
kama ci ba ta kuma cewa komai ba. Na jingina da bango na
rintse ido na ringa halarto Ubangijina kawai. Wallahi
mantawa na yi da duk wani wanda na sani, wuya ta yi
wuya.
An samu kwana uku ana mana haka ba mai kulamu
sai ran da za a kawo abinci, idan an tafi kai ka ce ba wani
dan adam mai lumfashi a cikin gidan. Ni kuma na kai
matukar galabaita yunwa da kishirwa, na neman halaka ni.
Rannan dai da aka kawo abincin na kalli katon na ce, Don
Allah ruwa " Ya wani tsare ni da ido, 'nima na kafe shi da
shi. Ina ta addu'a mai kuma ya tona sai ya juya ya fita, can
kamar ba i dawo ba sai gashi ya kawo cikin fan bokitın
fenti, na damki ruwan nan na sha na sha, haka suma suka
sha 'yar yarınyarta Ummi aka ba ta ta moda, duk sai mu kai
gefe muna maida numfashin azaba, sai da muka huta sosat,
nima dai anar na yi shahada na ci abincin kamar yanda
Fatima ke mini na ci bayan na tufe shi da addu;'a kamar
65
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
yanda nake musu kullum.
Wurin misalin hudu na yamma, Sadik da Halifa da
Umar suna rakube a kusa da ni, Ummi ta ringa wani irin
kuka mai ban tausayi, Fatima duk ta dada gigicewa tana ta
safe da marwa tana jijjigata, amına yarinyar ta ki shiru, duk
ma wani motsi da a kai sai ta kuma bude wuta, ba uwar ba,
har mu mun tsure na ce ta saukota, ta sauko ta na karbeta na
sata kafadata ina jijjiga ta. Ina! Sai na saukota kan cinyata
ina karanta mata abin da ya sauwaka daga Alkur'ani,
maimakon ta yi kukan sai kuma wata irin shakuwa kut-kut,
duk sai muka dada gigicewa, to abin ne Allah cuta, Allah
magani, kar mu cika motsi kuma a zo a ci kwalarmu, ga
kuma cuta ina za mu yi?
Uwar addu'a haka nima, sai ta ware ido ta ja ajiyar
zuciya mai tsayi, sai ta lumshe ido barci ya dauketa, mu
duk muka maida ajiyar zuciya. Fatima ta yi gajeran
murmushi ta ce, 'Wai yau mun ga idi." Na ce, "Umh! Ke
dai, Allah dai ya taimaka ta samu barci, ina jin tausayinta
ina tausayawa kan mu." Ta ce, "Haka ne na gode Sakina.".
"Kar ki damu yiwa kai ne, ni da ke ai duk daya nc.
Ta amshe ta ta kwantar kan dan zanin goyansu, na
matsa gaba na jingina da bango ina abun da zai fisshe mu.
An fi awa uku, Fatima ta ce, "Kin ga Sakina, anya ko
yarinyar nan da ranta?" Gabana ya yi wata irin faduwa
matsananciya,na matso ina kallonta kamar yanda take yi,
nima sai na ga komai na ta ya saki kamar ba ta numfashi,
na daga hannunta sai ya biyo ni da sauri na ware idonta shi
ma ko motsi. na ji wani dom a raina na runtse ido na yi
shiru, sai hawaye ne yake zuba. Ta yi ta kallona, ina bude
ido ga mamakina sai na ga murmushi take. Та се, "Tafa
mutun ko?" Ban ce komai ba. Ta ce, "Na sani tun fazu na
66
"Haske Maganin Duh" Hauwa i, Lawan
dai gaya miki ne don ki tayanı tabbatarwa, to ni ba abin da
zan cewa Allah sai in ta gode masa ina karawa, na san ya
amsa mini addu'ata, tun da na shigo gidan nan na daga
hannu na roke shi cewa idan ya kaddari karar kwananmu ni
da Ummi nan gidan to ya kashe mu cikin suttura ba tare da
wadannan azzaluman sun cutar da gangar jikinmu ba. Allah
ya amsa tun da ya karbi Ummi a gaban idona ba tarc da an
rabata da ni ba, ina ji ina gani an kcta mini ita, ko kuma ni a
daukc ni a barta ina kallo. To mai abun ya karbi abarsa
cikin suttura, mu kuma sauran mu ya kashe mu cikin imani
da suttura."
Kuka nake yi sosai da a ce ruwan ido na karewa da
dai zuwa yanzun ruwan namu idon ya gama karewa, saboda
azabar kuka. Ta lullufeta tana mai shafa fuskarta.
"Ummi Allah ya jikan ki da Rahamarsa
mayalwaciya, mu ma tafe muke da izinin Allah. Allah ya
suturce miki gangar jikinki kar ta tozarta, Allah na gode
maka kai mini baiwa a lokacin da nake kishirwar samu, ka
kuma karbi abinka lokacin da ya dace. Ummi na same ta ne
a lokacin da nake cikin shekara ta goma sha daya da aure.
A lokacin da takaici da gore-gore su kai mini yawa na naki
haihuwa tun daga miji na har zuwa 'yan'uwansa wanda ya
tilasta mini barin Katsina bisa yardarsa na taho Kano
neman karatu. Ina shekara ta biyu a makaranta Allah ya
bani cikin ta, yanzun gab nake da kammala karatuna ita
kuma ta shiga cikin shekara fayar farko a irin lokacin da
iyayc, 'ya'ya ke s higa ransu sun fara gane yawancin
abubuwa, sun fara takawa ana ta gwalan-gwalanton magana
wanin sha'awa to sai ga shi kuma abin da Allah ya yi
mana."
Na ce, 'Haka Maman Ummi ki yi hakuri an taba
67
"Haske Muganin Duhu"_ Hauwa G. Lawan
ranki." Ta cc, 'Wallahi ko daya ba na tarc da damuwa,
hakan da Allah ya yi mini babbar rahama cc." Na gyada
kai. Ka ji fa uwar da aka karbe mata 'ya take farin ciki daga
baki har zuci, lallai wahala ta yi wahala. Allah kasa mu
dace, amin.
Haka muka tusa gawar Ummi muna kallo, ranar dai
ba wanda ya runtsa har yaran mun zama abin tausayi
kwarai ainun, lokacin ba mu abinci ya yi. Wannan gabjcjen
katon da yake kawo mana abinci ya shigo dauke da
abincin, shi da kansa ya gane akwai sauyi sosai a tare da
mu, ya kalle mu da muguwar fuskar nan tashi daya bayan
daya, har idonshi ya kai ga Ummi da ke kudundune cikin
zanin goyanta ba kofar da za ta iya shakar numfashi, ga
yanayi na uban-uban zafi. Ya tsaya jim can ya ce, "Wannan
fa da aka kudundune ku ka sa gaba?" Ba wanda ya yi
magana sai ni na cc, "Ta mutu nc?" Shi kan shi kalmar ta
buge shi sosai, don yanda ya nuna ya dawo ya tsugunnaya
bude fuskar yarinyar kamar mai barci. Ya mayar ya rufe ya
mike zai fita na yi karaf na ce, "Don Allah ka taimake mu
tun da dai ta zama mushe kar ku cutar da ita ka haka mata
raımi ka binne ta." Ya zuba mini shegun idanunsa, zuciyata
ta ringa bugawa ina fargabar abin da zai mini, amma a
zuciyata addu'a kawai nake yi bai ce komai ba, ya kada kai
ya yi gaba.
Fatima ta ce, "Ina jiye miki sharrin mutanan nan fa,
ki daina yawan magana da su, kin ga ke budurwa ce, za su
iya amfani da wannan abin su cutar da ke." Na ce. "To ya
za mu yi Faty, zan kubucewa kaddara ta ne? Ni'da ke cikin
ko min su? Amma Allah yana ji yana gani, komai da yake
gudana a doran kasa."
Ya tafi sham har kamar ba zai kuma waiwayarmu
68
"Haske Maganin Duhu" Hauwa C, Lawan
ba. Bayan Azahar ana zuga uwar rana, ya shigo ya kama
mu ni da Fati ya kullc mana hannayc da baki ya hankadа Reyarmu ya sunkuci Ummi, sai yaran suka fashe da wani
irin kuka mai ban tausayi, ya maida kofa garam ya kulle, ya
ce mu yi gaba tsayin katangar gidan, haka muka ringa tafiya idanunmu sun yi rauni sosai, saboda rana mu kuma ba ganinta muke ba, tun da muka shiga gidan.
Can bayan gidan ya yi da mu tafiya sosai gidan
babba ne. Gidan gona ne irin kallon da mutane suke masa.
amma ashe da wata manufa a karkashinsa. Muka sami wani
guri ya tsaya ya sauke Ummi, sai ya janye wani kwali, ashe
ko rami ne ya haka, ya dauki Ummi har zanin goyanta
muna gani ya turata, ya sanya kasa ya ringa rufeta har sai
da ta rufu ruf, ina ganin uwar ana fara zuba mata kasa ta
runtse idonta hawaye ya zubo mata. Bai ce mana cikan ku
ba, ya tiso mu gaba ya hankado mu dakin da muke, ya cire
mana abin da ya kukkulle mu, ya yi gaba.
Wannan ya nuna baya bukatar maganarmu yana
fargabar kar mu yi wani yunkuri, amma mu ai ya yi mana
Haji da Umara ai.
Kwanammu tara, aka karo wasu yara su biyu đuk
mata. A lokacin ne suka shigo da wai da shi suke kira Oga.
Na yi tsaye baki bude inan kallon Ogan, kai duniya! Hinn!
Kyakkyawan mutum, Bafullace sosai, wanda zai gaza
shekaru arba'in a yanayinsa ya fi kama da liman ba wai đan
ta'adda ba, ashe shi ne Ogan. Ya kare mana kallo ya kafe
idonshi a kaina ya tambaye su wannan fa wa ya kawo ta?
Ya cc, 'Ai ita ce ta gurin Falalu, waccan matar kuma ita ce
Oska ya kawo, wannan yaran kuma ni na kawo su su uku ai
ka sani. dayar an yi amfanj da ita da su Alhaji Zarai suna
bukata." Ya gyada kai.
69
"Haske Maganin Duhи" Hauwa G. Lawan
"Okey, a cigaba da rike su ga wasu na hado daga a
Jos da na je na taho da su, cikin satin nan za a bukaci kudi
sosai, ku ma kuma za a ganku." Suka tafa sosai, daya yaron
ya ce, 'Ka ce za mu yi iyo a ruwa a gari, mu sha ruwa mu
kwanta cikin ruwa, a lullubemu da yayyafin ruwa."
"Sosai ma, su Ladi za su fantama ai." Suka kyalkyale da
dariya, ya matso sosai gabana yana mini wani duban
kankanci na sha'awa, ya kai hannu ya shafi kuncina ya сс,
"Yah baby how far?" Yana rufe baki, hannuna ya yi
kwanciyar ruwan zafi a fuskarshi, ji ka ke kaukau! Har sau
uku, abin ka da farin mutum sai gurin ya yi ja. Ba shi ba, ba
yaransa ba har irinmu sai suka bude baki ba su taba zaton
zan iya wannan karfin halin ba, nima ban zaci hakan ba,
kawai ji na yi ina yi.
Ya dafe kunci, yana mini wani irin kallo. Daya daga
cikin yaran ya iso da gudu ya damke ni ya bani
kyakkyawan mari guda biyu, zai mini naushi, shi ogan ya
janye shi ya ce, "Kyale ta, kyale ta, kawai ku shirya mini ita
zan dan huta da ita, wannan shi ne kawai zan huce, amma
ku tafi da ita ku rage mata gashin kanta, idan na gama
ganawa ta zan zo." Kan ka ce me? Sai aka mini wata irin
damka, na saki fitsari da wata irin kara, saboda tsananin
azaba.
Haka aka tankada ni suka, biyo bayana. A cikin
gidan a kai wani loko da ni aka kai ni gurin aski, abin
barber ne sosai, irin wanda ake aski, shi aka mini kwalkwal
ina ji ina gani. Dayan ya ce kawai a aske ragowar dayan ya
ce a'a, kasan dai Ogan maye ne kamar dan bunsuru, ya fi
son ya ringa ganin dan duhu-duhun, ji fa wannan yarinyar
da muka aske mata ba fada ya yi ta yi ba, yana ta sakin
maganganu? Su kai dariya suka tafa. Sai suka fita suka a
70
"Haske Maganin Duhu" _Hauwa G. Lawan
nuna mini bandaki wai na yi wanka na gyara kaina kar
Ogansu ya ji tsami. Ban ki ta su ba, nima ko don na sami
sa'ida na yi wanka, na dauro alwala na yi sallah, ina ta kuka
ina gayawa Allah ya dube mu ni da jama'ar da aka sato ya
tsare mu. Amin.
Na idar na zauna ina ta raba ido ni daya da solin
kaina, ina fargabar abin da zai faru next. Ba a neme ni ba
har tsayin daren ranar. Sai dai wajen tara an kawo shayi da
biredi na kuma sha soisai bayan na yi addu'a, suka fice, m
sa sakatu na zauna jiran tsammani. Ni da kc wannan mataki
na karshe a rayuwa, zugun din da na yi sai ya bawa barci
damar sace ni. Tabdi! Barci na yi sosai har Assalata m
farka firgigit, ni kaina na yi mamakin barcin na share miyan
barci na fada bandaki na yi alwala na yi sallah, na san
hakan baya rasa nasaba da wanka da dan dan tea da na sha
Ina zaune har wurin sha biyu wannan katun da yake
kawo mini abinci ya shigo, amma hannunshi baya dauke da
komai, ga mamakina sai ya zauna dab da kujerar da nake
zauna ina jiyo wani masifaflan tashin warinsa, sai ya yi dan
murmushi ya ce, "Baby you are so beautiful fa. "Ganin da
na yi jiya ban ji da dadi ba, sai kawai babara ta fado mini
gara na yaudare su ko hakan ya zame mini mafaka ta samtta
tsira. Na yi dan murmushi na kashe ido na ce, 'A hakan duk
kun tsotse ni?" Sai ya wani wangale baki ya ce, "Haba dai
ai kin san dai na ganki tun zuwanki ko? Kuma ma yanzun
ai yana nan rashin kula ne, baki gane har Oga jiya ya yaba
ba? Yanzun ma shi ya turo ni ya ce in je masa da ke, amma
ni alfarmar da nake neima idan ya ci ya rage dan Allah ki yi
mini alfarma nima ki fan sam mini, kuma ki kwantar da
hankalinki duk abin da Oga ya nema ki bashi ina mai
tabbatar miki in dai ya samu abin da yake so sakin kì zai yi,
71
"Huske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
kuma ko shi din bai yi hakan ba ni na yi miki alkawarin zan
kyale ki ki gudu a lokacin da basa gidan saboda ni din ni ne
mai kula da gidan nan, makullan ko'ina a hannuna sukc,
muma da muke zaune ciki ba wai dan san mu ba nc, kawai
don ba yanda za mu yi ne."
Na ce, "Haba dai kamar ya ya? Kai da ba kullcka a
kai ba, kana da damar da za ka gudu?" Ya girgiza kai ya сс,
"In ma na gudu ina za ni? A cikin gari ni din ai mai laifi ne,
wannan ita ce babbar katanga da ba za ta bari a ganınu ba,
bare a kama mu, don masu gidan su ne da garin ta kowacce
fuska mu din daga 'yan sacc-sace na unguwa aka kawo mu
nan, aka jibge dole ba don mun so ba muke bin umarnin
don rana zafi inuwa Kuna nc.
Talaka gatanshi kawai Allah ne, zafin talauci, rashin ilimi, rashin gata, karancin ci da sha, shi ya assasa wa
iyayenmu sakin mu uwa tumaki, ya zama kawai ana rayuwa
irin ta 'yan marina kowa da inda yake fuskanta, mu ba su ba
ne gabanmu don ba abin da za mu kalla mu ji dadi daga
gare su, sai dai ya taba mana zuciya, haka suma din mu ba
abin kallo ba ne gare su min zame musu liability, kullum
kuma sai daulo musu magana muke yi. To wannan ne ya sa
mu gara ramoa, tsakanin karya da gaskiya. Rayuwa ta yi wa
talaka karantsaye, shiwagabanninmu sai Allah ya yi musu
kamun kazar-kuku, abubuwa da yawa akwai sakaci da son
zuciya, kan su kawai suke da niyyar bautawa, ainma ha wai
al'umma ba, sabanin 'yan mazan jiya da suka gabau,
irinu Sardauna, Tafawa Balewa, Malam Aminu Kano,
Gambo Sawaba, Sabo Bakin Znws. Wada Nas, Mal awan
Mai Turare, hakika sun bautawa Kasarsu da ru da
jikkonansu, masu arzikin cikinsu sun bautawa har da
aljihunansu, amma na yanzu fa common consider idan ka
72
"Haske Maganin Duhu" Hawwa G. Lawan
ga bujimaycn da ya daure abin zai ba ku inamaki out of his
salary."
Na gyada kai na ce, "Wannan kuma ai ba dabara ha
cc, duk rashin tawakali ne da karbar kaddara da kuma
rashin mai da dukan al'amura gare shi, falalar Allah tana da
iyaka ne? Wani abun sai bayan an haifi jikokin mutum za a
kuma samun shi na daga falalar Ubangiji, to don me mutum
zai hakura ya zauna sai wani ya ba shi? Ku ji tsoron Allah,
akwai mutuwa, akwai kwanciyar kabari, akwai kuma
hisabi, wannan babu fashih ko kadan. Gani muke uwa
karya kamar abun ba zai faru ba."
Ya gyada kai, "Haka ne, to muna nan muna neman
shiriyar Allah." Na ce, 'Wallahi ba ku nema, domin zama
ku kai har sai Allah ya shirye ku. Me Malam mai Ahalari
ya ce, yana daga alamar rashin arziki da tabewa da damsil
basirati." Ya mike da sauri, "To Sayyada za a yi ne, yanzun
dai ki zo mu je gun Oga yana jira, kuma kar ki yi masa
gardama, abun da duk ya nema ki bashi, in Allah ya yarda
za ki bar gidan nan. Ni din ma na hakura da sudin da na
nema." Ban ce komai ba na mike, ya tusa ni gaba mu kai
can bayan gidan wani builsne mai kyau, kamar gida
guda muka shiga ciki nan zauna a falo, shi kuma ya shiga
ciki gurin Ogan.
Na kalli kofar falon ta glass ce akwai makullinta
jiki, ta waje kuma akwai padlock, a jiki an dai sakale tun da
kofar bude take, guda biyu Ma dan vi jim oan ji ba su da
alamar fitowa na lashi sadaf da sa akollin
kwashe wayar Ogan, na tice na sa masu maxulhn, na kuik
su na sarkafe su da duk padlock din, na sheka a guje
kaina ban san inda na nufa ba, saboda girman gonar 1
kuma sanin kanta na yi ba, kawai sa na gani kofar fakin ida
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawun
aka fito da mu, shi din na gane shi tun da na fito har sau
biyu, har na gota na dawo da baya ankwace sakale a bayan
aka sarkafa, cikin hukuncin Ubangiji ba a datse da kwado
ba, na ware ta da sauri, a nufina duk mu kubuta, ko kuma
dai wasu daga cikinmu wanda Allah ya nufa.
Suka min caa da ido, ina haki na ce. "Duk ku fito
kowa tasa ta fishshe shi, amma a nutse don haka. Mu kai
wani gu a nutsc cikin sanda da karfin Allah, ashe gun kofar
muka nufa babban get, an kukkulle da kuba ta ciki, muka
zare a hankali mu kai waje da gudu, bayan mun sarkafe su
ba kwado. Na ce, "To kowa fa tasa ta fishsheshi, da dabandaban muka zo don haka kowa ya yi ta kansa. Na sani
kawai Ubangiji ne ya amshi addu'armu ya kubutar da mu
daga wannan masifa, mma ya ya su da suke wannan
mugun aiki za su yi sakaci har nu rai takwas mu gudu?
Allah kenan, shi ne ya shirya komai ba wai iyawarmu ba,
girman gidan gonar nan ya isa, ana kiwon dabbobi da
mutane. A saida mutum, a saida dabba.
Muka runtuma a guje gabas, gudu muke har ba mu
san inda za mu ba. Mun yi gucy a kallah na minti arba'in ba
ko hutawa, kuma duk tare muke, sai Khalita, daya daga
cikin yaran nan kawai sai ya ci da baka ya fadi, ni ce a
gaban su sai na tsaya na daga shi, ya kalleni har yana
numfashi sama-sama, ragowar ai ba su tsaya ba, gaba su
kai, na waiwaya gaba, na waiwaya baya na ce, "Daure ka
tashi kawai ba gurin tsayuwa ba ne nan." Ya yi shiru yana
fidda numfashi ta hanci, ta baki. Ai kawai sai ji mu kai dindin ana hom. kafin na juya tuni Khalifa ya rigani da ka
tsalle ya figa a guje, nima sai na runtuma ban ko tsaya ba,
muka nausa. T'o ka ji rabuwarmu da su. Ina wannan gudun
ne, ban kuma san mai ya kuma faruwa da ni ba, sai da na
74
"Haske Maganin Duhu"
bude idona na gan ku. To ka ji."
Huwwa G. Lawan
Barista ya ja doguwar ajiyar zuciya ya ce, "Tabdi! Lallai kunstsalle rijiya da baya, kuma ke din sai kika zama
rahama gare su, don an yi amfani da ke ne, wajen kubutar
da su, idan har sun sami nasarar hakan. Ko ya tasu ta kasance? Allah masani, to Allah ya cigaba da tsaremu
lafiyarmu da imaninmu, ya cigaba da tsare mu daga sharrin
duk abin da ya halitta. Amin. Amma dai ni ai ni a kaiwa
wannan hidima, kila da hakan ba ta faru ba da abn da
hanyar ganinki har na kwashi wannan roman." Ta doki
kafadarshi ta ce, "Ko?" Ya gyada mata kai cikin wani
shauki, ta kara matsawa kusa da shi, ya amsheta suka
kasance cikin aminci da rahamar Allah mai yawa.
Rayuwa ta yi musu yanda suke so, har'yan canjin
sun samu. An siyo mata mota takumbo Hondu Civic, mai
kyau kalar ja. Ta yi tsalle ta yi murna sosai, ta yi godiya, ya
dungureta ya ce, "Da'allah ja can kin cika ni da hayaniya
kina nufin wannan ce godiyar?" Ta rike kugu la ce, "Haba
nawa share kawai, ka dai bari ni idan na ringa maka godiya
yau sai ka gudu bari dai duhu ya shigo, za ka sha mamaki."
Ya yi dariya ya kwantar-dai a jikin kujcra yana