An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HASKE
MAGANIN DUHU
HAUWAʼU ABUBAKAR LAWAL
Mei Tue)
Huske Maganin Duhu Hauwa G. Lawan
HASKE MAGANIN DUHU
NA
HAUWA GANDHI LAWAN
MAITURAREN KAMSHI
(Mrs. Yusuf Garba Mustapha) 08090664904 Or 07029324870
1
"Huske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawun
Hukkin Mallaka: Hauwa Gandli Lawan Mai Turaten
Kamshi.
Copy right(C): Hauwa Gandli awwn Mai Tutaren
Kamshi.
GODIYA
Ga Allahu Rabus Samawati, wal ardihi, Rabbl Muta w
Haruna, Allah ba zan butulce maka ba. Ina godiya da tarin
ni'imomin da kai mini. Allah ka sanya ni daga cikin masu ibadа
da godiya, amin. Albamdulillah. Salati ga Muftahu Rahma,
Nurizzatiyyi, Sayyadil Wujudi, Katimun Nabiyina wallmursali
Sayyadina Habibuna, Muhd Rasulillah (S.A.W.) shi da iyalanта
da duk másu sonsa suke bin tafarkinsa amin Madallah da
Ubangijin haske da duhu.
TUKUICІ
Ga malanan da suka fara karantar da ni, har zuwa yau,
Allah ya kai haske kaburburansu. Amin.
INA GODIYA
Ga duk wani mai sona, a duniya tin daga samuwa ta har
zuwa yau, la dalilin hasken karatu, ko kuma wani dalilin na
daban. Yaushe zan butulce? Kai I love you so much e
Musamman Fatima Aliyu Isa (Zahra).
SADAUKARWA
Wannan littafi na sadaukar da duk ladan da Allah zai ba
ni ta hanyarshi ga Ruhin SANI LAWAN MAITURARE (Young.
Doctor) yaron da danginsa suka sa buri da shi, ba ga mu ba,
gwamnati ma ta yi jajen rashinsa, domin ta yi alfahari da shi
kwarai, tun da sau biyu yana wakiltarta a Kasar India, da Rasha,
kan harkar lafiya. Ya mutu ne a daidai lokacin da yake fafutukar
neman ilimi. Ashe kaunar shi, ajalinsa a cikinsa ne. Ina mana
ta'aziyyar mutuwar Malam, tare da dimbin abokanka, domin duk
ran da suka tunaka sai sun yi jimani, irio mutanen da a cikin
miliyan ake fidda daya. Duk cikin dangi an shaida ba kamar
Malam, sani yana da shekara goma sha biyu ya sauke alkur'ani,
2
"laske Maganin Duhu" Manwa G. Lawaп
sha biyar ya haddace ya kuma rubuta shí da hannunsa. Mutum m.
mai matukar nutsuwa da tawali'u, Karami, amma babba ne a
cikin yara, tun yana raye ake cewa wannan tamkar waliyi yaku.
ashe hoto ne kawai aka ba mu na shi, ya yi mana wata irin
rayuwa mai cike da alfanu da izna mai yawa. Allah ya jikan Sani
Lawan Maiturare (Malam), don Allah ina rokon kulhuwallahu ko
kala daya ce ga wanda ya karanta shahin nan zuwa ga ruhin
Malam Saı. Ya rasu yana da shckara ashirinn da uku, ban tabа
ganin mai basira irin shi ba. Malaman shi ma shakkar sa suke vi,
ashe an bude komai ne na fan lokaci. Allah mun gode maka da
ka ba mu shi ka karbi abin ka. Mota ce ta yi ajalinsa, tun daga
inda a kai hadari a kai nisan lafiya zuwa asibiti, don ceton ranshi.
cikin nutsuwar shi yana karanta Al'kurani dab da za a kai shi
asibitin rayuwar ta kare. Ya bar Ummanshi da jimami, Allah va
jikanka da Rahamarsa. Amin.
INA SON KU
Rahma Idrisu
Aminar Dambatta (Yarinya, Maman Sani)
Mariyata Sada ('Yar Mutan Katsina)
Hafinata B.1. (Sharri Kayan Kwalba)
Fauziyyar Q for Q (Auren Kudi)
Allah ya barni da ku, da kune nake ganin nasarar
rubutuna, Na gode.
ALBARKARMU TARE
Ga Kawata Kubran Namarwa, tare.da iyalanta. Ina goıva
la, yaushe san butulce?
ALLAH YĄ AMFANA
A
Auren Shatu na Aishatu CGarba Mustapha (tiwato
Aisha) tare la Angonta Ibrahim. Allah ya bıuda zuriya dayyi a.
WEL COME TO THE WORLD Mustlupha Aminu (ia
Mustapha.llah ya raya mana kai da albarku, ya bawa babarкa
nauyin daykar hidimarku. Ya hawa Mananka laliya: Anti
Fauziyyahya Kura Muhd.
3
"Huske uganin Duии" Hанwа . Lawan
IASKE MAGANIN DUIU
udu ne take yi, irin gudun da ya yi kama da G"gudun ceton rai. Gudun daga ka ga mai
yinsa, muhimmin lamari ne ya koru shi
domin babu ruwanta da duban inda take ajewa da dauke
Kafa. Neman h aske kawai take, don fita daga duhun da la
baro.
Lokact faya, wani irin duhu ya ziyarс
Kwakwalwarta, cikin dakiku da su kai kama da na kiftawar
ido sassan jikinta ya amsa, ba tare da bin shawarar
zuciyarta ba. dole jikin ya bi umarnin kwakwalwarta
Lokaci daya haske ya dauke mata, ta yi warwasa a doran
Kasa, komai na jikinta ya yi laushi lubus. Mutuwa ce suma
ne?
Barista Muttaka, da ya fito daga kwanar makarantar
Musa Iliyasu, akan idonshi yana kokarin fitowa ya ga
gilamwarta a guje, har sanda ya karasa fitowa titin sosai.
vana hangena a gujen gudu take yi kamar walkiya. Har
abin ya dan taba zuciyarsa. Ta mirmow dinshi sai da ya
waiwaya bay. don ya yi isegumin shin wannan yarinyar ita
da wa? Bai hango kowa ba, bai ga kowa ba, wanda yake da
alaka da gudan nata, baya ga daidaikun jama'ar da ke yawa
a titin sabuwar Jami'ar suna sabgoginsu. Ya hau titin sosai.
mma yana cigaba da panintą, lokaci guda ya ga ta yı
laduwar bazata a gefen hanya warwas.
Lokac a ne zuciyarshi ta ba shi shawarar yin wanı
abu. Cikin how speed ya gangara gefen hanyar inda take
kwance a nace, ya fito da hanzarinshi ya isa kanta
Gabanshi yai wata irin taduwa lokacin da ya hada ido da
jemammiyar uskarta. da sassan jikinta kwance sun bi Kasa
"Ya A lahu." Shi ya ambata ya kawo masa dauki. Ya
"Haske Maganin Duhu". Hauwa Ci. I awan
duba gabas da yamma, kudu da arcwa ko zai ga mai kawo
agaji. Kowa ta kanshi yake, motacin da ke titin wuccwarsu
su din kawai suke. Ya yi A'uziyya don kariya. Sannan ya
koma ya bude motar ya ciccibcta ya sakata a ciki. Cikin
hanzari ya tashi motar. A asibitin Saudat da ke nan Rijiyar
Zakin ya mika ta gun taimakon gaggawa (Emergency),
likito da nos-nos suke masu kyakkyawar maraba ta hanyar
ba su duk wata kulawa da ta dacc. An bata gado, an sa mala
drip, amma har lokacin ba ta dawo ba. Sai ranta da ke
kaiwa yana kawowa.
Barista Habib ya kura mata ido, don nazarta wasu
yanayi da ya ganta a ciki. Na farko ya karanci akwai alamar
matukar galabaita da jemewa a jikinta wanda ya assasa
fitowar idanunta wajc kuru-kuru. Sannan kalar fatarta da
gani ta dara wacce take a yanzun hasawa, a gefen fuskarta
akwai tambari na mari da yakushi. Sannan gashin kanta
askc yake kwal-kwal. Lallai nan gurin akwai bayani.
Yarinya ce da a tsinkayc da kyar ta haura sha tara.
Sannan mai matsakaicin tsayi. "Yar jika-jika mai kyan sura.
Duk daga inda ta fito ba daga daula ba'ne, daga wahala ne.
Wai me ya koro kwado daga ruwa zai fada wuta?
Dogon likita kakkaura baki, ya dan doki bayan
Barista ya ce, "Take casy man, insha Allah za ta farko
normal. Wuya ce dai ta sha matsananoiya, insha Allah nan
da goman dare za ta dawo hayyacinta, mun ba ta
magunguna masu karfi da za su taimake ta samun haka."
Suka kalli agogon a tare, su kai dan murmushi. Ya ce, "Na
gode likita To zan iya barinta kenan in je kawo mata kayan
bukatu? Na san zan jya dawowa kafin karfe gwiman."
"Yes man you can go, ba wanikabuszamú ba ta duk
kulawar da ta dace." Likitan ya fada.
5
"IHaske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
"Na gode kwarai, Allah ya biya." L.n ya yi
murmushi, ya juya ya fita ya turo nurse biyu don su kula da
ita, kafi mai ita ya dawo.
Ya fito daga asibitin cikin godiyar Allah, da raunin
jiki. Zveiyarshi cikc take fam da wasiwasi iri-iri, to yanzu
ya zai yi? Gidansunwai zai wuce ya gayawa Hajiya ab
da ke fara, kuma shirn kawo i zai yi shi din ya ci gaba a
kujiba-kujibarsa har yarınyar dai ta dawo hayyacinta
sada ta da iyayenta? Abin da ya sani Hajiyarsa mace
ba ta son kwashe-kwashc, yanzun yana gaya mata bal ale
shi da fadanta za ta yi, ta ringa shiga tana fita kullum ita
abin da take cewa, "Shegen karambani ne da fan adaı
haka kawai Allah va bar bawanshi a rana kai kuma ¿a
rawar kai sai ka kinkinwo shi ka.aido shi inuwa. To yayin
da ya tsane kai ne lamba wan da zai jawo ya danna ka wuta,
don haka jama'a su yi hattara, jama'ar yau wuyar sha'ani
garc su.
To ko kuma gidan Yaya Zainab zai je ya fayyace
mata komai? Itama din dai bari ya ja akwai sauran lokacin
shaida mata. A çikin motarshi duk yake wannan tunanctunane, har zuwa inda y a yi parking a kofar gidan iyayenshi
cikin Kofar Nassarawa, huda yake tare da mahaifiyarshi a
cikin apartment fin mahaifinshi da ya mutu ba bari shi ya
gyara yake z a insa. Ya shiga ciki, ya vi wanka,
hadi da alv alar sallar Magriba. Sannan ya fada cikin
gidansu gurin Hajiyarsa. a taradda ita tana addu'a kai
tsave ya wuce cikin kicin yana bude-hude. Cikinsa sai guda
yake yi don avabu. yu..wa.
Ya yi masifa far. dni da yu yi karo da ane da cot
ya dahu ya yı dindim a cikin flask. Ya yi saurın rufcwa
lokacin da turirinsa ya yi masa oyoyo. Ya bufe womar
6
,
"Haske Maganin Duhu" Hauwa . Lawan
miyar lafiyayyar miyar kubcwa busassa ya sa cokali ya
tuno zuka-zukan naina ne na saniya, sai a kansu ya wuce ya
dau tsokoki uku masu lafiya ya danna a baki. Yanda su kai
masa dadi a rai, ya so a ce dai abin da zai gamsarshi ne ya
sanu. Amma yanda ya kwaso yar taballan nan haka sakin
ya lafci bakin tuwon nan, ai sai ya yi masa illa a hanji. (Ku
ji ni da Barista yana kushe gargajiyar Bahaushc, ai ko ba za
a raina ta ba).
Ya koma falon gun hajiyarsa tana shafa addu'a ta ce,
"Muttaka an dawo?" Ya durkusa a gabanta ya ce, 'Wallahi
Hajiya Allah ya nufa. Ya wunin yau?"
"Komai lafiya."
"Ya wurin aikin naka, yau kam dai ka dan yi nutso
da yawa, ina jin tun wayewar garin sai yanzun na ganka."
Ya yi gajeran murmushi.
"Hajiya neman ne ya jawo tsayin lokacin, kuma
Hajiya tun dan shayin da na kurba da safc ba komai a
cikina yunwa nake ji sosai." Tana murmushi.
"Ai akwai lafiyayyens tuwan dawa, miyar busassar
kubewa, hadda man shanu a dakin girki." Tana ta dariya,
don dai ta san ba a take yi ita ma, ta san dai Muttaka ba
ma'abocin tuwo ba ne, tun yana yaronsa. Ya mike tsaye ya
ce, "Na tafi neman abinci Hajiya."
'Allah ya kiyayc hanya, ai dai ga irinta nan, ni ko
saboda kai-kai daya ba zan fasa girkin tuwona ba, ko-kuma
hayan na yi girkin, ka sani girka ma wani ba, da dai su
Maryam na kusa ne. To wannan daiin da ni ce kai, wannan
wulakancin duk da akc mini da yanzun na nemawa kaina
mafita, in yo dallelen aurena, shi kenan bakina alaikum,
abin da duk nake so shi zan bada umarnin a girka, amma
ina dadin rabe-rabс?"
"Haske Maganin Duh" Hauwa G. Lawan
Bai ce komai ba, ya kada kanshi ya kara gaba, Inda
sabo ya saba mitar Hajiya a kan aurc. Ta kan manta komai
fin da yake yi lokaci nc, Allah na kawo lokacin auren shi
kenan sai ya yi, amma shi din wurin shi bai wani fiyс
damuwa ba. Hidimomin gabanshi su ne mafi rinjayen
abubuwa da yafi maida hankali a kan su.
Ya fito kofar gida ya yi tsayc jim da tunanin ina ne
ma zai nemi abinci ko kuma shayi zai sha? Kai ina shayi
fin ai ba abinci ba ne. Mutum tun da Rabbi ya hudu rana a
ce bai ci komai ba sai ruwa? Kai can't be possible. Irin
wannan lokacin bai fiye son shiga gidajen 'yan'uwansa ba,
saboda dai lokaci ne da ko wanc maigidanci yake zaune
yana hutawa cikin iyalinsa. Dole uwar naki tasa ya dannan
gidan yayansa na biyu.
Ya tarad a tsakar gidan an shimfida katuwar
tabarma, yayansa da 'ya'yansa guda hudu suna zaunc suna
cin abinci da yin hirа.
Ya yi sallama yaran da yayan nasa suka amsa, ya
karaso gurinshi suna gaisawa da tambayar ya aiki, sannan
ya yi masa Bismillah. Ya kalli kwanon da ya kusa cinyewa
yay cc, 'A'a yaya karasa kayanka kawai, ni din ai babbar
yunwa nake ji ba wai Karama ba. Ina matar ne ta zo ta
sallame ni?" Kafin yayan ya bashi amsa ya daga murya
yana mata kwakwazo. Ta fito cikin kwalliyarta tana kamshi
mai sanyin dadi. Ya harareta da cewa, "Sai ki wani shige
faki kina ta batan lokaci, wa ya gaya miki anawa maigida
haka, ai shi maigida da wuri ake sallamarshi da abin da zai
kare cikinsa, tun da shi ne mai nemowa, wanda ko ke
nemowa ba a gyara mai wata ran idan ya fita sai an bi sahu
don nemo shi."
Ta ja kujera 'yar tsugunno ta zauna ta ce, "Haka ne
8
"Haske Maganin Duhu" Nauwa (. Lawan
miyar lafiyayyar miyar kubewa busassa ya sa cokali ya
tuno zuka-zukan nama ne na saniya, sai a kansu ya wuce ya
dau tsokoki uku masu lafiya ya danna a baki. Yanda su kai
masa dadi a rai, ya so a ce dai abin da zai gamsarshi ne ya
samu. Amma yanda ya kwaso yar taballan nan haka sakin
ya lafci bakin tuwon nan, ai sai ya yi masa illa a hanji. (Ku
ji ni da Barista yana kushe gargajiyar Bahaushe, ai ko ba za
a raina ta ba).
Ya koma falon gun hajiyarsa tana shafa addu'a ta ce,
"Muttaka an dawo?" Ya durkusa a gabanta ya ce, Wallahi
Hajiya Allah ya nufa. Ya wunin yau?"
"Komai lafiya."
"Ya wurin aikin naka, yau kam dai ka dan yi nutso
da yawa, ina jin tun wayewar garin sai yanzun na ganka."
Ya yi gajeran murmushi.
"Hajiya neman ne ya jawo tsayin lokacin, kuma
Hajiya tun dan shayin da na kurba da safe ba komai a
cikina yunwa nake ji sosai." Tana murmushi.
"Ai akwai lafiyayyens tuwan dawa, miyar busassar
kubewa, hadda man shanu a dakin girki." Tana ta dariya,
don dai ta san ba a take yi ita ma, ta san dai Muttaka ba
ma'abocin tuwo ba ne, tun yana yaronsa. Ya mike tsaye ya
ce, "Na tafi neman abinci Hajiya."
'Allah ya kiyaye hanya, ai dai ga irinta nan, ni ko
saboda kai-kai daya ba zan fasa girkin tuwona ba, ko-kuma
bayan na yi girkin, ka sani girka ma wani ba, da dai su Maryam na kusa ne. To wannan daiin da ni ce kai, wannan
wulakancin duk da akc mini da yanzun na nemawa kaina
mafita, in yo dallelen aurena, shi kenan bakina alaikum,
abin da duk nake so shi zan bada umarnin a girka, amma
ina dadin rabe-rabс?"
7
"Haske Maganin Duhu" _ IHauwa G. Lawan
Bai ce komai ba, ya kada kanshi ya kara gaba. Inda
sabo ya saba mitar Hajiya a kan aurc. Ta kan manta komai
fin da yake yi lokaci nc, Allah na kawo lokacin auren shi
kenan sai ya yi, amma shi din wurin shi bai wani fiye
damuwa ba. Hidimomin gabanshi su ne mafi rinjayen
abubuwa da yafi maida hankali a kan su.
Ya fito kofar gida ya yi tsaye jim da tunanin ina ne
ma zai nemi abinci ko kuına shayi zai sha? Kai ina shayi
fin ai ba abinci ba ne. Mutum tun da Rabbi ya hudu rana a
ce bai ci komai ba sai ruwa? Kai can't be possible. Irin
wannan lokacin bai fiye son shiga gidajen 'yan'uwansa ba,
saboda dai lokaci ne da ko wane maigidanci yake zaune
yana hutawa cikin iyalinsa. Dole uwar naki tasa ya dannan
gidan yayansa na biyu.
Ya tarad a tsakar gidan an shimfida katuwar
tabarma, yayansa da 'ya'yansa guda hudu suna zaune suna
cin abinci da yin hira.
Ya yi sallama yaran da yayan nasa suka amsa, ya
Karaso gurinshi suna gaisawa da tambayar ya aiki, sannan
ya yi masa Bismillah. Ya kalli kwanon da ya kusa cinyewa
yay ce, 'A'a yaya karasa kayanka kawai, ni din ai babbar
yunwa nake ji ba wai karama ba. Ina matar ne ta zo ta
sallame ni?" Kafin yayan ya bashi amsa ya daga murya
yana mata kwakwazo. Ta fito cikin kwalliyarta tana kamshi
mai sanyin dadi. Ya harareta da cewa, "Sai ki wani shige
faki kina ta batan lokaci, wa ya gaya miki anawa maigida
haka, ai shi maigida da wuri ake sallamarshi da abin da zai
kare cikinsa, tun da shi ne mai nemowa, wanda ko ke
nemowa ba a gyara mai wata ran idan ya fita sai an bi sahu
don nemo shi."
Ta ja kujera 'yar tsugunno ta zauna ta ce, "Haka ne
8
"Haske Muganin Puhu" Hauwa G. Lawen
kam, ai ka gani da idonka inda nake kokarina ko? Ba na bar
ma dan'uwanka da yunwa bare kuma sanyin idamunka."
"Ban san wasa fa Hauwa ke din sana'ar da kika iya
kenan bar tirenin din wasu kike yi, ni tashi ki ba ni abinci
wanc maigida ne kuma kike magana bayan ni, gashi nan
kina ta sakaci ulcer ta kusa cafke ni, idan na shuri kasa na
ga wanda za a bari da takaba. Tun safe kin bar hanjina sai
bude-bude suke." Ta yi dariya mai isarta ta ce, "Haiya
ratata, dariyar mai mata uku, kanka ake ji wai mahaukaci ya
fada ruwa, ya ce wankana nake yi. Ni din ai na san kai ba
ganinka ake yi ba, sai ranar da cikinka ke zikiri ka lalubi na
Hajiya ka ji ba kanta, sai ka fara bin gidajen, tamkar
dillaliya uwar gulma. In dan Aljannar gurinka ne ka ke mini
wannan isar take kayarka ba sai ka dage kafar ba, bare na
samu na shige. Na gode da takan, abincin kuma dai ba ka
sanar za ka zo ba, bare a sa sanwa da kai, sai abi wani
sarkin, ama dai ba Ado ba."
Ya kwantar da kai, "Plcase uwargida, daga ke fa ko
kallon wata ba zan kuma ba, barc na yi kari, tashi za ki ki
dan lalubo ko' naki ne, ke din ai waliyya ce, abincin ba
damunki ya yi ba." Ta ja tsaki.
"Ni da amaryar ka Karamin dana huta da ganinka
kana mini shishshigi a tukunya,"
Ya ce, "Plcase manta la'allah ki yi wani abu man."
Ya juya yana kallon wan.
"Yaya sa mini baki mana matar nan fa so take ta
karta mini."
Yayan da ya yi burus a gurin bai ku sa musu baki ba,
yana dai ta cin abincinsa ne yana kallon shirmensu, shi da
'ya'yansa. Ya ture filet din abincinsa ya mike ya ee, "A'a ni
me yc nawa a ciki tsakaninku, ami nemowa da mai girkawa
"Haske Muganin Duhu" _Hauwa G. Lawan
C
1
sai ku sasanta." Ya yi shigewarsa falonsu. Ya bishi da kallo
galala, sai da ya kule ya dawo da kallonshi gare ta ya
sassauta murya yana ban baki, sannan ta tashi ta shako
masa filet da dambun shimkafa mai kyau. Nan ya lalace yana ci yana santi, yana kuma ba ta labarin abin takaicin
wai da Hajiya ta yi bakin tuwo (Gardi da gyale). Ta yi dariya ta ce, "Ni kam kana ba ni mamaki matarka kam ta banu idan ita din mai son tuwo ce, ce nake yi tuwo ba abin marmari ba ne? Ni kam idan na yi kwana biyu ni dai maigidana ba mu ci ba duk ran da na yi za ka'so ka ga garar da za mu kwasa muna santi, sai dai yaranka ma kai suka biyo, da na ce tuwo an ringa zumbure-zumbure kenan, haka
za su ringa can kulati-kulati. Don shi Nuraddin ma, idan ya
ga tuwo kuka yake yi ya ce ba shí ba shi ba a bashi abinci."
Yce, 'A'a Madam da gaskiyarsu ki ringa girka
musu kawai abin da suke so, tun da dai na kawo komai na
!aje a wadace a gida." "Haka ne sai dai ka manta ba ka kawo
maigirki ba ka aje, ni din ai ba zan iya wannan ba, yanda
dai Hajiya take yi nima haka hake mai ci ya ci, mara ci ya
bar shi, idan yana da abin da ci ya ci, idan babu a sha ruwa
ce a ja lahaula
"Ke an gaya miki yunwa na jin lahaula ne? Ai da a
baki rubutu gara kwadon rogo."
Yara na gefe, suka kyalkyale da dariya, shi ma ya
taya su ya ce, "Allah ko, ku dai ku yi hakuri, ku kuma sha
kuruminku da zarar na kawo sabuwar Anti i cin tuwan
dare ya kare shi yake lalata hanji, kuna ganin arnen nan ya
hade rai sai ku zuro a guje gurinta za ta ba ku abinci mai
dadi ku ci." Yara suka fara eh suna murna. Nuraddin ma
cewa ya yi shi din can zai koma da zama. Ya bubbuga
u bayansa kai dai kawai ka yi addu'a Allah ya kawo ta gari.
10
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
Ya ture kwanon ya ce, "Madam godiya sakallah, kin fita ko ba sabulu, kofar Jannatin nan yanzu you are free to enter, ai kin yi abin da Allah ke so. Bari ki ga na tashi na koma asibitin ko, 'yar mutane ta farko?"
Ta cc, 'Wa kc nan?"
Nan ya labarta mata labarin komai, ta yi sakale tana
jajantawa ta ce, 'Barista to haka za ka tafi ba dan wani abu
da ko za ta ci, idan ta farkan?"
"Ai ina jin dai a asibitin ma suna bada abinci kin san
private ne."
"Duk da haka a dan rika mata wani abun, ka san dai
ai ba ko wane private ba ne suke ba da abincin, kuma ko
suna badawa mutum kan bukaci wani abu daga waje."
"Haka ne, to me za ki ba mu?"
"Ka ga a zuba mata dambun shinkafar nan abun
marmari ne, kila ta so; kuma ina da wani sauran feffsuf zan
hada mata." Ya yi zugum a ransa da tunanin ya ya marar
lafiya zai wani so Dambu? To amma kar ya watsa mata
kasa a ido, dole ya amsa yana ta godiya, ya saka kayan a
bayin motarshi. Sannan ya koma gida ya canza kaya ya sa
jallabiya mai dogon wando da gajeran hannu. Ya yi ma
Hajiya sallama zai je ya dawo, ta ce, "Cin abincin ne dai ya
yi nisa haka, duka a lungun ba abincin?" Yana sosa keya
yana dariya ya ce, "Haba dai Hajiya an samu gidan
Kuluwa, kin san ita ba ta karanta, ba kamar su o'o ba da
abinci baki da baki don kar irinmu su samu."
"Maganinka kenan, mai kwadayi mai bin gidaje, in
da kana da taka shekar mai zai dame ka, ba sai yanda ka yi
ba?" Ya gyada kai, alamar amincewa, ya fito.
Daidai lokacin da ya danna kan shi fakin, a daidai
lokacin rayuwar yarinyar ta dawo. An kuma yi sa'a shi da
11
"Haske Maganin Duhu"_Hauwa G. Lawan
likitan suka shigo tarc misalin tara da arba'in da hiyar, ta
raba idanu kan kowa. Lokaci daya me ta tuno oho, kawai
sai ta yi wani masifaffan yunkuri ta duro daga gadon igiyar
Karin ruwan ta biyo ta. Likita da Barista suka kawo agaji da
hanzari suka cukuikuycta. Fadi takc "Don girman Allah ku
kyale ni, ku rabu da ni, kar ku cutar da ni, ba abin da na yi
muku. In kun kyale ni ba zan gayawa kowa ba, na yi muku alkawari."
Likita fadi yake, "Take casy baby, mu nan da kika
gani ba macuta ba ne, rayuwarki muke kokarin cetowa, daga hannun da kika fada, kin ga ni nan likita ne, wannan
kuma shi ya kawo ki, ki nutsu." Ta kalli barista a zabure,
sai raba ido take kamar na tsohuwar maiya.
Da kyar dai suka lallaba ta ta zauna, amma sai kallo
take, duk wani motsi sai ta zabura. Tana wannan