"Sorry Oga, wa ya gaya maka ana fushi da amarya ranar
auranta? See yo, good night, and habe a nice dream with
me. "Ba ta jira ya ce komai ba ta wuce gidansu.
Washe gari ranar Juma'a ita ce ranar da ta yi walima
da kawayenta d.an'uwana da misalin karfe hudu na
yamma, wallma: masia iain an ci kaji an sha su
kafirin da, an more 'yan uwa da dangi, kawaye duk sun vi
kara shi ma taron ya watse lafiya inda kowa ya taho do
ledar ko jakar biki da silbeniyos, na bikin, saboda haduwт,
haduwarsu a hoton sai an tanka a kan ce kai tubarkailsh
nice coupk
Ranar Asabar, ranar ce da faruruwan al'um
Musulmi suka shaida daurin aurensu, inda honourable mai
49
"Haske Magunin Duhu" Hauwa G. Lawan
Dala ya daura auren, Grandikadi na Kano ya wakilci ango.
Taron da ya samu halarcin manya da kananan mutane, 'yan
kasuwa da ma'nikatan gwamnati, lauyoyi ranar su ce, don
akan idonsu aka daura a kan sadaki naira dubu ashirin da
Barista ya biya tun a waccan karo an fada jama'a sun
shaida.
Bayan dangin ango sun tafi, wadanda ya rage daga
Gangaren amarya aka goce da fito musu da tuwon shinkafa,
waina, sinasir, funkaso, da ruwan lemo. Sai gani kike
mutane na sabe babbar riga ana zuba loma, bayan ka gyatse
sai kuma a damka maka goro da alewa na shaidar ka halarci
daurin auren Sakina da Barista Muttaka. Suma taron na su
ya watsc sumul uban amarya da danginta sai watse baki
suke, fadi suke ku gaida gida mun gode.
Ango bayan sun ja tawargarsu suma din dan
reception suka tafi a can Amir Place inda za su dan ci
abinci ai hirar sada zumunci aga wanda ba a gani ba. Ango
can na hango shi baki kamar gonar auduga, ya kasa zaune
ya kasa tsaye, an yi masa karin girma, ya táshi daga gwauro
ya koma mai daraja mai aure. Can na gano maku su Barista
Ibrahim ana wakewa da pride rice da pep-checken ana
korawa da Ziza milk. Taro kam ya yi dadi kwarai yanda
ake so ka jiyo mini shewar abokai ciki ya dauka an ji wara
mai maiko da magi.
Yawancin manyan abokanshi sai bayan 1.a'asar suka
bar s hi, kowa kuma ya kama gabanshi bayan an yi hotunan
tarihi da yawan rai.
LAHAIDI ita ce final day, da duk wani jan rai da
wahalarwar da ake ce Barista za dai a bashi matarshi, kuma
ita ce ranar da Hajiya ta cakare cikin atamfarta Super, ka ji
mai girman rata, take ta hidimar bikin autan mazanta
"Haske Maganin Duhu" Hauwa Gi. Lawan Muttuka, badakala dai ta Rare tuwon ne ko rice? Yau za ta
sallame shi ya yi gaba can Sharada Kwanar Cianduje, inda
ya dandasa gininshi fan karamin gida mai azabar kyau, to
Allah ya sa alhairi.
A Bangaren amarya Amma da Ummi suma dai yau
ne suke gwangwaje shagalin bikinsu na 'yar 'ya mai rabon
ganin badi ko mai ta hadiyo? Matar da ta je kanwar lahira
ta ga kannen azara'ilu ta dawo. Lallai ma gani, kila twintwince za ta fara bawa Barista a wata taran farko. Suma an
yi cikar mamaki, jama'a sun amsa kira an yi kara sosai,
taron wuni ya kare sumul, jama'ar da ba su zuwa kai
amarya suka ragu, yayin da wasu ma sai lokacin suke
Iekowa kamar makota za a tsegumi, Samira nawa aka jera
ko ba hakan ba ne?
Kai Allah dai kai mana mai nice gidan amaryar dai
amsha Allah, ango ya bugu dangin amarya sun kwalu,
kowa ya tatse aljihu ya yi kuka, don kawata gidan ni wata
haduwar ma ido kawai nake ba ta. To ban san ko me ye ba,
bare na fesa maku, sai dai na ratse kitchen inda na lalace
don kiris ya rage na zaci a Cedi-cedi and Sons nake sai da
na ji an rafka guda, sannan na farko, abin da na ce, 'Kai
Masha Allah, Allah dai nima taimake ni ka ba ni 'yar
budurwa man mai albarka, kyakkyawa, ka arzurta ta da miji
nagartacce, wanda ya san ciwon kansa. Amin, don Allah
kumá ku ce, do ni gidana cike yake da president, governor,
minister, and commisioners, ai kun gane ko?
Karfe goma aka kawo Sakina gidan fama, ta tsarkake
kanta tun a gida da alwala, don haka cikin tsarki ta shigo da
kuma Kafar dama. Jańa'a suka rfka guda dangin miji da ke gidan suka tabbatar ta sun ta iso, sai su kai zumbur don
girmama ta, da taran Excellency kamar yanda Brista ya ce.
51
"Haske Maganin Duhu"_ lauwa G. Lawan
Kowa ya yi nasa guri, komai ya yi tsit. Gidan sai
Ramshin sabunta, saboda kaya sabbin ma'aurata. To Allah
ya sa a sabunta sabuwar rayuwa mai cike da haske ba duhu,
Barista da 'yan abokansa uku suka rako shi sayan
bakin al'ada, sun sayi fuska dai bakin bai samu zayiwawa
ba, amarya ta kudundune kuke take yi, kun ji gulma bayaа
ita ce a da mai karfafawa ogan gwiwa ga kuma reshe ya
juyc da mujiya? Ai dama haka ne idan giji ta zo kuma sai
aeman sauki yanzun bayani ya rage na Barista.
Ya rasa inda zai sa ranshi, bakin nan wasai you dai
kanwa ta kar tsami. Allah ya mallakamar Sakinarahi. Yo yi
wa abokan rakiya bayan dan shakiyancin da aka sabana
al'ada, sannan su kai masá fatan alhdiri suka tafi.
Ya shigo cikin aminci, inda ya bar ta nán take sai dai
ta bufe fuskarta da gani, kuma ta ci uban kuka. Ya zauna a
kusa da ita ya ce, 'Sannu dai Sakina ya gajiya?"
"Lafiya lau." Ya dan rike hannunsa ta yi' saurin
janycwa ya yi murmushi ya ce, 'A'a excellency har yau
ma?" Ta harare shi ya ce, 'Na gane, amma kafin mutattauna
tashi mu je mu yi sallar godiyar Allah yau fa kin záma
tawa." Da kyar ya lallaba suka yi sallah an dade ana godiya
ga Allah da ya kawo wannan rana, mai tarin albarka da
tarihi.
Komai ya lafa har an sami sake inda ake cin yar
kazar nan da lemun amarci, ya yi kokari kwarai wajen
hilarta, har ta saki ranta ta tsakuri abin da ya kawo. Suna
hira jefi-jefi, har suká gama. Ya ce, 'Todan tashi ki yo mini
kwalliya da daya daga cikin kayan barcinki musamman
wannan jar rigar." Ta dan sha kunu, ta ce, "Ni ba zan zo da
su ba" Ya share kamar bai gani ba, ya ce, "Ai ko kamar dai
na ga an kawo miki akwatunanki bari mu ga." Ya mike ya
52
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
dumfare su, ya bude ya lalubc rigar, ai ko ya samu
mutunin nan ya daukota ya matsa dole aka sa, daga sawar
nan ba a Karc Kalau ba. Duhu sai na budo haske.
Ban muku tsegumi ba, Barista fa da 'yan'uwanshi
sun yi kokari sosai da sosai sun wa Sakina lefe mai kyau
daidai su, akwatunta saiti guda-guda da kit, turmin kayanta
hamsin cif, su Super nc, England, lesis, Galilas, da
materials, sai mayafai da Undis su ma masha Allahi duk
classical ba na banza. To Allah ya sa rai ya more abinsa.
Amin.
Barista Muttaka Lawan Kofar Nassarawa, shi ne da
na goma sha biyu a gidansu, kuma a cíkin maza shi ne
Karami. Mazansu su takwas ne, matansu su biyar. 'Ya'yan
Hajiya Uwa su tara ne, maza bakwai mata biyu, autar ita ce
Maryam. Ragowar 'ya'yan hudu na uwargidanta ne wacce
Allah ya yi wa rasuwa da dadewa, mazan ta uku mace
daya, to ga zuriyar gidansu maza ne suka fi yawa.
Alh. Lawan shi ne mahaifinsu mutumin kirki, wanda
ya shirya rayuwar gidansa cikin soyayya da aminci, da
wayewa, domin wayayyen mutum ne dan kasuwa, wanda
ya yi kasuwancinsa a ciki da wajen kasar, don ita Hajiya
Uwa 'yar kasar Salo ce, mahaifinta dan can ne, kasuwanci
ya kai shi garin ya auro ta, ta zo ta zauna cikin aminci
karkashin jarumar uwargidanta Hajiya Baraka, to da
albarkar 'ya'ya sai a kai rayuwa mai inganci maí cike da
rufin asiri mai yawa.
a
Duk 'ya'yansa ba wanda bai yi karatun boko da na
Arabi ba, don haka yawancin 'ya'vansa manyan ma'aikatan
gwamnati ne. Yaya Musa ne kawai babban dan kasuwa
Kwanar Singa, amma yawanci daga Dircctor, sai manyan
officers. Rayuwarsu gwanin sha'awa da zumunci da hadin
53
a
"Haske Maganin Duhu"_Hauwa G. Lawan
kai mai yawa, ba ruwansu da wani 'yan ubanci ko wani
bambanci, to kowa na rayuwarshi cikin rufin asiri ba mai
nema gurin wani, sai dai idan hidimarsu ta samu sai su
hadu su rufawa juna asiri, sai ka ga komai a can a can.
Kuma komai daya zai godanar 'yan'uwan na sani, tun kafin
baban ya rasu ya fito da tsarin mitin duk Lahadin karshen
wata, inda dukansu za su hadu a ci abinci a gaisa da juna, ai
hirar zumunci a kuma tattauna matsalolin da ke da akwai.
Wanda yake da matsala a taru a warware ta a cikin
gida ba tare da wani ya ji ba. To wannan gini da ya yi har
yau bayan ranshi hakan suke yi, shi ya sa aka hada karfi da
karfe a aurar da Barista, yanzun Maryam ce kawai ta rage
auta a gidan ita ma Allah ya ba ta miji na gari. Hajiya kuma
ya ja da rai ta ga auran autan mata lafiya, kamar yanda ta ga
auran autan maza lafiya.
Da safe misalin bakwai Sakina cc zaune gaban
diresin miro tana lakutar mai kamar ba ta so. Barista ya
shigo ya dafa kafadarta ta wani kara marairaicewa, har da
'yan kwalloli a cikin idonta, ya kuma gigicewa.
"Come one, excellency, ki daure don Allah ko sallar
ne kawai ki yi ni na dau nauyin yi miki komai." Ta share
kwallar ya cc, "O'o pls ki gafarce ni, ni kuma yanzun ai sai
kin amince, daure ki tashi ki yi sallar lokaci na tafiya." Ya
ringa kokarin daga ta dan tawul din jikinta zai zame ta yi
saurin ture shi, ya ko matsa. Ta ja can gefe tana kunkuni,
ya yi dariya a ranshi, amma a fili ya ce, "Ban ji ba
excellency." Ta hada rai.
"Na ce kaya zan sa."
"Okcy, to bari na jira dai a waje, wannan ma lokaci
ne, wata ran ni za a kira na sa kayan." Ya yi mata gwalo ya
yi waje. Ta yi kwafa ta sanya kayanta cikin dauriya da.
54
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
karfin hali. A ranta ta ce tabdi wai dama ashe auran bala'i
ne? Heус amma akc ta rawar kai an ya zata jurc? Jíya ta
kusa shekawa barzahu, amma duk Allah da ta ringa ambata
bai ko ji sau daya ba. Kai lallai Barista mugu ne ashe dama
abin da zai mata kenan, shi ya sa idan ya yi mata kyauta ya
hana ta godiya wai toshiyar baķi ce, dama da sani ai.
Da ta idar da sallah ta ja jiki, kan gado tana can
kasar zuci ta ji hadari na ihu kafin nan sai ruwa ya goce mai
karfi, sai kawia ta rintse ido, ita ma barci mai karfi ya
dauketa.
Barista ko na can kitchen yana dafa mata ruwan
shayi da kwai, ya dunduma mata ragowar kazarta. Sai ya
samu tuni ta yi barci, ya kalleta cikin tausayi wani irin so
mai yawa ya yi gaba da shi. Sai ya koma da baya a hankali
ya juye mata su a cikin flasks shi kuma ya karbi shayi, ya
zo ya ratsata ya raba ya kwanta shi ma din dai barcin ya yi.
Ba su tashi ba sai bayan goma, ko da ta tashi sai'ta ji ta
samu relief sosai a kan da har tana iya hada kafafunta da
kuma wałwala ta farka sai ta sa hannu ta bubbuge shi. ya yi
firgigit.
"Ya ya my dear any problem?"
"Nothing rana ta yi fa, kar kuma mu zo muna yin
baki a taras ko barcin safe ba mu tashi ba."
Ya bararraje a gadon amarci ya ce, "Akwai mai bin
mu bashi ne? Kuma dama wa ke zuwa gidan amarci da
safe?" Ya janyo ta.
"To ya kike jin ki yanzun"" Ta hangaбе, уа сс,
"Haba dai kar ki kary a mini gwiwa man, you look freesh
yanda idona ya gani." Ta dan harare shi.
"Bari ni na shiga kitchen tun da kai kana nan." Ya jawo
hannunta ta fada mai ya cc, "Mc za ki yi?" Ta kashe ido.
55
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
"Abinci man ko ba ka da bukata?"
"Na gama miki karin kumallo excellency, bari mu je
kawai na baki." Cikin shagwaba ta cc, "Lah! Ogana kai ne
ka yi da kan ka maimakon ka huta?"
"Ke duk aikin da ki kai daran jiya, yau kuma don
rashin ga ta da so da tausayi sai a kara miki wani? Ai ki
bari kawai sai kin dausashc, sai kuma mu yi handing over."
Ta sa hannunta buge shi su kai dariya. Shi din ne ya ciyar
da ita abincin, har suka koshi, a tare su kai dan gyaregyaren da ba a rasa ba, ya yi kwalliya haka ita ma, sai suka
kuna turaren wuta, su kai zaune a falo ta nade cikin jikinshi
shi kuma ya ci gaba da riritata, suna kallonsu suna hirar
soyayarsu. Misalin sha biyu ragowar 'yan biki 'yan gidansu
suka fara zuwa, sai ya yi sallama ya fito nemo cefa ne, don
yin girkin amarci.
To haka dai suka ringa kwankwadar amarci, suna
ririta junansu har ba sa son wani abu ya zo ya ratsa su. A
hutun amarcinsu ya kai ta gidan Hajiya sau biyu daya da
daddare daya kuma wuni guda ta yi, aka ringa zagawa da
ita gidan 'yan'uwansa cikin unguwa tana gaida su suna sa
albarka, ana lallai Muttaka ya yi sa'ar amarya mai kyau,
saura kyan hali, shi ma ana fata. Lokacin da ta shiga gidan
Anti Hauwa nan ne tafi sakewa, don ta same ta warkan da
ita, kuma tun kafin ma ta zo ta sha samun sakonninta, don
haka mafiyawan zama a gidanta ta zauna, sai da Muttakan
ya dawo suka koma gidan Hajiya a can su kai cimar 'dare
shi ma din dai na Hauwa ne.
Rayuwar amarcinsu mai dadi, har ya gama dan
butunshi na amarci ya koma aiki, ita kuma ta ci gaba da
zaman gida tun har lokacin ba a gama sassantawa da
malaman jami'a da gwamnati bare a janye yajin da suka
56
"Haske Magunia Duba" Manwa C. Lawan daka suna hambuda. To Allah ya kyauta.
A wannan lokacin ne barista ya cc, "Ki dai y addu'a
wasu 'yan canjina su gama hafuwa a samu 'yar karamar mota ko ta dari uku a saya kafin ku koma makaranta." Ta
Kankame shi cikin jin masifar dadi. Ta co, "Ogana anya ha
za a takura ba?"
"To toe ye you deserve that, kuma dolc ina da hali
haka za a yi saboda dai ba zan juri kai ki makaranta kullum
na dauko ki ba, saboda ni din mai sabgogi nc, wata rana ma idan na fita sai dare, to wa zai dauko ki? Karfina bai kai na
aje dircba ba, ya ringa mana wannan sintirin, rufin asirina
kawai a samu 'yar motar."
Та сс, "То Allah ya rufa asiri ya bada yanda za a yi.
Amin."
To rayuwa tana ta cigaba da tafiya ana ta samun
cigaba daga bangarori da yawan gaske. Masoyan na dafa
mannewa juna, kullum Barista ya tuna sai ya kara godewa
Allah da wadanda suka sace ta su kai sanadin haduwarsu
har ya ganta ya aureta.
Rannan da ta bashi farin ciki da ya ji dadi, kawai sai
ya burkitata ya ci kwalar rigarta, sai ta daga hannu sama ta
langaßc kai ta cc, "O! Na shiga uku, wane bashin kuma na
ci?" Ya yi dariya.
"Kullum zuba miki ido nake yi na ga ranar da za ki
biya, amma na ga baki da niyya, to yau ni na tambaya, sai a
bani na sha." Fuskarta ta nuna yanayin mamaki.
"Me kuma Ogana?"
"Tun sanda muka kulle nake baza kunne na ga ranar
da za ki bani labarin abin da ya same ki lokacin Gatanki,
amma ban ga alamar hakan daga gare ki ba, ni kuma yau na
shirya ji in kuma baki son gaya mini ne to na sani." Ta ja
57
Jaske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
fasali ta sauke hannunta kasa, ta cc, 'Oh, ni na zaci wata
abuwarce ashe ma bacin rai ne, ai fahimta na yi kamar jin
zafin abin kakc sosai wanda har ba ka maraba da jin
labarin, tun da sai ranka sai ya baci kake gwaba mini
zancen, shi ya sa ban yi karmbanin fada maka ba, tun da dai
ba abin.alhairi ba ne."
Ya cc, "Gaskiya ne hasashenki, kullum in na yi niyar
tambayarki şai gabana ya yi ta faduwa, ni kuma tsoro na
daya kar garin bani labari ki gaya mini wani ya cuce ni ya
shigar mini gonata, to gani nake wannan zai karya mini
zumudin da nake yi a kan ki, to shi ya sa nake jan bakina na
yi shiru, kar kaza da tone-tone ta tono wukar yanka
wuyanta."
Ta kalleshi wani iri, "To da kuma ka samun already
haka ta farun sai ka maida ni gida?"
"Haba-haba dai, hakuri kawai zan yi na cigaba da
sonki da tausayinki don zan gano kin ci azaba ba 'yar kadan
ba. Kullum kuma na yi sallah na ringa tsinewa wanda ya
cucan don ni aka kwara. To Ailah ya amshi rokona ya
hadani da salihar mace tsarkakkiya, Um hum! Ina jin ki."
Ta yi shiru lokaci mai tsayi, har kamar ba za ta yi
magana ba. Can kuma sai ta muskuta ta ce:
Wata rana, ranar Juma'a da safe, ina kwance na yi
juyi na kuma juyawa, raina ne a bace, idan na tuna karatu
ya taho gangara haka sakin ana neman tauye mu, kan ban
da haka na maye aka tsiri wani yajin aiki rana tsaka don
kawai a cuce mu? Sati biyu ya rage kawai mu shiga level
di0 don mun yi hutu, mun dawo har an turamu T.P. to me
kuma akė so? Na ja 'tsaki na kuma juyawa kawai sai na ji
zaman gidan duk ya gundure ni, dan tun da a kai yajin aiki
ina gida ban je ko'ina ba, ina ta hutawa to yau hutu na ji duk
58
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
ya gundure ni, kawai ai na mike tsidik na jawo wayata
samfurin I..G. na duba agogo sha daya da kwata, kai tsaye
na nufi bandakinmu, na yi wanka, na shirya tsaf. Na sami
Amma na ce mata yau dai zan je gidansu kaflin. Ta kalli
aggo, amma dai kin dau rana ga shi kuma yau Juma'a ba
kya tsoron go-slow din 'yan masallaci. Na ce, "Amma kafin
ai su fito na kai da sauran lokaci sai dai idan mota na rasa."
Та сс "Тo Allah ya kiyaye a gaida su Ummanta."
"Za su ji." Na amsa na fito. Ashe tsautsayi nc ya
kirani ya fito da ni daga gida, dama mutuwa na yi haka za a
ce tana kwance fa ta tsiri tafiyar. To komai da Allah ya ga
dama shi yake hukuntawa a kan bayinsa, mu dai na mu
mika wuya ne kawai da fatan dacewa.
Na a fitowaje na shaki iskar waje na ji wani sanyi
raina, amma can kasan zuciyata ina jin wata sarewa kamar
zan lossing ban dai dawo ba na ringa tafiyata a hankali. Har
na fito titin Isyaka Rabiu na shallaka a hankali na yi tsaye
jiran mota.
Kamar da gayya motar Jakara shiru, ta fito daga
dabai mu samu ta tafiya shiru, ga uwar ranar bazara, ga shi
ranar Juma'a lokacin hudowarta. Ina nan tsaye ina raba ido,
tsakanin karya da gaskiya sai ga wata plashing car ta wuce
idona kamar walkiya na bita da kallo a raina motar ta yi
mini sosai kalarta dark blue, ilonda new mode/. Na ce kai
masu kudin nan suna hutawa, to Allah ya ba mu mai
albarka na halak. Wallahi kamar kiftawa da Bismillah, sai
kawai gani na yi motar tana dawowa baya a hankali, na
juya baya inga wanda takewa ribas, ban ga kowa ba, ni
kuma lokaci daya sai na shiga nutsuwata'na dauke kai daga
kallon kurullar da nake mata. Ta yi parking daf da ni,
gilashin motar ya sauki shuu, wani inatashin yaro ne sosai
59
"Haske Maganin Duhu" _IHauwa G. Lawan
wanda kudi da hutu sun gama huda mishi jikinsa,
kyakkyawa mai hasken kala, sai dai ba fari ba nc da gani
hutu ne dai. Cikin sanyin murya ya cc, "Assalamu
Alaikum." Na kasa kin kula shi, na amsa ba yabo ba fallasa.
Sai ya balle motar ta shi ya fito hannunshi rike da wani dan
carbi yana ja. Ya matso kusa da ni ya kuma mini sallama,
na amsa, ya ce, "Ba ki jin rana madam, ranar fa ta bude
sosai."
"Eh ina jiran motar Baban kowa ne yanzun zan bar
gurin da ikon Allah."
Ya ce, "Haka don Allah idan ban miki shishshigi ba
mc ye sunanki?" Yana tambayar cikin yalwar fara'a. Na yi
dan gajeran murmushi na fada mishi, shi kuma ya gayan su
nansa Falalu. A raina na ce, tabdi kai daban sunan daban
me ye wani Falalu? Hira mai yawa muka yi inda ya gaya
mini shi din dan kasuwa ne da yake safara tsakanin Kano
da Legos, yana kawo kayan da suka samu komai ya zo kasa
siyarwa muke yi, har ciniki dala ma yi suke na ce, to da ya
gama zukanin ya ga kamar maganar ba ta gamshe ni ba
bare wannan ya rude ni, sai ya ce ina jin dai Sakina kin
fahimci abin da ya tsaida ni na 6ata lokaci a nan ko? Kin
san 'yan magana na cewa in ka ga kare na shinshinar
takalmi dauka zai yi, gaskiya sonki nake yi da kuma aure,
har na wuce zuciyata ta ringa gaya mini ga matata can
uar 'ya'yana na gano. nan komo da baya. Zancen shi sai
ya ban dariya, kai in gajarce maka labari har sai da na bashi
kwatancen gidanmu da komai da komai. Ya amince zai zo
yan da daddare. Bayan nan ya ce, "Sakina tun da motar nan
da ba ta samu ba, bari kawai na kai ki, sai na zo na wuce
masallaci kar na rasa Juma'a."
Na ce, Wallahi ba komai, kai wuce warka kawai ni
60
"Haske Maganin Duhи" _ Hauwa G. Lawan
tafiya ta ba mai zafi ba ce Jakara na a cikin gari kawai na
nufa." Ya cc, 'Shi kenan ma hanya ta ce, ni din Makwarari
zan shiga ba sai kawai na aje ki ba." Na kafe ba na shiga
lift, ya kafe sai na shiga a cewarshi wannan din in Allah ya
yarda motar mijina ce. To rabon kaddara sai kawai na
saddakar na shiga don kar na bata mishi lokacin masallaci.
Ina shiga motar wata irin tsigar jiki na ji, amma sai na
alakanta hakan da sanyin rabar da na ji a cikin motar ni da
na fito daga rana. Ashe abun ba haka ba ne, komai da zai
faru lokacin ne ya faru. Ina ji ina gani aka wuce kwanar
shiga Jakara aka karya kwanar hanyar makabartar dan
Dolo, a kai cikin unguwar Tudun Yola daga nan aka dau
hanyar Kauyan Bajallabe, to daga nan ne kuma na rasa saiti
komai da za a yi ban sani ba, ban kuma sanin ba, sai !
okacin da na farko daga barcin dole zan yi juyi a tunanina
ina kan gadon Amma ne sai na ji ni a tsandaurin sumunti,
nan da nan tunanina ya dawo na bude ido da sauri, sai gani
na na yi a wani daki ni da wasu yara kanana uku da wata
mata mai goyo sun tsura mini ido.
Gabana ya yi wata irin mummunar faduwa, don
tsabar mamaki na tashi da sauri na ce, "Ina ne nan?" Yaran
suka fashe da kuka, cewa suke Anti ki kai mu gidanmu za
su kashe mu sun kashe baby. Kai ba sai na yi wata
zanbarma ba, kalamansu sun dawo da ni nutsuwa sosai, na
fashe da wani irin kuka na tsananin tsoro da nadama, amma
lokaci daya na toshe bakina, hawayc ne kawai ya ke ta
zubowa, na yi kuka, kuka mai isa ta, har ina jin kuma na
sare' garama kawai na vi shiru na kuma zuba ido na jira
hukuncin Allah mai girma
Mu kai wuki-wuk da mu har lokavin da dare ya
raba ni da matar nan ne kawai ba mu yi barci ba, ni tunani
61
"Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan
nake ita kuma tana ta kokarin jijjiga yarinyarta da ke son
yin rigima, don ma 'yar mai tsananin hakuri cc, ban ji ta ce
komai ba, tun da na zo, sai ko yanzun illa dai makale take
da nonon uwar rai-da-rai tana tsotsa uwar ta yi wani irin fita
daga hayyacinta. Ina tausayin kaine amma taukys matar
nan da yaran nan ya kashe ni kawa. Kai lallai lahıra da
kallo, irin wannan rashin imani karara?
Na muskuta ina ta kallonta har 'yar ta samu ta yi
barci akan zanin goyansu ta yi ajiyar zuciya mai karfi, sai
kuma ta matsa gefe ta jingina da bango ta runtse ide, ina
ganin la66an bakinta na fahimci addu'a take yi. Wannan sai
ya tunasar da ni addu'a, ni da nake da yawan addu'a, amına
bala'i ya buga mini kai na manta da komai.
Cikin sanyin murya na ce, "Ke kin dade a nan ne?"
Ta dago kai ta bude ido karo na farko da mu kai magana
tun da nan dira a gidan. Ta ja fasali ta ce, "Yau kwanana
hudu da shigowa gidan nan, kuma a cikin kwanakin a
daukc mutum hudu a fi da su ba a dawo da su ba, ciki
har da 'yar yerinyar da aka sato wadannan yaran tare da su.
Mu kam muna cikin bala'i nu babba, kila kwanakinmu ya
kare, kila kina taimakon Allah da Rahamarsa su sauka ta
inda ba mu zata ba, wannan ikon ne, ga Allah idan ya ga
dama zai yi yande yake so." Na gyada kai na yarda da duk
abin da ta ce. Na cc, "Ke din waye ya kawo ki?" Ta ringa
gırgiza kai tana hawaye, tabbas abin da za ta fada mai ciwo
ne. Ta cc, "Hmn! Ni din mutuniyar Katsina cc. amma ina
ziunenan Kano, saboda karatu da nake yi nan Kabuga
dab gidan Biredin Kowa na So. Jin da na vi an cc ana
y.wan sacc-sace a Kano, kuma an