Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 10
suka tafi." "Da kyau kin ga abin da nake gaya miki ko? Kila dai wata matsalarce ta 6oye shi, ya ku kai da shi?" "Lafiya lau, shi ma din abin da ya ce kenan, wai ba na tsoran kuma abin zai kara sa ni fita. Na ce, yaya Muji ne ma fa ya kai ni." Ta ce, nan ma haka kanwar tashi ta ce mai kirki kuwa, wayayya." "Wallahi Amma ai na santa haka sama-sama dai makarantarmu daya sai dai na fita da shckara daya, kuma karatunmu yana da alaka da juna." "To da kyau Allah ya kula alkhairi ya sa haske a cikin lamarin, amin." Ta amsa a ranta, amma sai ta yi- saurin matsawa daga gaban Amma. Tun bayan sallar Magriba take baza kunne ta ji aike har bayan karfe goma, sai ta saddakar bai sami zuwan ba ne, ranta ya yi mata wani iri, ta lashi zumar fa mai zaki, dole ta kudundune a gadon Amma rungume da waya tana wassafa shi a ranta wannan lunanin sai ya sakar mata barci mai dadi. Cikin barei ta ji wayarta da 'ke karkashin pillow tana ringing, ta yi firgigit ta tashi, kowa-a dakin ya yi bari, Amına kuma na dakin Bat an. Ta awo pillow sai ta ga sunan Maryam. Muryarta ta yı sanyi kwarai ta amsa, "Hellow Maryam kun je gida lafiya?" 36 "Huske Maganin Duhu" Mawwie , Lawan "Ke Maryane ce za ta kira around this tim, e za la ee miki? Kin kalli agogo ko Karfe nawa?" Ta kuma ym cooling ta ko kall agogon ta ce. "Biyu da rabi." Ya ce. "Good, yanzu lokacin soyayya ne Ya na ji ki socondkokm yi barci ne na tashe ki?" Ta kuma muskutawa ta rike wayar sosai ta ce, "Ni ko mai zai hana ni barci har zuwa wannan Jokacin? Tashi dai na yi da ka kira." Ya ce. 'Ni ko kin ga soyayyarki ta hana ni barci. yanzun haka tangararau nake, bayan na gama rubucс- rubucena ma Film nake kallo yanzu, na ce to bari na tashe ki mu gani tare ko ma raya daren tare." Ta yi dif. ya се, "Kin yi shiru'?" "Me zan сс?" "Au! Ba ki ji abin da na ce ba, na maimaita?н "A'a na ji ka sarai, amsar ce dai ba ni da ita." "Ko? Гo пi ina da abin fadi, kin san yanzu mai jarumin film fin da nake kallo yake wa budurwarsa?" 'A'a." "Na gaya miki?" 1a yi shiru. Ya cc, 'In ba ki so ki hana ni in ba háka ba zan ada." Ta yı dan mumushi yana jinta la ce, "To ka yi-hakurı." "Na yi wallahi, don abin da girna a gunki, ni din ha komai ne a guna ba, saboda dai na biya sadaki, kuma ni ji nake ma ina ma-taré da kemake Karkashin mayafi daya." Tạ ce, Sai da sate." Ya kyalkyalo die dariya va de "Ke ashe matsoraciya veke Aia kiwaflai ban лаба soyayya ba, thon naka zluk soyayyata hakuri za ki yiki dauka. don duk akan ki zan Kare Kartina na f hude wuta sai hakuri." Ta ja fasali ta ce," To shi kenan "Yanzun in hakura in bar ki ki yi barein su kama na "Haske Magunin Duhn" Namwa C, Lnwa "Kin yi shiru, kin amince kenan?" Nan ma shiru Ya yi dariya ya ce, "Matsoraciyar soyayya, bari na Kyale ki tun da ta Kare miki." Ta ce, "Haba dai ogana na dai Kyate ka ne." "Au! Haba bufe mini mayafim ki to na shiga." Ta Kyalkyale da dariya ta ce, "Good night." Ba ta jira mar za1 ce ba ta kashe wayar. Zuciyarta ta ringa bugawa da sauri da sauri. saboda tsananin jin dadi na soyayya, abin da take matukar bun ga mijinta ya so ta ya rirıtata, ya koyar mata soyayyarshi mai dadi, ta ko samu. Kai godiya ga sarki Allah da iyayenta da su kai hikimar ba ta shi a matsayin mijinta. Wadannan tunanc-tunanen masu dadfi suka saukar mata da barci mai dadi da nutsuw a, har ya so makarar da ita sallar Asubahi sai da aka fito masallaci, sannan ta farka ta shiga bandaki ta tsaftace kanta ta dauro alwała ta zo tana sallah ta dade tana sujjada tana Kara godıya ga Allah ga ni'imar da ya yi mata da wasu bukatu a kan shi. Da safe da kuzarinta take komai, rabonta da cikakkiyar walwala irin wannan tun kan a sace ta, donin da ta dawo wani irn sanyi ta yi komai ba ta taba za fafa shi, ita da ta riga ta sallama. Ba dan ila din mai addu'a ba се. kafin dasbayan abin ai da ta zaue ko kuma kafin ta dawo daidai a raya, irin abubuwan da ta gani. Kowa ya amince farin cikinta da raharta ya dawo. saboda soyayyar Muttuka. Da rana misalin sha biyu. ya.o bai shigo ba ya aiko da kan waya Starcom sabuwa lal yu се a bata zai dawo da daddare, ta arusa da farin ciki nmai yawa ta nunawa su Amma da Ummi stna sun yi farin cıki. dauma tun jiya aka tsaiguntawa Baban zıwan Barista tun da hat an lara Korafin bai zu ba, shi dfin shiru ya yi hai ce kumau ha. 38 "Ilaske Maganin Duhu" _ Hawwa 6. Lawan har ta g ana tsegumi ta fita. A ransa ya ce mata kenan ma duniya. Da yamma ta bayar aka sayo mata kayan ciki mai kyau, ta yi masa farfesu da dankalin turawa dakwa-dakwa Ai ko kamar a unguwar ya yi sallar Magriba, don ana idarwa ba dadewa ya aiko. Amma ta cc, "Wannan dai ko tuwan dare dai bai tsaya ya ci ba." Ta cc, Ba sai ya ci wannan farfesun ba." 'Au! Barfesu abinci ne?" Ta yi smilling. "To Amma ai tuwo ku kai, yanzun sai kawai na lafta mishi tuwan dawa na kai masa?" "To me yc, tuwo ba abínci ba, an gaya miki kowa ke ce, da ke gudun tuwo, kila shi a gurinsa ya zama abincin marmari." Ta taбc baki. "Ni dai bari na je idan zai ci sai kawai na dawo kar na yi kayanshi na dawo da shi, kin sanfa 'yan yanzu ba kamar ku ba ne, wani baya son cin mai nauyi da dare." Ta cc, "Allah ya kiyaye Sakina." Ta gama shiryawa da atamfarta Super England wacce ta yi mata Nevia ro!! on dinta sure cool blue, sai powder ta beauty fair, sai uma turarenta da take mayaia Lailatus Sahra. Ta yafa gyale ma hadin kayan, ta yi kyau kamar yau ne dai za ta shiga dakinta. Ta tura Aisha ta kai masa abin da ta shirya masa da dan lemunta na zo6o. Yz ko ba ta kudi ya ce su raba ita da Kannenta. Ta yi sallama dakin Muji a nan a kai aro za a soj r. Yana kishingiufe sai yá tashi zaunc, yana cowa 'Ati lale a amaryata kın yi kyau, kamar in saki gaban mota in ta yawo da ke." Ta vi smilling mai kyau da yake kawata fuskarta,:a je gabansa ta dan rankwata tana ganda shi. Ya shaki Kamshinta ya cc., "Kai na gode duk Allah "IHavke Maganin Duhи" Haun 6. Lawu dadada mini rai, ya kin wuni lafiya?" "Lafiya lau, ya su Hajiya da Maryam?" "Duk lafiyarsu lau, suna gaida ki har da Antic Hauwa ma." "Waccc kenan?" "Matar Yayana da na fi shiri da ita." "To ina amsawa ya gajiyar aiki?" "Gata nan, amma ai an fara kawar mini da ita, jibi fa irin kwalliyar da aka mini." Ta yi murmushi ta zauna soxai ta janyo tire din ta ce, "Bari na ba ka wannan kila dai ba a tsaya an ci abinci ba." Ya ce, "Kamar ko kin sani na ranas mu dai snacks kawai na ci." Ta tsaya da bufe kwanon ta ce, "Haba dai ya zama da yunwa irin wanna?" "To ya za'a yi kai ka katangala rai ba gata, sai sanda ka samu sukuni dan abin da aka girka a sammaka, in bai maka ba duk ka ita gari nema." Ta yi jagale. Ya сс, 'Ai gara ki yi, ki yi ki zo ko ura dai na zama dan gatan nan, a daina mun gori duk inda nt je neman abinci. Allah tsine ranar da Hajiya ba za ta yi mini gori ba, hakuri kawai nake yi tun da na san ba mai ba nhi." Ta yi dariya ta ce, "Har da Hajiyar?" Ya пкс hабa. "Tabfi! Ai gara kowa ma da ita Hajiyar, ke dai bari kawai garama na koshi, yau idan ta yi mini tayin abinci na ce na ci a gurinki." Ta yi dariya. "To ai ni wannan dai ba abinci ba ne, abin washe baki ne, amna dai a gida sun yi tuwo Amma ta ce na zubo maka, ban zubo ba, bari na je." Ya yi saurin daga mata hannu ya ce, 'Aa wait, wane irin tuwo?" "Na dawa." "A'a kaı bar shi, ba ni wannan din ma kawai ya isa." Tå sunne kai tana dariya ta cc. "Ba dai kai ma arne da cot (fin nan baya cikin 'yan kayanka ba?" Ya ce, "Ke dai bari." 40 "Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan Ba ta labarin artabunshi na tuwo da su Hajiya, su kai ta dariya ta zuba mishi: farfesun, ya fara ci. Ta ce, "Bari na zo." Ya ce, 'Kar ki dadi." Ta yi murmushi ta fita tana shiga gida ta gayawa Amma abin da ke da akwai ta ce, To me za a ma shi ina da guntuwar miyar rana, na san za ta ishe shi cin abinci." "Amma bada kudi a je kantin Isuhu a sawo kus-kus leda daya, sai a dafa da sauri." Ta ce, 'Shi kenan je ki." Yana ta zukar rumanshi ya yi mishi dadi, ta dawo. Ya ce, "Zo nan mu ci tare." "Na gode na koshi." "Au! Haka za ki ringa mini kina cinye abincin kina kylale ni?" Ta ce, "A'a, ka yi hakuri ba zan kuma ba." "Na yi." Ba a kai minti ashirin ba, sai ga kus-kus ya sauka, yana tururi, ya ce, "Ke wahala ki ka je kika sa mutane?" "Haba wahala ka manta kai din dansu ne da suke ji da kai?" "Eh ban manta ba, duk da haka kamar an takura." "Ko daya wallahi." Ya ce, 'To na gode kwarai." Ta jawo ta fara zuba mashi. Ya ce, 'Ba kuma isa ba, sai kin matso mun ci tare, don wannan dai yanzu ya sauka bare ki ce kin ci tuni, kuma a filet daya za ki zuba" Ta ce, To Oga." Ta zuba kus-kus da miyar a tire ta samo cokali, ta ringa hilatarshi suna hira ya ci sosai yana haduwa da fef-suf din shi, ya koshi sosai, har ya ringa jin kasala da barcin bayan koshi. Та се, "Кo na miko filo ne?" "Haba dai idan na yi miki barcisya zaki yi da ni?" "Sai na lullube ka na yi ta gadinka, har sai ka tashi." 41 "Haske Muaganin Duhu"_Hauwa G. Lawan Ya yi dariya. "Na Ki wayo; so kikc na bar tarihi a ce nan da yana neman auranta har barci yake musu à gida." "To maye duk a cikin so ne.", "Haka ne, to zo matso ki yi mini tausa mu ga ko barcin zai zo." Ta yi saurin ja baya, har abin ya bashi da ya ce, 'Kin ga dadina da ke baki da jarumta, da ni ce ke zuwa kawat zan yi mc ye a cikin tausar?" "Ba komai, ba sai na zo ba, na amince ni fin oa ni da jarurata." Ya ce, 'Gaske kuwa." Sun yi hirarsu mai dadi, har kusan goma saura kwata ya сс, "Вari na tafi, sai kuma na kira midnight call, kin san ai ba iya barci zan ba, tun da kuma ke kin shigo system din." "Haba dai ka yi hakuri ka yi mini, rashin barci illa ne da shi babba, gshi da safe ba samu za kai ka rama ba harkokinka za ka fita.' Ya ce, "Shi kenan na ji ko kokenki za a duba mai yiwuwa." Ta yi masa rakiya har gurin motar shi, ya bude ya dauko mata leda Viva, cike da kayan shafeshafe da dan na kusa da baka. Ta ce; "Haba baka gajiya ne, hidima dai dazuma fa na ga waya ko godiya ban ba." Ya tabe baki. "Ke kin san ko irin dadin da za ki jiyar da ni, ki ke waint surutu dan ra kawo wannan? Toshiyagbaki ce fa, ta yanda za a ringa lri na ina ta iyo a cikin ruwa yanda nake so." Ta yi saurin dafe fuska, zancen ya girmi kakarta, ta mika mar wayarsa, ya amsa ya dungura mata ledar ta amsa bashi griri, ya bige d "lasoraciya sat da safe, ai mafarki mai kyau, amına kar amin rowa, a dan buda mini." Ta yi saurin juyawa tana daya hannu ta shige gida, sai da ya ga shigarta, sannan ya ja mota cike da 42 "Haske Muganin Duhu" farin ciki ya tafi. Hauwa G. Lawan Ta shiga gida ta aje kayan, sannan ta dawo ta tattara kwanokan da ya ci abinci, ta shiga/gida da shi. Muji ya ce, "Ya dai tafi ko? Ni barci nake ji." Ta ce, "Ya tafi an gode wallahi." Ya ce, "Ba wani an gode miko ledar za ki yi mu ga, mai kuma mutum zai samu a ciki." Amma ta ce, 'Wannan dai halin banza ne haka girma yake?" Ya ce, "Umum Amma kar ki ce komai, idan na hana dakin nan fa haushi za ku ji ai ko gara nima a ba ni toshina kawai." Ta zazzage kayan gabansu, set ne na kayan shafa Niven kamar ya san irin su take shafawa, sai Dove shima set här da turarensa. Sannan biskit da alawas masu dadi da inibi a ledarsu nunannu. Ya dau biskit daya da alawa ya fasa ledar inibi ya diba, ya ce, 'Sai da safe." Amma ta harare shi ya yi dariya ya yi gaba. Ita ko sai dariya take ina ruwan sakis gonar auduga akwai fara'a kamar ni a gari. Ta rarrabawa kowa kayan kwalam, kayan shafawa ko ta kammale kayanta a daki, ta yi barcinta mai lafiya. Bai ko kira din ba. Da ya je gida su Hajiya sun rufe kofarsu sai kawai ya kulle ainahin kofar gidan ya yi addu'a ya je ya yi sallar Isha'i da Shafa'i da Wuturi ya yi addu'a ya kwoa da tunanin uwargidanshi à ransa. Wani irin hasken su ke haskawa a ranshi har kamar ya faso kirjin ya fite. Yo ringa tunanin ashe haka so yake? Lallaí a ringa ganin bekensa da ya gaza to ina kuma gaya ci harawa ya yi birgima a cikinta? Wayyo da wannan sambatun wani irin barci mai dadı ya yi gaba da shi. Bai aje shi kusa ba sai a fadar Sakina tsundum. Soyayya ruwan zuma, in ka sha ka ba ina masoyi. Allah ya hada kowa da masoyinshi na alhairi. Amin, ('Yan mata a yi kokarin tsarkake soyayya don ta yi danko ta yi 43 "Haske Maganin Duhu" Hauwu G. Lawan inganci'in an je fa. Ni da kaina zan bada tsaraba don a mocc ta da kyau. Dariys). To haka dai, wata irin soyayya mai danko ta shiga tsakanin, wanda har absa iya boycwa ko a gaban waye ne. Fadi take Ogana shi kuma ya ce Excellency ta ce kaza-wakaza. Har dai rannan Amma ta ce, "Ba dai kya ko jin ku. a Sakina gaban kowa fada kike Ogana-Ogana, sai ki nu mini wanda bai d Ogan?" Ta sunkuyi da kai wata kımya matsananciya ta ratsata ta ce, "Ki yi hakuri Amma. Ta ce, 'A'a ke kadai, ni me ye nawa? A dai ringa farsa baki." Haka abin yake shi din ma Hajiyar har mamaki take wai yau Muttaka nee gigi a kan mace, abin da baya kayansa, ta dai ar ace iokacin ne dai kamar yanda ya sha fada mata. Kornai Saki.a z2 ta yi sai Oga ya sani ya bada approval, in ko fita ce in ta furta tana san zuwa guri kaza ba musu zai anince in lekacin ya yi masa to sai ya yi kokari ya kai ta, in kuna yana da ta shi sabgar ne sai a sa wani lokacin ya kai ta. Dukkan 'yan uwanta sun san shi farin sani, da ke kuma shi ma mutum ne wayayye, najama'a, mai sabgar jama's. ya sa ko'ina ya shiga sai an kas6e shi, an kuma yaba ra shi tko ...a. Kyakkyawa da shi, gogagge, kalar kya. dai liasawan da sıka sami nutsuwa da kwanciyar ankali. gashi da dogon hannu (Kyauta). To wannan ya a yake da farin jini sosai. Hakan abun yake a gurinta, ba ta aje shi kusa ba, Kaunarshi Lke sei a ganinta bayan iyayenta ba mutumin da ya san darajarta nye d shi. Ko: Kuma la haka ne? Don haka dukkansu s amine: su du. hadi ne kawai daga Allah. A zuciayr ta da take tunani idan ta aure shih ta huts da takaicin dai duniya, kui... haka ne, yayin da 'ya mace "Huske Maganin Duhu" llauwa G. Lawan ta yi sa'ar namijin kwarai a kai sa'a ita din ta san darajarshi sai su mori rayuwarsu mai kyakkyawan inganci. Ku ji ni da Sakina na ta sambatu ta ji gardin soyayya, ta dauka da son soro da nan daki are ekual a ina? Bari dai ma ji ma gani an bunne tsohuwa da ranta. Komai aka samar to dole ya zama kararre, illa Ubangiji wanda yakc (Al-Hayyu, Al-Kaiyumu). wanda mutuwa ba ta karshensa, farkon da bai da farko, haka kuma Karshen da bai da karshe. Allah kenan. Lokacin bikin ya karato sosai, har ya kasance sauran kwana ashirin da uku, wato tsayin sati uku da kwana biyu, a yi abin. Yayin da masoyan ke ta nuna maitar junansu a sarari, har gani suke anya ko za su kai l abari irin wannan zumudi ko dai iyakarta kenan? Wannan ce damuwar da Barista yake yi a wani dare da ya zo mata da katiunan daurin aure. Ta ce, 'Haba, Ogana mantas kawai da ranka da lafiyarka za ai komai har ma ka girbi abin da ka shuka da hannunka. Kana mantawa da Allah ne da sanya so da ki a doran kasa, duk fa albarka so ne mu, domin karfin son da Allah ke wa Rasulillal (S.A.W.) shi fa muke dangw ala." Ya ce, 'To Allah ya sa muna raye amin." Ta gyara zama. "Ni dai tsoron dai da nake ji daya Barista a wayi gari ka daina sona, ka daina shagwaba ni, da riritani, to ina zan saka kaina?" Ya ce, "Au! Kina shakkar son da nake miki kenan?" Ta girgiza kai alamar a'a. Ya сс. "To trust me my dear edcellency zan baki mamaki, ke kin ko s.an amfaninki gare ni?" Ta cc, "Na sani, wai lokacin da ka gama tsotsewa aya zakinta ba tofar daı tukar za kai ba?" Ya cc, 'Eh to haka ne, ba haka ba, ya danganta daga wanı zuwa wani, wanı da ya tsotsen sai ya tofar, vani ma 45 "Haske Maganin Duhи" Hauwa 6. Lawan ko gama tsotse dan ruwa-ruwan bai ba zai zubar domin shi burinshi dama ya ji gardin ayar kawai ne, amma yayin da wani kuma sai ya taunc ya tsotse tas karshe ya hadiyc tukar don in ta je cikin maganin basir za ta yi masa. Kin ga a nan ra'ayi nc kenan, ya danganta da kai fahimtar da kai wa aya, da kuma irin darajojinta da suka zo kunnenka. Kuma kin sani sosai a cikin kayan sawar ki akwai atamfar da ta yi miki, kallon farko za ta kwanta miki a rai ne, sai ki sawo a tsala miki dinki ki yi ta ji da ita, kina lallabata ta inda har ta tsufa da kyanta, kuma duk wani biki na musamman da ita za ki. Amma wata fa ga ta nan ne dai, wani ma wanki daya za ki yi mata ta fita a kan ki ki bayar. Ko na yi karya?" Тa girgiza kai. "To kin ga is like that, don haka ba na fatan Allah ya sa na dainan sonki, zan ta addu'a Allah kullum ya kara mini sonki, ke kuma ya kara miki ganin darajata sai ki ga mun yi rayuwarmu mai dadi, har ai ta sha'awar mu a ringa Allah ya ba ku mu samu ko Allah ya samu a danshinku ko baki fata?" Ta, kashe masa ido da yin wani smilling mai burgewa irin wada yake kashe shi. Ya cc, 'Au! Za ki fara ko? Ni fa sati ukun nan kamar shckara uku ne nake ganinsu." Ta се, "Haba dai Oga, rufe idonka kafin ka bude har an yi an gama ma." Ya ko rufe ya bude, ya ce, "Ya ba ai ba?" "Gajan hakuri ka yi, da khari na ce ka bude da kan ka." Su kai dariya. To haka dai har vau saura kwana uku a sata a lalle amarya ta je gidan gyaran jiki an gyarcta, an mulmule a sumul, ke kya ce 'yar baby ce natural bcauty skin fin nan ya dad fitowa zahiri ga wani hadaddan kamshi, duk notsi kamar eso turare take y In ta kallc kı kya ce wani abu ta disawa idanunta,, don wani hadaddan kyau da ta yi. Barista 46 "Haske Maganin Duhu" Hauwa G. Lawan har baya iya cewa komai, sai ya zama so silent, sai dai ya yi zuro yana kallonta. Har sai ta gaji ta ce, "Kai, Oga gaskiya kar ka gama kalle ni tun ban shiga dakina ba, irin wannan kallo?" Sai ya yi dan 'gajeran murmushi ya yi irin abin tausayin nan, ta ce, "Ya nc, ba baka sai ido da kunne?" Sai ya yi dariya. Ko ni miyau na hadiya mukut, ina zan kai ta? Ai sai irin su Oga Barista. Yau Alhamis yau ce ranar da za ai kamunta, kamun da aka shirya yinsa a gidan Yaya Zainab a harabar gidanta. An shirya gun da fararen kujeru sun zagayc shi, sai aka bar tsakiyar ba a sa komai ba sai aka shimfida katuwar tabarma, aka dora kafet. Sannan dadduma da dan tuntun taushin nan nan sarakai, nan ne amarya ta zauna tarc da kawaycnta sun zagayeta a gefe danginta ne uwa da uba, gefe kuma nan aka warewa dangin miji ina za su zauna don zaman kamu, a daya gen kuma Sayyada Tasallah Nabulsi Bako ce, malama da za ta yi wa'azi a gurin kamun. Yanda na ga yanayin kamun ya yi matukar kyau da Isari, an gabatar da wa'azi mai tsauri dangane da wuta da wadanda za su shige ta. Sannan an kuma karkato akala kan aure bautar Ubangiji inda malamar ta kare bayani da wata 'yar Hausa da Hausawa ke fadi, Duniya sai da kudi, lahira sai da hali, zaman gidan miji sai hakurin. Wannan haka vake kam, gidan miji fagfe ne na yaki ko kai nasara ko va vi nasara a kan ka, don haka sai ka kulla damarar cin ka0 da ko wane irin hardship a cikinsa da fatan ganin bayana, ha kamar yanda 'yan mata da wasu sakarkarun zawarwane ¡unani ba. aure a hole kawai a ji dadin una Tabdi kan ka ji ladi daya. ka ji wuya goma: Take care, labbas za a hoie, mma me kar ka sa holewar ita ce ginshiki ka gane bauta ka 47 "Haske Maganin Duhu" Hanwa i. Lawan je yi, in ko aka ce bauta, magana ta kare, bawa ai wahalalle ne sai yanda Ubangijinka ya yi da kai. An gama taron wa'azi lafiya lau, jama'ar da za su tafi sun ware wafanda kuma za su yi wa amarya rakiya fatin da dangin ango suka shirya da su kai wa lakabi da Grooms night, suna nan an shiga shiryc-shiryen tafiya. Na hango amarya shingin kiris ta dige don azabar kyau, ta ci wani irin kaya, shi ba lcss ba, ba matcrial ba, yo ni na kasa ganc ko me yc, hatta takalmin kalarsu daya sai gwaggoron mai kalar zaibar kayanta. Kai masha Allah, amarya dai da kyau, ranar auranta. Takwas da rabi dai-dai aka fara turo motocin daukar wafanda za su, ba su da wani yawa su ashirin ne kawai. daga shakikan kawaye sai kuma wasu daga cikin yayyanta 'yan gidansu. Kowa ya tafi sai amarya da babbar kawarta, inda daga baya angon ya iso cikin Humer Jeep ya gigice ganin amaryarsa ita kuma sai wani karairaycwa take tana narkwwa, 'yar fara'ar da ya saba gani ma duk babu daya kalleta sai ta wani marairaice. Ya makalo hannunta yana shakar kamshinta ba dan idon Maimuna Nagudu ba da ba abin da zai hana shi matsata. Haka dai ya lallaba suka isa motar, har Allah ya kai su Hotel de Francais inda za a yi. Gaskiya biki ya yi biki, 'yan mata ku sha shagali. bikin ya yi armashi matuka. Goma da rabi aka watsc. amarya ita ta fara tafiya da angonta. Maimakon ya kai ta gida, sai yav branch a See Sweet and Bakery ya hade ra ta-ce, "Lafiya ni fa na gaji barci nake ji, duk yau ban huta ba." Ya kalleta ta wani masifar hade rai, sai ya rage fara'ar fuskarshi ya e, 'Wai lafiya ne tun da aka fara bikin nan kı ke wani ciccm magani, ko kin ga wani ab da bai gamsar kı ba ne?" 48 "Haske Maganin Duhu"_ Hauwa G. Lawan "Ko daya kawai magana ce ba na so, ka kai ni gida na buta." "In na ki fa?" "Ba lallai, sai na bi motar haya." Ya kofula don haushi ya ce, "Baki da hankali ai ke, garin gantalin yawan motar haya ne ai aka kusa cire miki kai." Ba ta ce komai ba, kuma fara'ar da yake nema bai samu ba, ya ce, "Bari na shiga na samo miki ice cream da cake, don na ga baki ci komai ba gurin dinner din." Ta yi saurin cewa, "A'a in don ni ce wallahi ka bari, kafin na fito daga gida sai'da na kai linta, ni ba na bukatar komai sai kwanciya, sai dai kai ko bukatar ka." Yan da take magana tana basarwa ta ma ki ta kalle shi, sai abin ya bashi haushi kawai ya kada kai ya figeta sai gida. Koda ya ajeta bai kula ta ba, sai cewa ya yi, "Komai dai wayon amarya dole wata rana za a sha manta, a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe." Ta kalle shi a hankali ta bude kofar motar ta sauka ta rufe masa ta leka ta windo ta yi masa wani shegen kallo ta ce,

Chapter 4 of 10