gani yanda tayin wani mugun rama gaba daya yanayinta yaacanja
K'asa tayi da Kai Hawaye nakokarin zubowa daga idanuta muryarta narawa tace Abba akwai kudi a gunka kabani nasalamin Mai Naffee
Abba yace kishiga ciki zanje nasameshin shigewa ciki tayi Dakar ta inya bude baki tayi sallama
Mama dake shara sake tsitsiyar dake hannuta tayi kallon Ummeey tayi cike da tausayawa hawayene suka zubo daga idanun Mama
Karasawa tayi Ida Ummeey take
Kama hannuta tayi tazaunar da ita a kan taburma cikin murya Mai rauni Mama tace Ummeey lafiya Naganki da akwati kiga yanda Kika dawo saikace wace tashekara Tana jinya Kode kiyin rashin lafiyane
Abba nasalamar Mai Naffee din gidan ya shigo Dan bazai inya fita ko inaba gani Ummeey dayayi bakaramin tayar Masa da hankalin yayiba Zama yayi a gefenta..
Kallo iyayyen nata tayi taga gaba dayasu fuskarsu dauke da damuwa
A Ranta tace kowane halin zasu tsici kansu idan sukaji ya Muhammad ya sakeni tausayinsune ya kamata
Abba ne ya dubeta cike da kullawa yace Mamana lafiya kuwa Naganki cikin irin Wana yanayi
Hawayene suka zubo daga idonta a hankalin tabude bakinta tace Abba ya Muhammad ya sakeni yamin sakin uku Abba tuda ka Aura dani ga ya Muhammad yake azabtar Dani haka nake rayuwa a gidansa kullu cikin duka da zagin
An wayi gari abuda zanci yafi karfina a gidansa saka makon kwashe kayan Abinci da Momy tayi
"Umma Hauwa itace tasai da wayanta tamin cefane kayan Abinci ta aika Hauwa takawomin hata magani dazan sha. Hauwa ce tasayamin
"Wlh Abba nason ace mutuwa ce zata fitar Dani daga gidan ya Muhammad kodan gani daurewar farin cikika Abba naki sanar daku halin danake cikine saboda banason hankalinku ya tashi fashewa tayi da kuka
Itama Mama kuka tasa tace kagani ko Mallam yariyarna babu iri rok'oka da batayiba akan kabarta ta Aure wada take Son ama kaki kace lalle sai zabinka
Gashina Kuma zabin naka Yana Neman kashemin Yar, kaduba yada Muhammad ya dawo min da Yar, wlh daga shin har mahaifiyarsa bazan ya femusu cutarmin da rayuwar Yar,ta da sukayiba" !
Tsantsar bacin Rai ya bayana a fuskar Abba yace Mamana kuka ya Isa haka kishare hawayeki kidau Wana abuda ya faru a matsayin kaddara wada bamu isa mutsalakeba
Mamana akwai wani Siri dazan sanar dake nangaba kad'a Anane Zaki gane
dagani har yayana Abdallah mun Aura mikin Muhammad ne don gani mun inganta rayuwarki
Sai gashi abuda muke gudu shine ya faru
Share hawayenta tayi tace Abba kadena bani hakuri nasan bazaka tabayin abuda zai cutar daniba Kuma wlh nadau hakan a matsayin kaddarata kallon Mama tayi tace
Mama Dan Allah kidena kuka banason kisaka damuwa a ranki komai ya riga da yawuce Kallonta Ummeeyn tayi Tanajin radadin a zuciyarta
Shikasa Abba daurewa yake danji yake Kamar ya zubar mata da Hawaye musama idan ya daura idanusa a kanta
Yakanji zuciyarsa namasa k'una Anya kuwa zai inya yafewa muhammad iri cutar da yayiwa Ummeey
Wayasa ya ciro ya Kira yayanasa yake sanar dashi sakin da muhammad din yayiwa Ummeey
shima Abba bakaramin firgici ya shigaba saka makon jin Wana mumunar labarin yasanar dashi yayi gashina zuwa gidan yazu, sana ya kashe wayansa
...............Fitowa Abba yayi daga d'akinsa ya Taran da Momy zaune a fallo tadaura kafa daya kan daya karasawa Abba yayi Ida take fuskarsa babu annuri yace d'anki ya sanar dake abuda ya aikata.......
Ya mutsa fuska Momy tayi tace Alhaji in bada abunka akwai abuda My Son zai aikatane batare daya nemin shawarataba
Inade akan sakin Wana yariyarce
to ya sanar Dani ya mata sakin uku saboda bata da kunya batasan darajar manyaba hanufa tad'aga tamari Meenat saboda raini Meenat sa,artace to ko Mai Aiki gidasu tafi Ummeey daraja da kima
shikuma My Son yaga bazai inya Zama da itaba shine ya kad'ata gidasu sana yahada mata da tukunci duka aini sonayi daya karya banza
Cikin bacin Rai Abba yace kun tafka babban kuskure daga ke har d'anki zakuyi danasani a kan Abubuwa da kuka aikata
Fita yayi daga gidan ransa a bace Kai tsaye gidasu Ummeey ya wuce Yana insa ya Taran da Abbata a kofar gidan
Shiga cikin gidan sukayi Mama ta shifuda musu tabarma takawo Masa ruwa da Abinci
Itama Ummeey fitowa tayi Durkusawa tayi a gabasu tagaishe da Abba
Shikasa Abba bakaramin tsorata yayiba gani yada tarame talalace gawani baki da tayi kiyi hakuri Mamana Allah baya barin zalinci shine zai bimiki hakinki akan wadanda suka zalinceki
Shima Abba nasiha ya mata sosai kudi yabata masu yawa da kyar Ummeey takarba nama Saida Abba yabata Rai sana takarba babu Abuda zatace da Abba saide San barka tutana karama Abba ke da'wainiya da ita harzuwa girmata
................. Meenat nasamu kullawa daga gun Muhammad din komai take bukata Tana samu daga gareshi Momy tanemo musu Mai Aiki ita takeyi duk wasu ayukan gidan
Abuda Muhammad ya lura dagane da ita batasan komaiba dagane da abuda ya shafin addini batason yin sallah idan Kuma ya takura mata sai tasaka kuka gashi shikuma bayason bacin Ranta haka zai hakura ya kyaleta ama Abu Yana damusa gashi ko wankan tsarki batayin saide tayi wankata da sabulu
Zaune suke a fallo suna kallo, tadaura kanta a kan cinyarsa sallama sukaji dago Kai Muhammad yayi yaga Ashe Momy ce
Murmushi yayi yace Momy barka da zuwa Zama tayi a kan kujera tace yauwa My son
Kallon Momy Meenat tayi tace Hy !! Momy y kk? Momy tace lafiya Lou Meenat y gida ? Yatsina fuska tayi tace normal!!
Ama Momy ya kamata idan zakizo kina sanarwa Dan gaskiya banason Ana zuwa min gida batare da nabada izziniba
Daure fuska Muhammad yayi yace baki da hankaline Meenat Momy nawa kike fadawa haka to kishiga hankalinki
Kuka tasa tace baby nikakeyiwa hayaniya kasanfa banason anamin fada...
DAGA ALKALAMIN
Ummeey Muhammad Lawan
Yar Autar dashen Allah_*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*
FOR MORE INF...
08140801885
Page 77 & 78
_______________" Rugumeta yayi a jikisa I,m Sorry Baby rainane ya b'acin banji dadi maganar da Kika fadawa Momy ba
Momy zata inya zuwa gidana a duk lokacin da taga dama
Turro, bakin tayi tace nifa Baby banason a yawaita zuwamin gida in Kuma Momy tanace sai tazo to gaskiya saide nabarma gidanka '
Kallon Momy tayi tace , Sorry Momy kizauna a gidanki Ida kina bukatar gani Baby sai kikirashi a waya zaizo har gida ya sameki
Dan banason ganin tarkace a gidana mikewa tsaye Momy tayi cikin b'acin Rai tace amade yariyar nan baki da kunya
Nida gidan 'Da,na zakice sai nanemin iziniki agunki kafin nazo to wlh kiyin kadan yariyar kibin a hankalin in kuma bahakaba yazu , yazu zansa ya sakeki tuda baki da mutunci
Kuka Meenat tasa tafara buga k'afafu Baby kanajin abuda take fadamin wlh bazan yardaba sai kadaukamin Matakin a kanta
Muhammad ' kasa ya kullule yarasa ya zaiyi da Wana lamari ga ran Momynsa ya b'acin sai banbami takeyi
Ga Meenat sai kuka take
jin kuka nata yake har cikin ransa please....Baby kidena Wana maganar tayaya Zan dau mataki akan Momyna kikwantar da hankalinki yazu zata barmiki gidanki share hawayenki kiga banason gani bacin ranki
Share hawayeta tafarayi tace to Baby tatafin yazu Dan nagajin dajin hayaniyar nan
Kallon Momy yayi yace Momy kiyi hakuri Meenat yariyace karama yarintane yake damunta muje namaidaki gida
'Momy tsabage b'acin Rai kasa yin magana tayi
Fita zasuyi daga Fallon Meenat tace Baby Ina zaka Kuma ?
Juwowa yayi yace zankai Momy gidane ama bazan dadeba Ina kaita zan dawo
Kallonsa tayi karmar Mai Shirin yin kuka cikin shagwaba tace nifa babu idan zaka kabarni nikad'an a gidan
gulma da ya kawota shizai Mai data
Muhammad yace Momy kiyi hakuri kije gida nima inaxuwa anjima takaicine ya Kama Momy masifa tadingayi zagin Meenat Muhammad sai hakuri yake Bata
Fita tayin daga gidan Rai a bance shikuma Ida Meenat din take yanufa sai wani cin magani takeyi rarashita yafarayi Dan a duniya babu Abuda yatsana sama da bacin Ranta
................... Yau kimani wata biyu kena da dawowar Ummeey gidasu tafara murmurewa kyauwuta ya fara dawowa Dan Tana samu kullawa daga gun iyayyenata
Fitowa tayi cikin shirita ta iske Mama a tsakar gida Tana wanke wanke tace Mama sanu da Aiki dama Ina son zanje gidasu Hauwa ne bata masan nadawo gidaba
Kallonta Mama tayi tace aiko da kinkyauta kigaishesu. Ummeey tace to zasujin insha Allah
Tashi Ummeey tayi tace Mama sai nadawo Mama tace a dawo lafiya
Tana fita gidasu Hauwa tanufa
Tana shiga gidan tatara da Hauwa a tsakar gida Tana wanki karasawa tayi tarugumeta tabaya tare da fadin nayin kewarki Yar,uwata
Murmushi Hauwa tayi tace nima haka Sister wlh kulun cikin tunaninki nake d'azuma Saida mukayi hiranki da Umma take Tabayana yaushe zanje nadubaki
Ummeey tace Allah sarki Umma ai wlh sisters babu Abuda zace daku saide Adu.ah
Keni banji motsin Umma ba kode batanane Hauwa tace eeeh wlh Umma tafita unguwa gashi sai yamma zata dawo
Wai nikan Sister meye sirrine Naga kincanja bakamar Ranar danaje gidanki nagankiba wlh sister dana dawo gida kasa barci nayin sai tunaniki nakeyi
Murmushi Ummeey tayi tace kiyin hakuri sister nasan namiki laifi ban sanar dake cewa nakai kimani wata biyu Ina gidamuba Aurena ya mutu ya muhammad ya sakeni batare da wani Abu ya shiga tsakanina dashiba
Farin cikine ya lulube Hauwa tace Alhamdulillah Allah nagodema daka cire k'awata daga cikin wanan k'angin Ina rok'on Allah daya gagauta saka Miki iri zalincin da ya Muhammad ya Miki
Murmushi Ummeey tayi tace sister zaifi kyau mumanta da baya mutinkari gaba Allah Dee yasa inya bakin wahalar kenan
Hauwa ta Amsa da Ameen Cigaba sukayi da hiransu cikin kwanciyar hankalin kamar karsu rabu Ummeey batabar gidasu Hauwa ba saikusan yamma
BAYAN. WATA HUDU
..................Yau kimani wata hudu da mutuwar Auren Ummeey kwance take a kan gaddo zuciyarta cike da tunanin Haydar din tunani take ta Inna zata fara nemansa Dan a yazu bazata inya rayuwa da kowane dan, namijiba idan bashiba
Zubur tamike sakamokon tu,nawa da wasikar da yaturo Adam ya kawo mata a cikin wasikar yasaka number wayasa Ida yace idan Tana bukatar temako tasanar dashi
tashi tayi tabude wata jakar litatafai Ciro wasikar tayi hamuta na rawa tafara daukar number Kiran layin tayi tajin ya danga cikin zazakar muryarsa Mai narkar da zuciyar yace.....
DAGA ALKALAMIN
Ummeey Muhammad Lawan
Yar Autar dashen Allah_*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*
FOR MORE INF
08140801885
Page 79 & 80
_____________"HELLO!!!!! HELLO!!!!!
Sauti muryarsane ya dakin dodon kunanta wada hakan ya hadasar mata da farin ciki a zuciyarta
Ajiyar zuciya tasauke Mai karfi hawayen farin cikine suka zubo daga idanuta cikin muryarta Mai sanyi tace Haydar........ Ummeey ce sai Kuma tafashe
Mikewa yayi tsaye ciken da mamaki yace Ummeey Ashe dama zank'arajin wanan zazak'ar muryarna taki wace take sani farin ciki Koda Ina cikin bacin Rai
Kukan Mai kikeyin kidena kuka
kukaki nad'agamin hankalin kunuwan Haydar bazasu inya jure jin kukan Ummeey ba
Share hawayenki Ummeeyna kisanar dani maike faruwa
Share hawayeta tayi tace Haydar nakirakane domin nasanar dakai Aurena ya mutu nakai kimani wata hudu Ina gidamu
Lumshe idanu yayi ya budesu yayi a hankalin zuciyarsa cike da farin ciki Bude bakinsa yayin yace Alhamdulillah Allah nagodema daka dawomin da farin cikina dama inajin a jikina duk da anyin sanadiyar rabani dake watarana dolle Zaki dawo gareni
Allah bazai taba barisu suk'wacemin keba sai gashi cikin ikon Allah kin dawo gareni
Wani dadi Ummeey tajin Yana ratsa dukan sansan jikinta Murmushi tayi gamin da fadin hakika Kai masoyin gaskine bayin gangancin baka Amanar zuciyataba
Yaushe zakazo Gombe danyin
bayin ga shukar da tadade Tana bukatar ban ruwa Ummeeynka namararin kallon Wana kyakyawar fuskarna taka wace ke dauke da annuri a Koda yaushe
Murmushi yayi yace gobe Insha Allah Zan shugo Gombe !!! Gombe gari masoyiyata
Lumsheee idanu tayi tanajin wani sanyi a cikin Ranta budesu tayi fuskarta dauke da Murmushi tace Allah Ubangijin ya kaimu gobe da Rai da lafiya
Amsawa yayi da Ameeen sana sukayi sallama zuciyoyinsu cike da son ganin junnasu k'urawa waya dake hannusa yayi idon
gani lamari yake tankar a mafarki
daga hanuwansa yayi sama ya Allah idan mafarki nake ya Allah kada kabani ikon farkawa yazu
Murza idonsa ya farayi yaga abun a zahiri yake faruwa
murmushi yayi gamin da fadin koyanzu Naga ribar hakurina yau ga Ummeey a hanuna Ya Allah kaji Tausayina kada kabari tasake kufcewa daga gareni
Kiran wayan Adam yayi Adam dake kwace a d'akinsa yaji wayasa na ringing daga wayan yayi dauke da far,a akan fuskarsa hello, Haydar kana lafiya ?
Lafiya lau nake Abokina Ina cikin farin ciki wada ya mamaye dukan sansan zuciyata Adam Ashe rabon mutun bazai taba kubce masaba Auran Ummeey deee baiyin Rai ba yazu take sanar Dani takai kimani wata hudu a gidasu babu Aure a kanta
Mikewa Adam yayi zaune cikin mamaki yace Haydar kana nufin Ummeey bata da Aure Auran Ummeey ya mutu
Alhamdulillah duk da ba,a farin ciki da mutuwar Aure ama a wanan karo nakasance cikin jin dadin dajin mutuwar Auren Ummeey
Ina tayaka murna Abokina da dawowar masoyiyarka gareka yanzu yaushe zamu Gombe
Haydar yace nariga nasanar da Ummeey gobe Insha Allah muna hanya Adam yace to Allah ya kaimu gobe
Haydar yace Amiin ama Dan Allah banason Rukkayah tasan da maganar mutuwar Aure Ummeey Rukkayah Tana da kishin sosai wlh mudin tasan Aure Ummeey ya mutun to daga ranar nayi bankwana da farin ciki a cikin gidana har yazu Rukkayah bata Dena fushi daniba saboda suna Ummeey danasawa yar'ta Taki tafitar da Wana Abu a rainta.
Wlh kishin Rukkayah har tsoro yake bani Adam yace kwantar da hankalinka Abokina dazaran mun dawo daga Gombe zansamu Rukkayah zan mata bayani insha Allah komai zai tafin daide
Haydar yace nagode Abokina gobe karfe 8:00 zamu tafi Adam yace Allah yakaimu gobe kashe wayansa yayi yanufin gidan
Koda ya insa gida ya Taran da Rukkayah zaune a fallo tanayiwa Ummeey wasa itako sai kyalkyallewa da dariya takeyin
Zama yayi a gefenta sanu da dawowa tamasa Amsawa yayi dauke da far'a akan fuskarsa hannu yasa dauki Ummeey
Kallon Rukayyah yayi yace Momy Ummeey gobe inaso zanyi tafin kallonsa itama tayi tace Allah yakamu gobe ama wane gari zaka Haydar yace Gombe zani
Gabantane ya fadin kallonsa tayi cike da tuhuma mezakayi a Gombe bayan nasan baka da yan'uwa a can
Ina da yan'uwa a Gombe Mana ko kin manta Kakarmu Inna nacan tare da Adam zamu tafin
Zamu kaiwa Inna ziyara kiga ai zataji dadin ko Kallonsa take batare da tayin maganaba zuciyarta naraya mata Abubuwa daban daban
WASHE GARI
Damisalin karfe 8:00 Adam ya inson gidan Haydar Rukkayah gaishe da yayannata tayin fuska a hade Dan ita bata yarda dasuba gaba dayasu haushi yayan natane ya kamata
Musamama da takalin fuskar Haydar din taga sai murmushi yake sai kace wani sabon ango
Haydar yace Rukkayah zamutafi kikulamin da kanki kikulamin da Ummeey na zamu wuce sai Allah ya dawo damu lafiya
Dak'ar ta inya bude baki tace a dawo lafiya Allah ya kiyayye hanya kwana nawa zakuyi
Haydar yace kwana biyu zamuyi shuru tayi batare da tace komaiba
Fitowa sukayi daga gidan suka shige mota suka dau hanyan Gombe Haydar sai far'a yake bakisa yaki rufuwa
Damisalin karfe 12 :30 suka in son cikin gari Gombe tsayawa sukayi a masalacin sukayi sallah
Anguwarsu Ummeey suka nufa
Ummeey sai shirye shirye tarbar Masoyinata takeyi girki tayi musu shikafa da wake da Mai da yajin sai kunu ayyah
Dan tasan Haydar din nata dason Abinci gargajiya zuwa tayi tashiya ciki shigar doguwar riga kayan bakaramin kyau suka mataba wayatane tayi Kara dauka tayi takara a kunenta fuskarta dauke da murmushi Sallama tayi
Amsawa yayi yake sanar da ita suna kofar gida kashe wayan tayi cikin sauri tanufi hanyar waje Tana fitowa tatar dasu tsaye jikin mota kallon kallon sukeyiwa juna zuciyoyinsu cike da shaukin So
wani kyau yaga tagara Masa duk da rama dayaga tayi hakan bai hanashi gani kyautaba sallama tamusu sana tagaishesu Amsawa sukayi gaba dayasu suka Amasa.
a hankalin tabude bakinta tace Haydar.... Ashe Idanuwana zasu Kara ganika" Allah nagodema daka dawo min da masoyina a Lokacin Dana cire Rai dasamusa
Murmushi yayi yace Ummeey ai Mai Rai baya fitar da Rai daga rahama Ubangiji kullun inajin a jikina watarana Zaki dawo gareni burimu Zai cika namalakar junamu
Saide akwai maganar da nakeson sanar dake Ummeey.... nayin Aure dago Kai tayi da sauri tadaura dara daran idanuta a kansa tace Haydar kayi Aure?
Eh nayi Aure Ummeey har Allah ya azurtani da samun karuwa yar'mace
Ummeey tace natayaka murna lale wanan matar takasance Mai sa,a
a rayuwa tasamu mijin daya tankar ya dubu dazan ganta Dana Bata shawara tarike mijinta hanu biyu Dan samu irinsa a fadin duniyarna sai Ansha wuya
Mamakine ya Kama Haydar gani yada bata nuna damuwarta akan Auren da yayiba lalai Ummeey tadabace a cikin mata
Kallon Adam Ummeey tayi tace Adam Naga kayi shuru bakace komaiba murmushi Adam yayi yace Mai zance Amaryamu ai Wana zance namasoyane
Saide namiki wani albishin wada shi Haydar din ya manta bai fadamikiba
Itama murmushi tayi tace Ina sauraroka
Adam yace Ummeey saboda irin son da Abokina yake Miki ya dau alkawari idan Allah yabasa yar' mace zaisa mata sunaki
Sai gashi Allah ya azurtashi da samu yar' mace Kuma yasamata sunaki
Wani dadi Ummeey tajin Yana ratsata tace Haydar Ashe kaunar dakamin hartakai haka kasawa Yar,ka sunana
wayo dadin zanso Naga Wana yariyar zason gani yar' masoyina Allah yarayamin Mai sunana Haydar Kai masoyine nagaskiya Ina Alfahari dakai Haydar
Mushiga cikin gida kucin Abinci kuhuta shiga sukayi cikin gidan Ummeey takawo musu Abinci zuba musu tayi a plate
Basu wuri tayi Dan susamu sucin Abinci
Suna gama cin abincin sai ga Abba ya shigo mamane take sanar dashi zuwansu Haydar din karasawa yayi Ida suke gaishesa sukayi cike da mutuntawa. an wanan karo Abba yajin dadin zuwasu Haydar din
Adam ne yace Abba yauma de musake dawowane a kan maganar Aure Ummeey dan Allah Abba katemaka kabawa Abokina Auren Ummeey
Kallonsu Abba yayi yace na'amince zan bawa Haydar Aure Ummeey Ama Ina da sharadin zaka turomi mahaifinka a gabansa
zan fadamuku sharadina idan kun Amince to Zan Baku Aure Yar,ta zufane ya karyowa Haydar Abba yace kakwantar da hankalinka Haydar Wana karo bazan hanaka Aure Ummeey ba saide idan kune kukaga bazaku inya Aurentaba...
DAGA ALKALAMIN
Ummeey Muhammad Lawan
Yar Autar dashen Allah_*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*
FOR MORE INF
08140801885
Page 81 & 82
______________Adam yace toshikenan Abba babu damuwa insha Allahu zamu sanar da Dady sak'onka Kuma nasan Dady zai yarda da duk wani sharudanka matukar bai sabawa addiniba
Zamu tafin masaukimu zuwa gobe zamu dawo wata killama tare da Dady zamu dawo Abba yace Allah ya kaimu gobe
Atare suka Mike tsaye sukayiwa Mama sallama Ummeey fitowa tayi daga d'aki domin tayi musu rakiya
Kallon masoyin nata tayi taga yanayisa gaba d'aya ya canja gabantane yafadin cikin tashin hankalin tace Haydar Wana karoma Abbana yakin Amince da maganar Auremu koh wayooo Allah nashiga Ukuna sai Kuma tafashe da kuka Mai cin Rai
Kallonta Haydar yayi gamin da fadin menene abun kuka anan bafa abuda kike tunanibane Abba ya Amince zai bani Aurenki.
Ummeey tace Adam dagaskene abuda yake fada kode akwan wata matsallane kuke boyemin
Murmushi yayi yace gaskiya Haydar ya fada mikin
Ummeey tace tomeyasa naga yanayiku gaba daya ya canja bayan ba a haka kuka shiga gidamuba kushiga gidamu dauke da far,a akan fuskarku
Kun fito Kuma fuskarku dauke da damuwa
Dan Allah kusanar Dani Mai Nene dalilin canjawarku
Murmushi Haydar yayi yace Ummeey Abba yace zai bani kee naturo Dadyna ama Kuma akwai sharudan dazai kafa Mana
Hankalina yatashine saboda bansa wane irin sharadin Abba zai kafamanaba yazu kishiga gida zamuwuce gidan Inna idan muhuta zankira Dady nasanar dashi duk yada mukayi da Dady zakijini zuwa dare
Ummeey bazanbar Gombe ba har sai Abba ya baniken An tsai da Ranar bikin sana Zan koma Kano
Murmushi tayi tare da fadin Allah ya Amince zanso gani Wana Rana Mai cike da dinbin tarihi
Ranar da muka Dade Muna mafarkin zuwata Murmushi yayi yace Zan wuce Ummeeyna saimuyi waya
Toh Allah ya tsare Ango Ummeey Dady Ummeey dariya yayi Dan har cikin ransa yajin dadin Wana suna data kirasa dashi
Shigewa Mota Adam yayi tare da fadin idan nabiyema Haydar saimu akwana anan batare da kasaniba Dan Naga kuna cikin shaukin son
Kallonsa yayi gamin da fadi wlh Adam Idan inatare da Ummeey mantawa nake da komai a cikin wanan duniyar
Subar kofar gidasu Ummeey batare da son ran Haydar ba gidan Inna suka nufa
Inna tayi farin cikin daganinasu susamu tarba tamusama daga gun Inna
Haydar ya Kira Dady yake sanar dashi duk abuda ya faru bai Boyemasa komaiba Dady ya Masa Alkawari gobe zazo yasamu Mahaifin Ummeey farin cikine ya Kama Haydar wada ya bayanna a kan fuskarsa
Yasanar da. Adam yayi yada sukayi da Dady shima Adam yajin dadin da Dady ya amince zaizo gobe
Dady yasanar da Ammy mutuwar Aure Ummeey Kuma gobe zaije Gombe nemawa Haydar din Aure Ummeey Ammy tayi farin ciki sosai tayi musu Allah yasaya alkairi.
WASHE GARI
Damisalin karfe 1:30 Dady yashigo cikin gari Gombe kira Haydar yayi yasanar dashi insowarsa Haydar da Adam ne sukaje Taran Dady
Basu bata lokaciba suka nufin gidasu Ummeey dama Kuma Ummeey tasanar da Abba Mahaifin Haydar din nazuwa yau shima Abba yasanar da yayanasa zuwasu
Abba da yayanasa suyi matukar farin ciki da zuwan Dady sun karbesa cikin girmamawa da karanci
shikasa Dady yajin dadin irin karamawar da yasamu daga gun su Abba
Dady yace Alhaji nide sunana Alhaji Museen nine Mahaifin Haydar Allah ya jarabin Haydar da son Yar,ka wada kaddara tazo lokaci guda tarabasu Haydar yashiga cikin mawuyacin halin sakamokon rasa Yar,ka da yayi
Dan bakaramin son yakemataba sanadin hakan ya harfar Masa da ciwo zuciya
mutsici kamu cikin tashin hankalin
Musha wuya sosai kafin musamu Haydar ya dawo hayancinsa
Jikin Abba yayi Sanyi tausayin Haydar din yakamasa lalai bai kyauta musuba yayi sanadiyar shigarsu cikin wani halin ya jefasu cikin garari to Yaya zaiyi dolle sumasa Uzuri shima ba,a son ransa ya aikata hakanba yayi hakane domin inganta rayuwar Yar,tasa kallon Mahaifin Haydar din yayi yace...
DAGA ALKALAMIN✍🏻
💞Ummeey Muhammad Lawan💞
🥰Yar Autar dashen🌲 Allah. _*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 14