mikinfa
Murmushi takaici tayi tare dafadin Ya Haydar dama Kai a tunanika nicema zamuku breakfast ita wace kakwana a gunatan bazata muku breakfast diba
Ya Haydar kafitamin daga d'akina bana son ganika ai dama nafadama turanar da nashigo gidanka bazan iya hada mijin dawata yan'maceba
Rashine yabaci take yanayisa ya canja idanuwasa sukayi Jan
Yace Rukkayah nikike d'agawa murya kike fadamin bak'ake magaganu saboda nakara Aure
Too inason sanar dake Ummeey itace zabin Raina Ummeey itace mace da nafara son a rayuwata har gobe banida Kamar ta Kuma banajin zan inyayiwa wata yan'mace son danakewa Ummeey kema shedace akan hakan
Dan haka kishiga hankalinki kishi ba hauka bane wlh idan kikace Zaki rainani a gidana bazaki taba jin dadi a gunaba
Mikewa tayi tsaye cikin masifa tace Ya Haydar kayi duk Abuda zakayi wlh dadai nake dakai tudaga Ranar daka Bude baki kace an daurama Aure da Wana figagiyar yariyar kafita daga Raina
Daga hanu yayi zai mareta saikuma ya tsaya cak
Girgiza Kai yayi cikin bacin Rai yabar dakin yanufi bangare Ummeey
Yana shiga ya tarda ita zaune a fallo Tana ganisa tamike tsaye fuskarta dauke da Murmushi tace barka da dawowa Habibi
Murmushi karfin halin yayi yace Habibty Ina Kika shiga d'azu natashi bangankiba
Murmushi tayi tace Habibi ina can kitchen Ina had'a Mana breakfast
Cikin mamaki Haydar yace breakfast Kuma kina Amarya Kika shiga kitchen
Murmushi tayi tace muje mukarya ko Habibi
Tudaga Wana lokaci kullu Ummeey ita takeyin girkita har lokaci data cika sati guda a gidan Hayda
Haydar yasanar da Adam iri Abubuwa da Rukkayah take Masa Adam dakansa ya zo har gidan yasameta yamata fada sosai
Ammmy itama tazo gidan tahadasu tayi musu nasiha akan sujin tsoro Allah suzauna da junasu tsakani da Allah
GOMBE
Tuda Muhammad yasanar da Meenat Abubuwa da suka faru Meenat tace bazata zauna dashiba yazamo dolle ya saketa Rashi mutunci take zuba Masa na yau daban nagobe daban
Da Abu ya Ishesa yaje yasamu Dad dinta yasanar Masa halin dasuke ciki
Dad yace Kai dama kasan Mahaifin naka matsiyacine shine kazo ka Auri Yan,tah
Too yazamo maka Dole karabu da Meenat Dan ba ajinka bace nifa dama na Aurama Meenat ne saboda Naga Mahaifika sananeni a garina
Too ama tuda Har Arziki banasabane too wlh yazamo Dole kasaki Meenat
Dan bazata zauna da matsiya ciba Babu irin cin mutunci da Dad din Meenat bayiwa Muhammad ba
Haka Muhammad yabar gidan cikin takaici da danasani Aura Meenat
gidasu Muhammad yawuce ya Taran da Momy da Abba zaune Durkusawa yayi a gabasu yace_*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*
For more information
08140801885
Page 101 & 102
Barkaku da hutawa Abba dago Kai Abba yayi
ya kallesa tare da fadin yauwa barka de Muhammad dafatan kuna lafiya ya iyalin
D'ago Kai Muhammad yayi tare da sauke idanuwasa akan Abba cikin sanyi jiki yace Abba Babu lafiya tun Ranar da Meenat tasamu labarin dukiyarka ta Ummeey ce
Tudaga Wana lokacin tabi tad'agamin hankalin Wai ita bazata zauna daniba saide narabu da ita
Yazu hakama daga gidasu nake nasanar da Dad abuda kefaru saide shima Dad yace Meenat bazata cin gaba da Zama daniba
Mikewa tsaye Abba yayi yace Wana ai matsalarkuce Kai da Mahaifinyarka
Kafun yayi wata magana. Abba. Yabar gun ya wuce d'aki
Momy nagani Abba ya shige. daki takalin. d'anata ciki tausayawa tace My Son yaushe raboka daxuwa gidanan kaga yada duk kabi karame sai kace wada yayin jiya
Shima kallon Momy yayi tare dafadin Momy ai komai jinya baikaini shiga cikin tashin hankalinba Momy inason Meenat banason rabuwa da ita Dan Allah Momy kitemakeni muje kibata hakuri tayi hakuri mucigaba da zamamu
Momy idan narasa Meenat zanshiga cikin tashin hankalin
Hararasa Momy tayi cikin k'unar Rai tace My Son kokaki ko kason yazamoma dolle karabu da Wana yar'iskar yariyar
Yariyar dabata San mutuncin kaba bare har kayi tunanin zata mutuntani a matsayina na Mahaifinyarka kaduba iri cin mutuncin da yariyarna tamin ama wai kana ikirarin cewa bazaka iya rabuwa da itaba saboda ita tahaifeka
Wacece Meenat da har kake tunani bazaka iya rabuwa da itaba
akwai Mata kyawawa a duniyarna wada sukafin Meenat My Son kana da kyauwun da kwar jini wada duk wata Yar Mace zatason kakasance Mijinta
Tashi zakayi mutafin gidanka a gabana nakeson kadan k'arawa Meenat saki d'an d'an har guda uku
Sana narama irin wulakanci da tayimin tashi mutafi nasan Abbaka bayazu zai fitoba zanje har nadawo batare da yasaniba
Mikewa Muhammad yayi jikinsa a sanyaye suka nufin gidanasa
Suna shiga sukatara da Meenat zaune a fallo Tana gani Momy tamike tsaye cikin tsiwa. tanuna Ta da yatsa 👉tare dafad'in
Wakekan wace iri maran zuciyace nace bana buk'atar ganiki a gidana Ama saboda naci sai kizo too wlh idan ke manyace saide kicin kanki Dan nikan nafin karfin...Bata karasaba tajin saukar Mari a kan fuskarta
Kafin Momy tasauke hanuta daga kunci Meenat itama Meenat din tashararawa Momy Marin jikake Tasssssssss
Wani hucin Muhammad yayi ya danko Meenat ya fara dauketa da Mari Yana dukanta keeee Dan Ubanki Mahaifiyata Zaki Mara saboda baki da kuyan tooo wlh yau sana kusan kasheki a gidanan
Bai bartaba Saida yamata duka lilis sana ya kyaleta tare da hada Mata da tukwuncin saki har guda uku
Dakar Meenat ta iya daga kafafuta tanufi daki saboda dukan da Muhammad din ya Mata bana wasa bane
Momy ko zuciyarta tayi fari kyal take tanemin duk wani bacin Ranta tarasa
Momy batabar gidan ba har Saida taga tafiyar Meenat Muhammad dakasa ya maida Momy gida
Abba barcisa yakesha Dan baimasan bata gidan ba
Meenat Tana insa gida tasanar da Mom irin dukan da Muhammad yayi Mata masifa Mom tadigayi tace baza yardaba yau saitaga waye gatansa a garin Gombe Kiran Dad tayi a waya tasanar dashi ran Dad bakaramin bacin yayiba a ransa yake ayyana irin wulakanci da zaiyiwa Muhammad
GIDAN HAYDAR
Haydar nanunawa Ummeey Tsatsar kauna wada har baya iya boye iri Son dayake Mata gawani irin kullawa da yake nunamata
Itama Ummeey bata dawani buri da yawuce taga tasanya mijinata cikin farin ciki duk wani abuda tasa zai farata Masa shitakeyi
Tana bashi kullawa tamusaman
Tana riritashi takar jariri shikansa Haydar jishi yakeyi tankar wani sarki sai a yazu ya Kara tabatarwa Ummeey itace farin cikinsa musamama gani irin kullawar da take nuna Masa Tare da Yar,sa Ummeey k'arama gawani irin shakuwa data shiga tsakanisu
Ummeey Bata samu nutsu idan bataga yariyar a kusa da itaba duk da irin wulakanci da Rukayyah kemata akan yariyar ama hakan baisa tayin zuciyaba
Dan jin yariyar take a rain tankar ita tahaifeta
Wani lokaci idan taje daukarta haka Rukkayah zata hanata taita fada Mata bakaken maganganu itama yariyar Tana ganita zatafara zillo Tana kuka sai taje gun Anty nata
Takaici ya Kama Rukkayah duk kuka da Ummeey k'arama zatayi bazata barta taje gun Ummeey ba saide idan Haydar dine ya dauketa ya kaita gun Anty nata shikasa Haydar Yana mamakin sauyawar Rukkayah lokaci guda takoyo wasu munanan d'abi,u marasa kyau
Haka rayuwa taci gaba da tafiya duk Ranar da Haydar yake d'akin Ummeey to a Ranar daga ita har Haydar din suna cikin fari da Anashuwa idan Kuma zai koma d'akin Rukkayah da kuka suke rabuwa wani lokacin saboda kewar mijinata har kasa barci takeyi Dan bakaramin shakuwa sukayi a Soyayyah ba wada takai takawo basa son suyin nesa da juna
Shima a bangare nasa hakane take kasancewa duk Ranar da yake d'akin Rukkayah jishin yake tankar maraya Dan Bata da Aiki sai mita da k'anana magaganu Kuma hakan nafaruwane tadalilin zafin kishin datake dashi
Zaune take tanayiwa Ummeey k'arama wasa sai kyalkyalle Dariya sukeyi Mikewa Ummeey tayi zubu sakamokon tunowa da tayin da photuna da Mama tabata na Mahaifiyarta wada kwata kwata tamata dasu sai yazu tatina dasu d'aki tanufa tadauko jakar
dawo Fallon tayi Tazauna kusa da Ummeey k'arama
Bude jakar tayi tafara fito da photuna idanuwata suka sauka akan photo wata farar Mata kyakyawa Tana murmushi aka dau photo ga hakworin makka sanye a bakita
Tsirawa photo idon tayi tanajin kaunar Mahaifiyarta nashigarta Hawaye sukafara zirya akan fuskarta
Zuciyarta namata rad'ad'in tausayi Mahaifiyartane ya cika Mata zuciya cin gaba da kallon photuna take
kallon photon Mahaifinata Dana Mahaifiyar Tata take
kuka tasa tare dafad'in Allah yajikanki Mahaifiyata Allah ya Kai Haske cikin kabarinki inama ace Mutuwa batayin gagawar rabani dakeba Dana kalin wanan kyakyawar fuskarna taki dana kwanta akan ciyarki nima najin d'umin jinkin Mahaifinta wayoo Allah mutuwa tarabani da Mahaifiyata batare da najin dumin jikintaba Kara fashewa tayi da kuka Mai sauti
Shigowa Fallon yayi bakisa dauke da sallama a rude ya yakarasa Ida take yace Subbahananllah Habibty Mai yafaru kike irin Wana kuka sanar dani cikin gagawa tukan zuciyata tabuga
Sai a lokacin Haydar ya lura da photuna dake gabanta gabansane ya fadin hanu yasa ya dauki photuna zare idanu yayi yace Habibty.... Ina kikasamu photo Anty Aysha
Kukan tane ya tsaya cak idanu tazira Masa tace Wana itace Mahaifiyata sune photuna da Abba kefadin Mahaifiyata tabashi a lokacin da take Shirin barin duniya
Zare idanu Haydar yayi yace Ummeey karde ace kee. Yar' uwatace Wana ai Anty Aysha ce k'anwar Dadynace Uwa daya Uba daya kimanin shekaru Ashirin kenan da b'acewarta Babu Ida Dady bai nemin Anty Aysha ba ama bai sametaba idai hakan takasance sainafi kowa farin ciki
Ummeey k'aramace tasa kuka sai a lokacin Haydar ya lura da ita daukarta yayi tare da Ciro wayasa a Aljihusa Kiran Dady yayi
Dady dake gida zaune suna hira shida Ammmy yajin wayasa nakara d'agaawa yayi yace Assalamu alaikum...
Cikin zumud'in Haydar yace wa,alaikumu sallam Dady Albishirika dariya Dady yayi yace yau Kuma nazamo kakanka kenan
Haydar yace wlh Dady yau nazomaka da Albishi wada zai dawo maka da farin cikinka wada ya dad'e da gushewa
Dady yace kayya kaide Haydar fadin duk Abuda kakeson fad'a Ina sauraronka amani Babu abuda zai dawo min da farin cikina
Haydar yace koda sanar dakai nayi nasamu Labari Anty Aysha
Zaro idanu Dady yayi tare da mikewa tsaye yace Haydar Ina wasa dakaine ko son kake kafamemin tabo daya dad'e a zuciyata
Haydar yace wlh Dady dagaske nakema Ashe Ummeey yar' Anty Aysha ce dazu Naga photo Anty Aysha a gun Ummeey
Dady yace katabata Haydar photo yar'uwata Aysha kagani
Wlh Dady Anty Aysha ce tun lokacin da Abba Ummeey yasanar damu Labari Iyayyan Ummeey sai nake gani kamar Anty Aysha ce Mahaifiyar Ummeey ama sai zuciyata takasa gaskata hakan
Ajiyar zuciya Dady ya sauke Mai k'arfin tare da fadin Ganinan zuwa gidan naka yazu kashe waya Dady yayi
Haydar nagama waya da Dady Kiran Adam yayi yake sanar dashi komai
Adam bai bata lokaciba ya inso gidan
Kallon Ammmy Dady yayi yace tashi mutafin gidan Haydar yazu yake sanar Dani Matarsa Ummeey yar' Aysha ce
Mamakine ya Kama Ammmy tayaya Haydar yasa Ummeey Yar Aysha ce
Mayafin Ammy tadaka suka nufin gidan Haydar din suna insa Dady ya kurawa Ummeey idon sai a lokacin Dady ya lura da komai nata na Aysha ne turanar da ya fara ganin Ummeey yaga taso tayi Kama da Yar,sa fatima
Dauko photunan Haydar yayi ya nunawa Dady da Adam kallon photuna Dady yayi sai yafashe da kuka Mai tsuma zuciya yace Tabbas Wana koshaka Babu Aysha ce taho gareni Yan'tah kizauna kusa dani Dan najin kamshi Yar, uwata atare dake Ashe kedin jinace
Karasowa tayi ta dukusa agaban Dady tace Dan Allah kadena zubar da hawayenka akan Abuda Allah yarigada ya tsara Mana
Karasa K'anwarka a lokacin da bakayi zatoba sai gashi cikin rahamar Ubangiji Allah ya hadaka da jinita a lokacin dabaka taba tsamaniba
Share hawayesa Dady yayi ya Ciro wayasa yakira Abba Ummeey yasanar dashi cewa shine yayan Aysha
Abba yayi farin cikin sosai dajin Wana dadad'an labari yace Suma gobe Insha Allah zasuzo Kano
A Ranar Dady yayi kukan farin ciki godiya yayiwa Allah daya kaddara haduwarsa da yar' Aysha itama Ammmy farin cikine ya cika Mata zuciya tare da Taya Dady murnar haduwa da yar' Aysha Dan ita kanta tasan irin kaunar dake tsakanisa da yar'uwar tasa
Adam kaga ikon Allah ko Ashe Ummeey yar' uwatace nikaina Ina mamakin irin zazafar kaunar danakewa Ummeey har nakejin a Raina dana rasata gyara narasa Raina
Murmushi Adam yayi yace HAYDAR ai jini daya ya wuce wasa
WASHE GARI
Da sasafe Su Abba sukaka dau hanyar Kano Muhammad shikejan Motar sai Abba dake kusa dashi Mama Abba suna gidan baya
Sushigo Kano kicin kwoshin lafiya Haydar da Adam susuka tarosu
A Wana Ranar bakin Ummeey yakin rufuwa saboda murna gani iyayyenata a Wana Rana su Abba suga karamci da girmamawa daga gun Haydar da Iyayyesa
Bayan su Abba sunci abinci suhuta Abba yace Yaya Abdallah ya kamata muyi Abuda ya kawomu Dan a yau mukeson komawa Gombe
Dady yace yakamata kubari zuwa Gobe sai kutafin Dan a yau inason Muje har Bauchi Muhada Ummeey da Mahaifita Alhaji Sadiq
Abba Muhammad yace badamuwa da yau da gobe duk dayane a guri Ubangijin
Abba yadubin Dady yace Alhaji kaga yarda Allah yake ikonsa Aysha Tasha yawo bulayin Neman kan ama Batasamekaba
Harta koma ga Allah Tana Mai mararin gani fuskar yayanta Ama Allah bai nufaba
Abba yasanar da Dady komai tudaga Ranar da ya fara ganin Aysha a bakin shagonsa
Kuka Dady keyi Kamar wani karamin yaro Yana tuna irin shakuwar da sukayi da yar' uwarsa cikin Kuka Dady yace inata Kiran wayan Aysha ba,a dagawa daganan jikina yabani da Akwai matsala nakira wayan mijinta anane yake sanar Dani an nemin Aysha ba a gantaba nashiga tashin hankalin da rudani bad'an kad'anba
A Ranar natafi Bauchi nabada cikiya gidajen Redio da Talevion
Ama ba a daceba Aysha ita kada'nce Yar Uwata bani da kowa sai ita haka itama Bata da kowa saini tsawan Wana lokaci kullun zuciyata da tunani Yar uwata take kwana take tashi har nakamu da cutar hawan jini
Gaba daya wada suke gun Saida suka tausayawa Dady rabuwa da d'an uwa akwai zafin Dady shikadai yasan irin rad'ad'in dayakeji a ransa shima Haydar kuka yake tare da tausayawa Mahaifinashi Dan tuda yake da Dady nasa bai taba gani kuka Shiba sai yau
Dakar Su Abba suka samu suka rarashi Dady sana yayi shuru ama yanajin ciwo rabuwa da Yar,uwarsa
Ammy itama kuka take Dakar Akasamu sukayi shuru
Rukkayah jikintane yayi sanyi nadama da danasani suka shigeta Ashe Ummeey yar' Uwar mijin natane.
Kiran Alhaji Sadiq Dady yayi yake sanar dashi gasuna zuwa gidan nashi
Tashi sukayi gaba dayasu suka dau hanyar Bauchi suna insa cikin garin Bauchi Kai tsaye gidan Alhaji Sadiq suka nufa
Suna insa gidan Alhaji Sadiq Da kasa ya fito ya tarbesu cikin karamawa
Cikin suka shiga ya kaisu katafare Fallosa na Alfarma wata datijuwa ce tashigo hanuta dauke da Fruit ta anjiye a gabasu Sana tagaishesu
Hajiya Saratu ce tafito cikin takun k'asaita tazauna kusa da Mijinata ko kallonsu Batayiba barai susa ran ran zata gaishesu
Bayan sugama gaisawa Dady yace Alhaji Sadiq yau muzo maka da babban Albishin wada zai sanyaka cikin farin cikin maran yankewa farin cikin da bazai taba gushewa daga garekaba har Ranar da zaka koma ga mahalincinka
Alhaji Sadiq kakalin Wana yariyar da kyau dawa tamaka maka Dady yanuna Ummeey
d'aura idanusa yayi akan Ummeey sai yazabura ya Mike tseye tare dafadin Alhaji Museen Wana yariyar Bata da maraba da Aysha
Gani Wana yariyar danayi ya famenin tabo dake zuciyata Allah sarki Aysha kitafi kibarni cikin tunaniki
Alhaji Museen kahaifin yariyar Mai Kama da Aysha
Dady yace Alhaji Sadiq bani nai haifintaba Wana yariyar Yar,kace Yar,da Aysha tahaifa cikin rudun Alhaji Sadiq yace Dan Allah Alhaji Museen kada kamin wasa da zuciyata
Dady yace Alhaji Sadiq tsakanina dakai Babu maganar wasa Ummeey Yar,kace take Dady yasanar dashi duk Abuda ya faru hata Labari haduwarsu da Haydar hazuwa Aure Dady bai boye musu komaiba
Alhaji Sadiq jiyayi tankar Amasa bisha da Aljannah rike hanu Ummeey yayi tare dafadin Museen kayi gaskiya Wana yariyar jininace Allah sarki Aysha Allah ya jikanki Allah yasa mutuwa tazamo hutu a gareki
Durkusawa yayi a gabansu Abba yace Alhaji nagode nagode Allah yasaka maka da mafifincin alkairi kirikemin Yar,ta riko nagaskiya duk wada yaga Ummeey yasan tasamu tarbiya Tagari kallon Mama yayi yace Hajiya nagode Allah ubangijin yasaka muku da Alkairi
Abba yace Dan Allah Alhaji kadena Mana godiya wlh duk abuda mukayiwa Ummeey bamu fadinba Ummeey Takasance Yan,Tagari wada muke Alfahari da ita tuda muke da Ummeey Bata taba tsalake Umarnimuba
K'arrra Hajiya Saratu tasa Tana tsale tanafadin shikena tawa takare dama boka yace duk sanda nabari Wana yariyar tazo duniya ide sukayi idon biyu da Alhaji shikena duk wani kullin danayi zai warware shikenan
Sai Kuma tafara dariya Tana fadin. Alhaji Nina maka asiri narabaka da danginka nice nasa Aysha tabar gidanka Nina turo Yan,daba akan sukasheta shine tagudu wayo nacuci kaina dariya Saratu take iya karfita Tana fadin tacuci kanta cire Dan kwalin tayi tabaza gashita tabar gidan aguje
Kowa nagun sai Allah wadare yake da halin Saratu shikasa Alhaji Sadiq jiyayi Kamar an sauke Masa kaya Mai nauyi akansa
saka makon Asiran da suka warware atare dashi
Ummeey kuka take tare da tausayawa iyayyenata
Hirace tabarke a tsakanisu Alhaji Sadiq yakira Yan uwa da dangi yasanar dasu haka suka diga zuwa suna gani Ummeey dagi gaba daya sucika da farin cikin gani jini Alhaji Sadiq din Dan dama Yana fama da rad'adin rashin Haihuwa
Kyautuka masu yawa sufito daga hanu Alhaji Sadiq. Daga cikin harda kyautar kujera makka ya bawa su Abba hada Dady da Haydar da Adam harda Rukkayah da Mama da Muhammad
Sanan kowane su ya hada musu da mukulin Mota godiya sukayimasa Mai tarin yawa tare da Aduoin samu nasa a rayuwa
Alhaji Sadiq ya rokin Alfarma agun Haydar akan yabar Masa Ummeey tayi Koda sati guda sanan yayi Masa Alkawari da kansa zai maidata har Kono
Haydar de ba a son ransa ya Aminceba Dan a zahiri gaskiya baya kaunar yayi nesa da Matarsa ama Babu yada ya inya haka suka bar Bauchi batare da Ummeey ba
Sun Abba sukoma Gombe cikin farin cikin da murnar sada yar'tasa da Mahaifinata
Ummeey nagani soyayyah da kullawa daga gun Mahaifinata harma da dangisa kowa nahaba haba da ita
Kullun suna tare da Mahaifinata yana Bata Labari irin Zama dasukayi shida Mahaifiyatata itama tasanar dashin iri rayuwar da tayi da irin gata da Abba da Mama suka nuna Mata
A Ranar da tacika Sati a Ranar ne Mahaifinata ya maidata har gidanta tare da daleliyar sabuwar motar Haydar yayi murna da dawowar Ummeey Dan bakaramin kewar juna sukayiba
BAYAN WATA UKU
Jirgisu ya tashin zuwa kasa Mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin tun acan Ummeey take fama da kasala da rashin jin karfin jikin
Tun bayan tafiyarsu Abba aiki hajjin Alhaji Sadiq yaje Gombe yasa aka rushe gidan Abba akamasa gini zamani tare da zuba masa kayan Alatu a gidan Saida Aka Gama komai Sana Alhaji Sadiq yasanar dasu Abba
Godiya Abba yadiga Masa tare da Adu,oi masu tarin yawa
Bayan sugama aikin hajin su dawo kasarsu Nijeria su Mama da Abba suka wuce Gombe
Abba yacika da mamakin gani yanda gidansa ya koma tankar nawani hamshakin Mai kudin farin cikine ya Kara lulube Abba da Mama lalai Ummeey Alkarice a garesu godiya suka Kara yiwa Alhaji Sadiq
Rukkayah tanemin yafiyar Ummeey akan Abubuwa data aikata Mata take Ummeey tayafe Mata sun hada kansu suna zaune lafiya hata girki tare sukeyi renon Ummeey K'arama ya koma hanun Ummeey
BAYAN WATA SHIDA
Ummeey tahaifin Dan,ta namijin Ranar suna yaro yacin sunna Abba Ummeey wato Muhammad za,Ana cemasa Shurabeel
Abba yayi farin cikin dasamu Mai suna
Ummeey Takoma wankan gida nama dak'ar Haydar yayarda Saida Ammy tasa baki sanan ya yarda suka tafin da Mama
Mamace tace Ummeey kiga muma mun dawo Yan,gayuko Mahaifinki Alhaji Sadiq shine ya canja Mana rayuwa ya Mai damu Yan,gata
Anane Mama take sanar da ita irin Abu alkairi daya musu harda su Gwogwo Asabe
BAYA KWANA ASHIRIN
Haydar yazo dubasu shida Adam Kuma Alokacine Adam Yaga Hauwa yaji takwanta Masa a Rai
Ya Muhammad Kuma tuda Ummeey tadawo wankan gida yake zuwa gidan suta hira Kamar ba muhammad din daya tsanetaba
BAYAN SUN GAMA WAKA
Ummeey taje har gidasu Hauwa tagaishe Da Umma Sana tabata kudin masu tarin yawa Umma taita godiya sosai Ummeey tace Umma kidena godemin wlh bazan taba manta alkairiku gareniba
A Ranar da zata koma gidanta Saida tayi kukan rabuwa da Iyayyenata Haydar dakansa yazo ya daukesu suka koma Kano
Hauwa da Adam soyayya suke zubawa bana wasaba
BAYAN SHEKA BIYU
Rukkayah tahaifin d'an namijin yaro yacin suna Dady Museen za Ana kirasa da Shaheed
Baya haihuwar Rukkayah da wata biyu Ummeey tasake Haihuwar d'an namijin yaro yacin sunna Adam za Ana kirasa da Shureen
Momy har Kano tazo neman yafiya agun Ummeey
Ummeey tace aini Momy nariga da nayafe Miki tuda jimawa godiya Tadigayimata Tana samata Albarka Ummeey tajin dadin zuwa Momy tahad'a Mata Tara ta Arziki Sana tayi tafiyarta
An daura Aure Hauwa da Adam sutare a gidansa dake kusa Dana Haydar Fatima ma sudawo uguwar da Zama
Alhaji Sadiq Mahaifin Ummeey ya Aure Gwogwo Halima dama mijinta ya dade da mutuwa suna zaune lafiya Hajiya Saratu kan hauka muraran sai bin jujin takeyi
Mahaifin Meenat nakan hayarsa tazuwa gidasu Muhammad daniyar ya wulakantashi yayi hadari Mota yasamu karaya a ciyoyisa guda biyu gashi bayasa ya bugu baya iya komai saide Amasa Meenat tayi bak'in tarame tadawo Abu tausayi taje tasamu Muhammad akan yayi hakuri ya Mai data d'akinta ama shin Muhammad yakin kuka take Tana danasani kashe Aureta datayi
Su Abba sucigaba da kasuwancisu Kuma Allah yasawa kasuwanci Albarka dukiya sai habaka takeyi idan kukaga Abba da Mama Bazaku ganesuba
Muhammad yasamu wata yariya Mai suna Hafsat ya Aureta suna zaune cikin rufin Asirin
BAYAN SHEKARA DAYA
Hawa tahaihu tahafin Yar, mace yariya taci sunata zainab
Ummeey k'arama tagirma tayi wayo sosai yariyar Mai shiga Rai mutane
Rayuwa tayiwa Haydar dadi Haydar yazama d'an gata a gun matan nasa
Sumai dashi tankar wani Sarki
ALHAMDULILLAH.
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH DUKAN YABO DA GODIYA SUTABATA GA ALLAH MADAUKIN SARKI WADA YA YONI YA YON KOWA ALLAH MAI DARE MAI RANA
ALLAH KAYIN DA'DIN TSIRA GA SHUGABAMU ANNABI MUHAMMADU SALLAHU ALAIHI WASSALLAM INA KARA GODEWA ALLAH MADAUKIN SARKI DA YABANI IKON GAMA WANAN LITAFIN MAI SUNA ZABIN ABBANA CIKIN KOSHIN LAFIYA
ABU DA NARUBUTA DEDE INA ROKON ALLAH YASA YA ANFANA MUTANE WADA KUMA NAYI KUSKURE ALLAH YA YAFEMIN
INA MIKA SAKON GODIYA GAREKU MASOYAN WANAN BOOK NA ZABIN ABBANA MUSAMA MASU COMMENTS INAYIN KU SOSAI DINA💞💞
ALLAH YABAR KAUNA ❤️
MUHADU A SABON LITAFINA MAI SUNA SHAGALIN AURE DATIJO
ZAIZO MUKU NAN BADADADEWABA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14