da number Yaya Musa akaina
Nayanke shawara zuwa tsoho gidansa kozasamu wada yasa Ida ya koma
Koda naje gidan Suma cewa sukayi basusan Ida ya komaba haka naita yawo a cikin garin Kano
Duk wada nabukaci ya teemakeni sai yakin wasu har guduna sukeyi
To kaji dalilin zamana a bakin shagonka saka makon gajiya da nayi da bulayin Neman yayana
Dagani har Ameenah Tsitar kamu mukayi cikin tausayin Wana baiwar Allah
Kamar yarda Ameenah tayi Mata alkawari zamu temaketa
Haka nasanar da ita tacigaba da Zama harzu lokaci da Allah zaiyi ikonsa
A RANAR DA AYSHA TA CIKA KWANAN BIYAR A GIDAMU
A Ranar ne Nakuda tatasowa Ameenah misalin karfe 1:30 nadare nafito Neman Abu hawa domin kaita Asibiti ama bansamuba sakamokon daren da yayi
Haka naita bulayi a cikin anguwa ama bansamu Abu hawaba hankalina ya tashi sosai
Gida nakoma Dan naje Naga wane halin Ameenah keciki
Inazuwa nasameta a wahale Aysha nakanta Tana Mata sanu
Damisalin karfe 3 : 20 Ameenah tahaihu tahafin d'ata namiji ama kash!!!!!!!!!! Dan Bezo da Raiba
Ameenah tayi kuka Kamar Ranta zaifita nima kawai daurewa nakeyi Dan nikadai nasan irin radadin da nakeji a Raina Allah yasani muci buri a kan Wana cikin saide kana naka Allah nanashi saide Kuma na Allah shine dedeee
Muna cikin Wana yanayi itama Aysha nak'uda tataso Mata gadan gadan kafin nafita Nemo Naffe har tahaifi santaleliyar Yar,tah mace
Bayan tahaihune jini ya b'allee Mata a zahiri gaskiya hankalina bakaramin tashi yayiba
Nazo zanfita Dan Neman Mai Naffee saiji Muryarta nayi Tana fadin Mallam...tsayawa nayi cak jin muryarta kasa kasa Tana fadin Mallam ga Amanar yariyata nabar muku ita kuriketa Amanna
Wana jakar kudine a cikin da gwalagwalai namalaka makasu halak malak kakulamin da yariyata a cikin jakar akwai photo mahaifita a cikin Alahaji Sadiq sananene a cikin garin Bauchi a G.RA yake da Zama
Dan Allah Mallam Ina rokonka kada kasada Wana yariyar ga Mahaifinta danyin hakan tankar salwantar da rayuwata ne
Dan natabata idan Saratu tasan Ida Wana yariyar take bazata tab'a barita a rayeba
Dan Allah Mallam inason kazamewa Wana yariyar Uba a gareta kekuma Ameenah inason kizame Mata Uwa
Hawayene suka zubo daga idanun Ameenah cikin kuka tace kidena fadin haka insha Allah Zaki tashi zakiyi rayuwa tare da Yar,kin cikin Amince da kwanciyar hankali
Kallonta nayi cikin sanyi jiki nace da ita Nagode Aysha da Wana kyauta mafi girma da daraja da kikamin
Nakarbi Amanar da Kika bamu Zan rike Wana jariyar tankar Yar Dana haifa a cikina Zan nuna Mata duk wani gata da yadace Uba yabawa Yar,sa
Bazan karbi Wana dukiyarba da Kika malakamiba saide Zan dakawa yayana ya diga juyata har zuwa lokacin da Allah zai rayamin Wana jaririya Zan danka Mata kayanta mudin tamalakin hankalin kanta
Cikin zafin ciwo tace nagode Mallam Allah ya sakamaka da mafifincin alkairi
Sai mukaji tayi shuru jijigata Ameenah tafarayi Ashe Rai yayi halinsa haka naje nasanar da limamin unguwarmu a
cewa Allah ya karbi rayuwar Yar uwata
Aiyi Jana izzarta an kaita makwancita nakira yayana nashaida Masa komai
Shima yayana Abdallah yasanar da baba
Baba yakirani ya min nasiha akan narike Wana yariyar da Amana kada nakuskura nasanar da ita cewa bamu muka haifetaba saide idan lokacin da Zan Aura da ita nakan yazamo Dole
mijin da zai Aureta yasan gaskiya wana lamari
Murufe Wana Sirin muhudu muka sanar da Yan,uwa da saura dangi cewa Ameenah ce tahaihu
Dagina gaba daya suzo suna nasawa yariya suna Mahaifiyarmu Ummulkhari
Bayan suna natafi Gombe nasamu yayana Abdallah namika Masa Amanar dukiyar Ummeey da gwalagwalai ta akan ya sayar dasu ya diga juya kudin tuda shin ya kware a harkar kasuwanci
Dakar Yaya Abdallah ya karbi Wana dukiya sanan yasanar dasu Halima cewa tadalilina wani ya temakesa ya Raya Masa jarin
Allah ya Albarkaci kasuwanci Yaya Abdallah lokaci kalilan arzikin yayana ya habaka
Habiba nagani arzikin mijita ya habaka tasake daurawa kanta girman Kai gawani tsanar da takeyiwa Ummeey saboda taga yayana Yana daukar duk wani d'awainiyarta
Rayuwa taci gaba da tafiya Ummeey tagirma ta malakin hankalin kanta naci gaba da ajiyar photo Mahaifinta
Wasiyar da Baba ya barwa yayana Abdallah itace Muhada Ummeey Aure da Muhammad Dan gudun kada Wana sirin namu ya fita
Sanan ya zabin nadawo Gombe ne Dan nasanar dashi cewa Ummeey tasamu Mijin Aure a lokacin suna tare da Haydar
Babamu yakin Amincewa da wanan hadin tsakani Haydar da Ummeey duk Dan gudun kada wata Rana Ummeey tawulakanta a gusa
Shine baba yace mu dawo Gombe dazama to dalilin Dawowarmu Gombe kenan Wana itace wasiyar Mahaifimu
Muhada Ummeey da Muhammad Aurene saboda gudu tonuwar Wana Siri
To kuji takai tace tarihin Ummeey
Mamana dafatan kifahici koke wacece Kuma Ina rokonki kada matsayimu ya canja a guki har gobe mu iyayyenkine...._*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*
For more information
08140801885
Page 97 & 98
______________Dago Kai tayi tadaura daradaran idanuwata akan Abba wasu hawayene masu zafi suka zubo kan Fuskanta
Cikin wata iriyar murya tace Abba. Mama kalmar godiya tayi k'ank'anta a gareku saide nayi muku Adu'ah
Allah Ubangijin ya saka mukun da mafifincin alkairi Allah ya biyaku da gidan aljannah
Abba da Mama bani da wasu iyayyen a Wana duniyar saiku kune kuka raineni tun Ina tsuman Haihuwa harzuwa girmana kuka bani tarbiya Tagari kuka dau duk wata d'awainiyata bana manta irin wahalhalu da Abbana yasha akaina duk Dan ganin ya inganta Rayuwata bakutaba gajiyawa akan d'awainiyar da kuke daniba.
Wlh yau zuciyata cike take da farin ciki inajina tankar wace akayiwa bishara da Aljannah
Gani nake nafi kowa sa,a a cikin Wana duniyar Allah nagodema daka sanya rainona a hanusu Abba da Mama
Mutane masu karanci wad'ada suka fifita fari cikina akan nasu Basu da buri daya wuce suga sun ingata Rayuwata
Wlh iyayyena matsayiku bazai taba sanjawa daga gareniba saima darajarku da kimarku da suka dad'a nikuwa a zuciyata har Abada kune iyayyena wada nake Alfahari dasu
Cikin jin dadin kalaman da suke fitowa daga bakin yar'tasa yace Mamana tsakanimu dake Babu godiya duk abuda mukayi mikin mumikine saboda musauke nauyi dake kamu
Mahaifiyarki tamalaka manake halak malak tadanka Amanarki a hanumu
Mukarbi Wana Amanar muka yimata Alkawari zamu rikeki bisa Amanna har zuwa Ranar da Zamu Aura dake
Allah nagodema daka bani ikon cika Wana Alkawari da nadaukarwa Aysha Allah Kaine sheda akan iri rikon danayiwa Wana yariyar idan har akwai Ida nagaza Allah kayafemin
Ummeey zatayi magana Abba Muhammad ya dakatar da ita tare da fadin
Ummeey Abbaki ya sauke nauyi dake kansa sai Kuma niiiii
Nima a yau Zan sauke kayan daya dade yanamin nauyi a kaina a yau Zan danka mikin dukiyarki
da tayi kimani shekaru Ashirin a hanuna Ina juya mikinsu
Cikin ikon Allah Allah ya Albarkaci Wana dukiya tabukasa harta jawo an malakin manyan kadarori kamar su filaye da gidaje
Yazu Zan dankamiki dukiyarki Kamar yarda muka tsara nida Abbanki duk lokacin dakika malakin hankalin kanki zamu dank'a mikin dukiyarki a hanuki
Muso mudank'a mikin dukiyarki tun lokaci da muka hadaku Aura da Muhammad ama sai nayi wani tunani nace mubari zuwa nagaba tukunna muga irin rikon da Yaya naki zaimiki
Sai Kuma yayi mikin rikon irin na zalinci wlh nayi danasani hadaki Aure da yayanki. Muhad'aki Aure dawada Kwata Kwata Bai dace dakeba..
Mikewa Momy tayi tsaye cikin tashin hankalin tace wlh bazai inyuba Wana gaba daya shirine iri na Muhammadu wato Tana kabulo yazu Kuma Too wlh bazai iyuba bazan taba barika kayi nasara a kan Mijinaba
Alhaji ka dawo cikin hayacinka
Natabata Muhammadu wani Asiri yasake maka Dan ya rabaka da dukiyarka
Tooo wlh baka isa karaba mijina da dukiyarsaba
Tsawa Abba ya dakamata wada ya hadasa Mata tsorasa a Ranta
Cikin bacin Rai Abba yace kada nakarajin kice wani Abu Ana gurin ai dama Iri Wana Ranar nake guje muku dagake har d'anki Ranar da zakuyi nadaman da danasani akan Abubuwa da kuke aikatawa
Gaba dayaku kusan waneneni kafin shekaru Ashirin dasuka wuce
Bazansa kaina daga cikin Tallaka ba haka Kuma bazance nimai Arziki bane
Saide nasan Ina da narufin Asirin
A cikin lokaci kalilan kikaga canji a tatare Dani ama baki taba Tabayata ta dalilin Wana canjiba bare harkiyi tunani ta Ina nasamu Wana dukiyar
Haka mukaci gaba da rayuwa dake batare da kitaba min magana akan Arziki da kikaga nayi lokaci gudaba. Saima murna da farin ciki da kikeyi mijinki ya zamo Mai Arziki baki damu kisa dalilin samuwar saba
Yan,uwana su Halima da Asabe suzo susameni da maganar
Ama sai naboye musu gaskiya lamari nace musu Muhammadu ne yahadani da wani mutumin a can Kano ya bani jari sana suka samu nutsuwa a rannsu
Gaba daya dukiyar da kuke tikaho da ita too kalilance tawa a ciki saura dukiyar Ummeey ce
Hata gidan da Muhammad keciki shima natane
Dago Kai Muhammad yayi a razane yace Abba gidanta Kuma tayaya gidan daka malakamin zaizamo nata
Murmushi Abba yayi yace kwarai kuwa gidan Ummeey ne da dukiyarta aka gina Wana gida hasalima Mahaifita shine ya bukaci Dana danka Wana gidan a hanuka tuda Kaine zaka zamo mijinta
Too kaji dalilin baka Wana gidan danayi
Zufane ya ketowa Muhammad take nadama da danasani suka kamasa inama ace zai iya maida hanu Angogo baya daya mayar
Ya goge duk wani laifin daya aikata a gareta
Gwogwo Halima tace tooo suuu Habiba karyar Arziki yakare ko Ashema Arzikin dakike gadara dashi na Yar,mune
Mama ce tace Halima kibar Wana maganar ai komai yariga da yawuce kuskurene Ariga da anyishi saide muyi fatan Allah ya yafemana
Gaba dayasu suka Amasa da Ameeen Momy ko jitake Kamar tanitse kassa saboda kuyan Abuda ta aikata
sai yazu take danasani Abubuwa data aikatawa Ummeey Ashe yariyace Mai Arziki nadiga musguna Mata batare datasaniba wayooo Allah nacuci kaina nacuci d'ana yazu da a gidan d'ana take da gaba daya Wana Arzikin ya Zama nasa. a Ranta tace yazuma lokaci bai kureba zanyi duk yada zayi dangani tadawo gidan d'ana
Ummeey tace Abba bana bukatar komai daga gareku kugama min komai a rayuwata bazan tab'a biyaku iri d'awainiyar da kukayi daniba
Abba Wana dukiya takuce bazan karbi ko sisiba nabar muku bana bukata komai daga cikin
Abba Muhammad ne ya kaleta cikin mamaki yace kada kiyi haka Mamana bazamu dau ko kwadala daga cikin dukiyarkiba
A lokaci da Mahaifinki yake cikin halin matsi rayuwa bar karbi ko kwadalla daga cikin Wana dukiyarba bare yazu
Rokonsu Ummeey tadigayi akan surike Wana dukiya ama su Abba sukakin
Haydar ma rokonsu yake akan sukarba tuda ita tabar musu
Dakar Su Abba suka Amince nama Saida Ummeey taita kuka Tana rokonsu
Sunyarda zasu rike dukiyar ama bada gidaje da filaye Wanaka suce bazasu karbaba
Ummeey ta Amince da hakan ama badan Ranta yasoba Dan ita gani take Babu abuda zatayi dasu
Sanan tace Abba Dan Allah acikin gidaje inaso Abawa Gwogwo Halima da Gwogwo Asabe
Abba gidan da Yaya Muhammad keciki shima nabar masa
Dago Kai yayi cikin sauri ya sauke idanusa Akanta wani irin kallo yake Mata Mai cike da nadama yace Ummeey yazu duk irin abuda na aikata mikin har zakin iya min kyauta Mai girma irin Wana
Kallonsa tayi tare dafadin ya Muhammad kaifa d'an uwa nane Kuma yayana wlh kafin k'arfin komai a guna Zan iya malaka maka duk wani Abu dana malaka batare danaji d'ar a Rainaba
Tsura Mata idanu yayi Yana Mai jin haushin kasa tayaya akayi tunda baigane Ummeey itace mace data dace dashiba
Innallillahi wa,Inna ilaihir raji u nacuci kaina nasake reshe narike ganye narabu da yariya Mai tarbiya naje nadaukowa kaina masifa nabiyewa Son Zuciyata naki yarda da ZABIN da ABBANA yamin
Kallonta yake yanajin wani mahaukacin Sonta nashigarsa batare daya shiryaba a hankalin ya bude bakisa wada ya Masa nauyi yace nagode Ummeey hakika kincika Yar halak wace idan aka Mata Shari take sakawa da alkairi
Kiyafemin Ummeey hakika nacutar dake a zaman damukayi dake nak'utatawa Rayuwarki nazalinceki nazauna dake a gidana a matsayin Matata ama nakasa sauke nauyi da Allah ya dauramin
Nakasa kusatarki amatsayinki na Matata Ummeey idan har baki yafeminba basan Ida zansa kainaba hakinki bazai barniba a cikin Wana duniyar tudaga yazu hakiki ya fara bibiyata Dan Allah kiyafemin
Ummeey tace kadena rokona ya Muhammad nariga da nadad'e da yafema
bazan tab'a iya rikeka a Raina ba kakwantar da hankalinka komai yariga da ya wuce kaifa yayanane wada duk duniyarna bani da d'an uwa daya wuceka
Muhammad yace nagode Ummeey Ina mikin Adu,ar Zama lafiya a gidan Aurenki Allah yabaku zuri,a d'anyiba
kallon Haydar yayi Yana maijin radadin a ransa yace inatayaka murna Haydar kayi dace Mata Mai hakuri da tarbiya Dan Allah karikemin K'awata Amanna hawayene kekwokarin zubowa daga idanusa yayi sauri kau dakansa gefee
Murmushi Haydar yayi tare da fadin karka damu yayamu insha Allah Zan rikema kan'warka da Amanna
Gwogwo Asabe da Gwogwo Halima godiya suka rigayiwa Ummeey harda kuka farin cikin sana sukariga samata Albarka
Mama ne tace Ummeey kiyiwa Yaya Abdallah godiya da iri d'awainiyar dayayi dake tukina karama har zuwa girmaki hata kayan dakin shiyamiki da kudinsa
Ummeey tace tooo Mama kallon Abba Muhammad tayi tace Abba nagode da irin d'awainiyar dakayi Dani Allah ya biyaka da gidan aljannah
Murmushi Abba yayi tare da fadin Amiiiin Mamana karki damu ai nima mahaifinkine
Abba yace Mamana tashi kutafiko kada dare yayi muku a hanya
Narai narai tafarayi da idanu tace Dan Allah Abba kabari sai gobe inaso muyi bankwana da Mama
Abba yace wane irin bankwana zakuyi wada bakuyishi daba kee tashi kibi Mijinki
Matsawa tayi kusa da Mama tare da fadawa jikinta tasa kuka
Rarashita Mama tafarayi tare da Mata nasiha akan tabin mijinta ta zauna da Abokiyar zamanta tsakani da Allah
Sana shima Abba ya daura danashi itade Ummeey sai kuka takeyi a Ranta tanajin zafin rabuwar da zatayi da iyayyenata
Abba ya sanar da Haydar nada wata daya zasuzo Kano domin daukar Ummeey susadata da Mahaifinata
Haydar yace Allah ya kaimu lokaci kowa naguri yanayiwa Ummeey fatan Zama lafiya Mai daurewa a gidan Aure nata ama bada Momy da k'ya shi da hassada ya cika Mata zuciya
Suna shiri tafiya saiga Hauwa tashigo rugumeta Ummeey tayi tare da fara wani sabon kuka rabuwa da Aminiyartata
Dakar suka rabu kowanesu zuciyoyinsu cike da rad'adin rabuwa da junasu
Haydar ne ya bude Mata Motar tashiga shima shiga yayi ya tada motar zuciyarsa cike da farin ciki
Ummeey nagani sufara tafiya kuka tasa tanajin ciwo rabuwa da Iyayyenta
Jayota yayi jikinsa takwanta akan kafad'arsa a yacin gaba da tukin
Damisalin karfe 6 : 20
Suka inso cikin Kano Yana Isa gida Mai gadin ya wagale Masa gate
shiga ciki gidan
yayi parking fitowa yayi daga Motar zagayawa yayi ya bude Mata Motar
hanuta yarike tafito daga cikin Motar
cikin gidan suka nufa kwokari zare hanuta take daga cikin nasa ama tagagara
Kaitsaye fallonsa suka nufa wada yasha kayan Alatu lumshe idanu Ummeey tayi sakamako wani sanyayen kamshi dadi daya bugir hancinta
Kallonta Haydar yayi fuskarsa dauke da Murmushi yace Bissmillah ga guri kizauna baneje naduba Antyki
Sukuyar da Kai tayi kasa Tana wasa da yatsun hanuta tace tooo a dawo lafiya
Wucewa yayi bangare Rukkayah Yana shiga ya tarada ita zaune da Ummeey akan cinyarta tacin kwaliya cikin wani had'aden less na Alfarma sai kamshi take zubawa
Kallonta yayi fuskarsa dauke da Murmushi yace Uwar gida sarautar Mata Uwar gida ran gidan idan bakee babu gidan Haydar
Ya mutsa fuska tayi tace yau Kuma Tana kabulo aini ya Haydar bazaka yaudareni da Wana dadin bakinakaba tuda har kakara Aure too wlh kaficemin a Rai yazuma bansa Mai ya kawoka dakinaba
Baiji dadi maganar data fada masaba ama saiya basar
Hanu yasa ya dauki Ummeey dagata sama yayi yace baby Abba yau kiyi sabuwar Momy Kuma Mai sunaki zamuje kigan Momyki ko
Mikewa Rukkayah tayi cikin fushi tace bani yar'ta Kuma wlh Ummeey bazata taba Kiran wata baza da Momy ba karma kafara Abuda zai dameka Dan wlh bazai iyuba batakai matsayi da yan'tah zata kirata da Momy ba
Murmushi yayi yace tooo naji Momy Ummeey yazude muje fallona akwai maganar dazamuyi
Zatayi magana Haydar yace Dan Allah kada kimin musu Matata kiyin hakuri Mujemu kinji My Love
Turo baki tayi taraba tagefesa tawuce shima b bayanta yabi suka nufin fallo
Zama tayi akan kujera tadaura kafa daya kan daya shima Haydar Zama yayi a gefesu ya fara Adu'ah yaroki Allah daya bashi ikon yin Adalci a tsakani mataye nasa
Kallon Rukkayah yayi gami da fadin Momy Ummeey kice babba a gidan na Dan Allah inason kuzauna lafiya keda ka'warki kuhada kanku kada kubada kofar da shaidan zai samu dama dazai tarwatsa Mana farin cikin gidamu
Kekuma Ummeey Rukkayah yayarkice Dan Allah kibata girmata a matsayita nababa kuhada kanku waje Samar da Zama lafiya gidan nan
Kallon Rukkayah yayi yace Momy Ummeey kina da Abu fadin
Ya mutsa fuska tayi tare da fadin nide ya Haydar kafi kowa sani banason raini bazan dau raini daga gun matarkaba
Dan wlh mudin tace zata rainani too wlh jikintane zai gaya Mata gyara tun wuri tashiga hankalita
Murmushi Ummeey tayi tace karki damu Antyna bazan taba mikin wani Abu da ya danganci rainiba aike yayatace tayaya Zan Rana yayata
Nide fatana Allah Ubangijin ya hada kamu Allah yabamu Zama lafiya
Allah Kuma yabawa Mikimu ikon yin Adalci a tsakanimu
Mikewa Rukkayah tayi tsaye tare da wuga Mata harara tace kaji dashi makira daukar Ummeey tayi tabar dakin shide Haydar ya Mata uzuri dan yasan zafin kishine kedamuta_*ZAƁIN🤵🏻♂ABBANA👳🏼♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share
_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link
_*WHATSAPP LINK*_
https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA
_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*
For more information
08140801885
Page 99 & 100
______________Kallonta yayi yace Habibty tashi mushiga cikin kooo
Shuru tayi nad'an wani lokaci sana tace Habibi Dan Allah kaje kararashi Antyna Naga Ranta yabaci
Kura Mata idon yayi tare dafadin karki damu Antyki nada da sauri fushi ama zata huce zuwa safiya
Shuru tayi a Ranta Tana fadin yazu a haka zan zauna da Wana matar Dan nalura Tana da zafin kishin Allah kabani ikon jure duk wani Abu dazan gani daga gareta
Mikewa yayi tsaye yace Habibty tashi mushiga cikin
Tashi tayi batare da tace komaiba tabi bayasu suka nufin bangare nata suna shiga Fallon mamakine ya kamata gani irin kayan Alatu dake Fallon saikace fadar shugaban kasa
Hawaye fari cikine suka zubon daga idanuta a hankalin tafurta Ina Alfahari daku iyayyena sanyin idaniyata Allah ya Kara muku nisan kwana Mai anfani
Juyowa yayi ya kalleta yace Habibty Yanaga kitsaya lafiya Dee koh
Sukuyar da Kai tayi batare datace ufaba
Suna shiga cikin dakin Alwala sukayi suka gabatar da Sallah nafila sudade sunayiwa Allah godiya daya malaka musu juna amatsayin ma'aurata
Kiran Adam ne yahigo wayansa dagawa yayi yace ganinan fitowa
Bai dad'e da fitaba ya dawo hanusa sanye da ledee
Ajiye ledan yayi a gabata budewa yayi gashashiyar kaza ce a ciki hannu yasa ya yago kazar tare damik'a mata Bismillah Habibty buda bakinki kici Wana dadad'ar kazar
Girgiza Kai tayin tare da fad'an nakwoshin Habibi
Idonsa nakanta Yace kiyin hakuri Habibty kici Koda Kadane zanji dad'in idan Kika Amince kikacin
Mika Mata yayi yace bud'e bakin ko Habibty Bude bakin tayi dakansa yake Bata kazar a baki har sai da ya tabatar tak'oshi sana ya kyaleta
Shigewa Toilet sukayi domin wake bakisu suna fitowa daga Toilet
rakubewa tayi a gefe Kallonta yayi yaga jikinta a sanyaye Alamu tsoro sun bayana a tare da ita
Habibty Yanaga kitsaya a nan taho muje mukwanta
gani yayi Bata daniyar zuwa Karasowa yayi Ida take rike hanuta yayi suka nufin Ida gadon yake Zama sukayi a bakin gadon
gabatane ya fadin Hawaye suka fara zirya akan fuskata
hanu yasa yafara share Mata Hawaye
yace Mai Kuma yafaru Habibty konamikin wani abune da har yasakin zubar da Hawaye
Girgiza Kai tayin cikin kuka tace bakamin komaiba Habibi
Kura Mata Sexy eyes d'insa yayi masu daukar hankalin yace too Mai yasakin kuka sanar Dani
Habibty kisan kuwa irin rad'ad'in danakeji a Raina idan Naga Hawaye nazubowa daga Wana kyakyawar fuskarna taki
Sukuyar da kanta tayin kasa tace nima basan dalilin kukanba jinayi kawai inayi
Tooo kuka yayi hakuri karyasake zuwa Dan nasan soyake ya hanani more wana dare na angwancina Mai cike da dinbin tarihi
Dare Dana daden Ina tanadin zuwansa
Daga Mata gira yayi tare dafadin koba hakaba Habibty shuru tayi batare datayi maganaba Dan tsoronsa yagama ciki Mata zuciya zare hanuta tayi daga cikinasa ta hayen kan gadon kwanciya tayi a gefen gadon gabanta nafaduwa
Shima hayewa gadon yayi ya kwanta daf da ita tare da manata a jikinsa wani irin Abu yajin ya tsikareshi tudaga tsakar kansa harzuwa tafin k'afarsa jin yayi yashiga cikin wani irin yanayi hugging d'ita yafarayin cikin wani irin yanayi na shaukin Son
Cikin kwarewa ya fara sarafata saikace wani mayu wacin zaki
Kokari rabata da kayan dake jikinta yafarayin
sauri tayi tarike hanusa cikin kuka tace Habibi Dan Allah kada kamin komai wlh Ina tsoro
Cikin wahalaliyar murya yace Sorry Habibty bazan iya jurewaba nadade Ina mararin ganin Wana Rana
Kiyin hakuri Habibty kishayar dani ni,imar dake tatare dake nayi mikin Alkawari bazan mikin da zafiba
Rabata yayi dakayan dake jikinta yacin gaba da sarafata Adu'ar saduwa yayi a hankalin yasamu ya shigeta
wani irin Kara Ummeey tasa sakamakon wani a zabeben zafin dataji tak'asanta
Shiko Haydar baimasan tanayiba kuka take Tana rok'osa daya kyaleta
Haydar wani irin Santi dadin yake wada tuda yake baitaba jinshi cikin irin Wana yanayiba
Bai kyaletaba Saida ya tabatar yasamu nutsuwa sana ya kyaleta
Ummeey bakaramin galabaita tayiba saboda bak'aramin gurzar Tasha a gunsaba gawani zabeben zafin datakeji Yana ratsata
rugumeta yayi a kirjinsa yace Habibty wlh sai yazu nakara tabatarwa keta dabance a cikin mata
Kijiyar dani dad'in iri wada bataba jiba
Kishayar dani zuma kaunarki iri wace bantab'a shaba
Habibty ban,taba Tsitar kaina cikin farin ciki irin nawana Ranarba
matsayiki dabane a Raina nayi mikin tanadin Soyayyah zalla ba sirki Zan shayar dake ruwa kauna Mai hade da zuman Son Mai zak'i
A hankalin tabude bakinta tare da fadin Habibi Zan juri duk wani zafi da radadin mudin Zan sakaka cikin farin ciki Habibi burina Naga farin ciki nagudana akan fuskarka
Ashirye nake a koda yaushe wajan gani nabaka hakinka.
tare da saka cikin fari ciki Mai daurewa
Habibi Dan Allah karikeni Amanna kafi kowa sani cewa zuciyata dakai tasaba kada wata Rana kajuyawa zuciyar data zautu da muradin son kasancewa tare dai baya
Nikuma nayi maka Alkawari Zan kasance Mai biyaya a gareka zakayi Alfahari dani a matsayina na matarka.
A cikin Wana Dare Ummeey da Haydar sun daukawa junasu Alkawari Mai tarin yawa sukasace cikin fari ciki tare da shaukin son
WASHE GARI
Washe gari da safe Haydar yanufin bangare Rukayyah ya tarda ita kwace a kan gadon Ummeey nazaune a gadon sai wasa take Tana ganishi tafara dariya Tana k'okarin zuwa gusa daukarta yayi Yana murmushi yafara Mata wasa Ummeey sai kyalkyallewa da dariya takeyi
Kallon Rukkayah yayi cikin mamaki yace Momy Ummeey lafiya Naganki akwance a irin Wana lokaci
Tashi tayi zaune cikin gatsalin tace lafiyarce takawo haka kallon raini takemasa
Girgiza Kai yayi tare dafadin Ina breakfast dimu Naga shuru baki kaimanaba shine nazo nadauka Mana
Takaicine ya Kama Rukkayah a Ranta tace ama Wana mutumin ya Raina min wayo
Gani yayi Bata daniyar magana yace Rukkayah magana nake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 14