Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
Momi ta ɗago tana watsa musu harara kafin ta taso har gabansu. "Ku wasu irin mayu ne? wai ba'a faɗa muku bama ra'ayin haɗin auren nan ba kwaɗayi ne yasa Za'a ɗauki ƴata a bawa Ɗan uwanku to ni dana haifeta bana so Itama bata so don Allah ku ɗauki gayyar tsiyarku kuje kucewa Ubanku bama........ Da sauri Anty Nafi tace. "Kai kai baiwar Allah ya kike abu irin na Mutane marasa kan gado Shin ba mijin kine ya kawowa Baba tallan ƴarki ba har kike kiran kayanmu da gayyar tsiya wallahi ke kam baki gaji arziƙi ba duk inda kika fito daga tsiya kika fito Yau inda ina da iko sai na hana Saadik ya auri ƴarki sai kace autar mata kije kiga yadda ƴammata suke tururuwa akan shi ke an samu an liƙa masa jarabar ƴarki har kina da bakin magana" Anty nafi ta kai maganar cikin Ƙunar rai. Tabbas yadda su Farida suke jin zuciyoyin su bada ban taci darajar Baba Amadu ba da babu abin da zai hana su gargasa mata baƙaƙen maganganu amman wata fuskar tafi gaban mari taci arziƙin auren ƙanin mahaifin su sabida haka da sauri suke ficewa daga parlourn. Momi dan izzah da ƙasƙanci takan akwatinan ta dinga bi tana takawa tana tafiya zuciyar Aunty Nafi tai zafi ji take kamar Ranta zai fita dan ɓacin rai bata taɓa ganin mace mai izza da wulaƙanci da rashin sanin darajar mutum irin matar nan ba. Sai a titi suka haɗu da junan su Ya minau mai rauni tuni ta soma kuka. Umar ya samo musu ɗan sahu suka hau duk cikin su babu wanda ya iya magana, har suka ƙarasa Gida. Yanayin da suka shigo gidan kaɗai shiya fahimtar da innah abin da ke zuciyoyin su. Saadik yana zaune saman kujera ƴar tsugunno yana wanke takalmin training ɗinshi. Farida randa ta nufa tana shan ruwa. Su kuma suka zauna saman tabarma. Kukan ya Minau ne ya cika kunnuwan su. "Don Allah Innah ki cewa Baba yabar batun auren Saadik da Ƴar gidan Baba Amadu haba talauci hauka ne duk wahalar da muka sha ganin munyi komai cikin tsari abin ya kasa yiwuwa matar nan takan akwatinan da muka kai ta dinga bi tana takawa bayan cin mutunci da muzancin data mana.........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *15* Idanunta yayi burɗun burɗun yayi wani irin ja, fuskarta ta kumbura sabida tsananin kuka wanda take yin sa cike da tsana da ƙiyayya. Daga ita sai ɗaurin ƙirji daga dokin wiyanta zuwa cinyoyinta duk dilka ce Aunty Mariya ta sa wata mai gyaran jiki ta shafa mata gefe guda kuma ga haɗi na musamman a kofi wanda zuma ce da sauran ingantattun magunguna na gyaran jiki Aka zuba mata zata sha. "Rabi ba zaki ɗauki kofin nan ki kafa a bakin ki ba sai ranki ya ɓaci?" Cewar iyah wadda take zaune ta saka Adan a gaba. Hawaye ta share babu damar musu ta ɗauki kofin tana sha tana yatsine fuska. "Ina tausaya miki Rabi zaki je ki rayuwa wadda ba iri ɗaya data gidan ku ba, dama shiyasa ake son iyaye mata su horar da ƴaƴan su akan ayyukan gida da tarbiya sabida baka san ina ɗanka zai je yayi rayuwa ba, zaman aure zama ne na har abada sabida haka ki daure ki koyi tarbiyar zama da miji da kuma ƴan uwan shi sannan ki tina mijinki nada uwa nan ma sai kin koyi tarbiyar zama da ita" Duk abin da iya take faɗa tana jinsa ne ta bayan kunnenta domin tabbas bata shirya zaman auren ba babu wanda zata bi babu abin da zatai musu tinda har ya kafe sai ya aure ta, to ta ɗaura ɗamarar gasa shi  sai ya gwammace kiɗa da karatu tinda har ya nace sai ya aure ta. Tana kuka tana komi ta shanye maganin aka kammala mata gyaran jikin Aunty Mariya tace ta shiga wanka ga ruwan ɗumi can a toilet yana jiranta. Sai kallon banza take watsa wa dangin mahaifiyar tata waɗanda suka zo biki don wasu ma sai ranar ta sansu don ba shiga cikin su take yiba, ta tashi a wulaƙance ta shiga wankan. Wai inda aka ci sa'a ma tana shakkar Iyah don tsohuwar batai mata da daɗi shiyasa har ta ke yin abun da Aunty mariyar ta sakata. Koda tayi wankan ma zamanta tayi a ɗakin Iyah taƙi fitowa tana jin ƴan uwan iyah nata tsokanarta amman taƙi magana dama iyah ta kashe bakin kowa duk wanda ya tambayi bai ga Maryam ba sai tace maryam kam Kunya ta hanata zuwa wajan biki tana can gidanta tace gasu Mariya nan sune iyaye, tinda duk tsiya naka nakane baka bada fuska a wajan wani don ya ɓaci duk baƙin halin Maryam ƴarta ce, abin da yasa ma ta ɗauko Adaah tasan ba za'a wanye lafiya bane da Maryam shiyasa Abbah yace tayi taron a gidanta a ɗauki amarya agidanta dama ɗaurin aure a Ƙofar Gidan Baba za'a ɗaura tinda shine maɗaurin auren dama. Wajan magariba wasu daga cikin Dangin su Iyah suka dawo daga gidan Amarya sai dai motar data ɗauki kayan ɗaki ta dawo da fin Rabin kayan ɗakin a cewar wata daga cikin ƴan uwan iya ai kujera ma guda ɗaya ce doguwa kaɗai ta shiga falon, Uwar ɗaka kuma sun saka katifa don gadon ma yaƙi shiga sai akwatinan da aka sa don su madubi ma duk sun ƙi shiga sabida kayan ba ƙananu bane. Ataƙaice dai yadda suka sanar da Iyah falon ya sami carfet sai doguwar kujera guda ɗaya sai labulaye suma ba duka ba uwar ɗakan kuma katifa da akwatinan Adaah, Kitchen ma Gas yaƙi shiga sai tukwane da ƴan tarkacen ƙananun kaya ne suka sami zama sabida rashin wadataccen faɗi a gidan Iyah ta maida ajiyar zuciya tace. "Ai babu damuwa Allah ya sa albarka hakan, bari naiwa mahaifinta magana in yaso sai a maida kayan kawai" Sabgar haɗa miyar taushen biki aka cigaba da yi. Adaah na ɗaki tuni zazzaɓin takaici yayi awon gaba da ita ***** "Yanzu saratu duk yadda Jiddah tayi wa Saadik halacci haka zai mata kawai sai ganin katin ɗaurin aure mukai ana rabo?" Cewar wata maƙociyar su Jidda mai suna talatu. Umma ta kama haɓa tayi tagumi Cikin damuwa tace. "Ni duk ba wannan ba, na samu wannan uwar nacin ta rabu da shi gaba ɗaya ta fitar da shi daga zuciyarta ta nuna da shi da babu duk ɗaya amman taƙi kullum kuka wallahi jiya daga ni har mahaifinta bamu rintsa ba ni yaya zanyi ne" Ummah ta faɗa duk damuwa ta bayyana a saman fuskarta. "Hmm saratu ai tashi tsaye zaki ki samawa ƴarki farin cikinta, wannan aure ai na kwaɗayi ne naji ance ƴar ƙanin mahaifin sace mai kuɗi kuma ita kaɗai ubanta ya haifa kinga da zarar ta haihu ai dukiya ta su ce sabida haka idan har kina buƙatar taimako akwai wani da zan haɗaki da shi a jawo hankalin Saadik ya birkice muku" Umma tai jimm kafin tace. "A iya ganin idanuna ai kamar soyayyar da yake wa Jiddah ma ta wadatar in muka ce zamu haɗa da bin malamai zamu shiga haƙƙin sa, Ni kin san talatu bana harkar biyar malaman nan nafi gane tsaiwar dare, Nidai barni in raina ya ɓaci zanyi faɗana sosai amman bana raba imanina biyu in har Allah yace jidda matar Saadik ce zasu yi aure amman in har Allah bai ƙaddara ba babu wanda ya isa ya basu junansu" Cikin rashin samun nasara talatu tace. "Haka ne saratu to Allah ya daidata lamarin bari na ƙarasa gida" Ummah ta raka talatu har bakin ƙofa ta tafi. Ɗakin jiddah umma ta shiga ta sameta kwance da rigar baccin jiya a jikinta, ummah ta sami guri ta zauna a gefenta tare da kamota zuwa jikinta. "Kinga har yanzu jikin ki akwai zazzaɓi don Allah jiddah ki bar wannan damuwa nina fiki shiga tashin hankali amman yaya zamuyi mahaifin ki ya baki haƙuri nina baki haƙuri amman kinƙi daina kukan nan" Muryarta sanyi ƙalau tace. "Ummah kawu Saadik fa aure zaiyi gobe, duk yadda nake son shi ya kasa aure na a karon farko sai wata haba umma ta yaya zan sami Nutsuwa umma ki taɓa zuciyata kiji yadda take harbawa" Cikin faɗa ummah tace. "Zaki kashe kanki, ne a banza kinga sun kasa bikin su? ko kinga sun dena shirin su ina ba har lefe ya haɗa mata ba to in zaki gane karatun ɗa namiji ki gane, ni inda kinyi zuciyata da shi da babu duk ɗaya ki tattare su har mahaifiyar tashi ki watsar itama banda munafurci meye a auren da bakwa so harda gayawa maƙota su zo suga lefe in zaki buɗe idanunki ki kalli gaskiya ki buɗe, don Allah ko yayi miki magana karki kulashi ki gasa mai maganar da zatai mai ciwo" Jidda ta juya tare da lumshe idanunta tana jin son shi aduk kan gaɓɓan jikinta soyayyar shi na motsa mata kamar yanda Numfashinta ke fita sam bata jin maganganun umma zuciyarta ta tafi tunanin shi har umma ta gama faɗanta ta fita. A hankali ta jawo wayar umma data ɓoye a ƙasan pillow ta miƙe tare da rufo ƙofarta gudun dawowar umma. Ta kunna wayar tare da zuba wa wayar ido can kuma ta shiga Jera lambobin sa data haddace su akanta ta shiga kira. Saadik dake kwance don har lokacin bai ji daidai a zuciyar shiba, tinda ya dawo daga sallar asubah yake juyi a katifa yana jiyo sautin share sharen tsakar gida da yara keyi sai haɗa kayan gidan suke sabida shirin ɗaurin auren gobe. Baida niyyar tashi bare akai ga batun yayi wanka, gaba ɗaya jikinsa yayi masa nauyi dama abinka da jikin wahala an saba fafutukar nema. Wayar shi  ta shiga ƙara alamun kira na shigowa, a hankali ya lalubi wayar ganin lambar dake yawo a saman screen ɗin wayar yasa shi sakin murmushi har kiran ya katse sannan ya shiga kira yaushe rabon daya ji muryarta yaushe rabon da su haɗu gaba ɗaya ta yi masa yaji ta ɗauke masa wuta tinda maganar auren shi ta fasu shi kuma yana jin nauyin zuwa inda take duk da akwai shirin kai kuɗin auren shi gurin ta kamar yadda baba ya sanar da shi. Bayan ta ɗaga wayar shuru tayi masa. Cikin tattausar murya yace. "Ƴammatana an dena fushin dani kenan?" Turo bakin ta tayi kaɗan kamar yana kallonta kafin ta share hawaye. "Sabida kaga ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba ya sa ka zaɓi yi min haka?" Ya saki murmushin takaici. "Hawwa yaya kike so nayi ne mu duka bamu isa mu ja dayin Allah ba" Sai ta saka kuka. "Dama haka zaka ce daga nai magana sai ka faɗi haka amman ai wani abin ma akwai son zuciya acikin sa" Ta faɗa har lokacin tana kuka! "Kinga idan kin san ɓacin rai kika kira ki sa min zan kashe wayata haba ke wace mutum ce yaya kike so nayi ne kin san abin da yake damuna kin san meke zuciyata so kike na bujirewa mahaifina ne sabida farin cikin ki ko yaya?" Ya faɗa yana hucin ɓacin rai. Cikin sanyin murya tace. "Kayi haƙuri nima bani na ɗorawa kaina soyayyarka ba ka tayani da addu'a Allah ya yaye min" Sai ta saka masa rauni a zuciyarsa muryar shi a kwance ya shiga rarrashinta. Sai ga shi ta ware tana dariya, sam ta mance ma da damuwar data shiga cikin kwanakin nan ta kuma yi watsi da huɗu bar umma ta saka aranta Saadik ne farin cikin rayuwarta. Lokaci mai tsayi suka ɗauka suna hira kafin suyi sallama shima yaji wani sashi na zuciyar shi ya sami nutsuwa jin tana cikin farin ciki. Innah ce ta turo ƙofar ɗakin nashi ta shigo bakin ta dauke da sallama. Da sauri ya tashi daga kwanciyar da yake. Ya shiga gaishe da ita cikin ladabi "Sadauki ina ta zuba idanun ɓullowar ka gidan shuru, shiyasa nace bari naji ko lafiya?" Ya sauka daga katifa ya miƙe ƙafafun sa ya zube su a ƙasa yana cewa. "Lafiya lau, innah zan shigo sai nayi wanka yau na tashi da nauyin jiki ne" Ta kalle shi da kulawa "To  kayi hanzarin fitowa ciki ka sa wani abun acikin ka kaga rana harta fito" Cikin kulawa yace. "In sha Allahu" Innah ta fita shi kuma wata wayar ya ɗaga wani mutumin sa ne dake siyan ƙarafan shi a kasuwa suka gaisa mutumin yace. "Malam Saadik ashe lokaci yayi Allah yasa akhairi jiya Yaron ka ke faɗa min nazo shagon naka baka nan yace kuna shirin biki ne amman abin alkairi yazo ba labari" Yayi ɗan murmushi kaɗan. "Wallahi abin ne yazo babu shiri amman kayi haƙuri" Mutumin yace. "Ba damuwa ba zan sami damar zuwa ba, amman ga saƙo nan ba yawa na sa maka ta account Allah yasa albarka" Saadik yace. "Harda hidima to Allah ya sa ka da alkairi na gode ƙwarai" Sukai sallama daya duba kuwa dubu ashirin ne mutumin ya tura mishi. Wanka yayi ya shirya cikin ƙananun kaya ya fita cikin gida A bakin ƙofar kitchen ya sha shayi da biredin da innah ta haɗa masa Atm ɗin shi ya bawa Umar yaje P.o.s ya ciro masa dubu ashirin ɗin da mutumin ya turo masa gaba ɗaya ya bawa Innah yace ayi cefane anjima zai kawo shinkafa zai je janguza domin tafi sauƙi acan. Inna ta karɓi kuɗin ta ƙirgi dubu goma ta miƙa masa sauran. "Dubu goma ta isa sadauki ina da shinkafa ta ba sai ka siya ba, ka bar kuɗin ka ni ba wani taro zanyi ba idan ƴan uwana sun zo sai ƴan uwanku na makoɗa shikenan sai waɗannan yaran" Ya ɓata fuska. "Innah me kike siyarwa da zaki ce zaki hidimar ƴan biki nifa innah ban so ki ɗaga hankalin ki Allah ya rufan asiri komai zanyi" Fafur taƙi amsar kuɗin nashi. Sabida tausaya masa take nauyin yayi masa yawa yayi nasu yayi na marayun gabansu sannan ga na gidan shi zai fara. Haka ya fita ba dan yaso nauyin data ɗora wa kanta ba, zuwa rana ƴaƴan innah sun hallatara sai matar ƙaninta da matar yayanta sai Yayarta da Anty nafi sai wasu daga cikin dangin su Baba na makoɗa da suka zo miya su Aunty hajjo suka ɗora a ranar dai kwanan hira akai damma burin da suka ci abikin bai cika ba sabida ɓacin ran da suka kwaso washe gari maƙota suka shigo tayin kwasar tuwo wajan takwas an haɗa komai na ɗaurin aure. Tin ƙarfe goma su nura suka ishi Saadik daya shirya sufa sun kintsa sabida goma da rabi za'ai ɗaurin auren. Cikin farar shadda ɗinkin babbar riga da ƴar ciki ya shirya kansa da hula da agogon silver fari a tsintsiyar hannun shi sai baza ƙamshi yake da ka ganshi kaga ango ya fita ƙofar gida abokan shi suma duk farar shaddar suka sanya irin tashi suka sanya shi a tsakiya suka shiga cikin gida Innah ta saka sabuwar atamfa sai gaisawa take da ƴan uwa ta waya waɗanda basu sami damar zuwa bikin ba. Tana ganin tawagar su saadik ta saki Murmushi tana kawo hannu ta rungume shi bayan ta kashe wayar, sai ta hau kuka! Saadik ya sa hannu yana share mata hawayen nata su Ya Minau mai za  suyi  inba dariya ba gaba ɗaya yadda Innah tai ya bayyana tsantsar soyayyar da take wa Saadik da ƙyar ya cireta daga jikin shi suka fita wajan ɗaurin auren Ƙofar gidan sune wanda tuni ya cika da mutane sabida Abba yayi gayya Baba ma yayi gayya. Ƙarfe goma da rabin safiya alƙawarin Allah ya tabbata Aka ɗaura auren. Abubakar Muhammad Makoɗa.                        Da Rabi'atu Ahmad Makoɗa. Akan sadaki mai daraja shaidu suka shaida,bayan anyi addu'a tare da fatan alkairi ga amarya da ango Baba da Abbah kowa ya shiga gaisawa da mutanan shi. Duk yadda saadik yaƙi faɗin ɗaurin auren nashi hakan bai hana jama'a tururuwar zuwa ba haka kowa ya dinga janshi ana hoto sai dai fuskar shi sam babu sukuni musamman daya ga yayyen jidda da mahaifinta sun tawo wajan shi suna yi masa Allah ya sanya alkairi. Ƙwarya ƙwaryar walima suka yi ba wani waje suka jeba anan ƙofar gida su Babawo suka dinga raba abinci a ledar takeaway wa abokansu wanda shi sam bai da labarin wannan hidima sai yanzu daya ga suna yi. Sai wajan ƙarfe ɗayan rana jama'ar suka rarragu sannan ya sami keɓancewa da Abbah da baba da wasu daga cikin ƴan uwan su na makoɗa Su babawo na waje suna jiran shi, shi kuma yana tsugunne a soron wajan mahaifan shi. Abbah ya dube shi. "Abubakar Ga amanar Rabi'atu na sabida yau ina jin na sauke nauyin dana ɗaukarwa kaina ko yanzu Allah ya karɓi raina burina ya gama cika don Allah don Annabi ka riƙe min ita amana" Muryar Abba tai rauni sosai wanda hakan yasa jikin Saadik yin sanyi shima baba nasiha ya dinga masa kafin ya bashi umarnin zuwa gidan iyah shida abokan shi domin su gaisa da ƴan uwan amarya. Ba don yaso ba yabi umarnin mahaifin nashi. Mota suka hau ta wani abokin su zuwa hotoro sabida Baba ya sanar mai acan ake taron da yake yasan gidan kakar tata shiyasa suka tafi can kai tsaye Da yake motar gida ce sunyi saurin ƙarasawa gidan Iyah nan ɗin ma akwai taron mutane. Ƴan uwan iya suna ganin tawagar angwaye suka hau buɗa harda masu fesa turare har falon Iyah akai wa su Saadik iso wadda ta cika da farin ciki maɗaukaki. Suka zazzauna a saman kujerun falon masu tsokana nayi masu hotuna nayi. Daga ɗaki Aunty mariya taitai da Adaah ta fito wajan angon nata taƙi sai ma kifa ciki datai a kan gado tana rusa kuka. Da ɓacin rai Aunty mariya take sanar da iya batare da kowa ya kula ba. Cikin hikima iya ta dubi saadik. "Kasan kishiyar tawa da kunya taƙi fitowa tin safe ko zaka shiga ku gaisa ne?" Kanshi a ƙasa yace. "A,a dama mun leƙo ne mu gaida ku nan ma ya isa" Ƴan uwan iya ne sukai masa caa akan sai ya shiga sun gaisa da amaryar tashi ba dan yaso ba ya miƙe Aunty mariya tai masa iso zuwa ɗakin Iya. Ya dakata a bakin kofa batare daya ƙarasa cikin ɗakin ba. Sautin kukan ta ya cika ɗakin da ƙyar ma idan tasan da shigowar shi. Miƙewa tai tana rangaji zata shiga toilet sabida fitsarin daya ciyota, haɗa ido sukai da juna atare gaban su ya faɗi. Kasa taka ƙafarta tai sabida nauyin data mata. Shi kuma ya tsinci kanshi da kafeta da ido yana hango ramar datai ta ƙara baki idanunta ya faɗa lallai ba ƙaramar tsana taiwa auren shiba kamar yadda shima ya tsani auren nata. Ƙaramin tsaki taja kafin ta juya da sauri ta shige toilet ɗin ta banko ƙofar. Murmushin gefen baki ya saki tare da juyawa yabar ɗakin. Sallama sukai dasu iya suka fita zuwa mota suka nufi gida. Sabida yawan mutane yasa yayi kwanciyar shi a shagon Nura duk da abokan su nata shigowa suna masa Allah sanya alheri. sallah kaɗai ke tada shi don bai shirya tinkarar gida yanzu ba sabida mutane. Ƙarfe Shiddan yamma motocin dasu saiti suka nema dan ɗauko amarya suka jeru a ƙofar gidan Innah ƴan uwansu na makoɗa ne mutum biyu suka shiga motar don ɗauko amarya. Cikin mutunci su Aunty mariya suka karɓi masu ɗaukar amarya wadda sai da akai da gaske sannan ta shirya aka fito da ita tana kuka kamar ranta zai fita. Har motar ta tsaya a ƙofar gidan Innha Adaah tana kuka Aunty Mariya da wata ƴar uwarsu suka kamata kanta a lulluɓe suka shigar da ita gidan Innah wanda wannan shine zuwanta na farko gidan a  tun  tasowar ta da girman acire ƙuruciya bata sani ba ko an kawo ta amman dai da girmanta wannan ne karon ta na farkon zuwa gidan. A rumfar innah suka zaunar da ita duk yadda aka so innah tai magana taƙi kanta yana ƙasa ba zaka fahimci abin da yake ranta ba ganin lokaci naja ne yasa suka miƙar da Adaah suka nufi gidanta da ita. A ƙaramin falon ta saman doguwar kujerar da aka saka guda ɗaya suka zaunar da ita Lokacin daga ita sai Aunty mariya sauran mutanan sun fita a hankali Aunty mariya ta yaye mata mayafin. Tare da ce mata. "Rabi'atu kinga dai yadda Allah ya tsara miki rayuwarki ko ba a faɗa miki ba kin san gidan da kika shigo sabida haka ki cire duk wata izza da taƙama ki biyayyar aure in sha Allah zaki alfahari da wannan auren naki" Ita dai kuka take har Aunty mariya ta gama mata nasihar tabar gidan falon ya rage da ga ita sai halinta. Idanunta ta buɗe tana bin falon da kallo duhu ne sosai acikin sa don hasken fitilar dake kunne ya fara mutuwa alamun batir ɗinta yay sanyi, ga uban sauro wani irin zafi ke shiga jikinta ware idanunta tai wannan wani irin gida ne acikin wannan gidan zatai rayuwa ita da ko wanki bata taɓa yi a rayuwarta ba amman shine za a kawota wannan gidan wanda ko kitchen ɗinsu na gida bai kai girma ba. Dunƙulewa tai guri ɗaya ta daddage ta zunduma ihu mai cike da tashin hankali fargaba ɗimuwa damuwa.......... SHIN WACE IRIN RAYUWA ADAAH ZATAI A GIDAN SAADIK? SHIN WANI IRIN ZAMA ZATAI A TSAKANIN UWAR MIJI? DA KUMA BUDURWAR MIJI WADDA SUKE TSANANIN SON JUNA? SHIN ZATA RABU DA MAHIR? WANI IRIN SHIRI HAJIYA LUBNA ZATAI AKAN CIKAR BURINTA? WANI IRIN MATAKI MOMI ZATA ƊAUKA AKAN AUREN? SHIN AUREN JIDDAH DA SAADIK ZAI YUWU? SHIN ZAMAN ADAAH DA SAADIK ZAI YUWU WANI IRIN ZAMA ZA SUYI WACE IRIN RAYUWA ZA SUYI ZATA SO SHI? KO SHI ZAI SOTA? GA DAI ADAAH A GIDAN TALAKA ƊAN GWANGWAN MAI CINIKIN ƘARFE DA ROBOBI YA ZATA SHIN FIƊA RAYUWARTA AGIDAN SHI WADDA ITA TA TASO GIDAN HUTU GIDAN JIN DAƊI WANDA KO WANKI BATA IYA BA BARE SHARA BARE ƊORA ABINCI SHIN YAYA ZATAI DA RAYUWAR GIDAN TALAUCI? AKWAI TARIN ABUBUWAN DA BAN ZAYYANO BA. SOYAYYA ƘAUNA SADAUKARWA YAUDARA CIN AMANA DUK ACIKIN LITTAFIN SO DA ALƘWARI TABBAS IDAN GANGA TA CIKA ZAƘI FASHE WA ZATAI BAN CE NA KAI BA AMMAN ZAN ƘAYATAR DA IKON ALLAH. DUK WANDA YA SAKA KUƊI YA SAI RABO YA RANTSE BAƘON LAMARI AI BAI NADAMA BA, BARE KUMA WANNAN DA AKA ƊAUKI TSAYIN LOKACI ANA SHIRYA SHI DUK DOMIN JIN DAƊI DA FAƊAKAR DA MASOYA KU SHIRYA BIYONI CIKIN TAFIYAR SO DA ALƘAWARI LABARIN SAADIK DA ADAAH DA JIDDAH YANZU MA AKA FARA WASAN DUK SHINFIƊA MUKAI A FREE PAGE YANZU LITTAFIN ZAI FARA RAYUWAR ƳAR MAI KUƊI MAI IZZAH DA TAƘAMA AGIDAN ƊAN JARI BOLA. WANNAN SHINE ƘARSHEN SHAFIN KYAUTA MA'ANA LAST FREEE PAGE BIYA........ 500 NAIRA A SAKAKI A PAID GROUP ZUWA ASUSUN BANKIN 0078174806 STERLING BANK KO KUMA 9022260850 OPAY BANK, GA MASU SON A SAKA SU A GRP KENAN WAƊAN DA SUKE SON NAKE BASU A PRIVATE KUMA BA SAI NA SAKA SU A CIKIN GROUP BA SU 1000 NAIRA ZA SU SAKA A BANKIN SAMA, A TURO SHAIDAR BIYA ZUWA WANNAN LAMBAR 09022260850. NOTE! Idan na kammala littafin nan complt ɗin sa zai koma 1000 naira ne kamar koda yaushe idan ina rubuta littafi farashin sa 500 naira ne idan na gama shi kuma complt 1000 naira ne. WANNAN KARON BEST IN REALITY MUKA TAƁO. AUTAR MANYA.🌹 Marubuciyar..... *RABON WANI* *BAƘON LAMARI* *RABO YA RANTSE* *FITAR RABO* *ƊAN MAJALISSA* *HASKE* *KOBA SO* *ZUMA A BAKI* *BAƘAR FATA* *ƁOYAYYAR ƘAUNA* *BA SONTA NAKE BA* *AUREN BARE* *DA IZZATA* *YANKAN ƘAUNA* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi

Chapter 9 of 10