Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 10
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION                      *001* Lumshe idanunshi yake yana shaƙar sassanyar iskar dake kaɗawa a harabar ƙaton gidan a hankali yake jan tsaki ƙasa ƙasa yana sake duba agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannun  shi ya kai mintina goma a zaune babu alamun zata zo, tsaki yaja a karo na barka tai gaba ɗaya ranshi ya gama ɓaci a duniya idan da abin da ya tsana shine jira Kasancewar shi mutum mai kazar kazar da zafin nama, marar haƙuri da ɗaukar raini Zuciyarshi ce take zafi nan da nan idanunshi yayi jajir Gumi na yanko masa daga saman goshin sa ƙurawa hanyarta idanu yayi har ya tashi ze bar wajan ƙamshin turarenta yayi masa sallama tun kafin ta ƙaraso wajan ƙamshin haɗaɗɗan turarenta ya gama cika wajan. Tafiya take kamar ba zata taka ƙasa ba, cikakkiyar Budurwa ce Ƴar Gajera  baƙa mai jiki, baƙinta irin mai ƙyallin nan ne dan irin sune ko man saka haske suka shafa ba lallai ya amshi fatar suba amman da yake akwai hutu da jin daɗi a tare da ita se Baƙin nata ya murje ya ƙara mata ɗan karan kyau. Babu wani abu a fuskarta mai haske se fararen idanunta waɗanda baƙa ƙirin ɗin ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata idanun nata Zanan idanun nata kuma se yayi kamar ta shafa kwalli daga saman hancinta kuma gumi ne wanda ze tabbatar maka da ita ɗin babu sauƙi mafaɗaciya ce bata wasa ba, tana tafe tana huci harta ƙaraso inda yake.         Ƙerere ta tsaya a saman kanshi tana karkaɗa jikinta ta saka hannu ta kama ƙugunta, Nuna wa yayi kamar bai san da wanzuwarta a wajan ba, wanda hakan seya ƙara tunzura zuciyarta wannan wani irin ƙasƙanci Abbanta yake son yayi mata duk faɗin samarin ta babu wanda Abbanta zece ta aura se wannan gajan kuma yaro ƙarami wanda bai fi sa'an haihuwar ta ba dan bata jin zai girme mata, tun jiya take son fahimtar da Abban ta cewar ita fa tana da wanda take so yake son ta amman yaƙi sauraren ta akan wannan kucakin, Tun da take da Abbah bai taɓa Yi mata faɗa kamar na jiya ba kuma duk silar zuwan wannan yaron da Baban Chiranchi Ya turo wai ya aure ta Tsaki taja acikin zuciyarta tana kau da tunanin Ɓacin ran da suka kwasa jiya ita da Momi Mahaifiyarta akan zuwan wannan ƙolon. Jitai zuciyarta na ingizata akan ta gargasa masa baƙaƙen maganganun da zai ji haushi Ya ƙi dawowa. Saadik wayar shi ya ciro ya kunna data ya shiga facebook ya na duba posting ɗin jama'a gaba ɗaya ya shagala ya ma mance da ƴar rainin hankalin yarinyar dake gabanshi wadda taci albarkacin Mahaifin shi wanda umarnin shi ma yabi har yazo wajanta dan shi ne ya tursasa shi akan sai lallai yazo ya nemi auren ƴar ƙanin nashi ko Allah yasa ta silar hakan zumuncin su ya ƙara ƙarfi. Bai taɓa zuwa gidan Kawun  nashi da girman shi ba, se yau hasalima ita yarinyar da aka turo shi wajanta bai ko taɓa saninta ba bare yasan sunanta duka se yau ɗin da yazo gidan bisa tirsasawa da bin umarnin mahaifan shi. Takaicin yarfin daya mata ne ya fusata ta cikin zafin zuciya ta miƙa hannu ta warce wayar hannun nashi tai wurgi da ita jikin ginin dake kallon su kafin ta soma magana a zafafe! "Aikin banza aikin wofi an gaya maka talaka yana da alfarmar wulaƙanta mai kuɗi kai ɗan gidan uban waye! da zaka....... Bata ƙarasa faɗin maganar ba tai saurin faɗuwa a wajan tai zaman ƴan bori hannu biyu ta sa tana dafe kuncin ta sabida azababbiyar gilmawar wutar data gani a cikin idanunta. Ba kuma wutar bace zafin Hannun Saadik! Ne ya gigita ta, Akanta ya tsaya yana huci bayan ya ƙarasa sauke mata marika har guda uku a jere Huci ya saki mai zafi yana Naushin Iska Allah ya bashi zafin rai na masifa sam baya ɗaukar raini baya son wasa shiyasa ko acikin gidansu Yara na shiga hankalin su in suka jiyo muryar shi kai babban ma idan Saadik ya rikice masa shiga hankalin sa yake. Cikin dakakkiyar Muryar shi wadda ta ratsa dodon kunnenta ta kuma hautsina mata ƴaƴan hanjinta yace mata. "Wuce kije ki tattara min wayata banza shasha sha ballagazar mace"! Kuka take Tuni Kuncinta ya haye kuma taƙi koda motsi a wajan sabida masifar kafiyar ta. Tsaki yaja cike da fushi ya wuce fuww yabar mata wayar batare daya haɗa wayar tashi ba,bare ya ɗauka, sabida yana jin idan har ya tsaya a wajan ze ɓallata ɓallin masifa wannan tasa yayi gaggawar barin Gidan. Ta ka ƙasa yake kamar ze tsaga ta tsananin zafin zuciyarsa tasa har numfashinsa na ƙoƙarin barin gangar Jikinsa. Daga gadon ƙaya zuwa ɗorayi Chiranchi da ƙafa yaje gida Yana shiga Ɗakinsa dake soron gidan ya shige tare da faɗawa saman katifa yana lumshe ido hoton fuskarta yake gani acikin idanunshi gaba ɗaya haushi da tsanarta na mamaye zuciyar sa, sam baya son mutum mai izgili da girman kai, baya son mutum mai wulaƙanta mutane, domin baka san baiwar da Allah yayi wa kowa ba. Anya zai iya bin umarnin Baba? shi kam yana jin yafi ƙarfin mace ta wulaƙanta shi duk kuɗinta duk mulkinta domin bai nema daga wajanta ba, Shi talaka ne amman mai zuciyar nema domin ta ko ina Allah bai kassara shiba ya bashi rai da lafiya da dakakkiyar zuciyar neman halak ɗinsa uwa uba wadatar zuci wadda yake jin in mace huɗu ya aura zai iya ciyar da ita da halalin sa. Mirginawa yayi tare da miƙewa, ya fita cikin gidansu bakin Rijiya ya tsaya zai ɗebi ruwa a bokitin daya riƙo don ya watsa a jikinsa sabida Zafin ranar da ake tsulawa a garin. "Kawu Saadik kawo na zuba maka ruwan" Inji Khadija ɗaya daga cikin Jikokin gidan nasu waɗanda Innar shi ke riƙewa a wajanta. Fuska babu walwala ya miƙa mata Bokitin ta cika masa shi da ruwa ya ɗauka ya koma cikin ɗakin shi ya shigar banɗaki ya watsa a jikinshi ya fito Farin yadi marar nauyi ya saka ya fesa turare mai sanyin ƙamshi ya fita zuwa cikin Gidansu sai Lokacin yaji zuciyar shi na masa sassauci na daga Ƙuncin daya kwaso Innah na tsige zogale Zarah na gefenta nashan Koko. Da gudu ta aje kofin tazo Jikin shi ta ɗane shi ta hau yi mashi surutu. "Kawu Saadik Innah tace dambu zatai mana, Kuma Ɗazu Baba yace kaje wajan Matarka wai aure zaka yi?" Murmushi ya yi kaɗan tare da shafa kanta. "Zarahh Sarkin surutu mai shan koko da rana" Sai Lokacin Innah tayi magana. "To ya za'ai kasan Rigimar Mutuniyar taka nayi ranar abincin ne yau wai Ummi na aika kai ɓarzar tsakin masara Wallahi tafi awa biyu nace Nanah ta bita itama shuru, Ita kuma wannan sarkin cin se kuka take yi shiyasa na bata sauran Kokon Babanku" Matsowa yayi ya zira hannu cikin zogalan yana tayata Aikin zagewa. Batare daya ce komai ba. "Wai yaya kukai da Gidan Kawun naka?" Cewar Innah. Cikin son ya basar da maganar dan tina wa ma ɓata Masa rai yake, Ya ɗan langwaɓe kaɗan tare da cewa. "Innah nima fa yunwar nake ji, amman zan fita shago In kika gama ki bawa wani ya kawo Min" Sarai tasan dan ya basar da maganar ne, Setai murmushi ta shiga yi masa fatan dawowa lafiya zarah na bashi saƙon abin da zai tawo mata dashi yana Murmushi yana amsawa har ya bar Gidan. Ido jajir ta faɗa cikin katafaren falon gidan nasu wanda ya kusa girman wani gidan ihun ta har cikin ɗakin baccin momi wadda ta fito a guje dan masifar sauri zaninta har kunce wa yake yi a gigice ta nufi wajan Yarinyar tata Ƴa ɗaya tamkar da Goma kenan Ƴar gata dangin kitse a barka a inuwa ka daskare a saka ka a rana ka narke, Cikin tattali da Riritawa tamkar tsoka ɗaya a miya ta Rungumeta duk a kiɗime take mata magana. "Babyn momi waya taɓa min ke kika shigo kina kuka kin san yadda kukan ki yake ɗaga min hankalina wallahi kaina har juya mini yake sabida azabar faɗuwar gaban da kukan ki ya haifa mini" Shure ƙafafunta take tana ƙara sautin kukan tana janyo hannun Momi zuwa fuskarta Jikin Momi ne ya hau rawa sakamakon shatin yatsun data gani kwance a kunci shalelen tata a zabure tace. "Kan uba waya miki wannan illar lallai ya tafka ganganci domin zanyi shari'a da kowa ye sannan kuma zan ɗaure kaf ahalin su har igiya tayi rata dan uban sa!" Sangartaccen kuka ta kuma saki lokacin Momi ta zauna ta ɗorata a kan cinyarta In kaga yadda sukai zaman seka yi dariya sabida ita aba ƙatuwa an tashi an ɗora ki a saman cinya ko Kunyar hawa ita kuma bata jiba. Cikin siririyar muryarta wadda in kaji ta seka rantse bata ta bace domin muryar irin ta ƙananun yara ce, Tace. "Ba wannan gaulan da Abbah ya turo bane ya mare ni dan cin zali ban masa komai ba" Tunkuɗe ta momi tayi ta tashi a zabure tana sintiri a falon Fuskarta fal bala'i wanda ta hau surfashi har seda muryarta ta dashe. "Dama nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, Mai talaka ya sani akan mace face ya mai da ita baiwar sa wato shi dan ubansa har wuyan sa yayi kaurin da zai mareki an gaya masa bakin rijiya wajan wasan makahone to aikuwa zan tauna tsakuwa don aya taji tsoro sabida wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa" Gaba ɗaya kalamin Momi sun sanyata acikin duhu don waɗannan karin maganar bata sansu ba bata iya suba seta zubawa Momi idanunta da suka kumbura suka ƙara girma sabida kuka. A sassauce momi ta dawo gareta ta sunkuya gabanta haɗi da dafa gwiwowin ta kana tace mata. "Shalele na kwantar da hankalin ki babu wani ɗan iska faƙirin talakan da za'a aura Miki ni za'a wa tawaye rabu dani da Abban ki yadda Allah ya bani ke ƙwaya ɗaya tal wallahi ba zan yadda rayuwarki ta salwance, a gidan talaka ba, ai se duniya ma tai min dariya ƴaƴan aminaina daga mai auren Ƙusan gwamnati sai mai auren ɗan kasuwa shahararre sannan ni tawa ta auri ɗan jagaliya talakan banza ina sam sai dai in ba ni maryam bace na haife ki" Kwantar da kanta tayi a cinyar momi tana jan ajiyar zuciya. kafin tace. "Momi in kika min haka zan ƙara alfahari dake, wallahi Ina da wanda nake so Habib yana sona ina sonshi Ɗan ajinmu ne tare muke lecture da shi baban shi mai kuɗi ne Tun tuni yake son na bashi dama amman naƙi gashi nan Abbah yayi min shigar sauri kuma ba kowa bane zai zuga Abba se Baban Chiranchi dama kince ba ƙaunarki yake yi ba" Hura hanci Hajiya Maryam take tana kaɗa ƙafafu ita kaɗai tasan tawayen da zata wa Alhaji Amadu Mijinta in ya dawo Jira kawai take ya shigo gidan ba zata tsaya ayi mata sakiyar da babu ruwa ba. Tashi tayi daga jikin Momi ta nufi bedroom ɗinta Yadda ta bincike Wardrobe ɗinta ɗazu haka tazo ta tarar da ita bayan kafin ta fita seda ta cewa Maimuna Mai aikinta wadda aikinta agidan shine gyara mata ɗakinta da kuma bata abinci da kai mata ruwan wanka ta gyara mata kayan kafin ta dawo amman shine bata gyara ba, Sabida haka Rigar jikinta ta cire ta janyo zani ta ɗaura ta fito falo tana kwaɗawa maimuna kira Lokacin Momi bata falon ta shige room ɗinta. Cikin tsumar Jiki maimuna ta ƙaraso gabanta ta zube tana cewa. "Ai mini afuwa uwar ɗakina banji kiran bane se yanzu" Tsaki taja mai ƙarfi tana zabgawa maimuna harara kafin tace mata. "Ai ba zaki ji kirana ba, Munafuka kina can kina kallo kamar wadda ta warke a makanta dan Ubanki ni zan gyara Miki ɗakin?" Nan da nan jikin maimuna ya hau rawa abin tausayi ta soma bata haƙuri, Tsaki taja ta wuce saman seater ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya. "Na baki Minti Biyar kije ki gyara Mini ɗakina sakarai" Da sauri maimuna ta wuce bedroom ɗin nata, Ita kuma zama tayi a falon tana karkaɗa ƙafa tana Ayyana Zafin shigar marin daya mata ɗazu Tsintar bakinta tayi da furta Allah Ya Isa! Muryar maimuna ce ta dawo da ita daga tunanin data faɗa. "Uwar ɗakina na kammala Allah ya huci zuciyarki" Bata ko kalli Maimunan ba ta miƙe ta shiga ɗakin kwanciya tayi akan gado tana janyo wayarta dake gefenta tarin Kira daga Saurayin ta Habib harda ɗan guntun saƙon shi Ƙorafi ne akan Yana ta kira bata ɗauka ba. Mayar da wayar tayi ta aje sam ita soyayya bata gabanta, duk da tana da masu sonta samari da masu aure masu kuɗin gaske kawai bata sauraron sune ta ɗan fi kula Habib shima tsananin nacin sa gare ta ne yasa take ɗan kula shi a waya da kuma in sun haɗu a school. Kiran nashi ne ya katse mata tunaninta. A hankali ta ɗauka kamar bata so. "Amincin Allah ya tabbata a gareki sabihata hasken idanuna my madarata" Haɗe ranta tayi sam kalamin bai wani ratsata ba meye wani madara dan iskanci itafa bata son irin haka ta lura yawanci maza jikinta suka fi so ba ita ba, dama Allah baya haɗa maka duka duk yadda takai da halinta ita ɗin ba mutuniyar banza bace tana da taka tsantsan wajan kare mutuncinta ta wannan fagen za'a iya bata lambar yabo ta ɗaya. "Sweet ina maki magana kin min shuru haba mana" Tashi tayi zaune tare da cewa. "Look Habibu nifa bana son wannan kashe murya da kake yi min ni ban maka shagwaɓa ba sai kai zaka yi min goɗai goɗai dakai haba mana" Daga ɓarin shi yaɗan zare ido Gabanshi ya faɗi, shifa wani bin har shakkar yarinyar yake ita ko ɗan feeling ɗinnan bata ji kamar wata dutse, Amman ba ze sare ba zai cigaba da lallaɓata har haƙon shi ya cimma ruwa dan shi kam ya kwaɗaitu da Yarinyar daga ganinta zatai ɗanɗano a matsayin sa na shahararran ɗan Duniya wanda yasan mace ciki da bai sabida yana da kuɗi mahaifinsa na sakar masa kuma yana da ɗaurin gindi wajan tsohon nasa shiyasa yake facakar sa yake hurɗa da duk maccen daya ke so. Ita kaɗai ce tai masa zarra duk wannan kwanton da yake mata Kansa yake wa tanadi amman yasha gwadata ta hanyoyi da dama ya gano zafin kai kawai gareta amman bata biyar mazan banza. Cikin ƙwarewa da harkar bariki yace. "To yi mini naji please zumana" Yadda ya fitar da sautin seda ya rikita ta matse Jiki tayi kamar mai jin sanyi kasancewarta mace mai tsananin buƙata wannan dalilin yasa take nesanta kanta da maza domin ta gano ba son ta suke ba Jikinta suke maitar so shiyasa take ƙaurace wa masu sonta domin ta kare martabarta. Muryarta a shaƙe tace. "Zanyi sallah Habib sai anjima" Murmushi ya saki daga jin muryar tata yasan ta kamu seya kuma jefa mata wata maganar wadda ta sanya ta saurin kashe wayar gaba ɗaya ta wurgata can ƙarshen gadonta, ta kama Lips ɗinta tana cijewa Idanunta lumshe tana Sakin zazzafan Numfashi kafin a hankali ta Miƙe ta shige toilet wanka tayi ta ɗauro alwala sai Lokacin ta sami damar sallar azahar ta haɗe da la'asar babu ko kunyar Ubangiji na haɗe sallolin data yi. Kallo ta kunna ko zai ɗebe mata kewa sabida jiyo sautin maganganu daga Room ɗin Momi tasan ƙawayen nata ne ƴan gado da suka saba cika masu gida kusan koda yaushe suna hanyar gidan nasu. Ko wacce matar wani ce don a ƴan group ɗin su momi babu matar talaka, dukkan su matan masu da shi ne. A wannan kallon ta lalace har akai magariba da ƙyar tai sallah ta cigaba da kallon nata, bata damu da karatu ba duk da suna exams sabida akwai wata ƙawarsu mai ƙoƙari da take taimakonsu. Su kuma suke bata kuɗi don ita ba ƴar masu kuɗi bace bayan sallar isha'i ta kashe kallon ta kunna wayarta ta kunna data ta shiga grp ɗinsu suka hau Hira da ƙawayenta. Kiran Abba ne ya shigo wayarta ya bata umarnin ta fito yana falo Hijabi ta sanya akan kayan baccin data saka ta fita falo  inda ta tarar da Momi da Abbah a zaune Momi se kaɗa ƙafa take tana hura hanci Shima Abbah babu walwala a fuskar shi kallo ɗaya tayi masa tai ƙasa da kanta domin yau babu wannan sassaucin da riritawar da yake yi mata. A ƙasa ta zauna tai ƙasa sosai da kanta kafin tace. "Abbah barka da dawowa gani" Da hannu ya amsa mata kafin ya gyara murya yace mata. "Rabi'ah ni wanene a wajan ki?" Jikinta ya hau rawa kirjinta yana bugawa ta ɗago tama kasa furta koda kalma guda ɗaya sabida tsananin ta shin hankalin daya ziyarce ta. Ya buga mata tsawar data sa ta ɗimauce wa. "Nace ni waye a wajanki?" Da sauri tace. "Ba.ba.na" Muryarta na rawa. "Idan har ni Ahmadu nina haifeki to baki da miji sai ɗan Yayana sabida haka ki fara shiri a ko wani Lokaci zan iya ɗaura Miki Aure da ABUBAKAR" Wani irin tsalle tayi sai gata a gaban Abba... 09022260850 ​    *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *002* Ta sa hannu ta kama ƙafafun Abba tana wani irin kuka mai cin rai wanda yake bayyana tsananin ƙiyayyarta ga auren da ya ke shirin yi matan. "Abba kaiwa girman Allah kada ka min auren dole, Abba bana son shi bana ƙaunar shi ba kalata bane ta ko ina nafi ƙarfin shi Abba shifa talaka ne ni kuma Mai kuɗi ta yaya zaka haɗani da ƙasƙantaccen mutum........ Gigitaccen mari Abba ya sharara mata abin da bai taɓa yi mata ba kenan tunda tazo duniya shine duka koda wasa bai taɓa dukan Adaah, ba, sabida soyayyar da yake yi mata amman a yau furucinta ya saka ya mareta Cikin ɓacin rai yace. "Ni zaki watsa wa ƙasa a ido wani bambanci ne tsakanin ki da shi yana ɗan Yayana cikin mu ɗaya da mahaifin sa to bari Kiji Komai zaki sai dai kiyi amman Muddin Nine mahaifin ki auren nan babu fashi" Yana gama faɗin haka ya wuce fuww yabar falon. Adawiyyah, ta zube a wajan tana wani irin kuka, Momi tsananin baƙin ciki ya hanata yin magana sai faman huci take yi kafin ta yunƙura ta kamo Adah tayi cikin Room ɗinta da ita. Zaunar da ita tayi a saman Gado tana rarrashinta. "Nina san asiri sukai wa Abbanki domin nasan a duniya bai da wani farin ciki sama dana ki amman a yau bana hango soyayyarki a idanun shi sai tsananin tarin rikici" Ido shaɓe shaɓe da hawaye ta kalli Momi. "Shikenan ni yanzu aura min shi zaku yi momi bakwa sona in dai kuka aura min mai suffar samudawan can wallahi bai da imani ko kaɗan gashi talaka ƙawayena ma suka san Shina aura wallahi kashina ya bushe" Momi ta rungumeta tana ta rarrashinta tare da bata ƙarfin gwiwa akan lallai lallai zata san yadda zata yi auren nan ya lalace. Anan ɗakin momi tayi sallar isha'i ranar Ko abincin dare bata iya ciba itama momi bata je ɗakin Abbah ba domin fushi ta ɗauka dashi sosai. Se bayan Adaah tabar ɗakin ne momi ta ɗauki waya ta kira ƙawarta. Bayan ƙawar tata ta ɗauki wayar tare da cewa. "Hajiya maryam yaya naga wayarki da wannan dare ina fatan dai lafiya?" Momi cikin damuwa tace. Hajiya lubna dole kiji wayata a wannan lokaci domin Alhaji ke son ɓallo min ruwa ɗazu nake son gaya miki to naga bamu kaɗai bane shiyasa. Hajiya lubna tace. "Ina sauraron ki Hajiya maryam" Momi ta karkace tana zayyanewa Hajiya Lubna abin da yake faruwa sabida akaf duniya babu wadda momi ta yarda da ita kamar Lubna ƙawarta ce Aminiyarta. Seda Hajiya lubna ta gama jin komai sannan taja tsaki! tana cewa. "Akan wannan ƙaramar maganar har zaki ɗagawa kanki hankali, mai akai da auren talaka, in kika kuskura ƴarki ta aure shi to se kin siyar da akuya ta dawo tana ci miki danga, sabida haka ni a ganina wannan matsalar ƙarama ce kota ƙarƙashin ƙasa kibi ki lalata abin" Momi ta yarfe zufa! A raunane tace. "Lubna kin san halin mahaifiyata  ba son biye biye take yi ba, har baki tai min muddin nabi wata hanya don biyan buƙatar kaina" Lubna taja tsaki! "To Iyah tasan sanda zaki To shikenan ni dai iya shawarata dake kenan in zaki yi kiyi in ba zaki yi ba shikenan su waya san abin da suka banko suka ruɗa miki Mijin naki" Momi da damuwa tace. "Ni ban san me nayi wa Baban chiranchi ba, baya ƙaunata ko kaɗan haka kwanakin baya yace se lallai Alhaji ya ƙara aure da ƙyar maganar ta mutu mai nayi Musu da zafi" Ta faɗa tana kuka don lokacin zuciyarta ta karye. Da wannan damar Lubna ta zugeta tas nan suka ɗaura alƙawarin gobe zasu yi sammakon zuwa wani ƙauye, duk akan su rusa maganar Auren Adaah. Lubna hatsabibiya ce ta gasken gaske ita ce sitiyarin momi a bin malamai kaɗai suka banbanta Ita Momi tana tsoron bakin da mahaifiyarta tai matane shiyasa bata biyewa lubna ta nan ɓarin ba, Amman a duniya Momi bata da aminiya kamar Lubnah. Da shirin fita momi ta kwana a iya zamanta da Abbah bata taɓa bin wata hanya don cikar burinta ba amman akan auren da yake son ƙaƙabawa ƴarta tana jin sai inda ƙarfinta ya ƙare. Tun asubah datai sallah bata koma bacci ba wanka tayi ta zauna jiran drivern Hajiya Lubna da zaizo ya ɗauketa bata jin ko Abba ma zata gayawa inda zata je tunda tasan a fushi yake ba lallai yabi ta kanta ba, Sedai wajan ƙarfe Bakwai na safiya wayar ƙaninta Abbas ta

Chapter 1 of 10