Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
wannan wahalar dan wa nakeyin ta hatta mahaifiyata fushi take dani duk akanki" Adaah ta nisa kafin tace. "Momy nifa fahimtata ce baki ba, wallahi gaba ɗaya Mahir ɗinne bai yi mini ba kar nazo na aure shi ku sami matsala da aminiyarki" Momi ta kwantar da murya ganin yadda jikin Adaah yayi sanyi tace. "Ki haƙuri ki min biyayya, Adaah ki auri mahir kodan mu bawa marar ɗa kunya kinji ƴar albarkar momynta in sha Allah wannan haɗi namu alheri ne abin da nake so dake da zarar abbanki ya dawo ki kafe kice ke Mahir kike so kinga daya bamu dama mu dama a shirye muke" Adaah cikin rashin madafa tace. "To Momy zan yi yadda kike so ɗin amman nikam bai mini ba" Momi tayi murmushin cin nasara kafin tace. "Zai miki ne da zarar kun zauna waje ɗaya Allah dai ya maki albarka" Kwanciya Adaah tayi a cinyar Momy idanunta suka cicciko da ruwan hawaye don dai kawai bata son ta zubawa momin ƙasa a ido ne sannan kuma ta bata tausayi na wahalar data ce mata ta sha shiyasa zata karɓi auren Mahir ɗin. Sai dare sosai Momi tabaro ɗakin Adaah har sai da ta tabbatar ta saki jikinta damuwar da ke tattare da ita ta kau sannan tai mata sallama ta baro ɗakin ta koma nata waya tayi wa Hajiya Lubna akan gobe mahir ɗin zai iya dawowa su gana da Adaah dama ɗazu ciwon kaine ya saka bata fito ba. Makirin murmushi lubnah tayi tare da cewa. "Kai haba Maryam wajan jibi ya dawo abarta ta ƙara hutawa shima kin ganshi tinda ya dawo ya ɗagamin hankalina akan ciwon kan nata" Daɗi ne ya rufe momi cikin farin ciki tace. "Ga wanda ya dace ƴata ta aura wanda ya san darajarta yasan damuwarta harya ji ya damu da damuwarta ba wancan shegen baƙin mugun ba, daya zo ya gargasa mata baƙaƙen maganganu ba, ta mutu ko tai rai shi babu ruwan sa tinda su in da zata mutu ba so zasuyi domin suci gado" Hajiya lubna mai zatai in ba dariya ba. "Kai ƙawata baki da dama wallahi" sallama sukai suka kashe wayar ranar Momi taji iska mai sanyi na shigarta domin tana jin ta gama da Kaso Hamsin cikin ɗari sauran yaƙin gabanta kuma na Abbah ne don tana jin sai dai duk abin da zeyi yayi amman bafa zata bar wannan aure ba muddin tana da numfashi! tinda har ta sami nasarar shawo kan Adaah sannan shima Mahir ya karɓi abin hannu biyu to fa tana jin sauran yaƙin gabanta ba komai bane. ** Washe gari wajan ƙarfe goma na safiya Iyah na zaune a falonta gabanta kuma Alkur'ani ne mai girma ta karanta shi, ta shafa ta aje shi a gefe ɗaya, sannan ta juya ta kalli Abbas dake zaune a gefenta yana waya, bayan ya kammala tace masa. "Abbas kira min Amadu Mijin maryam jiya nayi mafarki marar daɗi ina fatan Allah ya tsare Maryam daga sharrin dukkan abin ƙi" Abbas ya shiga kiran Abban Adaah a waya wanda sai da wayar ta katse sannan Abbah ya kira. Cikin girmamawa suka gaisa da Abbas sannan ya miƙawa Iyah. Abbah ya shiga gaisar da iyah cikin mutunci da sanin ya kamata. Iyah ta gyara murya kafin tace. "Amadu yaya batun auren Rabi ne naji kwana biyu baka bugo munyi magana akai ba" Daga wajan Abbah cikin farin ciki yace. "Alhamdulillahi Iyah dama yaron namu ne ya nemi da a ƙara masa lokaci sabida ya gama shirye shiryensa, shiyasa ma maganar ta ɗan kwanta" Cikin dattijantaka iya tace. "Haba Amadu shifa irin wannan aikin alherin ba a jinkiri wajan aiwatar da shi sabida magauta wannan abu fa duk na cikin gida ne sabida haka, ni zan sa akira min Ɗan uwan naka ai da lambarshi a wayar Abbas, se muyi maganar data kamata ayi a ɗaura auren nan sabida ina gudun kar maganar ta lalace" Abbah yayi murmushi cikin ƙarfin zuciya yace. "Da ikon Allah maganar ba zata lalace ba iya" Sallama sukai cikin mutunci kafin ta umarci Abbas daya kira mata lambar baba, wanda Lokacin yana kasuwa kiran ya shigo sama sama suka gaisa dan bai ɗauki murya ba, sai da ta masa bayani sannan ya gane nan suka kuma gaisawa a mutunce sannan ta shiga yi masa maganar data sa ta kira shi a wayar. Baba ya nisa kafin yace. "Ni bana gida ne, ina wajan nema amman bari na sa a sako miki lambar wayar sadaukin sai ki masa waya kuyi maganar, kinsan yaranmu sai haƙuri shi yace yafi son yayi komai kamar yadda ake yi a yayin aure to kuma abin ka da marar ƙarfi fafutukar ake yi" Cikin Nutsuwa Iyah tace. "Haba haba malam kamar ba gida ba nifa yadda na ɗaukaki wannan aure abin sai ya baka mamaki maza turon lambar mijin nawa muyi magana" Baba ya sa dariya yana cewa. "To to iya angode da karamci" Ya kashe wayar tare da miƙawa wani yaro dake gefen shi yace ya turawa lambar data kirashi lambar wayar Sadauki. Baba yana ta murmushin karamcin iyah wato albasa ce batai halin ruwa ba, inda tayo ruwan da batai yaji ba. Minti kaɗan lambar ta shigo wayar Abbas shi kuma ya kira wa Iyah lambar wadda taita ringing ba a ɗauka ba. Da yake fita zai yi sai ya aje mata wayar yace koda za a kira seta ɗauka suyi maganar. Tai mashi fatan alheri ya fita. ****** An sallamo Jiddah daga asibiti sai dai har zuwa lokacin Ko waya Saadik bai sake yi mata ba, kuma dama bai faɗawa Innah suna asibitin ba bare suje dubiya, Gaba ɗaya ran ummah ya gama ɓaci mita take tana cewa ga baki ga hanci ai ko iyayensa ne sa zo dubiya bare shi. Duk Jidda tabi ta damu ta ƙara komawa ƴar firit sabida Mitar umma da kuma damuwar rashin Jin Saadik.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *10* Zaune yake a bakin rijiya hannun shi riƙe da kofin da Innah ta cika masa shi da koko gefen shi kuma ƙosai ne wanda yake dangwala da yaji yana ci yana korawa da kokon. "Haba kokai fa nina fi son ka dinga cin abinci sosai koka yi ƙiba kaike nan sai tsayi babu kauri" Saadik ya ƙunshe dariyar shi sabida gudun kada ya ƙware sai da ya kammala sannan ya ɗago idanun shi ya kalli innah tare da ce mata. "Haba hajjaju kullum fa sai na fita filin ball na ɗan motsa sabida naga har tumbi ya fara zamarmin ni kuma bana son shi, ni banga rashin ƙibata ba" Innah tayi murmushi. "Sanda kana yaro kafi haka fa yanzu duk ka rame sai tsayi ma sha Allah, nidai Sadauki ka dinga zama kana cin abincin ka sosai" Tashi yayi da kofin da plate ɗin Ƙosan daya kammale ya miƙa gaban kayan wanke wanke wanda Khadija ke zaune tana yi sannan ya ƙarasa wajan Innah ya mata sallama sabida shago zai fita addu'ar alkairi ta dinga yi masa har bakin ƙofa ta raka shi Ɗakin shi ya shiga ya ɗauki wayar shi da makullin shagon da Umar ya bashi ɗazu da Asubah da suka fita masallaci ya rufo ɗakin ya fita. Yana fita suka haɗu da Baffa mahaifin Jidda shima da alamun fita zaiyi da ɗan sauri ya ƙarasa wurin Baffan suka gaisa ya ƙara masa ya mai jiki. Saadik na durƙushe baffa yace. "Malam Abubakar kafa yi haƙuri da halin mata naji duk abin da Saratu tayi maka a asibiti kuma nai mata faɗa ai wannan shashancine dama ina son ma na gana da mahaifinka gwara ko kuɗin auren ne ku kawo asan inda magana ta dosa in yaso ta na kammala karatun nata sai ayi biki ina ga abin da zamuyi kenan Amman kayi haƙuri don Allah" Saadik ya shafa kai tare da cewa. "Haba Baffa karka sa damuwa acikin ranka, Ni ban riƙe abun ba ina ga ita Ummah fahimta ce batai ba Allah dai ya shiga lamuranmu gaba ɗaya" Baffa ya ansa da "Amin" Saadik ya miƙe yayi hanyar fita daga lungun shi kuma Baffa ya ƙarasa wajan Babur ɗinshi da zai hau ya fita. Sai da yaje shagon ya zauna sannan ya ga kira da sabuwar lamba a wayar shi, ya ɗan shiga mamaki sai da ya sallami matasan da suka kawo masa wani Fayif sannan yabi kiran. Cikin kamilalliyar muryarshi Yayi sallama, daga ɓarin Iyah ma ta Amsa cikin Nutsuwa. "Dama naga kira ne ɗazu" Ya faɗa kafin yayi shuru yana sauraron abin da za'a faɗa. "Eh nice nasa a kira min mijin da bai kawo min kayan faɗar kishiya ba" Yadda ta faɗi maganar yasa yayi murmushi mai sauti duk da bai fahimci abin da take nufi ba. "Kakar Rabi ce in babu damuwa ko zaka zo muyi magana" Ya shiga tunanin wace rabin wace kakar rabin maganar iya ta kuma katse masa tunanin shi. "Rabi wadda zaka aura mana ƴar ƙanin mahaifin ka amadu" Sai lokacin ya tina Iyah bata bari ya shiga dogon nazari ba ta ce masa. "Hotoro zaka zo tsamiyar boka anan gidana yake inda hali ina neman ka yau, In kazo seka min waya Abbas ya ƙaraso dakai" Jin muryarta da alamun girma ya kamata yasa ya ƙanƙantar dakai tare da cewa. "In sha Allah zanzo idan anyi sallar la'asar" Iyah tayi masa godiya ta kashe wayar. Yaɗan nisa yana tunanin kiran data ke masa kafin ya watsar da abun ya shiga sallamar mutane bashi ya sami kanshi ba sai dab da magariba kawai bari yayi idan anyi magaribar ya je don yadda ya gaji ma bada ban ya mata alƙawari ba da baze iya zuwa ba. A masallacin da yake kallon shagon shi yayi sallar magariba da yake yau basuyi awon ƙarafe da robobi ba jikin sa tsaf yake sabida haka titi ya ƙarasa ya tari Napep zuwa hotoron da yake akwai go slow saboda magariba ce ƴan kasuwa da ma'aikatan gwamnati na tashi daga aiki bai ƙarasa ba sai wajan sallar Isha'i koda ya sauka ma sai da yayi sallah sannan ya shiga layin da Abbas yayi masa kwatance a bakin layin ya dakata ya kira Abbas wanda ya ƙaraso suka shiga Gidan Iyah. Cikin mutunci suka gaisa da Abbas sannan ya shigar da shi falon iyah tana zaune a ƙasan Carfet gabanta kuma kwanon tuwo ne da alamun ta kammala cine. Saadik ya ƙarasa gabanta a nutse ya shiga gaishe da ita. Iyah ta miƙe da sauri ta shiga wani lungu jim kaɗan sai gata da ƙaton tire wanda ta zubo masa Ruwa da lemo da Fulas ɗin Abinci a gefe. Zata aje yayi saurin tashi ya karɓa ya aje Dattijuwa ce sai dai Jikinta irin na fulani ne a murje yake babu gigita bare rakwarkwaɓe wa a tare da ita. Samun gurin zama tayi ta zauna cikin sakewa tace. "Ango na ga kayan sanyi nan ka sha na sanku sarai da son sanyi ga tuwon amaryarka nan kaci nan gida ne karka ƙi ci dan Allah" Ruwan ya ɗauka ya sha kaɗan ya aje. Tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cikin rashin sakewa. Iyah ta gyara sosai ta fuskance shi tare da cewa. "Wato zaka ji wani iri ne nasan sanda na maka waya, dama ba komai bane yasa na kiraka sai maganar auren ku da Rabi, Ni na haifi maryam mahaifiyar Rabi" Da sauri Saadik ya kalli Iyah ko kaɗan daga kammani har hali ba iri ɗaya bane da waɗancan sabida Ita wannan Tsohuwar akwai ta da mutunta ɗan adam da sanin ƙimar shi saɓanin su. Ta nisa kafin ta cigaba da magana. "Munyi magana da mahaifin ka ɗazu yace kace masa sai ka kammala shirin ka kafin ayi batun aure ban da abin ka naga duk gida ne mene zai saka ka ɗaga hankalin ka, kaga duk abin da kake da shi kayi fatana Allah yasa inga wannan aure da raina da lafiya domin shine babban burina" Saadik ya shiga mamakin furuncin nata kafin ya maida ajiyar zuciya yace. "Haka ne Baba, amman kin san lamarin yadda ya zo minne duk da bai zo min cikin shiri ba dama abin da Allah ya hore min shi zanyi kuma na gode da karamci" Iya ta kalle shi wani farin ciki na ƙara ninkuwa a zuciyarta tabbas Jikarta tai sa'ar miji. "Kayi haƙuri da duk abin da zaka gani ko kaji nina haifi Maryam nafi kowa sanin halinta, Kuma dukkan wani hali nata ƴarta rabi shita kwafe sabida haka don Allah don Annabi ka zama namiji ka tsaya sosai akan tarbiyar Rabi domin daɗin dana ji da Allah yasa jininta zata aura ba bare ba, sabida haka kayi haƙuri ka rungumi wannan aure ina da yaƙinin alheri ne in sha Allahu" Ƙasa yayi da kanshi yana jin ninkin sassaucin zuciyarsa na game da damuwar auren kafin yace mata. "In Allah ya yarda Babah Nagode Allah ya ƙara girma" Iyah ta miƙe tare da cewa. "Ɗan ci tuwon tsofi bari na baka guri" Ruwan kaɗai ya ƙara sha ya saka hannu ya rafka tagumi, Minti kusan goma Iyah ta dawo wurin yana ganin ta dawo ya miƙe yana mata sallama Dubu biyu ya zaro ya aje mata tare da cewa taci goro har bakin ƙofa ta bishi tana masa tsiyar baici tuwon ta ba shidai Murmushi kurum yake harya fita daga gidan. Wani irin ƙima da darajar tsohuwar na ninkuwa a ranshi tabbas! ya ga karamci da mutunci a tattare da ita kuma daga gani macece data san karamci. Ya jima a titi kafin ya sami abin hawa aiko kira ne rututu Innah ke masa. Sai da ya shiga abin hawan ya zauna sannan ya ɗauki wayar tata tambayar shi take a ina ya tsaya ta aika shago akai masa abinci baya nan. "Innah ina abin hawa ganinan In sha Allahu" Ya kashe wayar ya jingina da ƙarfen napep ɗin yana nazarin maganganun tsohuwar can wato sudai mutan da suna da kirki da karamci bai taɓa ganinta ba sai yau amman jinta yake kamar mahaifiyar Innah sabida abin da tai masa. Har ya ƙaraso gida yana ta Murmushi shi kaɗai a babban titi ya tsaya yayi siyayyar kayan shayi sabida Ya gaji da cin ƙosai da Kunu koda koko gaskiya gobe shayi za'ayi. Yasai Liptom yasai madara da su sugar ya tsaya yasai ƙwai tare da ƙaton burodi. Sauran canjin daya rage ya sayawa Innah kifi karfasa yasan tana son karfashe musamman wanda ya kwana domin maggi yafi ratsa shi idan ya tsumu. Sai daya kammala siyayyar sannan ya ƙarasa gida ya shigo lungu suka haɗu da Babu, wanda shima dawowar shi kenan gaisawa sukai babu ya shiga gida shima ya ƙarasa gida sabida su Babu a farkon Lungu gidan su yake gidajen su na kallon na juna dana su Nura saiti su kuma su Saadik nasu gidan a ƙarshen lungun yake akwai tazara a tsakanin su. Yana ƙoƙarin shiga gida yaganta a raɓe a bakin ƙofa yi yayi kamar bai ganta ba. "Kawu Saadik" Ta faɗa murya a shaƙe. Juyar da kai yayi zai shiga soro tayi saurin tare gaban shi. "Don Allah karka shiga ka bari muyi magana" Cak ya tsaya tare da zuba mata ido. "Dan Allah kawu Saadik kayi haƙuri da abin da ummah ta gaya maka nasan shiya ɓata maka ranka" Shuru yayi mata. "Allah fa nace" Ta faɗa tana yin ƙasa da kanta gaba ɗaya jikinta yayi sanyi na yanayin shi data gani. "Kin gama zan shiga gida kin tare min hanyata" Ta langwaɓar da kanta. "Kawu Saadik Allah fa nace maka" Shuru yayi mata. "Kawo kayan na riƙe maka mu shiga gidan" Nan ma yayi mata banza. "Lahh kawu saadik ledar burodin ta fashe, kawo na riƙe kada ya faɗo" Shuru yayi mata ganin hakan yasa ta fashe da kuka ta durƙushe a wurin ta dinga zunduma masa ihu! ganin zata jawo hankalin mutane kansu yasan ya yayi gyaran murya tare da cewa. "Kinga in magana zaki ƙara jawo min dan Allah jeki bana neman duk wata magana mai zafi a yanzu ki barni da abin da yake damuna" Share hawayen take tana cewa. "Kawu saadik yaya zanyi na cire soyayyarka a zuciyata duk yadda naso na rabu dakai kamar yadda Umma ta faɗa min na kasa duk rufe idon da zanyi hotonka ke yawo a idanuna" Ya jingina da bango. "To kibi maganarta mana, ai shawara ta baki kinga tin kafin ki mutu azo ana nine sila gwara kin kama kanki" Sai ta ɗago ta kalle shi da kyau. "Nike nan nake haukana ka dena sona sabida ka sami wadda ta fini ka sami ƴar masu kuɗi ko?" Maganar data faɗa ta ƙarshen nan ita ta karya masa zuciya wato ko yayi niyyar yi mata ƙaura inta masa laifi akwai abubuwan da in tayi kota faɗa masa yake sawa yayi saurin janyewa daga ƙaurace matan. "Hauwa waye yace maki ƴar masu kuɗi ce?" Ta tashi tsaye ta na turo baki. "Zancen duniya yana ɓuya ne" Yayi murmushi mai ciwo. "Baya ɓuya kam amma nayi mamaki kuma in tunanin ki haka ne to kinyi tunanin ƙarya domin ni har yanzu banga kuɗin da zai sa na auri mace ba kawai shi aure nufi ne na Allah" Hawaye ta goge. "To yanzu ka daina fushin dani?" Ya tsira mata ido. "Ki nutsu Hawwa wannan shirmen naki ki daina ta yaya zaki je wurin ummah ki haɗa min sharri ni yaushe na tsallake na barki a sume?" Ya faɗa yana zuba mata girman idanun shi. Ƙunshe fuska tai a cikin hannayenta. "Kayi wa mai so uziri man kawu" Murmushi yayi. "Shine aka ce shi mai son yayi ma masoyin sa sharri yanzu fisabilillahi haka mukai dake" Ta tura ƙaramin bakinta gaba kaɗan tare da cewa. "Bana baka haƙuri ba ni ya kamata ma a rarrasa da aka ma kishiya amman ni na zo biko Nikam wannan mallaka da kama zuciyata har tai yawa" Bai niyyar dariya ba amman seda ta sa ya dara. Da sauri ya faɗa soro yana ta dariya shirmen jidda wani bin mamaki yake bashi in tai wani abun kamar ƴar fari koda yake akwai ƙuruciya a tare da ita. Juyawa Jidda tayi don ba zata iya binshi gidansu ba tana jin kunyar suman data yi da abin da ta dinga faɗa akan shi a gaban Innah da baba sai yanzu abin ke bata kunya ita ɗaya inta tina seta rufe fuska tana murmushi. Saɗaf saɗaf ta shiga gida ta faɗa ɗaki domin umma bata san ta fita ba sai dai duk abin da tayi umma na kallonta ta window ɗaga murya umma tayi tare da cewa. "wallahi jidda kin bani kunya na dena shiga tsakanin ki da Abbakar in sha Allah duk abin nan da kukai amman saida kika tare shi ai da fitarki da shigowarki duk ina lura" Ƙunshewa tai a ɗaki kamar ruwa ya cinyeta har umma ta gama ɓaɓatunta daga ƙarshema baccine ya ɗauketa. Cikin gida ya shiga har lokacin dariyar yake sai da ya ƙarasa tsakar gidan sannan ya daidai kansa duk su innah na baje a tsakar gida suna shan iska. Yayi sallama su ummi suka shiga yi masa sannu da zuwa. Ya kalli salmanu dake kan rijiya yana cin tuwo. "Kai yau ina ka shiga?" Fuska a ɗaure yayi maganar. Salman ya shafa kanshi. "Kawu munje kallon kilisa ne" Girgiza kanshi yayi bai ce komi ba ya ƙarasa kusa da Innah sai dai jikin salman yayi sanyi sanin shuru Kawu Saadik ba alheri bane ƙarshe zane shi zai sa Umar ko Usman suyi da safe sabida ya hana shi zuwa kallon Kilisa abin da yasa ya faɗa yasan inya masa ƙarya zai bibiya shiyasa kai tsaye yace masa ga inda yaje. "Ai salmanu kamar mai kunnen ƙashi yake Allah dai ya shirya mana zuri'a sam baya jin magana" Inji innah. Saadik bai ce komi ba ya aje ledojin hannun shi tare da ma innah sai da safe. Gaba ɗaya agajiye yake ne. Yana shiga ɗakin sa,salman ya biyo shi da kwanikan abinci ya aje daga bakin ƙofa sannan ya tsugunna yace. "Kawu don girman Allah kayi haƙuri" A hankali yace "Jeka salman Bording ɗin maza kawai zan nema maka wallahi na gaji da jamin magana da kake yi" Sum sum salman ya miƙe jiki a sanyaye yabar gun yasan kawun nasu baya son naci. Sai da yayi wanka sannan yaci abincin taliya ce jallof mai ruwa ruwa yasan innah shi kaɗai taima sabida sanin aminin taliyar ne. Ya jima bai bacci ba dan sai da yayi nafila ya daɗe yana addu'a akan lamarin auren nashi sannan ya kwanta. ********* Yau gidan na Momi ya kacame Maimuna sai shiga take tana fita tsakanin Kitchen da dining ana shiryawa Mahir abinci momi sai nan nan take da Adaah gudun kada ta Botsare anci sa'a tai wanka ta shirya ta zauna zaman Jiranshi wajan Magariba ya ƙaraso gidan a babban falon da maimuna ta shirya masa abinci Momi ta sauke shi sai da Ya cika cikin shi da ci da sha sannan Adaah ta miƙe ta isa wurin shi yana zaune a saman Kujera ya wani harɗe ƙafa........ SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *11* A lokacin da take zama a saman kujerar, lokacin yayi daidai da sanda gabanta yayi mugun faɗuwa hannu ta ɗora a ƙirjinta wanda ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi a hankali ta lumshe idanunta ta buɗa akan shi wanda shi sai murmushi yake yi mata tsintar kanta tayi itama da sakar masa murmushin tana jin wani abu na fusgarta mai kama da so! Ya matso kusa da ita ya zauna ƙamshin su ya gauraya wuri ɗaya. A hankali ya miƙo hannu zai taɓa nata hannun sai tai maza ta zame tana yin ƙasa da kanta. "Yaya jikin naki?" A hankali ta furta. "Da sauƙi Alhamdu lillahi" Cikin ƙwarewa da iya hira da ƴammata yace mata. "Baby tin jiya ban kwana cikin daɗin rai ba, sabida tinanin ciwon kanki" Cikin sanyin murya tace. "Ai naji sauƙi fa" Bata da wani saurayi sai Habib duka shima sau ɗaya ta bashi dama sukai hira ranar daya kawota gida sabida haka sam bata da ƙwarewa a hira da Saurayi tinda ba zancen takeyi ba, sabida haka Mahir ne ya dinga hirar tana amsawa da "Eh" Ko ta ɗaga masa kai bai tafi ba sai bayan magariba har bakin Motarshi ta rakashi. Ita dai koman ta ya tsaya tin sanda sukai ido huɗu da shi bata sake samun sukuni ba, Wani irin sonsa ne taji yana fisgarta. Sam wannan aibun nashi data dinga gani jiya ya gushe a guje ta faɗa falo tana kiran Momi. Cikin sauri Momi ta fito gabanta na faɗuwa zatonta ko wani abun ne sai dai ga mamakinta ganin Adaah tayi tana murna tana tsalle cikin farin ciki tace. "Momy wallahi yayi min ashe Jiya ban zauna da shi bane, Nikam Ina sonshi Momy har yafi Min Habib sau dubu" Momi ta rungumeta itama tana murnar tare da cewa. "Barka Ƴar albarkata" Nan suka shantake suna hirar yadda zata kaya ba tare da tinanin ayi sallah ba bare azo kan Azkar! Da maɗaukakin farin ciki Mahir yake tuƙi ya matsu yaje gida ya faɗawa Hajiyarsa yadda sukai da Adaah sabida haka da farin ciki yakai gida shima tindaga bakin Ƙofar falo yake kiran Hajiyar tasa, Wadda itama ta taso tana cewa. "Me ya faru ne wannan kira haka?" Kamota yayi suka zauna ya shiga bata labarin yadda sukai da Adaah sosai tai farin ciki da jin yadda komai yazo cikin sauƙi. Jin hankalinta take yayi mugun kwanciya kuma ta shaida alƙawarin aikin malam daya mata akan lallai sai ya juya hankalin Adaah ya dawo kan Mahir wanda ga shi kuwa tin kafin aje ko ina aikin yaci kwalliya ta biya kuɗin sabulu ƙarashen ne ya rage mata. ****** Washe gari da safe Saadik ya shiga cikin gida wajan Baba yaje suka gaisa wanda yayi shirin fita kasuwa. Shima bai wani zauna ba ya fita Ƙofar ruwa yaje wajan wani mutumin sa wanda suke harkar Ƙarafe dashi cikon kuɗin da ya biyo mutumin ya karɓa daga Ƙofar ruwa kawai Gidan Aunty Aminah ya wuce rana gatsal a garin haka ya shiga gidan duk Gumi ya gama rufe shi. A falonta ya zauna suka gaisa Miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki Sai gata da manyan ledoji har guda uku ta aje a gaban shi. Sannan ta fita kitchen ta haɗo masa abinci da ruwa mai sanyi ta kawo masa gaban shi tana zama a kusa da shi tare da cewa. "Auta sha ruwan sanyi kaci mutuniyar

Chapter 6 of 10