bala'i ne ya kwanta Jijiyar dake kanshi ta Miƙe babu abin da jikin sa yake sai rawa yana mazari kamar wanda yasha maganin tauri Ƙafarsa ke takawa tana wa gangar Jikinsa linzamin Isa gabanta, wanda ita kuma Adaah keja da baya gaba ɗaya idanun shi ya tsoratata ga gida babu kowa yana binta tana yin baya tana yarfe hannu.
Cikin Hukuncin Allah sai da yakai ga sunje ƙarshen Falon ta raɓe da bango ta ɗora hannunta duka a fuskarta ta rufe gaba ɗaya yanayin sa ya firgitata sai tace ita bata taɓa ganin Namiji mai Irin suffar shiba Ingarman namiji ne kamar wanda yake cin ƙarfe.
Hucin Numfashin sa mai zafine ya daki fuskarta hannu yasa ya tokare bangon data raɓe ɗin wanda Sauran kaɗan fitsari ya biyo ta jikinta sabida kaɗuwa.
"Dani da ke waye sakarai?"
Ya nisa kafin ya cigaba.
"Sakarai shine mai cusa kanshi inda ba'a neman shi, tallanki aka min aka liƙamin ke yau ɗinnan sai da Ubanki ya biya gidanmu ya ƙara roƙata akan nazo wurin ki To bari Kiji bakya Birgeni baki min ba cutar dani akai da Biyayya zan karɓeki danni bana Bijirewa mahaifina Amman wallahi ban taɓa ganin halittar dana tsana na ƙyamata Lokaci ɗaya ba kamar ki, Kisa a ranki zanyi auren cikon Umarni ne dake ba domin soyayya ba ƙazama wadda bata san Ciwon kanta ba bata san martabar Jikinta ba shasha sha"
Ya faɗa tare da jan wani irin tsaki mai ƙarfi ya juya da sauri yabar falon
Da wani irin yanayi Adaah ta zame daga tsaye ta zauna ta ɗora hannu aka tana rusa Kuka.
Ba'a taɓa Yarfata kamar yanzu ba ya cuceta ya danƙara mata maganar data fi marin daya mata Jiya illah.
Tashi tayi tana watsi da kayan falon tana kuka tana ihu tana Jin dama Allah zai karɓi ranta kafin Lokacin auren su yayi.
Da sauri yake fita daga gidan Ko ina na jikinsa Rawa yake har Lokacin idanunshi a juye suke kamar ya sha ƙwaya Allah ne kaɗai ya kaishi Titi Lafiya ya tari abin hawa zuwa gida.
Ya ci alwashin Ba zai ƙara komawa wajanta ba, Kuma Yana fatan Allah yayi gaggawar Watsa lamarin auren su baitaɓa ganin Mace irin ta ba wai dame taƙe taƙama ne haka? Gumi ne ya cigaba da yanko masa ta ko ina Kirjinshi na masa zafi da taimakon Allah ya ƙarasa Gida yana shiga ya faɗa ɗakin shi ya rufe kanshi.
Babu abin da yake se mayar da Numfashin Bacin rai, a haka ya zauna har Lokacin magariba yayi lokacin yaji zuciyar shi tayi sanyi sai yayi alwala ya fita masallaci.
Tin suna tafiya mai daɗi har sai da Momi ta ƙosa ta dubi Lubna wadda take ta Hira da Drivern ta da alamun sun saba irin tafiyar.
"Waini Lubna ina zaki kaini ne har yanzu bamu ƙarasa ba duk sammakon da Mukayi"
Lubna tayi dariya tare da cewa.
"Cinikin kanki zanyi don Kin san Kanki zeyi kuɗi"
Dariya sukai Driver yana karkata kan motar suka nausa Cikin Jeji Momi ido kawai take zarewa Ko yaya Motar ta Bugu Momi seta hau salati Gaba ɗaya tsoro ya kamata haka sukaita tafiya har sanda suka shiga ƙauyen.
Tafiya kaɗan sukai suka ƙarasa Ƙofar Gidan Mai Rumfar Kwano mata ne zazzaune ga masu awara nan da masu wainar Gero ga masu Nama driver yayi parking Suka fito Ƙafafun Momi duk sun kumbura sabida zama Hajiya Lubna wajan mai nama taje ta siyo Musu Ita kuma Momi wajan zama ta samu don ta gaji sosai.
Bayan Lubnah ta miƙawa Driver Ƙullin Nashi ta iso wajan Momi suka fara ci batare da tunanin Yin sallah ba.
Seda akai la'asar layi yazo kansu Lubnah ta dakatar da Momi ta fara shiga sannan daga baya ta Kira Momi.
Babban mutum ne zaune akan farin Buzu ya sha manyan kaya ɗakin sa babu wata alama da zata Nuna wa Mutane yana Tsubbu Irin sune masu ci da Buguzun Suna tsubbu ta ƙarƙashin ƙasa a fili Kuma suna Nuna wa jama'a su Na Allah ne.
Seda ya cewa Lubna ta rufe ƙofa sannan ya janyo kwanon sha ya zuba ruwa ya ɗora hannu akai ya tura gaban Momi.
Zaro idanu Momi tayi tare da cewa.
"Ranka ya daɗe wannan Ƴata ce Adawiyyah da Mijina a cikin Ruwa"
Dariya yayi tare da shafe saman Ruwan Hoton su Adaah ya baje.
Kafin yace.
"Kinzo da Buƙata Biyu ta farko a Juya kan Mijinki akan auren Ƴarki Na biyu Kuma a raba shi da Ɗan uwan shi kwata kwata"
Momi ta Gyara zamanta sosai Cike da mamaki tace.
"Ƙwarai Ranka ya daɗe, Ƙawata ta jima tana gayan yadda ka shahara a fannin aiki amman naƙi zuwa sai yau Allah yayi, wallahi yayan Mijina ne ya sakoni a gaba na samu ada na rabasu da Kisisina, To yanzu kuma kwatsam suka Bullo da Maganar haɗin gida da ɗan shi da yarinyata Kuma wallahi ba dan Allah suka shirya hakan ba sedon kwaɗayi da son cin dukiyar Mijina"
Ɗaga mata hannu yayi tare da ƙara janyo kwanan sha ya Ɗora Hannu.
Akai ya kuma tura mata gabanta.
Zare ido tayi ganin Hoton Mahir Ɗan Hajiya Lubna na yawo akan Ruwan.
Ya kuma janye Ruwan ya maida kwanon sha ɗin yace.
"Waye kika gani a ruwan?"
Da sauri tace.
"Yaron wajan Hajiya Lubnah ne Mahir"
Yayi dariya sannan yace mata.
"Kinga wannan yaron shine mafitarki da ƴarki Sabida haka zan baki maganin da zaki zubawa Mijinki a ruwa in ya sha zai baku damar Fito da zaɓinku Ina so bada ɗaukar Lokaci ba Ki zaɓa mata wannan yaro domin Shi aljanu suka Nunan a matsayin Hasken Ƴarki"
Cike da ɗunbin mamaki Momi tace.
"Jiya ma sai da nayi maganar Mahir da Adaah take cewa ita Inda Abban ta ya bata zaɓi data Fito da wani saurayin ta shine nace mata Ga Mahir Nan Ɗan aminiyata ashe kaga na faɗa akan Gaɓa Ni wallahi da wancan auren ƙaddarar gwara Mahir Ɗari Bisa Ɗari"
Fuskar Hajiya Lubna ta Bayyana da tsantsar farin ciki bata zaci Komai zaizo da sauƙi haka ba.
Maganin daya bawa Momi Ta ɗauka ta bata tasa ajaka, Kuɗi masu kauri Momi ta Kuma dire masa ta fita tabar Lubna aciki domin suyi sallama.
Zuciya ɗaya Momi ta ƙarasa Mota.
Bayan fitar Momi Hajiya Lubnah ta Matsa gaban Malamin tare da cewa.
"Wallahi ban zaci abin zaizo da sauƙi ba, Ita ce ƙawar tawa dana so na kawo maka ita amman da yake tana da wata Irin Uwa Mai Kafiya ita ce ta hanata Bin malamai wanda Nina fahimci kamar mahaifiyar tata ta gano Wasu al'amurane ko zaka duban?"
Ya janyo ƙasa yayi abin da zaiyi sannan yace.
"Kawai macece mai ibada amman bayan nan babu komai, Kuma Ƙawar nan taki zata baki haɗin kai sosai akan haɗin auren ƴaƴanku sai dai banyi zaton wannan lamarin zai kunno ba da takan Mijin nata zamu fara bi, Sabida mutanan suna da ƙarfin Ibada aikin zaiyi wahalar shiga Jikinsu sai dai ita Yarinyar zamu tura mata nata aikin duk da tana da kafiya da taurin kai"
Hajiya lubna tace.
"Nima bata gaya min ba sai da taga abin yafi ƙarfinta kasan a hankali nake so mubi abin sabida bana son wata Ƙofa da zata nuna cewar da wata manufa Mahir zai Auri Ƴarta, Malam Mijinta Ƴarta kaɗai ya haifa kaga Idan ɗana ya auri yarinyar zamu sami dama sosai tinda Ni yanzu mai gidana ba kamar daba abin kawai fafa ce nake Musu dan bana son ƙawayena suga gazawa ta amman wallahi ranar da Maryam tace min Yayan Mijinta ya turo ɗansa Auren Ƴarta ban Rintsa ba Ni ina nan ina faman yadda zanyi na Ɓullo mata da Maganar su kuma suna can sun Min shigar sauri"
Dariya yayi tare da cewa.
"Aiko furucin data wa ƴarta na Auren ɗan naki aikin dana sa a gabane mai zafi ƙawarki ta fiki son duniya fa Lubna Amman zaku sami alheri sosai In Auren nan ya haɗu sabida naga dukiya sosai"
Shirya yadda zata kasance suka yi har ta Miƙe sukai sallama ta ɗauki Jakarta ta fita.
Jiki a sanyaye ta shiga motar Momi tai mata Murmushi.
"Wato Lubna naji daɗin maganganun Malam se naji kamar nayi tsuntsu naga wannan aure ya tabbata"
Lubnah tace "Kayya Maryam baki gani Mahaifin Mahir bai kai mahaifin Adaah ba?"
TsakiMomi tayi.
"Haba Lubna ta yaya zaki faɗi haka bayan Kuma kuna da shi daidai gwargwado ai dama ƙwarya tabi ƙwarya ne wallahi da Adaah ta auri wancan gwara Mahir ɗin sau dubu mayi tuwo na mai na nida ke"
A zuciyar Lubnah Murna take tana fatan haƙonta ya cimma ruwa batun yau take kwaɗayin ɗanta ya Auri Adaah ba sabida su Gaje arziƙin mahaifin Adaah ganinta ta Hanyar auren ne kaɗai zata Iya haɗa kafaɗa da Maryam wadda ta fita jin daɗi ta ko ina.
Momi keta jan Hajiya Lubna da Hira Amman ita Lubna gaba ɗaya bata tare da Nutsuwarta Idanunta ya rufe akan tunanin cikar Burinta tana Jin Kozata rasa Komi nata seta san yadda akai Mahir ya aure Adaah Domin da arziƙi a garin wasu gwara a nasu garin, Don ba tin yau Ni'imar Maryam take tsone mata idanu ba.
Basu ne suka shigo gari ba sai bayan Isha'i a ƙofar Gida suka sauke Momi wadda Hajiya Lubna take ƙara gargaɗinta akan tafa yi amfani da maganin nan kartayi wasa dashi.
Da shigar Momy Gida Room ta wuce tai wanka sannan ta zauna rama sallolin kanta babu tunanin komai ta kwanta a saman gado sai bacci.
Wajan taran dare wayarta dake yashe acan gefe ta soma ƙara ɗauka tai ganin Kiran Abbah Sama sama suka gaisa ya shiga tambayarta Abbakar yazo wajan Adaah rasa yadda zatai tayi seta Amsa masa da yazo kashe wayar yayi ita kuma ta Miƙe da hanzari ta nufi ɗakin Adaah sabida gajiya bata barta taga halin da ƴar tata ta wuni ba.........................
Bayan idar da sallar Isha'i Jidda ta fito daga cikin Gidansu Hannunta ɗauke da Jug wanda ta ciko shi da Kunun aya Shi take son kaiwa sabida yau azumi tayi bata gama abincin dare ba.
Tana Ƙoƙarin saka ƙafa a soron Gidan shima yana Ƙoƙarin Shiga Yana kallonta ya ƙaraso Ita kuma ta dakata tana Juya masa Baya........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*008*
A hankali yayi tattaki zuwa gabanta ya jingina da jikin bango yana kallonta ya harɗe hannunshi a saman ƙirjinshi ita kuma sai kuka take babu ƙaƙƙautawa gaba ɗaya ta cika mishi kunne Rintse ido yake yana faman hura iska daga cikin bakin shi, bai san ta inda zai fara da Rigimarta ba, Kuma bai shirya rarrashin Rikincinta ba domin yana jin makaman yaƙin shi sunyi kaɗan wajan tunkarar Rigimar Jiddah.
Sai da tayi kukan mai isar ta sannan ta shiga mai da Numfashi kamar wadda tai wasan ƴar tsere a hankali ya Kusanci dab da ita Cikin Nutsuwa Muryarshi tayi Mugun sanyi yace.
"Wai mai aka yi maki ban san waya taɓa min ke ba shiyasa na barki kiyi kukan ko zuciyarki zatai sanyi seki faɗa mini damuwar ki?"
Wani kallo ta watsa mai da dukkan Girman idanunta waɗanda sukai jajir kafin tace.
"Ina fatan Allah yasa kunnuwa na ke min gizo daga abin da naji Baba yana faɗa maka, In kuma gaskiya suka ji ina fatan nice ba wata ba"
Cikin dake wa ya dube ta.
"To tinda kinji ai shikenan Kinga bakina ya huta da surutu maganin mai laɓe"
Juya wa yake Ƙoƙarin yayi Cike da Jarumta.
Da sauri tai tsalle ta Cakumo shi ta riƙe masa Riga gam tana Huci kamar ba ita ba.
"Wallahi baka isa ba sai ka faɗamin manufarka Dole ne kayi min ƙarin bayanin abin da Kunnuwa na suka ji"
Da kallo yabi hannunta dake Riƙe da rigar shi cije gefen baki yayi yana girgiza kai kallo ɗaya yayi mata tak tai saurin Sakin Rigar tashi yaja tsaki Mai ƙarfi cikin Fushi yace.
"Tin da kema kin soma zama mara kunya zan saita ki kwanan nan karki ga ina sakar miki ki nemi raina ni wallahi ranki zai yi mugun ɓaci, Maganar da kika ji Baba yana min kuma aure ne zasu mini na zumunci sauran ƙarin bayanin Kuma laɓen da kikai sai ya ƙarasa maki shi"
Da sauri ya fice daga gidan gaba ɗaya ya barta a wajan.
Idanunta ne suka soma juyawa wani irin Mugun jiri ya kwasheta.
Baba dake fitowa daga cikin gida ne yaci karo da Jiddan kwance kamar marar rai cikin tsumar Jiki Baba ya koma gida ya shiga Kiran Innah yadda Baba ke Kiran innah ne ya jawo hankalin su Khadija duk suka Biyo Baba wanda yake Cewa Innah.
"Hafsatu zo ki gani tawo da ruwa Yarinyar mutane mai ya sameta"
Innah har zaninta na kuncewa garin sauri haka take bin bayan Baba itama yadda taga Jidda abin ya bata tsoro haka Ummi ta Ebo ruwa a kofi Innah ta shiga zubawa Jidda a jiki da shafa mata a fuska amman ko gezau da Ummi da khadija ne suka kama Jidda kamar gawa suka shiga gida da ita bisa umarnin Baba a rumfar Innah aka shinfiɗe ta, a tabarma Baba ya ce da Innah ta cigaba da shafa mata ruwa In bata farfaɗo ba su tafi asibiti Kusan Minti Goma innah na shafa wa Jiddah Ruwa a fuska tana hura mata Iska gaba ɗaya duk sun firgita dan Khadija ma kuka take yi sosai, Sabida Jiddah Aminiyarta ce.
Sai can taja wani ƙaƙƙarfan Numfashi kafin ta tashi a firgice ta Rungume Innah se kuka mai ƙarfi ya tawo mata cikin kukan take cewa.
"Innah don Allah karki bari kawu Saadik! ya auri wata ba ni ba, Innah wai aure zakuyi mashi da wata?"
Baba ya kalli su Ummi waɗan da suka yi saurin ta shi suka bar wajan.
Rumfar tayi shuru babu abin da yake ta shi acikin ta sai sautin Kukan Jiddah.
Daɗa rungumeta Innah tayi gaba ɗaya abin duniya ya taru yayi mata yawa ga tausayin Jiddah na ratsa mata zuciyarta.
"Hafsatu sake ta dawo nan Hauwa'u zo kusa dani ki zauna muyi magana"
Baba ya faɗa a hankali shima jikinsa yayi sanyi matiƙa duk yadda yake zaton lamarin ya wuce Zaton sa.
Innah ta saki Jiddah wadda take ta faman share hawayenta Gaba daya wannan kunyar da take wa Iyayen Saadik ta kau idanunta ya rufe bata hango komi sai tina abin da kunnuwanta suka ji.
Baba ya kalleta Yana ƙara jin ƙimarta da girmanta a zuciyarshi duk wannan suman da kukan akan son ɗansu ne take yi lallai wannan yarinya ta cancanci komai na kyautatawa a wajan su.
"Hauwa'u ki nutsu kar shaiɗan ya saka ki ji wani abu acikin zuciyarki, Aure dai nufi ne na Allah shima kanshi sadauki! bai san da wannan aure ba, sabida magana ce ta ALƘAWARI! Wanda muka ɗaura nida ɗan uwana ga Hafsatu shaida ce abin da nake so dake shine ki kwantar da hankalin ki, wannan kukan ki daina auren ki da Sadauki babu fashi yadda yayi mana biyayya ya karɓi auren nan kema ba zamu hana ya aureki ba da zarar kin kammala karatun ki"
Har baba ya kammala maganganun shi Jiddah bata ce komi ba sai hawayen da take sharewa nasiha sosai Baba yayi mata kafin ya kira Khadija yace ta rakata Gidansu.
Bayan fitarsu Jiddah Innah ta kalli Baba ranta a jagule tace.
"Gaskiya Babansu ya kamata a duba yaran nan shi kanshi Sadauki ba auren yake soba dan Allah karku cutar da su"
Ya ɗaga mata hannu tare da cewa.
"Don Allah Hafsatu kibi yadda nake so bana son ƙananun maganganu Sadauki fa Namiji ne yana da damar auren mace har huɗu sabida haka muyi wa lamarin fatan alheri"
Ba don ran Innah yaso ba sai don tsananin Biyayyar Mijin nata yasa taja baki tai shuru Baba ya saka takalman shi yabar gidan Itama fita tayi wajan daka daddawarta bayan ta gama daka wa ta ɗora sanwar tuwon dare.
Sai dai ƙasan ranta damuwa ce fal.
Nana tana zaune a tabarma tana tankaɗe, Innah ta dube ta.
"Nana ɗauko min wayata ki kiramin Babar su Hassan"
Da yake bata kiran sunan Aunty Aminah Babbar Ƴarta sai dai tace mata Babarsu Hassan, ko wannan yarinyar.
Nana ta ɗauko wayar ta kirata mata Aunty Aminar ta miƙa mata.
Wayar tana Ringing! Innah ta kwaɗawa Ummi kira wadda take ɗaki tace mata taje wajan tukunyar tuwo taga in ruwan ya tafasa tayi ruɗe.
Aunty Amina ta ɗauki wayar tana sallama.
Inna ta amsa a nutse.
"Innarmu barka da yammaci yanzun nan fa maganarki muke da Saadik bai jima da shigowa ba"
Inna tai murmushi tana cewa.
"Au dama gidan ki ya tawo to ki faɗa masa ga Jidda can tana suma"
Aunty Amina ta hau salati tana cewa.
"Subhanallahi Innah Jiddan Saadik ɗin to garin yaya haka ta faru?"
Cikin damuwa Innah take faɗawa Aunty Amina abin da yake faruwa
Shuru Aunty Amina tayi tana sauraron Mahaifiyar tasu har ta gama maganganun nata, dama kuma hirar da suke da Saadik kenan daya zo mata da maganar don duk basu sani ba.
Nisawa Aunty Aminah tayi tare da cewa.
"Innah karki tashi hankalin ki Addu'ar dai da ake ita za a cigaba Yanzun nan Kawu Saadik yake faɗa min ashe aura masa Rabi'atu za ai to mudai bamu da ja don aure nufin Allah ne kuma muna fatan Allah yasa albarka a lamarin, ita kuma jidda haƙuri zatai tinda dai aure halal ne ba haramun ba"
Innah ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.
"Hakane yarinyar ta bani tausayi ne shiyasa naji duk hankalina ya tashi da lamarin to bari na barku ku tattauna ɗin amman kice mai ya tawo gida da wuri dan ban ganewa Hauwa'u ba"
Dariya Aunty Aminah tayi tana cewa.
"Wato abin cikin ƙwan yafi ƙwan daɗi innah kada fa Rabi'ah tazo ai mana ƴan ubanci"
Itama innar dariya tayi tana katse wayar.
Saadik ya shiga murza goshin sa cikin damuwa yace wa Aunty Aminah.
"Kinga sakarcin ko don Allah menene abin suma daga maganar aure nifa bana son damuwa Allah in batai wasa ba sai na fasa auren nata ma gaba ɗaya duk wannan damuwar don wa nakeyi in ba domin taba, ba zata tayani kwantar da hankalina ba sai ɗagamin"
Aunty Amina dariya ta saki tana kiran Hussaina ƴarta.
"Hussaina kawo wa kawu saadik ruwa mai sanyi dan naga sai gumi yake"
"Haba Yaya dole nai zufa nama rasa inda zan saka kaina ne"
Hussaina ta kawo masa ruwan a plate ɗin roba ya ɗauki guda ya shanye Ganin ya sami Nutsuwa Aunty Amina ta fara masa magana.
"Kabi komai cikin nutsuwa mu dama mata an sammu da kishi sai dai kowacce kalar nata daban Dan Allah kada kaiwa Jiddah magana marar daɗi kayi mata uziri ka rarrasheta, sannan batun lefen da kake min shima ba ka da matsala Abban su yana kawo min kayayyaki daga kasuwa ina siyarwa ina ɗora nawa, sabida haka zan daukar maka duk abin da kake so in yaso a hankali ni sai mu ƙarƙare"
Zuba mata ido yayi harta ƙare maganar.
"Yaya niko wani irin rashin imani zai saka na amshe kayanki na saidawa nakai lefe"
Yayi ɗan shuru sannan ya cigaba.
"Yanzu dai ki bani account number ɗinki na saka abin da ya samu zuwa jibi in sha Allah zan ƙara sai ku sissiyo ko keda Yaya Hajjo ne"
Ta kalle shi.
"In banda abin ka ba daɗin nakan kenan ba, karka takura kanka akwai kuɗi a wajena kasan Bikin Hussaina yana ta ƙaratowa to na ɗau dashin dazan ƙarasa siyayyar kayan kitchen in baka son na ɗauki kayan Abban nasu saina baka kuɗin daga baya ko yaushe ka samu sai ka biyani"
Murmushi yayi.
"Kai Yaya nifa bashin ne bana so"
Ta kalle shi.
"Auta na baka kyauta tunda baka son bashi"
Da sauri yace.
"Wallahi ba zan amshi kuɗin kuba kowa yana fama da kanshi da ɗanshi akan me"
"Saadik kenan ni na rasa irin zuciyarka Ubangiji ya sa kafi haka duk hidimar da kake mana kace kai taka tazo ba zamu taimaka maka ba, Bani manta Bikin jawahir kaifa kai mana kayan kitchen sannan Abbansu kasuwar bata garawa don Allah ka amshi kuɗin nan Saadik nasan rayuwar ana fama amman Allah zai warware"
Cikin son kauda maganar yace.
"Ki bani account ɗin sauri nake yi in yaso sai ki ma Yaya Hajjo waya ku tattauna nidai bana son ƙananun atamfofi gwara ko ba yawa a sayi masu aminci"
Duk yadda taso su sasanta ya amshi bashin kayan kona kuɗin yaƙi Sabida acewarsa kowa yana fama da kanshi ba zaka ɗora mai wahala ba.
Ya amshi Account Number ɗin nata ya saka mata Kuɗin da suka rage mai yayi mata sallama ya tafi gida duk da taso ya tsaya yaci abinci tinda an kusa gamawa amman fafur yaƙi tsayawa.
A bakin titi ya sauka ya shiga shagon mai fura da nono ya siyawa innah sanin tana son surki sannan ya saiwa Zarah alewa ya nufi lungun su.
Bai iya ɗakin shi dake soro ba sai da ya ƙarasa cikin gida ya sami su innah suna ƙoƙarin ɗaura alwalar sallar magariba da ake ƙoƙarin kira.
Ya miƙawa zarah alewarta wadda tazo ta ɗane shi yana kallon innah wadda ta zabga mai harara.
"Wai innah nikam mai nayi daga zuwana ga furarki na sayo"
Sai da ta ɗaura alwalarta sannan tace.
"Ka kyauta ka bar ƴar mutane cikin wani hali kai tafiyarka"
Ya wani zaro ido waje.
"Inna itan ce tace nai mata wani abun nifa kawai biyoni tayi da kuka shiyasa na bar mata wurin"
"Oho ca nake kasan sanda ta faɗin, yanzu kayi sallah sai ka leƙa gidan nasu kaji yadda take nima danai sallar zan shiga"
Ya miƙa mata ledar furar tare da amsa mata da cewa.
"To"
Yana juyawa ya nufi ɗakin shi da fitilar ƙaramar wayarshi yayi amfani wajan haska banɗaki yayi uzirin gabanshi tare da ɗaura alwala, ya fita masallaci.
Bayan ya idar da sallar magariba, ya dawo ɗaki yayi wanka Nura saiti ya kira a waya yana tambayar shi akan koya dawo Nurah yace mishi yana bakin titi yanzu zai shigo lungun da sauri yace masa inya shigo ɗin ya biyo don Allah zai rakashi Gidansu Jiddah.
Zama yayi yana jiran Nuran bayan ya katse wayar jim kaɗan nurah ya shigo tashi kawai yayi suka fita.
A ƙofar gidan su Jiddah suka dakata yana tunanin ta yadda zai sami yaron da zai musu iso zuwa gidan dan shi yana jin nauyin kiran Umma a waya yace yazo.
Ana haka Fa'izu yayanta ya ƙaraso ƙofar gidan yana ƙoƙarin kashe babur ɗinsa ya ga su Saadik waɗanda suka ƙarasa gaban shi suna miƙa mai hannu.
Cikin mutuntawa suka gaisa yace.
"Kuma kunzo basa gidan kenan? nima sai da na zo bakin layin ummah ke faɗa min, suna asibiti Jikin Jidda babu daɗi"
Da sauri Saadik ya kalli fa'izun gabanshi ya faɗi tofa abin yayi zafi kenan harya kai da zuwa asibiti.
Cikin sanyi yace.
"Okay wane asibitin kenan bari mu ƙarasa"
Fa'izu yace.
"Nan asibitin Charity na bakin titi ko wani acikin ku zai hau bayan babur ɗin muje tare?"
Saadik ya kalli nurah wanda shima ya kalli saadik ɗin kafin Nuran yace.
"A,a bari mu tafi bibbiyun tafi daɗi"
Fa'izu yaja babur ɗin nashi ya tafi su kuma su nufi bakin titi.
Gaba ɗaya Saadik ji yayi garin yayi masa zafi fargaba ta cika zuciyarsa sai dai da yake akwai shi da dauriya yasa fargaban bata fito fili ba.
Duk Hirar da Saiti ke yi masa kawai jinsa yake a haka suka ƙarasa titi suka sami napep tafiyar kaɗan ce ta kaisu asibitin wanda yake ɗan ƙarami ne na kuɗi.
Suka sauka tare da bawa mai ɗan sahun kuɗin shi, suka shiga cikin asibitin.
Suna shiga shima fa'izu na ƙarasowa sabida haka a tare suka ƙarasa cikin ƙaramin ɗakin da aka kwantar da jiddan bakin su dauke da sallama.
SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
*007*
Kwantaccen murmushi ya saki yana shafa saman kanshi da hannun shi guda ɗaya, haka nan ya ƙarasa gefen data mayar da kanta ya zuba mata ido tamkar ranar ya fara ganinta, Har Lokacin murmushin kuma bai gushe daga saman fuskar shiba.
Turo baki tayi gaba tana ƙoƙarin sake juya masa baya yayi saurin jan gefen Hijabin ta ya wani marairaice kamar wanda yake roƙar ta gafara