Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 10
tare da ficewa daga soron. Beyi gigin bin bayanta ba dan yasan rigima ce zata kaure musu ƙarshe inta saka mai rigima ya karɓi abincin ba iya ci zai yiba inya bayar kuma taji haushi. Sai kawai ya shiga ɗaki cikin hukuncin Allah yana shiga ana kawo Nepa ya jona cajin ƙaramar wayarsa. Yana ƙoƙarin cire shirt ɗin jikinsa ƙaramar wayar tasa ta shiga Ƙara alamun kira yana shigowa Bayan ya ɗaga Muryar Abokin shi Nura saiti ta cika masa cikin kunnen shi. "Wai dan Allah dagiya ina ka shiga ne?" Saadik ya ɗan ja tsaki kaɗan. "Yanzu dai meke tafe dakai ko tambayata ka kirani kayi? kaje shagona baka ganni bane koka zo gida bani nan?" Saiti yayi dariya tare da cewa. "To sarkin fushi nai maka magana ne naji shuru, ko baka kunna Data bane yau?" Takaicin ɗazu ne ya faɗo masa ya fesar da huci mai zafi. "Bari kawai Nura wayar ma bata wurina Allah yasa sim ɗin yana wannan wayar" Da sauri Nurah yace. "Garin yaya matsala ta samu?" Cikin son kauda zancen sabida shi gwanin zurfin ciki ne yace. "Ya ake ciki ne kana shagone koka shigo?" Nura yace. "Yau na sami cinkoso ne a wajan IBB Road kasan hanyar tamu sai a hankali, Amman gani nan dama Najika shuru ne nace bari na taɓaka kako san yau Za'a Buga wani zazzafan wasa?" Duk yanda Saadik ke son kallon Boll sam yau ya mance zasu je kallo kwata kwata sabida haka tsaki yaja dan baida karsashin fitar ma gaba ɗaya Nafila zai yi kawai ya kwanta yasan Baba zai fita waje shan iska bayan ya gama jin Labaran sha ɗayan dare ya rufo gida shiyasa zeyi kwanciyar sa. "Nura Kuje kawai kaida su Babu danni gaskiya yau ɗinnan ba zan iya zuwa gidan kallo ba" Daga haka ya kashe wayarsa gaba ɗaya ya mayar chaging ya koma ya kwanta ya zurfafa acikin tunanin wannan lamari mai girma daya faɗo masa ko a kanshi bai taɓa tunanin Baba zai masa auren dole ba, dan shi kam wannan aure na dole ne yana zaman shi lafiya Baba ya bashi Umarnin zuwa inda za a ɓata mishi rai. Maganganun Baba na jiya da daddare ne suka soma dawo masa cikin kansa. "Sadauki!Waye mahaifinka?" A lokacin sun kammala cin abincin dare ne duk suna zaune a Rumfar Baba shida Baban da Innah wadda take cin Gyaɗa marau marau. Ya Nutsu sosai tare da cewa. "Baba duk duniya ban san wani a wannan matsayin na uba ba face kai" Baba yaji daɗin kalamin shi duba da yanda yayi Murmushi a lokacin haɗi da samai albarka kafin ya fara dirar mashi da maganar data haifa masa ɗaukewar Numfashin wucin gadi. "Sadauki jiya mahaifin Wannan yarinya Hauwa'u mai haƙuri da kawaici ya kirani akan maganar auren ku sabida karatunta daya kusan zuwa ƙarshe, Bayan nai masa na'amm da maganar sai na ɗauki wayata na Kira ɗan uwana wanda duk duniya bani da kamarshi Amadu uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya nina saki Nono ya kama na shaida masa batun Auren ka" Baba yaja fasali. Saadik yaji wani irin farin ciki a zuciyarshi. Innah ma sai ta hau murmushi sabida Jiddah ta cancanta ta zama surukarta duba da yanda yarinyar ke son ɗan nata tilo tal namiji aduniya kuma auta acikin ƴaƴanta waɗanda dukka mata ne Allah ya bata shi kaɗai ne namiji acikin su kuma shine auta. Maganar baba wadda ta katse Murnar Innah da Saadik ita ce ta cika Kunnuwan su. "Sai dai Amadu ya katsen hanzari, ya mini kyauta kuma na amsa tinda bahaushe yace yaba kyauta tukwici dik da kyautar dama bata yanzu bace amman Lamarin daya zo ya cuɗe a tsakanina da shi yasa na fidda rai akan kyautar ta shi Sadauki Amadu yace kaje ka Nemi auren ƴarsa RABI'AH duk da maganar ba sabuwa bace a wajena nida Hafsatu mahaifiyarka Tin ranar da Aka haifeka da Amadu ya ɗaga ka yace In har Matar sa ta haifi ƴa mace yayi ALƘAWARIN ba tada Miji sai kai to yanayin yadda Zumuncin mu ya lalace da shine yasa Ban ɗauka zai cika wannan Alƙawarin ba sai kuma gashi ya cika don yace sadaki kaɗai zaka bada Rabi'atu dai ƙanwarka ce da ubanta dani cikinmu guda dan haka In har ni na haifeka kamin alfarma kaje ku sasanta In yaso ita Hauwa'u sai ka aure ta inta kammala karatunta ba zan hanaka auren wadda kake so ba Amman Nima ka auri wadda Mukai Alƙawari Nida ɗan uwana ko Allah yasa silar auren ku zumuncin mu ya daidaita" A lokacin jikin Saadik babu abin da yake sai rawa hatta bakin shi Gumi ya jiƙa masa rigar shi, Dama ga zafin ɗaki dan lokacin babu wutar Lantarki. Inna zatai magana Baba ya ɗaga mata hannu alamun baya buƙatar cewarta, Sai taja baki tayi shuru. Numfashi ya dinga ja yana ambaton sunan Allah kafin ya samu Nutsuwar Furtawa Baba Kalmar. "Amman Baba hakan ba zai jawo mana ƙasƙanci ba, Mutumin da baya neman ka Yana matsayin ƙaninka amman ya nuna yanzu Shi mai Kuɗi ne ya janye zumuncin dake tsakanin ku, Baba ka rabu da shi Ka Nema min Auren Hawwa'u ita ce wadda take matiƙar sona domin Allah Nima Kuma nake sonta Amman ita waccan da ban santa ba bata sanni ba Ko sunanta ban sani ba tayaya zan aureta Baba?" Baba yayi murmushi irin nasu na manya kana yace. "Ka bar batun Amadu Yaro ne ɗan halak Shu'umar macce kawai Ya haɗu da ita Ina son ka auri Rabi'ah ne Ko ta sanadin auren ku Allah zai sa Zumuncin mu yayi ƙarfi nida ɗan uwana, Fanni zamantakewa kuwa nasan Autana Ba ragon namiji bane in mace Huɗu ya aura zai iya ɗaukar Nauyi ci da shanta Hauwa'u Kuma In Allah ya yarda bata da Miji Sai Kai Kodan karamcin Mahaifanta garemu" Yayi Biyayyar Amsawa Baba tare da amsar Auren ne badan komai ba sai dan tsan [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *005* Da sassarfa yake tafiya cikin gidan nasu harya ƙarasa cikin rumfar da mahaifin nashi tare da ɗan uwan shi, suke zaune da sallama a bakin shi Ya Nemi Gurin zama daga Nesa dasu yaɗan Sunkuyar da kanshi a ƙasa. "Sadauki! dama Babanka Amadu ne yazo min da magana shi ne nace a kira ka Amadu ga ɗan naka nan sai kuyi maganar" Har Lokacin bai ɗago kanshi ba Abbah ya gyara Murya tare da cewa. "Kwanakin baya na taɓa zuwa da maganar ka fara zuwa Inda nake a kasuwa amman ka nuna baka ra'ayi shine nace yanzu meze hana kazo wajan nawa Kodan Iyalin da zaka fara riƙewa kasan yadda rayuwar ta koma, Batun auren ka da ƴar uwarka Ina son daga na dawo ai maganar auren ku sadaki kaɗai nake buƙata zan baka Gidan zama da Mota sannan kuma ga kasuwa duka Allah ubangiji yasa wa auren ku albarka Amin" Baba ne kaɗai ya taya Abbah amsawa da Amin amman gogan naku ko gezau bai yi ba sai da Baba ya kuma cewa. "Wai Sadauki! ba kaji maganar Kawun naka bane?" A hankali ya ɗago fuskar shi wadda tai jajir abin ka da fari yawanci in yana cikin damuwa Fuskarshi ja take Musamman saman Hancin shi. Murya a shaƙe kamar an masa dole yace. "Abba nagode da karamcin auren da kabani ma kaɗai ya wadatar sauran duk na yafe, da farko ina da sana'ata duk da a wajan wasu kamar ta ƙasƙanci ce amman ni a wajena sana'ata tana da Muhimmanci a gareni domin da ita na dogara har na tsaya da ƙafafuna, Gwangwan nake kamar yanda ka sani ina Auna ƙarafa ina siya nima na siyar na sami abinci, Sannan Batun Auren gaggawa dan Allah Abbah ayi min uziri kaɗan zan ƙarasa shirina sabida Kutsen da aka min son samu na zauna agidan kaina amman hakan baze samu ba dan haka zan kama haya Kuma zan mata lefe daidai ƙarfina son samu ta saka kayan Da Mijinta ya ɗinka mata sabida haka ayi min uziri har na kammala komai sena yi magana" Gaba ɗaya Abbah shagala yayi da kallon Saadik a ranshi kuma yana jin wannan shine Mijin da ya cancata Ƴarsa ta aura sabida ta Ko'ina jarumi ne, Baba kuwa baiji mamakin furucin ɗan nasa ba Yasan shi sarai shiyasa yaƙi amsawa Abbah tayin daya masa Sabida yasan da wiya Saadik ya amsa aikuwa gashi nan ba'a je ko ina ba yaƙi. "Shikenan Abubakar! Allah yasa albarka a lamarin Na gamsu da bayananka, Kuma Ina fatan Zaka riƙe ƴar uwarka da amana" Bai Motsa ba, bai kuma tankawa ƙanin mahaifin na shiba. "Zaka iya tafiya" Cewar Baba. Da sauri Abba yace. "A,a dan Allah Abubakar, ka ƙara komawa wajanta Ku sake tattaunawa sabida Ku fahimci Juna don zaman lafiyar auren ku shine kwanciyar hankalin mu" Tausayi Abba ya bawa Saadik da ɗan sassauci yace. "In sha Allah" Yana danne takaicin ta na jiya dan shi ba soko bane baya jin zai iya kai ƙarar mace bada ban haka ba da yace ya mata faɗa ta gyara kalamanta dan gudun kumburin baki. Kafin Saadik ya kai da ficewa Abbah ya dakatar dashi tare da ɗauko waya ya shiga Kiran Adaah Ƴar Mulkin anci sa'a tai tashin wuri tana bakin gado taga Kiran Abban ta ɗauka Magana ɗaya yayi mata ya kashe wayar Umarni ya bata kamar haka: "Ki shirya Anjima kaɗan Ɗan uwanki zai ƙara zuwa Ku tattauna Saura naji Kin masa Shirme" Tana shirin magana ya kashe wayar ƙafa ta fara dirawa tana ita Babu inda zata kuma fita Seta tafi wajan Momi sai dai koda taje Room ɗin Momi bata sameta ba. Juyawa tayi cikin Rooom Ɗinta tana gunguni. Tashi Abba yayi bayan ya direwa Baba damin Kuɗi Amman fafur Baba yaƙi amsa Da damuwa Abba ya maida kuɗin gaba ɗaya Yanayi Baba baiwa Abba daɗi ba wato shi horo wani bin base an maka faɗa ko an maka magana ba. In har kana da hankali in ka ɓatawa Mutum rai zaka gane a mu'amalance kuma cikin sauƙi. Sanda Saadik ya fito daga Rumfar Baba ɗakin sa yayi Niyyar wuce wa sabida yana son yau yakai wasu ƙarafa daya siya can ƙofar ruwa shine yasa ma har yayi tashin wuri. Innah ce ta tare shi da Kofi fal koko aciki. "Dan Allah karka fita baka sa komai cikin kaba zoka sha kokon nan yaji sugar na sanka gwanin shan zaƙi" Murmushin daya kasa yi a rumfar Baba ya sakar mata yana ƙarasowa gabanta. "Innah akwai abin kari a ɗakina fa Naga ni baki sako min tuwo ba Ƙosai kika zubon da Kunu" Ya faɗa cikin tausayin mahaifiyar shi wato shi ta bambanta a wajan karin kumallon ta soya mai Ƙosai tai masa Kunu gida Kuma tuwo ɗumame da koko. Bai bata zarafin magana ba ya karɓi Kofin yana ɗan Kurɓar Kokon adaidai nan Abba da Baba suka fito Fuskokin su ƙunshe da Murmushi wanda zai nuna maka girman soyayyar Junansu a fili. Har gaban innah Abbah yazo tare da aje mata kuɗi yana cewa. "Gashi innah babu yawa ban san laifin dana wa yaya ba samsam yaƙi amsar kuɗina, wallahi ason samuna Yaya ya daina fita saida naman nan" Baba yayi dariya kana yace. "Wato so kake zuciyata ta mutu kenan ai in kaga na dena saida naman nan Ciwo ne ko Mutuwa amman ba zan zauna na kashe zuciyata ba" Sai Lokacin Saadik yayi wani basaraken Murmushi tare da cewa. "Haba Baba in sha Allahu cikin farin ciki da lafiya zaka daina wannan saida naman nan kusa" Yana faɗa yaja baki yayi shuru shidai Abbah Murmushi yake wani farin ciki yana ƙara baibaye masa zuciyar sa. Rabon daya sami farin ciki irin wannan harya manta dama haka kasancewa Cikin ƴan uwa yake yasha auna zuwa sai Hajiya maryam ta tare shi da zantuka a haka yake shagala sai yau Allah ya ƙaddara zai shigo wanda rabon daya zo ɗin ya jima ada kuwa Kullum ne in zai fita sai yazo wajan ɗan uwan nashi. Sallama sukai, Da Innah Da shi da Baba suka fita sai dai Ko a ƙofar Gidan ma Baba yaƙi shiga motar Abbah babu yanda Abba bai da shi akan yazo su aje shiba Amman yaƙi Jikin Abbah ne Yayi sanyi tabbas yasan ɗan uwan nashi ya janye masa ne sosai tinda har yaƙi amsar Dukkan ta yin daya mashi. Bayan motar su Alhaji Amadu ta tafi Baba ya fita titi ya tari abin hawa zuwa kasuwa yana jin hakan yafi masa Mutunci duk da shi ba zai ce ga wani abu da Amadu yayi mishi ba, Amman Gorin da matarshi tazo har Gida tayi musu shida Innah yasa suka tattare lamarin Amadu suka aje Kuma Allah ne ma ya rufawa Matar Amadun asiri data zo harta tafi Saadik baya gida domin ba zai ɗauki ƙasƙanta Iyayen shi ba Shiyasa daga Innah har Baba basu faɗawa kowa a ƴaƴan suba hatta shi Amadun bai sani ba kawai dai sun kama kansu ne. Daga cikin gida Saadik ya tokare a gefen katanga. Ya cigaba da sauraron innah wadda take miƙo masa kuɗin da Abbah ya aje mata. "Auta ungo waɗannan kuɗaɗen kai da kake da hidima a gabanka Ko wani abun ka rage danni babu abin da zanyi dasu hidimar gabanka tafi tawa" "Haba innah dan rashin imani a baki kuɗi na saka hannu na karɓa, In da dai ina da Dama da tin yana nan zance kada ki amsa masa kuɗin sa to kin riga da kin karɓa lokaci ya ƙure" Innah ta zuba masa ido kafin ta janye kuɗin ta aje a gefenta kana ta dube shi a nutse. "Zauna muyi magana Sadauki" Da yake ita da Baba ba kasafai suke faɗin Saadik ɗin ba sunfi kiran shi da Sadauki! Ya nemi guri a bakin ƙofar Kitchen ya zauna. "Mai yasa kake da sa abu aranka ya kamata zuwa wannan Lokacin , ka rabu da ƙullin ƙanin mahaifin ka a zuciyarka, Wallahi Ba laifin shi bane a rayuwa babu abin da Amadu baiwa mahaifinka ba macece Allah ya bashi marar mutunci a tarihi ban taɓa ganin mace marar kirkin Maryam ba Amman shi ka duba kodaga mu'amalar shi damu kasan akwai ƙauna mai girma" Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace. "Nifa innah ba ƙullin shi nayi ba, meze sa na ƙulle shi a raina bayan alhakin kulawa daku ba a kanshi ya rataya ba, kawai Innah bana son ka cika zaƙewa ne a lamarin mai kuɗi, Banyi niyyar bayyana wa kowa ba" Sai yaja bakin shi yayi shuru ya kasa ƙarasa maganar da yake son faɗi. Ta zuba masa ido tana son jin sauran ƙarin bayanin. Ya fesar da zazzafan Huci yana shirin yin magana. Suka jiyo muryar Faridah tana kiran Sajjad Sai dai tuni shi Sajjad ɗin ya biyo ƙanwar sa Sajidah sun shigo tsakar gidan Innah. Har rige rigen hayewa cinyar innah suke suna dariya Faridah ma dariyar take bayan tai sallama tana cewa. "Karfa ku ɓallamin cinyar uwata wallahi sena zane yaro" Innah tana dariya tace. "Baki isa kin taɓa yaran nan a gabana ba, keda Hajjo ƴaƴan ku basu da sakewa sam sam bini bini kun daki yaro ku haka nai rainon ku" Dariya faridah ta saki tana kawowa Saadik dukan wasa kasancewar shine sakon ta. "Dagiya ba magana ne ka wani cinno baki ko shagwaɓar autan ce ta tashi yau?" Harara ya ɓalla mata da sauri tai masa gwalo ta shige ɗakin Innah ita kuwa Innah me zatai In ba dariya ba Dama indai Faridah ta zo se sunyi faɗa da Saadik, Kuma dama sun saba tin kan tai aure ita tsokana shi fushi datai masa zai kamata ya zane wani bin sai Baba ya kawo musu ɗauki to ko datai auren bata daina tsokanar shiba shiyasa basa wani shiri yafi shiri da Marigayya Mai sunan Innah Aunty uwani ita ce Mahaifiyar su Ummi wadda ta rasu a garin haihuwar zara shine Yaran nata suke hannun Innah da Baba, Kasancewar Aunty Uwani akwai haƙuri ita ce mai ɗaukar Rigimar Saadik, akaf ƴan uwan nashi. Farida ce keta ƙwalowa Innah Kira daga cikin ɗaki tana cewa. "Innah wannan sabon Hijabin naki ne ina so wannan Sabuwar Doguwar Rigar ma ina so" Tsaki yaja yana cewa. "Kedai Kinji Kunya wallahi nan gaba kaɗan zan soma rufe ɗakin Innah duk sanda Kika zo sekin Rabata da kayanta" Dariya ta saki tana cewa. "Allah ma dai yasa kafin kazo duniya nazo" Wannan kalma tana ƙona masa rai tsaki yaja wanda Innah ta fara magana. "Kinga fito ki tsincen shinkafa tinda Allah ya kawo ki, Dama su Khadija sai ƙarfe Biyu suke shigowa gida sabida makarantar tasu akwai tazara" Daga ciki farida tace "Innah yau base kinyi girki ba, Abban Sajjad zai koma Gida Anjima kafin nan Mai aikina ta gama abinci zata zubo mana na faɗa masa ma yace zai kawo" Innah salati tahau yi tana tafa hannu. "Faridah wannan wani irin sakarci ne Ban hanaki dafo mana abinci in zaki zo ba to ni wannan abin kunyar bada ni ba" "Innah wallahi shine yake sawa Ko gidansu In zani sai yasa an wa Mama Girki kuma yace dake da mama duk iyayensa ne yau ma Na shirya a makare ne shi kuma yana sauri zai ajeni da senai girkin zan tawo se kawai na barwa mai aiki nace tayi" Innah tace. "To madalla zan tuntuɓi shi Mijin naki na kuma haneshi, dammu ma Allah bai hanamu abinci ba" Dariya faridah tayi sosai kafin ta furta. "Innah shima ba raina mana yayi ba kawai kyautatawa ce, kuma Innah idan yazo ɗin ki tambayeshi wallahi Innah babu yadda za'ai na ɗauki abincin Mijina ko wani abun daya kawo Gida nayi kyauta dashi batare daya sani ba Komai zanyi tare da sanin sane da amincewar shi. Murmushi Innah tayi. "Na sani faridah Ina dai ƙara gargaɗin ki karki yarda Ki bada Kome ye na mijinki batare da sanin shiba, Kuskuren da yawanci mata suke kenan Kyautar kayan abinci komai ma suna iya badawa dan sunga na mijin sune wannan Kuskurene babba ba'a hana ka bada ba Amman ya zama ka bayar da Amintar sa da yardar sa wannan In kayi hakan babu laifi" Saadik ne ya katse maganar tata yana cewa bari ya tashi fita zaiyi Ƙofar Ruwa yabar su Umar a shago in an gama Girki a miƙa Musu. "Dagiya zona aike ka Ƙarshen waya ka siyo min Gurji" Seda ya taka bakin Ƙofar ya hangota kwance a gadon Innah sannan yace. "Inda kina da Biyayya da Har mai Gurjin zan kawo Miki amman Ji bakin ki wai Dagiya mtss" Farida dariya innah dariya Shidai kama Hanya yayi ya fice daga tsakar Gidan waya kaɗai ya ɗauka ya rufe ɗakin shi ya fita Titi  seda ya biya ta ƙaton shagon shi wanda ya cika da ƙarafe buhunna robobi kala kala gasu nan Umar yana ta auna ƙarfe a kilo Usman yana bawa wasu Yara canji. Sallamar shi yasa suka Jiyo suna masa barka da shigowa ya sami saman Banci ya zauna. "Kawu Saadik! dama tin ɗazu muke Jiranka masu ƙarfan Motar nan sun zo wai ba zasu siyar Dubu Goma ba" Ya ɗan kalli Umar yace. "Sai nawa suka ce?" Umar yace "Sun ce sai dubu sha uku" Ya ɗan murza kanshi tare da cewa. "Ba matsala, Usman haɗa min ƙarafan can, Ka kira min Babur a titi" Ya juya yana kallon waje Inda shi kuma Usman ɗin ya fita da sauri. "Ina salman ne?" Ya furta. "Kawu Saadik wallahi sai ka zane Shi sannan zai Nutsu ɗazun nan naganshi da Tawagar ƴan Goburawa wai sun tafi Boll ko makaranta yau bai je ba" Ya ɗan kalli Umar kafin yace. "Kana kallon shi ba zaka Hukunta shi ba ni kake jira na zane shi kome?" Umar ya sada kai ƙasa bai kuma magana ba Usman ya zo ya kama kayan suka soma fitarwa wajan Baburin ɗan sahun da Usman ya kira seda suka cikata tab sannan Saadik ya hau gefen Drivern suka tafi. Ya jima a kasuwar kafin ya kammala komai Lokacin Ƙarfe Huɗun Yamma Sallar la'asar yayi sannan ya tari abin hawa. "Gadon ƙaya" Ya faɗa a dake sabida son ya cika alƙawarin daya ɗauka. Domin yana jin Yadda ya gajin nan baze iya Komawa Gida sannan ya kuma fita wani Gurin ba da kwatancen da yakewa mai ɗan sahun suka ƙarasa Har bakin Gidan kawun nashi ya fito ya bawa mai Ɗan sahun kuɗin shi ya taka har bakin gate ɗin gidan Tarin takaicin Jiya ya shiga Faɗo masa aranshi kawai dan karya ma Kawun shi gardama ne yasa zai ƙara zuwa wajanta Amman da baya  jin zai ƙara komawa inda take. Mai gadi ya leƙo ta ƙaramar Ƙofa yana tambayar waye? Ya gyara tsaiwa kafin yace. "Baƙo ne" Mai gadin yace. "Alhaji baya nan Hajiya babba bata nan sai Hajiya ƙarama" Tsaki Saadik yaja kafin ya koma da baya yana ƙoƙarin tafiya mai gadin yace. "Bismillah ai na gane ka kaine wanda ka zo jiya" Bai tanka masa ba, sabida shi wani bin baya son yawan magana yana tafiya iska tana kaɗa shi sabida yalwatuwar ganye da bishiyun dake cikin gidan. Zama yayi a ɗaya daga cikin ƙayatattun Kujerun dake zagaye da Farfajiyar gidan da sauri mai gadin ya wuce shi ya ƙarasa Bakin Ƙofar falo ya shiga Kiran Maimuna, Wadda takewa Adaah Hidima maimuna ta fito daga Kitchen tana amsa Kiran mai gadin wanda ya sanar da ita ga baƙo nan yazo da alama wanda jiya yazo wajan Hajiya ƙarama ne ya dawo. Maimuna ta koma ciki Ƴar Mulkin tana zaune a falo na biyu ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya tana waya da Habib Ganin Maimuna bai sa ta katse wayar ba maimuna ta tsugunna har sai da ta kammala wayar sannan Maimuna cikin ladabi tace. "Ranki ya daɗe kinyi baƙo yana waje" Taɓe baki tayi sam tama mance da sharaɗin Abbah na wayar daya mata akan zuwan wancan Ƙolon bata Motsa daga inda take zaunan ba kamar an mata dole tace. "Kice masa ya shigo ciki in ya shigo kuzo tare ki tawo Min da Ruwa a cup da Moper" Daga haka ta koma ta kwantar da kanta ajikin kujerar da take kai. Maimuna cikin ladabi ta ƙarasa wajan Saadik, yadda yake a zaune seta daburce sabida masifar kwarjinin daya mata da ƙyar ta iya haɗa kalmar ya ƙaraso Ciki ta miƙe. Kamar baze tashi ba se kuma ya miƙe ɗin shima suka ƙarasa Ciki seda Maimuna ta ɗauko mata ruwan da Moper ɗin sannan suka ƙarasa shiga Ciki yana biye da maimuna. Wadda ta aje saƙon ta juya da sauri shiko daga bakin Ƙofa ya tsaya cak ya tokare shibe shiga ba shibe koma ba........ 09022260850. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *006* Kallo ɗaya yayi mata yayi saurin kawar da kanshi, Gaba ɗaya shigar da take jikinta bata kamata ace ɗa namiji ya sameta a cikinta ba, Juya masa Baya tayi ta cigaba da danna wayarta bata jin zata masa magana idan zasu shekara a haka. Shima daga ɓarin shi gefe ɗaya ya zubawa ido sabida Gudun kar Idanunshi su ƙara mugun gani, Sai dai daga cikin zuciyar shi tafasa take kamar zata tsaga masa ƙirji ta fito wannan wace irin Yarinya ce wadda bata da Kunya bata da Tarbiya ko kaɗan sam baiji sha'awar auren ta ya kawota gidan shiba, Inda yana da dama da ya warware maganar auren su saidai Iyayensu sun riga da sun yi Alƙawari babu yanda za'ai yayi silar Rusa wannan Alƙawarin. A fusace ta yunƙura daga kwanciyar ta nufo ƙofa zata fita Jikinta sanye da Doguwar riga mai hannun shimi wadda tai matiƙar kama mata jikin nata surarta mai ɗaukar Hankali ta bayyana kanta babu ɗankwali Siririyar kalaban dake kanta duk ta Miƙe tsaye sabida ita bamai yawan gashin ka bace. Ƙoƙari take ta raɓe shi sai dai hakan ba ze yuwu ba sabida Ya riga ya tokare ƙofar. "Malam zan fita ka wani zo ka cika mana wuri sai kace gidanku" Har ga Allah shi bema san ta ƙaraso ba hankalin shi ya tafi tunanin neman mafitar zamewa auren ta sai jin dirin muryarta yayi a gab dashi cike da rashin kunya. Yana ɗago kanshi da nufin ya kalleta tana mai juyawa ita kuma da sauri wannan ruwan da Maimuna ta kawo mata ta ɗauko babu tunanin komai tayo kanshi da ruwan mai yawa a cup ga ɗan karen sanyi ta juye masa shi tas a jikinsa damma tsayinta bai kai ko kafaɗar shiba da tindaga saman kanshi zata zuba Ruwan. Tsayawa yayi yana kallonta ruwan na ɗiga daga jikin rigar shi Adaah dariya ta sa tana Nuna shi da yatsa. "In banda kai sakarai ne ta yaya zaka yarda da maganar aure na kalleni" Ta faɗa tana juya jikinta sannan ta nuna shi. "Kalleka dan Allah kayi kama da kalata jiba kayan jikinka wani ƙazami dakai wawa Mtsss" Ta faɗa tana Ƙoƙarin Nufo shi. Ƙura mata ido yayi wanda yayi jajir har wani ruwan

Chapter 3 of 10