Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑 POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD TYPING ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯🙏 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.... WANNAN SHINE LITTAFIN NA DAYA 👇👇 Daga wannan rana zakunan nan ba su sake dawowa ba, har tsawon kwana ashirin da biyar. A sannan ne Jafar ya dubi su Gulzum ya ce, "Ya ku abokan tafiya ku yi sani cewa zama anan ba na mu ba ne. Zai fi kyau mu kara gaba ko ma bar wannan wuri mai tsananin hadari, in ba haka ba kuwa a ci gaba da kashe mu daya bayan daya, har mu kare" Koda jin wannan batu sai gaba dayan su hankalinsu ya dugunzuma kuma suka aminta da shawarar. Dan hak Nan take suka yi bankwana da mutancn wannan gari. Mutanen suka yi ta kuka, saboda shakuwa sannan suka yi musu sallama suka tafi. Jafar, Yclisa, Gulzum da Mazalish suka kama hanya suka yi ta tafiya a cikin daji batare da sun san inda za su dosa ba. Suna cikin tafiyar ne Suka yi mugun gamo. Ba wani abu ba ne ya ritsa su face katon zakin nan mafi girma daga cikin shaidanun zakunan nan. Ga shi a wannan lokaci babu mai makami a cikin su Jafar, shi ma kuma Gulzum bai taho da majajjawarsa ba. Nan fa aka fara kallan-kallo tsakanin zakin da su Jafar. Su Jafar suka fara ja da baya a hankali shi kuma zakin ya fara gurnani. Kafin su yi wani yunkuri zakin nan ya yi sufa ya dira akan Mazalish. Nan take ya cinye rabin jikinta, Koda ganin haka sai Gulzum ya yi kukan kura gami đa daka tsalle ya ribaci zakin suka kama kokawa. Su fada nan, su tashi can. Zakin yai ta kokarin ya hallaka Gulzurm, shi kuma Gulzum ya raba hannayensa tsakanin bakin zakin yana ƙoƙarin ya bara bakin zakin gida biyu. Da yake zakin yafi Gulzum girma nesa ba kusa ba, sái nauyinsa ya rinka rinjiyar Gulzum ya kasa samun damar bara bakin nasa. Su dai su Jafar sai suka koma gefe guda jikinsu na karkarwa suna kallon ikon Allah cikin tsananin tsoro. Sai da aka shafe sa'a uku ana dauki ba dadi tsakanin zakin nan da Gulzumn ya zamana gaba dayan jikin Gulzum ya farfashe bisa yakushin da zakin ke yi masa jini ne ke zuba. Sai da ya rage saura kiris karfin Gulzum ya kare. Kawai sai aka ga kibiyar dutse ta taho da gudu ta cake a cikin idon wannan zakin. Nan take zakin yai tsalle sama ya fado kasa matacce. A lokacin ne Gulzum ya sandare ya fadi kasa sumame. Koda su Jafar suka waiga bayansu sai suka ga ashe tsohon nan ne na garin wadancan mutane da suka taimaka ya tabe baka ya harbi wannan zaki. Tsohon ya dagawa su Jafar hannu yana mai yin murmushi a garesu, sannan ya juya da baya a guje ya nufi can kan tsauni inda sauran tsirarun 'yan uwansa suke. A guje su Jafar suka karasa kan aljani Gulzum suka iske shi yana numfarfashi sama-sama. Gulzum ya mike zaune da kyar ya dubi gawar Mazalish sai ya fashe da kuka, su ma su Jafar saii suka kama kukan. Anan wajen suka kwana suna kuka. Sai da gari ya waye rana ta take, sannan suka sami 'yar nutsuwa. A wannan lokacin ne suka fara shawarar tashi su ci gaba da tafiya, amma sai Jafar ya kawo shawarar cewa a bari dai zuwa kwana uku don Gulzum ya yi jinyar jikinsa. Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga wata babbar inuwa ta rufe su daga sama. Cikin firgici suka daga kawunansu sama, ai kuwa sai suka yi arba da ita. Ba komai ba ce, face narkekiyar macijiyar nan mai kawuna barkatai; wadda ta taba hadiye su. Kuma ita ce dai suka gani a fadar sarki Azmul Gallar a can duniyar sama. Kafin wani daga cikinsu ya yi wani yunkuri tuni macijiyar ta sauko da kanta guda kasa ta hadiye su ta bace bat tamkar bata taba wanzuwa a wajen ba. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar, bayan sun zama saura su uku kacal, a cikin wannan tafiya ta su ta cikin kundin tsatsuba, maimakon su shida. Al'amarin boka Shamharu kuwa; bayan ya sallami su Markahul Sabus sun tafi nemo abubuwa uku tare da aljani Durmazulu wadanda za'a yi amfani da su wajen kera kubar Muftahul Zarbil, sai ya đauki Samaratu mahaifiyar Markahul Sabus ya shiga cikin dakin halwar tsafinsa. Ruhin sarkin Lu'umanu kuwa yana take masa baya. Da shigar su cikin đakin sai Shamharu ya ajiye Samaratu a kan wani farin tebur tamkar an ajiye kwayar gero a babban daki. Shamharu ya dubi Lu'umanu ya ce, "Ka ga wannan hatsabibiyar bokanyar.tana da matukar hadari a garemu, kamar yadda danta Markahul Sabus ke da hadari, shi ya sa na riketa anan, domin ka da Markahul Sabus ya yi wani yunkurin da zai iya cutar da mu." Koda jin wannan batu sai Lu'umanu ya dubi Shamharu cikin yanayin mamaki ya ce "Ya shugabana ashe har da wani aljani da zai iya zamo abin shakka a tare da kai?" Shamharu yai murmushi ya bude baki zai ce wani abu sai kawai suka ga wani hadimi ya shigo cikin dakin dauke da gangar jikin Lu'umanu. Gaba daya jikin hadimin jini ne ke zuba idanunsa na rufewa da budewa da kyar. Cikin daka tsawa Shamharu ya ce da hadimin, "Ya kai Azmandu me ya faru gareku? Ina gimbiya Sima wacce na ce ku kwato ta da karfin tsiya ku zo mini nan da ita?" Cikin karfin hali Azmandu ya ce, shugabana ka yi sani cewa kamar yadda umarcemu mun tare su jarumi Hubairu yayin suke kan hanyarsu ta zuwa wani gidan kaya tarihi. A wannan lokaci suna tare da tsaron su Aljani Abtarul Hudes. Nan take gagarumin yaki ya barke inda suka yi mana rufdugu suka karkashe mu, suka daddatsa na datsawa. Da kyar na samu na sungumo gangar jikan Lư'umanu na gudu har na iso nan." Koda Azmandu ya zo daidai nan a zancensa sai ya sulale ya fadi kasa matacce. Nan take Shamharu ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa. Gaba daya fadar ta kama girgiza. Ya ce, "Lallai makiyanmu sun sami galaba akan mu." Kawai sai ya shafi wani madubin tsafi take hoton duk abin da ya faru ya bayyana tun daga lokacin da sarki Hudes ya yi sallama da su Hubairu kawo izuwa zuwan su birnin Laharim har aka daura auren gimbiya Sima da Jarumi Hubairu, kuma aka Musuluntar da duk mutanenn kasar. Koda gama ganin wadanna al'amura sai Shamharu ya fashe da kuka don tsananin bakin ciki. Haka shi ma Lu'umanu ya kama kukan saboda ganin cewa Shamharu yana yi sannan Ya ce, "Ya shugabana ka yi mini izini, kuma ka hadani da dakaru masu yawa mu je mu kone birnin Laharim gaba dayansa ya zamana ko kaza daya ba za ta rayu ba." Shamharu ya girgiza kai ya ce, "Ai.wannan damar ta wuce mu tuntuni. Ka yi sani cewa duk wanda ya doshi hanyar garin daga cikinmu nan konewa zai yi, tun da garin gaba daya ya zama na Musulmai. Wannan dalili ne ya sa har yanzu na kasa kawar da garin su Hudes. Ya kai Lư'umanu ka yi sani cewa yanzu ba mu da wata sauran dama wacce ta wuce mu kammala kera kubar Muftahul Zarbil, wacce za mu iya bude fadar sarki Azmul Gallar da ita, don na dauko kundin tsatsubansa na karance shi. Idan har na karance wannan littafi sai na kawar da dukkanin Musulman duniya, Don haka yanzu bari mu ga halin da su Markahul Sabus ke ciki ko suna samun nasara." Nan take Shamharu ya sake shafar madubin tsafinsa. Sai ga hoton duk abubuwan da suka faru ga su Markahul Sabus, lokacin da suka je birnin dodannin nan don debo narkakken dutse. Koda Shamharu ya ga abin da ya tar sai ya kyalkyale da dariyar farin ciki, shi ma Lu'umanu sai ya taya shi. Daga can kuma sa Shamharu ya murtuke fuska ya dubi Lu'uman ya ce, "Na umarce ka daga shiga cikin ganga jikinka ka tafi izuwa bakin gabar teku ta duniya ka tsaya a wajen Da zarar Su Markahu Sabus sun iso sun debi rabin ruwan tekun ka kwace abubuwa ukun da ke hannunsu, sannan ka kashe su gaba daya, ka taho mani da abubuwa don mu yi saurin kera kubar Muftahul Zarbil. Ni kuma yanzu zan tafi wani kebabben waje inda a can ne zan iya yin bincike na gano halin da sarki Azmul Gallar ke ciki, don kada ya shiyar mana wani tuggun da zai rusa mana al'amura." Koda jin haka sai ruhin sarki Lu'umana ya ce,"An gama ya shugabana." Nan take ruhin ya shiga cikin gangar jikinsa ta yi motsi, kuma ta zama haske ta 6ace. Bacewarta ke da wuya sai shi ma Shamharu ya zama bakan gizo ya disashe ya bace daga cikin dakin halar yana mai kyakyata dariyar keta, sai dai bai san cewa ya yi babbar mantuwa ba. Mantuwar kuwa ita ce bokanya Samaratu mahaifiyar aljani Markahul Sabus, wadda ke ajiye akan farin tebur. Koda Samaratu ta ga an fita an bar ta, ita kadai a cikin wannan daki na halwar tsafin Shamharu sai tá shiga bincike a cikin kayan tsatsubar sa. Lokacin da bincikenta yai nisa sai ta gano hanyar da za ta karawa kanta karfi da kuma yawan fukafukai. Nan take ta aikata hakan. Ai kuwa tana gamawa ta ji wani irin karfi ya shigeta mara misaltuwa. Kuma nan take fukafukanta suka zama guda miliyan daya, kamar na aljani Durmazulu. Koda ta ji wannan sabon al'amari a jikinta sai farin ciki ya lullubeta. Nan take ta fita daga cikin dakin halwar tsafin. Fitarta ke da wuya ta yi arba da masu tsaron fadar. Nan fa fada ya kaure tsakaninta da su. Cikin abin da bai wuce rabin sa'a ba Samaratu ta kashe gaba dayan masu gadin fadar, sannan ta fice daga cikin fadar gaba daya. Kuskuren da ta yi shi nc da ta manta ba ta dauki addar tsafin nan ta Shamharu ba wacce ake matukar nema ruwa a jallo, don hada shirin kawar da Shamharun daga doron duniya. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin bokanya Samaratu da masu gadin fadar Shamharu wacce ke tsibirin Baharzus, a Can sararin samaniya. Ita dai wannan fada sai da aka ginata a duniyar kasa, sannan aka dauketa aka kaita can kokoluwar samaniya aka ajiyeta, amma aihinta ba a can saman take ba. Al'amarin su Jafar kuwa bayan macijiyar nan ta hadiye su sai ta bayyana a fadar sarkı Azmul Gallar. Koda bayyanarta sai ta wangame baki ta amayar da su Jafar a gaban sarki Azmul Gallar. Suka fado kasa a jigace. Jikinsu na fitar da turiin zafin da ke cikin macijiyar. Sarki Azmul Gallar ya dube su ya kyalkyale dariya, sannan ya ce, "Ya ku wadanna shaidanu masu taurin rai ina yi muku barka da zuwa fadata a karo na biyu. Ku yi sani cewa a wannan karo na so na hallaka ku ta hanyan sanya ku a cikin sundukin haske, don ku je ku narkar da duniyarku. Ba don komai ba sai don na yi amfani da kasar duniyar ku na kera kubar Muftahul Zarbil wacce da ita ne zan iya kulle nawa litafin na kundin tsatsuba, amma sai ga shi bukata ba ta biya ba, domin iskar cikin kundin tsatsuban Shamharu ce ta tarwatsa sundukina, kuma tá zùke ku daga ciki ta sake mayar da ku izuwa cikin kundin tsatsuba. Ku yi sani cewa a halin yanzu tuni na yi sabon bincike har na gano wata sassaukar hanyar ta kulle nawa kundin tsatsuban, har ma na kera kubar Muftahul Zarbil. Yanzu zan kai ku cikin fada ta wacce aka kira ' Saubatul Askur' inda na ajiye nawa kundin tsatsuban, kuma a gaban idanun ku zan kulle shi da kubar Muftahul Zarbil." Kafin wani daga cikin su Jafar ya ce wani abu tuni sarki Azmul Gallar ya yi tsafi, sai suka bace suka bayyana a cikin fadar Saukatul Askur da su, da shi gaba daya. Fadar Saukatul Askur na da matukar fadi da tsawo domin za'a iya sa fadar ta Shamharu guda goma a cikinta. Gaba daya fadar an gine ta ne da zallan dutsen lu'ulu'u. Duk abin da idanu suka yi arba da shi a cikin wannan fada ba su taba ganin makamancinsa a wani wuri ba. A bangaren arewa a jikin bango wani gabjejen littafi ne ja. A jikinsa an rubuta Kundin Tsatsuba. Su Jafar suka daga kawunansu sama su ukun suna kallon katon littafin wanda inda zai fado musu ya turmushe su, gaba daya hallaka za su yi saboda girma da kuma nauyinsa. Jafar ya waiga baya ya dubi sarki Azmul Gallar ya ce, "Ya kai wannan sarki shin za ka iya gaya mini ko shafi nawa ne a cikin wannan littati?" Azmul Gallar yai murmushi ya ce, "Shafi dubu gomna ne a cikin wannan littafi kuma gaba daya sirrikan tsafina ne a ciki." Nan take Azmul Gallar ya sake yin tsafi sai ga wadansu 'yan wadannin dodanni guda uku, masu siffa irin ta sarki Azmul Gallar, suna dauke da wata katuwar kuba wace aka kera ta da zallan zinare. Azmul Gallar ya bushe da dariya ya ce, "Yauwa ga kubar Muftahul Zarbil nan sai ku zuba ido ku ga yadda za'a kulle Kundin T'satsubana da ita' Ita kanta wannan kuba ta Muftahul Zarbil gimanta ya wuce misali, domin ko aljanı Gulzum bai isa ya iya raba ta da kasa ba, saboda nauyin ta. Su Jafar suka zuba ido suna kallon 'yan wadannin dodannin nan uku da ke dauke da kubar, don su ga ta yadda za su iya kaita sama inda katon kundin tsatsuban yake, har su kulle shi. Tun da tsawon su ma bai kai izuwa farkon littafin ba. Yayin da wadannan wadannin suka je gaban littafinn dauke da kubar sai suka tsaya cak. Nan take kubar ta tashi sama da kanta ta soka kanta a tsakanin littafin ta nutse, sannan ta murda sau uku. Kubar ta ciro kanta ta fado kan hannun aljanun suka damketa. Koda faruwar hakan sai sarki Azmul Gallar ya bushe da dariya. Sannan ya ce, "An gaishe ku sarakan tsaro, Maza ku mayar da kubar Muftahul Zarbil ma'ajiyarta, ku ci gaba da tsaronta." Nan take dodannin uku suka tafi da kubar suka bace daga cikin fadar Saukatul Askur. Bacewar su ke da wuya sai sarki Azmul Gallar ya dubi su Jafar ya ce, "Ku yi sani cewa zan ba ku aiki na karshe wanda daga kansa ne kuma za ku san matsayinku. Walau dai ku tsira da rayuwarku, ko kuma ku hallaka. Wannan aiki ba na komai ba ne face na ba ku damar karasa karanta ragowar shafukan kundin tsatsuba na Shamharu a cikin kwanaki talatin kacal. Kun sani cewa a halin yanzu kuna kan shafi na ashirin da biyu ne. A yanzu haka na yi wata tsatsuba wacce za ta taimaka muku ku iya karanta shafi dari uku da uku a cikin kwana goma, kun ga kenan a cikin kwana talatin za ku iya kammala karatun littafin tun da har kun shigo shafi na ashirin da biyu a yanzu." Koda jin wannan batu sai mamaki kama su Jafar fuskokinsu na nuna alamun cewa wannan abu ba zai yiyu ba. Yelisa ta dubi sarki Azmul Gallar ta ce, "Ya kai wannan sarki yanzu me ye ribarka idan muka kammala karatun kundin tsatsuban Shamharu?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Azmul Gallar ya tuntsire da dariyar har da faduwa kasa don dadi. Sannan ya mikc tsaye ya ce, "Ai idan kuka kammala karatun Shamharu tamkar an baje mini gaba dayan kundin sirrikan tsafin sa ne akan fafai, don haka nan take za gama da shi. Domin shi kadai ne kishiyata a doron kasa." Kafin su Jafar su kara cewa wani abu sal sarki Azmul Gallar ya nuna su da dan yatsansa. Nan take wata irin shudiyar iska mai hade da wuta ta fito daga cikin danyatsan nasa ta durnga shiga cikin jikin su Jafar. Koda iskar ta gama shiga sai katuwar macijiyar nan ta sauko da rankwalelan kanta guda ta hadiyesu. Sannan ta bace bat daga fadar tabar sarki Azmul Gallar na kyalkyala dariyar mugunta. Su Jafar dai ba su tsinci kan su a ko'ina ba sai a gaban kudin tsatsuba kuma shafi na ashirin da uku ne a gabansu. Nan da nan shafin ya karanto kansa da sauri-sauri ya zuke su, suka fada ciki. Haka komai ya dunga faruwa gare su cikin sauri a duk inda suka tsinci kan su a cikin kundin tsatsubar、 Hakika sun hadu da masifu iri-iri tamkar za su hallaka, amma babu wanda ya mutu sai dai sun sha bakar wuya. A cikin kwana goma suka gama shiga cikin shafi na dari uku da ashirin da hudu ya zamana saura shafi dari shida da saba'in da shaida. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar bayan sun sake ziyarar fadar sarki Azmul Gallar a karo na biyu. Ziyarar da ita ce ta kawo sauyin tsarin karatunsu na kundin tsatsuba. SHIN SU MARKAHUL SABUS ZA SU SAMO SAURAN ABUBUWA GUDA BIYU WADANDA DA SU NE SHAMHARU ZAI IYA KERA KUBAR MUFTAHUL ZARBIL? YAUSHE NE SARKI MUZULUCH ZAI GAMA AIKAYAR BAWA MOZUR DA GIMBIYA SUHAILA? SHIN SU JAFAR ZA SU KARASA KARANTA SHAFUKAN KUNDỊ GUDA DARI SHIDA DA SABA'IN DA SHIDA? INA LABARIN BOKANYA SAMARATU WACCE TÀ KARAWA KANTA KARFI DA YAWAN FUKAFUKAI A FADAR SHAMHARU KUMA TA KẠSHE DUKKANIN MASU GADIN FADĄSA TA GUDU? MU HADU A MUFTAHUL ZARBIL LITTAFI NA BIYU DON JIN CI GABANA WANNAN LABARI DAGA MAI DEBE MUKU KEWA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9