tana mai cewa, "Ya kai dan uwana idan har rayuwarka za ta zamo cikin hadari, gwara na janye wannan yaki, domin kai kadai ka rage mini a duniya. Ka sani cewa ba mu da sauran 'yan uwa ko dangi."
Sa'adda Haiman ya ji wannan batu na 'yar uwarsa sai shi ma jikinsa ya yi sanyi, bai san saad da ya fara zubar da hawaye ba. Cikin damuwa ya dubeta ya ce, "Yake 'yar uwata ki yi sani cewa abin kunya ne ga babbar nasarauta kamar tamu a ce ta ji tsoro ta janye yaki. Haka kuma raini ne abin da jarumi Mikdad ke nufin yi a garemu, don haka dole ne mu kare mutuncinmu ta kowanne hali. Ba gudu, ba ja da baya, ko ruwa ko iska sai mun ga bayan makiya. Tabbas yau mijinki sarki.Shaubatul Azlam wanda ya kasance babban masoyinki a da yanzu ya zama babban mikiyinki, kuma ba komai ba ne ya haddasa hakan ba face.hassada da kyashin ganin ke ma kin zama Sarauniya, mai mulkin babbar kasa kamarsa.
Haka dai Haiman da Ashikatul Ashiriya suka ci gaba da tattauna wannann al'amari har zuwa wani lokaci. Sannan aka tashi daga majalisin kowa ya kana gabansa.
Duk wannan tattaunawa da aka yi ni Suhaila ina labe ina sauraro, don haka sai hankalina ya dugunzurma na shiga tunani a raina cewa, ba zan taba bari ba rayuwar dan uwan.mahaifiyata ta salwanta a wannan yaki ba. A wannan rana dai yadda na ga rana haka na ga dare. Zuciyata ta cika da tunani da kuma sake-sake, amma ban samu mafita ba.
Kashe gari mayaka suka sake fita filin daga. A wannan rana jarumi Haiman ya yi shigar rigar karfe, kuma fuskarsa rufe take da hular karfe, ba'a ganin komai a fuskarsa face idanuwansa. Hakika shigar da ya yi mai matukar kwarjini ce da burgewa dole ne idan aka ganshi a ji tsoronsa, saboda cikar surarsa ta sadaukan taka da kuma muggan makaman da ke jikinsa. Tare da shi akwai wadansu jarumai mutum bakwai suma sun kasance masu kwarjini da cika ido. Kuma duk irin shigar da ya yi suka yi abin gwanin sha'awa.
Wadannan jarumai bakwai tare da jarumi Haiman su suka zamto akan gaban sauran dakarun Ashikatul Ashriya bisa dawakansu. Duk wanda ya gansu a wannan lokaci dole ne ya firgita, kuma dole ne su burge shi. Tuni dama su jarumi Mikdad sun iso filin daga, kuma shi ma yana kan gaba tare da su Hukashatu. Koda aka yi arba tsakaninsu Haiman da su Mikdad sai kowa zuciyarsa ta buga, aka fara kallan-kallo. Mikdad ya Jubi Hukashatu ya ce, "Wadannan kuma su waye daga cikin mayakan Kisra, wadanda ba su bayyana kan su ba, a jiya sai yau?"
Hukashatu ya hadiyi miyau, sannan ya ce, "Ya shugabana ba ni da labarin su waye, amma ga dukkan alamu yau yakin nan zai yi tsamari matuka"
Mikdad yai ajiyar numfashi ya ce, "Kwarai kuwa, domin da ganin wadannan mayakan sun cika jarumai. Ina son mu kasance masu jajircewa iyakar yin mu don babu mamaki kwarjininsu ya zamo na banza, mu gama da su cikin kankanin lokaci."
A yau dai mayakan birnin Kisra sun fito ne da sojoji ninkin din na jiya. Wato maimakon miliyan daya su miliyan biyu ne, Su Mikdad ba su farga da haka ba, sai daga baya lokacin da sahun mayakan na farko ya gama fitowa sai kuma ga wani sabon sahun sun jero hankali daya bayan daya, har suka gama jeruwa. Mayakan dai sun kasance rukuni-rukuni. Akwai mahaya, maharba, 'yan masu, da kuma masu takubba da garkuwa.
Koda ganin wannan gagarumin shiri, sai gaba dayan dakarun jarumi Mikdad suka karaya, fara ja da baya, su Hukashatu ne kadai suka daure suka tsaya kusa da Mikdad, su ma jira suke su ji ya ce a janye yakin. Cikin tsananin fushi Mikdad ya juya ya dubi mayakansa guda dubu saba'in ya daka musu tsawa yana mai cewa, "Ashe har kun manta da yakin da muka jiya ne? Lallai mu ne muka yi nasara, kuma ina mai tabbatar muku da cewa yau ma mu ne za mu samu nasara. Na rantse da kaifin takobin nan duk wanda ya gudu daga cikinku bayan yakin nan sai na bishi duk inda ya shiga na sare shi."
Koda jin wannan batu sai dakarun nan suka daddawo kan sahu suka tsaya. Hukashatu ya kara matsawa kusa da Mikdad ya ce, "Ya shugabana ka yi sani cewa babu alamar nasara a yau. Ina ganin zai fi kyau mu janye yakin nan."
Cikin harara Mikdad ya dubi Hushakatu ya ce, "Ya kai Hushakatu ka yi sani cewa yau ba gudu, ba ja da baya. Na rantse da darajar uwata ko zai rage saura ni kadai a filin nan sai na yaki wannan runduna. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan za ku tayani yakin nan ku tayani, in kuma ba za ku tayani ba kowa ya kama gabansa."
Koda jin haka sai Hukashatu ya dubi Maharaz, Ubaiyu, Sariku, Mukauzur da Mukaifa ko dayansu zai ce wani abu, amma duk sai suka yi shiru ba su ce kala ba.
A wannan rana da gimbiya Ashikatul Ashiriya ta fito kallon wannan yaki, kuma nima sai da na fito don mu ga karshen tika-tiki, don ko haufi ba mu da shi akan cewa sai mun sami nasara akan wadannan abokan gaba. Da ni da mahaifiyata muna cikin harabar katangar garin ne bisa wani dogon mumbari wanda daga kansa muna iya hango duk abin da ake faruwa a filin da hankalinmu da kuma nutsuwarmu akan kallon fadan Haiman da Mikdad. A wannan lokaci mun ga gwagwarmayar jarumai irin wacce ba mu taba gani ba. Mikdad da Haiman suka ci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin kwarcwa, juriya da bajinta da kuma zafin nama, tamkar jukuriansu ba na jini da tsoka ba ne.
Wani lokacin sai ka ga har katantanwa suke a kasa kamar mazari, wani lokacin kuma su rinka alkafura a sama tamkar tsuntsaye. Sai da suka kusan shafe rabin sa'a a haka ba tare da dayansu ya sami nasarar yankar daya ba, ko sukarsa.
Al'amarin da ya fusata su kenan su biyun, suka sauya salon fada. Salon kuwa shi ne hadawa da duka hannu da kafa. Nan fa tsagwaron karfi ya fara amfani, kuma sai abun ya zama gasa, domin idan daya ya sami nasarar naushin daya sai ka ga shi ma dayan ya yi wata hikimar ya samu nasarar ramawa.
Haka dai suka ci gaba da wannan fafatawa. Ba za to, sai Mikdad ya yi wani irin tsalle a sama
kamar an cilla kibiya aka harboshi yi yi alkalira ya juya jikinsa kafafunsa suka yi sama, kansa ya yi kas, yana rike da takobinsa hannu biyu ya laftawa Haiman sara a gadon bayansa. Take takobin tasa ta datsa sulken da ke jikinsa ya đare sannan ta ratsa ta shafci naman jikinsa, nan take jini yai tsartuwa. Haiman va kurma ihu ya tan taga-taga kamar zai fadi ya durkusa bisa gwiwarsa ta dama. A lokacin ne Mikdad ya dirgo kasa bisa kafafunsa, yana mai murmushin samun nasara. Kawai sai ya sake daga takobinsa sama ya rike ta da hannu biyu ya nufi inda Haiman ke tsugunne don ya karasa shi. Ba zato, ba tsamani sai Haiman ya yi sufa da bayą shi ma kamar an cillo shi da kibiya yana rike da takobinsa a mike ya yi saitin kirjin Mikdad.
Cikin zafin nama Mikdad ya goce, amma duk da haka sai da takobin Haiman ta nutse a gefen kafadarsa, ta hudo baya.
Mikdad ya kwarara ihu bisa tsananin radadi da zafi da ya ji. shi kuwa Haiman sai ya zare takobin ya sake kai masa wani saran a wuyá. Mikdad ya kare saran sa'adda jiri ya debe shi ya fada akan fuskarsa. Amma sai ya sake tasowa da sauri cikin matukar juriya suka ci gaba da artabu tamkar a sannan suka fara. Ni kam ban san sa'adda na yiwa Mikdad tafi ba. Mahaifiyata kuwa ta kalleni ta daka mini harara.
A can bangaren su Hukashatu kuwa al'amarin ya sha banban, domin kare jini, biri jinin da suke yi, har ma ta kai ga mutuwar wasu daga cikin manyan jaruman da Haiman ya zabo. Wato abokan kafsawar su ne suka sami nasara akan su. Mutum biyu kuwa sun yi ragas da Ubaiyu da Sariku. Yanzu dai saura mutum biyu wadanda suke mugun dauki ba dadi da Hukashatu da Mukaifa. Tabbas Hukashatau ya samu ya kashe abokin fadansa. Kuma sai da ya taimakwa Mukaifa, sannan suka kashe nasa, abokin gamin Mukauzar da Maharaz kuwa suna can tsakiyar fili suna taimakawa sauran 'yan uwansú.
A wannan rana ta biyu an ci kasuwar mutuwa a wannan gagarumin yaki, domin sai da aka kashe dakarun Ashikatul Ashiriya guda dari takwas da arba'in. Su kuwa dakarun jarumi Mikdad sai da aka kashe dubu hamsin da tara ya zamana saura su dubu goma da daya kacal. Wannan lokaci jarumi Mikdad da jarumi Haiman sun yi laga-laga da juna, ba sa iya gani sosai saboda jini ne kawai ke kwarara a jikinsu kuma jiri na dibarsu, suna faduwa da tashi, amma saboda bakin naci ba su daina kaiwa juna farmaki ba. Kai har sai da ta kai ta kawo cewa duk su biyun sun zube kasa suna haki, kamar ran su zai fita, sai kallon juna suke kawai sun kasa koda motsi ne.
A daidai wannan lokaci ne aka buga gangar tsai da yakin. Nan fa kowanne bangare suka ja nasu-ina-su aka watsc daga filin daga.
Lokacin da aka shigo da jarumi Haiman cikin harabar birnin a dauke cikin halin suma, kuma duk jikinsa jini ne ke zuba. Koda sarauniya Ashikatul Ashiriya ta ganshi cikin wannan hali sai ta rusa kuka. Ta rungume shi tana ihu, don a tsarnmarninta mutuwa zai yi. Ba ita ta dawo cikin hayyacinta ba, sai bayan da aka yi masa magani ya farfado, har ya bude idanu. Cikin karfin hali Haiman ya dubi sarauniya yai mata murmushi, sannan ya bude bakinsa da kyar ya ce, "Ya ke yar uwanta ki yi sani cewa wannan yaki ya zo karshe, albarkacin kabarin
mahaifinmu idan aka yi fita ta uku sai na kashe Mikdad."
Koda jin haka sai Ashikatul Ashiriya ta sake fashewa da kuka ta ce, "Haba dan uwana guba fa ka ga irin raunikan da ke jikinka?
Shin ba ka halin da ka shiga bane? Na rantse da darajar karagata ba zan bari a hallaka ka ba a wannan yaki. Ni kam daga yau zan hakura na janye, kuma zan mika Suhaila ga abokan gaba."
Koda jin wannan batu sai Haiman ya yunkura cikin juriya ya tashi zaune ya dubi Ashikatul Ashiriya idanunsa na zub da hawaye ya ce, "Yanzu kina nufin cewa dan uwa yafi da kenan?"
MU HADU A PART G DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI..**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA👆👆
PART G ❤️
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI, king 👑 of adventures story 🥰
Typing: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY..
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD..
Idan masu karatu Basu manta ba, daman mun tsaya ne a dai-dai wannan wurin, Kuma Allah mai kowa da komai ya bamu ikon cigaba a yau din nan..
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA
Koda jin wannan batu sai Haiman ya yunkura cikin juriya ya tashi zaune ya dubi Ashikatul Ashiriya idanunsa na zub da hawaye ya ce, "Yanzu kina nufin cewa dan uwa yafi da kenan?"
Ashikatul Ashiriya ta ce, "Kwarai kuwa. Ka yi sani cewa idan na rasaka na rasaka kenan har abada tun da kai kadai gareni, ita kuwa Suhaila ko na rasata nan gaba zan iya sake haihuwar wata 'yar kuma na kaunace ta fiye da yadda na kaunaci Suhaila."
Haiman ya share hawaye, sannan "Yake 'yar uwata ki yi sani cewa idan har Mikdad zai iya mikewa ya ci gaba da yaki a gobe tabbas nima zan mike, Haka kuma idan har bai janye mana ba mu ma ba zamu janye ba. Har yanzu ina nan akan bakana na kare mutuncinki da mutuncin 'yarki, ba kuma zan daiña ba face na daina numfashi a doron kasa."
Koda jin haka sai Ashikatul Ashiriya ta rungume Haiman suka ci gaba da kuka tare. Duk wannan abu da ya faru tsakanin Haiman da mahaifiyata ina labe ina kallonsu. Tuni idanuna suka ciko da hawaye saboda tausayinsu, zuciyata kuwa tayi bakikkirin ba komai a cikinta face tunaninnyadda zai tsayar da wannan yaki ta kowane hali don kawai Haiman ya tsira da rayuwarsa, ya zamana cewa ba a yanke kaunar dake tsakaninsa da mahaifiyata ba.
A wannan dare ban yí barci ba, saboda tunanin hanyar da zan bi na yi maganin wannan babbar matsala. Sai da dare ya raba amman wata dabara ta fado mini ba.
A can sansanin su jarumi Mikdad kuwa sun shiga cikin wani hali na tsananin bakin ciki bisa rasa rayukan da aka yi masu yawa. Shi dai jarumi Mikdad bai dawo cikin hayyaicinsa ba, sai bayan rabin sa'a. Yana farfadowa ya yi arba da Hushakatu, Mukaifa, Mukauzar da Maharaz tsaye a kansa kowannensu a matukar jigace, kuma ga raunika a jikinsu barkatai duk da cewar sun yi wa kansu magani, suna cikin yanayi na rashin cikakkiyar lafiya. Cikin alamun razana Mikdad ya ce "Ina Ubaiyu da Sariku?"
Koda jin wannan tambaya sai duk suka sunkui da kai kas ba su ce komai ba. Hakan ne ya sa Mikdad ya fahimci cewa su Ubaiyi sun mutu. Kawai sai ya takarkare ya kwarara uban ihu mai firgitarwa, wanda saboda amonsa sai da mutanen cikin birnin Kisira suka jiyo shi duk da cewar akwai tazara mai dan nisa tsananin sansanin da bimin, Ni kaina da na ji wannan ruri sai da hantar cikina ta kada.
Jarumi Mikdad ya fashe da kuka yana mai alhinin Ubaiyu da Sariku har ma ya fara surutai kamar wanda kwakwalwarsa ta tabu, yana mai cewa "Waye ya kashe mini 'yan uwa?
Ya akai kuka bari aka kashe su?"
Koda Hukashatu ya ga wannan hali da Mikdad ya shiga sai ya fara rarashinsa yana mai bashi hakuri akan ya rungumi kaddara. Da kyar ya shawo kansa ya dina kukan. Mikad ya dubi Hukashatu da su Mukauzar ya ce, "Wai shin har yanzu baku gano mani wane ne wancan jarumin da nayi kare jini biri da shi ba? Ni kam na fara zargin cesa koma wanene ya na đaya daga cikin mutanen da aka ba mu horon yaki tare abirne Rum. Duk abin da na iya na dabarun yaki shima sai naga ya iya shi.
Hükashatu ya ce, "Ya shugabana hakika maganarka gaskiya ce, domin muma abokan gamin namu duk haka suka kasänce. Na so ace mun samu nasarar bude fuskar daya dagá cikin mutanen kafin a tsaida yaki amman abu ya citura.
Mikdad yai ajiyar zuciya ya ce, "Ba komai duk yadda zan yí sai na yi dan na ga fuskar abokin gwaina a karo na biyu. Haka dai su jarumi Mikdad suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai sai a sannan ne su Hukashat suka fita daga cikin tantin jarumi Mikdad suka tafi nasu tantin, shi kuma sai ya kwnata ya kama aikin rago saboda gajiyar da ke jikinsa. Yayin da yai nisa a cikin barcí kawai sai yaji ana táshinsa. Cikin firgici Mikdad ya bude idanunsa kawai sai ya yi arba da ni tsaye a kansa. Hannuna na rike da wata zabgegiyar wuka na dora kaifinta a bisa makögwaransa. Danyatsana daya yana a kan bakina ina mai nuna masa alamar kada ya kuskürá ya yi magana. Kawai sai na budi baki cikin yin magana a hankali yadda na wajen tántin ba zai jiyo ni ba na ce;
Idan ka yi kyakkyawan motsi sai na yanka maka makogwaronka.
Mikdad bai motsa ba, kuma tun da yai arba da ni sai ya kura mini idanu cikin tsananin mamaki ya kasa cewa komai yana mai yi mini wani irin kallo har da murmushi, wanda na kasa gane ma'anarsa Na dube shi ya kyau na ce, "Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa ni ce gimbiya Suhaila 'yar ga sarauniya Ashikatul Ashiriya wacce ake yin wannan yakin dominta. Ka yi sani cewa ban zo nanba wajenka don na hallaka ka ko don na hanaka yin wannan yaki, sai don na gargadeka da cewa kada ka kuskura ka kashe kanin mahaifiyata a wannan yaki. Idan kuwa ka kashe shi, kai ma sai na kashe ka. Kada ka yi mamakin cewa zan iya kashe ka, tun da yanzu ma ba ka san yadda aka yi na shigo har nan ba tare da wani ya gani ba. Kuma da ina son kashe ka ɗin, da tuni ka zama gawa."
Cikin matukar mamaki jarumi Mikdad ya ce, "Wanene kanin mahaifiyarki, wanda ba kya son na kashe shi a wannan yaki?"
Suhaila ta ce, "Shi ne wannan jarumin da kuka fafata wato wanda kuka yi kare jini, biri jini da shi. Hakika idan ka kashe shi ka yanke kauna mai girma wacce mutum bai isa ya iya misalta ta ba. Idan har ka bár shi da rai na yi alkawari zan kawo kaina gareka wajen sarki Shaubatul Azlam wato mahaifina. Ba na son ka janye daga wannan yaki, saboda wani dalili wanda ba zan iya gaya maka shi ba yanzu. Da wannan kalami nake maka sallama sai gobe a filin daga idan mun sake saduwa."
Koda na zo nan a zancena sai na juya da nufin fita daga cikin tantin, Mikdad ya ce,"Dakata yake wannan kyakkyawar 'yar Sarkin."
Cikin sauri na waigo muka sake duban juna har yanzu akwai murmushi akan fuskars Mikdad ya ce, "Na ji duk abin da kika fada kuma na amince. Amma nima ina son ki yi min wata alfarma guda biyu. Alfarma ta farko ita ce ina son bayan an gama yakin nan ki ba ni amsar tambayoyi guda uku. Tambaya ta farko ita ce; ina son na san yadda aka yi kika baro ciki birnin Kisra a cikin daren nan har kika shigo cikin wannan tantina, ba tare da wani ya ganki ba? Tarmbaya ta biyu ita ce ina son dalilin da ya sa kika ki kashe ni yanzu, tunda har kin sameni ina barci, kuma ni na kasance abokın gabarku ne? Tambaya ta uku ita ce ina son na san zabin zuciyarki shin tsakanin mahaifinki Sarki Shaubatul Azlam da mahaifiyarki Ashikatu Ashinya wa kika fi so?"
Koda na ji wadannan tambayoyi sai na cika da mamakin dalilinsa na gabatar da gareni Kawai sai na yi murmushi na ce "Na dauki wannan alkawari, kuma zan cika shi."
Cikin hanzari na fice daga cikin tantin. Ina fita na kama wani doki da ke wajen a tsaye na yi tsalle na haye kansa, sannan na zabure shi da gudu na nufi katangar birnin Kisra. Cikin firgici dakarun Mikdad suka farka daga barci, sakamakon karar sawun dokina. Cikin hanzari wasu daga cikinsu suka haye dawakansu suka biyo bayana suna masu tsakanin gudu. Kafin su cimmini tuni na isa bakin kofar gari masu gadi suka bude mini kofa na shige, sannan su ka maida kofar suka rufe. Lokacin da wadannan dakaru suka koma ne aka tambayi jarumi Mikdad wanene ya shigo cikin tantinsa haka har ya gudu ya tsira ba a kama shi ba? Mikdad yayi dan murmushi ya ce, "Gimbiya Suhala ce 'yar sarauniya Ashikatul Ashiriya wacce domin ta ne muke wannan gagarumin yaki." Nan fa kowa ya cika da mamaki aka yi ta ka-ce-na-ce.
Sai da aka kwana goma sha hudu ana jinyar marasa lafiya bisa wannan kazamin yakda aka yi, sannan aka buga tambarin kufsawa a karo na uku. Nan fa kowacce runduna ta fito flin daga. Wannan karon kuma mayakan Sarauniya Ashikatul Ashirya guda miliyan hudu ne, su kuwa mayakan jarumi Mikdad saura su dubu tara da dari tara da casa'in da tara. ldan mutum ya dube su ya kwatanla yawansu da abokan gaba sai ya ga kamar an baje buhun dawa an dora tururuwa guda daya cal akai. Shi
kansa jarumi Mikdad sai da tsoro da fargaba suka cika masa zuciya, sa'adda ya ga yawán abokan gabar.
Cikin sanyin murya da karayar zuciya ya waiga ya dubi dakarun nasa gaba daya ya ce,
"Ya ku mazajen kwarai ku yi sani cewa yau nai muku izinin ku janye daga wannan yaki, ku barni ni kadai na karasa aikina. Ku sani cewa Idan na yi nasara duk abin da sarki Shaubatul Azlam ya bani zn raba shi tare da ku, idan kuma ban yi nasara ba sai ku koma gare shi ku sanar da shi abin da ya faru.
Koda jarumi Mikdad ya zo nan a zancensa sai ya juya ya tunkari inda abokan gaba ke tsaye shi daya cikin kwarin zuciya da nufin yakarsu.
Lokacin da jarumi Haiman ya ga abin da ya faru tsakanin jarumi Mikdad da jama'arsa sai shima ya dubi miliyoyin dakarun da ke bayansa ya ba su umarmin kada dayansu ya yì wannan yaki. Kawai sai shi ma ya tunkari jarumi Mikdad da sauri, don su hadu a tsakiyar filin daga.
A wannan rana ma ni da mahaifiyata muna can kan katankar birnin Kisra muna hango abin da ke faruwa a filin daga. Na lura da cewa mahaifiyata na cikin tashin hankali da matukar damuwa bisa wannan haduwa da ke shirin wakana tsakanina jaruman biyu, wato Haiman da Mikdad.
Lokacin da Haiman da Mikdad suka zo daf da juna a tsakiyar filin daga sai suka tsaya.kawai suna kallan-kallo. Mikdad ya budi baki ya ce, Ya kai wannan jarumi ina son ka taimaka ka cire hular karfen da ke kanka, don na ga fuskarka kafin mu fara wannan yaki. Ka yi sani cewa ina ji a jikina cewa ni da kai mun san juna, dan haka Lallai mu taba haduwa a wani wuri dabam ba nan ba."
Koda jin wannan batu sai Haiman yai ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Hakika zancen ka dutse ne, amma ba zan iya bari ka ga fuskata ba, ina mai rokon alfarma guda daya a wajenka.
Alfarmar kuwa ita ce idan har ka sami nasarar kashe ni kar ka bude fuskata, har 'yan unwana su dauke gawata, idan kuma nine na sami nasara akanka zan tafi da gawarka na binne ta da kaina a cikin gidana, domin kabarinka ta debe mini kewa."
Cikin mamaki Mikdad ya ce, "Saboda me kake son ka tafi da gawata har ka binneta a gidanka?"
Haiman ya ce, "Saboda na yi alfaharin cewa na kashe jarumi, wanda ya shahara a duniya."
Yayin da Mikdad ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce, "In haka ne ai kaima ka cika gwarzon jarumi, shaharar ce dai ba ka yi ba amma idan har ka kasheni tabbatas za ka shahara."
Gama fadin hakan ke da wuya aka buga gangar fara yaki. Nan take Haiman da Mikdad suka fara artabu. Wannan karon dai kowa da sabbin dabaru yaki ya zo, don haka sa gumurzurn nasu ya zama abin sha'awa da debe kewa ga dukkanin miliyoyin jama'ar da ke filin.
Lokacin da gumurzan ya dau zafi sai hankalin jama'a ya dugunzuma, domin a ko yaushe komai zai iya faruwa ga dayansu, kuma babu yakinin cewa ga wanda zai samu nasara. Suna cikin matsanancin yakin ne Mikdad ya sami wata dama ya yi wa Haiman wani wawan naushi a fuska. Nan take Haiman ya ga taurarin wahala a idanunsa. Kafin ya watstsake Mikdad ya sake mangareshi da kafa ya fađi kasa wanwar takobin sama ta yi tsalle gefe guda.
A lakacin ne Ashikatul Ashiriya ta kurma ihu cikin tsananin bakin ciki da damuwa.
Mikdad ya taho kan Haiman rike da takobi ya tsaya, kumar zai sare shi, amma sai ya juya baya yana mai waigawa baya ya dubi can inda gimbiya Suhaila da mahaifiyarta ke tsaye. Koda ya dubi can inda Suhaila taken, sai ya yi murmushi ya kau da kai. Har yanzu Haiman yana kwance a kas, bai dawo cikin hayyacinsa ba. Cikin zafin nama Mikdad ya kama hular karfen Haiman ya tumbuketa sai ga fuskar Haiman ta bayyana, kuma a daidai lokacin ne ya dawo cikin hayyacinsa.
Koda Mikdad ya yi arba da fuskar Haiman sai bakin ciki ya turnuke shi ya fashe da kuka, kuma ya yi wurgi da takobin hannunsa. Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan, har ita kanta sarauniya Ashikatul Ashiriya Haiman ya mike
tsaye cikin sanyin jiki ya kama kafadun Mikdad ya tashe shi tsaye suka fuskanci juna.
Kowannensu na zub da hawaye. Kawai sai suka rungume juna suka sake fashe da kukan farin ciki. Gaba daya filin ya rude da sowa da tafi. Ita kuwa sarauniya Ashikatul Ashiriya sai ta sake cika da mamaki, kuma ranta yai bakikkirin. Kawai sai ta sauko