Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
"Ai kai ne akan gaba don haka sai ka ci gaba da tafiyar mu gani in ya so mu sai mu yi koya da kai." Ba tare da fargabar komai ba Haiman yå daga kafarsa ya dora a gaba, amma sai ya sakin karfinsa gaba daya yà fara da dora babban dan yatsan ƙafarsa, bisa ga mamaki sai ya ga inda ya dora kafar tasa bai rufta ba, don haka sai ya sake dira a wajen. Koda ganin wannan dabara sai ni dai Mikdad muka kwaikwaya haka suma sauran abokan tafiyar ta mu duk suka yi hakan. Duk da wannan dabara sai da mutum dubu biyu suka rufta cikin wannan dutsen suka halaka. Ni kaina akwai lokacin da kafata ta zame na rufta na cikin wutar amman sai jarumi Mikdad ya cillo mini igiya cikin zafin nama na kama igiyar shi kuma ya rinka ja har ya zaroni daga karshin dutsen da kyar. Tabbas in ba don ya kai mini wannan dauki ba da tuni na nutsć a cikin wannan narkakken dutse. Tun daga wannan lokaci na ji na fara son Jarumi Mikdad a cikin zuciyata saboda ganin yadda ya sallama rayuwarsa ya ceto ta wa, duk da cewa ga dan uwan mahaifiyata na jini a wajen, amman shi bai shirya sallamar da ta sa rayuwar dornin tawa ba. Haka dai aka ci gaba da tafiya tsawon sa'o'i uku, sannan muka zo karshin duwatsun muka sauko kan turba. Kwatsam! Sai muka ga an watso mana wata irin ragar karfe. Kafin mu an kara ragar ta kanannade kowa kuma anyi sama da mu, kuma köwa tasa da bam a cikinmu, sai gashi muna reto a jikin bishiyoyi. Ba zato, ba tsammani sai mukà ga wasu mayaka suna firfitowa daga sakuna wadanda adadinsu ya ninká na mu sau goma. Daga can kuma sai ga mahaifina Sarki Shaubatul Azlam a cikin mayakan yana mai nufo mu dauke da murmushi a bisa fuskarsa. Da zuwansa inda nake sai ya sa aka sauko da ni kasa aka warware ragar da ta rufeni na fito. Take muka rungume juna cikin tsananin farin ciki. Kawai sai na sa hannuna cikin jakar da ke rataye a kafadata na dauko littafin nan wanda a jikinsa aka rubuta mabudin arzikin Kisra, na baiwa mahaifina sarki Shaibatul Azlam, na ce masa, "Wannan shi ne abin da ka dade kana nema, ba ka samu ba sai yau." Cikin murna ya karbi littafin ya ce, "Ya ke 'yata aikinki ya yi kyau, kuma yau nasa miki albarka irin wacce wani uba bai taba sawa yarsa ba ba. Yau ne burina na duniya zai gama cika. Yanzu sai ki zo mu wuce gaba don mu ida kogon Baitul Husuk" Duk wannan abu da ke faruwa su Haiman na sakale a sama cikin ragar karfe, suna masu kallon su cikin tsananin mamaki. Har mun juya za mu tafi mu bar su a wajen sai na tsai da mahaifina na ce, "Ya kai Abbana ina son ka yi mini wata alfarma guda daya" MU HADU A PART J DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI 🙏💯**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA DAYA 👆❤️ PART J 🌹❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑 POSTING ** NAJIBULLAH MUHAMMAD** TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.... Duk wannan abu da ke faruwa su Haiman na sakale a sama cikin ragar karfe, suna masu kallon su cikin tsananin mamaki. Har mun juya za mu tafi mu bar su a wajen sai na tsai da mahaifina na ce, "Ya kai Abbana ina son ka yi mini wata alfarma guda daya" Cikin mamaki Sarki Shaubatul Azlam ya dube ni ya ce, "Wace irin alfarma kike son na yi miki?" Na dube shi cikin alamun shagwaba na ce, "Ina son mu tafi da jarumi Mikdad saboda ya ceci rayuwata, yayin da muke kan duwatsun can. Na san idan muka tafi muka barshi a haka yunwa da kishirwa ce za ta kashe shi." Koda jin wannan batu sai sarki yai shiru yana tunani. Daga can sai ya ce,"Shi kenan na amince za mu tafi tare da shi, amma ba za'a fito da shi ba, daga cikin ragar karfen nan ba, domin kin san cewa hadari ne yin hakan." Kawai sai na yi murmushi ga mahaifina na ce, "Na amince. Nan take aka sauko da jarumi Mikdad kasa daga kan bishiya yana cikin rigar karfen. Sannan aka zura wata 'yar sanda a cikin ragar daga samanta sai dakaru biyu suka yi kama-kama, suka daga ragar sama sandar na bisa katadunsu aka ci gaba da tafiya, muka bar jarumi Haiman da sauran dakarun Mikdad sakale kan bishiyoyi cikin ragar karafa. Koda na waigo na dubi fuskar Haiman sai na ga yana zubar da hawayen bakin ciki, nadama da kuma takaicin wannan makirci da na kulla musu shi da 'yar uwarsa sarauniya Ashikatul Ashiriya. Haka dai aka ci gaba da tafiya har tsawon yini guda. Ba mu ya da zango ba sai gabanin Magariba a cikin wani daji mai yawan yabanya. Bayan an zauna ana hutawa sai aka raba abinci da abin sha, aka baiwa kowa. Amma ban da Jarumi Mikdad wanda ke cikin ragar karfe a rufe. Kawai sai na dauki nawa abincin na je na tsuguna a gabansa na ce, ya zuro hanunsa mu ci tare. Ba tare da gardama ba kuwa ya zuro hannun nasa muka fara cin abincin, dama na san cewa yunwa na nukurkusarsa sosai. Muna cikin cin abincin ne ya dube ni ya ce, "Wannan kyakkyawar 'yar sarki ina mai tunasar da ke cewa ina binki bashi na wadansu tambayoyi guda uku, wadanda kika yi mini alkawarin amsa su bayan an gama yaki. Tambaya ta farko ita ce ya akai kika baro cikin birnin Kisra kika shigo tantina, da ke sansaninmu har kika riskeni ba tare da wani ya ganki ba? Tarnbaya ta biyu kuwa ita ce ina son nasan dalilin da ya sa kika ki kashe ni a wannan lokaci da kika sameni ina barci, tun da na kasance abokin gabarku? Sai tambaya ta karshe wacce ita ce ina son na sani shin tsakanin mahaifinki Sarki Saubatul Azlam da mahaifilyarki sarauniya Ashikatul Ashiriya wa kika fi so a tsakaninsu?" Koda Mikdad ya zo nan a zancensa sai na bushe da dariya na ce, "Kwarai kuwa na yi maka alkwarin ba ka amsar wadannan tambayoyi don haka yanzun nan zan sanar da kai, a daren da na riske ka a cikin tantinka na biyo ne ta wata barauriyar hanya, wacce ta bullo ta can bayan sansaninku. Ma'ana ba daga bangaren kofar binin Kisra na fito ba. Sai da na yi dogon zagaye ta cikin daji kuma kafin nà fito dama tuni na sa an samo mini sutura irin ta dakaru yakinka tun a filin yaki a jikin wata gawa. Don haka sa'adda na shiga cikin dakarunka sanye da wannan sutura ba su gane cewa ni ba dayan su ba ce. Shi ya sa na sami damar shiga har cikin tantinka hankali kwance. Sai bayan na shiga tantine na cire suturar sannan na fiddo da wukar na dora akan makogwaronka. Ya kai Mikdad ya ki sani cewa ba wani dalıli ba ne ya sa naki kashe ka a wannan lokaci face tun a filin yaki ka burgeni, bisa ga irin jarumtarka, domin a rayuwata ina son mazaje masu tsananin karfi da jarumta. Dangane da tambayar ka ta karshe kuwa, na san za ka yi mamakin amsar da za ta fito daga bakina. Ko shakka babu bana kaunar mahaiyata sarauniya Ashikatul Ashiriya a zuciyata daidai da dakika guda, kuma ina matuƙar son mahaifina sarki Shaubatul Azlam, kamar yadda nake son kaina. Ya kai wannan jarumi mai ban al'ajabi ka yi sani cewa ba Ashikatul Ashiriya ba ce ainihin mahaifiyata ba. Mahaifiyata sunanta Mulaisu, kuma kuyanga ce ga sarki Shaubatul Azlam. A rana guda Mulaisa da Ashikatul! Ashiriya suka haifi 'ya'ya mata, suna gama haihuwa ne Mulaisa ta mutu ta bar jaririyarta kyakkyawa a raye, ita kuma jaririyar Ashikatu Ashiriya sai ta mutu ta bar uwarta a raye. Wannan lokaci Ashiriya ba ta cikin hayyacinta dan haka ba ta san abin da ke faruwa ba. Koda ganin haka sai sarki Shaubatul Azlam ya sa aka dauki jaririyar Mulaisa aka baiwa Ashikatul Ashiriya don kada ta farka ta ga cewa jaririyarta ta mutu ta kamu da bakin ciki kasancewar ta dade ta neman haihuwa shekara da shekaru ba ta samu ba. Kafin sarki Shaubatul Azlam ya shirya hakan sai da ya gargadi gaba dayen kuyangin dake wajen kan cewa komai daren dadewa duk wacce ta furta wannan sirri a bakacin ranta. Daga wannan rana Ashikatul Ashiriya ta ci gaba da rainon jaririya har aka radawa yarinya suna Suhaila. Wannan Suhailar ce ta girma ta zama budurwar da ake ba ka wannan labari yanzu. Ya kai jarumin jarumai ka yi sani cewa ban san wannan sirrin ba sai a ranar da mahaifiyata ta ce za ta tafi dani birnin Kisra saboda mutuwar mahaifinta. A sannan ne sarki Shaubatul Azlam ya kebe da ni a cikin turakarsa ya zaiyane mini wannnan al'amari, kuma ya bani labarin littafin mabudin arzikin Kisra da kuma kogon Baitul Husuk, sannan ya nemi hadin kaina bisa kan yadda za mu mallaki wannan littafin. Ba wani abu ba ne ya sa na aminta da shi har na ba shi hadin kai face na dade ina jin labarin irin tsananin son da yake wa mahaifiyata kuyanga Mulaisa, don an ce lokacin da ta mutu sai da ya kwana bakwai baya iya ci da shan komai, kuma kullum ba shi da aikín yi face zama a gaban kabarinta yana rusa kuka" Koda na zo ran a zancena sai na dubi jarumi Mikdad na ce ina fatan yanzu ka gamsu da amsashin tambayoyinka? Mikdad yai ajiyar zuciya cikin tsananin mamak sannan ya ce, "Hakika na gamsu, babu shakka na yi mamakin yadda 'yar ta guji uwarta mahaifiya ta gudu wajen mahaifinta. Tabbas yanzu kaina ya waye, kuma kin fitar da ni daga cikin duhun fahimta." A wannan lokaci ne Mikdad ya bukaci ruwa na sa aka kawo masa ya sha. Daga nan aka mike aka ci gaba da tafiya. Da mun yi 'yar tafiya kadan sai na fiddo littafin nan na duba taswirar hanya, sannan mu kara gaba. Tafiya sannu-sannu, mu kwana nan mu tashi can. Sai da muka shafe kwana goma sha biyu, sannan muka iso bakın kofar kogon Baitul Husuk. Nan fa kowa ya bude baki yana kallon abin mamaki. Domin duk yadda muke zaton kogon zai kasance ba haka muka iske shi ba. Kogon Baitul Husuk ya kasance babban gari wanda aka gina shi da zallan duwatsun wuta. Katangar kuwa tsawonta ya wuce kima. A tsakiyar katangar an yi wata gabjejiyar kofa ta murtukaken karfe mai tsananin kauri, sannan tana da rubi biyu wato za'a iya budeta tamkar littafi. A saman katangar kuwa cikin sararin sama wani irin jan haske ne ke kyalkyali yana fitar da wata irin farar walkiya mai ban tsoro da kuma wani irin shaudin hayaki. Kai da gani kasan cewa tsaro ne na sirrin tsafi. Gaba dayan mu sai muka yi turus kowa ya tsaya aka rasa wanda zai je kusa da kofar garin. A jikin kofar muna iya hango wani zagayayyen rami mai wasu hudoji guda biyu. Kawai sai na dubi mahaifina sarki Shaubatul Azlam na ce, "Ai sai mu karasa gaban kofar can don mu san yadda za mu budeta mu shiga." Shaibatuh Azlam ya ce "A'a ba zai yiyu ba, ke dai ki sake duba mana cikin littafin nan ko an yi bayanin yadda za'a doshi wannan gari." Ba tare da gardama ba na bude shafin da ke gaban shafikan taswirar hanya. Nan take nayi arba da zane hoton katangar Baitul Husuk a kasanta kuma aka yi bayani kamar haka: "Ya kai matafiyi ka yị sani cewa idan kana son ka kusanci wannan gari dole ne ka yanki babban danyatsanka ná hagư ya dinga digar da jini har ka je daf da kofar in ba haka ba kuwa za ka sandare ka yi matuwar tsaye. Koda gama karanta wannan bayani sai na zare wuka a jikina na yanki babban đanyatsana na hagu na nufi katangar Baitul Husuk jini na diga. Sai da na je daf da kofar garin na tsaya, sannan mahaifina ya yi yadda na yi ya biyo bayana. Daga nan sauran abokan tafiya suka kwaikwaye mu. Harta jarumi Mikdad wanda har yanzu yana cikin ragar karfe sai da aka yanki danyatsansa, sannan aka wuce da shi. Bayan kowa ya iso inda muke tsaye sai na sake bude litafin izuwa shafin gaba inda na yi arba da hoton kofar garin mai dauke da zagayayyen rami mai hodoji guda uku. A kasan kofar aka yi bayani kamar haka..... Ya kai matafiyi ka yi sani cewa idan har ana son a bude kofar nan dole ne mutum biyu wadanda suka kasance jinin sarautar birnin Kisra ne su zura yan 'yatsunsu daidai na hagu a cikin hudojin nan guda biyu. Koda gama karanta wannan jawabi sai sarki Shaubatul Azlam ya dafe kai da hannu biyu.cikin tsananin bakin ciki da damuwa. Sannan ya ce, "Ya ke 'yata ki yi sani cewa kofar nan ba za ta bude ba face sarauniya Ashikatul Ashiriya da dan uwanta Haiman sun zo sun zura 'yan yatsun su a cikin ramikan nan guda biyu. Kin ga kenan ashe duk wannan wahalar da muka sha ta zama ta banza. Koda jin haka sai jikin kowa yai sanyi aka zube kasa, aka kwanta ana bakin ciki. Sarki Shaubaul Azlam ya sake dubana ya ce, "Ya ke yata yanzu menene abin yi? Shin za mu koma da baya ne mu nemi Haiman wanda ba tabbacin cewa yanzu na raye, sannan mu nemo sarauniya Ashikatul Ashiriya don su bude mana kofar nan ko kowa za mu ci gaba da zama ne mu yi tunanin wata dabara? Yayin da na ji wannan jawabi daga mahaifina sai na ce, "Ya kai Abbana ai tunda muka zo nan babu batun komawa da baya kuma, har bukatarmu ta biya. Ka yi sani cewa an ce mai nema baya rasa motsi. Me zai hana mu yi iya kokarin mu tukun na in ya so idan muka kasa sai mu yi tunanin mafita. Cikin alamun damuwa Sarki Shaibatul Azlam ya ce, "Wane irin kokarin kuma zamu iya yi yanzu" "A sami wasu mutum biyu daga cikinmu su zura 'yanyatsunsu a cikin hodojin nan mu gani ko za'a dace." Amsar da na ba shi kenan. Koda jin haka sai gaba daya dakarun nan suka fara ja da baya cikin tsoro, suna sunkuyar da kawunansu kas. Cikin fusata sarki Shaibatul Azlam ya danko mutum biyu ya ce, "Ku aikata abin da ake so ko yanzun nan nasa a fille muku kawuna. Koda jin haka sai dakarun biyu suka tafi Izuwa gaban kofar sunan kuka jikinsu na karkarwa don tsananin tsoro, A haka dai suka daure suka zura 'yanyatsunsu cikin hudojin nan guda biyu. Faruwar haka ke da wuya aka yi Vata irin tsawa mai tsananin firgitarwa wacce ta sa kowa ya firgice aka tarwatse da gudu. Har shi kansa sarki Shaubatul Azlam sai da ya ruga ya buya a bayan wata bishiya. Sai da aka ji an daina wannan tsawar sannan aka daddawo daidai a hankali, da zuwa aka iske dakarun nan biyu da suka zura 'yanyatsun su cikin hodojin a tsaye kuma a sandare. Gaba daya jikinsu ya yi fari fat, sannan ya bushe karau. Koda aka taba su sai suka burbushe suka zama gari. Al'amarin da ya yi matukar firgita kowa kenan aka kara matsawa ya daga bakin kofar. Haka dai muka ci gaba da zama a bakin kogon Baitul Husuk har tsawon kwana bakwai muna tunanin mafita, amma ba mu samu ba. A yammacin kwana na uku ne muka ga miliyoyin mayaka sun yi mana kawanya muka rasa ta inda ka fito, har suka mamayemu haka ba tare da mun ji motsin zuwansu ba. Saboda ganin tsananin yawansu ne muka saduda kowa ya ajiye makaminsa kas. Ba zato, ba tsammani sai muka ga sarauniya Ashikatul Ashiriya tare da dan uwanta jarumi Haiman sun ratso ta cikin tsakiyar bataliyar wadannan mayaka an buda masu hanya suna tahowa garemu. Koda suka zo daf da mu sai aka fara kallan-kallo tsakanin sarauniya Ashikátul Ashiriya da sarki Shaubatu Azlam aka rasa wanda zai ce wani abu." Koda sarki Muzuluch ya zo an zancensa sai yai shiru yana mai duban su Ruziyal yana mumushi, Al'amarin da ya jefa su cikin matukar damuwa kenan, don sun san cewa ba za a ci gaba da wannan labari ba, yanzu sai dai gobe, domin lokacin tashi daga fada ya yi. Sarki Muzuluch ya ce, "To anan zan dakata sai gobe kuma idan mun wayi gari ku komo don mu ci gaba." Yana gama fadin hakan ya mike tsaye ya shiga gida. Daga nan fada ta watse aka bar su Ruziyal su kadai a zaune suna ta juyayin wannan hikaya mai ban alajabi. Tsoho Rafkanagu ya dubi Ruziyal y ce, "Wai shin kowa da wannan hikayar da ta bokany Tazibul Luhucul wacece ta fi tsawo?" Ruziyal yai murmushi ya ce, "Haba Rafkanagu yama za'a yi ka yi mini wannan tambayar, ka tuna fa cewa har yanzu muna kan labari a cikin labari ne. Ka sani cewa sai da gimbiya Suhaila ta gama baiwa kuyanga Zulaiya labarin soyayarta da sarki Mikdad, wadda cikinta muke yanzu, sannan za'a dawo kan tushen labarin; har mu ji yadda karshne gabarta da jinjirin da ta haifa za ta kasance. Karka mancewa an ce wannan jariri zai girma ya zama garemu. Tabbas na san cewa dole ne wannan hikiyar tafi hikiyar bokanya Tazibul Lucuhul tsawo. Daga wannan furuci ne suka tsai da muhawarar ta su suka tashi suka koma masaukinsu. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su tsoho Rafkanagu da sarki Muzuluch na bimin Sin, yayin da suka fara sauraron hikayar farko daga gare shi, nan gaba kuma za su saurari hikayoyi guda biyu. Al'amarin su aljani Markahul Sabus kuwa lokacin da aljani Durmazulu yai ta tsalla gudu da su a sararin samaniya sai da suka shafe sa'a hudu sannan suka sauko kan dandagaryar turbar duniyar kasa, duk da cewa fukafukansa guda.miliyan daya ne. Saukarsa ke da wuya sai ya sake bude fukafukan na sa yai sama ba can.kokoluwa ba, ya durfafi 6angaren kudu ya ci gaba da tafiya, don zuwa nahiyar nan inda za su riski babban dutsen da babu wani dutse da yafi shi girma a duniya. Cikin alamun fushi boka Jinshann ya yi tsaki, sannan ya ce, "Ya kai jama'a ya kamata mu yi kan mu fada, mu yi karatun ta nutsu. Mu tuna cewa iya tsawon rayuwarmu a cikin bincike muke na tsatsube-tsatsube, amma har yanzu ba mu gano karshen tsatsuba ba, kuma ba mu sami komai a harkar nan tun da akwai irin su Shamharu da Sarki Azmul Gallar a duniya, wadanda ko rabi rabinsu ba mu kai ba. Shin bakwa tsamman cewa a cikin wahalar banza za mu sa salwantar da rayuwarmu?" Koda jin wannan tambaya sai boka Sulbaini yai ajiyar zuciya ya ce, "Zancen yaushe kuma ai tun ran gini tun ran zane, mun riga mun bar hanyar yin nadama. Ina mai shawartarka da ka sa a ranka cewa daga yau ka bawa ba ka da aikin yi face bauta. Wata kilama idan aka ga baka da sauran amfani a hallakaka." Koda jin wannan batu sai Markahul Sabus ya kyalkyale da dariya. Lokaci guda kuma ya bushe da dariya ya ce, "Ni fa shekarata goma sha biyar a cikin akwati a kurkukun sarki Lư'umanu. Kullum ba ní da aikin yi face kuka da wakokin bégen masoyiyata Fatisa. Har sai da takadaran yaran nan su Jafar suka zo suka fitar da ni, sannan na sani kaina. Daga nan kuma na fada cikin azabar cutar son gimbiya Sima. Ina ji ina gani aka rabani da ita da karfin tsiya na zo na fada tarkon aljani Rafkanagu. Daga nan na dawo hannun Durfus yau kuma ga shi na wayi gari a hannun Shamharu. Hakika Idan na tuno da irin gwargwarmayar da na sha a rayuwata na gacewa har yanzu ban cika burina ba, na duniya sai na ji na gwammace mutuwa da rayuwata. Yanzu gashi mahaifiyata ma Samaratu na can a tsare a fadar Shamharu ban san yadda rayuwata za ta kasance ba. Ni kaina ban san makoma ta ba. To wai shin ma me ya sa Shamharu ya tsare mahaifiyata a wajensa alhalin ban isa na yi masa komai ba. Ban ga dalilin da zai sa ya yi garkuwa da ita ba a kaina. " Koda jin haka sai aljani Durfus ya bushe da dariya, sannan ya ce, "Ya kai Markahul Sabus ka yi sani cewa ni kaina ina shayinka duk da cewar na san na fika karfi, kuma na fika karfin sihiri. Dalili kuwa shi ne abu na farko ko kadan ba ka da tsoro. Kasan kuwa an ce duk wanda ba shi da tsoro zai zama gwani. Abu na biyu kana da sa'a bisa al'amura domin ka gajeta. Ga yadda na sami labarin mahaifinka Larkul Bin Sabus an ce bai taba sa wani abu ba a gabansa facc ya samu nasara. Haka kuma komai wahalar abu sai ka jarraba yinsa koda kuwa ka san cewa za ka iya rasa rayuwarka." Yayin da Durfus ya zo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya ji dadi a ransa, sannan kuma ya ji kwarin gwiwa tare da sabon karfi a jikinsa. Haka dai suka ci gaba da hira ba su gushe ba, suna yi har aljani Durmazulu ya sauko da su kasa ya dira a wani jeji mai yawan manya-manyan duwatsu. Duk iyakar yawon Markahul Sabus a duniya bai taba ganin manyan duwatsu ba irin wadannan duk da cewa kuwa ya je karshen bangwaye hudu na duniya, sa'adda ya đebo sassan kubar, Muftahul Zarbil wacce aka bude kundin satsuba da ita. Koda saukar aljani Durmazulu yazo wannan wuri sai ya ce, "To sái ku sauko ku tafi neman dutsen da yafi kowanne girma, ni kam anan aka umarce ni da tsayawa sauran aiki na gareku. MU HADU A PART K DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI 🙏💯**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA DAYA 👆 PART K 👌🥰 NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰 TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Koda saukar aljani Durmazulu yazo wannan wuri sai ya ce, "To sái ku sauko ku tafi neman dutsen da yafi kowanne girma, ni kam anan aka umarce ni da tsayawa sauran aiki na gareku. Cikin karayar zuciya Markahul Sabus, boka Jinshan, boka Sulbani da aljani Durfus suka Sauko daga kan aljani Durmazulu suka nausa cikin jeji suna masu tafiya da kafafunsu bisa turba. Tun suna waigowa su hango aljani Durmazulu har suka daina hango shi saboda nisan da suka yi. Shi dai wannan jeji da suka shigo babu kaomi a cikinsa face duwatsu iri-iri, manya da kanana wani kalar ma ko a labari ba su taba jin irin shi ba. Tun da suka fara tafiya a jejin ba su hadu da wani abu mai rai ba kai ko giftawar tsuntsu ba su gani ba. Babu tsiron bishiya ko guda daya kuma babu alamar danshi bare a samu kogi ko korama. Dajin ya yi shiru tsit ba'a jin sautin komai face sahun kafafunsu. Al'amarin da ya kara firgita su kenan, zuciyoyinSu suka cika da tsoro. Markahul Sabus ya dubi aljani Durfus ya ce, "Ya kai Durfus kai ne aljani dan uwana wai shin a iya yawon da kayi a duniya ko ka taba zuwa wuri irin wannan?" Durfus ya gyada kai ya ce, "Ai ni ko a mafarkí ma ban taba ganin daji irin wannan ba. Ai kuwa in dai hakan ne koma wane Ubangiji ne ya hallaci daji nan ya cancanci aji tsoronsa, kuma a bauta masa. Shin a tunaninka akwai Ubangijin da kake tunanin shi ne ya halicci dajin nan?" Markahul Sabus ya tamabaya. Aljani Durfus yai shiru bai ce komai ba tsawon lokaci daga bisani yai ajiyar numfashi ya ce, "A gaskiya idan har akwai wanda zai iya halittar wannan dajin ba zai wuce Ubangijin addanin su jarumi Hubairu ba, don shi ne kadai na ga yana iya yin abubuwa da suka shallake hankalina da tunanina" Koda jin wannan batu sai Markahul Sabus ya ce, "ldan har haka ne kuwa ai babu wani Ubangiji mai karfinsa, kuma me ya sa kaki imani da shi?" Aljani Durfus ya ce, "Ai idan na yi imani da shi na daina tsafi kenan, har abada. Kasan kuwa tsafi gadona ne. Iyaycna ma da kakannina tasowa na yi na ga suna yi, don haka nima ba zan

Chapter 6 of 9