Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
jin wannan batu sai aljani Zarbala ya sake bushewa da dariya, sannan kuma ya fashe da kuka. Al'amarin da ya jefa gimbiya Suhaila da shi kansa boka Hazaru cikin mamaki kenan da damuwa. Daga can sai aljani Zarbala ya ajiye gwauron numfashi ya ce, "Yake Suhaila ki yi sani cewa har abada ba za ki iya kashe wannan da da kika haifa ba muddin mahaifin shi na nan raye a duniya" Cikin hanzari Suhaila ce, mahaifinsa ya mutum a cikin tekuma aka jefa gawarsa ai. Zarbala ya sake bushewa da dariya. Sannan ya ce, "Ya ke Suhaila ki yi sani cewa bawa Mozur bai mutu ba, yanzu haka yana can nahiyar kasashen bafar fata a cikin wata kasa da ake kira Malhiya." Nan take aljani Zarbala ya bude tafin hannunsa hoton bawa Mozur ya bayyana a kai sai gashi yana aikin karfi a wani daki da ake nika kwayar dawa. A wannan lokaci fuskar Mozur ta cika da gashi, amma duk da haka sai da Suhaila ta shaida shi. Zarbala ya rufe tafin hannun ya ce, "Ki yi sani cewa mijinki sarki Mikdad yaudararki ya yi na cewar ya mutu har ya jefa shi cikin teku. A ranar da aka yi bikin bautar ubangijinku Lazzatul Sakaru ne Mikdad ya gane cewa ba kya son bawa Mozur kuma ke ce kika yi ta kokarin hallaka shi. A bisa wannan dalili ne ya goya shi a bayan dokinsa ya tafi da shi can bayan gari inda suka yi sallama suna kukan rabuwa, har ya kawo kyautar darhami mai yawa ya bashi. Bayan sun rabu ne bawa Mozur ya ci gaba da tafiya a cikin jeji, ba tare da sanin inda ya dosa ba. Hakika ya sha wahala a wannan tafiya ta sa, domin ya sha gwagwarmaya da namun daji iri-iri kuma ya yi artabu da 'yanfashi kala-kala, amma da yake yana da nisan kwana sai da ya rayu. Sai da ya shafe wata uku yana tafiya, sannan ya isa wani gari na Nasara. Anan ne aka kama shi aka sashi a cikin jirgin ruwa suka tafi da shi izuwa nahiyar kasashen fata, suka sai da shi ga sarki Kairuz na birnin Malhiya. Saboda ganin cewar Mozur kakkarfa ne, kuma lafiyayyen bawa shi ya sa aka ba shi aikin nika kwayar dawa, yana juya wata katuwar na'ura wacce sai kato talatin sun hadu, sannan za su iya juyata. Yayin da aljani Zarbala ya zo nan a zancensa, sai Suhaila ta bushe da dariya. Sannan ta ce, "Ai kuwa in dai yana wannan aikin wahalar ba zai dade ba a duniya wahala zata takashe shi." Zarbala ya ce, "Kin yi kuskure kuma inaso kima daina wannan tunani. Ina mai tabbatar miki da cewa bincikena ya nuna mini cewa nan da shekaru ashirin ma su zuwa sai bawa Mozur ya zama sarkin birnin Malhiya, kumaa lokacin ne jaririn da kika haifa zai gawurta a duniya. MU HADU A PART E DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI NA KING OF ADVENTURES STORY ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI ✍️**MIFTAHUZZARBIL**💥💥 LITTAFI NA DAYA ✍️✍️ PART E ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🫅 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🏇 TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY ✍️✍️ INA MAKU BARKA DA JUMA'A, FATAN ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRAN WANNAN RANA YA KUMA KARE MU DAGA DUKKAN SHARRI NA HALITTA.. MARUBUCIN LITTAFIN YA CI GABA DA CEWA.... Zarbala ya ce, "Kin yi kuskure kuma inaso kima daina wannan tunani. Ina mai tabbatar miki da cewa bincikena ya nuna mini cewa nan da shekaru ashirin ma su zuwa sai bawa Mozur ya zama sarkin birnin Malhiya, kumaa lokacin ne jaririn da kika haifa zai gawurta a duniya." Koda jin wannan batu sai Suhaila ta fashe da kukan bakin ciki. Ta ce, "Ya kai wannan ubangin ka taimaka mini ta kowacce hanya na kashe bawa Mozur da dan da na samu tare da shi, in ba haka ba kuwa bakin ciki zai sa na hadiyi zuciya na mutu." Zarbala ya ce, "Ya ke Suhaila ki yi sani cewa in dai kina son ki kashe bawa Mozur da dansa dole ne ki yi shiri ki tafi har can birnin Malhiya da kanki kisa a kamo shi ki farke cikinsa ki fiddo hantarsa ki tauneta ki cinye. Kina yin hakan shi ma dan nasa take zai mutu. ldan kuwa kika bari aka shekara ashirin nan gaba ba ki yi haka ba bawa, to bawa Mozur zai zo har nan kasar ya sare kanki da hannunsa." Koda Aljani Zarbala ya zo nan a zancensa, sai Suhaila ta kwarara uban ihu, sannan ta sake fashewa da kuka ta ce, "Ai kuwa indai na cika basarakıya, 'yar sarakai gaba da baya sai na je har birnin Malhiya na kama bawa Mozur na aikata masa abin da ka urmarce ni da yi. Ya kai wannan ubangiji wai shin yanzu ba za ka iya taimakona ba a yanzu na hallaka wannan jariri da na haifa tun gabanin ya girma?" Zalbala ya ce, "Ai muddin ubangijin ku Lazzatul Sakaru na nan ba zan iya yin komai ba ga jaririnki, domin shi ne yake tsaro lafiyarsa. Yake Suhaila ki yi sani cewa a duk fadin duniyar nan babu wani aljani da ya zame mini alakakai face Lazzatul Sakaru, shi ne babban abokin gabata, a wannan zamani. Na yi yaki da shi a kallah sau dubu. Duk sa'add da muka yi yakin sai mun kwana dari muna gwabzuwa. Kuma kare jini, biri jini muke yi. Bisa dole muke rabuwal Idan muka rabu sai mun kwana dari muna jinyar raunikan jikinmu. Har yau, har gobe babu wanda ya taba samun galaba akan wani. Don haka ki tashi ki tafi babu abin da zan iya yi miki face ki je ki aikata abin da na uwarce ki da yi." Aljani Zarbala na gama wannan jawabi ne ya bace bat. Ita kuwa gimbiya Suhaila sai ta mike tsaye cikin karayar zuciya ta yi sallama da boka Hazaru ta tafi. Tun da Sühaila ta baro bimin Shuruba take ta sake-saken zuci akan yadda za ta shirya gagarumar tafiya izuwa birnin Malhiya wanda ke can nahiyar bakaken fata, don riskar bawa Mozur ta kashe shi. Ba ta gushe ba tana wanna tunani har sai da ta iso gida. A lokacin ne ta riski wani abin mamaki, wanda ya girgiza ta. Ba komai ba ne ta iske ba, face gawarwakin amintättun bayin nan nata guda bakwai, wato su Shaubil jere a kwance a kofar turakarta, sarki Mikdad na tsaye a kansu ya rike kugu yana murmushi. Suhaila ta yi kamar ta juya da baya, amma sai ta dake. Sarki Mikdad ya dube ta ya ce, "Sannu da zuwa, uwar makirai ga irin aikin ki nan da yai rashin kyau." Suhaila ta yi murmushi ta ce, "Ai wannan aikin yafi gaban tunani sai dai ni na yi shi da kaina," Koda jin haka sai idanun sarki Mikdad suka ciko da kwalla ya ce, "Yake matata hakika na cuci kaina a tun farko da na so ki a zuciya ta fiye da kima, kuma har gobe ina matukar kaunarki, amma kin sa mini bakin ciki wanda har abada ba zan iya mancewa da shi ba." Koda ya zo nan a zancensa sai hawaye ya zubo daga idanunsa. Al'amarin da ya karya zuciyar gimbiya Suhaila kenan, ita ma idanunta suka ciko da kwallah ba ta san sa'ad da ta fara zub da hawaye ba. Sarki Mikdad ya wuce ya tafi abin sa ya barta nan a tsaye tun tana tsaye sai da ta durkushe kasa ta ci gaba da kuka ba sassautawa. A daidai wannan lokaci ne kuyanga Zulaiya ta zo gareta ta dafa kafadarta ta ce, "Ya shugabata ina dalilin wannan kuka naki alhalin kina kan kokarin biyan bukatarki ne?" Sulaiha ta dago kai ta dubi Zulaiya ta ce, "Yake Zulaiya ki yi sani cewa har yau, har gobe akwai tsananin soyayya tsakanina da sarki Mikdad, soyayyar da har abada tana nan a cikin jinin jikinmu da zuciyarmu ba za ta taba gushewa ba, domin in da zan baki labarin yadda muka hadu da irin gwagwarmayar da muka sha kafin mu yi aure da kin yi matukar mamaki." Koda jin wannan batu sai Zulaiya ta ce, "Ya shugabata ina mai rokonki da ki ba ni wannan labari, don ya zama abin tarihi da darasi a gareni da sauran mutanen duniya, domin za'a yi mamaki irin tsananin soyayyar da kuka yi wacce a halin yanzu kamar babu ita, tun da kun bambanta akan ra'ayi na so da kin bawa guda daya, wato Mozur." Sulaita ta share hawayenta, sannan ta fara labari kamar haka. "Ni Suhaila na taso yarinya kyakkyawa, wacce babu kamar ta a duk fadin kasar Farisa, kimanin shekaru goma sha hudu kenan da suka gabata. Mahaifina sarki Shaubatul Azlam shi ne akan karagar kasar Farisa, kuma ya mallaki dukiya, bayi da barori masu dumbin yawa wadanda bai san iyakar adadin su ba. Mahaifiyata kuwa ita ce gimbiya Ashikatul Ashiriya, 'ya ga sarki Shaubatul Iklaf na birmin Kisra. A shekarar da na cika budurwa 'yar shekara goma sha takwas sai mahaifin uwata sarki Shaubatul Iklaf ya rasu. Yayin da labari ya riski mahaifiyata sai ta kamu da tsananin bakin ciki. Cikin gaggawa ta yi shiri ta tafi birnin Kisra. Bayan ta isa can an gama bikin binne gawa, sai majalisa ta zauna ta yanke shawarar cewa an baiwa uwata sarauta tun da ita kadai ce 'ya ga sarki Shaubatul Iklaf, don haka ita ce ta dace da ta gaje shi. Ba tare da bata lokaci ba aka dorata akan karagar mulki. Sai da ta yi wata guda akan karaga, sannan ta rubuta wasika ta aikawa mahaifina, cewa ga abin da ya faru gareta, don haka idan yana ganin zai iya baro mulkinsa ya dawo Kisra, shi kenan auren su na nan ldan kuma ba zai iya ba to sai dai su hakura da juna. To dama lokacin da mahaifiyata za ta tafi Kisra da ni ta tafi, don haka ina tare da ita a wannan lokaci. Yayin da wasikar mahaifiyata ta riski mahaifina, sai ya aiko da amsa yana mai cewa; ya hakura da aurenta, amma lallai ta bashi 'yarsa wato ni. Ita kuma sai ta ce ba ta san wanna magana ba. Abu dai kamar wasa, karama magana ta zama babbar, har sarki Shaubatul Azlam ya aiko da sakon karshe cewar ya bada wata guda a kawo masa 'yarsa ko kuma ya zo da shirin yaki. Wannan batu bai sa mahaifiyata ta karaya ba, face ma dada tunzurata da ya yi, ta ce ita ma a shirye take da yin wannan yaki. Haka dai kwana talatin suka cika mahaifiyata ba ta maya da ni wajen mahaifina ba. Al'amarin da ya fusata shi kenan ainun ya yí gagarumin shiri da mayaka dubu hamsin ya zo bakin birnin Kisra ya kafa sansani. Yayin da labari ya riski ga sarki Shaabatul Azlam na can ya sauka a bayan gari da mayaka dubu hamsin. Sai ta kyalkyale da dariya ta ce, maza a tura mayaka dubu dari su murkushe su. Hakika a wannan lokaci birnin Kisra ya fi kowanne birni yawan mayaka, don haka ana shakkar yin yaki da su. Ai kuwa sa'ad da aka gwabza wannan yaki su sarki Shaubatul Azlam ba su ji da dadi ba, domin sai da aka kashe kusan dukkanin mayakan nasa shi kansa da kyar ya sarnu a tseren. Bayan Saubatul Azlam ya koma birnin Farisa sai bakin 'ciki ya taru ya masa katutu a zuciya, bisa wannan abu da matarsa ta yi masa, wato mahaifiyata. Tun daga wannan lokaci ya shiga tunanin hanyar da zai bi ya yi ramuwar gaiya, kuma ya karbi 'yarsa da karfin tsiya. Ana nan cikin wannan hali wata rana sai sarki Shaubatul Azlam ya sami labarin wani gwarzon mayaki, wanda ake kira Mikdad bin Mas'ab. Mikdad ya kasance mutum ne mai yaki da zalunci a doron kasa, kuma ya fito ne daga bimin Misra. Tun bai fi shekara ashirin ba ya taso da sadaukantaka da kwazo a filin yaki. Bisa wannan dalili ne sarkin Misira ya ja shi a jiki har ya bashi sarautar sarkin yaki. Lokacin da Mikdad ya fahimci cewa sarkin Misra azzalumi ne mai cutar da talakawansa sai suka fara takun saka. A karshe dai sarkin Misra ya shirya wani makirci, don a kashe Mikdad. Da yake yana da sauran kwana a duniya sai ya haye wannan makirci ya samu ya sulale cikin dare ya bar birnin Misa. Daga wannan rana ya fara hada rundunar mayaka ta sa ta kan shi suna yawo a duniya. Duk inda suka zo giftawa suka ga ana zalunci sai su tsaya su yi maganin azzaluman. Abu dai da kadan-kadan ya girmama ya zamana Mikdad ya zama ya hada rundunar mayaka mai yawa da karfi, wadda ta shahara ta zamo abin tsoro har ana yi musu kirari da 'Dakarun Adalci. Sa'adda sarki Shaubatul Azam ya samu labarin wannan runduna sai ya aika musu da gayyata izuwa fadarsa. Ai kuwa sai suka amsa gayyatar inda yai musu tarba ta mutunci da karramawa. A wannan lokaci ne ya kadaita da jarumi Mikdad ya ce da shi, "Ya kai wannan gwarzon jarumi ka yi sani cewa ban kira ka nan ba sai don ka yi mini adalci bisa zaluncin da tsohuwa matata sarauniyar Kisra ta yi mini." Nan dai ya zaiyane masa abin da ya faru tsakaninsa da uwata. Bayan ya gama jawabi sai Mikdad ya yi shiru yana nazarin al'amarin cikin mamaki. Daga can sai ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa hakika matarka ta yi maka butulci, bisa gudunka da ta yi don ta sami duniya, kuma a gaskiyn bai kamata ta huna ka 'yarka ba. Amman ina son idan da hali ka janye yakin nan tsakanınka da ita, ka dauki hakuri kayi sani cewa komai daren da dadewa sai 'yarka ta nemeka da kanta domin 'da' baya gudun ubansa, amma mata na iya gudun mijinta ko kuma miji ya gujewa matarsa. Koda jin wannan batu sai kwallah ta zubowa sarki Shaubatul Azlam ya ce, "Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa zuciyata na tafarfasa a duk sa'ar da na tuna wannan al'amari, don haka ba zan iya hakura ba. Zan gwamma ce a ce bana numfashi a doron kasa da dai na zauna a cikin wannan bakin ciki." Koda jin haka sai jarumi Mikdad yai shiru yana tunani, yama rasa irin hukuncin da zai yanke. Daga can sai ya mike tsaye, ya fara kai komo. Sannan ya dawo ya zauna ya fuskanci sarkı Shaubatul Azlam cikin matukar damuwa ya ce,"Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa zan iya karbo maka 'yarka' a hannun sarauniyar Kisra, amma fa za'a yi asarar dubun nan rayuka. Ni kaina dole ne na rasa mayakana da yawa, wadanda nake matukar so. Don haka ba zan iya yin wannan yaki ba" Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin dakin da suke ganawa. Cikin sauri sarki Shaubatul Azlam ya mike ya ruga gare shi ya sha gabansa ya ce, "Ya kai Mikdad ka yi sani cewa; idan har ka je wannan yaki zan biya diyar kowanne soja naka guda daya da darhami dubu dari, kuma idan har ka sami nasara zan raba kasata biyu na baka rabi ka mulketa." Yayin da jarumi Mikdad ya ji wannan batu sai ya tsaya ya kasa fita daga dakin ya ci gaba da nazarin wannan al'amari. Daga bisani sai ya yi murmushi ya ce, "Na amince." Daga wannan rana jarumi Mikdad ya ci gaba da baiwa sojojinsa horo na musamman bisa wannan gagarumin yaki da za su tafi. Sai da suka kwana arba'in suna horar da kan su, shi kuwa sarki Shaubatul Azlam na kara taimakonsa da kayan yaki masu yawan gaske. Jarumi Mikdad ya hada zuga ta mayaka dubu dari, sannan suka tafi izuwa bayan birnin Kisra, suka ya da sansani. Nan take ya rubuta wasika ya aika da ita izuwa ga mahaifiyata wato sarauniyar Kisra. Ba zan taba mantawa ba da wannan rana da aka kawo wasikar jarumi Mikdad ba. A lokacin mahaifiyata na zaune a fada an kewayeta ana zartar da harkokin mulki, ni kuwa ina žaune daf da ita. Kawai sai ga wani gwarzon jarumi sanye da tufafi na kayan karfe ya shigo cikin fadar rike da wasika. Da zuwa sai ya fadi ya kwashi gaisuwa ga sarauniya. Sannan ya bada wasikar yana mai cewa "Ya ke wannan sarauniya ki yi sani cewa ni manzo ne daga jarumi Mikdad shugaban Dakarun Adalci, don haka ga sakon nan daga gareshi." MU HADU A PART F DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI NA KING OF ADVENTURES STORY ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI ✍️**MIFTAHUZZARBIL**💥💥 LITTAFI NA DAYA ✍️✍️ PART F ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI ✍️🫅 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🏇🫲 TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY ✍️✍️ MARUBUCIN LITTAFIN YA CI GABA DA CEWA.. Ya ke wannan sarauniya ki yi sani cewa ni manzo ne daga jarumi Mikdad shugaban Dakarun Adalci, don haka ga sakon nan daga gareshi." Nan take sarauniya Ashikatul Ashiriya ta ba da umarnin a bude wasikar a karanta ta. A wannan lokaci, idan mutum ya ga yadda na kwakumi mahaifiyata ina annashuwa ya san cewa ni cikakkiyar yar shagwaba ce. Nan dai maga-takarda ya warware wasika ya fara karantawa kamar haka: Takarda daga jarumi Uban jarumai, kuma shugaban Dakarun Adalci Mikdad bin Mus'ab, zuwa ga sarauniya Ashikatul Ashiriya. Baya gaisuwar ladabi da biyayya a gareki ya wannan Sarauniya mai cikar mulki da giman kasa, ina mai sanar da ke cewa na yada sansanin mayaka na na mutum dubu dari a bayan birninki. Ina mai shawartarki da ki bani yar gimbiya Suhaila cikin ruwan sanyi don na sadata da mahaifinta, sarki Shaubatul Azlam. ldan kuwa kin ki zan yake ki da karfin tsiya na tureki daga kan karaga, sannan na kamaki kina mai kaskanta na tafi da ke izuwa ga sarki Shaubatul, don ya yanke miki hukunci bisa cin amanar da kika yi masa. Da fatan zaki dauki wannan shawara tawa, domin an ce hanyar lafiya a bita da shekara. Yayin da magatakarda ya zo nan a karatun wasika, sai sarauniya Ashikatul Ashiriya ta bushe da dariya ba kakkautawa har izuwa wani lokaci. Daga bisani kuma sai ta yi shiru tana mai murtuke fuska. Cikin tsananin fushi tasa aka rubuta martanin wasikar kamar haka. Daga sarauniyar duniya, kuma dodanniyar sarakai gimbiya Ashikatul Ashiriya zuwa ga jarumi Uban jarumai Mikdad bin Mus 'ab. Ya kai wannan dilalin mutuwa ka yi sani cewa; fada da zaki ba abin wasa ba ne, domin shi ne sarkin karfi. Ina mai sanar da kai cewa nafi gaban wulakanci kuma ni warkice daidai da kugun kowa. ldan ba ka tabu ganin kogin jini ba, to za ka ganshi, idan har ka yi kuskuren fito-na-fito da ni. Ina sanar da kai cewa wadannan yan tsakin sojoji da ka zo da su sai mutststsike su. Missing 2 Pages Mu ne mala'ikun dare, masu tarwatsa alkarya. Kuma mu ne kaifi da tsini maganin fata mai tauri." Koda jarumi Mikdad ya zo nan a zancensa, sai ya zare takobinsa ya dagata sama yai kirari da karfi yana mai cewa "Dakarun..." Su kuwa mayakan nasa suka amsa gaba daya da fadin, "Adalci...." Sai da yai wannan kira sau uku suna amsa masa, a sannan ne ya zaburi dokinsa a guje ya nufi sansanin abokan gaba. Ai kuwa sai su ma jama'ar tasa suka rufa masa baya. Yayin da dakarun Ashikatul Ashiriya suka ga su jarumi Mikdad sun taho garesu, sai suma suka yi sukuwar rubdugu suka nufe su. Ban da ihun mazaje, da karar kofutan doki da haniniyarsu ba a jin komai. Kura kuwa ta tashi a turnufe sararin samaniya. Mazaje suka ci gaba da hankoron haduwa, don kowa hannunsa radadi yake yi. Koda aka hadu a tsakiya wato aka yi karon batta, sai wuri ya hargitse aka fara sara da suka. Karar Karafiyar makamai ta cika kunnuwa. Rurin maza ya yawaita gami da haniniyar dawakai. Sai da aka yini ana yaki a wannan rana. Duk inda ka duba filin daga gawarwaki ne birjik, kamar yabanya. Jini kuwa ya zama abin ado, a kasa da jikin mutane. Hakika a wannan kowa ya gane kurensa daga mutanen jarumi Mikdad har mayakan sarauniya Ashikatul Ashiriya, domin babu bangaren da bai yi mumrnunar asara ba. A bangaren su Mikdad sai da aka kashe masa jarumai dubu talatin ya zamana saura su saba'in. A 6angaren dakarun Ashikatul Ashiriya kuwa; mutum dubi dari uku ne suka salwanta ya zamana saura dubu dari bakwai. A wannan yaki dai jarumi Mikdad da jarumi Hukashatu ne kadai ba su sami rauni ba. Bayan Hukashatu akwai wasu zaratan jarumai guda shida wadanda Mikdad ke matukar takama da su, kuma yake matukar kaunarsu. Daga cikinsu akwai; Maharaz, Ubaiyu, Sariku, Mukauzar da kuma Mukaifa. Gaba dayan wadannan jarumai sun taka muhimmiyar rawa a wannan yaki, domin su ne jigon nasarar da su Mikdad suka samu. Koda Magariba ta doso kai, sai aka buga tambarin tsaida yaki, kowacce runduna ta koma sansaninta. A sannan ne aka fara ɗebe gawarwaki, don binnewa. Su dai su Mikdad anan in da suka yi sansani suka haka kabararruka suka binne mutanensu. Su kuwa mutanen Ashikatul Ashiriya cikin gari suka tafi da gawarwakinsu. Lokacin da labari ya riski sarauniya Ashikatul Ashiriya cewar an kashe mayakanta har guda dubu dari uku, sai hankalinta ya dungunzuma, ranta yai matukar baci. Nan take ta tara dukkanin yan majalisarta da manyan zakwakuran mayakanta wadanda ake takama da su a garin a cikin fada, don tattaunawa. Sarkin yakin birnin wanda ake kira Haiman bin Kairuh ya kasance dan uwan sarauniya Ashikatul.Ashiriya na jini, domin ubansu daya. Haiman bin Kairub ya kasance gwarzon jarumi na gaske, kuma ya gaji jarumtaka a wajcn mahaifinsu ne, to amma da yake shi ma matashi ne, mai karancin shckaru shi ya sa ba'a yi masa sarautar birnin Kisira ba, sai aka baiwa 'ya'yarsa. Wato gimbiya Ashikatul Ashiriya. A wannán lokaci shekarun Haiman ba za su wuce ashirin da biyu ba, kuma ya kasance kyakkyawan saurayi mai kwarjini da cika ido. Kallo daya za ka yi masa kasan cewa ya cika jarumi. Haiman ya kasance mai matukar biyayya ga yar uwarsa kuma baya son abin da zai sosa zuciyarta ko kadan. Lokacin da sarauniya Ashikatul Ashiriya ta zauna tare da su Haiman don tattaunawa bisa wannan mugun yaki da aka fafata, kuma ya yi ba zato, sai ta dube su daya bayan daya, sannan ta ce, "Ya ku dakarun kasar Kisra ku yi sani cewa zuciyata ta tafasa karnar za ta kone bisa wannan yaki da aka yi, kuma dakaruna sun ba ni kunya. Ya za'a yi a ce mutum dubu dari kacal sun yi fada da mutum miliyan daya, kuma har su kashe mutun dubu dari uku. Shin dakarun nawa barci suke yi a filin yakin ko kuwa ba su da makamai ne? Koda jin wannan tambaya sai kunya ta kama fadawan nan gaba daya suka sunkuyar da kai kas, aka rasa wanda zai ce uffan. Daga can sai.Haiman ya dago kai ya dubi sarauniya cikin.biyayya ya ce, "Ya ke Yayata ki yi sani cewa idan za'a kwana dubu ana wannan yaki ba za mu sami nasara ba, muddin jarumi Mikdad da manyan.sadaukansa guda bakwai na tare da shi. Wadannan sadaukai bakwai sun hada da Hukashatu, Maharaz, Ubaiyu, Sariku, Mukauzar da Mukaifa. Gaba dayansu abokaina ne, sun sanni na san su, sani ba na wasa ba, kuma akwai aminci mai karfi tsakanina da su. Wannan ne ya sa na kasa fita filin daga na tare su. Ki yi sani cewa sai da na yi shekara bakwai tare da su, muna karbar horon yaki a can birnin Rum. Yake 'yar uwata ina sanar da ke cewa ni kadai ne zan iya shirin da zamu sami nasara, bisa wannan yaki amma fa bai zamo lallai ba nima na rayu a wannan yaki. Na rantse da kabarin mahaifinmu ba zan bari ba a yi miki wulakanci ba muddin ina numfashi a doron kasa. Dole ne na kare martabarki da martabar kasata da kuma martabar jama'ata. Ina mai kira a garcki da ki kwantar da hankalinki ki sani cewa gobe zan fita filin daga, kuma zan zabo zakwakuran daga cikin baradena wadanda nake ganin da su ne zan iya tunkarar su jarumi Hukashatu. Hakika in dai muka kawar da su Hukashatu mun karya lagon jarumi Mikdad, sai na kamo shi da hannuna na gurfanar da shi a gabanki." Koda jarumi Haiman ya zo nan a zancensa sai Ashikatul Ashiriya ta mike tsayc ta rungume shi cikin farin ciki. Sannan ta kama kuka

Chapter 3 of 9