daga kan ganuwa ta hau doki ta sukwane shi izuwa fadarta. Koda ganin baka sai nima na sauko daga kan ganuwar na kama doki na haye nabi bayanta da sauri.
A can filin daga kuwa maimakon Haiman ya dawo cikin gari sai ya bi Mikdad suka tafi tare izuwa sansaninsu. A lokacin ne aka fara ɗebe gawarwakin da ke zube rututu a filin yakin.
MU HADU A PART H DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI..**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA👆
PART H ❤️
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI KING 👑 OF ADVENTURES STORY 🥰
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰
TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..
A can filin daga kuwa maimakon Haiman ya dawo cikin gari sai ya bi Mikdad suka tafi tare izuwa sansaninsu. A lokacin ne aka fara ɗebe gawarwakin da ke zube rututu a filin yakin.
Lokacin da Haiman da Mikdad suka zauna a cikin tanti sai aka kawo musu ruwa suka sha, Sannan Mikdad ya dubi Haiman cikin matukar bakinciki da fushi ya ce, "Ya kai abokina menene dalilin da ya sa ka boye mini fuskarka? Shin ka manta da alkawarin da ke tsakanin mu ne?"
Haiman yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Ya kai abokina ina mai rokonka da ka yi mini afuwa bisa wannan al'amari. Ka yi sani cewa idan naki Boye fuskata a gareka ba za ka yi yakin nan ba. Na sani cewa a rayuwarka ba ka da wani buri wanda yafi ka tara dukiya mai yawa, kuma ka yi sarauta. Na san cewa ba ka amince za ka yi wannan yaki ba, har sai da sarki Shaubatul Azlam ya yi maka alkawarin wadannan abubuwa guda biyu. A matsayina na dan uwan
sarauniya Ashikatul Ashiriya dole ne na kare mutuncinta da mutuncin kasarmu, ka ga kuwa ashe dole ne na yakeka tun da ka zo ne ka ci zarafinta. Ba zan taba amincewa da irin amanar da ke tsakanina da kai ba, domin ka ceci rayuwata sau bakwai, ni kuma na ceci taka sau tara."
Koda Haiman ya zo nan a zancensa, sai Mikdad ya ciza yatsa sannan ya ce, "Me ya sa tuntunı ba ka gaya mini cewa kai dan sarauta ba ne, na birnin Kisra? Ka ga ai inda na sani ba zan zo na yaki kasar ku ba"
Haiman ya girgiza kai ya ce, "Abin da ya sa ban sanar da kai ba shi ne; a wancan lokaci na baro gida ne ba da zummar komawa ba har abada, amma da na sami labarin cewa mahaifina ya rasu sai na sulale na barku a birnin Rum ba tare da na sanar da kowa ba. Niyata shi ne na zo nan gida a nadani sarki sai na aiko a zo da kai na yi maka waziri, don na shammaceka da mamaki. Sai dai Wani akasi da aka samu shi ne kafin na iso gida tuni yayata Ashikatul Ashiriya ta baro mijinta sarki Shaubatul Azlam har ta iso an gama bikin binne mahaifinmu. Da yake dama an sanar cewa na bar gida ba da zummar dawowa ba, sai aka baiwa Ashikatul Ashiriya karaga.
Duk da cewar na yi bakin ciki da na rasa wannan karaga, amma sai na daurewa zuciyata na rungomi kaddara tun da ina matukar kaunar Ashikatul Ashiriya. Wannan shi ne labarina ya kai abokina. Shin yanzu kana da bukatar wani taimako daga gareni?" Haiman ya tambaya.
Mikdad yai ajiyar numfashi ya ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa ni yanzu duk jikina ya yi sanyi. Abu na farko na yi asarar abokaina wadanda na ke matukar kauna a zuciyata, sanadiyar wannan yaki. Haką kuma abin da na yi wannan yaki dominsa na yi asararsa tun da ba zan tafi da Suhaila ba ga sarki Shaubatul Azlam.
Shin yanzu ni menene ribata a rayuwa? Ka yi Sani cewa tun da muka rabu ni da kai a birmin Rum ba ni da wani aiki face zub dą jini a doron kasa. Ya ya zan yi da alhakin rayukan da suka rataya a wuyana?"
Koda Mikdad ya zo nan a zancensa sai ya fashe da kuka. Cikin tausayawa Haiman ya rungume shi yana mai rarrashinsa, sannan ya ce da shi, "Ya kai abokina in dai akan wannan ne ka damu to ka kwantar da hankalinka. Tun da dai abu biyu kake so kawai a rayuwarka dukiya da mulki ka same su ka gama. Kada ka yi mini tambaya bisa duk abin da ka ga na yi kai dai kawai kabi umarnina. Ina son ku yi shiri kai da mutanenka ku hada naku, ina ku ku yi gaba. Kar ku tsaya a ko'ina sai a mararrabar hanyar nan wacce ta yi iyaka tsakanin wannan birnin namu.da birnin sarki Shaubatul Azlam. Ina nufin cewa a cikin daren yau za ku tafi. Ni kuma zan riske ku a can mararrabar kafin faduwar rana. Ina tabbatar maka da cewa zan sato gimbiya Suhaila na zo muku da ita. Daga nan sai mu wuce izuwa wajen Sarki Shaubatul Azlam. Tabbas idan ya ga Suhaila tare da kai zai cika alkawarinsa na baka dukiya mai tsananin yawa a tare da mulkin rabin kasarsa. Yanzu zan tafi don na gama shirina cikin sauri don na riske ku a can mararrabar hanyar."
Koda gama fadin hakan sai Haiman ya mike da sauri ya koma cikin bimin Kisra.
Tafiyarsa ke da wuya Mikdad da jama'arsa suka karasa binne gawarwakin mutanensu, sannan suka kwashi nasu-ina-su suka yi gaba.
Lokacin da Haiman ya koma cikin birnin Kisra dare ya yi sosai. Bai tsaya ko'ina ba sai gidansa, inda ya iske matarsa Islaira zaunc akan gado tana shafa kan dansu guda daya Jabir, wanda ke barci kuma ya kasance kyakkyawan yaro dan shekara tara. Koda Islaira ta dago kai ta yi arba da Haiman sai ta rugo gare shỉ cikin tsananin farin ciki ta rungume shi tana mai cewa, "Ya kai rabin rayuwata hakika yau inda ka mutu a yakin nan ban san halin da zan shiga ba. Ka yi sani cewa sai yanzu Jabir ya samu ya yi barci, domin tun da aka gama yaki yake ta tambayata ina Abbansa yake?"
Yayin da Haiman ya ji wannan batu sai ya cire jikinsa daga na Israila, sannan ya je ya zauna akan gadon kusa da Jabir ya sumbaci kumatunsa ya shafa gashin kansa. Haiman ya dago kai ya dubi Islaira cikin alamun damuwa ya ce, "Yake matata ki yi sani cewa zama bai Same ni ba, yanzun nan zan bar kasar nan."
Koda jin haka sai hankalin Islaira ya dugunzuma take idanunta suka ciko da kwallah ta ce, "Ya kai mijina hakika na san halinka in dai ka ce za ka yi abu, sai ka yi shi babu wanda ya isa ya hanaka, amma ina son ka sanar da ni wane wuri ne za ka tafi haka wanda saboda muhimmancinsa ba za ka bari ba sai gobe da safe, ko dan Jabir ya ganka ya sami nutsuwa ai ka tsaya, tun da ga shi yanzu barci yake yi?"
Haiman yai ajiyar zuciya ya ce, "Yake Islaira idan baki manta ba kamar shekaru biyu baya na taba shiga wani dakin sirri, wanda ban san da shi ba, a cikin gidan sarautar garin nan. Dakin na nan a cikin wani gidan kasa wanda kofarsa ke karkashin karagar mulki. Babu komai a cikin wannan daki face kayayyakin tarihin sarautar kasar nan. Anan ne na ga wani littafi mai suna 'Mubudin Arzikin Kisra.' Na karance wannan littafi wanda ya kasance dan karami ne, kuma babu komai a cikinsa face taswirar hanya wacce idan mutum ya bita za ta kai shi izuwa wani kogo, inda aka boye wata dukiya mai tsananin yawa gaske. Ga yadda tarihi ya nuna dukiyar tafi shekara dubu a cikin wannan kogo, wanda aka yi wa lakabi da 'Baitul Husuk.
Ina gama karanta wannann littafi fi ne na mubudin arzikin Kisra na ji motsi a bayana. Ina waigawa na yi arba da 'yar uwata sarauniya.Ashikatul Ashiriya. Kawai sai ta taho gareni ta fisge wannan littafi da ke hannuna ta mai da shi
inda yake, sannan ta dube ni cikin fushi ta ce Ya akai ka san da wannan dakin har ka shigo shi?
Koda jin wannan tambaya sai na dube ta cikin mamaki na ce, "Ya ke 'yar uwata ki yi sani cewa bisa tsautsayi ne na gane cewa akwai daki anan karkashin karagar mulki, kuma abin ya faru ne bisa sanadiyyar wata kyanwa da ta yi mini barna a cikin gidana sa'adda na biyota a guje da nufin datse ta da takobina. Koda kyanwar ta zo gaban karagar mulki sai ta yi tsalle ta dira kan wani abu mai kama da faifai. Tana dira akan abin sai na hango matattakalar bene a cikinta. Kai tsaye na shiga ciki har na iso nan na ga wadannan tarkace anan ne na gano wannan littafi."
Koda jin haka sai sarauniya ta ce da ni, "Daga yau na haneka da kara shigowa nan domin babu mai iko da komai na gidan nan face wanda ke kan karagar mulki." Nan dai ta tusoni gaba muka fita daga cikin wannan dakin sirrin. Daga wannan rana na shiga zullumi da tunani ina mai cewa a raina yanzu duk irin kaunar da nake yiwa 'yar uwata Ashikatul Ashiriya ashe ta banza ce tun da har za ta iya boye mini sirrin dukiyar da muka gada. Shi kenan yanzu ni na tashi a tutar babu kenan. Ba ni ga tsuntsu, ba ni ga tarko, wato ba mulki ba dukiya. Ai kuwa ba za ta sabuba na ce da kaina.
Daga wannan rana na kudurce a raina cewa komai daren dadewa sai na koma cikin wannan daki na sace littafin nan mai nuna taswirar zuwa kogon Baitul Husuk. Yake matata ki Sani cewa lokaci ya yi yanzu da zan sace wannan littafi, domin na je Baitul Husuk na debo mana wannan dukiya. Idan har na yi nasara zan turo a kai ku duk inda nake, don nu karasa rayuwarmu cikin jin dadi, kwanciyar hankali da wadata."
Sa'adda Haiman ya zo nan a zancensa sai matarsa ta fashe da kuka tana mai cewa, "Ya kai mijina ka yi sani cewa idan ka tafi ka barmu za mu kasance cikin matukar kewarka, zai fi kyau ka yi wannan tafi tare da mu."
Lokacin da Haiman yaji furucin da matarsa ta yi sai ya ce, "Ki yi hakuri ya matata ba zan iya yin wannan tafiya ba da ku, domin tafiya ce mai matukar hadari ni kaina bai zamo lallai na rayu har mu isa kogon Baitul Husuk."
Ba zato, ba tsammani sai suka ji an ce, "Kwarai kuwa." Cikin firgici Haiman da Islaira suka waigo sai suka dubi bakin kofa, sai suka yi arba da ni a tsaye kuma ina rike da littafin nan na mabudin arzikin Kisra. Cikin tsananin mamaki Haiman ya tahe tareni yana mai cewa, "Ya ke Suhaila ya aka yi kika san da wannan littafi, kuma yanzu menene nufinki na dauko shi?
Kawai sai na yi murmushi na ce, "Ya kai Haiman ka yi sani cewa babu wani sirri na mahaifiyata wanda ban sani ba. Kuma duk shirye-shiryenka da burin ka na duniya babu wanda ban sani ba. Na dade ina kiwon rayuwarku kai da mahaifiyata ba dan komai ba sai don na san sirrinku, kasancewar kun boye shi a gareni. Ka sani cewa ina matukar kaunar mahaifina sarki Shaubatul Azlam, kuma nafi kaunar na zauna da shi fiye da na zauna da mahaifiyata. Dama na biyo tane kawai saboda wannan littafin domin tuntuni mahaifina ya bani labarinsa, amma ya ce bai san a inda littafinnyake baa cikin gidan sarautar nan. Ni kuma sai na ci alwashin cewa duk inda littafin yake zan nemo masa shi. Bisa haka ne ya amince mahaifiyata ta taho da ni lokacin da mahaifinku ya rasu muka shirya cewa bayan na gano in da wannan littafi yake zai aiko da mayaka a ci birnin nan da yaki, don mu dauke littafin. To kuma sai ga shi ma yakin bai kasance yadda muke zatonsa ba. Haka kuma sai na tsinci dami a kala, domin ranar da ka shiga cikin wannan daki inda wannan littafi yake, har mahaifiyata ta rutsa ka a ciki, duk na ga abin da ya faru a tsakaninku.
Yanzu dai ga wannan littafi a hannuna sai mu tafi tare da ni, da kai da su Mikdad izuwa kogon Baitul Husuk mu debo wannan dukiya, Sannan mu wuce izuwa birnin Farisa wajen mahaifina saarki Shaubatul Azlam Ka ga kai ka samu dukiyarka, shi ma kuma abokinka Mikdad zai samu tasa dukiyar da kuma sarauta. Ina son ka sani cewa yawan dukiyar da ke cikin Baitul Husuk tafi gaban tunanin mai tunani, don haka komai babakeren mutum sai dai ya debi iya dibansa ya bar saura. Don haka ka kwantar da hankalinka kada ka yi tsammanin cewa sarki Shaubatul Azlam zai rike wannan dukiya duka
ya hana ka.
Mu hadu a part I Don Jin cigaban wannan Kayataccen Labari 🙏**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA 👆
PART I 💕
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰
TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..
Don haka ka kwantar da hankalinka kada ka yi tsammanin cewa sarki Shaubatul Azlam zai rike wannan dukiya duka
ya hana ka.
Sa'adda na zo nan a zancena sai Haiman yai shiru yana tunani. Abu na farko dai yafi son a ce shi kadai zai mallaki wannan dukiya ya zamana matarsa da dansa sun gajeta ko a bayan ransa. Yanzu idan ya kwace wannan littafi daga hannuna ya tafi kogon Baitul Husuk shi kadai ai ya ci amanar abokinsa Mikdad. Bayan ya yi dan dogon nazari sai ya dube ni ya yi murmushi. Sannan ya ce ya amince mu tafi tare.
Nan take ya yi sallama da Islaira muka fice muka barta tana ta kuka. Abin da ba zan taba mantawa ba shi ne wani irin kallo da na ga Haiman ya yi wa dansa Jabir wanda ke kwance a kan gado yana barci. Kallo ne mai cike da tsananin kauna da tausayi, wanda ka iya karya Zuciyar kowanne irin mutum. Ni kaina sai da na yi kwallah saboda sanin irin kaunar da ke tsananin da da mahaifi ta wuce tunanin mai tunani. Ga shi yana ji, kiri-kiri zai tafi ya barshi tafiyar da ba shi da tabbacin dawowa har su
sake saduwa.
Nan dai muka sulale muka bar cikin birnin Kisra, ni da Haiman muka nufi mararrabar hanya inda aka yi alkawarin haduwa da su jarumi Mikdad. Abin da Haiman bai sani ba shi ne tun a jiya na aiki manzo izuwa birnin Farisa don ya sanar da sarki Shaubatul Alzam cewa ya shirya dakarun yaki masu karfi su riskemu a hanyar da za'a bi a tafi kogon Baitul Husuk, kuma ya tabbatar cewa mayakansa sun yi kwanton bauna yadda za'a gama da su Haiman a cikin kankanin lokaci.
Al'amarin sarauniya Ashikatul Ashiriya kuwa, ba ta farga da duk abin da ke faruwa ba, sai da gari ya waye rana ta kwale. Sannan ta rude saboda rashin ganin 'Yarta Suhaila da jarumi Haiman. Cikin gaggawa ta shiga cikin dakin nan inda littafin nan na mabadun arzikin Kisra yake.
Koda ta shiga ta ga babu littafin, sai ta fito da gudu tana mai kwalawa 'yan majalisarta kira. Nan take aka je aka kirawo su, suká taru gabanta. Ashikatul Ashiriya ta dube su cikin tsananin damuwa ta ce, "Ya ku ginshikin Kisra ku yi sani cewa jarumi Haiman ya ci amanarmu ya sace littafin nan na mubudin arzikin Kisra, kuma ya sace 'yata Gimbiya Suhaila tun a daren jiya ya gudu. Yanzu menene abin yi?
Koda jin haka sai 'yan majalisar suka rude hankalinsu ya dungunzuma. Nan fa aka tunanin al'amari aka shiga tattaunawa. Daga bisani aka yanke shawarar a hada rundunar mayaka abi bayan su Haiman. Ai kuwa nan da nan cikin sauri aka shiga shiri sai da aka hada dakaru miliyan goma, sannan aka dunguma gaba daya aka tafi kogon Baitul Husuk. Sarauniya Ashikatul Ashiriya ce da kanta ta jagoranci wannan tafiya.
Lokacin da ni da Haiman muka isa mararrabar hanya, inda su jarumi Mikdad suka tsaya, don jiranmu sai muka iske su tuni sun kafa tantuna suna hutawa. Koda suka ganmu sai suka cika da murna, amma abin da ya baiwa Mikdad mamaki shi ne ganin yadda Haiman ya zo da ni, a saukake ba'a daure ba, kuma cikin kwanciyar hankali. Nan dai Mikdad ya bukaci su gana shi da Haiman ni kuma sai na dube su na ce.
"Ya ku wadannan jarumai ku yi sani cewa zaman mu anan na da matukar hadari, domin tabbas na san sai ta biyo bayanmu. Ban hanaku tattaunawa ba, amma ku yi zançen ku yayin da muke kan hanyarmu ta zuwa kogon Baitul Husuk."
Ba tare da wata gardama ba kuwa. Su Mikdad suka amince da wannan shawara. Nan da nan suka kwashe kayansu aka hau dawakai suka zaburi dawakansu da gudu, suka nausa jeji. Sai da suka yi nisa, sannan suka fara tafiya a hankali. Tsawon lokaci babu wanda ya ce kala. Babu abin da ya baiwa Haiman mamaki face ganin yadda hankalin Mikdad ya tattara akan gimbiya Suhaila, domin yana yawan satar kallonta. Haka dai aka ci gaba da tafiya ba tare da an tsaya ba, har sai da aka zo bakin wata korama wacce ruwa ke gudu a cikinta.
Anan aka sauko aka sha ruwa, suma dawakan suka jika makoshinsu, a sannan ne Haiman da Mikdad suka kebe gefe guda.
Haiman ya dubi Mikdad ya ce, "Ya kai abokina shin ka taôa jin labarin kogon Baitul Husuk?"
Mikdad ya ce, "Kwarai kuwa na ji an ce a nan ne wani boka ya boye dukiyar birnin Kisra gaba dayanta a wani zamani mai tsawo da ya shude, kuma an ce kogon Baitul Husuk yana da matukar girma har ma yafi birmin Kisra."
Haiman ya ce, "Wannan bayani haka yake, to ka sani cewa a halin yanzu muna tare da wani littafi wanda ke daukeda taswirar zuwa kogon da kuma sirin yadda za'a shige a debo dukiyar."
Koda jin wannan batu sai Mikdad ya rude ya ce, "Ina littafin yake?"
Haiman ya yi murmushi ya ce, "Yana tare da macen da kake matukar kauna a zuciyaka, wadda begenta ke neman zautar da kai."
Koda jin haka sai mamaki ya kama Mikdad ya ce, "Ya kai abokina ya aka yi ka sa cewa ina son gimbiya Suhaila?"
Haiman ya yi dariya ya ce, "Ai an ca labarin zuciya a tambayi fuska. Hakika na kula da irin kallon da kake yi mata ne tun da muka fara wannan tafiya. Me ya sa ba za ka gaya mata abin da ke ranka dangane da ita ba?"
Mikdad ya yi murmushi ya ce, "Ina ni ina yar sarakai alhalin na kasance dan takalawa. Bana zaton cewa Suhaila ma za ta soni,"
Haiman ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na san cewa Suhaila miskila ce, kuma mazari ce, amman ai babu wanda ya san inda ta sa gabanta, ka yi sani cewa babu wata 'ya mace da za ta samu namiji kamarka ta kishi, domin ka kasance kyakkyawa, kuma gaka sadauki mai dakawa maza gumbar wahala."
Mikidad yai murmushi sannan ya ce "Yanzu dai mu koma ga batun kogon Baitul Husuk. Shin yanzu kana nufin cewa can za mu je?
Haiman ya ce, "Ko shakka babu can za mu je, kurna ka yi sani cewa daga nan zuwa inda zamu dau hanya tafiya ce ta kwanaki bakwa kacal. lnda za mu dau hanyar kuwa wani wuri ne da ake kira Hajiril Asmal. Babu komai a Hajiril Asmal face wasu irin manya-manyan tsaunika tare da dogayen duwatsu iri-iri. Dole sai mun bi ta kan wadannan duwatsu sannan za mu je hanyar da za ta kai mu ga kogon Baitul Husuk. Ka yi sani cewa tafiya akan wadannan duwatsu ba karamin hadari gareta ba, saboda tsakanin tsawonsu da kuma kwazazzabon da ke karkashin su, ina tabbatar maka da cewa dawakai ba za su iya hawa kan wadanan duwatsu ba da tsaunika, sai dai mu hau da kafafunmu, sai mun yi tafiyar sa'a uku akan duwatsun sannan mu kai ga makurarsu mu sauka kan turba. To daga nan ne fa za mu
lalubı hanyar zuwa kogon Baitul Husuk."
Koda Haiman ya zo nan a zancensa sai Mikdad ya ce, Yanzu kai dakata haka da wannan bayani. Wai shin me zai hana idan mun sami nasarar shiga Baitul Husuk mun debo wannan dukiya mu yi sallama anan na debi iya rabona kai ma haka, sannan ka bani gimbiya Suhaila na tafi da ita ta zama abokiyar rayuwata?"
Koda jin haka sai Hạiman ya bushe da dariya sannan ya ce, "Idan har mun sami nasarar na yi alkawari zan yi maka hakan."
Anan dai suka daina zancen haka, kowa ya tashi ya hau dokinsa aka ci gabà da tafiya. Tafi sannu-sannu har kwanaki bakwai suka shude, muka iso Hajaril Asmal. Inda manyan tsaunikan nan suke tare da dogayen duwatsu iri-iri.
A tsawon kwanakin nan bakwai ni da Mikdad babu wanda ya ce da wani kala. Tsakanina da shi sai kallan-kallo, kuma duk sa'adda muka hada ido sai na ga yana yi mini wani irin murmushi, mai dauke da alamar tambaya. Dole na tsargu cewar lalai Mikdad na sona.
Lokacin da muka isa Hajiril Asmal sai kowa ya daga kai sama, yana kallon wannan duwatsun da ke wajen cikin tsananin mamaki. Wasu duwatsun sai ka gansu a fiffike, tamkar wuka aka fere su, wasu kuma sai ka gan su fadada kamar allon jiragen ruwa, Ni kaina da na karewa duwatsun kallo sai na ce, yabo ya cancanta ga ubangijin da ya halicci wadannan duwatsu. Da yake duwatsun akan wasu tsaunika suke, su kuma tsaunukan masu saukin hawa ne sai ba mu samu wata matsala ba. Anan kasan tsaunukan muka daure dawakanmu. Ni, Haiman, Mikdad da kuma dakarun Mikdad su dubu goma daya muka haye kan tsaunin farko, sunnan muka hau kan dutsen da ke kansa muka fara tafiya. A wannan lokaci idan mutum ya leko kasa, sai ya ga kamar a can sararin samaniya yake, domin dawakanmu sun zama 'yan mini-mini, kamar tururuwai. Alamarin da ya razana kowa kenan, domin duk wanda ya subuto ya fado kasa bisa ga tsautsayi to sunansa gawa.
Tun sa'adda muka zo Hajaril Asmal na ware idanu na ga ta inda mutanen sarki Shaubatul Azlam za su afko mana, amma ko alamar su ban gani ba. Al'amarin da ya tayar mini da hankali kenan domin na tabbatar da cewa in dai muka shiga cikin kogon, muka debo dukiyar ba tare da mayakan sarki Shaubatul Azlam sun riske mu ba, shi kenan har abada Haiman da Mikdad sun tsira da dukiyar. Ni kuwa burina shi ne kada kowa ya mallaki wannan dukiya face mahaifina sarki Shaubatul Azlam.
Wani babban abin tashin hankali shi ne lokacin da muka fara nisa akan duwatsun nan sai duwatsun suka fara daddarewa. Nan fa mutane suka rinka ruftawa suna fadawa can kasan su inda narkakken dutse ke tafasa. Da zarar mutum ya fada cikin narkakken dutsen sai ka ji wata irin kara cuss.....Kamar an zuba ruwa a cikin tafasasshen mai. Nan fa hankalinmu ya dugunzuma, kowa ya tsaya cak a waje guda domin ana tsoron inda za'a taka gaba ya zamana
wajen bai rufta ba.
Tsawon 'yan dakiku kowa ya ki yadda ya.ci gaba da tafiya. Daga can sai wani daga cikin dakarun Mikdad yai tawaye yana mai cewa, "Gaskiya mu dai ba za mu ci gaba da wannan tafiya ba, komawa za mu yi da baya. Wannan fa shine balai ne na farko tun kafin mu je inda za muga hanyar zuwa kogon Baitul Husuk. Wane ne yasan sauran masifun da ke cikin Baitul Husuk din?"
Koda jin wannan batu, sai wasu ma da cikin dakarun suka goyi bayan mai magana. Nan take wajen mutum dari suka juya da baya da niyar komawa inda muka baro dawakaansu.
Ai kuwa suna taka sawayensu ta ku daya duwatsun suka tsatstsage suka rufta da su cikin narkakken dutsen nan suka nutse ciki, dayansu bai tsira ba. Al'amarin da ya sake jefa tsoro a zukatanmu kenan gaba daya kowa ya aiyana a ransa cewa ya kawo kansa gida mutuwa.
Nan fa aka yi duru-duru ana kallan juna zuciyoyi na bugawa da karfi cikin tsananin tsoro. Haiman ya dube ni sannan ya dubi Mikdad ya ce, "Ku yi sani cewa mun riga mu shigo cikin bala'i don haka tsoro ba na mu ba ne, sannan tsayuwa anan ba za ta fishshe mu ba, dole ne mu ci gaba da tafiya."
Koda fadin haka sai na ce da Haiman,