iya bin ta da dai na ci gaba da shan irin wannan wahalar banzar"
Koda jin haka sai boka Sulbaini ya dakawa Markahul Sabus tsawa ya ce," Wacce irin magana banza ka ke yi ne haka? In da Ubangijin Hubairu na da ikon fitar da mutu daga cikin bala'i me ya sa tun farko Hubairu bai samu sa'a ba akan sarki Lu'umanu sa'adda ya raba shi da gimbiya Sima? Ca nake tare da kai muka ga abin da ya faru a tsakanin su a madubin tsafi sa'adda muka shiga fadar Shamharu da ke tsiburin Bahar Zus."
Kafin Markahul SAbus ya kara cewa wani abu saí suka ga wadansu irin dodanni gansama-gansama sun kewayesu.
Dodannin sun kasance duk jikinsu na dutse ne. Suna da matukar tsawo da fadi, domin tsawon su aljani Markahul Sabus ya zo iya gwiwar kafafunsu ne. Idanun dodannin ya kasance abin tsoro domin jajawur ne, wuta na huruwa a cikinsa. Idan suka wangamne bakunansu ma ba'a ganin komai a ciki face wata gagarumar wuta mai tsananin zafi. ldan kuwa suka zazzagi da hurshensu Sai ka ga wuta na zubowa kasa, kamar za ta kone dajin gaba daya.
Nan fa su Markahul Sabus suka tsure, jikinsu ya kama kyarma, kuma ga shi babu damar gudu. Nan take daya daga cikin dodanin ya sa yanyatsunsa biyu sai ya sure su Markahul Sabus su duka. Sannan ya dora su a kan dayan tafin hannunsa, Nan fa suka ga kamar an dora Su ne akan katon tsauni. Koda suka leko kasa sai suka ga cewa manyan duwatsun nan na dajin gaba daya sun zama yan mini-mini, tamkar yantsaki a gaban shanu. Wannan dodo da ya dauki su Markahul Sabus ya dubi yan uwansa ya ce "Kun ga wadansu irin halitu dana tsinta.
Yanzu me ya kamata na yi da su, na lankwame sune, ko kuwa na kai su gidana na ajiye a cikin keji don su rinka dcbewa 'ya'yana kewa?"
Koda jin haka sai Babban cikinsu ya daka masa isawa ya ce, "Ashe ka manta da dokar Sarki kenan? Ai cewa ya yi duk ranar da muka tsinci wani bakon abu mu kai masa shi."
Maitsuntuwar ya ce, "Af! Haka ne fa ai na sha'afa ne ka gafarce ni ya kai sarkin dogarai."
Gama rufe bakinsa ke da wuya suka juya da baya suka nufi yammacin dajin dauke da su Markahul Sabus bisa tafin hannu. Sai da suka yi tafiyar sa'a guda, sannan suka shigo cikin wata babbar alkarya mai manya-manyan gidaje wadanda aka yi su da zallan tubalin kasa. Jama'ar garin gaba daya irin wadannan dodannin ne masu jikin duwatsu. Mazansu da matansu, yara da manya haka suke sai harkokin gaban suke yi.
Koda suka kyailara ido suka hango su Markahul Sabus sai suka cika da mamaki, domin ba su taba ganin halittar ba. Nan fa aka biyo wadanda ke đauke da su du! Kamar ana bin mahaukaci a kasuwa. Nan fa aka ci gaba da tafiya sai da aka iso wata babbar fada, wadda itama da tubalin kasa aka yi ta; amma komai na adon cikinta da duwatsu aka yi shi. Zaune a katuwar wata kujera sarkin wadannan dodanni ne tare da matarsa a gefe. Koda shigowar dubun nan jama'a cikin fadar sai sarkin ya mike tsaye a fusace ya daka tsawa mai kama da saukar aradu ya ce, "Lafiya me ya faru aka shigo mini fada haka?"
Koda jin wannan tambaya 'sai kowa a zube kasa gabansa. Wanda ke dauke da su Markahul Sabus ya đan dago da kai yana mai nunawa sarki su ya ce, "Ya shugabana ga bakon abin da muka tsinta shi ya sa ka ga jama'a sun biyo mu haka suna kallon abin mamaki."
Cikin tsananin mamaki sarki ya mike tsaye sai ga shi kansa ya kusan tabo saman ginin fadar. Ya tako a hankali cikin irin tafiyar kasaita ya zo ya bude tafin hanunsa aka zuba su Markahul Sabus a kai ya kura musu idanu. Sai da ya gama nazarinsu sannam ya ce, "Ku kuma su waye daga ina kuka zo?"
Caraf sai Markahul Sabus yai gyaran murya ya ce, "Ya shugabana ka yi sani wa mnu baki ne, kuma mun zo ne daga duniyar bil'adama. Ba komai ba ne ya kawo mu nan ba face neman dutsen da yafi kowannne dutse girma a cikin duniyar nan, domin mu đebo wani abu daga cikinsa."
Koda jin wannan batu sai sarkin dodanni ya kwalla ihu wanda ya haddasa girgizarfadar gaba daya, kamar za ta rushe. Cikin tsananin fushi yai watsi da su Markahul Sabus a jikin bango duk suka fado kasa sumammu. Sai bayån da suka farfado ne ya dube su ya ce, "Ku wadanne irin shashashai ne, kuma mahaukata. Hakika Inda kusan masifar da ke tattare da babban dutse da ba ku nemi a kai ku kusa da shi ba. Ku yi sani cewa duk shekara wannan dutse yana ambaliya ya shigo mana nan. Idan ya shigo sai ya nike gidajenmu da mu kan mu. A kallah akan rasa rayuwa guda miliyan dari. Kusan ko yaushe wannan babban -dutse yana bindiga ne yana fashewa da tarwatsewa. Babu wani abu da ya isa ya doshe shi ba tare da ya nike ya zama gari ba.
Ya ku wadannan baki ku yì säni cewa yau saura kwana bakwai babban dutse ya yi ambaliya ya shigo mana. Wata kila rabon ku muta ne ku ka zo. Kun ga ma yanzu shi kenan ba sai kun yi wahalar zuwa can inda ya ke ba. In kuka saurara nan da kwana bakwai zai zo har nan ya riske ku."
Koda jin wannan batu sai hankalin su Markahul Sabus ya dungunzuma, suka rasa abin da ke musu dadi. Markahul Sabus ya dubi abokan tafiyarsa wato su Durfus ya ce, " Amma a gaskiya Shamharu ya raina mana hankali, domin ya za ai ya turo mu diban abin da ya san cewa ba a isa aje kusa da shi ba. Kuma ma inda abin zai debu me ya sa shi bai zo da kansa ya diba ba. Kawai dai yana son ya hallaka mu ne."
Koda jin haka sai Durfus ya ce, Wato ban da abin ka idan so yake ya hallaka mu ai take zai iya hallaka mu da naushi daya tak. Ni dai ina ganin cewa akwai dai dalilin da ya sa ya aiko mu din, "
Sarkin dodanni ya dubi sarkin dogarai ya ce "Kwashe wadannan bakin ka tafi da su gidanka ka tattauna da su, idan suna da wata hikima da za su iya yi mana maganin ambaliyar dutse su gaya maka ka zo ka shaida mini kafin nan da cikar kwana bakwai. ldan kuma ba su da ita ka lankwame su kawai mu huta da takaicin surutansu na banza,"
Sarkin dogarai ya ce, "An gama ya shugabana."
Nan take ya suri su Markahul Sabus su hudun ya fice da su daga cikin fadar.
Bayan 'yar gajeriyar tafiya nc, sarkin dogarai ya iso gidansa. Da zuwa ya iske matarsa da kuma 'yarsa wata karamar yarinya wacce ba ta fi shekara dubu arba'in ba a duniya. Su dai wadannan dodannin suna dadewa a duniya, don ana sanun masu shekara dubu đari biyu a cikinsu har ma dubi dari biyu da hamsin. Sunan wannan yarinyar yar sarkin dogarai Salusa. Salusa ta kasance mai kaifin basira, sannan kuma duk garin babu mai kankantar halittarta domin gaba daya girmanta bai wuce na aljani Markahul Sabus ba.
Lokacin da sarkin dogarai ya shigo cikin gidansa dauke da su Markahul Sabus, Salusa ta yi arba da su sai ta cika da farin ciki, domin dama labari ya risketa cewa ga mahaifinta can ya samo wadansu irin kananan halittu ya tafi dasu fada. A lokacin ta so ta je fadar đon ta ganewa idaunta, amma sai mahaifiyarta Arzula ta hana ta fitar. Har sai da Salusa ta yi kukan bakin ciki akan hakan.
Da shigowar sarkin dogarai sai ya bude wani keji wanda aka yi shi da wasu gunguma-gunguman duwatsu ya jefa su Markahul Sabus a ciki, tamkar an jefa su cikin wawakeken rami. Sannan ya rufe kejin. Arzula da Salusa suka matso gaban kejin suka kurawa su Markahul Sabus idanu. Salusa ta rinka kallonsu tana yì musu murmushi da dariya, ita kuwa Azula sai ta murtuke fuska ta ce, "Ya kai mijina me za ka yi da wadannan abubuwa ka zuba su a cikin keji haka?"
Sarkin dogarai ya ce, "Sarki ne ya ce na kawo su na ajiyc, domin su fadi hanyar da za'a bi a magance matsalar ambaliyar babban dutse kafin nan kafin kwana bakwai. Idan kuma ba su fada ba na lankwame su.
Koda jin wannan batu sai Arzula ta bushe da dariyar keta ta ce, "Haba wane su, wane wannan tunani. Ai tabbas sunansu lankwamammu, nan da kwana bakwai."
Ita kuwa Salusa sai ranta ya baci da taji cewar cinye su za'a yi nan da kwana bakwai.
Arzula da maigidanta suka tashi suka shiga cikin daki suka bar Salusa ita da kadai a gaban kejin da Markahul Sabus suke ciki Cikin yanayin tausayi ta dube su daya bayan daya, ta ce Ya ku wadannan halittu shin za ku iya tunanin hanyar da za'a bi a magance matsalar ambaliyar babban dutse?"
Gaba daayansu suka yi shiru aka tasa wanda zai ce wani abu. Daga can kuma sai Marhakhul Sabus ya dubc ta ya ce, "Ya ke wannan mai jin kai ki yi sani cewa ba za mu iya.yin komai ba danganc da matsalar ambaliyar dutse. Ki yi sani cewa mu ma nan an turo mu ne izuwa wannan duniyar ta ku, don mu debu narkakken babban dutse."
Koda jin wannan batu, sai Salusa ta rike baki cikin alamun mamaki, sannan ta ce, Ai kuwa an hadaku da aikin da ba za ku ya ba. Wanene wannan wanda ya turu ku dibar narkakken dutse?
Markahul Sabus ya ce, Wani shaidani ne da ake kira boka Shamharu."
Salusa ta zare idanu ta ce, "Me ka ce?"
Markahul Sabus ya kara maimaita sunan Shamharu, Salusa ta yi shiru tana tunani. Daga bisani sai ta dubi Markahul Sabus ta ce, "Kimanin shekaru uku da suka wuce na taba jin wannan sunan a bakin wadansu kananan halittu, wadanda suka zo kasar nan a cikin wani katon sunduki. Sundukin ya ratso ne ta cikin karfashin kasa a lokaci ni kadai ce a bayan gari ina farautar abin da zan ci. Koda na ji kasa na
girgiza sai na tsorata na koma bayan wani dutse na buya nesa kadan da inda na ga kasar na gingiza. Ai kuwa ba'a jima ba sai na ga wani katon sunduki ya burtso ta cikin karkashin kasa.
Koda ya tsaya cak sai na hango wasu halittu guda goma a cikinsa. Halittun irin su daya ne da kai. Nan take suka budc wata kofa da ke jikın sundukin suna dauke da wasu kayayyaki suka nufi hanyar da za ta kai ga inda babban dutse yake, Ni dai ina nan a labe ban fito ba, har darc ya soma banga halitun nan sun dawo ba. Kawai sai na je na tone kasa na mai da wannan sunduki ciki na binne. Har yau ban sake komawa can ba, kuma ban sake ganin wadannan halittu ba."
MU HADU A PART L DOMIN JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI 🙏💯**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA 👆❤️
PART L ❤️🥰
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰
TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Har yau ban sake komawa can ba, kuma ban sake ganin wadannan halittu ba."
Yayin da Salusa ta zo nan a zancenta, sai Markahul Sabus ya dubi su boka Durfus ya ce, "Me kuka fahimta dangane da wannan bayani?"
Gaba dayansu suka yi shiru. Durfus ne ya ce, "Ba mu fahimci komai ba."
Markahui Sabus ya ce, "Ni kuwa abin da na fahimta shi ne; Samharu ya taba turo hadimansa nan garin don su debo masa wannan narkakken dutse, kuma sun hallaka ba su sami nasara ba. "
Koda jin haka sai boka Jinshan ya ce, "Kwarai kuwa nima na fahimci hakan, yanzu da ka yi wannan bayani."
Durfus ya yi tsaki ya ce, "Gafara can sai da ka ji Markahul Sabas ya gama jawabi, sannan ta ka ce kaima ka fahimta. Ku fa bi'adama wani lokacin kun fiya shirme."
Markahul Sabus ya dubi Salusa ya ce, "Ya ke kawata yanzu ya za'a yi ki kaimu inda kika binne wannan sunduki?"
Salusa ta yi shiru ta daga kanta tana tunani. Daga bisani ta ce, "A gaskiya ba ni da tabbacin cewa zan iya gane daidai inda na binnc shi, amma ance mai ncma yana tare da samu, babu mamaki na gano wajen idan muka je muka duba. To amma, in ban da abin kuma ku da kuke cikin ke ji ya za'a yi na wajen da ku?"
Markahul Sabus ya ce, "Shin za ki iya fitar da mu daga cikin kejin nan mu sulale mu gudu tare da ke, don ki kai mu wajen da sundukin yake?"
Salusa ta ce, "Eh.....Abin dai kamar da wuya, don na san cewa iyayena za su sa saka idanu akan ku, to amma zan iya jarrabawa bisa sharadi guda"
Cikin hanzari Markahul Sabus ya ce Menene sharadin?"
"In dai na kubutar da ku zan bi ku mu je inda za ku koda kuwa can duniyar ta ku zaku koma. Ina son ku yì mini wannan alkawarin."
Koda jin wannan batu sai su Markahul Sabus suka dubi junansu suka yi shiru. Kawai sai Markahul Sabus ya ce, "Na yi miki wannan alkawari za mu tafi da ke."
Yana gama rufe bakinsa kenan, sarkin dogarai da Arzula suka fito daga cikin daki.
Arzula ta dakawa Salusa tsawa ta ce, "Me kike yi ne a wajen wannan kananan halittun? Maza ki bar wajen su ko kuma jikinki ya yi tsami."
Cikin tsoro da hanzari Salusa ta ruga cikin dakinta ta bar su Markahul Sabus.
Daga wannan rana Salusa ta zama abokiyar hirar su Markahul Sabus ya zamana tana debe musu kewa, amma sai ta ga cewa iyayenta ba sa kusa. Sai da aka kwana biyar tana fakon iyayenta don ta fito da su Markahul Sabus daga cikin kejin nan, amma ba ta sami dama ba. A kwana na shida ne da yamma likis ta ta samu damar, wato ana i gobe za a yi ambaliyar dutse kuma a ranar ne sarkin dogarai ya kudurce a
ransa cewa yana dawowa daga fada zai lankwame su Markahul Sabus.
Sa'ar da aka yi ita ce; a ranar Arzula tabi sarkin dogarai zuwa fada da yamma. Fitarsu ke da wuya sai Salusa ta bude kejin nan su Markahul Sabus suka fito. Nan take ta zuba su a cikin wata jaka, sannan ta dauki jakar ta fice daga gidan. Koda ta fita sai ta ruga da gudu ta nufi bayan gari. Haka dai ta yi ta gudu ba kakkautawa har ta iso wajen da take zaton anan ne ta binne sunduki. Nan fa ta hau tonon kasa a wuri-wuri har waje dari, amma ba ta ga alamar sunduki ba. Al'amarin da ya tayar mata da hankali kenan ta koma gefe guda ta zauna tana haki saboda gajiya. Sannan ta bude jakar nan da tasa su Markahul Sabus a ciki ta fito da Gaba dayansu sun jike sharfak da gumi tamkar a ruwa aka tsoma su, saboda zafin cikin jakar. Salusa ta dubi Markahul Sabus ta ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa nan ne inda nake zaton na binne sundukin nan, amma kuma ga shi na yi iyakar nema ban gani ba. Abin da nake tsoro shi ne idan iyayena suka dawo daga fada
ba su gan ku ba za su fito nemanmu kuma in dai suka riske mu ta ku ta kare."
Koda jin wannan batu sai Durfus, Jinshan Sulabaini suka tsure, hankalinsu ya tashi. Shi kuwa Markahul Sabus bai damu ba, sai ma ya dubi Salusa ya ce, "Haba kawata ki dai sake tunani da kyau. Lallai ina ganin cewa ba anan ba ne, kika binne sundukin nan."
Koda jin haka sai Salusa ta yi shiru ta shiga sabon tunani. Daga can sai ta yi murmushi ta kama hannun Markahul Sabus ta ja shi da gudu suka nufi wani 6angare dabam. Cikin sauri su Durfus suka rufa musu baya. Salusa ba ta tsaya a ko'ina ba sai da ta zo wani katon fili mai
tarin duwatsu. Da zuwa ta fara tone-tone a cikin kasa. Koda ta tona rami na uku sai ga sundukin a ciki. Cikin sauri su Markahul Sabùs suka taimaka mata aka tone wajen sosai.
Sundukin ya bayyana a fili karara. Koda ganin Sundukin sai mamaki ya cika su Markahul Sabus, suka tsaya suna kallonsa kawai.
Ana cikin haka ne Salusa ta ji alamun tafiya daga can nesa, don haka sai ta fargar da su Markahul Sabus çewa ga iyayenta can tafe sun taho nemansu. Cikin sauri Markahul Sabus ya bada shawarar a binne ramukan nan da aka tone. Haka kuwa aka yi, sannan suka bude sundukin nan suka shiga cikinsa suka zauna har ita kanta Salusa. Bayan an rufe kofar sundukin ne sai Markahul Sabus ya karewa sundukin kallo yai nazarinsa. Daga can gaban sundukin ne ya ga wadansu ramuka guda uku. A cikin kowanne rami akwai wani sirrin tsinken tsafi. Tsinken farko ja ne, na biyu kuwa fari ne, na uku kuma baki ne.
Markahul Sabus ya je gaban tsinkayen nan ya tsaya, sannan ya waigo ya dubi abokan tafiyarsa ya ce, "To ku shirya zan yi karambani. Idan muka yi sa'a sai mu tsira. Idan kuma ba mu yi ba gaba dayanmu za mu hallaka."
Su Durfus sai suka yi shiru ba su ce komai ba. Ita kuwa Salusa sai ta ce, "Ai gwararma mu hallaka da dai iyayena su zo nan su riske mu, domin su ma hallaka mun za su yi."
Salusa na gama rufe baki Markahul Sabus ya ja jan tsinken tsafin nan baya kadan. Nan take wani irin haske ya baibaye sundukin gami da wata irin gagarumar iska. Take sundukin ya nutse can cikin karkashin kasa, yana mai tsala azabben gudu. Sai da ya yi 'yar doguwar tafiya a can karkashin kasa sannan ya tsaya cak. A daidai wannan lokaci ne iyayen Salus suka zo wajen suna dube-dube. Koda suka ga dogon rami.zururu ba karshe a cikin kasa sai suka tsora suka.juya da baya suna masu fal fala gudu. Wannan rami da suka gani ba komai ba ne face hanyar da sundukin tsafi ya samarwa kansa, wanda su Markahul Sabus suka shiga.
Sai da su Markahul Sabus suka kwana biyu a cikin sundukin nan, sannan suka taba farin tsinken tsafi da ke cikinsa. Take sundukin ya taso sama da su har sai da ya dawo da su izuwa duniyar su Salusa. Da zuwà suka tadda babban dutse ya tarwatsa garin gaba daya sai ga narkakken dutsen na malala yana kwarara ko'ina. Cikin sauki da kwanciyar hankali suka tara jakar nan wacce Salusa ta zubo su a ciki.
Sai da jakar ta cika da narkakken dutsen, sannan suka kulle bakinta. Daga nan suka sake shiga cikin sundukin tsafi ya nutse da su cikin karkashin kasa. Bayan sun yi tafiya mai nisa sai kawai suka ga wani dogon abu ya shigo har cikin karkashin kasar ya catse sundukin yai sama da shi. Koda abin ya fito da su izuwa saman turba sai suka ga ashe hannun aljani Durmazulu ne ya yi wannan aiki. Take Durmazulu ya sa hannunsa guda ya fasa sundukin ya zaro su daga ciki daya bayan đaya.
Koda ya dauko Salusa sai ya dubeta da kyau sannan ya dubi su Markahul Sabus ya ce, "Wannan kuma fa a ina kuka samota? Tabbas ba da ita mu ka zo nan ba."
Markahul Sabus ya ce, "Haka ne, amma ai ita ce ta taimake mu har muka sami nasarar.debo narkakken dutse, kuma mun yi alkawarin tafiya tare da ita."
Durmazulu ya yi đan gajeran tunani, sannan ya dauko Salusa ya hada ta da su .Markahul Sabus ya aza su a gadon bayansa gaba daya, sannan ya bude fulkafulkansa yai sama ya kule a cikin gajimare. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su Markahul Sabus da aljani
Durmazulu bayan sun sami nasarar đebo ruwn narkakken dutsen da yafi kowannne dutse girma a duniya.
******** *********** ************
Al'amarin su Jafar kuwa bayan kwaran nan guda daya cal ya dauke su yai sama da su cikin kokoluwar sama sai gaba dayansu suka sume. Koda suka farfado sai suka tsinci kan su a gaban kundin tsatsuba a cikin ta su duniyar. Kuma shafi na shirin da daya ne dai a bude.
Jafar ne ya fara farfadowa, sannan Yelisa, Mashrila, Mazalish, Gulzum da sarki Arbir. Jafar ya mike zaune daga kwance ya dubi sauran abokan tafiyarsa yai ajiyar zuciya ya ce. "Kai jama'a bala'i fa yai bala'i, kuma masifa tayi masifa. Ni fa gaskiya na gaji haka. Wai shin babu yadda za'a yi ne mu kawo karshen litafin nan ne?"
Koda jin wannan batu sai Gulzum ya bushe da dariya ya ce, "Wa ya gaya maka cewa bakin rijiya wajen wasan yara ne? Ai shegen kunnen nan naka na kashi da bai jin magana ya janyo maka. Ina tabbatar maka da cewa wanda baya jin maganar iyayensa har abada ba zai taba ganin daidai ba. Ni kaina da ka ganni a cikin bala'in nan bakin iyayen ne ya bini. Duk wata fitina da kake takama da ita da rashin ji ba ka kaini ba, amma gashi yáu na raina kaina na kuma yi nadana."
Koda jin wannan batu sai jikin kowa ya yi sanyi hankalinsu ya dungunzuma. Nan take idanun Mazalish da na sarki Azbir ya ciko da kwallah suka fara kuka. Mazalish ta ce, "Ai duk ni ce abar tausayi a cikinku, domin ni soyayya ce ta jcho ni cikin wannan masifa na zamo sanadin mutuwar mahaifina, na baro uwata da
kasar mu. Ga shi har iyanzu ban hadu da masoyin nawa ba, kuma ga shi na fado cikin masifar da ba ta da farko bare karshe."
Wannan batu na Mazalish ya baiwa kowa tausayi, don babu wanda bai zubar mata da kwalla ba. Shi kuwa sarki Azbir sai yai ajiyar numfashi ya ce, "Ku tuna, fa cewa ni sarki ne a Kasata. Yau ga shi na wayi gari na rasa mulkina na rasa iyalina da dangina. Kai gaba đayan al'umata ma yanzu na san sun zama mayu irin mutänen Galbasa. To menene amfanin komawata kasar mu? Babu abin da ya kamace ni face mutuwa tun da ba ni da kowa wanda zan kalla na ji dadi a raina."
Kođa jin haka sai Mashrila ta fashe da kuka, sannan ta ce "Ya kai sarki Azbir ka yi sani cewa da ni da kai matsalar mu iri daya ce domin kuwa ni ma yanzu na tabbatar da cewa gaba dayan mutanen kasarmu sun halláka, Ba ni da wani masoyi da zan kalla na ji dadi face Jafar, tun da a hannunsa mahaifina ya danka amanata.
Koda jin haka sai kishi ya turnuke Yelisa amma wannan karo sai ta daure ta boye kishin a ranta ta ce, "Ni kam duk jin ku na kc. Ku yi sani cewa nima son zuciya ta ne ya jefa ni a cikin wannan masifa. Tun ban san me ye ràyuwa ba mahaifiyata ta rasu a sanadin bincike-binciken nan na tsafi. Mahaifina kuwa boka Jinshan ba shi da aikin yi dare da ranan face tsafi, kuma yana matukar kaunata, amma ga shi yanzu ya kasa tsamoni daga cikin wannan bala'il Asalima
shi kansa ban san a halin da ya ke ciki ba yanzu. Ni kam rayuwa ta fita daga raina, kuma ina ji a raina cewa gaba daya na tsani tsafi da duk ma'abotansa."
Koda jin wannan batu sai tausayin Yclisa ya kama Jafar yai ajiyar zuciya, sannan ya dubi Yelisa ya ce, "Ya ke kawata hakika zancen ki gaskiya ne, ni kaina haka nake ji a cikin zuciyata. Babu abin da ke kona mini rai face idan na tuno da cin amanar da na yiwa jarumı Hubainu. Idan ba ki manta ba mun yi masa alkawari cewar idan har ya taimake mu ya shigar da mu cikin fadar sarki Lu'umanu muka riski aljani Markahul Sabus za mu ba da gaskiya da addininsa na Musulunci. Amma maimakon mu yi hakan sai muka shammace shi muka make shi ya suma, sannan muka fito da Markahul Sabus muka gudu muka bar shi nan a kwance. In da mun karbi addininsa da yanzu duk