wahalar nan da muke sha ba mu sha ba."
Koda Jafar ya zo nan a zancensa sai kundinn tsatsuba ya bude kansa izuwa shafi na ashirin da biyu, inda suka yi arba da hoton wani kasurgumin daji a kasansa an yi rubutu kamar haka:
"Wannan daji, daji ne na masifa da bala'i, kuma an kirkire shi ne kimanin shekaru dubu da suka gabata. Mai karatu shigo cikinsa ka sha kallo "
Kafin su Jafar su ankara siriiyar muryar nan ta gama wannan jawabi. Nan take iskar cikin kundi ta fito ta zuke su duka suka zama yan mini-mini suka fada cikin kundin tsatsuba. Kawai sai tsintar kan su suka yi a cikin wani bakatafaren daji. Gabas da yamma, kudu da arewa iya ganinsu babu gida gaba, babu gida baya.
Dajin ya yi shiru tsit, babu alamar wani abu mai rai a cikinsa, kai ko irin iskar nan ma da za ka ji tana kadawa ganyayyaki na motsawa babu ita. Duk da cewar ga bishiyoyi nan birjik kala-kala da duwatsu. Jafar ya ce, "To yau fa gamu a cikin wani kurman daji, sai abin da muka gani kuma."
Yelisa ta ce, "Ai sai ku tashi mu nausa cikinsa don ba muga ta zama ba, tun da hutun jaki da kaya muke yi. Har yanzu fa a kaso goma ba mu yi kaso daya ba a cikin tsinannan littafin nan.
MU HADU A PART M DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI 🙏**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA 👆
PART M ❤️🌹
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰
TYPING ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Har yanzu fa a kaso goma ba mu yi kaso daya ba a cikin tsinannan littafin nan.
Nan take suka dunguma su duka suka nausa cikin dajin suka yi ta tafiya, ba tare da sanin inda suka nausa ba. Sai da suka yi tafiyar sa'a shida ba su hadu da komai ba, har Magariba ta doso kai. A wanhan lokaci nc yunwa da kishirwa suka baibayc su. Ga shi gaba daya babu inda suka ga alamar ruwa ko abinci.
Saboda tsananin galabaita har tangadi suke a hanya kamar wadanda suka sha gida, suka bugu.
Aljani Gulzum ne kadai ya rage mai sauran kuzari. Sai da takai cewa yana dibarsu kamar tsummokara yana sabawa a kafadarsa ana ci gaba da tafiya. Da dai ya ga cewar kwata-kwa basa sauri sai ya debe su gaba daya ya azasu a kafadar tasa hagu da dama ya ci gaba da tafiya.
Kwatsam sai yà hango wani dogon tsauni a gabansa. Gulzum yà ce a ransa, "Bari na hau kan tsaunin can ko zan hango inda za mu samu abinci da ruwa, ko wadannan malalatan su ci su sha, su farfado."
Cikin azarma Gulzum ya durfafi wannan tsauni. Da zuwa ya kama hawansa gadan-gadan. Da yake tsaunin na da matukar tsawo, sai da ya yi sa'a uku yana tafiya a kansa. Sannan ya iso samansa. Ai kuwa da zuwa ya juyo ihun mutane da kuma rurin zakuna. Koda ya hanga kasan tsaunin sai ya hango cewa ashe wani gari ne a kasa, kuma wasu irin murguza-murguzan zakuna ne suka farma garin suke ta cin mutane.
Girman kowanne za ki daya ya yi biyun aljani Gulzum. Cikin sauri Gulzum ya yi ruf da ciki akan tsaunin yana mai boye kansa da su Jafar. A wannan lokaci ne su Jafar suka farfado suka dawo cikin hayyacinsu. Koda suka kyalla ido suka hango yadda manyan zakunan nan ke barna a garin sai kowa ya yi lamo kamar ba shi da rai.
Hakika wadannan zakuna sun kasance ababan tsoro, domin gurnanin suma kadai ya isa ya sa mutum ya firgice ko ya zaunce. Komai karfin abu suna iya gatsa shi da hakoransu su taune, su cinye. Haka kuma komai giman gini idan suka bangaje shi da kirjinsu take zai rushe ya fatattake. Kai a wannan rana dai su Jafar sun ga abin al'ajabi da ban tausayi.
Cikin kankanin lokaci zakunan nan suka yi kaca-kaca da garin ko'ina ka duba jini ne ke malala da ragowar sassan jikin bil'adama. Sannan Gaba ɗaya gidajen garin babu wanda bai rushe ba, duk da cewar adadinsu ya wuce dubu dari.
Bayan zakunan nan sun gama barna sai suka hau kewaye-kewaye ko za su ga wadansu mutanen nan tamkar masu rangadi. Da suka gaji da kewayen ba su ga kowa ba sai suka ruga cikin dawa gaba dayansu tamkar an kora garkin shanu dubu. Karar gudun suma kadai ta isa ta firgita mutum, don sai da aka yi sa'a guda ana jin rugugin gudun na su, sannan sawu ya dauke garin ya sake yin tsit. Babu abin da ya bai wa su Jafar mamaki face toshewar basirar zakunan da ba su hawo kan tsaunin nan sun cinye su ba.
Sai da su Gulzum suka tsahirta sosai, suka tabbatar da cewa zakunah nan sun tafi. Sannan suka sauko daga kan dogon tsaunin nan suka shiga cikin wannan gari suka fara yawo a cikinsa. Su dai su Jafar babu abin da suke nema face abinci da abin sha, Shi kuwa Gulzum kokari yake kawai ya ga ko zai ga wani sauran mutum mai numfa shi. Babu abin da ya Kara tayar da hankalin su Jafar, face yawan gawarwakin kananan yara, har da ma jirajirai. Saboda tausayi sai da su Jafar suka kama kuka.
Ba zato, ba tsammani sai Gulzum ya ga wata Katuwar rijiya wacce aka rufe samanta da irin 6angorin dutsen dogon tsaunin nan na bayan garin wanda suka hau dazu. Koda ganin rijiyar sai Gulzum ya taimakawa su Jafar su sami ruwan sha. Koda ya bude rjiyar sai ya ga ashe a cike take dankam da mutane, yara da manya, maza da mata. Yayin da mutanen nan suka yi arba da Gulzum sai suka rusa ihu gaba dayansu cikin tsananin firgita, domin ba su taba ganin Aljani tunda suke a rayuwarsu ba. Ihun na su ne ya janyo hankalin su Jafar suka rugo wajen.
Koda su Jafar suka ga wadannan mutane sai suka cika da mamakin yadda aka yi har suka shiga cikin wannan rijiya mai zurfi gaba dayansu, alhalin babu matattakala a cikin rijiyar, kuma babu alamar wata igiya wacce suka zurata ciki. Har yanzu mutanen ihu suke yi da zarar sun dago kai sun yi arba da Gulzum.
Koda Jafar ya fuskanci hakan, sai ya sa hannaycnsa biyu ya tunkude Gulzum ya ce, Malam gafara daga nan ka ji ko kai ne kake tsorata su, suke firgita. Wata kila katon kanka ne da kwala-kwalan idannuka ke firgita su."
Cikin tsananin fushi Gulzum ya dunkule hannu zai yiwa Jafar rotse, amman sai Yelisa ta ce, Akul ka kuskura ka taba shi."
Koda jin haka sai Gulzumn ya tsaya cak. Jikinsa na karkarwa yayin da zuciyarsa ta hau tafarfasa kamar zata kone saboda takaici.
Mene ne dalilin da yasa wannan zakunan suke zuwa maku sannan da wane lokaci suke zuwa muku?" Jafar ya tambayi mutanen dake cikin rijiya.
Tsoho ya ce, "Ba su da wani zaba66e lokaci, amma sun fi zuwa a gefin Magariba sa'adda rana ke shirin faduwa, kuma ba kullum suke zuwa ba. Wani lokacin sai su kwana bakwai ba su zo ba, wani lokacin ma sai su yi wata guda."
Jafar yai ajiyar numfashi, sannan ya dubi Yelisa, Mazalish, Mashrila, Gulzum da sarki Azbir ya ce, "A cikin ku akwai mai dabara bisa yadda za'a bullowa wadannan mugayen zakuna? Gaba dayansu suka yi shiru aka rasa wanda zai ce wani abu. Daga can sai Mazalish ta ce, "Ni ina da dabara "
Cikin murna Jafar ya ce, "Yauwa sarauniyar hikima fadi dabararki mu ji. In dai muka yi nasara kin cancanci a sallama miki, domin wannan shi ne karo na uku da kika kubutar da mu daga baļa'i."
Mazalish ta yi mumushi gami da gyaran murya sannan ta ce, "Abin da za'a yi shi ne mu taimakawa mutancn nan mu hau da su kan dogon tsaunin su gina gidajen su akai. Sannan mu kera kibiyoyi da bangarin dutsen tsaunin tare da baka wanda za mu rinka harbin zakunan da su. Wata kila idan muka yi haka a dace har mu samu nasarar kashe su."
Koda jin wannan hikima sai farin cikin ya turnuke wannan al'umma gaba dayansu suka barke da shewa. Nan take aka fara aiwatar da wannan aiki. A wannan rana dai Gulzum ne yafi kowa gagarumin aiki, domin shi kadai ya rinka dibar mutanen nan da kayayyakinsu yana hawa da su kan tsaunin, sai da ya gama jide su gaba daya, sannan ya kwashi su Jafar ya hau da su. Ai kuwa yana gama aikin ne ya kwanta kasa wanwar yana faman haki cikin matsananciyar gajiya. Nan take mutanen garin su kuma suka kama aikin gina gidajensu ba kakkautawa. Nan da nan suka gama gina gidajen cikin abin da bai wuce sa'a hudu ba. Al'amarin da ya baiwa su Jafar matukar mamaki kenan, mutanen na da zafin hannu sosai, lullube mutarien nan
Bayan an garna gina gidaje, kuma sai Mazalish ta fara tsara yadda za a kera kibiyoyin nan da bangarin duwatsu da kuma bakan harba kibiyoyin. Nan fa aka shiga aiki gadann-gadan.
Sai da aka kera kibiyoyi guda dubu dari bakwai hade da bakan har basu. Daga nan kuma sai Mazalish ta fara koyawa mutanc yadda za su harba kibiyoyin har dai kowa ya kware. Duk wannan abu da ke faruwa Gulzum na gefe guda yana kallo kawai bai damu da ya koyi harba wannan kibiya ba. Sai da aka gama ba da horon harba kibiyar, sannan Mazalish ta dube shi ta ce, Ya kai Gulzum me ya sa ka koma gefe daya ka zauna ka Ki zuwa ka koyi wannan harbi?"
Koda jin wannan tambaya saí Gulzum ya yi murmushi sannan ya ce, "Ai kin san komai na babbar halitta babba ne. Ya za'a yi ki ban wannan mitsitsiyar kibiyar ki ce da ita zan yi harbi."
Mazalish ta yi murmushi ta ce, "Kwarai kuwa ka zo da bayani na kwarai."
Nan take Mazalish ta sa aka kerawa Gulzum majajjawa mai dauke da mulmulallun duwatsu guda biyu ta mika masa. Ta ce, "Ga naka makamin.
Idan har za ka dunga dukan wadannan zakuna da wannan majajjawa tabbas za ka ragargaje su.
Gulzum ya karbi majajjawar ya jinjina nauyinta a hannayensa ya ji ta yi masa yadda yake so. Sai yai murmushi ya ce, sarauniyar hikima, "Kin yi daidai yanzu ne na san cewa zan taka muhimmiyar rawa a wannan yaki da za mu yi da muggan zakuna."
MU HADU A PART N DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI 🙏💯**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA 👆❤️
PART N ❤️🌹
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰🙏
TYPING ABUBAKAR SALE ALQURAMEY 💯
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....
Gulzum ya karbi majajjawar ya jinjina nauyinta a hannayensa ya ji ta yi masa yadda yake so. Sai yai murmushi ya ce, sarauniyar hikima, "Kin yi daidai yanzu ne na san cewa zan taka muhimmiyar rawa a wannan yaki da za mu yi da muggan zakuna."
Daga wannan rana su Jafar da wadđannan mutancn gari suka ci gaba da rayuwa akan tsauni kullum sai dại Gulzum ya sauko kasan tsaunin ya je ya bude rijiyar nan mi đauke da ya'yan itatuwa da ruwa ya đebo musu iya eanda zai ishe su ci a ranar. Sai da kwanaki bakwai suka shude muggan zakunan nan ba su dawo ba, Kai abu dai kamar wasa aka tafi kwana goma shiru babu duriyarsu. Wannan ta sa aka saki jiki aka fara tunanin ba za su zo ba, sai bayan cikar kwana talatin.
A ranar kwana na goman ne da gefin Magariba sa'adda Gulzum da su Jafar suka sauko kasan tsaunin ne mike kafafunsu, kawai suka jiyo rugogin tahowar zakunan nan. Nan fa suka firgice suka dimauce suka ruga izuwa kan tsaunin. Amman sai suka rinka rikitowa kasa. Gulzum ne kadai ya iya hayewa can sama.
Koda Gulzum ya waiga baya ya ga su Jafar sun kasa hawowa sai ya koma da baya a guje ya kwasosu cikin zafin nama ya sake hawa kan dutsen yana ta tsala azabben gudu.
Ai kuwa yana gama hawa kan tsaunin ne zakunan suka iso inda tsohon garin da mutane yake. Nan fa zakunan suka fara kewaye-kewaye amma ba su ga ko mutum guda đaya ba. Al'amarin da ya fusata zakunan kenann suka kama ruri da wani irin kuka na takaici. Duk abin da ke faruwa su Jafar na hangowa daga can saman tsauni.
Yelisa ta ce, "Shegu yau dai sai dai ku ci kanku, ba za ku sami ko mutum daya ba."
Shi kuwa Jafar sai ya dubi Gulzum ya ce, Ya kai Babba ai sai ka tsokano mana zakunan don su zo bakin tsaunin nan a yi ruguntsumi mu da su?"
Gulzum ya dubi Jafar yai masa murmushi a karo na farko, tun haduwarsu ya ce, "Da kyau yaro yau kam ka yi karambani mai kyau ba iri wanda ka ke yi a baya ba, na banza da na wofi."
Kafin Jafar ya kara cewa wani abu tuni Gulzum ya takarkare ya kwarara uban ihu. Al'amarin da ya juyo da hankalin zakunan nan kenan gaba daya suka dubi kan tsaunin nan.
Koda suka hango su Gulzum da kuma ginin gidaje sai suka bazamo a guje suka durfafo tsaunin nan kai ka ce halittun daji ne duka ke gudun ceton rai. Karar sawayen su ma kadai sai da ta cika dajin gabadaya, kamar dodan kunne zai dode.
Kura kuwa ta turmuke ko'ina, tamkar ana yakin duniya. Idan mutum ya ga bataliyar zakunan a wannan lokaci sai ya yi tsammani yakin aljanu ake yi saboda tsananin yawansu da kwarjininsu.
Kai tsaye zakunan nan suka nufi kan tsaunin da nufin hawa, amma da sun kama shi sai ka ga suna zamewa gami da fadowa kasa. Koda ganin haka sai su Jafar da mutanen garin nan suka fara sakarwa zakunan nan ruwan kibiyoyi dutse.
Nan fa kibiyoyin suka rinka huda jikin zakunan Suna zubewa kasa matattu. Al'amarin da ya sa Zakunan suka kasa haukacewa kenan, suka ci gaba da kokarin hawa kan tsaunin saboda ganin yadda ake kashe yan uwansu, amma sai abu ya gagara.
Daga cikin wadannan zakuna akwai guda đaya mafi girma, kuma duk abin da ke faruwa wannan zaki yana tsaye daga can baya yana kallo.
Koda ya ga abin da ke faruwa ga 'yan uwansa sai ya harzuka, ya kama dawurwura a waje daya.
Haka dai su Jafar suka ci gaba da da harbe zakunan nan har suka kashe kimanin guda dubu dari shida da doriya. Duk wannan bai sa zakunan sun koma da baya ba. A lokacin ne kuma kibiyoyin su Jafar suka kare ya zamana.saura kadan. Koda ganin hakan sai wasu daga cikin, zakunan suka koma wajen babban nan na su kimanin su dari suka kewaye shi tamkar suna tattaunawa. Ba zato, ba tsarnmani sai wadannan zakuna guda dari tare da babbansu suka ja da baya-baya a jere a layi, sannan suka taho da matsayacin gudu. Koda suka zo daf da bakin tsaunin nan sai suka daka tsalle suka yi sufa iya karfinsu.
Ai kuwa sai ga su a sama, kamar an cillo su da kibiyoyi, suka yiyo kan su Jafar da mutanen garin. Kafin a ankara sun duro a kansu. Babban zakin nan dai akan sarki Azbir ya duro. Nan take ya gutsire kan Azbir ya taune, ya cinye. Kafin ya yunkura ya sake afkawa wani. Jafar ya tabe bakansa ya narka masa harbi a cinya. Kibiyar ta fasa cinyar zakin ya kwarara uban ihu tare da gangarowa kasa daga kan tsaunin. A wannan lokaci ana ci gaba da ruguntsumi tsakanin zakunan nan da su Yelisa da sauran mutanen garin. Tuni zakunan sun yi mummunar barna don sun ci sama da mutum dari.
Koda ganin haka sai Gulzum ya hau kan zakunan nan yana mai ragargazarsu da wannan majajjawarsa ta kulalun duwatsu. Duk zakin da ya kwalawa majajawar a ka sai ka ga kan zakin ya tarwatse, kamar an fasa kwakwa. A wannan rana Gulzum ya yi gagarumin aiki, don sai da ya kashe zahunan saba'in da bakwai daga cikin wadannan guda dari wadanda suka hawo kan tsaunin.
Bisa dole zakunan nan suka gudu daga kan tsaunin suka daina 6arna. Nan take dayandaga cikin zakunan ya sa bakinsa ya cisge kibiyar nan da ta huda cinyar babban cikin su.
Zakin yai ruri mai ban tsoro, saboda tsananin zafin fitar kibiyar. Duk da cewar jini na zuba sosai a cinyar zakin sai da ya mike tsaye ya taka kuma ya wuce gaba suka bi hanyar da suka fito. Suna tafe suna waigen tsaunin har suka kule a cikin dajin.
A sannan ne su Jafar suka dawo cikin hayyacinsu. Mutanen garin suka fara kuka, bisa mutuwar 'yan uwansu a wannan yaki. Ana cikin haka ne su Jafar suka ga gawar sarki Azbir, ga gangar jikinsa nan a kwance babu kai. Gaba dayansu sai suka fashe da kuka, suka yi ta kukan babu kakkautawa har izuwa wani lokaci mai tsawo. Tabbas idan mutum ya dube su a wannan lokaci dole ne ya ji tausayinsu. Cikin sanyin jiki, suka dauki gawar sarki Azbir suka sauko kasan dutsen suka haka kabari sukia binne shi.
Anann gindin kabarin suka ci gaba da kuka. Bayan sun yi kukan sun gaji sai Jafar ya.dube su daya bayan daya, ya ce, "Ya ku 'yan uwana abokan tafiya ku yi sani cewa gaba dayan mu nan za mu iya tsintar kanmu a cikin irin halin da Azbir ya kasance, don haka yana da kyau mu gafarci juna bisa abubuwan da suka faru a tsakaninmu a baya."
Jafar ya mike tsaye ya taho ga Gulzum ya durkusa a gabansa ya ce, Ya kai Gulzum ina mai rokonka da ka gafarce ni bisa duk irin bakaken maganganun da na gaya maka a baya. Ka yi sani cewa na yi nadama, tabbas yanzu na gane cewa rayuwar duniyar nan ba a bakin komai take ba,
in mu ne yau, gobe ba mu ba ne."
Koda Jafar ya zo nan a zancensa, sai hawaye ya zubowa Gulzum ya ce, "Ya kai abokina Jafar kasani cewa duk abin da ka yì mini a baya na yafe maka. Ina fatan kuma kai ma za ka yafe mini abin da nai maka."
Koda jin haka sai Jafar ya rungume Gulzum su duka suka fashe da kuka. Mashirila ta kama hannaycn Yelisa ta ce, "Ya ke kawata ki yi sani cewa ni da ke mun tsangwami juna kamar yadda Jafar da Gulzum suka yi. Ina fatan mu ma za mu gafarci kannu?"
Maimakon Yelsa ta ce wani abu sai ta rungume Mashinia suma suka kama kuka. A wannan rana dai su Jafar ba su sami walwala ba da nutsuwa. Haka suka kwana a cikin bakin ciki. Suma mutanen garin haka suka kasance bayan sun binne gawawakin yanuwansu da suka rasa akan wannan tsauni.
Kashe gari da sassafe Mazalish ce ta tashi kowa daga barci ta ce,"Ya ku jama'a ina son ku sani cewa lallai wadannan zakuna za su sake dawowa, kuma za su dawo ne da mugun nufi na karar da mu gaba daya, don haka dole mu yi sabon shiri, don karawa kan mu karfi da kariya. Bisa haka na yi tunanin wata sabuwar dabara.
Dabarar kuwa ita ce za mu gina keji da yawa, da zallan duwatsu, mai kanan kofofi, wanda za mu shiga cikinsa mu tsatstsaya. Muna daga cikin kejin ne za mu duinga harbin zakunan. Hikama ta anan shi ne ko da zakunan sun hauro kan tsaunin ba za su iya shiga cikin kejin su farmana ba. Haka kuma dole ne mu kera kibiyoyi da yawa wannan karon ya zamana sun ninka Wadancan da muka yi na farko. Ina ganın ina dai muka yi haka za mu kubuta daga sharrin wadannan mugayen zakuna masu kama da shaidanu."
Koda Mazalish ta gama wanna jawabi sai kowa ya yi na'am da shi. Nan take aka shiga aikin gina kejina da kera kibiyoyi. Haka dai aka yi ta aiki har tsawon kwana hudu ba tare da an tsaya ba. A kwana na hudun ne jama'a suka gaji likis dole aka tsaida aiki don a huta. A wannan lokaci an kera kibiyoyi sama da guda miliyan biyu. Su kuwa dakunan keji guda dubu arba'in
aka gina. Lokacin da aka zazzauna don a huta ne Mashrila ta zauna daf da Yalisa suka dubi juna suna murmushi. Jimkadan babu wanda ya ce kala, amma sai Mashrila ta ce, "Ya ke kawata kiyi sanı cewa ina mai yi miki fatan zaman alheri tare da masoyinki Jafar nan gaba cikin rayuwarku."
Koda jin wannan batú sai jikin Yelisa yai sanyi ta dubi Mashrila cikin mamaki da damuwa ta ce, "Haba kawata me ya sa kike magana irin wannan mai nuni da alamun ban kwana?"
Mashrila ta yi yake ta ce, "Dole ne ki ji Irin wadannan kalamai daga bakina domin inaji a jikina cewa ajalina na nan tafe a kusa. Tana gama fa din hakan ne sai ta fashe da kuka. Cikin sauri Yalisa ta rungumeta tana mal rarrashinta ta ce, "Ya ke kawata ki daina irin wannan furuci, domin babu wanda ya san gawar fari ai. Babu mamaki ma ni ce zan riga ki mutuwa.
Wannan kalamai na Yelisa ba karamin tayar da hankalin kowa yai ba. Haka dai aka ci gaba da wannan zama kowa na fadin albarkacin bakinsa Har dare ya raba aka je aka kwanta.
Sai da kwanaki goma sha hudu suka shude har a sannan zakunan nan ba su dawo ba. A ranar kwana na goma sha biyar ne da yammaci zakunan suka kawo farmaki. Cikih rudewa su Jafar suka hau diban makaman fada suna shiga cikin kejin da aka gina na duwatsu.
Sai dai kafin jama'a su gama shiga cikin kejin nan tuni zakunan sun dirga akan tsaunin sun fara barna. Wannan karon dai ba zakuna dari ba ne, suka
sami damar hawowa kan tsaunin. A kallah sun kai guda dubu.
Kaiço! Hakika a wannan rana mutanen garin nan sun mutu da yawa, domin duk inda ka duba akan tsaunin gawarwaki nc na mutane birjik. Kamar a makabarta. Jini kuwa har gudu yake akan tsaunin yana gangarowa Kasa. Su
kuwa su Jafar in ban da harbi babu abin da suke yI cikin tsananin sauri da zafin nama. Kusan a cikin dakika sittin suna iya harba kibiyoyi guda arba'in-arba'in, Duk da cewar suna kashe zakunan suma zakunan basu fasa daukar rai ba.
A wannan rana dai sai da aka shafe sa'a biyar ana dauki-ba-dadi tsakanin zakunan da su Jafar. Hakika Gulzum ya bada gagarumar gudunmuwa a wannan yaki, domin ya kashe sama da zakuna dari uku. Tun yana yin yakin da tsananin zafin nama har sai da ya jigata ya zamana juriya kawai yake yi amman ya gaji ainun. A lokacin ne wani zaki ya shammace shi ya kama gwiwar hanunsa da bakí ya gutsure katon nama. Gulzum ya kwarara ihu cikin tsananin jin zogi al'amarin da ya fusata shi kenan ya ji wani sabon karfi ya zo masa, ya ci gaba da ragargazar zakunan sai da ya sake kashe guda dari uku da arba'in a dan kankanin lokaci.
Yayin da ake wannan artabu ne wasu zakunà guda goma suka hada karfinsu suka rinka bangazar kejin da su Yelisa ke ciki da Kirjinsu. Tun kejin na girgiza sai da ya fadi kusa wanwar, ya ruguje. Anan ne fa zakunan nan suka yiwa Mashrila rufdugu. Kafin ka ce me sun yi gutsun-gutsun da ita. Cikin karaji Gulzum ya daka tsalle daga inda yake ya dira kan zakunan ya hau su da duka da wannan majajjawar tasa yai ta rotsa kawunansu suna zubewa kasa matattu. Hakika a waannan rana ba dan Gulzum ya kawo wa su Yalisa dauki ba da gaba dayansu sun hallaka, Gulzum dai bai gushe ba yana ragargazar zakunan nan sai da ya karar da su gaba daya. Ya zamana babu wani zaki a kan tsaunin rayayye, sai wadanda ke can kasan tsaunin.
Yayin da zakunan da ke kasa suka daina jiyo rurin 'yan uwansu na kan tsaunin sai duk jikinsu yai sanyi. Ba zato, kuma sai suka dunguma suka bi hanyar da suka fito, suka nausa cikin daji. Tun su Jafar na hango su sai da suka bace ma ganinsu.
Bayan tafiyar zakunan ne, kuma aka fara koke-koken rashi. A wannan rana su Jafar sun yi kuka mai tsanani fiye da wanda suka yi a ranar da sarki Azbr ya utu, saboda rasuwar Mashrila. Musamman ma Yelisa sai da ta suma sau uku, saboda tsananin kuka da bakin ciki.
Daga wannan rana zakunan nan ba su sake dawowa ba, har tsawon kwana ashirin da biyar.
MU HADU A PART O DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARI 🙏**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA DAYA 👆❤️
PART O ❤️🌹
NA