Kamar yadda ake ruwan sama, haka kananan halittun nan masu siffar fara suka rinka zubowa Kasa daga sararin sama, sai dai ka ga sun lullube Jikin mutum gaba daya suna gutsurar naman jikinsa. Nan fa ihun mutane maza da mata ya cike birnin Asgarwa. Ko'ina ka duba jini ne ke guda yana malala tamkar kwaranyuwar ruwan teku. Daga cikin tsirarun mutanen da har yanzu suke faman gudu kuma kwarin ba su riske su ba, akwai; Jafar, Yelisa, Mashrila, sark Azbir, Mazalish da kuma aljani Gulzum.
Gudu suke iya karfinsu, amma da sun waiga baya sai su ga cewa tsakanin su da kwarin bai wuce kamu uku ba. Suma kwarin iyakar kokarinsu suke gudun, har tashi suke a sama suna lankwayawa, don dai su cimna tsirarun mutanen. Su Jafar ne akan gaba, don sun fi mutanen garin gudu. Daga cikin mutanen garin akwai wani yaro mai matukar kokari shi ne ke bin su Jafar daf-da-daf. Duk da cewar yaron bai fi shekara goma sha uku ba, ya ninka su Jafar girma sau talatin don a tsayema yana iya hango tsakiyar kan aljani Gulzum, kuma yafi Gulzum fadi da cika ido.
Bayan wannan yaro sai kuma wadansu mutane guda arba'in, wadanda ke biye da suna ta tsala gudun iyakar karfinsu. Ba zato, ba tsamani sa kwarin nan suka cimma mutum na karshe. Daga nan kuwa sai suka ci gaba da dauki daidai a layi. Babu abin da zai ba mutum mamaki da wadannan kwari sai karfin su. Domin Idan suka yanyame jikan mutum suna gutsurarsa sai kaga har tashi suke da shi sama, yayin da suke bude fuka-fukansu. Cikin abin da bai wuce dari da ashirin ba, kwarin suka gama da mutane arba'in in nan ya rage saura yaron nan da kuma su Jafar.
Koda su Jafar suka waigo suka ga an karar da dukkanin jama'ar nan da ke bayan su saura yaron nan shi kadai. Sai hankalinsu ya kara dugunzuma, suka kara kaimin gudu, suna masu rusa ihu. Suma kwarin nan sai suka kara kaimi domin su cim musa. Ana cikin azababban gudun ne wannan yaron ya sauya hanya ya nufi wani wuri mai kama da daji. Koda ganin haka sai Jafar yabi bayansa, suma su Yelisa ba su yi sanya ba suka take masu baya, bisa dole suma kwarin suka sauya akala suka bi inda suka bi.
Shi dai Jafar tuni a ransa ya kudurce cewa da dan gari akan ci gari, don haka duk inda wannan yaro ya shiga nan shima zai shiga. Ai kuwa yaron bai durfafi ko ina ba sai wani katon kogon dutse mai gajeriyar kofar shiga. Haka dai aka kasa tsere tsakanin su Jafar da wadanan kwari har suka iso bakin kofar kogon nan, amman kwarin ba su cim musu ba, tsakaninsu bai wuce kamu hudu ba. Yaron nan dai sai da ya-wuce su Jafar ya zamo shine akan gaba.
Da yake yana da tsawo sosai ba zai iya shiga cikin kogon da gudu ba. Yana zuwa sai yayi sufa ya mikar da jikinsa ya fada cikin wannan kogon. Suma su Jafar duk sai suka yi yadda ya yi. Na karshen su na fadowa sai yaron ya dauko wani katon dutse acikin kogon ya toshe kofar shigowa da shi.
Ai kuwa kwarin nan ba su samu damar shigowa cikin kogon ba, sai suka yanyame wannan dutse suka yi suna ta wani irin kuka mara dadin sauti, wanda ka iya karmuntar da wanda ke kusa dasu Ashe dai sirrin wadannan kwari shine dutse, domin shi kadai ne abin da ba sa iya ci, amma ko karfe suka samu take za su rumurmushe shi.
A cikin kogon dutse kuwa su Jafar na ta faman haki sun kasa magana sai kallan-kallo ake yi kawai, tsakaninsu da wannan yaro, har izuwa lokaci mai tsawo. Daga can sai Jafar ya dubi wannan yaron ya ce, "Abokina mene ne sunanka?"
Koda jin wannan tambaya sai yaron ya yi mumushi yace, "Sunana Zalkum."
Jafar ya bushe da dariya ya ce, "Ai kuwa sunan ya daçe da kai, don wannan mugun tsayin naka ko Zalkalamu albarka."
Yaron dai bai fahimci abin da Jafar yake fadi ba. Su kuwa su Gulzurm sai suka buse de dariya. Dariyar ce ta sa yaran ya tsargu da cewar bakar maganar Jafar ya fada masa cikin fushi yaron ya yunkura da nufin ya make Jafar.
Sai kawai Jafar ya durkusa gabansa, cikin alamun tausayi ya ce, "Ka yi hakuri bawai ina nufin na muzantaka yasa na fadi haka ba. Ya kai Zalkum yanzu yaushe ne za mu iya fita daga cikin wannan kogon, kuma menene ya hana wadannan mugayen kwarin shigowa cikin kogon dutsen nan?
Kafin Zalkum ya ce wani abu, Gulzum ya rigashi cewa, 'Kash! Me ya sa wai kai baka da hakuri ne, ashe dai mara kunyar karya ne kai Jafar. Da tuni yanzu wannan yaron ya yi maganinka ka gane cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ce. Mu da ka raina ka kewa rashin kunya daman an ce ido wa ka raina, ya ce wanda nake gani kullum.
Koda jin haka sai Jafar ya yi tsaki, ba tare da yace komai ba. Sannan ya juya ya fuskanci Zalkum ya ce. "Kai nake sauraro ka bani amsar tambayoyina."
Zalkum ya yi murmushi mai kama da gurrnanin damisa, sannan ya ce, Ba zamu iya fita daga cikin kogon nan ba, sai nan da kamar sa'a daya, a sannan ne kwarin su koma inda suka fito. Abin da kuwa ya hana kwarin nan shigowa nan shi ne ba sa iya cin dutse, amma suna iya cin komai, kuma duk garin nan ni kadai ne na iya gano haka a jiya sa'adda suka zo mana na gudu cikin nan na 6uya, kuma na rufe kofar kogan da wannan dutse, kamar yadda na yi daza.
Ba don mutunen garin nan na da mugun yawa ba da tuni kwarin nan sun gama da mu gaba daya."
"To wai shin kamar wane lokaci kwarin suka saba zuwa maku, ko kuwa ba su da takamaiman lokaci?" Mazalish ce ta yi wannan tambaya.
Zalkum ya ce, "Ai kullum da safe suke zuwa kamar wannan lokacin, kuma babu wanda ya san daga inda suke zuwa"
Koda jin haka sai su Jafar suka jinjina al'amarin a ransu, kowa yai shiru yana tunani. Daga can sai Mazalish ta sake duban yaron ta ce, 'Shin kuna da sarki ne a garin nan?"
Yaron ya gingza kai, alaar babu, sannan ya ce, "Ai mu anan mai karfi ne kawai shugaba.
Don haka ba mu da tsayayyen sarki, idan yau wannan ne gobe kuma sai ka ga wancan ne, saboda shigowar baki ko yaushe."
Haka dai su Jafar suka ci gaba da zama abcikin wannan kogo, har sa'a guda ta cika, a sannan ne suka daina jiyo sautin kukan kwarin nan mara dadin ji. Hakan ne ya tabbatar musu da cewa kwarin sun tafi. Ba tare da fargabar komai ba suka janye katon dutsen nan suka fito daga cikin kogon.
Zalkum ne yai musu jagora suka koma cikin garin inda suka iske tsirarun mutanen da suka kubuta, sakamakon wanna annoba ta kwari. A lokacin da yawansu suna kuke-kuke ne musamman matayen da suka rasa mazajensu, sai kuma yara kanana da suka rasa iyayensu. Nan dai wadanda suka rayun suka rinka kwaso gawarwakin matattun suna tara su wajc guda, sannan su bunka musu wuta. Duk inda su Jafar suka gifta haka suke gani ana ta yi. Duk kokarin mutum bai isa iya lissafin adadin yawan gawarwakin ba, kuma duk inda mutum ya kai ga rashin imanı dole nc ya ji tausayi a wannan rana, musamman idan ya ga yadda kananan yara ke ta rusa kuka babu mai kula da su. Bayan su Jafar sun gama yawo a garin su gaji sai Zalkum ya ja su ya kai su gidan mahaifinsa.
Da shigar su cikin gidan sai Zalkum ya yi arba da mahaifiyarsa. Cikin tsananin farin ciki ta rugu gare shi suka rungumc juna, domin ba su yi tsammanin za su sake saduwa ba. Fatalis ta dago kai ta dubi Jafar, wadanda ke tsaye a bakin kofar, kamar wadanni. Sannan, ta janye jikinta daga na Zalkum ta ce, "Ina ka samo wadannan baki kuma?"
Zalkum ya ce, "Kamar yadda kika gansu tsulum haka nima na gan su. Su kan su ba su san yadda aka yi suka zo wannan duniya tamu ba."
Fatalis ta sake duban su Jafar da kyau ta ce, "Ya akai gaba dayansu suka kubuta daga sharrin kwarin annoba?"
Zalkum ya ce, "Haba! Ummata ai ba haka ake saukar baki ba, da zuwansu a hau su da tambayoyi. Ya kamata a ce ko dan ruwa mun ba su sun sha."
Fatalis ta yi murmushi, sannan ta ce da su Jafar, "Ku yi hakuri ku shigo ciki ku zauna."
Cikin murna su Jafar suka karaso cikin tafkeken falon mai đauke da wasu manyan kujeru wadanda aka kerars su da zallan karfen murjani. Koda Gulzum ya zauna akan daya daga cikin kujerun sai ya zama dan tsugut kamar dantsako a cikin keji. Koda ganin haka sai Jafar ya ki zama akan kujerar ya zauna a kasa. Yelisa ta dube shi ta ce, "Haba Jafar ya za kai mana kauyanci ne?"
Jafar yai murmushi ya ce, "Yelisa kenan ba kya ganin yadda Malam babba ya zama kamar sauro ne akan kujerar, mu kuwa ai sai mu zama kamar kwayar zarra."
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Basiru Aliyu Harande Zuru
Shehu Usman
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Asma Baffa
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Abdulaziz Sani Madakin Gini
Mukhtar Kwalisa
Xeemat
Ismail Abdullahi
Mukhtar Kwalisa
by Maimuna A A Rano
by Muhammad Abba Gana
by Binta Umar Abbale
by Mujahida Matar Malam
by Abdulaziz Sani Madakin Gini
by Rasheedat Usman
by Batul Mamman
by Aisha MB
by Aisha Muhammad Maman Shakur
by Habiba Abubakar Imam