Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels **MIFTAHUZZARBIL**💥💥 LITTAFI NA DAYA✍️✍️ PART A ❤️❤️ NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY ✍️ TO jama'a kyan Alkawari cikawa. Kamar yadda kuka sani cewa mun kammala littafin MATSATSUBI na uku, Wanda mukayi maku Alkawarin kawo maku cigaban littafin wato MIFTAHUZZARBIL, to lallai rana Bata karya sai dai Uwar diya ta ji Kunya. Allah ya kawo mu ranar LARABA Kuma insha Allah a yau zamu cigaba da littafin.. Allah ya temake mu Amin.🙏🙏 Najibullahi Muhammad #Lengends of KATSINA 💪 ✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓ Cigaban Littafin.... Kamar yadda ake ruwan sama, haka kananan halittun nan masu siffar fara suka rinka zubowa Kasa daga sararin sama, sai dai ka ga sun lullube Jikin mutum gaba daya suna gutsurar naman jikinsa. Nan fa ihun mutane maza da mata ya cike birnin Asgarwa. Ko'ina ka duba jini ne ke guda yana malala tamkar kwaranyuwar ruwan teku. Daga cikin tsirarun mutanen da har yanzu suke faman gudu kuma kwarin ba su riske su ba, akwai; Jafar, Yelisa, Mashrila, sark Azbir, Mazalish da kuma aljani Gulzum. Gudu suke iya karfinsu, amma da sun waiga baya sai su ga cewa tsakanin su da kwarin bai wuce kamu uku ba. Suma kwarin iyakar kokarinsu suke gudun, har tashi suke a sama suna lankwayawa, don dai su cimna tsirarun mutanen. Su Jafar ne akan gaba, don sun fi mutanen garin gudu. Daga cikin mutanen garin akwai wani yaro mai matukar kokari shi ne ke bin su Jafar daf-da-daf. Duk da cewar yaron bai fi shekara goma sha uku ba, ya ninka su Jafar girma sau talatin don a tsayema yana iya hango tsakiyar kan aljani Gulzum, kuma yafi Gulzum fadi da cika ido. Bayan wannan yaro sai kuma wadansu mutane guda arba'in, wadanda ke biye da suna ta tsala gudun iyakar karfinsu. Ba zato, ba tsamani sa kwarin nan suka cimma mutum na karshe. Daga nan kuwa sai suka ci gaba da dauki daidai a layi. Babu abin da zai ba mutum mamaki da wadannan kwari sai karfin su. Domin Idan suka yanyame jikan mutum suna gutsurarsa sai kaga har tashi suke da shi sama, yayin da suke bude fuka-fukansu. Cikin abin da bai wuce dari da ashirin ba, kwarin suka gama da mutane arba'in in nan ya rage saura yaron nan da kuma su Jafar. Koda su Jafar suka waigo suka ga an karar da dukkanin jama'ar nan da ke bayan su saura yaron nan shi kadai. Sai hankalinsu ya kara dugunzuma, suka kara kaimin gudu, suna masu rusa ihu. Suma kwarin nan sai suka kara kaimi domin su cim musa. Ana cikin azababban gudun ne wannan yaron ya sauya hanya ya nufi wani wuri mai kama da daji. Koda ganin haka sai Jafar yabi bayansa, suma su Yelisa ba su yi sanya ba suka take masu baya, bisa dole suma kwarin suka sauya akala suka bi inda suka bi. Shi dai Jafar tuni a ransa ya kudurce cewa da dan gari akan ci gari, don haka duk inda wannan yaro ya shiga nan shima zai shiga. Ai kuwa yaron bai durfafi ko ina ba sai wani katon kogon dutse mai gajeriyar kofar shiga. Haka dai aka kasa tsere tsakanin su Jafar da wadanan kwari har suka iso bakin kofar kogon nan, amman kwarin ba su cim musu ba, tsakaninsu bai wuce kamu hudu ba. Yaron nan dai sai da ya-wuce su Jafar ya zamo shine akan gaba. Da yake yana da tsawo sosai ba zai iya shiga cikin kogon da gudu ba. Yana zuwa sai yayi sufa ya mikar da jikinsa ya fada cikin wannan kogon. Suma su Jafar duk sai suka yi yadda ya yi. Na karshen su na fadowa sai yaron ya dauko wani katon dutse acikin kogon ya toshe kofar shigowa da shi. Ai kuwa kwarin nan ba su samu damar shigowa cikin kogon ba, sai suka yanyame wannan dutse suka yi suna ta wani irin kuka mara dadin sauti, wanda ka iya karmuntar da wanda ke kusa dasu Ashe dai sirrin wadannan kwari shine dutse, domin shi kadai ne abin da ba sa iya ci, amma ko karfe suka samu take za su rumurmushe shi. A cikin kogon dutse kuwa su Jafar na ta faman haki sun kasa magana sai kallan-kallo ake yi kawai, tsakaninsu da wannan yaro, har izuwa lokaci mai tsawo. Daga can sai Jafar ya dubi wannan yaron ya ce, "Abokina mene ne sunanka?" Koda jin wannan tambaya sai yaron ya yi mumushi yace, "Sunana Zalkum." Jafar ya bushe da dariya ya ce, "Ai kuwa sunan ya daçe da kai, don wannan mugun tsayin naka ko Zalkalamu albarka." Yaron dai bai fahimci abin da Jafar yake fadi ba. Su kuwa su Gulzurm sai suka buse de dariya. Dariyar ce ta sa yaran ya tsargu da cewar bakar maganar Jafar ya fada masa cikin fushi yaron ya yunkura da nufin ya make Jafar. Sai kawai Jafar ya durkusa gabansa, cikin alamun tausayi ya ce, "Ka yi hakuri bawai ina nufin na muzantaka yasa na fadi haka ba. Ya kai Zalkum yanzu yaushe ne za mu iya fita daga cikin wannan kogon, kuma menene ya hana wadannan mugayen kwarin shigowa cikin kogon dutsen nan? Kafin Zalkum ya ce wani abu, Gulzum ya rigashi cewa, 'Kash! Me ya sa wai kai baka da hakuri ne, ashe dai mara kunyar karya ne kai Jafar. Da tuni yanzu wannan yaron ya yi maganinka ka gane cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ce. Mu da ka raina ka kewa rashin kunya daman an ce ido wa ka raina, ya ce wanda nake gani kullum. Koda jin haka sai Jafar ya yi tsaki, ba tare da yace komai ba. Sannan ya juya ya fuskanci Zalkum ya ce. "Kai nake sauraro ka bani amsar tambayoyina." Zalkum ya yi murmushi mai kama da gurrnanin damisa, sannan ya ce, Ba zamu iya fita daga cikin kogon nan ba, sai nan da kamar sa'a daya, a sannan ne kwarin su koma inda suka fito. Abin da kuwa ya hana kwarin nan shigowa nan shi ne ba sa iya cin dutse, amma suna iya cin komai, kuma duk garin nan ni kadai ne na iya gano haka a jiya sa'adda suka zo mana na gudu cikin nan na 6uya, kuma na rufe kofar kogan da wannan dutse, kamar yadda na yi daza. Ba don mutunen garin nan na da mugun yawa ba da tuni kwarin nan sun gama da mu gaba daya." "To wai shin kamar wane lokaci kwarin suka saba zuwa maku, ko kuwa ba su da takamaiman lokaci?" Mazalish ce ta yi wannan tambaya. Zalkum ya ce, "Ai kullum da safe suke zuwa kamar wannan lokacin, kuma babu wanda ya san daga inda suke zuwa" Koda jin haka sai su Jafar suka jinjina al'amarin a ransu, kowa yai shiru yana tunani. Daga can sai Mazalish ta sake duban yaron ta ce, 'Shin kuna da sarki ne a garin nan?" Yaron ya gingza kai, alaar babu, sannan ya ce, "Ai mu anan mai karfi ne kawai shugaba. Don haka ba mu da tsayayyen sarki, idan yau wannan ne gobe kuma sai ka ga wancan ne, saboda shigowar baki ko yaushe." Haka dai su Jafar suka ci gaba da zama abcikin wannan kogo, har sa'a guda ta cika, a sannan ne suka daina jiyo sautin kukan kwarin nan mara dadin ji. Hakan ne ya tabbatar musu da cewa kwarin sun tafi. Ba tare da fargabar komai ba suka janye katon dutsen nan suka fito daga cikin kogon. Zalkum ne yai musu jagora suka koma cikin garin inda suka iske tsirarun mutanen da suka kubuta, sakamakon wanna annoba ta kwari. A lokacin da yawansu suna kuke-kuke ne musamman matayen da suka rasa mazajensu, sai kuma yara kanana da suka rasa iyayensu. Nan dai wadanda suka rayun suka rinka kwaso gawarwakin matattun suna tara su wajc guda, sannan su bunka musu wuta. Duk inda su Jafar suka gifta haka suke gani ana ta yi. Duk kokarin mutum bai isa iya lissafin adadin yawan gawarwakin ba, kuma duk inda mutum ya kai ga rashin imanı dole nc ya ji tausayi a wannan rana, musamman idan ya ga yadda kananan yara ke ta rusa kuka babu mai kula da su. Bayan su Jafar sun gama yawo a garin su gaji sai Zalkum ya ja su ya kai su gidan mahaifinsa. Da shigar su cikin gidan sai Zalkum ya yi arba da mahaifiyarsa. Cikin tsananin farin ciki ta rugu gare shi suka rungumc juna, domin ba su yi tsammanin za su sake saduwa ba. Fatalis ta dago kai ta dubi Jafar, wadanda ke tsaye a bakin kofar, kamar wadanni. Sannan, ta janye jikinta daga na Zalkum ta ce, "Ina ka samo wadannan baki kuma?" Zalkum ya ce, "Kamar yadda kika gansu tsulum haka nima na gan su. Su kan su ba su san yadda aka yi suka zo wannan duniya tamu ba." Fatalis ta sake duban su Jafar da kyau ta ce, "Ya akai gaba dayansu suka kubuta daga sharrin kwarin annoba?" Zalkum ya ce, "Haba! Ummata ai ba haka ake saukar baki ba, da zuwansu a hau su da tambayoyi. Ya kamata a ce ko dan ruwa mun ba su sun sha." Fatalis ta yi murmushi, sannan ta ce da su Jafar, "Ku yi hakuri ku shigo ciki ku zauna." Cikin murna su Jafar suka karaso cikin tafkeken falon mai đauke da wasu manyan kujeru wadanda aka kerars su da zallan karfen murjani. Koda Gulzum ya zauna akan daya daga cikin kujerun sai ya zama dan tsugut kamar dantsako a cikin keji. Koda ganin haka sai Jafar ya ki zama akan kujerar ya zauna a kasa. Yelisa ta dube shi ta ce, "Haba Jafar ya za kai mana kauyanci ne?" Jafar yai murmushi ya ce, "Yelisa kenan ba kya ganin yadda Malam babba ya zama kamar sauro ne akan kujerar, mu kuwa ai sai mu zama kamar kwayar zarra." Mu hadu a part B don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MIFTAHUZZARBIL**💥💥 LITTAFI NA DAYA✍️✍️ PART B ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY ✍️ Ina maku barka da juma'a fatan kunyi Sallah lafiya, to Allah ya sadamu da Alkhairan dake cikin wannan rana ya Kuma kare mu daga dukkan sharri na halitta 🙏🙏 Marubucin littafin ya ci gaba da cewa.... Jafar yai murmushi ya ce, "Yelisa kenan ba kya ganin yadda Malam babba ya zama kamar sauro ne akan kujerar, mu kuwa ai sai mu zama kamar kwayar zarra." Yelisa ta yi dariya Sannan ta je ta zauna kusa da Jafar, haka ma su Mazalish suka zo kusa da su duk suka zauna. Shi kuwa Gulzum sai ya kama muzurai yana hararar Jafar. Zaman su ke da wuya Fatalis ta tafi ta bar su da Zalkum suna ta kalle-kalle cikin dakin, suna mamakin yadda aka gina gidan cikin matukar kawatuwa. Jim kadan sai ga Fatalis dauke da wani katon daro mai zurfi. Da farko dai su Jafar sun za ta bahon wanka ne ta kawo musu, amma da ta ajiye shi a gaban su sai suka ga babų komai a cike face gasasshen naman rago. Rago ne sukutum gaba dayansa, kuma ba irin ragon da suka saba gani ba nc a can ta su duniyar. Wannan ragon girmansa ya wuce misali. Fatalis ta dubi Gulzum ta ga duk yafi su Jafar auki sai ta ya gi cinya guda ta ragon ta mika masa. Koda ya sa hannu biyu ya karbi cinyar sai nauyin cinyar ya rinjaye shi ya fado daga kan kujerar da yake zaune. Su Jafar kuwa suka tuntsire da dariya. Fatalis da ZaIkum ma sai da suka yi dariya. Fatalis ta sake yago cinyar gaba ta ragon ta mikawa su Jafar. Nan suma suka kama kokowa da naman domin ko rabin-rabinsa ba su iya cinyewa ba. Shi kuwa Zalkum da ya sanya hannunsa cikin kwanon sai ya gutsuro gaba dayan rabin ragon ya kama ci kamar mutum ya dauki cinyar kaza yana ci. Jafar ya sake bushewa da dariya ya ce, "Kai jama'a wanda duk bai yi yawo ba a duniya, hakika ya yí asarar kallo. Yau fa gamu a duniyar da mutane suka fi aljanu girma da karfi." Bayan su Jafar sun ci, sun sha, sun yi hani'an. Sai Fatalis ta dube su ta ce, "Ya ku wadannan baki kun ga irin masifar da ta addabe mu a garin nan, A sanadiyar wannan masifa ne na rasa iyayena, mijina da dangina kaf. Babu abin da yai saura a gareni face ɗana Zalkum. Ina mai roko a gareku da idan kuna da wata dabara da za ku yi, ku yi don ku magance mana wannan masifa." Yayin da Fatalis ta zo nan a zancenta sai su Jafar suka dubi junansu suka yi shiru aka rasa wanda zai ce kala. Daga bisani sai Yalisa ta dubi Mazalish ta ce, To ke uwar hikima wannan fagen fa naki ne me za ki ce?" Mazalısh ta yì murmushı ta ce, "Tabbas ina da dabara, kuma in dai aka yi abin da na cc a yi sai an yi maganin kwarin nan, amma fa dole ne a sallama rayuwar daruruwan mutane wadanda za'a dana tarko da su." Cikin alamun mamaki Fatalis ta dubi Mazalish cikin yanayin mamaki ta ce, "Wane irin tarko kike nufi? Mazalish ta ce. "Duk abin da zan fadi yanzu ba za ki fahimta ba, face an yi a aika ce. Yanzu ina son na yi miki wasu 'yan tambayoyi gudu uku sai ki bani amsarsu, sannan mu aiwatar da shirin hallakar da kwarin nan na annoba. Tambaya ta farko ita ce: shin a garin nan kuna da manyan duwatsun wuta kuwa?" Fatalis ta ce, "Kwarai kuwa muna da su a can bayan gari, kuma adadin su ma ya wuce kima." Mazalish ta ce, "Yauwa da kyau. Tambaya ta biyu kuna da kayan kira kuwa?" "Duk duniya babu wani gari da ya fi mu iya sarrafa karfe." In ji Fatalis. Mäzalish ta kara cewa, "Ya yi kyau. To ga tambaya ta karshe. Za ki iya tara mini karti guda miliyan daya, wadanda za su yi mini wani aiki?" Koda jin wannan tambaya sai Fatalis ta yi murmushi ta ce, "Idan ma kina bukatar karti miliyan dari za ki samu." Mazalish ta yi murmushi ta ce, "Abin nema ya samu. Yanzu ina son ku kai ni inda makerar ku take, idan mun je zan ware abubuwan da za mu yi amfani da su," Falalis ta yi murmushi ta ce, "An gama." Nan take Fatalis ta juya ta shiga cikin wani daki. Jim kadan ta fito a cikin shiri, domin har ma ta sauya tufafin jikinta, sannan ta dauko wani kaho mai kama da algaita. Fatalis ta kama hannun danta Zalkum, sannan ta dubi su Mazalish ta ce, "Ku biyo mu, mu tafi." Ba tare da kara cewa komai ba ta falfala da gudu suma su Jafar suka tayata. Haka dai suka yi ta gudu, har suka zo tsakiyar garin, sannan suka tsaya a wani makeken fili. Tsayawarsu ke da wuya sai Fatalis ta sa kahon nan a bakinta, ta busha shi ya fitar da wani irin sauti wanda ya cika garin gaba daya da amsa kuwa. Faruwar hakan ke da wuya sai ga dubun nan jama'a na ta rugowa wajen kai ka ce za su iya cika duniya gaba daya saboda tsananin yawansu. Al'amarin da yai matukar bai wa su Jafar mamaki kenan suka rude. Jafar ya dubi Yelisa ya ce, "Yanzu duk yawan mutanen da kwarin nan suka kashe ashe akwai ragowar su haka? Na rantse da darajar gemun ubana gaba dayan mutanen bimin Sin ba su kai rabin wannan al'ummar ba." Yalisa ta dube shi ta ce, "Kwarai kuwa, kuma ka ga an ce a duniyar mu babu wata kasa mai yawan jama'a kamar birnin Sin." Kafin cikar sa'a guda filin nan ya cika ya batse da mutane ko'ina ka duba su ne babu masakar tsinke. Fatalis ta daga wannan kaho da ke hannunta sama sai aka yi shiru kamar babu wani abu mai numfashi a wajen. Sannan ta ce, "Ya ku jama'ar wannan gari ku yi sani cewa; ban taraku anan don komai ba, face don na yi muku albishir da cewa yau mun samu bakin halittu wadanda za su yi mana maganin kwarin annoba, kuma ga su nan tare da ni." Nan take Fatalis ta ajiye kahon da ke hannunta ta kwashi su Jafar su duka shidan da hannu biyu ta daga su sama, kowa ya gan su. Nan fa wuri ya kaure da shewa da tafi, wasu kuma suka hau tsaki da da surutai suna cewa, "Ai wannan Zancen banza ne, ya zai a ce wadannan kananan halittun ne za su iya maganin kwarin annoba, wadanda ba su fi mu talitse su ba da kafa daya. Kamar Fatalis ta ji abin da wasu ke fadi sai ta ajiye su Jafar kasa a hankali, sannan ta ce, "Yaku ahalil Asgarwa kada ku yi mamaki akan cewa wadannan mutane za su iya taimakon mu, domin ita busira da hikima baiwa ce ba wai karfi ba ne, ko girmna A halin yanzu suna bukatar karti majiya karti mutum miliyan daya." Ba tare da wata hayaniya ba ko turmutsutsu sai karti miliyan daya suka ware kansu, gefe daya tamkar kirgarsu aka yi. Daya bai karu, ko ya ragu ba. Al'amarin da ya jefa su Jafar cikin mamaki kenan, don sun san cewa idan a ta su duniyar ne haka ba zai ta taba faru ba, sai dai idan harkar tsafi ce. Koda karti miliyan daya suka ware kan su sai Fatalis ta wuce gaba tare da su Jafar, sannan kartin guda miliyan daya suka bi su a baya. Nan fa suka yi ta tafiya har suka iso inda makerar garin take. Wohoho! Anan ne fa aka kure iyayen son kallo su Jafar, domin sai da suka yaji da ganin abubuwan al'ajabi. Duk wani abu da mutum ya sani ana yi don amfunin yau da kullum akwai shi a wannan makera, kuma da karfe zallah aka kera shi. Kayan aiki kuwa ga su nan birjik kala-kala sun fi gaban lissafi. Awannan lokaci ne su Jafar suka tuno da makerar nan ta garin sarki Azbir suka ga kamar shago daya ne a cikin katon gida, akan wannan makera. Jafar ya dubi sarki Azbir ya ce "Ina ma mutanenka zasu zo nan su yi kallo da sun san cewa sun cewa su Almajirai ne a fannin kira." Sarki Azbir yayi murmushi ya ce ai basu kai matsayin almajirai bama, domin almajiri ya fara samun ilimi, sai dai a kirasu jahilai. Ai wannan makera ita ce gagara gasa. Tun sa'adda suka shiga wannan nakera Mazalish ta nutsu tana kallon kayyyakin aikin. Duk abin da taga tana da muradi sai ta bada umarnin a dauko shi. Haka dai suka yi ta yawo a cikin makerar wadda girmanta ya kusa kai na gari guda. Sai da suka shafe sa'a hudu suna yawo a cikinta, amma ba su kai karshenta ba. A haka dai suka hada kayan aiki guda miliyan daya da rabi. Daga nan sai Mazalish ta sa aka ware mata wasu kwararru makera guda miliyan daya, sannan aka dunguma gaba daya aka tafi bayan gari, inda manyan duwatsun wuta suke. Da zuwa sai Mazalish ta sa aka kawo mata tawwada da alkalami da kuma takarda ta zana taswirar wani abu mai siffar kwai, amma cikinsa a rarake yake, kuma zanen wannan taswirar sai ta nunawa makeran nan ta ce da su, "Kun ga wannan surar da na zana, to ita nake son ku yi, amma da manyan duwatsun can, ma'ana ku fafe su ku yi musu siffar kwai, kuma ina son idan kun raba tsakiyarsu ku yi wa bakunan su yankan hakora, kamar na karfen wili, yadda idan aka hade su za su kulle kan su. Za'a daura doguwar, murtukekiyar sarka a jikin surar, amma ita ma ta duwatsu wacce za'a ja ta zuwa cikin kogunan dutse yadda mutane za su kamata su ja su hade surar ta rufe. Wannan sura ina son a kera guda miliyan dubu daya kafin nan da ketowar alfijir. kuma a kwashe su a kai su cikin gari har da wandan duwatsun guda miliyan dubu." Koda jin wanna batu sai Yelisa ta dakawa Mazalish tsawa ta ce, 'Amma dai ba ki da hankali ta ya ya za'a iya wannan aikin a cikin wannan lokaci da kika diba? Kuma koma an yi babu fa wanda ya gane abin da kike shirin yi." Fatalis ta yi murmushi ta ce, "Ni na gane dukkanin manufarta, ku saurareni da kyau na wayar mu ku da kai. Ba wani abu Mazalish ta ke Son a kera mata ba. face sundukin dutse, mai siffar kwai, wanda zaa yanka tsakiyarsa ya zamana za'a iya bude shi da rufe shi. Tana so ne a kera sundukin guda miliyan dubu daya. Shi dai wannan sunduki za a bar shi ne a bude kuma a sanya tsirarun mutane a ciki. ldan kwarin Annobar suka zo, za su cika cikin sundukin idan suka ga mutane a ciki. Da zarar sun shiga cike sai a bane su a ciki, kun ga kenan an rufe su ruf babu hanyar fita, wato an kama su. Wadannan mutanen da suka ci na cikin sundukin sune iyakar rabonsu." Koda Fatalis ta zo nan a bayaninta sai jama'a suka sake rudewa da sowa suna masu yiwa Mazalısh jinjina bisa wannan hikima tata. Duk da cewar Yelisa na yin adawa da Mazalish, wannan karon dai ita ma sai da ta yi mata jinjina, domin hikimar ta kai hikima. Cikin gaggawa aka kwashi kayan aiki da ma'aikatar aka hau aiki ba ji ba gani. Mazalish ta yi ta kewaye ma'aikatan tana kula da aikinsu duk inda ta ga gyara ta gyara masu. Nan fa su Jafar suka cika da mamakin sauri da kuma zafin naman wadannan mutane. Ai kuwa kafin raná ta fadi an kera sundukan dutse

Chapter 1 of 9