guda miliyan dubu daya tare da sarkokin da za'a daura a jikisu. Ana gamawa aka kwashe sundukan gaba daya aka kai su wurare daban-daban a cikin gari aka ajiye. Lokacin da aka kammala wannan aiki dare ya raba. A wannan lokaci su Jafar sun gaji likis duk da cewar ba su yi aikin komai ba face kai komo. A cikin wannan dare aka ware mutanen da za'a zuba a cikin sundukan dutsen don yin tarko da su. Abin mamakin shi ne mutanen ne suke kawo kan su saboda tsananin kishin kai da kuma kishin
iyalansu, ma'ana sun gwammace su sadaukar da rayuwarsu, da dai wannan kwarin annoba su ci gaba da zuwa suna yi musu barma. Babu wanda ya kwanta barci sai da aka gama wanna shiri tsaf. Ko'ina ka duba a fadin garin duwatse ne masu koguna. Gaba daya jama'ar garin suka shishshige cikin kogunan duwatsun suka rurrufe kan su.
Yayin da gari ya waye lokacin zuwan Kwarin annoba ya yi sai aka kasa kunne anan jiran a ji motsin. ldan ka dau ke mutanen da aka yi tarko da su a cikin sundukin dutse babu wani abu mai rai wanda yake motst a garin.
Bayan kamar abin sa'a sararin samaniya ta cika da kwarin nan suka fara saukowa kawa. Koda suka ga mutane a cikin kwanson dutse sai suka afkanmusu da ci. Nan fa ihun mutane da kukan kwarin ya cika gari.
Koda jin wannan hayaniya sai mutanen da ke rike da dogayen sarkokin nan na dutse suka jajja.
Nan take sundukan duwatsu suka rurrufe bam, ya zamana an kama gaba dayan kwarin nan a cikin sundukan dutsen. Abin da ya nuna alamar hakan kuwa shi ne: an daina jin kukan kwarin a lokaci guda. Cikin tsananin mamaki mutane suka firfito daga kogunan duwatsu a gurguje. Nan fa gari ya cika da sowa. Masu kida na yi masu rawa na yi, su ma su Jafar sai suka fito suka taya su murna.
Nan take Fatalis ta daga su Jafar su duka shidan zuwa sama jama'a suka yi ta yi musu jinjina.
Ana cikin tsakiyar wannan farin ciki ne wani kwaron annoba guda daya kacal ya sauko kasa daga can kololuwar saman a cikin tsananin gudu. Sai da kowa ya ga wannan Kwaro amma kafin a tarwatse tuni kwaron ya cafko jafar, Yelisa, Gulzum, Mashrila, Mazalish da sarki Azbir, ya daga da su sama. Kafin kiftawar ido ya kule da su a cikin gajimare. Su kuwa mutanen birmin Asgawara sai suka kama ihu da guje-guje, gaba daya garin ya hautsine.
Al'amarin su Jafar kuwa ba su ankara ba, sai gani suka yi an watso su cikin ta su duniyar ta cikin kundin tsatsuba an yarbar da su a gaban littafin Kundi Tsatsuba har yanzu shafe na ashirin da daya ne a bude. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar, bayan sun kubuta daga cikin sundukin haske na sarki Azmil Galar, sabon matsafin da ke son hallakar da duniyoyin Kasa gaba daya, kuma shi ne wanda ke son kera kubar Muftahhul Zarbil musamman, don ya rufe nasa kundin Tsatsuba da ke ajiye a fadarsa mai suna Saukatul Askur.
A can fadar sarki Muzuluch kuwa; na birnin Sin ba a sake zama ba a fada sai kashe gari. Tun da duku-dukun safiya Ruziyal, Rafkanagu da Hajarul Mukurus suka baro masaukinsu suka taho fada. Saboda zumudi ko karya kumallo ba su yi ba. Da suka zo kuwa suka iske fadar wayam babu kowa, face masu gadi Sai da suka yi zaman jira na sa'a biyar, sannan fada ta cika sarki Muzuluch ya fito daga cikin gida.
Cikin hanzari kowa ya mike tsaye har sai da sarki ya zauna akan karagar mulki, sannan kowa ya zauna. Daga nan jama'a suka kwashi gaisuwa su Ruziyal ne suka gaida sarki daga karshe.
Sarki Muzuluch ya dubi su Ruziyal ya bushe da dariya, sannan ya ce, "Ya ku manyan bakina ku yi sani cewa labari ya riskeni cewa tun da asuba kuka zo nan, ku ka zauna saboda dokin jin ci gaban hikayar bawa Mozur da gimbiya Suhaila."
Hajarul Mukurus ya risina ya ce, "Wannan gaskiya ne ya sarkin sarakai. Ni kam jiya bayan mun bar nan fada ban iya runtsawa ba saboda tunanin wannan labari. Da na rufe idona sai na ga hoton jaririn da Suhaila ta haifa mai kama da bawa Mozur."
Ruziyal ya ce, "Ni kuwa aiyanawa na dunga yi a raina ga jinjirin nan ya fara girma har ya zama saurayi."
Shi kuwa tsoho Rafkanagu sai ya ce, "Ni kumá a mafarki na ga ana ta gwabza yaki tsakanin bawa Mozur da mutanen gimbiya Suhaila."
Mu hadu a part C don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MIFTAHUZZARBIL**💥💥
LITTAFI NA DAYA ✍️✍️
PART C ❤️❤️
NA:. ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD KT☝️
TYPING: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY ✍️✍️
MARUBUCIN LITTAFIN YACI GABA DA CEWA...
Shi kuwa tsoho Rafkanagu sai ya ce, "Ni kumá a mafarki na ga ana ta gwabza yaki tsakanin bawa Mozur da mutanen gimbiya Suhaila."
Koda jin wadannan batutuwa sai sarki Muzulush ya sake bushewa da dariya ya ce, "Kun yi kidanku, kun yi rawarku. Amma dai koma menene yanzu ne za ku ji karashen wannan hikaya mai sosa zuciya, gami da ban al'ajabi.
Ina son ku nutsu kubini a sannu dan ku fahimci labarin sosai yadda idan na kare za ku iya yi mini tambayoyi na ba ku amsa." Sarki Muzuluch yai gyaran murya, sannan ya ci gaba da labari kamar haka....
"Lokacin da gimbiya Suhaila ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya, sakamakon ganin jaririn da ta haifa mai tsakanin kama da bawa Mozur, sai sarki Mikdad ya tsallaketa da kafafunsa bai tsaya ya kula da ita ba, bare ya damu da lafiyarta. Kawai sai ya nufi inda jinjirin ke kishingide yana ta tsala kuka. Da zuwa ya dauki jaririn cikin matukar farin ciki ya daga sama yana kallon fuskarsa. Take jaririn yai shiru ya daina kuka, kuma ya kama yiwa sarki Mikdad murmushi. Al'amarin da ya kara sa zuciyar sa Mikdad ta yi sanyi kenan. Ya ji farin ciki ya sake lullube shi. Su kuwa kuyangin da ke tsaye a wajen sai suka cika da mamakin abin da sarki ya yi, na halin ko in kula ga matar sa, wacce ta fadi kasa sumammiya. Tsawon 'yan dakiku sarki Mikdad na ta wasa da jariri yana jujjuya shi a hannu, sai gimbiya Suhaila ta farfado daga dogon suman da ta yi.
Koda ta yi arba da sarki Mikdad rungume da jariri cikin alamun farin ciki sa ta mike zumbur ta rugo garc shi da nufin fisge jaririn daga hannunsa, amma sai Sarki Mikadad ya goce ta kama iska ta fadi kasa. Kawai sai Mikdad ya yi wa kuyangin nan nuni da su fita su ba su wuri.
Cikin biyayya da gaggawa kuyangin suka fice gaba daya, suka rufe kofar dakin. Sannan Mikdad ya dubi Suhaila wacce ke zauna a kas dirshan ya ce, "Me za ki yi da dan, idan kin karbc shi daga hannuna?"
Suhaila ta ce, "Yanka shi zan yi, ko kuma na jefa shi cikin rijiya, don na huta da takaici."
Koda jin wannan batu sai sarki Mikdad ya murtuke fuska ya ce, "Yake matata ki yi sani cewa kin dade, kina zaluntata. Tun da na aurcki kika dakushe mini farin cikin rayuwata. Kin rabani da kwarjinina a cikin mutanena, kuma kin rabani da babban masoyina bawa Mozur, hakazalika kin maida ni tamkar rakumi da akala sai yadda aka yi da shi. Na yi hakuri da duk wannan hali da kika jcfa ni ciki, duk saboda kawai ina sonki, amma in so ki sani cewa a yanzu ba zan iya yin hakuri ki rabani da wannan dan wanda shi ne kadai zai đebe mini kewar masoyina bawa Mozur ba. Ina mai tunasar da ke cewa taba lafiyar wannan jariri a gareki na da matukar hadari, domin ya kasance dan baiwa, dan da aka samu cikinsa ranar bikin bautar maigirma Lazzatul Sakaru."
Yayin da sarki Mikdad ya zo nan a zancensa, sai gimbiya Suhaila ta fashe da kuka, sannan ta mike tsaye ta ce, Ya kai mijina ka yi sani cewa ko me zai same ni ba zan ji tsoro ba, har naga na kashe wannan jaririn. Ni kam da dai na zauna da wannan abin kunya, wato samun ciki da bawa, bawann ma wanda na tsana fiye da komai a rayuwa ta ta duniya, gwara rayuwata ta salwanta. Na rantse da darajar iyaycna in dai na gaji sarauta gaba da baya sai na ida nufina akan wannan jariri. Zai fi kyau a gareka ka rungumi kaddara ka bani jaririn nan yanzu na yi gutsun-gutsun da shi."
Cikin fushi sarki Mikdad ya dakawa Suhaila tsawa. Al'amarin da ya matukar ba ta mamake kenan, domin tun da ta aure shi ko bakar magana bai taba gaya mata ba. Kullum lalaminta yake, yana tausarta; kuma duk abin da ta ke so dole ya so shi, amma yau sai ga shi har yana da ka matsa tsawa. Sarki Mikdad ya ce, "Idan har kina son ki kashe wannan jariri, to sai kin fara kasheni, domin muddin ina nufashi a doron kasa ba za ki samu dama ba. Ina son wannan jariri fiye da yadda nake son iyayena, 'yan'uwana, mulkina da dukiyata. Haka kuma inan son sa fiye da yadda nake son kaina, don haka zan iya sallama rayuwata dominsa...
Kafin sarki Mikdad ya gama rufe bakinsa tuni Suhaila ta zare wata siririyar wuka da ke nutse a cikin tuffa ta rugo in da yake. Da zuwa ta kaiwa jaririn suka a ciki. Cikin zafin namu sarki Mikdad ya gotar da jaririn. Ai kuwa sai wukar ta nutse a cikin kafadarsa. Sarki Mikdad ya juyo da hanunsa guda ya make Suhaila ta fadi kasa sumamiya. Ba tare da ya cire wukar da ke nutse a kafadarsa ba ya fice daga cikin dakin a fusace, jini na diga daga kafadar tasa.
Kai da ganí kasan cewu jarumi ne shi, mai matukar juriya. Da fitowar sarki' daga cikin dakin Suhaila sai ya sa aka kawo masa doki, ya kama ya hau yana rungume da jaririn da hannu daya. Nan fa ya sukwani dokin a guje yai ta tafiya izuwa cikin gari. Koda ganin wannan al'amari sai fadawansa suka ruđe, suka cika da mamaki, don tuni labari ya riske su cewa yau sarki ya make gimbiya Suhaila da hannunsa har ta fadi kasa sumammiya.
Sarki Mikdad ya ci gaba da tafiya akan doki rike da jariri. Bai tsaya a ko'ina ba sai gidan boka Zardish. Da zuwa ya kwankasa kofar gidan da karfi. Cikin sauri da fushi boka Zardish ya bude kofar, amma koda ya ga sarki ne sai ya risina. Yayin da kuma ya ga wuka a nutse a cikin jikin sarki jini na zuba, kuma ga jariri rungume a kafadarsa sai ya rude hankalinsa ya tashi. Ya ce, "Ya shugabana wanene ya yi maka wannan danyen aiki haka?"
Kafin sarki ya ce wani abu, sai boka Zardish ya sa hannu ya zare wukar daga cikin kafadar sarki, sannan ya shafi raunin jini ya tsaya cak, ya daina zuba. Daga nan sai ya dauko wani garin magani ya shafa masa akan raunin.
Sarki Mikdad ya nunawa boka Zardish fuskar jariri ya ce, "Da wa wannan yaro ya yi kama?"
Zardish va dubi jariri ya ce. "Wannan ai dan bawa Mozur ne, kuma matarka ce ta haife shi. Tu ni maigirma Lazzatul Sakaru ya sanar da ni wannan labari."
Sarki Mikdad ya yi murmushi, sannan ya ce "Ya kai wannan boka ka yi sani cewa mutata Suhaila ta kawowa wannan jariri farmaki, don ta kashe shi. A kokarin kare shi ne ta caka mani wannan wuka, ni kuma na maketa ta fadi kawa sumammiya. Yanzu haka na baro ta can kwance ban san halin da take ciki ba. Ka sani cewa nazo nan garc ba dan komai sai don kawai na nemi shawarar ka bisa yadda za mu tsare lafi wannan jariri."
Yayin da boka Zardishi ya ji wannan batu sai ya bushe da dariya. Sannan ya ce, "Ya shugabana ka je ka kwantar da hankalinka kamar tsumma a randa. Ka yi sani cewa wanna jariri dane' ga maigirma Lazzatul Sakaru, dan haka shi da kansa zai kare abinsa. Ko ruwa ko iska duk bala'in da za'a vi babu abin da zai samu wannan yaro, tabbas sai alkawari ya cika akansa wato sai ya girma ya zama gwarzon zamani kuma mai arzikin da babu kamarsa, in da za ka iya tunawa a baya can matarka ta sa an sanya bawa Mozur a cikin buhun fata an daure, sannan aka kai buhun tsakiyar teku aka jefa, don kawai a hallaka bawa Mozur, amma da yake cewa akwai jinin maigirma Lazzatul Sakaru a jikinsa sai da ya kubuta. Yadda aka yi kuwa ya kubutan shi ne Lazzatul Sakaru nc ya tursasa wani katon kifi ya hadiye buhun fatar nan tun kafin ya nutse a karkashin teku. Kifi na gama hadiyar aka janyo shi da karfin tsiya izuwa gabar teku aka bare bakinsa. Take kifin ya mutu, shi kuma Mozur ya farfado daga dogon suma ya fita daga cikinsa. A Sannan ne wasu masunta suka kawo masa dauki suka dawo da shi gari."
Koda boka Zardish ya zo nan a zancensa sai sarki yai shiru yana mai juya al'amarin a cikin rasa. Daga bisani sai yai ajiyar zuciya ya ce, "Hakika maganar ka gaskiya ce, kuma na aminta da ita: amma ka sani cewa na san halin matata Suhaila sani na hakika. Akan wannan al'amari za ta iya sauya abin bautarta, don haka ba zamu zuba ido ba kawai dole ne dai mu baiwa Wannan yaro tsaro na musamman."
Boka Zardish ya yi murmushi mai nuna yadda da kai ya ce "Ya shugabana ka yi sani cewa na yi imani da mai girma Lazzatul Sakaru, kuma na tabbatar da cewa babu wani ubangiji mai karfi irin na sa, Don haka ko dame Suhaila take takama ba ta isa ta ga bayan mu ba. Da wannan bayani nake fatan za ka cire shakkar
komai daga zuciyarka, ka mikawa mai girma Lazzatul Sakaru al'amarinka"
Sarki Mikdad ya yi murmushi ya ce, "Shikenan na barka lafiya sarkin bokayen duniya."
Nan take sarki Mikdad ya juya akalar dokinsa ya tafi. Bai zame ko'ina ba sai wani gidan gonarsa da ke bayan gari. A cikin wannan gidan gona akwai wata amintacciyar kuyangarsa mai suna Harisha. Harisha macece mai kyau, amma kyawunta bai kai rabin na gimbiya Suhaila ba. Shekarunta za su kai talatin da uku zuwa da hudu, kuma tafi shekara biyar a cikin wannan gidan gona na Sarki Mikdad.
Sarki Mikdad yana zuwa gareta sai sau daya a shekara, kuma akwai dakaru guda dubu goma ma su gadin wannan gidan gona mai dauke da shuke-shuken
'ya'yan itatuwa iri-iri da kuma bangaren da ake kiwon namun daji kala-kala.
Shi dai wannan gidan gona yana da matukar girma sosai, kuma duk wanda ya shige shi zai ji kamar an sashi cikin aljannar duniya, saboda abubuwan da aka tanada a cikinsa na jin dadin rayuwa.
Koda shigar sarki Mikdad cikin gidan gonar bisa kan doki dauke da jariri, sai Harisha ta hango shi. Cikin farin ciki ta rugo tana mai yi masa barka da zuwa fuskarta cike da annuri da kuma mnamakin zuwan sarki a wannan lokaci, domin ba lokacin da ya saba zuwa ba ne.
Marisha ta sa hannu biyu tu karbi jaririn, kawai sai taga ashe bakin fata ne, cikin damuwa ta ce, "Ya shugabana menene gamun ka da wannan jariri"
Sarki Mikdad ya sc, "Yake Harisha labari ne mai tsawo dangane da wannan tambaya takı. Mu je ciki domin mu zauna mu tattauna.
Nan take wani bawa ya kamawa sarki Mikdad dokin ya sauka yabi bayan kuyanga Harisha izuwa cikin wani gini da ke tsakiyar gidan gonar.
MU HADU A PART D DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MIFTAHUZZARBIL**💥💥
LITTAFI NA DAYA ✍️✍️
PART D ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🫅
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🏇
Typing: ABUBAKAR SALE ALQURAMEY ✍️
MARUBUCIN LITTAFIN YA CI GABA DA CEWA..
Sarki Mikdad ya sc, "Yake Harisha labari ne mai tsawo dangane da wannan tambaya takı. Mu je ciki domin mu zauna mu tattauna.
Nan take wani bawa ya kamawa sarki Mikdad dokin ya sauka yabi bayan kuyanga Harisha izuwa cikin wani gini da ke tsakiyar gidan gonar.
Shi kuwa bawan sai ya ja dokin sarki ya kai shi karkashin wata babbar rumfa inda aka ajiyc dawakai ya daure dokin a jikin turke.
Wannan gini da ke tsakiyar gidan gonar dogo ne, kuma faffada yana da bene, hawa uku; kuma akwai matattakala wacce mutum zai hau ta kai shi har hawa na ukun. Kai da ganin wannan gini ka san babu mai mallakarsa sai masarauci. Harisha ta wuce gaba sarki na biye da ita har suka hau kan matattakalar benen. Kuyangi da bayi na ta kai komo a cikin gidan. Duk wanda ya ga sarki sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa. A haka dai sarki Mikdad da Harisha suka isa hat hawa na uku, inda suka iske wani katon falo da dakuna barkatai. Shi dai wannan falo an kewaye shi da shimfida ta wani jan kilishi mai taushi da ban sha'awa, kuma an zuba wasu kujeru na alfarma a kansa. Kayan kyale-kyale kuwa gasu nan birjik. iri-iri. In banda kamshin turare babu abin da ke tashi a falon, akwai kuma wasu kananan kyawawan tsuntsaye a cikin 'yan kejina masu debe kewa.
Sannna Furanni, kuwa iri-iri suma gasu nan abin dai gwanin ban sha'awa.
Da shigarsu cikin wannan falo sai sarki ya...
Suhaila ta ce, "Ya kai Shaubil na umarce ka da ku yi hawa kai da sauran 'yan uwanka guda shida ku tafi izuwa gidan gonar sarki da ke can a bayan gari. Kada ku je gidan sai da tsakar dare duk yadda za ku yi, ku shiga gidan ba tare da an ganku ba, ku dangana da cikin turakar kuyanga Harish ku yi mata yankan rago, sannan ku sato mini jaririna don tabbas nasan yana hannunta. Idan har kuka yi nasara bisa hakan ni kuma zan cika muku al kawarin nan wanda nan yi muku, sa'ad da na turaku kashe bawa Mozur, ku ka kasa."
Koda jin haka sai Shaubil ya durkusa bisa gwiwarsa ta hangu, sannan ya kama hannun gimbiya Suhaila ya sumbaci yatsunta ya ce, "Na rantse da tsananin kyawun nan naki sai mun cika wannan buri naki. ldan kuwa muka dawo babu nasara na yarda kisa a tsireni."
Yayin da Suhaila ta ji wannan batu, sai ta cika da murna. Nan take ta sallami Shaubil ya je ya tattara 'yan uwansa mutum shida, wadanda da su ne Isham, Akib, Zaubatu, Huruza da kuma Marutu. Wadannan bayi guda shida sun kasance jaruman gaske, kuma marasa tausayi. Masana makirci da kula kaidi. Cikin kankanin lokaci suka yi shiri suka bar cikin birnin Shaukib, suka nausa cikin daji, don su tattauna yadda za su samu nasara bisa wannan gagarumin aikin dake gabansu. Kafin su tafi sai da gimbiya Suhaila ta sanar da cewa zata yi 'yar gajeriyar tafiya ta kwana daya da yini ɗaya, don haka koda sun dawo ba su iske ta ba, to tana so su ajiye mata wannan jariri a raye, kuma a boyayyen wuri, domin da hannunta take son kashe shi har lahira.
Bayan su Shaubil sun tafi, sai gimbiya Suhaila ta kimtsa ta tafi izuwa wani birni da ake kira Shuhurba. Tsakanin birnin Shaukib da birnin Shuhurba tafiya ce ta yini daya kacal. Ba wani abu ba ne zai kai gimbiya Suhaila birnin Shuhurba face ziyarar wani boka da ake kira Hazaru bin Udes.
Boka Hazaru bin Udes na bauta ne, ga wani azzalumin aljani wanda ake kira Zarbala. Aljani Zarbala ya yi kaurin suna a cikin al'ummar aljanu, saboda tsananin zaluncinsa, domin sai da ya zamana gaba daya aljanun garin su sun gudu daga garin aka barshi shi kadai. Ya kasance mai tsananin karfin damtse, kuma idan yana yaki yana iya yin kwana arba'in bai huta ba, kuma bai ji yunwa ko kishirwa. Shi kadai yana iya fada da kartin samarin aljanu guda dubu ya tarwatsa su ya karya na karyawa.
Komai karfin sarki da yawan mayakansa aljani Zarbala na iya yakarsa ya kashe shi, ya gajc komai nasa.
Lokacin da Zarbala ya ga ya tumbatsa a cikin kasashen aljanu, kuma duk abin da yake ncma ya samu sai ya fara tunanin hanyar da zaibi ya mallaki bi'adama. Ya zamana yana sarrafasu kamar yadda yake sarrafa aljanu, wannan dalili ne ya fara jarraba karfinsa a garuruwan mutane. Da farko ya je wata kasa da ake kira birnin Sablub, wanda shi wannan birni ya kasance na ma'abota addinin Musulunci ne, aiko ana sai da ya raina kansa don anan ne rabin jikin sa ya kone. Tun daga wannan rana bai kara marmarin farwa kasar bila'adama ba, sai ya hada kai da boka Fazaru bin Udes suka ci gaba da zaluncinsu akan al'umma.
Lokacin da gimbiya Suhaila ta isa gidan boka Hazaru sai ta iske shi a zaune cikin dakin tsafinsa ya tankwashe kafafunsa hannaycnsa makale a bayan hammatarsa kuma ya rufe idanunsa kamar yana sauraron wani.
Suhaila ta tsuguna a bayansa ba tare da tayi motsi ba, har ta bude ba ki za ta yi magana sai ta ga ya daga mata hannu, alamar ta yi shiru.
Al'amarin da ya yi matukar ba ta mamaki kenan domin ita dai ta san ba shi da idanu a bayan kcyarsa bare ya san da zuwanta. Sai da Hazaru ya gama abin da ta iske shi yana yi, Sannan ya juyo suka faskanci juna ya yi murmushi a gareta ya ce, "Lale marhaban da gimbiya Suhaila matar sarki Mikdad bin Masub na birnin Shaukib."
Hakika Wannan bayani ya bata mamaki domin ba ta taba zuwa ba wajcnsa. Bai san ta ba, ba ta san shi ba; amma tana jin labarinsa da kuma irin aiyukansa na ban mamaki.
Koda boka Hazaru ya fuskaci cewar gimbiya Suhaila ta tsinke da al'amarinsa sai ya bushe da dariya, sannan ya ce, "Yake wannan matar sarkin ki yi sani cewa muna daga nan muke sanin duk abubuwan da ke faruwa a ko'ina cikin duniya. Ba wani abu ne ke tafe da ke ba face matsalar jaririn da kika haifa sanadivar samun ciki da bawa Mozur.
Koda jin haka sai Suhaila ta zare idanu waje cikin kaduwa da kakkarwar jiki, har tana tuntuben harshe, ta ce "Kwarai kuwa abin da ya kawo wajenka kenan."
Boka Hazaru ya sake bushewa da dariya. Lokaci guda kuma ya turbune fuska, ya ce, "Yake Wannan matar sarki a halin yanzu ba ki da wani buri wanda yafi kıga kin kashe wannan jariri, don ki huta da takaici, abin kunya da kuma bakin ciki.
To ki yi sani cewa kin dauko babban aiki wanda ya yi daidai da ki aza ganmo akan ki ki yi niyar dora duniyar nan gaba daya akan ki"
Cikin mamaki Suhaila ta ce, "Ban gane abin da kake nufi ba? Kana so ka ce dani
wannan aiki ba zai yiyu ba ne?"
Boka Hazaru yai ajiyar zuciya ya ce "Hakika kin zo da tambayar da ban isa na amsa ta ba, sai dai na hada ki da ubanjina mai girma Zarbala. Ki yi sani cewa ba a iya ganin Zarbala kai tsaye sai da shiri. Na umarce ki da ki mike tsayc ki je gaban wancan tukunyar ki dangwalo jini a cikinta ki lashe."
Cikin fargaba Suhaila ta mike ta je wajen wata katuwar tukunyar kasa. Da zuwa ta iske tukunyar a cike da jini mai tsananin karni. Sai da Suhaila ta toshe hancinta, sannan ta dangwalo jinin cikin tukunyar ta lashe shi da kyar tana yamutsa fuska. Faruwar hakan ke da wuya dakin Boka Hazaru ya kama girgiza. Daga can sai wani katon aljani ya fado tsakiyar dakin da karfi kamar an jcho tsauni. Cikin razani Suhaila ta ja da baya kamar za ta ruga da gudu, amma sai boka Hazaru ya rukota da sauri ya durkusar da ita kasa. Nan take aljanin ya dago kai ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya mai kama da rurin tsohon zaki uban dawa.
Shi dai wannan aljani ya kasance katon gaske, kuma mummuna, mai ban tsoro. Rabin jikinsa gaba daya a kone yake, kwata-kwata baya amfani da bangaren. Kallo daya za ka yi masa ka tabbatar da cewa sadauki ne, domin kirar jarumta ta bayyana karara a jikinsa.
Boka Hazaru ya yi sujjada ga aljain, sannan ya ce, "Lale marhabin da dodon mutane da aljanu. Ga baiwarka gimbiya Suhaila ta zo neman taimako da wayewa akan matsalolinta.
Koda