Musulunci
da yamma an gama tabbatar da duk abin da ake
bukata na hujja gare shi, kotu ta yanke masa
bulala dari gobe.
Suna zaune suna hira da Malam Liman
suna sauraren rediyo, anan ne yaji sanarwar
batan da yayi. Sam bai damu ba domin yasan
mahaifinsa ne ya saka ayi wannan cigiyar, don
haka ya kudura a ransa ba zai koma gida ba har
sai ya gama jinyar bulalar da aka yi masa sannan
ne zai dawo gida kuma da zummar tonawa kansa
asiri.
"Allah Sarki, Allah Ya bayyanawa iyaycn
yaron nan shi, ace saurayi mai wannan shekarun
ya bata har yanzu ba a ganshi ba?"
168
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri
Kalaman Malam Liman su ne suka doki
kunnen Hameed daga barin dogon tunanin da ya
tafi.
"Malam Aminu ban ji ka ce amin ba, ko
baka ji sanarwar 6atan yaro saurayi mai irin
shekarun ka ba?"
Sunan da ya fada masa kenan ba don haka
ba da yanzu asirin sa ya tonu a yau din nan, don
cewa zai yi ya koma gida gurin iyayen sa don
hankalin su ya kwanta.
Cikin sauri ya ce, "Amin Baba, naji, to
abin ne dai sai addu'a, kowa da irin nashi
matsalar".
Sun jima suna hira, daga bisani ya tafi ya
barshi a gurin yana tunanin halin da zai shiga
gobe, amma idan ya tuna cewa a gurin Allah ya
yi (free) ba shi da wani tabo sai na Aziza sai ya
samu yaji wani farin ciki ya kama shi, domin ya
san shi din ma zata yafe masa idan ya je ya roke
ta ya gabatar da cewa shi ne ya yi mata haka.
Matukar ta yafe masa to ko kashe shi za ayi to
ayi tun da ya tarkaka.
169
Zuri'a Daya-I _Sa'adatu Muhammad Waziri
A ranar da ya cika kwana hudu a gidan a
ranar ne aka yi masa bulala dari cif, haka aka yi
masa a bainar jama'a ana kirgawa, tana cika aka
saka kabbara tare da ce masa Allah Ya yafe
masa.
Duk wanda ke gurin sai da ya yaba da
karfin zuciyar Hameed, domin ya nuna jarumta.
Malam Liman sai da ya zubar masa da
hawaye ba don komai ba sai don birge shi da ya
yi, da tsayawa da kafarsa ganin yaji kunyar
duniya d da ta lahira, da kuma dada yaba da ya
yi gurin dagewa da sai an fitar da hakkin Allah
akan sa.
Tabbas a wannan zamanin da za a samu
samari da suke da karfin imani da 'yan mata
wanda za su bayyana laifin da suke yi don ayi
musu hukunci da shari'ar Allah lallai da mun
samu saukin wannan masifu da suke addabar mu
cikin birane da kauyukа.
Ya Allah Ka kawo mana Karshen
wadannan rashin zaman lafiya da ya addabi 'yan
uwa Musulmi a duk inda muke a fadin duniyar
nan, Ka tona asirin dukkna azzalumai da suka
hana mana zaman lafiya a kasar mu, ameen.
170
3
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Suna fitowa daga gurin da aka yi masa
bulala a gurin ya fadi sumamme, hankalin Mal.
Liman ya yi mugun tashi, domin ya yi matukar
kaduwa ganin yadda yanayin sa ya koma, ko ina
cikin jikinsa shatin bulala ne rudu-rudu.
Ya jima can sai Allah Yasa ya farfado a
haka cikin taimakon Allah suna shirin barin
gurin nan ya sake yanke jiki ya fadi, jama'a da
dama a gurin sun yi zaton ya mutu, canz sai ya
soma numfashi.
A na cikin wannan halin sai ga wani
babban Alhaji ya zo da motar sa zai fita aka daga
masa hannu akan ya zo ya taimaka musu. Yana
zuwa gurin sai ya ga kamar ya gane fuskar sa,
dubawar nan da zai yi kuwa sai ya ga ya gane
fuskar sa, a kidime ya се.
"Subhanallahi! Wannan ai Hameed ne,
bayin Allah ku taimaka min na shigar da shi
motar na kai shi asibiti, ai danmu ne yau kwanan
sa hudu ba mu ganshi ba".
A rude yake maganar yana ta faman cewa
a taimaka masa, hade da cewa.
"Hameed me ya faru da kai haka?"
171
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Mal. Liman ya ce, "Alhaji naji kanaccwa
Hameed, wannan fa sunan sa Aminu".
Bai jira ya saurari abin da yake cewa ba
aka taimaka masa suka saka shi cikin motar,
Mal. Liman ne ya shiga suka ja suka tafi abinsu.
Arewa suka nufa cikin tashin hankali, a
hanya ne Mal. Liman yake cewa.
"Aminu ne fa sunan sa ba Hameed ba
ranka ya dade".
"Malam don Allah ka barni haka, ko ma
dai meye sunan da ya fada maka wannan yaro na
ne, kenan da sunana ya yi maka amfani? Ni ne
Aminun shi kuma Hameed. To wai Malam meye
ne ya faru da shi har ta kai shi ga zuwa kotu?
Kuma naga duk jikin sa da jini, hatsari suka yi
ne?"
Duk a gaggauce yake masa wadannan
tambayoyin.
"Alhaji amma dai ba kai ne mahaifinsa ba
ko?"
"Eh ba ni na haife shi ba dan yayana ne da
muke uba daya da shi, ni ne nake bin mahaifin sa
a gurin uban mu".
1
172
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Yauwa ko da naji, muje ga zuwa asibitin
mu yi kokarin ceto ransa, daga nan sai na sanar
da kai halin da akc ciki".
Yana rufe bakin sa sai gasu sun shiga
cikin asibitin, a gaggauce aka fito da shi aka
shiga ciki da shi, nan likitoci suka fara aiwatar
da abin da ya kawo su.
Tsananin rudani da tashin hankali ne suka
bayyana a fuskar Alh. Aminu lokacin da ya
gama sauraron bayanin da Mal. Liman yake yi
masa na game da abin da ya faru ga Hamced.
Tsabar takaici sai da hawaye suka zubo
masa ba don komai ba sai don jin cewa ashe
Hameed ne ya jefa su cikin wannan bakin cikin
da ga a daya ZURI'Ar su suke ciki na tsawon
kwanakin nan.
Mikewa ya yi zumbur уa сс, "Пamced ba
shi da wani amfani a gurin mu a yanzu, yaje shi
da mahaifin sa mun yafe su cikin ZURI'A tun da
abin nasu babu tsoron Allah a ciki.
Wato dama yaya Jafar shi ne ya batar da
dansa don kada kowa ya ganc me ya faru shi ne
zai zo ya tayar mana da hankali, bamu fita daga
wannan ba ya kara jefa mu cikin wani.
173
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Tunda ya ci amanarmu mu kuma za mu
nuna masa cewa bai isa ba, domin sai mun datse
duk wata igiyar DANGANTAKA da take
tsakanin mu da shi, yajc su kara. Dan nasa ya
mutu tunda abin na shi haka ne nima na tsame
hannuna akan al'amarin sa".
Yana gama fada ya juya zai tafi, da sauri
Mal. Liman ya saka hannu bibbiyu ya riko shi,
ya soma сewa.
"Haba Alh. Aminu, bai kamata ka yanke
wannan hukuncin ba lokaci guda, shi komai na
duniya dan hakuri ne, duk abin da kayi hakuri
akansa to cikin yardar Allah zai zamo tarihi.
Ka tausayawa Hamed ka kuma duba
muhimmancin zumuncin Allah, idan kai ma kayi
haka kamar ka jagoranci cewa zumuncin ku ya
Kare".
Nan ya samu ya gaya masa duk abin da ya
faru da Hameed da mahaifin sa, ya kuma
tabbatar masa da cewa hakika Hamced ya yi laifi
ya kuma yi matukar nadamar abin da ya aikata
ba don mahaifinsa ya hana shi fadin cewa shi ne
ya aikata wannan laifin ba da tuni ya bayyana
muku kansa kun hukunta shi.
174
Zuri'a Daya-1 sa'adatu Muhammad Waziri
Sai da ya gama fada masa komai jikinsa
ya yi sanyi, nan take ya ji tausayin Hameed ya
kama shi, ya daina ganin laifin sa sosai akan na
mahaifin sa.
Babu abin da Mal. Liman ya boyewa Alh.
Aminu na game da labarin da Hamced ya fada
masa game da abin da ya faru da shi tun daga
ranar da abin ya faru har zuwa yau. =
Kwana biyu Hameed ya yi a gadon asibiti
bai san a wane hali yake ciki ba, Alh. Aminu ne
yake zaune da Mal. Liman suna jiyyar sa domin
babu wand aya fadawa cewa ya samu labarin
Hameed.
A rana ta uku ne ya dawo cikin hayyacin
sa, nan ne likitoci suke fada musu cewa ya kamu
da ciwon zuciya mai tsanani hade da ciwon
(ulcer) domin tsananin damuwar da yake ciki da
rashin cin abincin da yake yi.
Lokacin da Hameed ya dawo cikin
hayyacin sa da ya ga kawun sa a tare da shi ya
shiga rudani da mamakin ganinsa, nan ya shiga
kuka yana fada masa duk abin da ya faru da shi
tas, babu abin da bai fada masa ba.
175
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Bai wani mamaki ba domin ya samu duk
labarin gurin Mal. Liman, sai dai wani karin
baynin da ya yi masa a game da mahaifin sa nan
ya gaya masa ccwa don Allah Ya barshi ya
mutu, bai son komawa ya kara ganin Zuri'ar su.
Tausayin sa yaji sosai, ya ce ya daina kuka
kuma komai zai wuce insha Allah tunda ya yi
nadama, sai dai ya yi kokarin neman yafiyar
abin gurin yarinyar da mahaifinta, idan sun yafe
masa to ya yi (free) duniya da lahira tun da ya
fitar da hakkin Allah, idan sun yafe masa shi
kenan.
Zaune suke a falon ya gama labarta masa
halin da dansa Hameed yake ciki da kuma abin
da ya faru suka foye musu.
Zufa ce ta zubo masa, nan da nan hankalin
sa ya yi matukar tashi, ya mike tsaye ya yi saurin
dawowa gurinsa ya zauna kusa da shi, cikin
kidimewa ya ce.
"Aminu ka daure ka rufa mana asiri,
matukar babu wanda ya sani don Allah ka rufe
maganar nan a gurin nan, domin kada mu tozarta
ni da iyalina a cikin Zuri'a".
176
Zuri'a Dayo-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Ran Alh. Aminu ya yi mugun baci, ya cе.
"Haba Yaya, wai kai me yasa ka fiyc son
kanka ne? Kai komai kanka ka sani, baka son
farin cikin kowa sai naka da na iyalinka. Ka tuna
cewa uban yarinyar nan ya yi matukar yarda da
kai da danka, amma ace kai da kanka kasan abin
nan bayan ya faru amma ka ki ka je ka fada
masa da kanka, ka ce kuma wani ba zai je ya
fada masa. Yaron da kansa yana son ya fada
masa amma ka hana shi don kada ka tozarta,
amma kai danka ya tozarta tasu, to shin wannan
a ganinka shi ne Zumunci ko halacci?"
"Aminu wallahi nima ban yi farin ciki da
faruwar hakan ba, har yanzu ina jin bakin cikin
faruwar wannan al'amarin".
"Ban yarda ba, idan har abin nan bai yi
maka dadi ba to kamata ya yi ka hukunta
Hameed a idanun duniya, ka nunawa Zuri'ar ka
ccwa can cikin ka ya aikata ta'asa sai ka mika shi
ayi masa dukkan hukuncin da ya kamata, sannan
ka nuna kayi fushi da shi. Amma baka yi ba, don
son nuna kaunar da sai shi ne ya yi abin da ya
dacc.
177
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Don haka yau tun da komai ya zo kunne.
na da kaina zan je na sanar da kowa na Zuri'a din
nan yasan abin da danka ya yi mana".
Cikin sauri ya rike shi ganin ya mike zai
tafi, ya ce.
"Aminu ka tsaya ka saurare ni ka kuma
fahimce ni, wallahi ba a son raina haka ya faru
ba. Ina so don girman Allah ka rufa min asiri
kada kowa yasan mene ya faru, Aminu ka fadi
duk abin da kake so a duniyar nan ko mene ne
nayi maka alkawarin mallaka maka shi matukar
za ka rufa min asiri".
Juyowa ya yi yai maşa wani irin kallo na
rashin fahimta.
"Aminu ka daure ka rufa min asiri domin
zumuncin da yake tsakanin mu, wallahi ko me
kake so zan yi maka shi, ka fada das bakin ka".
"Jafar bani da abin da zaka iya bani, ka
barni na yi tafiya ta".
"Aminu don Allah jira ni na fito".
Yana fadin haka ya yi sauri ya shiga ya je
ya fito da tarin wani (files) ya zo ya ajje su gaban
sa, ya ce.
178
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
1
"Aminu ka zauna ka duba (company) na
ne da tarin manya-manyan filaye na ka zabi duk
abin da kake so na baka shi duniya da lahira
matukar zaka bar wannan sirrin tsakanin ni da
kai, hatta shi Hameed din ba zan so ya san
wannan sirrin ba, kai ko babban (company) na
kake so mutukar zaka tufa min asiri to a shirye
nake na baka shi yanzun nan zan saka hannu na
mallaka maka shi duk domin kada ka tozarta min
Hameed a idanun duniya".
Zaro idanu ya yi yana kallon sa cikin
mamaki, ya jinjina kalaman da yake masa
magana. Tabbas yasan girman wannan Company
din da suna da daukaka da ya yi a kasar nan,
domin da wannan komfanin Zuri'ar nan take ji da
shi, kuma nashi ne halak malak, babu kudinkowa, amma haka yake kokarin ganin ya sama
kuwa nasa Investment a ciki shi ne yake masa
maganar zai mallaka masa a matsayin toshiyar
baki. Nan take yaji yana son gasgata kunnen sa,
anya kuwa yaji abin da ya fada masa?
ba?"
"Aminu ko baka ji abin da na fada maka
Cikin sauri ya ce, " Company?"
179
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Eh shi nake fada matukar ka amince
zaka rufa min asiri to wallahi a shirye nake na
mallaka maka shi a yanzu cikin sirri".
Komawa ya yi ya zauna yana ajje
numfashi, ganin yanayin sa a haka sai yaji ya
fara samun nutsuwa don haka shima sai ya
zauna.
"Ba zan iya karbar wannan Company din
ba, domin ni kaina idan nayi haka na shiga
cikin tuhuma, don haka na yarda zan rufa maka
asiri, sai dai ka bani dukkan kananan
kamfanunuwan guda biyu na Lagos da na
Kaduna, idan kayi min haka nima zan fi samun
nutsuwadon babu wanda zai lura da haka, idan
ka amince to nima na amince ka dauko mu yi
yarjejeniya a yanzun nan".
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alh.
Jafar, cikin hanzari ya се.
"Wannan ba wani abin dimuwa bane, na
amnce matukar maganar ba ta fito ba shi
kenan, amma idan har ka kuskura magana ta
fito to dole ne ka dawo min da abu na".
180
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Hankalin sa a tashe yakc kallon Hamced
kwance kan gadon asibiti, tsananin tausayin
yaron nasa da kaunar sa su ne suka rufe shi
lokaci guda.
Hameed yana kallon mahaifin sa ya kau
da kai don baya son ganin sa, domin ya dauki
laifin hana shi sukuni da kwanciyar hankali
duk ya dora masa, domin da ya barshi ya fada
abin da ya aikata da duk hakan bai taso ba.
"Hameed ka cika kafiya da taurin kai, ka
kuwa san irin tashin hankalin da na shiga da
ban ganka ba, ashe kana cikin garin ka gama
rudar damu? To shi kenan yanzu ai kja huce
tun da kaje anyi maka bulalar ko?" Ya karasa
fada cikin kasa da muryar sa.
Runtse idanu yayi don bai son ganinsa,
-, haka ya karaci bayanin sa bai ce da shi komai
ba.
"Hameed ba Daddy dinka ne yake maka
magana ba ka rabu da shi?"
"Kawu me zan ce da shi bayan bai son
na samu nutsuwa cikin zuciya ta?"
181
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Alh. Aminu ya daka masa tsawa, ya ce,
"Hameed kana da hankali kuwa? Kasan me
kake fada kuwa? Mahaifinka ne fa?"
Cikin zubar hawaye ya ce, "Kawu to me
zan fada ban da haka? Matukar Daddy yana so
na ci gaba da rayuwa cikin walwala da farin
ciki to ya barni na je na wanke kaina gurin su
Abba, na fada musu cewa ni ne na cuci Aziza,
idan sun ji su yi min dukkan abin da idan suka
yi min zai zamo sun fauki fansar abin da nayi
musu.
Ko kuma shi da kansa yaje ya fada musu
cewa ni ne na aikata mata haka, tunda yanzu na
dan fara samun nutsuwa cikin raina a gurin
Allah na tsarkaka da laifin da nayi masa, don
haka ya zamar min dole suma na samu abin da
zai janyo nayi (free) a gurin su".
"Hameed baka da hankali, kana tunanin
akwai wani uba ko uwa da za su iya yafe maka
wannan laifin da tashin hankalin da ka saka su?
Idan kana tunanin za su yafe maka to kayi
karyha, gwara ka ja bakinka ka yi shiru tunda
Allah Shi Ya yafe maka". Cewar Alh. Jafar.
182
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Runtsc ido ya yi yana kokarin gyara
kwanciyar sa hade da datsc baki don zafin da
yakc ji a jikin sa.
Da sauri Alh. Jafar dya zo zai rike shi, ya
yi sauri ya daga hannu alamar kada ya taba shi.
Saroro suka yi suna kallon sa don abin
ya yi matukar bashi mamaki.
Hameed ya ce, "Daddy duk abin da kake
magana akai da gangan kake yin sa, ka sani
Allah Bai yafe hakkin wanda aka zalunta,
kawai son zuciya da son da kake min duk su ne
suka rufe maka ido, kana kallon gaskiya kake
kaucewa.
Dadddy, idan ba ka taimaka min gurin
Allah na tsira ba to me zaka yi min a duniyar
nan?" Ya fada yana mai kafe idanunsa akan
shi.
Jikin su ya yi sanyi, aka rasa mai iya
cewa komai cikin su.
"Kawu kai idan kana son na samu farin
ciki tun daz na fada maka komai kaje ka sanar
da su Abba su sani tun da shi Daddy ba zai iya
ba".
183
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Hamced naji, ka kwantar da hakalin ka
insha Allahu komai zai zo cikin sauki, muna
son abi komai a hankali don mu samu
zumuncin mu kada ya zo ya samu tangarda, abi
abin cikin kwanciyar rai da yardar Allah za mu
dai-dai ta yadda za'a fahimci juna".
"Shi kenan Kawu, ina jiran lokacin,
amma fa ba de dadewa ba. Ina son kafin a
sallame ni ku sanar da su don maiukar baku yi
min haka bą to ni da kaina zan je na fada musu
kamar yadda na kawo kaina kotun Musulunci
babu wanda ya sani to haka can ma zani ba tare
da kun sani ba".
Daga hannu ya yi ya dauke Hameed da
mari cikin kunar rai, sam ya manta a cikin
jinya yake. Cikin kaushin murya ya ce.
"Ranar kuwa da na tsine maka, na fitar
da kai daga jerin ahalina na har abada tun da
baka son rufin asirinmu, bayan wannan abin
duk din kada ka tozarta nake yinsa".
"Haba Yaya, me. ya yi zafi zhaka? Ko ka
manta a kwance yake bashi da lafiya ne?"
Huci yake yi kamar damisa, ya cе.
184
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Aminu ni yaron nan zai kawo wa
sakarcin banza don yana yin abu ina bin bayan
sa? Zo mu tafi, Allah Ya bashi sa'a yajc ya yi
duk abin da zai yi, ni kuma zai ga wane mataki
zan dauka akan sa".
Yana gama fadin haka ya sa kai ya fice
zuciyar sa na yi masa zafi, yana mamakin wai
Hameed dinsa ne ya zama haka.
Alh. Aminu tsaye gurin sa yana bashi
baki akan ya daina yi ma mahaifin sa taurin
kai, ya bi abin a hankali shi da kansa zai san
abin da zai yi.
Kuka Hameed ya fara yi, ya ce, "Kawu
ni kaina ba a son raina na fadawa Daddy zhaka
ba, nayi masa hakan ne don ya tsane ni ya
barni nayi abin da ya dace. Hakika nasan
saboda son da yake min yake hana ni na je na
fada, to amma ya za ayi na ci gaba da rayuwa
da kunci a rayuwata da hakkin da ba a yafe
min ba? Don haka Kawu dole ne na fada musu
idan ku ba za ku iya ba".
185
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Hamced ka bar maganar nan tun da
mahaifin ka baya so, ka bari cikin ruwan sanyi
zan yi masa dole da kansa zamu je gurin su mu
fada musu".
Farin ciki ya kama shi, ya ce, "Kawu na
gode sosai, kuma don Allah ka bawa Daddy
hakuri, na san ya yi fishi da abin da na fada
masa".
"Kada ka damu, zan ganar da shi kuma
insha Allah komai zai zo cikin sauki".
* * *
A 'yan kwanakin nan kullum cikin tashin
hankali muke a cikin asibiti, domin Aziza
kullum cikin firgita take da yawan yin kara sai
dai kuma yanzu sam bata son ganin namiji a
gabanta ko ma wane, domin ta dinga shiga
razana dole ya zamo mu mata da likitoci mata
su ne muke kula da ita.
Haka abin ya ci gaba da tsorata mu har
muke tunanin cewa ko ta samu tabin hankali
ne, bayanan likitocin suka yi mana shi ne ya
soma kwantar mana da hankali na cewa yin
186
1
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
hakan na nuni da cewa tunanin ta ne yakc
kokarin dawowa, kuma cikin yardar Allah za
ayi nasara.
Ban da addu'a babu abin da muke yi
kullum, sannan haka muke haduwa akan Allah
Ya bayyana Hamced da batan da yayi.
Zaune muke muna hira domin samun
labari mai dadi da muke yi gurin likitoci na
cewa kada mu daga hankalin mu na rashin
tashin Aziza daga bacci na tsawon kwana uku,
tabbas suna tunanin nasara ce domin hakan
yana nuna cewa kwanyarta na diban hutu ne,
kuma da alamu idan Allah Ya farkar da ita ta
dawo cikin hankalin ta domin sun taba samun
hakan ya faru a cikin wannan asibitin.
Murna muka shiga yi don sai muke ji a
ranmu kamar ma taji sauki.
Kwanan Hameed goma sha uku da bata
har yanzu bamu samu labarin komai game da
batansa ba, haka dai muka ci gaba da addu'a.
Kwance nake kan katifar dake kusa da
gadon da Aziza take kwance, lokacin ni kadai
187
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
ce a gurinta nima na dan kishingida bacci ya
kwashe ni.
Ji nayi ana kiran sunana hade da
bubbuga ni, sai nake jin kamar a cikin mafarki.
Ina bude idanuna kawai sai naga Aziza zaune
kusa dani, da sauri na murtsike idanuna ina
kallon ta cikin kaduwa domin ban san dame ta
tashi ba, ta dawo cikin hayyacin ta ko har
yanzu tana nan yadda take?
Rike hannuna tayi ta ce, "Granny ni ce
kuwa? Shin mafarki nake yi ko gaske ne abin
da ya faru dani? Shin me ya faru dani na ganni
a asibiti?"
Rudewa nayi, murna- murna kuka-kuka,
na rike hannunta na ce.
"Aziza kin gane ni, ni ce ko?"
Hawaye ne ya ciko idanunta, ta ce,
"Granny abin da ya faru dani ba mafarki nayi
ba gaske ne ko? (Please) Granny ki fada min
don na gasgata abin da nake ji a raina".
"Shin Granny da gaske Yaya Hameed shi
ne ya yi sanadiyyar zuwa na asibitin nan ko dai
mafarkin nake yi?"
188
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammod Waziri
Ji rayi gabana ya yi matukar faduwa,
hankali na ya tashi, na се.
"Aziza me kike cewa dani ne? Fada min
me kike son fada ko me kika gani cikin
mafarkin ki?"
Hawaye ne suka shiga zubowa a
idanunta, ta ce.
"(Please) Granny na roke ki da ki fara
fada min me ya faru dani don Allah, domin na
fara gasgata wani abu cikin raina. (Please) da
gaske ba mafarki nake yi ba yaya Hameed shi
ne ya cuce ni ya bata min rayuwata har na zo
nan ko kuma mafarki nayi?"
Dafe kirji nayi na shiga salati, hawaye na
zubowa cikin idanuna na cе.
"Hakika wani abu ya faru da ke Aziza,
sai dai cikin mu babu wanda yasan wane ya yi
miki wani abu".
Kuka ta saka mai tsuma rai, nan da nan
tayi sauri ta rungume ni ta shiga kuka tana
cewa.
189
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Granny na shiga uku na lalace, yaya
Hameed ya cuce ni, shi ne ya hakke min.
Wayyo Allah Granny, ya cuce ni".
Kara rudewa nayi na kara kankame ta
nima ina kuka ina sakin salati, haka ta shiga
kuka tana bani labarin duk abin da ya faru da
ita.
Tun da ta fara bani labari nake zubar da
hawaye domin tsabar kaduwa da tausayin abin
da ya faru da ita, daga ni har ita kuka muke
tayi, domin na rasa abin da zan iya cewa da ita.
Haka Abban ku da Ammin ku suka shigo suka
iske mu a cikin wannan halin.
Gaban su ne ya fadi da suka hangi Aziza
kwance kan gwiwata, da sauri suka karaso
gurin, ya се.
"Umma me ya faru da Ammi na?"
Jin muryar mahaifin ta tayi sauri ta mike
tana ganinsa da sauri ta zo ta rungume shi tana
kuka tana cewa.
"Abba Ya Hameed ya cuce niya bata min
rayuwa ta".
190
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Bambarekwai yaji kalaman nata, domin
sam bai fahimci abin da yake faruwa da ita ba.
Nan da nan ya ji shi wani iri tarc da jin wani faduwar gaba ya zo masa.
Sauri ya yi ya rike hannayen ta ya raba ta
da jikinsa, ya dube ta sosai ya ce.
"Ammi na me kike cewa dani ne?"
Kuka ta kara sawa ta sake rungume shi,
kallon sa ya mayar gare ni cikin rudani nima
kukan ya gani ima yi.
A rude ya ce, "Umma wai me ke faruwa
ne? Shin Ammi na ta warke ne? Wai me yake
faruwa ne? Ni fa na rude naji tana kiran
Hameed, me Hameed din ya zo ya yi? Ko an
ganshi ne?"
"Abba gani, dama ba bata nayi ba".
Gaba dayan su suka juyo suka kalli
bakin kofar shigowa inda suka jiyo muryar sa.
Hameed ne tsaye bakin kofar yana mai
kokarin shigowa.
"Kada ka sake ka karaso nan gurin Ya
Hameed, na tsane ka, ba zan taba yafe maka
191
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
ba, macuci, azzalumi, mara tausayi. Wallahi sai
Allah Ya saka min abin da kayi min".
Tana fadin haka ta fashe da kuka tayi
sauri ta hangi wani kwalbar lemo ta dauka da
sauri ta je ta doka masa a goshin sa, nan take
jni ya wanke fusakar sa.
Kowa na gurin kasa motsi ya yhi, ana
tsaye ana kallon ikon Allah. Nan da nan
Mustaphra ya kara rudewa domin har yanzu bai
fuskanci inda suka dosa ba.
Hameed yana tsaye yana mamakin
furucin Aziza nan take ya gane cewa tunaninta
ya dawo, murmushin farin ciki ya yi mai tare
da takaici.
"Ammi meye haka kuma? Me yayan
naki ya yi miki haka har kika ji masa wannan
rauni haka?" Ya fada cikin tsawa.
Cikin kuka ta ce, "Abba bai kamata kayi
mini tsawa ba don baka gane abin da Ya
Hameed ya yi min ba".
Tana gama fadin haka sai ta fashe da
kuka, Aisha tana kuka.
192
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Abba ka bar Aziza tayi min duk abinda
ranta yake so matukar idan tayi hakan zai sa ta
huce ta yafe min abin da nayi mata. Abba ba
ita ya kamata ka yiwa tsawa ba ni ya kamata ka yiwa tsawa, kamar yadda ta kira ni macuc,
azzalumi hakan nake, kuma na yarda na amsa
sunan da ta bani, domin babu irin roko da
kukan da bata yi ba akan kada na cutar da ita
amma nayi burus da ita sai da na hakke mata.
Abba ku yafe min, ni ne na cutar da
rayuwar Aziza, na zbata mata rayuwar ta, don
haka ku yi min duk abin da za ku dauk fansa
akan abin da nayi muku".
Zaman