ya ce, "Granny me ta
ce? Fada min naji ko ta fadi wane ya yi mata
hakan".
94
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri.
"Kwantar da hankalin ka Abdulhameed,
bata iya fadin kowa ne sai dai ta kira suna na da
Abban ku akan wai mu taimake ta".
"Daga haka bata kara ccwa komai ba, ko
ta kara ce muku wani abu?"
"Gaskiya babu abinda naji ance ta ce
tunda ni bana gurin".
"Toh me likitan ya ce game da dawowar
tunanin ta? Shin ya fada zai dawo ko ya tafi gaba
daya?" Alh. Jafar ya fada yana kallo na.
Maryam ta ce, "Yaya bai dai ce komai ba
akan haka, mu dai fatan mu dai Allah Yasa ta
warke ras, ba ma fatan ta warke ta kuma tashi da
mantuwar tunanin, don yin haka ba karamin
nakasa ta samu ba, domin da ita da
nakashasshiya duk daya ne ko ma yafi".
Ya ja ajiyar zuciya, ya ce, "Gaskiya ne".
Na yi duba ga goshin Hameed da yake
daure da bandeji, na се.
"Abdulhameed mene ya faru da kai a
goshin ka haka?"
Dora hannun sa ya yi akan goshin ya shiga
inda-inda, ya mai da kallon sa ga mahaifin sa,
zuwa can ya yi karfin hali ya cе.
95
e
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
warke ko da tunaninta bai dawo ba ni zan zauna
da ita, ban damu da su wane suka yi mata haka
ba, zan so na rayu da 'yar uwata a haka, ni dai
ina sonta, zan kuma dauki dawainiyarta a haka".
Duk jikin mu ya yi sanyi ni da Maryam,
take naji hawaye sun zo min, na ce.
"Abdulhameed kai yaro ne, a matsayin
shekarun ka ha karatun ka ai ya yi wuri ace kana
da aure, kuma ga ta da lalura, shin ya zaka yi da
karatun ka?"
"Granny idan za a yarda na auri Aziza a
yanzu a cikin wannan halin zan iya hakura da
komai har karatun na tsaya na lura da rayuwar ta
saboda nasan na girma zan kuma iya kula da ita
don haka yanzu na fadawa Daddy haka ne shi
yasa muka zo nan tare domin ke kadai ce za ki
yarda da haka a aura min ita".
"Umma wannan haka yake, gaskiya ya
fada, ki daurc ki yarda da hakan".
"Jafar babu damuwa tun da ZURI'A
DAYA muke, babu wani abu da zai gagara a
ciki, amma ku dan yi hakuri ka ci gaba da
fahimtar Abdulhameed, insha Allahu shi ne zai
97
Zuri'a Daya-! Sa'adatu Muhammad Waziri
auri Aziza bayan ta ji sauki, amma dai mu jira
mu ga yadda hukuncin da Ubangiji zai zartar".
"Shi kenan, Allah Ya bata lafiya, bari mu
karasa gurin Mustapha din".
Haka suka mikc suka shiga cikin gurin da
aka kwantar da Aziza, nan suka hangeta kwance
iyayenta sun zagayc ta sai kuka suke yi, gata nan
gaban su kwance babu awani alamun tana motsi
a tare da ita.
Suka yi sallama suka shiga, da yake
lokacin ana barin na jiki su shiga don haka suka
shiga tare gaba dayan su.
Tsananin tausayi da dana sani su ne
bayyane a fuskar Hameed, bayan sun gaisa ne
iyaye duk suka fita suka bar Hameed a gurin,
dukawa ya yi ya riko hanunta, nan take hawaye
suka wanke masa idanu, cikin kuka ya fara cewa.
"Aziza na ki yafe min abin da nayi miki,
ban san ni azzalumi ne ba sai bayan na hakke
miki, Aziza na ban taba tunanin zan jefa rayuwar
ki cikin wannan halin ba sharrin zuciya da
shaidan su ne suka kai ni ga haka.
Aziza me yasa na kasa tausaya miki ban
cutar da ke ba bayan irin roko da hakurin da ki
98
Zuri'a Daya-1. Sa'adatu Muhammad Waziri
ka ba ni, amma tsabar rashin tausayina na manta
da cewa ke Aziza na cc?
Hakika na san ba zaki taba yafe min ba
har tsawon farshen rayuwar mu, na tsani kaina,
na tsani rayuwata gaba daya tun bayan faruwar
al'amarin nan, Aziza ina tsoro kada ace ni ne da
hannuna zan yi sanadin mutuwar ki.
Wayyo Allah! Ya Allah Ka yafe min, Ka
bawa Aziza na lafiya ta warke, ta yanke min duk
hukuncin da take so, domin na zama azzalumi
akan ta.
(Why) Daddy? Me yasa baka hukunta ni
ba da ku ka gane kai da Momi abin da na
aikatawa 'yar uwata, kanwata? Me yasa ba kwa
so duniya ta gane cewa ni ne na cutar da Aziza
na? Daddy me yasa ka nuna son kai bayan kasan
ban boye maka cewa ni ne na cutar da Aziza ba?
Ya Allah Ka kawo hanyar da asirina zai
tonu a gane ni ne, domin naji a yanzu gaba daya
na tsani rayuwata gaba daya".
Nan ya shiga sharfar hawayen sa, ya kara
damke hannun Aziza ya ce.
"Aziza na ina so Allah Ya baki lafiya ki
tona min asiri, kuma ba zan karyata ki ba, ba zan
99
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
musa miki ba, domin nasan na cucc ki, na cuci
kaina, na kuma cuci ZURI'Ar mu. Na zamo
mugu, mara imani.
Aziza bana so ki yafc min har sai an
hukunta ni dai dai da abin da na aikata miki, ko
da kuwa kashe ni shi ne mafita gare ni, idan haka
ya faru to sai ki yafe min. Yau na zo gare ki don
ki yafe min, ba zan taba barin asibitin nan ba har
sai Allah Ya baki lafiya kin sa an hukunta ni da
hannun ki sannan zan samu nutsuwa a cikin rai
na, amma nasan ni da farin ciki har karshen
rayuwata, domin tun ranar da abin nan ya faru na
rasa farin ciki na har abada.
Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah Ka bawa
Aziza na laifya, ta dawo kamar yadda take
rayuwa".
"Ameen Abdul, bar kukan haka kayi
hakuri da sanin Allah, zata samu sauki".
Zumbur ya yi ya yi sauri ya dago kansa da
ya kifa a jikin gadon yana kuka, ni ya gani da
sauri ya cе,
"Granny yaushe ki ka shigo ban ji zuwan
ki ba?"
100
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Na ce, "Shigowa ta kcnan naji kana
addu'ar Allah Ya bawa Azizan ka lafiya".
Da sauri ya zo ya rike kafafuna yana kuka
yana cewa.
"Granny ya zan yi da rayuwata? Ya zan yi
da raina? Granny ba zan iya jure ganin Aziza na
cikin wannan halin bame yasa haka ya faru da
rayuwar Aziza? Me yasa na...".
"Kai Hameed haukan me kake yi haka
zaka tsaya kana kuka? Maimakon kayi mata
addu'a shi ne zaka sa ta gaba kana kuka kamar
kukan ka ne zai bata lafiya?"
Shiru ya yi bai dago kansa ba domin ya gano
muryar mahaifinsa ne ta katse shi da shirin
tonawa kansa asiri da yayi niyya.
Nan ya karaso gurinsa ya kama shi ya
dago shi, ya ce.
"Haba Hameed, ka daina irinowannan
surutan kamar karamin yaro, ka ci gaba da yi
mata addu'a, hakan yasa bana son barin ka zuwa
nan gurin domin idan ka ganta kara ta da
hankalin ka kake yi, don haka ka zo mu koma
gida kai ma ka huta, kada ciwon kai ya kama
ka".
101
Zuri'a Daya-I _Sa'adatu Muhammad Waziri
"Daddy babu inda zan iya komawa tunda
Allah Yasa ka barni yau na zo to na zo kenan har
sai Aziza na taji sauki ta yanke min hukunci da
hannunta kan abin da nayi mata".
Gaba daya hankalin mu ya tashi jin irin
furucin da Hameed yayi, da sauri muka hada
baki da Mustapha muka ce.
"Hamced, me ka yiwa Azizan?"
Juyowa ya yi gare ni ya fara kuka, ya ce.
"Granny na yiwa, Aziza laifin da ba zata
yafe min ba, domin na bari wani ya zo ya cutar
da ita banzo na taimake ta ba, don haka nasan ba
zata taba yafe min ba. Nasan a lokacin da abin
zai faru ta kira suna na don na cece ta amma ban
zo ba, hakan yasa na ce nayi mata laifin da ba
zata taba yafe min ba".
Gaba dayan mu sai a lokacin ne muka yi
ajiyar zuciya, domin mun gano nufin sa.
Mustapha ya karaso gurin sa ya riko
hannayen sa biyu idanunsa sun ciko da hawaye,
ya ce.
"Hameed ba kai kadai ne Ammi na ba zata
yafewa ba har dani, tunda ban zo nima na cece ta
ba.
102
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Hameed ka saki ranka ka daina kuka, kaje
kana addu'a akan Allah Ya bawa Azizan ka
sauki, Ya kuma tona asirin wanda suka yi mata
haka.
Ka wuce ku je gida Daddyn ka ya yi min
bayanin komai game da burin ka don haka ban yi
maka alkawari ba, mu jira har sai ta ji sauki na
bata dukkan farin ciki a rayuwarta, na kawar
mata da dukkan wani kunci da damuwar da ta
shiga.
Sai naga farin ciki a fuskar ta sannan zan
yarda nayi mata maganar auren ka, amma ban da
yanzu. Hameed na yarda da kai, na yarda da
kaunar da kake yiwa 'yar uwarka, kuma ina da
yakinin zaka iya bata dukkan farin cikin da nake
hangowa zata samu a rayuwar ta, domin ba ka
gujeta ba bayan wannan iftila'in da ya faru gare
ta. Don haka na gode, na gode, ka wuce kuje
gida domin ni kaina ba zan jure ganinka cikin
tashin hankali ba".
"Abba kayi hakuri, nasan ban kyautawa
Aziza na ba da na bari haka ya faru da ita".
103
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Na ce Hameed kada ka karya mana zuciya, ka wuce ka tafi abin ka, inshaa Allah zata
ji sauki".
Daga nan bai sake cewa komai ba ya sa
kai ya fice yana share hawayen da suke zubo
masa, jikin Alh. Jafar a sanyayes ya biyo bayan
sa shima suka fice.
Yadda al'amarin ya faru tun baya, a
lokacin da Hameed ya gama biyan bukatar sa da
Aziza bayan irin rashin tausayin da ya nuna
mata, da rashin imani, tun tana neman dauki har
ta yi shiru domin karfinta da kuzarin ta duk sun
kare, tuni ta suma ta fita cikin hayyacin ta, amma
duk da haka bai sa ya kai ga tausaya mata ba.
Bayan ya dawo cikin hayyacin sa ne ya
shiga rudani da fargaba domin ganin irin jini da
yake fita a jikin ta, nan ya rude ya shiga jijjiga ta
amma ina! Babu wani sauran numfashi a jikinta,
nan ya dimauce ya ci gaba da jijjigata tare da
kiran sunanta, amma ina! babu wani motsi,
hakan ya saka ma ransa cewa ta mutu.
Da gudu ya mike ya zo ya fita daga gidan
cikin rudani, amma sai da ya yi taka tsantsan don
104
1
4
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
haka zai jefa kansa cikin wannan tashin hankalin
da bai yarda zuciyar sa ta ingiza shi ya gwada
mata wannan rashin imanin ba. Hannu yasa akan
sa yana cewa.
"Wayyo Allah na! Wayyo Aziza na, me
yasa na yardar ma zuciya ta na cuce ki, na manta
da ke da kuma kukan da naga kina yi kina
rokona? Idan kika mutu ban san ya zan yi da
rayuwa na ba, wallahi nayi nadama, naji na tsani
kaina, na tsani rayuwar gaba daya, Da na sani shi
ne abinda nayi ne a yanzu".
Tabbs hawaye rahama ne, sai yanzu ne
Hameed yaji dan wani sanyi cikin ransa dalilin
zubar hawayen nasa, haka ya zauna yana ta yin
kukan sa tare da aikin da na sani da ya zamo
keya. Haka ya wanzu cikin wannan ranar ya kasa
assasa komai, don yana zaune cikin dakin yana
ta aikin zubar da hawaye.
Yana jin lokacin da iyayen sa suka dawo
cikin tashin hankali suna tattauna wulakanci da
keta haddin da aka yi ma Aziza, ga rashin
tausayin da aka nuna mata.
Hankalin sa ya kara tashi, domin bai ji
sunce tana raye ko a mace ba. Haka suka zo suna
106
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
buga dakin na sa, tunanin su ko yana ciki ya
barci, domin sun san halinsa, haka suka shiga
bugawa amma shiru babu shi babu alamarsa.
Har cikin dare suka zo suna buga dakin
yana jinsu amma ya ki motsawa ko nan da can,
yana guri guda ya takure da an buga sai ya
takure ya rungume jiknsa, ban da aikin zubar
hawaye babu abin da yake yi na tarin nadamar abin da ya aikata.
Su kuma hankalin su ya tashi, suka shiga tunanin ina ya nufa a wannan rana? Domin bai
taba yin haka ba a rayuwar sa, haka suka hana kansu barci suka zo bakin dakinsa suka tsaya
suna jiran ganin ta yadda zai bullo.
Suna cikin haka sai suka ga an kashe
wutar dakin, da sauri suka zo suka shiga kiransa
da bubbuga kofar akan ya zo ya bude, amma
ina! Ya yi shiru ya ki motsawa daga inda yakc,
nan mahaifinsa yaje ya zaga ta (window) ya
hango shi can matsin gadon sa ya takure yana
kuka kamar mai jin sanyi. Nan ya shiga kiransa
amma takar ba da shi yake ba, haka ya hakura ya
dawo bakin kofar ya shiga buga masa kofar,
amma yayi fumfurus da shi.
107
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Ransa ya yi matukar 6aci, ya shiga yi
masa fada tare da zaginsa amma ina! Haka nan
ya hakura mahaifiyar sa itama ta soma nata
amma babu yadda suka yi, dole suka rabu da shi.
Sun yi-sun yi akan ya fada musu me ya
faru da shi yasa ya kulle dakinsa? Amma ya ki,
can da yaji sun daina motsi a gurin sai yaje ya
bude kofar ya nufo falo, nan ya iske su suna
zaune sun yi jigum. Sun ganshi amma ko
mikewa ba suyi ba, suka zuba masa ido, haka ya
karaso falon suka ga goshinsa da jini jaga-jaga,
da sauri Alh. Jafar ya mike zai nufe shi cikin
tashin hankali.
"Hameed me ya faru da kai haka?" Ya
fada cikin rudewa.
Cikin kunar rai Haj. Asiya ta ce, "Daddy
kada ka kuskura ka karasa gurin yaron nan,
domin gashi a bayyanc, zarginmu ya zama
gaske".
Cikin tsawa da 6acin rai ya juyo ya
kalleta, ya се.
"Asiya kin san irin mugun furucin da kike
yiwa dan da kika haifa a cikin kuwa? Don kawai
108
Zuri'a Daya-1 Sc'adatu Muhammad Waziri
zuciyar ki tana zargin wani abu sai kawai ki
zartar da hukunci kai tsaye?"
"Daddy idan har kuna zargina da wani abu
to haka ne, ni ne na aikata, ni ne na jcfa Aziza
cikin halin da take ciki yanzu".
Tasss! Ya dauke shi da wani wawan mari,
sai da ya ga (stars) suna masa yawo a cikin
idanunsa, ya yi sauri ya dafe kuncin sa, ya yi
taga-taga zai fadi.
"Kana da hankałi kuwa? Kasan abin da
kake fada min da bakin ka? Yaushe ka fara
hauka nc?"
"Daddy wallahi sharrin zuciya da shaidan
su nc suka debe ni na aikatawa Aziza haka,
Daddy ku yafc min, wallahi nayi nadama fiye da
tunanin ku".
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Hamced
zargina ya zama dai-dai kenan? Ya Allah Ka
dauki riana da ganin wannan rana mai tarin
takaici, yanzu dama kaine ka aikata mata haka?
Amma dai ka cuce mu, ka janyo mana gori da
surutu cikin zuri'a, ka wulakanta mu, ka
wulakanta kanka. Ni Asiya yau naga ta kaina".
109
Zuri'a Daya-I sa'adatu Muhammad Waziri
Cikin kuka ya cc, "Mommy kiyi hakuri,
wallahi nayi nadamar abinda na aikata a
rayuwata".
Nan ya taho zai rikcta ta kauce itama cikin
kuka, ta cс.
"Wallahi idan ka taba ni zan tsine maka,
domin da ganinka gabana gwara gawar ka,
domin ka janyo mana bakin jini da gaba a cikin
lardinmu".
Cikin tsawa Alh. Jafar ya ce, "Asiya kina
hauka ne? Kin san wane furuci kike yiwa dana?
Kada ki kuskura ki furta masa tsinuwa domin
kina tsine masa nima zan datse igiyar auren mu
ni da ke ta har abada".
"Jafar me kake son fada min ne?"
Ta ambaci sunan sa kai tsayc cikin bacin
rai, sunan da ta dade bata ambata masa ba tun
lokacin da Allah Ya basu yara.
Cikin kunar rai ya ce, "(Okay) baki ji abin
da na fada miki ba kenan sai na maimaita?"
Nan take ya sake maimaita mata abinda ya
fada da farko.
Cikin zubar hawayc ta ce, "Idan har ni ce
na tsuguna na haifi Hameed to ba zan taba yafe
110
Zuri'a Daya-I Se'adatu Muhammad Waziri
masa abinda ya yiwa Aziza ba har sai yaje ya
bayyanawa duniya cewa shi ne ya yi mata
wannan rashin tausayin, amma idan ba haka ba
to na yafewa duniya shi har da kaima kanka".
Da sauri Hameed ya zo ya rungume ta yana kuka yana ccwa.
"(Pleasc) Momce ka da kiyi fushi dani,
idan har za ki yafe min to zan je na fadawa kowa cewa ni ne na cutar da Aziza ba kowa ba".
"Karya ku ke yi ke da shi, babu wanda ya
isa ya tona min asiri cikin zuri'a, na yarda cewa Hamecd shi ne ya aikata ma Aziza wannan danyen aikin, naji ni da kaina zan hukunta shi ba
tare da kowa ya sani ba. Amma ya je ya tunkari
Zuri'ar mu da wannan labarin ai tamkar kun tabа
min wuka a ciki ne. A barni da kaina zan
hukunta abuna".
"Yin hakan ba adalci bane Jafar, kuma ba
addini bane, tsabar son kanka da zuciyar ka shi
ne zai sa ka fadi haka. Bari na fada maka, idan
kana tunanin wannan shi nc soyayya ga abin da
ka haifa to kayi kuskure, domin ka jefa danka
cikin halaka, gwara kawai ka barshi a hukunta
shi kamar yadda shari'a ta tanada, amma yin
111
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
hakan babu abin da zai haifar maka sai larin
bakin ciki da nadama".
"Asiya ban taba tunanin ba kya son danki
ba sai yau, ya aikata laifi bai 6oyc mana ba shi
nc mu kuma za mu tonawa kanmu asiri duniya
da Zuri'a su zage mu, to ni ba zan yi haka ba, na
yarda yayi laifi a barni na hukunta shi da kaina".
"Sam wannan ba addini ba ne Jafar,
sannan kuma ba so bane. Me za ayi da yaron da
zai gwada wannan rashin imanin? Zan iya yafe
auren ka matukar ba ka bari an hukunta Hameed
ba, don na rasa wane irin so kake ma 'ya'yan da
har idon ka ya rufe baka son ganin laifin su ko da
kuwa wanc irin laifi suka yi? Duk cikin Zuri'ar
nan yaran gidan nan sun fita daban wurin
tarbiyyar su, wanda kuwa hakan duk ya samo
asali ne daga irin son da kake musu. Dalilin da
yasa kenan ta kai ga Hameed ya aikata wannan
rashin imanin".
Cikin tsawa ya cc, "Asiya ki rufc min baki
na ce, Hameed dana ne, ina son shi fiye da
dukkan yaran da na haifa, don haka banga abin
da zai yi na juya masa baya ba a fadin duniyar
nan, matukar nima zan iya hukunta shi da hannu
112
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
na. Ki zuba idanu ki gani, ni da kaina zan yi
masa abin da baki yi tunani ba".
Cikin kuka Hamced ya karaso ya rike
Kafar mahaifinsa yana ccwa.
"Daddy ka barni a hukunta ni kamar yadda
addini ya tanadar, domin yin hakan shi ne zai sa
na samu nutsuwa cikin zuciyata da kuma samun
gafarar Allah.
Daddy nayi nadamar abinda na yiwa
Aziza na, ban taba tunanin dai-dai da rana daya
zan cutar da ita ba, sai gashi zuciya ta sa ni na yi
aikin da na sani.
(Please) Daddy ka barni ayi min abin da
Momce ta ce, domin bana son tayi fushi da ni,
don ina son ganinta cikin farin ciki".
"Baka isa ba Hamced! Ba za ku kunyata ni
cikin Zuri'a ta ba da kuma idon duniya, saboda
zan zamo ba komai ba a cikin su, girmana da
mutuncina da daraja ta za su zube a wajen su, ni
kuwa da na rasa mutunci da daraja ta cikin
ZURI'A ta da idon duniya gwara na rasa shi a
idon matar da nakc aurc da kai dana na kaina.
Na yarda ban goyi bayan abin da ka aikata
ba, naji ciwo sosai har cikin zuciyata. Tunda
113
Zuri'a Daya-! Sa'adatu Muhammad Waziri
babu wanda yasan kainc ka aikata to ni dai da
hannuna ko baki na ba zan iya daukar wuka na
dabawa kaina ba, ma'ana na fadawa duniya ccwa
kai nc, don haka tun wuri mu rufe zancen a nan.
Matukar kaje ka tonawa kanka asiri ni ma
zan tsinc maka, zan kuma yanke duk wani alaka
a tsakanin mu ni da kai na har abada, don haka
ka tsaya kayi tunani.
Ke kuma na fasa sakin, kije ki fada, ina da
hanyoyi da dama da zan bi don ganin na hukunta
ki da su, kema kiyi tunani tona asirin ko rufa shi,
cikin biyu dole ki yi daya.
Kai kuma wuce muje ka ga likita don ya
duba maka wannan goshin naka".
Bai tsaya ya jira amsar su ba ya ja hannun
sa suka fice, kai tsaye mota suka je suka shiga
sai asibiti.
Tun da suka tafi Hameed yake kuka bai
sarara ba, haka mahaifin sa ya shiga tausar sa da
ba shi baki akan ya diana daga hankalin sa, babuabin da faru da shi sai alheri.
Bayan fitar su Haj. Asiya ta zube a kasa
tana kuka mai isar ta, tana tunanin irin rashin
114
Zuri'a Dayo-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
adalcin mai gidanta, tsabar rashin imani da
tsoron Allah ga irin abin da yake furta mata.
Tabbas tasan irin mugun halin sa da kafiya
da rashin kwantar da kai a cikin abin da yasa
gaba, bashi da mai sa shi haka ba shi da mai
hana shi.
Tabbas tasan rabuwar kan ZURI'Ar su ya
zo, domin babu wani da za a viwa haka cikin
Zuri'ar ya dauka, domin hakurin sa da son
zumuncin sa, donmn wannan keta haddin ya yi
yawa.
Sannan shin Jafar baya tunanin ccwa
wannan abin da yake wa yaransa shi ne gata ko
so? Sai kana daurewa yaranka gindi kana fifita
son su akan sauran yaran duniya?
Tabbas ka yi kuskure, dole idan baka
daina ba wata rana da kanka zaka dora hannu
kayi kuka.
Shin ma wai ina tunaninsa da
kwakwalwar sa suka nufa? Idan ni ko Hameed
wani bai fada ba ita idan Allah Ya tashi kafadar
ta zai rufe mata bakin ta ne akan kada ta fada?
To wannan nc bai isa ba".
115
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Nan ta daga hannu sama tana addu'a akan
Allah Ya bata lafiya don gaskiya tayi halinta. Da
wannan tunani ko nace addu'ar tayi dakinta, tajc
ta ja ta rufc zuciyar ta da kuncin abin da ya faru.
Sai da safc ta ganshi anyi masa (drcss) a
gurin da yaji ciwon, suna haduwa ta daure fuska
ya yi naciz akan ta saurare shi ta ki, dole ya
koma dakinsa ya kulle yana kuka. Haka yaji
gaba daya duniyar tayi masa ba dadi, ya kara jin
tsanar kansa da rayuwar ma gaba daya. laka dai
ya zamo abin tsangwama a gurin mahaifiyar sa,
dole yasa ya koma rayuwar sa shi kadai a cikin
daki.
Tun sanda mahaifin sa ya zo masa da
labarin abin da likita ya fada musu na cewa ba
lallai bane ta iya tuna abin da ya faru da ita ba,
domin ta samu ta yi wata irin razana mai tsanani
wanda hakan ya janyo mata fadawa cikin
mawuyacin hali.
Da farko ya yi murna har yake fatan Allah
Yasa kada ta dawo cikin hayyacin ta domin kada
ta tuna abin da ya faru a baya da ita, ta hakan ne
116
3
ZvriaDayarlarumuile adotu Muhammad Waziri
zai iye bin duk hanyar da zai janyo ya wanke
laifin d aya yi mata, amma fa a tunaninsa.
nibsb Amma tun sanda ya je ya ganta ya rasa ma kansa nutsuwahaka kullum zai kefe kansa a daki
ya shiga yin kuka idan bai samu nutsuwa ba sai
ya dauki Alkur'ani yana karantawa sai yajinya
nemi damuwar sa ya rasa.sgide sy unide iv ay ise
Sam Momin sa ta iki sauraron sa, küllum haka zai sa ta gaba yana kuka haka ita ma za tai
tayi, ita babban takaicin ta yadda Alh. Jafar ya yi
mata katanga da zuwa asibiti domin yana ganin
kamar idan ta je zata iya cewa Hameed nelya
aikata mata wannan al'amarinsı asnnaw A
asask nimob sbig owsb sue nilslasd nidest Bb
Hameed nedavakansa byamtakura ma
mahaifin nasa akan ala dole sai ya je asibitin ya
sake ganin halin da Aziza takedciki, domin shi
ma ya hana shi ganin yadda yake ce masa shi a
bar shi ya bayyana cewa shi ne ya aikata mata
haka ko ya samu ya samu nutsuwa, amma ya ce
masa bai yarda ba. inuw ab sysb snBWK CL SY
Ganin kafiyar da iya nuna na son ganinta
ya salya ce ya amince suje, amma ba zai barshi
sbud sy sb σε πολοτ αί anay nileb enilsd s syse
117
Zuri'a Daya-I sa'adatu Muhammad Wazji
shi kadai ba don gudun kada ya kwanto masa
kura.
Har cikin ran Alh. Jafar baya jin dadin
abin da ya faru da Aziza, ya so kwarai da farko
ya dauki mataki mai arfi a ranar da abin ya faru,
amma daga baya da ya gane abin a gindinsa yake
sai ya yi shiru ya shiga taka tsantsan da al'amarin
don kada abu ya fito aji kunya.
Dole ya sa yake faranta ran Haj. Asiya
don kada tayi fushi ta tona asirin dansu, amma
duk abin da zai yi mata a banza domin kawai
kallon sa take yi.
A wannan ranar ce suka je da Hameed din
da tashin hankalin suka dawo gida, domin kadan
ya rage Hameed ya tonawa kansa asiri.
A cikin mota ya shiga yi masa masifa da
inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, shi kuwa
Hameed shiru yayi yana dubansa, bai ce da shi
komai ba.
Da suka dawo gida haka ya shiga dakinsa
ya rufe kwana daya da wuni ya yi bai bude ba,
hankalin Alh. Jafar ya yi matukar tashi.
Washegari ko wurin aiki bai je ba, ya
tsaya a bakins dakin yana ta rokon są da ya bude
118
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
don da farko zaginsa yake ta yi ganin ya ki dole
ya dawo yana rarrashin sa da bashi baki akan zai masa duk abinda yake so idan ya budc kofar.
Haka yayi ya gaji ya koma ya dawo, haka
ya yi tsawon ranar shi ba abinda yaje ya fadawa
wani cikin 'yan uwansa ba abin da yake gudu ya
zo ya faru, domin dole ne sai sun so jin dalilin sa
na yin hakan, shi kuma ba zai iya fadawa kowa
ba.
Haj. Asiya ana kallon su babu abin da ta
ce da su sai tsananin mamakin irin kaunar da
yake nunawa Hameed kamar ransa, wanda hakan
ne ya janyo ya fada cikin wannan halakar. Don
tabbas ta san Alh. Jafar yana matukar son
Hameed fiye da komai a cikin rayuwar sa, ta san
zai iya aikata komai akan sa, don ya ga ya bashi
farin ciki.
Sai dai kuma a yanzu yanda ake da wuya
ya bawa Hameed farin cikin da yake so, domin
farin cikin sa a yanzu shi ne ya bar shi ya fada
cewa shi ne ya yiwa Aziza wannan aika-aikar.
Amma ina! ba zai taba barin haka ya fsaru ba.
Sai misalin sallar isha taje