ki
tana fada mas aya daina mata haka, ita bata so.
Nan zai shiga bata hakuri idan yaga ta
bata rai, ranar nan kawai sai gashi abin ya faru a
idanuna, hankalina ya yi mummunan tashi,
amma abin da yasa na kara samu nutsuwa jin irin
kalaman da Aziza tayi masa amfani da su.
"Hamee wai mene yake damun ka ne
haka? Na fada maka ka diana yi min irin wannan
70
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
wasan, idan ba haka ba wallahi zan kai karar ka
gurin Abba. Sai kace kai ba Musulmi bane, idan
ka kuma yi min haka wallahi zan daina yi maka
magana har abada tunda kai baka san abin da ya
dace ka yi ba da wanda bai dace ba".
Ina kallo ya durkusa yana bata hakuri da
kyar ta saurare shi, ganin yadda tayi masa yasa
na saki riana na tabbatar ko ina Aziza take zata
iya kare kanta da mutuncin ta, hakan yasa na
rabu da ita ban bari sun ganni ba. Amma daga
baya na kira ta cikin hikima ina fada mata tana
hankali da kanta gurin kowane irin da namiji, sai
dai ban nuna mata dawa nake nufi ba, amma
ganin ta fahimci abin da nake nifi kuma na san
dole ne ta kawo Hameed cikin ranta, don haka
sai na kara samun damar ci gaba da yi mata
nasiha don naga abin da nake faa mata yana ratsa
ta.
Tun daga lokacin na kara ganin tana
tsantseni da yayanta Hameed, hakan da na gani
sai yake kara sa ni sakin raina, domin shi kansa
ya daina shisshige mata.
Kullum rana ta Allah Aziza kara girma
take yi tare da bayyanar kyawunta, domin
71
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
lokacin makcrin budurcinta ya fara kera ta,
lokacin ne kyanta yake kara bayyana, kowa yana
yabawa da irin kyan da Allah Yayi mata. Duka a
lokacin shekarunta na haihuwa sun dan dara sha
hudu, idan kika ganta a lokacin za ki yi mamakin
saurin girman nata.
Nutsuwa da kamun kai kullum daduwa
suke a gurin ta, kaf cikin Zuri'ar babu wanda
baya kaunar halinta da irin kyawun halinta, don
haka kowa yake jin yana kara son ta saboda
ladabin da take da shi ga zumunci da nacin son
'yan uwa. Da wuya a garin Allah ya waye bata је
dukkan gidajen kawun nanta ta gai da su ba, idan
bata je da safe ba da yamma, wata rana har dare
yake zuwa ta gaida su, wadanda take tunanin ba
zata gansu ba sai a wannan lokacin.
Hakan yasa Aziza take kara farin jini ga
kowa, don bana jin da akwai wata diya da ake so
da kauna a cikin Zuri'ar mu domin ta ko ina
yabon halinta ake yi.
A cikin 'yan kwanakin nan haka nakc
kwana na tashi da wasu munanan mafarkai
marasa dadi, domin yinsu nake yi barkatai, sai
72
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
na kasa gane manufar su, sai idan na tashi na
bisu da addu'a akan koma dai meye Allah Ya
kare mu.
Na kassa nutsuwa da na fara ganin duk
lokacin da zan yi mafarkin sai na hango Aziza
cikin wani irin yanayi mara dadi, don haka nan
da nan na shiga addu'a akan ko ma dai meyе
Allah Ya tsare mu.
ashe tashin hankali ne mai tsuma rai da
bakin ciki, wanda ba zai taba goguwa ba cikin
zuciyar mu, sai dai babu yadda bawa zai yi da
kaddara, dole idan aka rubutata sai ya faru.
Wata rana Hameed yana gida ya kasa
samun nutsuwar ransa, ga so da kaunar Aziza
yana ta addabar sa, ya kasa samun nutsuwa,
bugu da kari ga gudun da tayi masa na nisantar
sa da tayi, domin sam yanzu bata barinsa yana
nanikarta kamar da.
Ranar anyi wata rasuwa cikin dangi kusan
kowa yana can ta wani yaro ne dan wajen
Lukman, to duk yawanci ana can. Haka Aziza ta
fito rike da ke a hannunta, domin kunyi matukar
73
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
shakuwa da ita, sam ba kwa son rabuwa, lokacin
shekarar ki uku da 'yan watanni.
Nan ta hango Hameed tsaye shi kadai
yana ta kai komo a wajen gidansu, yana ganinta
ya wani dimauce hade da jin wani mugun sonta
da sha'awarta duk a lokaci daya sun tsirga masa,
ganin irin kyan da tayi, yaji kamar yaje ya
rungumeta wanda yake ganin yin hakan ne zai sa
ya samu nutsuwar halin da yake ciki. To amma
babu dama don tuni ta toshe masa hanyar samun
wannan damar.
Cikin wani irin yanay yake mata magana,
ya ce.
"Matar daga ina haka? Kamar kuwa kin
san ke na fito ko zan hango ki sai gashi kuma na
ganki".
Tayi murmushi ta ce, "Ba wani nan, don
ka ganni ne yasa ka ce haka. To daga gidan
rasuwar nan nake Haana ta hana mu sakat shi ne
Ammi ta ce na zo gida da ita mu zauna ko tayi
barci, don taga alamun fita kawai zata yi a gurin,
gashi ta ishe mu da surutunta da baya karewa,
don ita ba zata gane wane hali ake ciki ba. Kuma
nima dama na gaji, ji nayi kai na ya fara ciwo shi
74
Zuri'a Daya-1_Sa'adatu Muhammad Waziri
ne nake son mu koma gida mu dan runtsa kafin
su dawo, gashi kuma rana ta soma takewa".
"(Okay) nima ban jima da dawowa daga
gidan ba, don bana son hayaniya. Oya to muje na
raka ku gidan mana".
"A'ah, da ka ma barshi mun karasa, kaima
kaje ka huta".
Bai bata amsa ba ya sa hannu ya dauke ki
ya saka ki a kafada suka jero suna hira, ke kuwa
kin fara surutunki kafin ku karasa har bacci ya
dauke ki. A haka ya kai ku har kofar gida, nan
ya tsaya yana janta da hira har ta soma gajiya,
nan ta ce masa ya miko ki taje ta kwnatar dake.
Cikin sauri ya mika mata ke, sai da yayi
wayon da ya hada hannunsa da kirjinta, sai tayi
kamar bata san yayi ba, don ko kallon sa bata yi
ba. A tunaninta cikin rashin sani ne, amma tana
daga ido suna hadawa sai ya sakar mata
murmushi, nan take taji wata kunya ta kama ta,
ta dai dake ta ce.
"Na gode, kaje abinka zamu shiga don na
fara jin kaina na sara min".
75
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Ya yi murmushi ya. ce, "Shi kenan ku
shiga, sai anjima din, idan kin gashi na shigo
muyi hira".
"(Okay) babu laifi, amma kai ma da ka
koma gurin makokin don kowa yana can kar ace
ba a gaka ba".
"Kai share kawai, nima baccin nake ji,
idan na tashi na je".
"Shi kenan sai anjima, bari mu shiga naji
hannuna ya fara sagewa, kasan Haana da nauyin
tsiya". Ta fada tana murmushi.
Shima murmushin yayi ta juya ta shiga, ya
bita da kallo har sai da ta shige ciki, nan da nan
ya kara dimaucewa da kuanarta da sha'awarta,
domin kasa iya daga kafarsa yayi, haka ya tsaya
a gurin yana ta sake-sake cikin zuciyar sa. A
kalla ya kai fiye da minti ashirin a gurin yana ta
sake-sake cikin ransa.
Nan ya yanke shawara ya shiga gurinta
kawai domin a yadda yake jin sa idan har bai
hada jikinsa da nasa ba bazai taba samun
nutsuwa ba, domin yau wata irinm sha'awace ta
addabe shi wadda bai taba jin irinta ba tunda
yake jinta akan Aziza, don yana jin idan bai je
76
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
garcta ba kamar zai iya mutuwa ko ya iya rasa
hankalin sa. Nan ya kara jin ya birkicc da ya
tuna surarta a danzun da suka.
Kai tsayc ta yanke ma kansa tunanin
kawai ya koma ciki ya kara ganinta, don yana
tunanin yin hakan zai zama ya samu nutsuwar
halin da yake ciki. Kai tsaye gidan ya shige, nan
ya iske ta kwance kan gado ta (window) din
dakinta.
Baccinta take sosai cikin kwanciyar
hankali, daga ita sai 'yar shimi mara hannu,
gefenta ke kwance kina barcin ki.
Ya jima tsaye yana kallon ta daga nan
shaidan ya shiga kawata masa ita cikin ransa,
haka ya shiga mugayen tunani daga karshe ya
samu ya shigo dakin. Ya jima akanta yana kallon
kyawun surarta.
Maganar gaskiya kyawun da Aziza take da
shi na jiki da na fuska domin Alah Ya yi ta mai
kyau, gashi kuma wani girma da tayi wanda bai
kai shekarunta ba, tsabar jin dadi da kwanciyar
hankali duk sune suka kawo haka, saboda idan
aka fada maka shekarunta za ka sha matukar
mamaki, domin haka allah Ya yi ta da karsashi
77
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
da kuzari. Don haka nan da nan ta zamo
cikakkiyar budurwa, sai dai idan ka dubi fuskarta
ko ka santa idan an fada maka shckarunta sai ka
jima kana mamakin hakan.
Cikin sanda ya dauke ki daga kan gado ya
dawo dake dakin Ammi kina ta barcin ki, haka
ya dawo cikin sanda duk tana barci nata sani ba,
ya jima yana tsaye zuciyarsa ta kasu biyu, yana
tunanin kamar ya afka mata amma yana tunanin
me zai je ya dawo? Tunanin da yayi matukar bai
yi abin da ya kawo shi ya tafi ba, to kuwa yasan
mutan gidan za su iya zuwa su tarar da shi a
haka.
Kai tsaye ya je ya rufo kofar, ya dawo
cikin sanda ya hau kan gadon da take ta bayanta
ya shiga shafa ta, haka ta dinga ji kamar a cikin
mafarkinta, nan tayi juyi. Ya dan tsaya da taba
mata jiki, ganin ta ci gaba da yin baccinta ya
kara ci gaba da shafa mata jikin, nan ta dora
hannunta a inda taji ana taba ta.
Tsaraf taji ta rike hannun mutum, a razane
ta bude idanunta zumbur tayi ta tashi zaune ta
cc.
78
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri "Subhanallahi! Ya Hamced meye haka
kuma me ya dawo da kai bayan mun rabu da kai?"
"(Plcasc) Aziza na ni da kc ne, kawai ki
tsaya ki saurare ni kiji me ya kawo ni". Cikin tsawa ta cc, "Ya Hamced ka fita ka barni, kana hauka ce? Kasan abin da kake fada
min kuwa? Wallahi idan baka fita ba zan je na
fadawa su Abba, ko ka fara shaye-shaye ne?"
Cikin irin wani yanayi na kamar 'yan
maye ya се.
"Aziza na (plcase) ki tsaya ki fahimce ni,
ki gane cewa ina cikin rudani na sha'awar sonki,
wallahi yadda nake ji na kamar zan iya rasa raina
idanz ban hada jikina da naki ba".
"Allah Ya tsare ni Ya Hamced da aikata
haka, ashe dama kai fasiki ne? Wallahi idan baka
fitar min daga daki ba zan kurma maka ihu kowa
yaji abin da ka zo yi, ai wannan keta haddi ne".
"Aziza ko me za kiyi sai dai kiyi, domin
ba zan iya jure irin halin da nake ciki ba na
tsawon shckarun da na shafe akan ki, ki kwantar
da hankalin ki ba cutar da kc zan yi ba, ki tuna
ccwa baki da wani miji sai ni".
79
Zuri'a Daya-1 sa'adatu Muhammad Waziri
"Allah Ya kiyaye min na aure ka Ya
Hamced, wallahi na tsanc ka har karshen
rayuwata, kuma na rantsc sai na fadawa kowa
abin da kake nufi akai na, banza mugu".
Nan ya fara matsowa kusa da ita, ta shiga
ja da baya. Sam ta manta bata nemi wani abu ta
rufe jikin ba, sai kawai hannu da ta sa ta
Kankame jikintata taho da gudu zata bude kofa
ta gudu, nan taji kofa a rufe babu kuma (key) a
jiki. Nan ta kara rudewa, ta juyo ta ga ya nufota,
nan take ta shiga kuka cikin karfinta.
Ciro (key) din yayi ya nuna mata, уa сe.
"Zan barki ki fita, amma sai kin yi min
abinda nake so".
Nan ta soma kurma ihu, ya yi sauri ya zo
ya toshe mata baki ya hade ta da jikinsa, sannan
ya ce.
"Duk ihun ki babu mai ji domin duk na
kulle gidan, sannan kuma ga sanin yadda ghidan
nan yake, duk ihunka a ko ina yake da wuya kaji
don haka sai ki yi ta ihun ki babu mai hana ni
burina".
Cikin kuka ta ce, "Ya Hameed kasan mc
kake fada min kuwa? Azizan ka ce fa, na roke ka
80
Zuri'a Daya-i Sa'adatu Muhammad Waziri
idan baka cikin hayyacin ka kayi sauri ka dawo
ka gane wa kake tare da ita. Ka daure kada kayi
abin da zai cutar dani, kayi hakuri ka bude min
na fita daga dakin nan".
Murmushyi yayi, ya ce, "Kalau nake,
kuma nasan Azizan nawa ne da ba ita ba babu
wanda zan yiwa haka, ki daure ki bani hadin kai
kawai Aziza, ba zan iya jure halin da nake ciki
ba a yanzu. Ki tuna fa ni ne zan aure ki, me kike
jin tsoro?"
Ganin ya yo kanta gadan-gadan yasa ta
soma ja da baya tare da hango abin da zata iya
tsare kanta, ņan idanunta suka hangi wani
kwalba na lemo, da sauri taje ta dauka ta shiga
nuna masa cewa.
"Wallahi idan ka matso ni sai na fasa
maka kai, idan kuma kana jin wasa nake ka
matso ka gani".
"Bana jin akwai wani wargi da zaki yi min
na fasa abinda zanyi tunda kin ki bina ta lallami,
don haka dole na aikata abin da nayi niyya tunda
daga karshe dai hannuna za ki dawo, ni kuma ba
zan iya jira har sai wannan lokacin ba".
81
Zuri'a Daya-I So'adatu Muhammad Waziri
Yana gama fadin haka yayo kanta gaba daya.
Ai kuwa bata yi wata-wata ba ta daga
kwalbar nan sai ta sakar masa a goshi, nan da
nan sai ga jini, haka nan ya cakumo ta tana ihu
ya tsikar da ita asa yana cewa.
"Ai tunda ta kaimu ga haka dole nayi
abinda na ga dama, idan yaso kome zai faru sai
dai ya faru".
Kuka take kamar ranta zai fita tana bashi
hakuri, amma sam yaki saurara mata, haka ya
shiga cire mata riga.
Zaune muke gurin makoki duk muna cikin
jimamin mutuwar, haka kawai sai naji gabana
yana ta faduwa, naji zaman gidan duk ya gundire
ni, sai dai babu yadda za ai na ce zan tafi tunda
mu ne manya a gurin dole na hakura. Sai dai
haka na dinga jin zuciyata babu nutsuwa, duk sai
na dinga danganta rashin jin dadin zuciyar tawa
da mutuwar da aka yi nc.
An yi sallar la'asar kenan Alsha ta matso
guri na ta се.
82
5
Zuri'a Daya-1I_Sa'adatu Muhammad Waziri
"Ummah, ni fa zan koma gida don tun
dazu ina nan sai yawan jin faduwar dgaba nake
tayi, na kuma rasa gane dalili. Kuma ni sam bana
jin haka sai yau, tunda garin Allah Ya waye nake
ta jina cikin damuwa amma da ina ta yawaita
azkar.
Na ce, "To Allah Ya rufa asiri, ina ganin
ki tashi ki tafi gida".
Ina sane na ce mata haka don kada na fada
mata cewa nima ciki wannan halin nake ciki na
daga mata hankali, domin tunani zata yi wani
abu ne zai same mu. Na ci gaba da bata kwarin
gwiwa akan ta dinga yin addu'a, nan take
hankalina ya tashi na dinga tunanin kowane abu
ne zai faru da Mukhtar akan hanyar sa ta
dawowa daga tafiyar da yayi, haka nima cikin
raina na ci gaba da yin addu'ar, amma ban nuna
mata cewa nima ina da tawa damuwar ba.
Tana shirin tafiya ne Habibu ya shigo
cikin gidan yana salati hade da hawaye a fuskar
shi yana fadin.
"Yau mun shiga tashin hankali a gidan Ya
Mustapha, 6ara yi suka shiga gidan".
83
Zuria Doyedodu lojodatu Muhammad Wazisi
поGabaki dayan mu muka mike cikin tashin
hankali,da rudu domin bamu san me suka yi ba.
da sauri najo na riko hannunsa na cemшk ви i
olen labibu iya salar dai suka yi basu cutar da
kowa ba2".sni sh amms ewumeb nitio snij вI
Cikin kuka ya ce, "Umma ban sani ba dai,
yanzu muna gamag sallah A aka" zo mana da
labarin". Yana fada yana kukasbig lat il ides! il
sbsl gdHankalin mu ya gama lashi gaba daya
ganin yana kuka,na co.w ilio smin sweo sism
inew iHabibu ban yarda da maganar ka ba,
ncye ya sa kaj kuka game da batun shigar
farayin? Ko'dai wani abu ya faru ne?ls swiwg
uds onAisha hankalinta ya yi mugun dugunzuma,
18Vand and rais is is on
nidio Mmma su Haana da Ammi na! Na shiga
uku, Allab Yasa ba wani abu ne ya faru dai su
ba". .d TWIth BWE e sni Bi BWOO EISM ogida Nan take hawaye suka homamfita daga
idanuna, kafin na ce da ita wani abu har tayi
waje da gudu, haka nima na biyo bayanta da
sauran jama'ar da muke gurinia nun usY
"nabig agiria Blue in sisd ariqalauM
४४ 84
Zuri'a Daya-1 _Sa'adatu Muhammad Waziri
Tashin hankali mara misaltuwa muka je
muka tarar wanda ya dugunzumá dukkan
hankalin ZURI'A.
Aziza muka gani kwance cikin jini a
hannun mahaifinta ya rungumcta yana ta sharбar
kuka, ya hana kowa ya taba ta, duk ya susucc
kamar wani karamin yaro dan goye.
Da sauri Aisha tayi kansa ta karbcta a
hannunsa ta shiga kuka, cikin tashin hankali ta
сc.
"Abba Haana! Me ya samu Ammi na? Ba
dai kashe min ita suka yi ba?"
Cikin kuka kamar yaro ya ce, "Aisha an
kashe mana rayuwa, an kashe darajar Aziza da
mu kanmu, domin wasu mara imanin sun zo har
gida sun hakke mata, ma'ana sun yi mata fyade".
Kurma ihu tayi ta saki Azizan ta riko masa
kwala, cikn kuka ta се.
"Me kake son fada min ne Mustapha? Mс
naji ka cc? Wayyo Allah na na shiga uku ni
Aisha".
Nan ta juyo ta kalli Aziza íayi saurin
rungumcta a cikin wannan hali sai gani muka yi
ta suma a gurin, ni kuma ina tsayc tsabar rudani
85
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
da na shiga sai ji nayi nima idanuna yana son
rufcwa, nan take naji jiri na dibana, a takc nima
na fadi sumammiya.
Salati suka shiga yi, dolc aka yiwa
Mustapha aka debe mu gaba daya don zuwa
asibiti, kusan babu wani namiji da yayi saura bai
bimu asibiti ba in dai dan Zuri'ar mu ne, haka
muka fice cikin tashin hankali.
Asibitin Malam Aminu Kano aka kaimu,
ni ce na fara dawowa cikin hayyaci na sai Aisha,
yawan kukan da take yi shi ne yafi dagawa kowa
hankali, kowa yana bata hakuri amma ina sai
kuka take. Nan ta cewa Allah Ya dauki ranta ta
huta da wannan bakin ranar da ya same ta.
Haka muka hadu muna bata ba baki akan
tayi hakuri ta rungumi kaddara babu wani bawa
da zai iya tsallake kaddarar sa. Tayi ta dai addu'a
akan Allah Ya tashi kafadar ta.
Tun sanda muka zo asibitin bab' akc ta
kokarin ceto ran Aziza amma ina! Har yanzu
bata iya motsi, ga dai alamu tana da rai ba
mutuwa tayi ba, amma idan ka ganta ai ka zata ta
mutu.
86
스
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Alh. Jafar, Alh. Aminu da Mustapha suna
zaune a (office) din manyan likitoci guda biyu
suna yi musu tambaya.
Dr. Sha'aibu ya cc, "Kamar yadda muka
tambaye ku cewa tsawon awanni nawa aka yi da
faruwar wannan al'amari ku ka ce baku ba.
Yadda binciken mu ya nuna ta shafe
awanni uku cikin wannan yanayi wanda jinkiri
da rashin samun taimako a lokacin da abin ya
faru ya janyo mata illoli da dama, na farko dai a
yanzu tana cikin koma zata jima a haka, idan
Allah Ya kawo cikin sauki zata iya farkawa ta
dawo cikn tunaninta, idan kuma aka samu rashin
sa'a zata iya zautuwa gaba daya ko kuma tayi
mantuwar abinda ya gabata a baya (losing
memory).
Illa kuwa ta mutuncinta anyi mata sosai,
amma zamu yi iya yinmu don ganin munyi
nasara akan aikinmu".
"Lahaula wala kuwwata illa billah! Ya
Allah Ka fiutar da yarinyar nan daga cikin
wannan masifa da ta samc mu". Ya karasa fada
yana kuka.
87
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Alh. Aminu ne ya dafa kafadar Mustapha
shima idonsa yayi jajir, ya сс.
"Kayi hakuri Mustapha, insha Allah Allah
zai yi mana sakayya, duk wanda suka aikata
mana haka".
Haka ya dora kansa a cinyar dan uwansa
yana kuka, уa сс.
"Yaya Aminu an cuci rayuwar mu, me ya
yi saura yanzu ga rayuwar Aziza? Ka dai ji irin
abin da aka fada".
Hawaye na zuba ya dago ya dubi Dr. Shu'aibu, ya сe.
"Doctor don Allah kuyi iya yin ku don
ganin kun ceto min rayuwar Aziza na, ban so na
rasa ta, ban so kuyi mata komai har sai kunga ta
dawo cikin hayyacinta".
"Alh. Mustapha ka taya mu da addu'a,
muma fatanmu da kokarin mu kenan garewta,
babbar addu'ar mu shi ne Allah Ya tsayar da
yawan firgitar da take yi, domin yin hakan kan
janyo abin ya taba kwakwalwar ta, domin yawan
tuna abin da ya faru a gareta ne. Kuma ba lallai
bane idan ta farka ta iya tuno abinda ya faru da
ita ba".
88
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Dr. Salisu ya kara da ccwa, "Wannan
matsalar ta samo asali nc da jinkirin kawo ta
asibiti, amma abu ne na Allah idan Yaso cikin
yardar sa sai kuga komai ya warwarc cikin
sauki".
"Amecn Ya Allah, Doctor mun godc,
Allah Ya bata lafiya, Ya kuma tashi kafadunta.
Don haka mu yanzu zamu je muyi (police report)
don su taya mu bincike su wane suka yi mana
haka? Kuma dole ne mu tuhumi masu gadin
(estate) dinmu". Cewar Alh. Jafar.
Cikin damuwa Mustapha ya dago
idanunsa jajaye, ya cе.
"Yaya Jafar babu wani hukuma da zamu
nema mu saka ta a cikin wannan abin da ya faru
damu sirrin zuri'armu ne, idan muka fitar da shi
duniya ta ji mun tonawa kanmu asiri, mu bar
komai cikin sirri cikin yardar Allah ko ma su
wayc suka yi mana haka da bakin su za su fada
mana, daga nan sai mu hukunta su don wallahi
ba zan nar duk wanda ya yi mana haka ba".
"Gaskiyar Mustapha, hakan ya yi, insha
Allah albarkar zumuncin mu sai Allah Ya
89
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
bayyana ko ma su wayc suka yi wannan rashin
imanin".
Alh. Jafar ya fada, daga nan ya ce.
"Doctor mun gode, ko zamu iya ganinta
yanzu?"
"Babu laifi ku din za ku iya ganinta,
amma mata saboda koke-koken su ba zamu iya
barin su ba".
"Mun gode". Alh. Jafar ya fada, haka suka
mike suka ce za suje dakin da take kwance.
Gata nan kwance duk an saka mata na'ura
masu taimakawar zuko numfashi, ta jikin na'urar
kawai ake iya ganin bugun zuciyarta.
Da sauri yaje ya rike hannunta yana
hawaye yana cewa.
"Aziza na, Ammi na me kika yiwa
wadanda suka yi miki haka? Ki yi hakuri ki yafe
min a matsayina na mahaifin ki ban tsare
rayuwar ki ba kamar yadda ya kamata, (please)
Ammi na ki yafe min, ban kyauta miki ba, ki
yafe min".
Nan kuka ya ci karfinsa, haka yayi ta kuka
kamar yaro dan goye.
90
3
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri
Alh. Jafar ne ya ce, "Haba Mustapha,
meye haka? Wannan ai sai ya kai ka ga yin sabo,
da kaine kake tsare ta ba Allah Mahaliccin mu
ba? (Pleasc) k3 nutsu kasan me kakc furtawa".
Daga kai ya yi alamar yaji, sun jima a
haka daga baya su suka fito amma shi ya ki
fitowa, dole suka hakura suka barshi don
likitocin sun ce idan shi ne zai iya zama a gurin
tunda ba wani hayaiya zai ba.
Haka muka zo duka muna hangenta ta
cikin glass kwance kamar wata gawa, banda
kuka babu abinda muke yi.
Satin ta biyu a haka amma babu wani
samun ci gaba jiya iyau, Mustapha duk ya zama
abin tausayi domin ko da yaushe shi ne a gurinta,
anyi-anyi da shi akan ya bar wani ya zauna a
gurinta ya ki, haka kullum yake wuni a gurin.
Ranar da ta kwan goma sha bakwai ne
yana zaune kusa da ita kamar yadda ya saba yana
mata karatu yana tofawa, can ya ga tana motsa
hannunta hade da girgiza kai, zuwa can sai ta
runtse idanunta ta kurma ihu ta cc.
91
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Wayyo Allah Abba ka zo ka ccce ni zai
kashc ni, zai kashe ni Abba, Granny zan mutu ku
zo ku cece ni!".
Da sauri ya mike yajc ya rungumeta yana kuka, yana cewa.
"Ammina fada min wanc yayi miki haka?
Fada min ina kusa da kc, babu abinda zai miki
ko waye, ki fada min wane ne?"
Tun daga wannan furucin da tayi cikin
firgita bata kara yin wani kalami ba ta kara
komawa cikin halin da take ciki, da hanzari ya
fito zuwa kiran likita, nan suka shiga gurin cikin
rudani. Nan dai suka ci gaba da aune-aune, nan
suka ce masa tunda har ta fara yin haka cikin
yardar Allah komai zai dai daita.
Kowa da yaji haka sai ya fara jin dadin
al'amarin, sai dai ni akwai wani abu da yake min
yawo a cikin zuciya, amma ban samu na furtawa
kowa ba na ja bakina nayi shiru, shi ne tun ranar
da wannan al'amarin ya faru babu wanda ya yi
maganar Hameed, bai kuma tako inda take ba, ba
kuma wanda naji ya ce min gashi ya zo. Don
haka na shiga shakku akan hakansai dai ban
92
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri
samu na tofawa kowa ba gudun kada ace ni ce
babba ni kuma na fito da wani abu.
Da yammacin ranar ne muna asibiti kusan
kullum anan muke kwana mu wuni, muna cikin
zaune na ce da Maryam.
"Wai na tambaye ki mana? Shin Hamced
tunda abin nan ya faru ya zo asibitin nan kuwa?"
"Umma ya zo mana, ina ganin ke ce dai
baki ganshi ba, yana zuwa bai jimawa sai ya
koma, shi kansa baki ga yadda ya shiga rudani
ba, haka ya ce ba zai jure ganin Aziza a haka ba
shi yasa ba ya son zuwa ya zo ya ganta a wannan
mawuyacin halin. Sau biyu muka hďu da shi a
gurin nan, da kuka yake barin nan don haka ina
tunanin shi yasa ma ya dauke kafar sa da zuwa
nan din"
Ajiyar zuciya nayi na ce, "To babu laifi,
na yi zaton tun sanda aka kawo ta bai zo ba".
"Ummah Aziza da Hameed sai Allah, na
yarda da UZURIn da ya bayar don naga irin
tashin hankalin da ya shiga, duk zuwan da yake
za ki ganshi cikin rashin nutsuwa, domin abin ya
yi matukar tadar masa da hankali".
93
:
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Shi kenan dai, Allah Ya tashi kafadar ta,
sannan Ya tona asirin dukkan azzaluman da suka
yi mata haka".
"Ameen".
Muna rufe bakin mu sai ga Alh. Jafar da
Hamecd sun shigo inda muke, suka yi mana
sallama muka amsa baki daya. Bayan nan Alh.
Jafar ne ya fara gaida ni sannan Hameed shima
ya gaida ni, kallon sa nayi na ganshi cikin tashin
hakali, na ga duk ya yi baki ya wani rame, duk
ga zulumi nan a tare da shi. Haka kawai sai naji
tausayin sa ya kama ni, na kuma tabbatar da abin
da Maryam ta fada min.
Cikin yanayin damuwa ya ce, "Granny ya
mai jiki? Da fatan dai ta soma jin sauki?"
Ya fada cikin wani irin yanayi gwanin ban
tausayi.
Na ce, "Eh sauki yana dai gurin Allah,
amma dai dazu ta soma magana har tana ce...".
Cikin sauri Hameed