Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
ta yiwa Hameed magan akan ya bude dakin, da yaji 119 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri muryar ta ne da sauri ya bude don ya ji dadi, don ko ba komai zai samu wata nutsuwar domin rashin wata nutsuwar har da rashin kulawar da yake samu gurinta, hakan ma ya sake sa shi cikin wani azabar. Lokacin da ya bude ta ganshi sai da itama hankalin ta ya tashi, abinka da tsakanin da da mahaifi. Cani tayi ya yi mugun fadawa cikin kwana daya da wuni daya babu ci babu sha, nan take taji kwalla ta ciko idanunta, tayi sauri ta kau da kai don kad aya ga ta tausaya masa. Da sauri ta juya zaya bar gurin, ya yi saurin riko hannunta, duk da ba shi da kwarin jiki sosai amma ya yi kokari ya yi mata wani rikon tsauri. Cikin kuka ya ce, "Mom me yasa ba kya tausaya min? Ki taimaka min na fita cikin kuncin da nake ciki duk da kuwa nasan ba zan taba samun wani farin ciki da sukun ba tun da na riga na yiwa rayuwar Aziza na illa, na san haka zan kare rayuwa ta. Mom da kina bani kulawa duk da na san ban cancanta a bani ita ba amma Momi idan kika duba nayi nadama, kuma a shirye nake da а 120 Zuri'a Daya-I sa'adatu Muhammad Waziri zartar min da kowanc irin hukunci ko da na kisa ne domin bai kamata a barni haka ba. Momcc sai yanzu na gane cewa ke kadai ki ke kaunata ba Daddy ba, domin ke cc ki ke so a hukunta ni shi baya so. Ganin halin da Aziza takc ciki a (hospital) yasa na kara tsanar kaina da fitar da ran idan ta mutu a haka ba zan taba samun rahamar Allah ba, domin ban ce ta yafe min ba. Don haka na yanke shawarar ko da Daddy zai kashe ni sai na tona asirin kaina don na samu nutsuwa. Don haka Momee ki yafe min, ki kuma ci gaba da nemar min gafara gurin allah, wallahi na tuba, kuma nayi nadama, ba zan sake ba". Hawaye ne sosai suka gangaro a fuskarta, ta sa hannu ta goge da dayan hannun, ta juyo ta kalli Hamced ta kara tausaya masa, ta cc. "Hamecd, mc yas aka yiwa 'yar uwarka haka?" Shima cikin kuka ya ce, "Momcc wallahi sharrin zuciya ne da shaidan, amma don Allah ki yafc min ko don wannan hawayen da na sa ki, (pleasc) mom na san ina cikin fushin Ubangiji". 121 Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri "Hameed, kana da wannan tunanin da kuma tsoron Ubangijin ka amma har kaje ka yi wannan mugun aikin? Hameed ba zan yi maka baki ba ko wani mugun kalami, jin furucin ka yau yasa na yafe maka amma dai dole ka bayyanawa iyayen ka ko me zai faru ya faru. Idan ka ci gaba da Istigfari da kaskantar da kai Allah Zai iya yafe maka naka laifin kai da shi, domin Yana son ganin bawan sa mai nuna nadama da neman tuba na gaskiya. Amma ba Zai iya yafe maka hakkin Aziza ba, wannan sai kai da ita". Ji ya yi wani sanyi da farin ciki sun tsirga masa, ya yi sauri ya rungume mahaifiyar sa yana kuka yana cewa ya gide, kuma ta saka ido zai yi mata abin da rake so. A wannan halin Alh. Jafar ya shigo cikin gidan, yana ganin Hameed wani farin ciki mara misaltuwa ya ratsa masa zuciya, ya ji kamar an masa albishir da gidan aljannah. Da sauri ya zo ya rungume shi, ya ce. "Haba, me yasa ka cika taurin kai ne? Na ce ka cire damuwa insha Allah komai zai zo cikin sauki, mu ci gaba da yin addu'a Allah Ya 122 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri bawa Aziza sauki. Sai dai ba zamu so ta tuno bin da ya faru a baya ba, don gudun tonuwar asitin mu. Hamced, kada kaji ina fadar haka kana ganin kamar ina farin ciki da abin da ya faru da Azizan ka, ko kadan wallahi duk loakcin da na zauna na tuno da halin da take ciki sai na ji ba dadi, amma idan na tuno kai ne ka aikata hakan sai gwiwoyi na suyi sanyi, domin babu abin da zan iya yi a ka". Hada idanu suka yi da mahaifiyar sa, ya ga bacin rai sosai a tare da ita, har ya yi niyyar yin magana ta sa hannu ta dakatar da shi ta cе. "Ban yarda da cewa kana tausayin 'yar dan uwnaka baidan har da gaske tausayin kake yi me yasa ba zaka tona asirin wanda ya yi laifin ba? Don kawai son zuciya irin taka da rashin son zumuncin Allah, kasan abin yana karkashin ka amma ka ki ka bayyana. Ni dai zan debar muku lokaci daga kai har shi, matukar ba ku bayyana ba to ni zan bayyana ko kuma shi Allah da Kansa Ya bata lafiya ta fada da kanta tunda komai a Hannun sa yakc Zai iya yin komai cikin kankanin lokaci". 123 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Cikin zafin rai ya ce, "Asiya na fuakanta yanzu duk abin da ya zo bakin ki kina rufc ido ki fada min ko? To kijc ki fadawa duk wanda za ki fadawa. Ciwo na Allah ne, idan Allah Bai ga damar dawo mata da tunaninta ba babu mai iyawa, domin da asitin Hameed ya tonu na gwammace Aziza taji sauki ba tare da tunaninta ya dawo ba, domin idan Allah Ya bata lafiya a shirye nake ni da Hameed mu shiga cikin rayuwar ta mu kawo mata dukkan farin ciki а rayuwar ta, domin shi ne zai aure ta don ya wanke dukkan laifin da ya yi mata". Cikin mamaki ta ce, "Jafar kai ne da kanka kake irin wannan maganar kamar ta yara don kawai son danka ya rufe maka idanu? To lallai ka ke yi da gaske, domin wata rana kana tare da daukar jin kunya". Tana gama fadin haka ta juya ta bar su a gurin. Bayan ya bita da kallo ta wuce, sannan ya dawo da hankalin sa kan Hamced, ya dube shi sosai ya ga yadda ya koma cikin kwana daya da wuni daya, domin dazun bai gama lura da 124 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri yanayin sa ba, ganinsa ya bude yasa murna ta mantar da shi. "Hameed, kaga kuwa yadda ka koma cikin kwana daya kawai? Haba my boy, me yasa ka cika kafiya da taurin kai? Me yasa ba ka tausaya min ne? Kaga halin da nake ciki tunda abin nan ya faru har yanzu nima bana cikin walwala domin na san kaima ba ka ciki. Hamced ka saki ranka don Allah ka dawo cikin walwalar ka kamar yadda kake can da". Murmushi Hameed ya yi na takaici wanda daga ka gani ka san ba cikin dadi aka yi shi ba, anyi ne kawai, ya ce. "Daddy walwala ta fa ka ce? Daddy tuni na manta wannan cikin rayuwa ta, Daddy na san tunda na taso kake bani farin ciki dai-dai da rana daya ba ka taba bari na rasa wani farin ciki ba indai daga garc ka ne, to (why) yanzu ka hana ni samun sa a yanzu bayan yanzu ne nake bukatar sa? Daddy tsawon kwana ki kana hana ni duk abin da nake so, ina ta bin umarnin ka don kada na 6ata maka wanda kai da kanka ka hana ni zuwa asibiti gurin Aziza duk da kuwa zan iya zuwa a 125 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri sacc baka sani ba, amma duk nayi don kai ma na baka irin farin cikin da ka jima kana bani". "Hameed ban taba hana ka wani farin ciki ba har yanzu, ka fada min wanne farin ciki na hana ka samu a yanzu?" Ajiyar zuciya Hameed ya yiya ce. "Daddy farin ciki daya nake so na ga na samu, idan kayi min haka to Daddy zan san cewa kai mai son farin ciki na ne. Ba komai nake so ba illa ka barni naje a hukunta ni, ma'ana zan jc kotun Musulunci a yi bulala domin a fitar da hakkin Allah a kaina, daga nan sai na je gurin su Abba na fada musu cewa ni ne na aikatawa Aziza wannan danyen aikin". Cikin huci da masifa ya сe, "Hameed baka da hankali ne? Kana son tube min rigar mutunci na a cikin 'yan uwana bayan duk irin zafin da nakc yi akan wannan faruwar al'amarin daga baya su ji cewa daga gindina abin yake me kake tunanin za su dauke ni? To kuwa indai wannan shi ne farin cikin naka to sai dai ka ce tunda nakс ban taba baka shi ba. 126 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Abu daya zan yardar maka, shi nc kajc duk inda za a fitar maka da hakkin Allah, ma'ana ayi maka bulala. Na yarda da wannan don kada ka yi tunanin bana tsoron gamuwa da Allah, amma ni dai ba zan yarda 'yan uwana su san cewa kai ne ka aikata wannan rashin imanin ba". "Shi kenan Daddy, zan yi abin da ka cc zan je a yi min bulalar". Runtse idanu Alh. Jafar ya yi, ya cc, "Hamced ban son kaje a taba lafiyar ka, kaje kayi ta Istigfari Allah Zai yafc maka". "Daddy nutsuwa nake son na samu ta fasrko, matukar aka yi min bulalar nan zan fiye zaton samun rahama tunda Allah ne Ya fada da Kansa. Na sani idan na dukufa da ilstigfari Allah Ya dubi zuciya ta zai iya yafe min, amma tunda ga yadda Ya ce mu bi dole ne mu bi hakan. Daddy a yadda nake ji matukar aka ce kashe ni za ayi idan na yi haka zan kubuta gurin Allah har da cewa Aziza ta yafe min, to zan yarda a kashe ni". "Hameed ka yi min shiru, bana son jin zancen mutuwa! Ba haka Allah Ya ce ba, ga saurayi da bai taba aurc ba bulala dari, idan mai 127 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri aurc ne kuma a jefe shi har sai ya mutu. Haka itama macc idan bata da aure bulala dari, idan mai aure ce a jefe ta, sai dai idan tana da ciki shi nc za a bari ta haihu ta gama shayarwa daga nan sai a jefe ta. Don haka kai ba kisa za a yi maka ba, bulala се. Tunda kana so kaje ni ba zan iya kai ka ba, amma bana so ka yi a garin nan domin ba zan jure ganin ka cikin jinya ba". Cikin farin ciki mai hade da kuka ya ce, "Daddy na gode, zan yi duk abin da ka ce, sai dai ina neman wata alfarma a gurinka, kafin wannan ina so muje da kai a matsayin ka na mahaifi na domin mu yi koyi da Sahabin Manzon Allah (S.A.W), Umar (R.A) da hannunsa ya kai dansa aka hukunta shi, don haka nima zan yi farin ciki a ce mahaifina ne da kansa ya kai ni aka fitar da hakkin Allah akai na". Hawaye ne suka zubo a idanun Alh. Jafar domin tausayin dansa da yaji ya kama shi, tabbas ya yarda cewa sharrin shaidan ne da rudin zuciya suka debe shi ya afka wannan ta'asar, gashi da kansa yake neman ayi masa hukuncin da Allah Ya tanadar wa mai irin laifin sa. 128 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Saka hannu ya yi ya goge hawayen, ya сe. "Hameed naji zan kai ka da hannu na, to amma ka dan bani lokaci kadan ina wani shiryeshirye ne". Murmushi ya yi ya zo ya rungume mahaifin sa yana masa godiya da ya amshi bukatar sa. Alh. Jafar ne da kansa ya je ya hado masa kayan abinci, ya saka shi a gaba yana bashi a baki kamar wani karamin yaro, haka ya soma ci sosai domin rabon sa da cin abinci har ya manta, sai dai ruwa kawai yake ta'ammali da shi. Haj. Asiya tana can daga nesa tana hangen irin so da kaunar da Alh. Jafar yake nunawa dansa kamar shi kadai Allah Ya mallaka masa a duniya. Ta yi kwafa ta bar gurin, domin tana labe duk taji abin da suka yi magana akai, ta yiwa Allah godiya tare da cewa Allah Yasa ya aikata abin da ya ce zai yi. * * * Watannin Aziza biyu a kwnace da sati biyu, sai dai muce sauki yana gurin Allah, domin dai har kawo wannan lokacin tana cikin doguwar 129 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Wazii suma (Coma), abin da likita dai ya fada mana shi nc tana rayc dai har yanzu, kuma cikin kowane lokaci zata iya farkawa. Mu dai kawai muna jinsa ne kawai, tabbas ba don na'urorin da muke gani suna amfani a jikinta ba da sai muce ta jima da mutuwa bai son gaya mana ne. Abban ki duk ya kare ya kasa yin komai, jinya ta mata ce amma da shi ake yi, ya daina zuwa wurin aiki sam, ya yi baki duk ya rame domin yadda yake nunawa idan Aziza ta cuka wtaa uku bata dawo cikin hayyacin ta ba zai shirya fita da ita kasar waje, haka likitocin suka shiga bashi hakuri akan ya dan kara hakuri. A lokacin babu wadda muke tausayawa kamar ki, kullum sai kin yi kuka ke dai Aunty ki Aziza za ki wajen ta, a lokacin da ki ka ganta kwance cikin na'urori duk sai kika tsorata kike ta yin kuka wai ke a tashe ta ku tafi gida. Lokacin babu wanda bai zubar miki da hawaye ba don tausayin ki, haka dai muka ci gaba da rayuwa cikin jiran tsammani. Da yake Allah maji rokon bawansa ne, Gagara misali, wata rana na shiga bandaki Ammin ku ta futa waje don yin rakiyar 'yan 130 Zuri'a Daya-1 sa'adatu Muhammad Waziri dubiya da suka zo, Abban ku yana can masallaci kamar yadda ya saba yana karatun Alkur'ani. Ina fitowa sai kawai na iske Aziza zaune kan gadon esibiti ita kadai garau da ita sai dubedube take, cikin murna da doki na ce. "Aziza na!". Na fada cikin karaji da doki, sannan na daga hannu sama na fara yiwa Allah godiya. Abin mamaki Aziza bata juyo ba bare ta lura da abin d anake yi, ita dai hankalin ta gaba daya yana kan robar igiyoyin da suke jone jikinta su tabi da kallo tana mamakin yadda aka makala mata su. Da sauri na zo gabanta na rike hannaycn ta, hawaye na zubo min na ce. "Aziza ba ki ganni bane? Granny dinki ce fa?" Wani irin kallo na rashin' fahimta ta bini da shi kamar tana so ta yi tunani, sai ta kasa, nan dai Allah Ya taimaka ta cc. "Wace ke?" Murmushi nayi mai hade da kkuka, na sake damke hannuwan tana ce. 131 Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri "Aziza Granny ce fa? Ko baki ganc ni bane?" Dai-dai lokacin Aisha ta shigo dakin tana hango Aziza zaunc da sauri ta karaso gurin cikin murna, ta ce. "Umma ba dai Ammi na ta farfado ba?" Ta fada cikin karaji. Itama binta tayi da kallo irn na rashin fahimta, bata ce da ita komai ba, haka ta kura mata ido ta kasa cewa da ita komai. Ta rike hannunta tana murna, ta ce. "Ammi na baki gane ni bane? Ni ce fa". Shiru tayi har yanzu ta tsaya tana kallon mu daya bayan daya kamar tana so ta tuno wani abu, sai ta kasa. Aisha ta soma rudewa da ta shiga tambaya ta cikin kuka. "Umma, ko dai Ammi na ta dawo kurma ne?" Girgiza kai nayi, na ce, "A'ah, tana magana don tayi min magana kenan sai kika shigo". Nan ta dubi Aisha ta ce, "Kema wace?" 132 Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri Ta nuna ni, ta cc, "Ke kince min Granny, ni Aziza, ita kuma ta ce miki Umma, ni kuma Ammi, to ita kuma wace? Ni kuma wanne ne suna na, Aziza ko Ammi? Ni fa ban san wace ni ba, ku kuma su wane?" Nan da nan tashin hankali mara misaltuwa ya bayyana a tare damu, muka shiga cikin rudani da fargaba, kan kace komai Aisha ta juya ta fice da gudu cikin kuka. Nima hawaye ne ya shiga zubo min, nan take naji tausayin Aziza ya kama ni domin tunaninta na baya ya gushe kamar yadda likita ya fada a baya cewa idan ba a yi nasara ba tunaninta zai iya gushewa na wasu lokaci, idan kuma Allah Ya nufa zata iya dawowa cikin hankalin ta ba tare da gushewar tunanin ta ba. Kalaman likitan ne suka dawo min cikin kwanya ta, nan take hawaye suka shiga zubo min a fuska ta, sai kawai na ga Aziza ta sa hannu tana goge min hawayen, ta ce, "Mene ya sa ki kuka? Wai ku din su wane ne? Na tambaye ku ba ku bani amsa ba". Na bude baki da niyyar bata amsa kenan sai ga Abban ku nan da gudu tare da wasu 133 Zuri'a Daya-Sa'ádatu Muhammad Waziri. likitoci guda ukuisun 'shigo dakin, yana zuwa ya yi saüri ya riko Aziza ya rungume ta yana kuka yana yiwa Allabi gödiyada Yasa ta farfado. Nan ya shiga cewand sl iM thmA ok алiу л Бан "Ammi na Allah agodea damYarbaki kadiyallai sism illsd sidesi man ab aski insbuntana rungune darita bayanaryavgama mürna yaşakestáziya raba tanda jikin şaya shiga dubanta yana cewa. eluri midio ubra ab smmisna kin yi shirubakicce dani komai bayko nimasbaski gancni.ba?"oiveaust sn elsi sy stilinbastayis da kalloutances Al ina kakeskai kdmasaMcyegsunandkaNa jiwka ce minsAmmi nabsurero hakal sworders syi iss stainamut nidio Muwnshis yayis maîuhade dåslkukamуа shigagirgizarkaityana cewa.nb ost sd et nilsdasd nizlio disi newAbbablil namsis nim odiAhb yswed okst asn st eyaswk ans! uddaal taki aniurnatakamashia da yajin ta ambaci sunan sa, cikin dokisyarceswsd nim сgog onsw Kigalánk2ul id s2 εγ οποM" Girlidaszmasa kai tayiy/sarinan daree,Aah nishan sanka bad BYin sh ided obud s uesw eb sust buy bol nadd A By isa 138 134 Σ Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Tashin hankali ne ya sake bayvana a tarc da shi ganin yadda ya gigice yasa likitocin suka ce damu muyi hakuri mu basu guri za su yi aikin su. Dole amu musa musu ba haka muka fito jikinmu babu kwari, muka tsaya jiran ikon Allah, domin duk mun shiga cikin rudani. Sun dauki tsawon lokaci kafin su fito daga baya, can sai gasu nan sun fito. Muna ganinsu muka yi saurin mikewa daga inda muke zaune, muka yo gurin su a sukwane. Abban ku ne ya ce, "Doctor lafiya dai? Ya ake ciki ne?" "Ku kwantar da hankalin ku, babu damuwa, mun yi mata allura ta koma barci. Su za su iya shiga kai kuma muje zuwa (office) za muyi maka karin bayani". Suka tafi mu kuma muka shiga ciki, cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. Mun dan jima kadan muna jiran dawowar sa muji ya akc ciki? Sai gashi nan ya shigo cikin sanyin jii, muna ganin shi sai muma muka kara shiga cikin damuwa, domin bamu san da me ya zo mana ba. 135 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Guri ya zo ya samu ya zauna hawaye cike. a idanun sa, kowannen mu ya shiga jero masa tambayoyi. Cikin karfin hali ya ce, "Aziza tana cikin tashin hankali domin likitoci sun ce ta manta dukkan tunanin ta na baya, ba zata taba iya tuno abin da ya faru da ita a baya ba, komai na cikin kwakwalwar ta ya shude, ba zai dawo ba sai lokacin da Allah Ya tsara hakan, don su kansu sun ce basu da tabbacin tunaninta zai dawo ko ba zai dawo ba, saboda muguwar firgitar da tayi a lokacin da abin yake faruwa, hakan yasa abin ya taba wurin ajiyar tunanin ta. Don haka sai dai mu ci gaba da addu'a da zubawa Sarautar Allah ido, sun ce abin da muka koyar da ita ko muka ganar da ita shi yanzu da shi zata dauka". Gaba dayan mu sai muka sa kuka da yin Salati, muka bi Aziza da kallo akan gadon da take kwance tsabar tausayin ta da muke ji, yarinya karama ta gamu da babbar kaddara rayuwar ta. a 136 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Zuba mana idanu ya yi muna ta kuka domin kasa ccwa damu komai yayi, domin shima ya yi nasa kukan har ya gaji. Muna cikin haka sai ga Mukhtar nan ya zo shi da Mama, shi ne ya samu ya hakurtar damu ya nuna mana babu yadda za muyi sai dai mu rungumi kaddara, haka Allah Ya shiryawa rayuwarta da mu kanmu baki daya. Sai yammaci sosai sannan ta farka, tana bude ido babu wanda ta kira sai Abban ku. "Abba!". Abin da ta fada kenan duk muka juya da muka ji muryarta, domin a tunanin mu ta gane mu, ta dawo cikin tunaninta. Haka kowa ya fara murna, lokaci daya muka hada baki muka ce. "Ammi kin tashi ne?" ba. Har da Mukhtar, domin yana nan bai tafi Sai hanlkalin ta ya yi kansa, domin kafin ta kwanta dazu bata ganshi ba, kallon sa ta shiga yi sannan ta ce. "Kaima din Abba na ne?" 137 Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Wazíri Gaba daya sai suka yi saroro suna kallon ta, haka itama ta kura masa ido tana son jin karin bayani daga gare shi. Ganin yadda take mana kallon tuhuma sai Mukhtar ya yi sauri ya cе. "Eh, ammi ni (Uncle) ne, Uncle Mukhtar suna na, wannan Abba, ga Ammin ki sannan kuma ga Granny dinki". Murmushi tayi ta ce, "Uncle dinku ku nawa ne?" "Eh mana". Ya fada yana murmushi". "To na gode". Ta fada ba tare da tayi masa murmushi ba. Hannu ya mika mata kamar yadda suka saba a da can idan ya yi mata abu tayi masa godiya sai ya miko mata hannu su tafa, shiru ya gani bata miko masa ba, sai jikinsa ya yi sanyi, tausayin ta ya kama shi, nan ya kara tabbatarwa cewa bata ita tuna komai. Haka ya mayar da hannunsa domin ya lura ba zata iya gane me yake nufi ba. Nan da nan labari ya bazu cikin ZURI'A cewa Aziza taji sauki, duk wanda yaji sai ka ganshi ya zo amma idan ya zo ya ga bata gane 138 1 Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri shi ba sai su ji ba dadi, haka za su koma tausaya mata, wasu kuwa saj dai su yi ta kuka. Haka ta tsaya tana ganin kowa sabo domin duk ba wand ata gane, dole tayi hakuri ta daina tambayar su wane su domin ance mata duk 'yan uwańta ne. Alh. Jafar tunda ya ji ance Aziza ta farfado hanalin sa da na Hameed ya yi mugun tashi, domin jira suke su ji anyi sallama ance su fito ana tuhumar Hameed abinda ya aikata, don haka bai samu ya je asibitin ba domin yana cikin zulumi. Amma kuwa Haj. Asiya cikin tawaga ta bi 'yan uwanta suka je dubiya, ta sani sarai bata ganc kowa amma ta ki gaya musu domin bata son ganin kwanciyar hankalin su, ba don komai ba sai don yadda ya mantar da Hameed da kudurin sa tun yana nacin har ya daina domin kullum sai yana bashi UZURIn karya dole ya barshi bai je anyi masa bulalar bayau tsawon wata uku kenan cif. 139 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Bayan kwana uku da faruwar haka Alh. Jafar ya shigo gida da murna ya kira Haj. Asiya da Hameed yake fada musu ya samu labarin cewa Aziza bata iya tuna abin da ya faru da ita a baya, haka ya daga hannu ya yiwa Allah godiya a gabansu. Suka bishi da kallo kamar ta6a66e, ganin irin kallon da suke masa sai yaji wani iri, kai tsaye ya cсе. "Ba za ku hana ni murna ba domin addu'a nayi akan rufuwar asirin mu kuma allah Ya karba don haka dole ne nayi murna, don haka ku shiga ku shirya muje mu duba jikin nata yanzu". Babu wanda ya yi masa musu, haka suka bar yaran a gida suka taho abin su. A can asibiti tunda Aziza ta ci abinci a ranar ya shiga tayar mata da zuciya, amai take babu misaltuwa. Hankalin su ya tashi, suna tunanin ko wani abu ta ci ya tayar mata da zuciya. Ni kuwa tuni na rude hade da fargaba Allah Yasa ba abinda nake zato bane, haka na ja baki na nayi shiru. 140 Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri Zaune muke muna jiran dawowar Abban ku likita ya kira shi, hira muke tayi ita kuma Aziza ta sha magani bacci ya dauke ta. Bamu yi aune ba sai muka ga Mustapha ya shigo a rude yana kuka, gaba daya mikewa muka yi muna jiran me zai ce damu? Mukhtar ne ya fara tambayar sa da cewa, "Yaya me kuma ya faru naga kana kuka?" Cikin uka ya mika masa 'yar takardar da take hannun sa, ya ce. "Mukhtar wata masifar ce ta kara samun mu gaba dawa, duba takardar nan ka gani, likita ne ya ce min Ammi na dauke da ciki wata uku cif". "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!". Abin da gaba dayan mu yake fitowa daga cikin bakunan mu, mikewa nayi amma ban san lokacin da na koma na zauna ba. Gaba dayan mu babu wanda yakara čewa komai, sai tausayin kanmu da na Aziza da ya kama mu. Haka na mayar da kallo na gareta tana ta baccin ta cikin kwanciyar hankali, hawaye suka zubo daga idanu na. 141 Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri Mustapha ya soma kuka kamar Karamin yaro yana cewa. "Ya Allah Ka tona asirin wanda ya janyo mana wannan tashin hakalin, Allah kada Ka barshi cikin nutsuwa da farin ciki". "Ameen Ya Allah, Allah Ka saka mana". Cewar Mukhtar, haka duk muka yi jigum babu wani mai iya cewa komai tsabar jin radadin abin da kunnuwan mu suka jiyar mana. Sallamar Alh. Jafar da iyalansa ita ce ta janyo hankalin mu zuwa gare su, ganin mu duk a tsaye cikin yanayin tashin hankali su ma sai suka razana, da sauri ya karaso cikin gurin ya yi saurin rike hannun Mustapha ya ce. "Mustapha, me ya faru? Ba dai rasuwa Azizan tayi ba?" Cikin kuka ya rungume dan uwansa ya ce. "Yaya Jafar ba mutuwa tayi ba, amma a yanzu zan so ace. Aziza ta rasu domin ta ramu nutsuwa akan wadannan masifu da suke ta faruwa da ita, daga wannan sai wannan. Wai likita ne yanzu yake fada min wai tana dauke da juna biyu na tsawon wata uku". 142 Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri Mutuwar tsaye Alh. Jafar ya yi, nan da nan yashiga cewa. sa. "Ya Hayyu Ta Kayyumu!". Abinda ya yi ta maimaitawa kenan a bakin Hameed da yake gefe dora hannu bjyu yayi akai yana salati hade da kuka, haka itama Haj. Asiya. Ya koma gefe yana ta buga hannunsa a jikin garu, nar da t Mukhtar ya yi sauri ya rike shi ya се. "Hameed baka da hankali? So kake ka ji ma kanka rauni ne?" "Uncle ka barni, bani da wani amfani a rayuwata tunda har...". "Hameed ba zaka yi shiru da bakinka ba sai kana mana surutan banza!". Alh. Jafar ya katse shi cikin hanzari, da sauri ya zo ya rike masa hannu ya се. "Hameed, idan ba zaka tsaya ka kwnatar da hankalin ka ba zan hana ka zuwa nan gurin, baka ganin mu ma kullum hakuri muke yi? Yadda kake jin abin nan mu ma haka muke ji". 143 Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri Abba ya karaso gurin shima ya ce, "Hameed mu dauki kaddara, haka Allah Ya rubutawa 'yar uwarka tun fil'azal, babu wanda ya isa ya goge ko ya hana faruwar hakan". Kuka sosai Hameed ya saka ya sulale kada yana

Chapter 6 of 9