An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ZURI'A DAYA
SA
BY
'ADATU WAZIRI
HAUSABOOK.COM
GOMBE
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
ZURI'A DAYA-1
ammacin ranar asabar an tashi
da muku-mukun sanyi da hazo
a kwaryar birnin Kano, tun da
garin Allah ya waye babu wani hasken ranar da
ya fito, haka garin yake a lumshe gwanin dadi
ga mazauna birnin.
Sanye take cikin kananan kaya, dogon
siket ne na (jeans) dogo har zuwa kafarta hade
da karamar riga a jikinta, sannan ta dauki wani
jaket ta dora akai irin mai tarin gashin nan a
hannunta da wuyanta buzaza kamar gashin
mage, kanta sanye da hular sanyi da yayi
kokarin boye tarin yawan gashin kanta.
Ta turo kofar get din gidansu ta fito
cikin (estate) din su ta ga gurin wayam kaf
babu kowa a waje, haka ta runtse idanunta ta
huro numfashin da ta shaka nan take ya zamo
hayaki, damuwa ta ziyarci kyakkyawar
fuskarta, nan ta shiga addu'a cikin ranta na
cewar Allah Ya kawo lokacin da burinta da
mafarkinta zai zamo gaske, ranar da zata wayi
A
3
ZURIA DAYA
SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Uaziri
ZURIA DAYA-1
ammacin ranar asabar an tashi
da muku-mukun sanyi da hazo
a kwaryar birnin Kano, tun da
garin Allah ya waye babu wani hasken ranar da
ya fito, haka garin yake a lumshe gwanin dadi
ga mazauna birnin.
Sanyc take cikin kananan kaya, dogon
siket ne na (jeans) dogo har zuwa kafarta hade
da karamar riga a jikinta, sannan ta dauki wani
jaket ta dora akai irin mai tarin gashin nan a
hannunta da wuyanta buzaza kamar gashin
mage, kanta sanye da hular sanyi da yayi
kokarin boye tarin yawan gashin kanta.
Ta turo kofar get din gidansu ta fito
cikin (estate) din su ta ga gurin wayam kaf
babu kowa a waje, haka ta runtse idanunta ta
huro numfashin da ta shaka nan take ya zamo
hayaki, damuwa ta ziyarci kyakkyawar
fuskarta, nan ta shiga addu'a cikin ranta na
cewar Allah Ya kawo lokacin da burinta da
mafarkinta zai zamo gaske, ranar da zata wayi
3
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
gari ta ga (estate) din su ya rayu kamar yadda
yake a da can da ZURI'Arsu take guri guda.
Haka ta taho tana bin tarin jerin gidajen
da tun tasowarta ta iske su a haka wanda take
kokarin sanin dalilin barin shi haka.
Tabbas tana iya tuno wani abu a
(memory) dinta ada can, tasan da kowane gida
cike yake da jama'a amına ta rasa sanin dalilin
da yasa lokaci guda ya zamo haka. Tun tana
nacin tambaya har ta gaji ta daina, domin ba a
taba bata wani labari da zai sa ta fahimci komai
ba. Haka ta hakura da fitar da tunanin sanin
komai game da gidajen.
Abu daya ne yafi damunta ganin tun
sandá suka taso su kadai ne suke ryauwa a
cikin (etate) gida biyu su kadai suke zumuncin
su kamar basu da wasu dangi a duniyar sai iya
su kadai.
Ko da yake ba zata kira kanta da mai
damuwa ba domin babu abinda ta rasa na jin
dadi a rayuwa, ko da yaushe suna cikin farin
ciki a rayuwar da suke a cikin gidansu. Babban
abinda ya sanyata damuwa shi ne kawayenta
4
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
da suke yawan mata tambaya akan wadannan
gidajen meye dangantakar su?
Bata san lokacin da ta ce musu na wasu
(family) dinsu ne da suka bar kasar gaba daya
suna can (abroad). Karyar da tayi musu ya
tsaya mata a rai, domin haka yasa abin yake
damunta da kaunar da take ma ZURI'Arta ta
take jin tana (missing) dinsu, duk da kuwa bata
tabbatar da hakan ne kuwa ko ba hakan banc?
Ita dai tana jin a jikinta kamar ta rasa wasu
jama'a da ta rayu da su a can da, to amma jin
babu wani da ya taba fada nata hakan sai take
ganin kamar wani tunani da wani buri nata
yasa take saka haka a cikin tunaninta.
Walwala da daddadar rayuwar jin dadin
da suke yi cikin gidajen su guda biyu yasa take
mantawa da tunanin da yake zo mata rai a duk
lokacin da tayi kokarin fadin wani abu akan
abin da take yawan tunani akai, sai ta ga babu
wanda zai mayar da hankali akan abin da take
magana akai, wannan tun kafin ta kai haka take
yi ma iyayenta, amma sai su mantar da abin su
5
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
dauke shi shirme. Hakan yasa ta bar abin
ranta, take ganin kamar shirmenta ne.
a
Nan take ita ma ta shiga mantawa da
hakan, ta shiga harkokinta tunda kaf cikin ZURI'Arta babu wanda ya taba zama ya fuskanci abinda take nazari akansu. Tabbas
jikinta ya bata kamar ba a so ta san komai na
rayuwar baya da akai sam bare ana hira da ita
don tuno mata rayuwar yarintar ta.
Ta jima a wajen tana ta zagaye a wajen,
nan take taji wata (idea) ta zo mata, take ta
juya ta koma cikin katafaren gidan nasu, kai
tsaye dakin kakarta ta nufa.
"Salam Granny".
Kwance ta ganta ta lullube jikinta da
tattausan bargo tana kallon tauraron dan Adam
cikin tashar Sunna T.v.
Da sauri ta zo ta janye bargon da take
rufe da shi tana dariya, ta ce.
"Wai Granny har wani sanyi ake a garin
ne da za ki shigo daki ki wani buya? Ki fito
kawai ki mu zazzaga waje ko kashin ki zai
6
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
kara kwari, amma idan kika zo kika zauna nan
ba dole ki ji sanyi ba".
"Toh 'yar nema, kin fiso sanyi ya karasani, aj sai ki tashi muje. Dadinta ma ina
da ke, sai ki tsaya ki yi jinyata".
Dariya ta saki, ta ce, "Wayyo Granny na,
ai ni ba zan so na ganki cikin larura ba, domin
zan shiga damuwa. Nafi so kullum na ganki
cikin koshin lafiya da nishadi ko na saki gaba
ina tsokanar ki, haka yafi min dadi, amma ba
na ganki cikin wahala ba".
Murmushi tayi ta ce, "Ja'ira, to rufa min
bargona naji dumina, don har na soma jin sanyi".
"Hahaa! Granny idan ba ki fito kin yaki sanyin nan ba zai kwantar mana dakc, gwara
kawai ki fito mu dan fita waje, don kina faki
ne shi yasa kike ta jin wannan sanyin, amma ni gashi da na fita babu wani sanyi da nake ji. Zo
muje kawai kema ki dan motsa jikinki, kya dan ji dadin jikin naki".
7
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Murmushi ta sake yi ta ce, "Gaskiya fa
kika fada, to miko min hijabi na saka ki gani
muje ko da nan da bakin get ne sai mu dawo".
Nan murna ta kama ta, domin ta nan ne
zata dana mata wani tarko ko hasashenta zai
cimma, domin ta san babu wanda zata bi ya
fada mata abinda take son ji sama da kakarta,
domir babu wata hanya da zata bi don zuwar
musu da abin da take muradin son ji.
Lokacin da suka fito basu iske kowa ba a
wajen har suka zo bakin (gate) din, nan ta ce
mata.
"Granny mu fita muje har zuwa karshen
gidajen nan sai mu dawo, kinga kema sai ki
karajin kuzari a jikin ki".
Ba ta musa ba, haka suka taho suna hira,
hankalin Granny gaba ya yi wani guri,
matashiyar budurwar ta ce.
"Granny nayi miki wata yambaya kuwa
da ta dade tana damuna".
Ta daga idanu ta dube ta, ta ce,
"Raihanatu ina jinki, game da me kike
son yi min wannan tambayar?"
8
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Zan kuwa fada miki, na jima da burin
samun wannan damar bana samu, ni kuma ba
komai bane yasa na damu nima na saniba sai
yawan tambayar da kawaycna suke min wanda
ni kuma sai na rasa me zan ce da su? Dole sai dai
na yi musu karya, sai bayan nayi hakan sai nake
jin damuwa cikin raina".
"Raihanatu yi min tambayar ki, matukar
ina da masaniya zan baki haske akai ko mene ne
kuwa".
"Granny ba akan komai bane illa ina son
sanin tarihin wadannan gidajen da tun tasowa ta
na gansu a haka babu wani mahaluki da yake
rayuwa a cikin sa in banda wanda muke rayuwa
a cikin su guda biyun nan.
Shin MEYE DANGANTAKAR MU da
wadannan gidajen masu kama da wadanda muke
ciki a zaune? Shin su wane suka taba rayuwa
cikin sa ko kuma babu wanda suka taba rayuwa
tun sanda aka gina su? Idan kuma akwai su wane
ne, kuma ina suke yanzu?
Na jima ina jin a cikin tunanina na yarinta
kamar na taba rayuwa da wasu a cikin rayuwata
6
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri sai kuma ina jin kamar a mafarki hakan ya faru dani.
Na sha yiwa Abba da Ammi tambayar
gakan sai suna zamar da abin shirmc, haka kema
da su Mamah Mce duk babu wanda yake zama
ya bani damar sanin wani abu a game da gidan,
kai hatta Ya Abba Junior haka yake min, na rasa
meye dalilin hakan?"
Nan take wasu hawaye masu dumi suka
gangaro daga idanunta, nan da nan ta sa hannu ta
share, ta ce.
"Raihanatu kin yi gaskiya, kuma na kara12
yabawa da hankalin ki da tunanin ki, tabbas
dukkanin mu muna sane da abinda kike nufi da
gangan muke nuna miki bamu gane komai a tare
dake ba, dalilin mu kuwa bama son tuna abinda
ya faru a baya ya sake dawowa cikin rayuwar
mu, duk da kuwa an nuna anfi karfina dole na
hakura na bar abin don bani da mataimaki. Na
jima zuciyata tana saka min kamr ke ce za ki iya
taimaka min, amma sai naga babu wata hanya da
hakan zata faru".
Nan da nan hankalinta ya tashi ganin
yadda hawaye ke fitowa ta fuskar Granny dinta.
57
10
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri "Granny me ya faru kikc kuka? (Plcase) idan tambayar da nayi miki ne yasa ki kuka ki yafe min, ba zan sake ba, mu bar maganar mu
koma gida".
се.
Murmushi tayi mata ta girgiza mata kai, ta
"Raihanatu kar ki damu, babu komai, muje inda kike so sannan kiyi min duk tambayar da kike so zan baki amsa, amma da fatan za ki ja bakinki ki yi shiru, domin gudun rashin fada miki wani abu zai zo ya sake afkuwa, domin ni
tuni na hango hakan, saninki da abin da ya faru a
baya ina ganin hakan zai iya janyo mana haduwar ZURI'Armu, haduwa guri DAYA.
"Raihanatu duba tun daga can gidajen har
zuwa nan duk na ZURI'A DAYA ne, tun taletale guri daya aka rayu, sai gashi lokaci daya ZURI'A ta tarwatse, duk yawan gidajen nan an
zamo gida biyu ne kawai suke rayuwa a cikinsa. Rashin hakuri da duba meye kansa zumuncin
duk shi ne ya kawo rabuwar ZURI'A din hade da
son abin duniya da bakin hali da rashin yarda da kaddara, wadannan su suka yi uwa suka yi makarbiyar tarwatsewar ZURI'A DAYA.
11
Zuri'a Daya-1 _Sa'adatu Muhammad Waziri
ZURI'Ar da ta ginu da son juna da
zumunci tayi suna, amma sai gashi lokaci daya
ta tarwatse kowa ya kama gabansa, babu wanda
yasan halin da wani yake ciki. Bugu da kari da
takama da tarin dukiyar da ke cikin Zuri'ar duk
sun taimaka gurin rashin tausayi da son duba
muhimmancin meye Zumunci? Duk da kuwa
akwai manya a cikinta amma shaidan da son
zuciya bai sa an duba hakan ba, haka aka bari
Zumuncin Allah ya watse".
"Rehana ki mu koma gida muje mu zauna
na warware miki dukkan sarkakiyar da guguwar
da ta shigo ta tarwatsa mu yau tsawon shekaru
kusan ashirin babu daya cikinmu da ya waiwayi
dan'uwansa don zumuncin Allah, tsabar shaidan
ya gama nasara akan abin da ya yi niyya, amma
na so ace yayanki Abba yana nan na baki
wannan tarihin".
"Granny kina so ki ce min shima Ya Abba
bai san komai ba har nakc tunanin ya sani?"
"Ba zai rasa sanin wani ba tunda shima bai
da wayo sosai abin ya faru, sai dai na san zai iya
tuna wani abu da ya faru da sauran 'yan uwansa.
Ke dai mujc za kiji yadda asalin ZURI'Arki
12
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
suke, cikin yardar Allah sai mun samu ta dawo
yadda take da can duk kuwa da abin yana da
matukar wuya saboda ba a rabu ta dadi ba".
Haka suka dawo cikin wani irin alhini, a
falo suka ci karo da kannenta suna ta kallo,
kanwar ta Zulaiha ta ce.
"Aunty Haana ina kika je ga wayar ki a
hannu na Zahra tana ta kiran ki na ce mata kin
fita kin bar wayar a falo?"
"(Okay) Zuly, ki rike min wayar a
gurinki, kowa ya kira ki ce bana kusa".
Farouk ya ce, "Aunty Haana na karba na
dana (game) don Allah?"
Haana shi ne sunan da kowa yake kiranta
da shi, domin sunan kakarta ta ci Raihanatu, shi
ne a gida suke kiranta da Haana har can ma
(school) haka kowa ke kiranta.
"Oya Ya Zuly ta baka ka dana din".
Nan ya shiga murna, ita kuwa ta shiga
tsokanar shi akan ba zata bashi ba daga karshe
dai ta bashi, sannan ita kuma ta juya ta bi bayan
kakarta.
1
1
,
1
1
1
1
13
Zuri'a Daya-1 sa.upatu Muhammad Wazin
Zaunc ta iske ta tana jiran zuwanta, layi sallama ta shiga. Guri ta nuna mata ta zauna, ta
Cc.
"Raihanatu ki nutsu ki bani hankalin ki,
yanzu zan baki cikakken tarihin ryauwar
ZURI'Ar ki da taki rayuwar gaba daya".
Ji tayi dadi ya kama ta, ta ce.
"Yauwa Granny, shi yasa nake son ki,
idan na gama ji ni kuma sannanzan fada miki
burina da mafarki na akan ZURI'A ta".
"Babu laifi, Allah Ya cika mana burinmu
da mafarkinmu, yanzu za ki ji komai domin
kema hakan ya zama izna gareki da mutanen
duniya gaba daya, domin darasin dake cikin
labarin".
*
"Zuri'ar Alhaji Nasir Dan fillo Zuri'a ce da
tayi fice da suna daga cikin tsatson su, asalin su
mutanen Rano L.G.A ne, sannan Fulani ne na
asali gabansu da bayan su, sun fito cikin yankin
fulanin garin 'yan asali.
Tun duniya na kwance Allah Ya yi masa
tarin dukiya mai dumbin yawa tarc da wayewa ta
14
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
duniya, wasu Turawa da aiki ya hada su tare har
aminci da sabo ya shiga tsakanin su ta harkar
sana'ar auduga.
Da girman sa sosai suka sa ya shiga
makaranta wanda hakan yasa ya goge sosai ta
yadda za su cigaba da gudanar da sana'ar su
cikin kwanciyar hankali ba tare da wasu sun
tsaya suna y musu tafinta ba.
Basirar sa da kwazo da amana da yake
nunawa a tsakanin su, hakan ya kara daukaka
darajarsa gare su. Ana cikin hakan ne suka dauke
shi zuwa kasar su can Burtaniya, da da farko
anki yarda a gurin iyayensa domin surutu ne ya
yi yawa cikin rigarsu wanda har ya kusa yin
tasiri, amma kasancewar dagacin garin yasa baki
dole iyayensa suka hakura suka saki lamarin tare
da sharadin duk abinda ya faru ga dansu da shi
za suyi kuka, haka ya amsa da ch ya yarda.
Sai da ya shafe shakara uku bai zo gida ba,
babu irin masifa da surutu da ba a yiwa dagaci
ba, daga baya ya ja bakinsa ya yi shiru domin
yasan babu abada zai faru da shi domin ba
wannan ne farau ba don haka bai wani saurari
hayaniyar su ba.
15
Zuri'a Daya-1 _Sa'adatu Muhammad Waziri
Rana daya sai gashi ya dawo gida tarc da
tarin alherin da ya bawa kowa mamaki, da da
farko kamar basu gane shi ba tsabar kyau da fari
da yayi hade da gogewa irin na 'yan boko, hakan
ba karamin dadi ya yiwa iyayensa ba ya zamo
shima tamkar Bature ba dan kauye ba.
Haka iyayensa suka rufe ido da kunyar su
suka je suka ba ma dagaci hakurin irin abinda ya
faru a baya can. Murmushi ya yi ya nuna musu
babu damuwa komai ya wuce.
Bayan komai ya, nitsa ne suką yanke
shawara da dansu akan da kansu za su je gidan
dagaci su nema masa auren diyarsa, bai yi musu
musu ba sai dai ya nuna musu yana son komawa
idan ya dawo sai ayi auren da duk wacce suka
zaba masa.
Fau-fau suka ki yarda, suka ce ba zai bar
kasar nan ba sai tarc da aurensa, sai dai idan anyi
ya barta ya tafi.
Bai yi musu ba ya ce to, su fan bashi
lokaci kadan zai yi magana da iyayen gidansa.
Lokacin da suka je gurin dagaci kan batun
auren diyarsa da suke nema yaji dadi sosai,
16
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
lokaci guda ya amince, da yake dama yana da
yara mata.
Dukkanin su Fulani nc, dama basu fiye
bawa junan su aurcn wasu ba idan ba Fulani 'yan
uwansu ba, dama tun can da akwai DANGANTAKAR AURE a tsakanin lardinsu.
Lokacin da Alhaji Nasir yaji wadda aka zabar masa zai aura yayi murna sosai domin
dama tunda yaji an ambaci auren yaran gidan dagaci ita ya kawo a ransa, domin ya santa
tuntuni har ya taba kawo ta cikin ransa ga wadda
yake son aura, amma sanin wannan zamanin
duniya tana kwance kai da baka da wani a
aurenka na fari sai abin da iyaycnka suka zaба
maka yasa tuni ya yi watsi da hakan.
Lokacin da ya diba don komawa
Burtaniya a lokacin ne iyayen gidansa suka dira
a Rano suka cc sun bashi goyon baya yayi
aurensa ya tafi da matarsa can su zauna, ai kuwa
ba karamin farin ciki ya dadu a zuciyarsa ba,
cikin kankanin lokaci aka daura auren Alhaji
Nasir da Haj. Kubra.
Bayan bikin su irin na Fulani da akai mai
tarin al'adu wanda hakan ya kara burge iyaycn
17
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
gidansa Turawa, domin dama haka suke da son
al'adun gargajiya (culturc). Bayan biki da sati
daya suka dage Burtaniya abinsu.
A kalla sai da suka yi shckara biyar cikin
shckarun nan sau uku suka zo ganin gida,
lokacin da suka dawo Nigeria har sun samu
karuwa na yara biyu, Bara'atu da Ja'afar, sannan
re suka dawo Rano da zama.
Nan fa arziki ya ci uban na da, domin a
cikin birnin Kano suka bude wani katafaren
(Company) a cikin kwaryar Kano na audiga,
kuma shi ne yake kula da komai, sai dai tura
musu da komai can suka daina zuwa shi ne yake
musu komai.
A cikin ZURI'Ar mahaifinsa aka kara aura
masa wata mai suna Safiyya, suka zauna lafiya
ita da Haj. Kubra lafiya lau, suka hade kansu
zaman lafiya, babu wanda yake jin kansu. Sai da
suka shekara hudu kowacce na haihuwa, nan fa
ya fara tara ZURI'A, a wannan lokacin ne
mahaifiyar sa ta nuna tana sha'awar ya auri 'yar
kanwarta da suke ciki daya.
Nan fa Haj. Kubra da Safiya suka ta da
hankalin sa akan su sam basu yarda ba, tashin
18
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
hankali babu irin wanda ba su yi masa, shi kuwa
ya dage akan cewa babu wanda ya isa ya hana
shi bin UMARNI da mahaifiyar sa ta ba shi.
Wannan kurarin da ya yi bai sa sun saduda
ba, nan ya ga abin nasu sai dada yawa yake yi,
haka ya sa su gaba ya cc suk wacce zata iya
zama da shi to ta shirya don babu abin da zai
faru a gurinsa. Nan suka hada baki suka ce masa
bai isa ba.
Tsawa ya yi musu, ya ce wacce ba zata ita
zama ba to ta tattara ta bar masa gidansa, suka ka
da baki suka cc babu inda za sujc su da shi mutu
ka raba.
Haka ya koma Rano can wata riga ta
asalin Fulani inda nan dangin mahaifiyar sa
suke, nan suka gaisa da Gwaggonsa mahaifiyar
Aziza da ake kira da Azi, wadda ita ake son hada
su da ita. Da kyar ta yarda suka gaisa saboda
kunyar da takc ji tashi, nan yayi kokarin su hadu
da Azi amma fau-fau taki zuwa don kunyar sa da
take ji, sai 'yar uwarta kanwa garcta wadda suka
zamo tamkar Hassana da Usaina, wato
Raihanatu, ni kenan".
19
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Sai a lokacin ta saki murmushi, ta kalli
IHaana, ta cc.
"Kina biye dani ko?"
Haana ta gyara zama, ta cc.
"Granny har da ke cikin labarin kenan?
Gaskiya ina jin dadin labarin, to ya aka yi? Anyí
auren kuwa sun zauna lafiya a gidansu? Gaskiya
labarin yana min dadi".
Murmushi tayi ta ce, "Bini a hankali za ki
ji komai, saurin me kike yi? A sannu za ki ji
komai, ina yi miki baya ni ne dalla-dalla don ki
fahimci komai yadda za ki gane kowa cikin
Zuri'ar ki, ba kiji komai ba ke dai ki bani
nutsuwar ki kawai".
Ta cigaba, "Ba irin kokarin da ban yi da
Azi Innawuro ba taki yarda su hadu da Alh.
Nasir amma taki, domin mace ce miskila da
kunyar tsiya, ba wai son shi ne bata yi ba, tsabar
kunya ne irin nata. Haka ya hakura ba don ya so
ba, sai dai dani ya yi hira a ranar. Sai washegari
da ya dawo aka tursasa dolc suka hadu.
Cikin dan kankanin lokaci magana tayi
karfi, magana ta yadu kowa yana sawa al'amarin
albarka. Amma a 6angaren iyalinsa kuwa Haj.
20
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Kubra da Haj. Safiya sun hade kansu sai rashin
kyautatawa suke masa babu sassauci, haka suka
hade kansu ya kasa sarrafa su, dolc ya tattara su
ya barsu don basu isa su hana shi abinda ya yi
ra'ayi ba.
Haka har Allah Ya yi aure tsakanin Alh.
Nasir da Innawuro, aka dauko ta daga riga zuwa
kwaryar cikin birnin Kano, wanda tunda take
zuwanta garin Kano sau daya, sai gashi zama na
dindindin ya kawota. Gata a lokacin ita cе
karama cikin su, duk sun girme mata, haka aka
kawo ta cikinsu.
Tsananin kewar da muka yiwa junanmu
shi ne ya hana ta sakewa a gidan, ga uwa uba
wata tsangwama da take fuskanta gurin abokan
zamanta, domin sun hade mata kai ta kasa sakin
ranta, kullum cikin kuka take akan wai ita a
mayar da ita gida, ba zata iya zama ba. Nan ya yi
ta tausarta ta ki, dole sai da ya zo ya sanar da
mahaifiyar sa halin da suke ciki, da kyar ta ce to
idan dai ana son zamanta sai dsai a kawo mata ni
nmu zauna tare.
21
Zuri'a Daya-I So'adatu Muhammad Wazir
Abin sai ya bata dariya, ta ce idan haka ne
ta kwantar da hankalinta a yau zata sa a kawo ni
matukar zata saki ranta.
A ranar kuwa na zo gidan, gani na tare da
ita yasa ta saki ranta. Sai dai a lokacin zamana a
gidan na fuskanci irin zaman takurar da take a
ciki, amma tsabar hakuri irin nata da zurfin ciki
bata taba fadawa kowa ba.
Haka süka hadu suna dada nuna mana
kiyayya da wariyar launin fata, gaba daya sai
suka dauki tsanar suka mayar da ita kaina don
sun ga ni ce nake tanka musu, sai dai ma tana
bani hakauri. Dole tayi mini na daina kula su
don bana son ganin 6acin ranta, domin ita dama
haka take da hakuri da rashin son tashin hankali.
Ana cikin wannan irin zaman Allah Ya
bawa Innawuro ciki mai tsananin wahala, domin
ta sha bakar wahala kamar ba zata dorc ba. Nima
na rasa nawa kwanciyar hankalin ganin 'yar
uwata tana cikin damuwa da wahala, a wannan
lokacin har gida sai da aka mayar da ita da ciwon
ya yi tsanani.
Cikin ikon Allah da cikin ya yi kwari sai
gashi ta warc, sannan aka fara kokarin
22
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
komawarta gidanta. A wannan lokacin Baffanmu
ya ce babu inda zan koma, nayi zamana saboda
manema na suna ta damuwa akan yaushc zan
dawo? Kuma girma na ya yi yawa. A dolc na
hakura na dawo na tsayar da wanda nake so a
aurar dani.
Babu yadda na iya dole ina kallo ta dawo
ita kadai, satin ta daya sai ga Goggo Hanne
(wato mahaifiyar Alh. Nasir) ta zo gidanmu, ta
ce na hada kayana na koma Kano gurin 'yar
uwata.
Murna gurina kamar na zuba ruwa a kasa
na sha, babu yadda Baffa ya iya dole ya hakura
na dawo gurinta. Nan na kara samun labarin
wani sabon takura da kishiyoyinta