suke mata.
A ranar sai da muka rabota da su domin
babu wacce na ragawa a cikin su, dama kuma
suna jin shakkata domin tun da na dawo gidan
kishin ya koma kaina har Allah Ya kawo lokacin
haihuwar ta, ta haifi da namiji mai kama da
ubansa fitik, don duk cikin 'ya'yan sa babu
wanda yake da tsananin kama da shi irinsa.
23
Zuri'a DayaI Sa'adatu Muhammad Waziri
Murna a ranar tamkar akansa ya farа
samun haihuwa, wanda hakan ya dasa tsana da
Kiyayya akan wannan haihuwar.
Ko kadan Alh. Nasir baya iya 6oye
murnar sa ta haihuwar yaron, ranar suna aka saka
masa suna Mustapha.
Shekarar Mustapha biyu a duniya a
lokacin ne Baffan mu ya matsa min akan dole sai
na baro nan na dawo gida, ya gaji da masu yi
masa maganar aure na. Wannan karon haka
muka hakura na dawo gida cike da kewar 'yar
uwata da dana Mustapha.
Maganar bikina ta kankama, har an fara
shirin biki wanda zan aura ya ce ya fasa, ni dai
nasan ba laifi nayi masa ba dole aka nemi sanin
dalili aka rasa, haka aka hakura dole.
Da Baffana ya zaci ni ne na ki shi, wasa
gaske har mutum uku suna sake fitowa rimi-rimi
sai magana ta rushe. Baffa ya shiga damuwa,
Alh. Nasir da kansa ya zo ya roki Baffa ya barni
na koma can ko mijina a can yake da kyar ya
yarda don dai babu yadda zai yi nc.
Lokacin da na dawo nan na iske 'yar uwata
Innawuro na fauke da ciki na biyu wanda sam
24
Zuri'a Daya-I _Sa'adatu Muhammad Waziri
bata wahala kamar wancan ba, haka murna ta
kama ni domin dama ni da za a barni tare da 'yar
uwata mu rayu guri guda da haka ya fi min dadi.
Wannan haka yake itama a gurinta, domin
idan ina tare da ita ta fi jin dadin gidan da kuma
samun sukunin tsangwamar da take samu gurin
abokan zamanta, domin har yanzu sun ki su
barta ta sake a cikin gidan su, kuma suna bakin
cikin zamana a gidan, domin babu abin da nake
bari Innawuro tayi da kanta, komai ni ce nake
mata na hidimar gida da na yaro wanda ya
danganci na mijinta ita ke yi da kanta, su kuma
hakan na kona musu rai.
Daf da cikinta ya kusa isa haihuwa lokacin
abokin Alh. Nasir ya fito za'a yi mana aure, an
gama shirin komai za ai biki ranar da Innawuro
ta haihu ta haifi diya mace, a ranar muka samu
labarin Allah Ya yiwa Alh. Kabiru rasuwa,
hankali na ya tashi har na fara tunanin ko ba zan
taba yin aure ba daga wannan sai wannan.
Ranar suna aka sanyawa jaririya suna
Maryarı, lokacin 'ya mai kama da uwarta fitik
kamar an tsaga kara, haka muka wanzu cikin
murna da kuma jimamin rashin da muka yi na
25
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Alh. Kabiru, babu wanda bai tausaya min ba
amma ni samun Maryam shi ne ya kara dauke
min damuwar, tun daga lokacin na fara fitar da
rai na akan aure.
Mustapha na da shekara hudu Maryam na
da shekara daya a duniya Innawuro ta samu cik
wanda tun daga samun sa take cikin matsala, ga
kuma laulayi na kin karawa, domin kullum tana
cikin larura, dole yasa aka cire Maryam daga
shan Mama ganin itama ta fara yin rashin lafiya.
Kullum muka zauna ni da ita ta dinga yi
min magana akan cikin nan, da kuma cewa.
"Rehana anya kuwa wannan cikin zai
barni na rayu da ku? Domin tunda nake ban taba
daukar ciki mai wuya haka ba. Idan har na mutu
ki daure ki kular min da Maryam da Mustapha,
ki rike su tamkar yadda za ki rike yaran da kika
haifa a cikin ki, bana so ki bar su hannun su
Saude, domin ba za su rike su tsakani da Allah
ba. Domin na fuskanci tsanar da suke min ita ce
ta koma kansu idan har na haifi wannan cikin
shima ki hada ki rike, domin ji na nake kamar
rayuwata ta zo karshe.
26
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Hankalina ya yi mugun tashi domin
kalamanta sun taba zuciyata, nan take na nuna
mata kada ta ji komai yadda ta haifi sauran haka
ma wannan zata haihu lafiya, ciwo ne kawai yasa
take wannan sambatun.
Kullum muka zauna sai tayi min wannan
zancen, nan take na ce ni dai ta daina. Da ciwo
ya yi yawa dole muka tattara muka koma Rano,
watanmu kusan uku a can ta warware sarai. Sai a
lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa, amma kullum muka cauna sai ta ce min.
"Raihanatu, don Allah ki kula da yaranki
sosai, ga amanar su nan duniya da lahira".
Haka zan nuna mata ta daina min irin
wannan zancen, ganin bana so yasa ta daina yi
min.
Tun komawar mu Rano sau biyu ne zan cе
ga kafar su Saude a gidanmu, domin ni a gurina da zuwan su da rashin zuwan su duk daya.
Ranar da suka yi zuwa na uku ne a nan ne
Innawuro ta nemi su yafe ma juna, su kansu sai a
lokacin suka ji nadamar abinda suke mata.
27
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Cikinta wata takwas bai isa haihuwa ba
rana daya wani ciwo ya tasar mata, kwananta
biyu a asibiti ta ce ga garinku nan.
Tsananin rudani da rikicewa babu wanda
ban shiga ba, domin ban taba dandana jin zafin
mutuwa irin wannan ba. Babu yadda za mu yi
dole mu dauki hakuri da kaddara.
Alh. Nasir ya yi matukar jin mutuwar nan,
amma duk da haka sai ya nuna yafi tausaya min
da yaran da aka bari.
Haka kowa ya zo gaisuwa sai ya tausaya
min, Mustapha da Maryam kuwa suna nanike
dani, babu wanda suke yarda da shi sai ni. Da na
kalli yaran sai naji kuka ya zo min.
Ana gobe sadakar arba'in muna zaune da
su Baffa da Innar su suka zo min da wani labari
da ya ruda ni rudu na gaske kuwa, na cewa wai
gobe a gurin addu'a za a daura aure na da Alh.
Nasir a yi madadi da ni.
Kuka na saka musu na ce ban yarda ba na
auri mijin 'yar uwata, aka yi aka yi dani na tsaya
da kukan na ki. Nan wasu daga cikin iyayen mu
maza da mata suka shiga saka baki tare fa fada
min cewa Alh. Nasir nemi hakan da kansa.
28
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri
Ya cc, "A rokar masa gurinki, ba don
komai ba sai don saboda yara sun riga da sun
gama sabawa da ke, babu wanda suke sani bayan
ke".
Shiru nayi ina kuka, mahaifiyar sa ta
karbata ce,
"Raihanatu ko ba don komai ba don
yaranki ki daure ki maye gurbin 'yar uwarki,
domin kin fi kowa sanin zaman da za su yi a
gidan ubansu idan ba kya kusa da su. Sannan
kuma da ana mutuwa a dawo idan ki ka yiwa 'yar
uwarki haka ta dawo ta gani zata yi murna da
farin cikin kin kula da yaran ta, na tabbata ta
baki amanar yaranta a hannun ki".
Nan nayi shiru na dinga tunanin irin
maganganun da muke yi da ita akan yara, tun
kafin ta kwanta rashin laifyar nan. Na ci kukana
na koshi, babu yadda na iya dole na amsa musu
na yarda.
Nan farin ciki ya cika su, suka shiga saka
min albarka da nuna min cewa dama haka Allah
Ya rubuta, shi yasa tun farko Allah bai kaddara
yin aurena ba, domin a lokacin shekaru na sun
29
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
dan soma dagawa sabanin yadda akewa kowacce
budurwar are a kauyen mu.
Da daddare Alh. Nasir ya zo ya yi min
godiya da taimakon da nayi masa, kuma insha
Allahu ba zai taba barinta cikin damuwa ba, zai
mata duk abinda take so ita da yaransa.
Kuka na saka mishi domin ban san da
wacce kalma zan ce da shi ba, ganina cikin
damuwa ya bani hakuri ya ce na tashi na koma
cikin gida.
Kafin na koma ciki aka kawo min yara
suna kuka, a wannan lokacin naji dole ne ma na
saki riana na auri Alh. Nasir domin yaran su
tashi gaban mahaifinsu, don mu samu damar
basu tarbiyya ni da shi.
Ganin yadda suka yi shiru a jikina sai ya
samu damar cewa.
"Raihanatu ko ba don ni ba don yaran nan
da suke ganinki kamar wacce.ta haife su ki yarda
ki maye gurbin 'yar uwarki matukar ba kya so su
san maraici".
"Babu komai na amince, ita kkuma Allah
Ya jikanta da rahama".
30
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Murna ya nuna sosai, ya yi min godiya, haka muka rabu na shiga ciki da yara. Maryam
na rungume a kafada ta shi kuma Mustapha na rikc masa hannu muka shige muka bar shi zaunc
a gurin.
Washe gari haka aka hada daurin aurenmu
da addu'ar arba'in din Innawuro, mutane da dama
sun nuna farin cikin yin haka, addu'a aka yi sosai
a gurin. Tunda ana cikin alhini ba wani shagalin
biki don haka aka tsayar sati mai zuwa zan tare
dakin 'yar uwaia nade da yara na biyu.M
a
Sam Alh. Kabir bai sanarwa da matansa
maganar auren mu ba, don bai barsu sun zo
Ranon ba, haka ya ce su zauna a Kanon su yi
duk abinda ya dace, sai washegari ya zo musu da
abarin daurin auren, haka suka ji abin sama.
Take hankalin su ya yi mummunan tashi, suka shiga ce mas aya ci amanar su ya yi aurc ba tare
da sanin su ba. Ganin da yayi za su bata masa
okaci ya tafi ya barsu a gurin.
Haka dai na zo na tare a dakin 'yar uwata, gori da takaici da habaici babu abin da ban uskanta gurin A'i da Saude ba, duk bakina
amma na kasa yi musu komai, da zama ya fara
31
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
zama na gaji da abin da suke yi min na fara tanka
musu.
Ke na takaita miki daga ni har yaran sai da
zaman gidan yaso ma gagarar mu, da kyar ya
tsaya akan gidansa abubuwa suka dan soma
sauki, da suka ga an soma girma sai suka saduda.
Haihuwa ta uku, da fari na haifi Aziza, sai
Mukhtar wanda ya ci sunan Baffanmu da Allah
Ya yiwa rasuwa, sai dan auta na Usman. Kafin
su girma Allah Ya dauki Aziza da Usman, Ya
bar min Mustapha da Maryam da Mukhtar.
Ita kuma Haj. A'i tana da yara biyar masu
rai, su ne Bara'atu, Jafar, Lukman, Habib sai
Shchu da aka sa ma sunan Usman nawa. Ita
kuma ta binnc uku duk mata.
Sai Haj. Saude tana da hudu, Aminu,
Hamza, Aminatu da Hajara. Kinji yaran nan
guda goma sha biyu da na lissafa miki su ne suka
hadu suka gina junan su, suka zamo ZURI'A
DAYA, ta cikin ZURI'Ar su ne aka samę ku,
kuma cikin su har yanzu suna nan babu wanda
ya rasu, sai ba a guri daya suke yanzu ba, za kiji
dalilin da yasa duk suka watsu cikin duniya".
32
Zvri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
"Raihanatu na faro miki labarin nc tur
daga tushen ku, don ki ganc komai dalla-dalla,
shi yasa na yi miki haka saboda kada zuwa gaba
ki cc ba ki gane kowa ba tunda na ware miki
daki-daki kin gani".
Haana tayi murmushi cikin alhini ta ce.
"Granny na tausaya miki wallahi, kuma
kin yi kokari sosai. To shin ina su Haj. Saude da
Haj. A'i? Suma suna raye ko sun rasu?"
Tayi murmushi ta ce, "Raihanatu kenan, ai
baki ji komai ba, ki biyo ni a sannu domin yanzu
ne zan fara baki labarin komai har zuwa yau din
nan da muke ciki, domin duk abubuwan da kika
ji a baya somin tabi ne, ke dai ki saurare ni".
Ta gyara zama ta cc, "Tam".
"Kamar yadda na fara fada miki zaman
kishi muka yi sosai da kishiyoyi na har sai da
yara suka girma aka dasa musu 'yan ubanci,
wannan baya son wannan dan dakin, amma
nawa ne kawai ake yiwa haka.
Da kansa Alh. Nasir ya ganc haka, ya tara
kan yaransa gaba daya da matansa ya ce matukar
ba a kawar masa da wannan muguwar al'adar ba
to gaba daya zai kori matan ya sakc wasu.
33
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Sanin zafin sa da suka yi da kuma ganin
tarin dukiyar da yake da shi a yanzu, domin akan
arzikin sa na da sai mucc ya ninka zaman sa a
wannan lokacin, don yanzu komai nashi ne na
kansa ba tare yake da na kowa ba. Domin ba
gidansa kadai ba, 'yan uwansa na jini babu
wanda bai dagawa kafa ba ya gina kansa, kusan
duk kannen sa sai da ya dawo da su cikin garin
Kano suma suka kafa kansu.
Don haka ya tsaya sosai akan iyalinsa, sai
da ya kawar da wannan bambancc-bambancen
ya gina kauna da soyayya tsakanin yaransa.
Hakan ba karamin dadi naji ba, domin burina
kenan naga mun samu hadin kan yaranmu. Babu
laifi nima mun dan samu dai daituwa da abokan
zamana.
Arzikin Alh. Nasir kullum daduwa yake
yi, domin ya rungumi zumuncin Allah, duk
wanda ya raße shi shima sai ya yi arziki, domin
bashi da bakin ciki matukar zaka yi gaskiya to
zai daga maka kai ma ka tsaya da kafar ka.
Da yaransa da na 'yan uwan ya tsaya akan
su, duk abin da zai wa dansa shi zai yiwa dan
dan uwansa don haka duk 'wanda ya gama
34
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
karatunsa wajc yakc tura shi ya karo karatu tun
duniya na kwance.
Haka ya shiga gina manya-manyan
(company) a garuruwan Arewa yana diban
jama'a yana sawa ciki, duk burinsa adan yaransa
sun girma bai da burin barinsu aikin gwamnati,
yana so su hadu a gùri guda don su zama wani
abin kwatance a duniya.
Bara'atu ita ce diyar da muka fara aurarwa
cikin Zuri'ar, domin dama ita ce babba kaf cikin
su, itama din auren dangi aka yi mata da dan
yayan Alhaji Nasir wanda shima shi ne babba a
cikin jikokin gidan.
Jafar, Lukman, Aminu da Hamza su ne
manya a ciki, su ne aka fara aurarwa bayan auren
Bara'atu, duk auren gida aka yi musu domin anji
dadin na farko. Dukkan su sai da suka yi digirin
farko, wasu sun yi na biyu wasu kuma sai da
akai musu aure sannan suka yi digirin na biyu.
Haka Zuri'ar ta zamo ta 'yan boko, hatta
mu ma da ba wani bokon muka yi ba sai muka
taso kamar 'yan boko, domin muna auren 'yan
bokon, ga kuma 'ya'yan mu 'yan boko.
35
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Kasancewar mu daga tushe daya muka
fito duk dinmu Fulani ne kuma na yanki daya,
sai aka dinga kiran ZURI'Ar mu da gidan farare.
Maganar kyau kuwa muna alfahari da ZURI'Ar
mu, don wasu suna dauka ccwa muna da
dangantaka da Larabawa, nan kuwa basu sani ba
asalin Fulanin Rano ne".
Haana tayi dariya ta ce, "Kai Granny, irin
wannan kura kai haka".
"Ba kurara kai bane, gaskiya na fada
domin mu Fulanin na yankin mu daban muke,
kuma kema kin san haka a gareki".
Haana tayi murmushi ta ce, "Granny na
yarda, ci gaba da labarin ki, ina son ki ci gaban
naji an fara gangarowa don kina ta samin kaunar
ZURI'A ta har na matsu naji karshen labarin".
"Lokaci guda Zuri'ar mu ta fara yaduwa
domin 'ya'yanmu sun fara ajje mana jikoki, haka
muka dauki soyayyar mu duk muka dora su
akansu. Sai dai kaf cikin Zuri'ar babu wanda
yayi farin jinin Abdulhameed dan Alh. Jafar,
domin yaro ne abin so daga zuciyar mu baki
daya.
36
Zuri'a Daya-I Sa'adaty Muhammad Waziri
Ba komai ne ya jawo haka ba domin shi
ne jika namiji na farko a cikin Zuri'ar, sauran
duk mata ne, don an haifi har (twins) suna
mutuwa, akansa ne dai suka fara tsayawa.
Shekarun Hamecd biyu aka yi auren Mustapha da kannen sa uku, Amina, Hajara da
karamar su Maryam, duk cikin dangi suka samu
mazajen su, Mustapha ne dai'ya dage sai da ya
auri ba 'yar dangi ta jini ba, ita 'yar aminin Alh.
Nasir ce, mutanen Garo ne, suma Fulani ne na
asali, suma haka suke kamar Larabawa.
Hameed ya tashi cikin gata da soyayyar
iyaye da kakanni, domin kowa da irin son da
yake nuna masa, har gatan ya so ya yi masa
yawa, ba ya laifi ayi masa fada.
Ganin yadda ZURI'A ta soma yawa farin
ciki yana ta samuwa a cikinta yasa Alh. Nasir
yin tunanin yiwa yaransa gini yadda za su hadu
guri daya har karshen rayuwar sa, don baya son
ya ga abin da zai raba kansu.
Don haka ya samu katon fegi (wato fili)
iya ganinka ya ce anan yake son ya gina ma
zuri'ar sa gidaje inda za su dunkule guri guda har
37
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
zuwa lokacin da kowa zai yi nasa iyalin suma su
zauna ciki.
Lokacin duniya na kwance, ga filayc nan
ko ta ina, kuma gashi babban mutum da sukc da
alfarma a wannan gwamnatin, don haka ya zuba
kudinsa sosai ya samu abin da yake so don har
matansa mun fara yi masa surutu ya ce mu dai
mu barshi, yasan abinda yake, kowa ya zo ya ga
filin sai ya girgiza kai.
Haka aka fara gini iri daya har gidaje
sama da sha biyu, kuma duk tsarinsu iri daya, sai
dai guda daya da ya bambanta da sauran wurin
girma. Nan ya fara gaya mana cewa gida ne zai
gina tunda yara maza har mata kowa ya dawo
gurin da mazajen su, wanda kuma ba su yi aure
ba gashi nan guri yana jiransu. Kowa ya shiga
nuna murnar sa yiwa Allah godiya ganin inda
aka tanadar musu don rayuwa guri guda.
Tunda aka yi kokarin daina nuna wariyar
daki da daki sai rayuwar tayi dadi, kowa ka gani
yana farin ciki da abin da dan uwansa zai samu.
Soyayya da kaunar juna ya gama kewaye zuri'ar,
babu wani mai kuka da dan uwansa.
38
Zuri'a Daya- Sa'adatu Muhammad Waziri
Nan ma ya je Kaduna ya kara gina wasu
gidajen masu tarin yawa, duk don yaransa da
'yan uwansa. Tarin ariziki dai na ko maye Allah
Ya bawa Alh. Nasir, sai dai fatan samun na
labira shi din ma a zahiri kowa yana hango masa
hakan.
Shekaru biyu da gama ginin ya tattara kan
ZURI'Ar sa guri guda, shima yana cikin su,
kowa da gidansa a ciki mata da maza.
Burin sa ma sen ganin zuri'ar sa guri guda
ya cika, don haka ko da yaushe yana tare da su
idan ya fito daga gidansa ya ga tarin gidajen
'ya'yansa saı ya shiga farin ciki da yıwa Allah
godiya da Ya yi masa arzikin yara da na dukiya,
yana fatan Allah Ya hada kansu.
Gidaje ne a jere wasu na'kallon wasu, ko
da yaushe Alh. Nasir yana tare da jikokin sa a
falon sa suna ta zuba hira, don a lokacin yana da
tarin jikoki sun kai kusan goma. Babban wanda
ya yi fada da farin jini shi ne Hamced.
Kullum burin Hameed Allah Ya bashi
kanwa mace, amma har yanzu shiru domin
Gannen sa duk maza ne a cikin family din, duk
lokacin da ya tamibayi kakansa cewa shi fa yana
39
Zuri'a Dage-i Sa'adalu Mukammad Waziri
son a haifo masa kanwa mace sai ya cc ya
kwantar da bankalin sa gashi nan iyayen sa
kwanan nan za su haifa masa duk kanne mata.
Lokaci guda aka yi haihuwa hudu duk
maza ne, nan fa Hamecd ya yi ta rigima wai shi
bai ga mace ba a ciki, duk kanne maza aka yi
masa. Hatta mahaifiyar sa Ilaj. Asiya itama
namiji ta haifa, sai Haj. Aisha ce mátar
Mustapha ita ce kadai a cikin su bata haihu ba.
A icker's ne Haj. Asiya ta се,
"Abdulhameed ka kwantar da hankalin ka, kaje.
gidan Ammin ka Aisha ita ce zata haihu, sai ka
ce mata ta haifo maka kanwa mace".
Abinka da yaro da kuma abin da yake so,
nan kuwa tayi masa hakan ne don ya yi mata
shiru daga rigimar da yake damunta da shi.
Yana fita daga gidan kuwa bai zame ko
ina ba sai gidan Ammin sa, nan ne ya iske mu ni
da Aisha da Mustapha muna zaune a a falo muna
hira, sai gashi nan ya shigo.
Cikin harshen Fulatanci nayi masa
magana, naicc ya zo gurina. Da yake lokacin
muna yi musu duk sun iya sosai, sai ya make
40
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
kafada ya ce shi ba gurina ya 2o ba, gurin
Amminsa ya zo, duk sai muka sa dariya.
Sai ta kira shi, ya zo jikinta ya kwanta
yana taba tudun cikinta.
Ta ce, "Hameed me kake so na baka nc?
Oya fada min".
"Ammi baby girl nake so ki haifo min na
samu kanwa, Mama ce ta ce na zo gurinki na
fada miki ki haifo min baby girl tunda su basu
haifo ba".
Dariya muka yi gaba dayanmu, domin
abin nashi gwanin dariya, nan ta cе.
"To Hameed, kai tayi min addu'a idan kayi
sallah, Allah Ya sauke ni lafiya na haifo maka
baby girl din da kake so".
Haba! Nan da jin ta fadi haka ya shiga
murna yana tsalle wai za a haifa masa baby girl,
bai jira kowa ba ya juya ya koma gida a guje yа
fadawa Maman sa.
Tun daga ranar kullum Hameed sai ya zo
gidan wai ya duba ko an haifa masa baby girl
dinsa, lokacin yana da shekara shida a duniya.
Jin shiru baby bata zo ba ya fara nuna
damuwar sa, lokaci guda ya dauke kafa ya daina
41
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
zuwa, a ccewar sa ya yi fushi tunda Ammi ta ki
zhaihuwa.
Nan ta shiga nuna masa lokaci ne bai yi
ba, ya kara hakuri.
Ya ce, "To tunda haka ne zan dawo gidan
na jira har sai kin kawo min babyn".
Gudun fitinar sa yasa ta ce masa to, nan ya
juya ya koma gida ba jimawa sai gashi da
kayansa tili a hannu wai ya dawo gidan gaba
daya sai lokacin da babyn ta dawo zai koma
gidansu. Duk wanda yaji labarin sai yayi dariya
ya jinjina rigimar Hameed.
Ganin da gaske yake nan Aisha ta shiga
addu'a Allah Ya bata diya mace don ta cika ma
Hameed burinsa, duk da kuwa itama burinta
kenan haihuwar diya mace.
Kullum idan ya tashi babu abin da zai
tambaya sai cewa, "Kin haifi babyn nawa?"
Sai ta ce a'a, addu'a ce baya yi sosai idan
yayi sallah.
Sai ya cc, "Eh haka ne, jiya sau haka nayi
addu'ar". (Ya nuna yatsun sa guda biyu)
42
Zuri'a Daya-! Sa'adatu Muhammad Waziri
Tayi murmushi ta cc, "To dinga yi sau da
yawa zaka ga na haihu lafiya, na kawo maka baby girl din taka".
Nan zai shiga murna, ya cc, "Tam".
Cikin yardar Allah wata Alhamis da
daddare Allah Ya sauki Aisha lafiya, ta haifi
katuwar 'yarta mace jajir da ita, lokacin IHamced
yana bacci bai tashi ba. Cikin kankanin lokaci
labari ya iske ko ina cikin Zuri'a, tun daren aka
cika gidan da murna.
Aisha ta yiwa Allah godiya da Ya cika
mata burinta Ya bata abin da take son samu.
Bayan an dan nitsa ne nan aka shiga taya
Hamced murna ya samu abinda yake so, ba а
tashe shi ba sai da garin Allah Ya waye tangaran,
lokacin ne ya farka. Kukan baby din ne ya tashe
shi, zumbur ya mike ya ce.
"Lah! Ammi kin haifi baby girl din ne?
Don jiya na yi miki addu'a da yawa sosai".
Murmushi tayi ta ce, "Eh mana, ai tun jiya
kana barci kanwar taka take ta neman ka baka
tashi ba, shi ne yanzu ma take kuka da bata
ganka ba".
43
Zuri'a Daya-i Sa'adatu Muhammad Waziri
Dariyah ya saka yana kallonta, ya ce,
"Lah! Ammi dama ta sanni nc?"
Gaba daya dariya gurin aka saka, nan ya
shiga murna da rawar kafa wai shi a bashi ita ya
dauke ta, nan dai aka taimaka masa ya daukc ta
ya shiga murna hade da yin shirmen sa na yara.
Haba! Abin nema ya samu gurin Hameed,
sam bai son abin da zai raba shi da 'yar kanwar
sa, ko da yaushe yana like da Ammin sa, da ta
fara kuka zai tambayi me aka yi mata take kuka?
Haka zai ce a bashi ita ya rarrashhe ta.
Haka dai ya zamana shi ma ya zama dan
riano, don haka zai zauna ya tankwashc kafa а
dora masa ita ya rike, da ta soma kuka zai cе a
karbe ta.
Ranar da Alh. Jafar ya zo ganin yarinyar
lokacin ba ya gari akai haihuwa, da ya ganta zai
tafi sai ya се.
"Hameed, ai sai ka shirya mu koma gida
tunda anyi maka abinda kake so".
Ya tuburc ya ce ai shi babu inda zai tafi,
ya dawo gidan Ammi tunda ita ce ta haifa masa
baby girl, ba zai koma gidan Mama ba tunda ya
ce ta haifo masa baby girl ta ki.
44
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Dariya aka yi gaba daya domin shirmen
Hameed din ko yaushe gaba yake yi, hakan yasa
kowa yake son zaman sa a gidan domin yana
nishadantar da mutane.
haka?"
"To idan na kenan na fadawa maman taka
Ya gyada kai alamar, "Еh".
Haka nan kuwa akai fafur ya ki komawa
don haka dole aka barshi zuwa kwana biyu, ana
tunanin da kansa zai nemi gida.
Ranar suna jaririya ta ci sunan murgayiya
'yar uwata Aziza, mahaifiyar sa. Ni ce na ce a
saka, da shi sunana ya ce, na ce masa a'ah gaba a
saka ni.
Ni da kaina na ce kada wànda ya boye
mata sunanta, kowa yana kiranta da haka domin
zan dinga jin dadı ina yawan tuna 'yar uwata.
Haka kuwa aka yi, Aisha ce kadai ke
kiranta da Ammi na don alkunya, haka sauran
surukan amma cikin yara kowa da sunanta yake
kiranta, ni kuma nafi son haka, dole sauran
iyayen ma maza suke kiranta da haka.
Abin kamar wasa Hameed kememe ya ki
gidan su, dole haka aka hakura ya dawo gidan
45
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
gaba daya. Tun daga nan ya zamo dan gidan, har
zuwa girman sa.
Amma kafin nan kusan kullum da shi ake
rainon Aziza, idan Aisha tana aiki shi ne yake
zaune yana kula da ita. Wani ikon Allah 'ya tana
girma kamanninta yana fitowa sak da na mai
sunanta, tamkar ita ce ta haife ta. Iko ne na
Allah, babu abinda ba ya iyawa tabbacin Shi ne
Yake da komai a hannun sa.
Tsananin shakuwa da kauna gami da sabo
shi ne ya kullu tsakanin Ammi da Hameed da
kanwar sa Aziza, don yadda suke a yanzu ko
mahaifiyar sa bais shaku da ita ba kamar suka
shaku da Aisha.
Kowa ya yi farin ciki da hakan domin shi
wata rana ma mantawa yake da zmaman sa, haka
yake jinsa cikin wani sabon duniyar.
Azizas haka ta soma wayo, babu wanda ta
fi sani a rayuwar ta daga Amminta sai Hameed
dinta. Haka yarinya ta taso da karsashinta da
komai, kowa yana son ta domin kaf cikin su ita
kadai ce;ya mace kamara. Haka kowa ya dauki
son duniya ya dora shi akan Aziza.
46
uri'a Daya-1 __Sa'adatu Muhammad Waziri
Kullum gidan cike yake da yara, cikin