su
babu wanda ya isa ya taba ta sai Hameed ya
bashi dama. Idan kuwa aka samu wani abu na
sabani ya shiga tsakanin su, to ranar baka isa ka
ga Azizan sa ba, don ko kofar gidan ba zaka zo
ba bare ka shiga gidan nasu.
Haka yaran za su ta kawo masa (sweet)
daya nashi daya na Aziza, duk wanda bai kawo
na Aziza ba to ranar ba za ayi wasa da shi ba.
Lokacin da Aziza ta cika shekara uku haka
tayi wayo da surutu cakwai kamar kanari, gata
'yar dabas a kasa, sai dan banzan wayo da
surutu.
Tun rana karama Allah Ya dasa mata
kyau, wayon ta da surutun ta shi ne ya kara mata
farin jini har sai da ta zo ta zarce farin jinin
Hameed. Ita kuma tunda Allah Yasa tayi kafa ta
zamo bata son zama, kullum ta shiga wannan
gidan ta fito wannan, haka ZURI'A gaba daya ta
dauki son duniya ta dora shi akan ta. Kowa so
yake ta zo gurinsa, kuma duk wata fita da
iyayenta maza za suyi sai an kawo mata
tsarabarta daban.
47
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Duk ranar da Hameed ya dawo daga
makaranta bai ganta ba haka zai ta da hankalin sa
ya fita neman ta gida-gida har sai ya nemota
sannan ne hankalin sa zai kwanta. Nan zai ta yi
mata fada yana cewa ta daina fita yawo, idan ba
haka ba zai daina kawo mata (sweet) daga
makaranta. Hkaa zata ce masa ta daina, gobe
kuma sai ta sake.
Haka wata rana ta faru lokacin Mukhtar ya
zo ya fita da Aziza suka tafi yawo har lokacin
dawowa daga makarantar Hameed yayi ya dawo
gida bai ganta ba, ya shiga duk inda yake tunanin
zai ganta bai ganta ba. Bayan an fada masa ga
inda suka je haka ya je ya tsaya da (uniform) bai
cire ba ya tsaya bakin get yana jiran dawowar su
yaji shiru, da yake dama shi din dan shagwaba
ne nan ya samu guri yana kuka wai Azizan sa.
Haka ya zauna yana kuka, nan ya hangi
motarsa ta dawo, nan ya hangi Aziza ta fito da
gudu daga motar ta zo ta rungume shi tana
tambayar cewa.
"Yaya Hameed me aka yi maka kake
kuka? Ko Ammi ce ta dake ka?"
48
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Turc ta yayi ya ce, "Ba ke ce na ce ki
daina fita yawo ba sai ina nan mu fita tare, kin ce
kin daina sai kuma gashi kina tayi".
Mukhtar ya ce, "(Sorry) Hamced, laifin (Uncle) ne ba na Ammi na bane, shiru ka daina
kuka tunda mun dawo".
Nan ya share hawayen sa ya ce, "To (Uncle) nayi shiru".
Ya sa hannu ya goge hawayemn sa,
sannan ya mika hannu zai riko Aziza, ta ture
masa hannu wai ita tayi fushi, ta wani make kafada.
Mukhtar ya rike haba, ya ce, "Ammi na ya
haka? Kin manta da Yaya Hameed dinki ne?
Baki ga akan ki yake kuka ba da bai ganki ba?
Oya maza bashi hakuri".
Turo baki tayi gaba, bata ce komai ba sai
ta mika masa hannu wai ya rike ta su tafi. Dariya
da mamaki ne suka kama Mukhtar, ya jinjina irin
tarin karancin shekarunta sai wayon tsiya da yin
abu kamar 'yar shekara goma. Anan dai suka
shirya ta dalilin sa.
Tsananin shagwaba da rashin kwaba da
sangarci gurin Hameed ba a magana, domin baya
49
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
yin komai sai abinda ransa yake so, don haka
6aci yake yi son ransa ana biye masa, domin
abin d ayake na shagwaba Aziza ma bata yi
tsabar gata da yake samu ta kowane bangare na
iyayen sa.
Alh. Nasir yana matukar farin cikin ganin
yadda 'ya'yansa suka hada kai guri guda suna
zumuncin su yadda yake so, hakan yasa ya kaга
gina musu wasu gidajen a can Kaduna, ganin
wasu suke rike da manyan kamfaninsa a can,
don haka yadda ya gina na Kano haka ya gina
tsantsarin su daya komai da komai, don haka ya
ce, ko da wasu za su koma can ya kasance kowa
yana da nashi a can, don bai son ya ga ya raba
kan yaransa ta kowane fuska.
Kullum burinsa akan yaransa shi ne su
hada kansu guri guda su yi zumunci kada su bari
wani ya zo ya shiga tsakanin su har a zo a raba
musu zumuncin su. Sau da yawa haka zai zhada
su yara da mu ioyayen su yana ta yi mana nasiha
akan zumuncin Allah.
Aziza na da shekara biyar aka yi mata
kani mai suna Nasir, a lokacin ne ma aka haifi
Muhammad kani na biyu ga Hameed. Sannan sai
50
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
a shckarar Allah Ya bama Maryam haihuwa, ya
bata da namiji, ta yiwa Mustapha takwara, wato
Ya Abban ki. Sannan kuma a wannan dai
shekarar Murja matar Alh. Aminu dan wajen
Haj. Saude itama ta haifi da namiji mai suna
Sameer.
In takaita miki a shękarar nan dai sai da
kusan duk yaran mu suka haihu, a kalla cikin
shekaru biyu sai da muka yi jikoki sun kai
bakwai, kuma duk maza, mata biyu.
Amma bayan shekara daya sai da muka
rasa mutum uku, cikin su na farko Kabir wanda
yake bin Hameed, sai Nasir kanin Aziza, sai
kuma Fiddausi 'yar wajen Hajara.
Shekarun Aziza goma a duniya lokacin
Allah Ya dauki ran Alh. Nasir, rasuwar da har
yanzu bamu mayar da gurbinta ba, tsayawa baki
zlabarin irin tashin hankalin da muka shiga ba
zai yiwu ba, domin kowa yasan mun yi rashin
babban bango.
Ya je wata Umra ne cikin Azumi yana
dawowa da sati biyu Allah Ya aiko masa da
ciwon ajali, wani zazzafan ciwon ciki ne ya
51
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
kwantar da shi, kwana biyu Allah Ya amshi
abinsa.
Babu wanda bai ji mutuwar nan ba cikin
Zuri'ar, to amma babu yadda za muyi dole muka
hakura muka dauki dangana da ta zamo mana
dole, domin kowa dan haka ne.
Bayan sadakar uku haka dangi suka hada
mu suka shiga yi mana nasiha mu da yaran mu
akan mu hada kanmu domin wannan shi ne
babban burin dan 'uwansu, da wasu maganganu
da suka dinga fada mana wanda mu kanmu
bamu sansu ba, suka ce duk shi ne ya basu
wasiyya idan ta Allah ta kasance gare shi to sai
su sanar mana. Nan dai muka kara yin kuka da
jin irin abubuwan da ya so ganin munyi.
Tafiya ta soma tafiya babu wata matsala,
domin manyan da suke tare damu suna dora mu
akan hanya, haka aka ci gaba da gudanar da
rayuwa tamkar mai gidan yana nan, sai dai abin
da ba za a rasa ba. Haka manyan yaranmu suka
tsare mana mutuncin mu, babu abninda muka
nema muka rasa.
F
52
furi'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Lokacin da aka zo rabon gado al'amarin ba
karmain bamu mamaki yayi ba na jin irin tarin
dukiya da kadarorin da ya mutu ya bari, sai a
sannanZuri'a ta kara tabbatarwa cewa Alh. Nasir
ba karamin miloniya banc, tsayawa na fada miki
irin tarin dukiyar da kowa ya samu bata lokaci
na.
Abin godiyar Allah Zumuncin mu haka ya
ci gaba da dorewa ko da yaushe, sai dai abu daya
ne ya soma bamu tangarda akai, shi ne Hameed.
DOmin sam baya ji, tsabar gata da shagwaba da
yake samu yasa ya fara kawo matsala, sai yanzu
ne aka fara gano cewa yawan gatan da yake
samu nes yasa ya dawo baya jin tsoron kowa.
Hameed ya fara bawa kowa matsala da ya
fara abu anyi masa fada sai ya hau yin fushi da
mutum ko ma waye, ganin yawan fadan da
Abban ku yake masa akan rashin jinsa yasa ya
bar gidan ya koma gaban mahaifansa, nan suka
gyara masa daki ya koma abinsa.
Shiru kwana biyu Hameed ya diana
shigowa gidan, Amminsa da kanta ta zo gidan
wai ta zo bikon danta. Lokacin suna zaune a falo
ita da Haj. Asiya wato mahaifiyar sa ta ce.
53
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Yaya na biyo sawun dana, kwana biyu
naji shi dif, ke kuma ba ki dawo min da abina ba,
ko nima har dani a cikin laifin? Don naga da ya
ficc bai kara waiwayo ni ba".
"Hmm! Ai kin san halin dan naki da taurin
kai da kafiya, tun jiya nake cewa ya koma yana
ce min wai shi takura masa ake yi".
"Yaya takura kuma? Kin san halin Abban
su dai, nasan akan yawon nan da ya fara ne suke
samun takun saka".
"To ai shima bai kama ta yana yi masa
haka ba, nawa Hameed din yake da za ana matsa
masa kamar wani mace?"
Muryar da suka ji ta doki kunnen su nan
take suka juya suka ga Alh. Jafar ne yake
maganar, kai tsayc yanayin fuskar su ta sauya.
Kallon junan su suka yi jin irin furucin da
yayi, ko da yake Aisha ce kawai ta fi nuna
mamakin saßanin ita Haj. Asiya.
"Aisha kar ki damu, Hamced ya same ni
da kansa ya ce ya gaji da zaman can ya dawo nan
ya dan huta don ya bukaci can ya dawo, don
haka ina son a bashi wannan damar domin da
can shi ne ya nema muka bar shi ya dawo
54
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
hannur ku, amma tunda yanzu ga abin da yake
so sai ku barshi yayi, da fatan ba za ku damu ba
tunda yanzu ya fara girma bana tunanin za a
hgana shi samun 'yancin sa ba".
Aisha taji kalaman nasa sun yi mata wani
iri, don bata taba zaton wannan furucin daga
bakin babban yaya ba.
Ta cc, "Shi kenan yaya Jafar, zamu bar shi
mu gani ko kwana biyu zai hucc".
"A'a ku barshi dai kawai, bana yin tunanin
ma zai koma ma gaba daya".
Gabanta ya fadi ta ce, "Yaya na ga kamar
cikin bacin rai kake, ko ya fada máka anyi masa
wani abu ne da ya 6ata maka rai?"
Girgiza kai yayiya ce, "Ko kadan kada ki
sa ma kanki damuwa, shi ne dai ya bukaci haka a
ransa, ni kuma nake son nayi masa abin da yake
so".
"Shi kenan Yaya, babu laifi tunda ka ga
hakan ya fi kuma mu ba zamu yi fishi da shi ba,
muna nan muna jiran dawowar sa nasan da ba
zai fushi da iyaycnsa ba".
Tana gama fadin haka ta mike cikin
sanyin jiki.
55
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Haj. Asiya ce ta rako ta har bakin get din
gidan, ta cс.
"Aisha kada ki nuna damuwar ki, naga
kamar ranki bai so ba, ni na rasa me yasa Daddy
ya fada miki wannan maganar, amma don Allah
ki nuna komai ba komai ba, wannan sirrin mu ni
da ke ba tun yau ba yake son Hameed ya dawo
hannunsa, nayi-nayi ya fada min dalili amma
yaki, dole na rabu da shi tunda haka ya faru ki
bar shi mu zuba masa ido, nasan halin Hameed,
muna nan zaune zai ce zai koma gidan su.
Ran Aisha yayi fari domin jin kalaman da
Haj. Asiya ta yi mata, bata san lokacin da ta saki
murmushi ba, ta ce.
"Yaya na gode sosai, insha Allahu nima
zan bar wannan maganar cikin rai na, babu
wanda zan tonawa ita".
Nan dai suka yi sallama cikin dadin rai,
amma dai cikin ran Aisha ta tafi a was-wasi na
cewa to mene ne dalilin da yasa yaya Babba
yake son Hameed ya bar gurimu ya dawo
hannunsa bayan irin tarin zumuncin da suke yi
da dan uwansa, domin kaf cikin DANGIN
JUNAn ba sa taba yin abu kansu tsaye ba tare da
56
Zur'a Daya-I Sa'adaty Muhammad Waziri
sun yi shawara da shi ba tsabar girman da suka
bashi, haka kuma ya samo asali ne gurin mahaifinsu.
To amma mai zai sa a fara samun baraka
ta gurinsa yana matsayin shi ne babba cikin
(family)? Dolc ne ta boye wannan matsalar, ba
zata bayyanawa kowa ba, domin ta hango so da
kaunar dansa a idanunsa wanda take tunanin
matukar za a nuna ja akan abin da yake so to
tabbas wata matsala na iya faruwa. Don haka
duk ma mai zai faru ba zata taba bari Mustapha
ya fuskanci komai ba cikin wannan lamarin,
domin zai iya yin wani tunani da zai zo ya cutar
da ZURI'Ar su, saboda haka ita kuma ba zata
bari gakan ya faru ba cikin yardar Allah.
Aziza ta shiga nuna damuwar ta ganin
kwana blyu ba ta ganin Ya Hameed dinta, domin
kwana blyu ba sa taßa 'yar tsamar da suke yi da
juna.
Kai tsaye gurin mahaifinta ta nufa ta ee,
"Abba wai me yasa Ya lameed ya ki dawowa
ne? Na je gidan Daddy na ee masa ya dawo ya ki, wallahi nima zan koma can kuma idan na tafi
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
ba zan taba dawowa ba sai ranar da ya dawo
sannan zan dawo".
Murmushi yayi ya cc, "Ammi na kenan, to
ya zan yi da yayanki? Baya jin magana, na san
fushi yayi da ni amma na san zai hucc, amma
idan kinga za ki koma can to bi shi, nasan idan
ya ganki wata kila ya yarda ya biyo ki ku dawo
gida tare".
Haba! Nan Aziza ta shiga murna da tsalle
wai za ta koma gidan Daddy gurin Ya Hameed
dinta. Da gudu ta nufi dakin Amminta ta na fada
mata abin da Abba ya се.
Itama murna ta nuna domin dai tasan irin
shakuwar da ke tsakanin Hameed da Aziza ta
tabbata daya ba zai iya rayujhwa ba tare da dan
uwansa ba, dole ta san duk inda daya yaje sai
dayan ya bishi. Nan da nan ta kwashi kayanta
bai fi kala uku ba ta juya ta fice da gudu tana
murna.
Mustapha da Aisha suka bita da kallo
suyna mata dariya, domin ganin irin murnar da
take yi.
Mustapha уа сс, "Aisha zan so naga
kaunar nan da yaran nan sukc wa junan su ta
58
Zuri'a Daya-1 Sa'adntu Muhammad Waziri
dore har zuwa girman su, domin sai na hada
auren su cikin yardar Allah, saboda na yarda da
kaunar da sukc wa junan su".
Murmushi tayi ta cc, "Allah Ya nuna mana
hakan, da kuwa an karfafa zumunci domin
wannan shi ne burin Alh. Abbas kuma insha
Allahu sai mun cika masa burinsa wanda yana
kwance cikin Rabarinsa rahma zata na zuwar
masa domin ZURI'A DAYA za su hadu su yi ta
yada Zuri'u cikin yardar Allah".
"Allah Ya amsa wannan fata naki, Ya
hada kan ZURI'A dinmu ta zamo DAYA, yadda
babu inda baraka za ta zo mana".
"Ameen". Ta fada cikin farin ciki.
"Ya Hamce! Ya Hameed!! Ya Hamced!!!
Kana ina ne ina ta kwada maka kira ka ki ka
amsa, Aziza ce fa".
Da sauri ya fito daga shiryayyen dakinsa
daga shi dogon wando da farar singilet a jikinsa,
don kwanjinsa ya fara fitowa na matasan samari,
lokacin shekarun sa sha shida.
Farin ciki ne ya bayyana a fuskar su
lokaicn da suka ga junaware hannu ya yi ta zo ta
59
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
fada jikinsa ya wani runtse ido na jin dadi, daga
nan sai ya sakcta, ta сс.
"Ya Hameed (guess what)?"
Ya runtse ido ya bude, ya ce, "(No idea)"
Murmushi tayi ta ce, "Baka ga me yake
hannuna ba? To nima na gudo daga gida na biyo
ka gidan Daddy, nima ba zan koma ba sai
lokacin da zaka koma sai mu koma tare".
Tsalle ya yi ya rike hannunta, ya ce,
"Yauwa Aziza na, wallahi dama kullum
tunaninki nake yi, sai naji kamar naje na sato ki
ki dawo gidan Daddy mu zauna da ke, amma sai
ina jin tsoron Abba kamar ba zai barni ba. Kin
san Abba yana da fada da tsawa, ni kuma bana
son fada shi yasa na dawo nan, da na fadawa
Daddy ya cè na dawo ba zan koma ba".
"Nima ba zan koma ba, a nan zamu yi ta
zama ni da kai tunda Abba yana maka fada da
tsawa, kuma ni bana son naga an yiwa Ya
Hameed na tsawa da fada".
Murya suka ji ance, "Yauwa yaran Daddy,
ku shirya ku zo mu fita abinmu ajc a siyowa
Aziza komai sabo, ba zata yi amfani da kayanta
60
furi'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
na gidan Abbanta ba, daki itama za a gyara mata
irin na yayanta Hamecd".
Juyowa tayi cikin farin ciki da ta ganc
wanc yake maganar, Daddy dinsu nc. Da sauri ta
jc ta rungume Daddy, ta dce.
"Yauwa Daddy na, kaima baka so na koma ko?"
ta cc.
Cikin murmushi ya ce, "Iih Ammi na".
Nan Haj. Asiya ta karaso gurin ckCKın fara'a
"Aziza waio kema kin biyo yayanki kun yiwa Ammi da Abba yaji ko?" "Eh Mami ba zamu koma ba tunda Abba
yana yiwa Ya Hameed dina tsawa da fafa, shi
kuma baya so, ya ce ba zai koma ba, anan zamu
yi ta zama tare ko Ya Hamced?"
Daga mata kai yayi yana ta murmushi
alamar ch haka nc.
"Mami ina ne dakina da za a gyara min na
kwana? Amma fa ni kadai ba zan kc kwana da
su Muhammad ba tunda ni ce babba irin Ya
Hamced".
сс.
Dariya suka saka gaba dayan su, Daddy ya
61
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Gaskiyar ki Ammi na, dole ne a baki daki
a shirya miki shi sosai har sai ya fi na yayanki kyau".
Murna da tsalle ta shiga yi tana cewa.
"Ych! Daki na zai zama (very beutiful) ya
fi na Ya Hameed".
Ta shiga yi masa gwalo, nan da nan ya
kufula doimin dama sun saba da hakan dama
kwana biyu ba su tabа ba.
Abinka da Aziza dama gata gwanar tsiwa
da tsokana shi kuma Hameed da bi sanin ya fara
girma haka ya biye mata suna ta guje-guje a
cikin falon, iyayen na musu dariya. Nan dai ta
samu ta buya jikin Daddy doinsu, babu yadda
zai yi dole ya rabu da ita yana cewa zan kama ki
ne za ki gane kuren ki".
Haka dai rayuwar su ta ci gaba da gudana,
tuni Aziza zamanta ya koma gidan su Hameed,
kowa ya yi farin ciki da hakan. Sai dai ni ce
kawai da naji raina bai so ba, ba don komai ba
sai irin sake da nake hangowa a cikin gidan
domin kaf cikin Zuri'ar mu babu gidan da
Turanci ya ratsa da boko irin gidan Alh. Jafar,
domin ganin yadda naga suke rayuwar su na
62
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
sakc. Sam ba ya tsawatar wa yara, yaro sai abin
da ya ga dama shi zai yi ba kuma wanda ya isa
ya hana shi.
Na so na nuna ccwa Aziza ta dawo gida,
amma gudun kada na haifar da wata matsala
cikin ZURI'A sai na ja baki na nayi shiru, domin
da na ce wani abu za a iya canza min abin da
nakc nufi.
Hakan yasa na yi wata hikima nayi shiru,
sai dai abu daya na sa cikin raina zan saka idanu
akan rayuwar Aziza a cikin gidan, domn ban so
ta tana mace ta taso da tarbiyyar taurin kai.
Haka na yi wata hikima da wayo da
dabara, nakan shiga gidajen sauran yaranmu ba
don komai ba sai don kada su gano cewa gidan
Jafar kadai nake zuwa ayi tunanin da bana zuwa
sai da jikata ta koma gidan sannan na tsiri zuwa,
sai na mayar da abin cikin hikima yadda babu
wani da zai zarge ni da wani tunani, yau naje
gidan wannan gobe naje gidan wancan, hakan
yasa na fara janyo Aziza jiki na.
A duk ranar da naje gidan nasu nakan
ganin abinda raina baya min dadi, domin sai ina
ganin Hamced na yawan jan Aziza jikinsa, wata
63
Zuria Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
rana idan tana zaunc zai zagayo ta baya ya
rungume ta a gaban kowa a cikin gida yake yі.
Ranar nan na zo gidan nayi mata wayo na
cc ta zo mujc gidan kawunta, nan nake mata fada
cikin wayo ina ccwa.
"Ki daina bari yayanki Hamced yana
kwanciya a jikinki ko ya rungume ki haka kawai,
domin yin hakan babu kyau. Amma idan wani
guri yajc ya dade ba ki ganshi ba za ki iya yi
masa oyoyo. Kał ki manta fa girma kike yi, wata
rana Abbar ki ma da kansa za ki daina yi masa
haka".
Nan dai da dabara na ganar da ita, wata
rana kuwa da na zo gidan da kaina naga tana
cewa ya daina yi mata haka, bata so. A gaban
iyayensa hkaa suka ji kunya, amma sai suka
basar kamar ba su ji me take fada masa ba.
Da kamar abin ya yi sauki, wata rana da
naje gidan sai na ise shi da ita da Kannen sa а
falo ya kwanta daga shi sal singileti da wando
gajere, wal ya gaji suna yi masa tausa, ita kuma
kadai ee mace eiki.
4
uri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Nan na zo na tsawatar masa, nace kada ya
sake ya Kara yin haka, wai bai san ya fara girma
ba?
Ina fadin hkaa karaf a kunnen Jafar ya
shigo cikin falon, nan naga yanayin sa ya sauya.
Nima sai nawa ya sauya, na cc.
"Jafar, wai me yasa za kuna barin yaran
nan haka ne ba za kuna nunawa Hameed girma
yake ba?"
Allah za a "Ayi hakuri Gwaggo, insha
kiyaye. Kai Hameed maza tashi ka bar gurin
nan".
Ransa 6ace ya bar gurin yana kumburo
baki abinsa, jikina babu dadi muka gaisa ban
wani jima ba na fito na tafi gidan Aisha. Nan na
labarta mata da abin da yake faruwa, nan ta
kwantar min da hankali, ta ce.
"Ummah kada ki ji komai, na tabbata
Yaya Asiya za ta lura da su, cikin ikon Allah Zai
kare komai".
Duk irin nusarwar da take min na jita ne
kawai, amma bana jin jikina da zuciyata sun
amince min.
65
Zuri'a Daya-I sa'adatu Muhammad Waziri
Kullum hankalina ba ya kwanciya da
tunanin haka nakc kwana nake tashi, ganin rai na
ya kasa kwanciya yasa na tari Mustapha da
maganar, nan ya kwantar min da zuciyata da
kuma nuna min matukar muka nemi Aziza ta
dawo gida za su zargi wani abu, amma shi da
kansa zai je ya kwaso su tunda dama nasa ne.
Jin haka sai raina ya yi sanyi domin na
tabbatar idan yaran a gurin Aisha suke babu abin
da zai daga min hankali, don nasan tana da kula
duk da kuwa ba yara ne a gabanta ba amma tyayi
na riko na gani.
A cikin kwanaki uku da muka yi maganar
sai ga Aziza da Hameed sun dawo gida gurin
Aisha, sai a lokacin hankalina ya kwanta domin
nasan dole ne Aisha zata na kula da su duk da
kuwa irin tsohon cikin da take da shi.
Tun sanda suka dawo Hamced ya dinga
jinsa duk a takurc, ko me yake yi sai yana ji
kamar ana takura masa. Haka ya koma shan
ruwan tsuntsayc, yau yana nan gobe yana can,
haka ya sabar ma Aziza yau idan bata ganshi ba
gobe zata ganshi. Hikimar sa nana ko zata koma
ta bishi amma sai ya ga ta ki komawa, dole sai
66
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri yakc dawowa, domin sam beya sakcwa idan yana gidan domin baya samun dama yana hada jikinsa da nata.
Ana cikin wannan halin ne Allah Ya sauke
ta lafiya, ta haifo ki, kyakkyawa da ke kamar 'yar
uwarki Aziza, domin tun zuwanki duniya kowa
ya zo ya ganki sai ya ce kina kama da Aziza,
kamar daga jikinta ki ka fito don kama.
Haba! Murna gurinmu babu misaltuwa,
nan muka godewa Allah da zuwanki duniya".
Haana tayi murmushi ta ce, "Kai Granny
dama dani? A raina na zata wani ne ko wata,
amma gaskiya kin iya labari".
Murmushi tayi ta ci gfaba da cewa, "Aziza
ta shiga murna da tsalle wai itama tanyi kanwa
su zamo su biyu, ta daina zuwa gurin kowa tunda
ga shi itama an yi mata baby girl abin da take so
kenan dama.
Tsananin kaunar da Aziza take nuna miki
ya yi yawa, domin bata barin kowa ya dauke ki
sai ita, don sabod ake ma sam bata son zuwa
makaranta, kullum sai anyi da gaske sannan take
tafiya.
67
Zuri'a Daya-I _Sa'adatu Muhammad Waziri
Haka Hameed shi ma ya shiga nuna miki
Kauna, don haka kowa sai da ya nuna farin cikin
zuwan ki duniya. Ranar suna aka rada miki
sunana Raihanatu, domin dama burin Mustapha
kenan ya haihu ya yi min takwara.
Tun bayan sunanki da sati Aziza ce da
kanta ta ce ita zata zaba miki sunan da za ana
kiranki, ita ce ta zaba miki suna Haana, madadin
ana kiran ki Raihanatu.
Kowa yaji dadin sunan, haka kuwa kowa
yake kiran ki har yanzu.
Tunda aka haife ki Aziza bata kara yarda
ta je gidan kowa ba, haka Hameed yayi zuciya
tun da ya koma gida bata yarda ta bishi ba,
dalilin haka yayi fishi ya daina zuwa gidan gaba
daya.
Sai a lokacin ne hankali na ya yi matukar
kwanciya tun da Hamced ya fita daga cikin
rayuwar Aziza, ni dai ban san meye dalili ba
haka kawai nakc jin ban son naga tasu ta zo
daya, saboda wasu dalilai da yadda nake jin wani
abu a cikin rai na.
Haka kullum zai zo yana ta lallaba ta akan
ta dawo gidansu don yafi son yana ganinta
68
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
kullum a kusa da shi, shi idan yana nan shi sam a
takure yake saboda haka ta bar nan su koma
gida. Ta ki yarda ta ce shi ya dawo dai ita ba zata
iya tafiya ta bar Haana dinta ba, dole ya hakura
ya rabu da ita.
Cikin watanni biyu zuwa bakwai sai da
muka samu karuwar haihuwar yara mata har
biyar, Haj. Bara'tu ta haifi Fadila, Asiya Haaya,
Aisha ke, Maryam Rauda, Habiba matar
Mukhtar ta haifi Sameeha.
Mun yi farin ciki Zuri'a sai kara habaka
take, sai ya kasance gida dai dai ne a wannan
lokacin ake haifar da namiji.
Shekarun ki biyu da watanni a duniya,
lokacin ita kuma Aziza ta shekara sha uku cif,
kasancewar ta mai garin jiki ga kuma jin dadi da
kwanciyar hankali babu abinda yake damunta,
nan da nan ta fara zama budurwa, haka nan
kyanta ya sake bayyana, kowa yana yaba
kyawunta da surar da take da shi.
Loakcin shi kuma Hameed yana da
shekaru sha tara domin anyi-anyi da shi a fitar
dashi waje karatu ya ki wai shi a nan zai yi wai
69
Zuri'a Daya-1 _Sa'adatu Muhammad Waziri
don ya gama karatun sa ya auri Aziza, domin shi
ya ce ita zai aura.
Haka kowa ya yi murna domin dama
kowa ya saka ran haka, ba don komai ba sai don
sanin shakuwar su da irin muna kaunar da ya yi
mata tun ranar da aka haife ta haka dama iyayen
suka kulle cewa za a hada su aure idan har sun
girma.
Tun lokacin da Aziza ta fara zama
budurwa shi kenan Hamced yake kiranta da
mata, baya jin kunya a gaban kowa da haka yake
kiranta kasancewar ita din mai kunya ce a duk
lokacin da ta ganshi cikin jama'a sai tana buya
don bata so yana sa ta jin kunya.
Haka zai taso wata rana haka zai ke rikota
yana son hada ta da jikinsa, ita kuma sai tana