kukan ba don komai ba sai don tausayin
Abba, yadda yą gama yarda da shi amma ace shi
ne ya yi sanadin jefa rayuwar 'yarsa cikin
wannan halin. Tabbas yasan ba zai taba gafarta
masa ba har zuwa karashen rayuwar sa.
ya ce.
Bayan sun dan nutsa sai Uncle Mukhtar
"Yaya Mustapha to me yasa tun farkon
zuwan mu nan basu yi mata wankin ciki ba? Ai
da tuni an zubar da shi. To yanzu meye abin yi
don ba zamu barta da cikin wani ba wanda bamu
san asalin sa ba".
Alh. Jafar da Asiya hade da dansu suka
hada idanun su guri guda cikin rudani.
Cikin alhini Mustapha ya ce, "Mukhtar
nima nayi musu wannan tambayar, sun ce min
duk abin da nake tunani sai da suka yi a farko,
suka ce idan an kawo yara da hakan ta faru da su
144
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
shi ne abin da suke fara yi. Mu aynzu babu
abinda za muce sai yadda Allah Ya yi da ita".
"Yaya mu fitar da cikin nan daga jikin ta,
shi ne kwanciyar hankalin mu".
"Mukhtar meye ribar mu na yin haka?
Idan mun kashe rai me za muje mu ce da Allah
tunda Shi ne Ya aiko hakan ta faru to da sanin
Sa, sai mu tsaya mu ga yadda Zai canza mana.
Amma ni dai da hankalina ba zan ce a cire cikin
nan ba, idan kuma an samu akasi an rasa ranta da
abin da yake cikin ta ka ga mun yi laifi biyu,
dole haka zamu hakura mu karfi kaddara.
Idan kana jin tsoron surutun jama'a to
kowa yasan ba rashin tarbiyya bane ya kaita taje
tayi cikin, cikin karfi aka hakke mata. Haka idan
kana tunanin cikin ZURI'A kake tunanin ayi
mana gori, to duk ZURI'A DAYA muke, duk
wanda yake cikinta abin nan ya shafe shi. Don
haka mu dai mu yi fatan Allah Ya raba ta da shi
lafiya, su kuma wanda suka aikata ko ya aikata
gashi nan ga duniyar, Allah Yana gani, Ya fimu
sanin me Ya tanadar masa, ko iya hakkin mu ma
ya ishe shi kafin aje gare ta".
145
Zuri'a Daya-! Sa'adatu Muhammad Waziri
Gaba daya duk wanda yake gurin babu
wanda jikinsa bai yi sanyi ba, domin kalaman sa
sun taba zuciyar kowa a gurin.
Gumi ne ya keto a jikin Alh. Jafar, domin
bashi da wata kalma da zai iya fada sai cewa
yake.
"Allah Ya kyauta".
Haj. Asiya kuwa ban da kuka babu abin da
take yi, haka tayi sallama da mu ta ce ba zata iya
tsayawa a gurin nan ba, da tasan haka zata zo taji
wannan bakin labarin da bata zo ba.
Babu wanda ya iya cewa da ita komai,
haka ta fice tana kuka, kowa da abin da yake ji
cikin ransa.
Hameed ne ya mike daga inda yake ya
nufo kan gadon da take kwance hawaye na zuba
a fuskar sa, ya zo kanta ya tsaya ya sa hannu ya
shafa kanta, baccinta take abinta, nan ya shiga
kuka mai tsuma rai domin ya kasa ya furta komai
banda kuka.
Na karaso gurin na dafa kafadar sa, na ce.
"Abdul babu abin da zamu yiwa Aziza sai
addu'ar Allah Ya raba ta lafiya da abin da yake
jikinta, tawakkali shi ne abin yi a gare mu ba
146
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
kuka ba tun da abin haka yake tun ran gini tun
ran zane".
Daga kai ya yi bai iya cewa komai ba
banda tsabar malala da hawaye suke a fuskar sa.
syb Aisha na gefe tayi jigum bata iya wani
kwakkwaran motsi tsabar kaduwa da jin abin da
ya faru da diyar ta, sam ta kasa yin kukan sai na
zuci da take yi sv
.30 к Наmеed na mikewa zai fita sai Aziza ta
farka daga baccin da take yiutana farkawa sunan
Abbata fararkira, otzil ey aan ab πενί
si sniDa sauri ya kárasa gurinta yana tambayar
larmedako so? ko me yake mata ciwo2slal ccad
Jin nuryar Aziza yása Hameed ya kame a
Isaye, watonlyay yiN mutuwartsaye. Nan take
zuciyar sästaoshigar bugawaakai-akai, domin
tsoro ne yalgama kama shiusb sER падоя вов!
"Abba kai na,skainag zais cire, rzafivyake
min, wayyo ciwo abba, don Alláhrikemin kaina
zai fashoAbinida dake fadi kenansbsl BT
Da sauri Abban ya rike mata kanokamar
yadda ta nemayya shigaitofa matá addu'a, nan da
nan ta soma lumshe ido alamui ta fara jin yana
lafa mata.
201 147
Zuri'a Daya-i Sa'adatu Muhammad Waziri
Daga masa hannu tayi alamun ya fara saki,
ya ce.
"Ya daina miki ciwon ko?"
"Eh".Ta fada.
Haka ta dinga bin kowa da kallo daya
bayan daya, ta ga duk dinsu cikin tashin hankali,
ta so tayi magana sai ta fasa.
Can ta hangi Hameed ya ba da baya ya
tsaya kyam, sai hankalinta ya yi wajen sa, ta се.
"Abba wancan wane ya tsaya haka?"
Nan da nan ya kirkiro murmushi ya ce,
"Yayanki nc, yana ta zuwa baya ganin ki kina ta
bacci lokacin. Hameed, zo ga kanwar ka tana
tambayar ka, yau da rabon za ku gaisa".
Ji yayi kamar an dauki guduma an doka
masa a tsakiyar kansa, nan take yaji kafar sa
tana kokarin kasa daukar ganganr jikinsa, ya ji
juyawar ma tana gagarar sa.
"Hameed!".
Ta fada hade da runtse idanunta na dan
waşu lokaci.
Damm! Yaji hantar sa tayi rawa, ya yi
kamar ya furtsa da gudu.
148
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
Sunan ta ci gaba da maimaitawa, ko yana jinta. Jin yawan ambaton sunansa ya kara
tsinkewa, gabansa ya ci gaba da dakan uku-uku,
haka ma Alh. Jafar shima rudewa yayi dolc kasa
komai yayi yana jiran ya ga me ya yi saura? Sai
dai cikin ransa yana ta kiran sunan Allah.
Runtse idanu Hameed ya yi kawai ya
saddakar, ya juyo ya nufo gurin lokacin ita kuma
hankalinta ya fisga zuwa wani guri.
Yana zuwa kusa da gadon ta juyo, tana
ganinsa ta ji wani irin mugun firgita ta sosai, nan
da nan ta shiga saukar numfashi akai-akai, ta
saki baki hade da tsananin tsoro da ya mamaye
fuskar ta.
Wata muguwar kara ta da kururuwa ta sa,
nan da nan ta rungume Abbanta tana kankame
shi jikinta na rawa, nan take hankalin kowa ya
tashi.
Nan take Alh. Jafar ya dakawa Hamced
tsawa akan ya zo ya fice daga dakin tun da bata
son ganin shi.
Mustapha ya ce, "Haba Yaya, meye na
daukar zafi haka? Ammi na ba wani bane fa
yayanki Hameed ne, bude idanunki ki ganshi".
149
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Girgiza kai tayi ta kara rungume shi tana
kuka, jikin kow aya yi sanyi, nan kowa ya shiga
zancen zuciya yana mamakin wannan al'amarin.
Hamced ne ya yi karfin halil ya zo da
sauri ya kama hannunta ya dago ta yana kuka
yana cewa.
"Aziza na kalle ni sosai ki gani, ni ne yayа
Hameed dinki ba wani bane, ki cire idonki ki
kalle ni sosai don ki shaida ni".
Yanayin kukan da yake da irin nacin da
yake akan Aziza ta dago ta kalle shi ta ki, hakan
sai yasa kowa yaji tausayin sa.
Da kyar ya samu ta dago ta kalle shi,
amma cikin rudani, tana kallon sa tana ajje
numfashi da sauri irin na razana.
Da sauri ta fisge hannunta daga nashi ta
koma jikin babanta tana cewa.
"Abba bana son shi, bana son shi, Abba
(please) ya tashi bana son shi". Tana fada
idanunta a rufe.
Nan ta shiga kurma ihu dole Alh. Jafar
yasa sai da ya fice sannan aka samu tayi shiru.
Ana cikin haka sai ga (Nurses) guda biyu
sun shigo dakin cikin sauri don suga me yake
150
2
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
faruwa, nan daya ta tsaya tayi ta koma taje ta
kira likita.
Nan da nan sai gasu su biyu, nan suka zo
suka ganta a dimauce, suka nemi a basu guri su
duba ta, haka suka fito jiki a sanyaye muna ta
jima me hakan yake ufi?
Sun dan dauki lokaci zuwa can suka fito,
Mustapha kawai suka nema akan yaje suna son
ganinsa, har Alh. Jafar zai bisu suka ce ya yi
hakuri shi kadai suke bukatar gani. Bai yi musu
ba ya barsu suka tafi tare abin su, haka suka
shiga (offuce) abinsu.
Hankalin Alh. Jafar ya yi mugun tashi,
domin bai san me za su frada masa ba, amma
haka ya yi kokarin danne tashin hankalin sa don
kada a gane yana cikin rudani a zargi wani abin.
Guri suka bawa Mustapha ya zauna, nan
daya daga cikin su ya сс.
"Alh. Mustapha don Allah muna son yi
maka wasu tambayoyi duk da kuwa ba aikin mu
bane yin bincike".
"Ina jinka Doctor, wani abu ku ke son sani
a garc ni?"
151
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
"Eh, akan ma'salar yarinyar gurinka ne,
domin yadda binciken da gwajin da muka yi ya
nuna mana tunanin ta yana son dawowa a
kowane irin lokaci, domin a yanzu wani abu ta
gani da ya razana ta yake son tuno mata abin da
ya faru da ita".
ya ce.
Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar sa,
"Kai Allah na gode Maka".
"A cikn ku wane bakon fuskar da ta gani
ya ta da mana da hankali wanda ganinsa ne yasa
wurin ma'adanar tunaninta ya dan soma
motsawa, sannan meye dangantakar sa da ita?"
Shiru Mustapha ya yi yana musu wani irin
kallo na rashin fahimta, can ya ce.
"Wai me kuke magana akai ne?"
"Alh. Mustapha ka kwantar da hankalin
ka, muna son gano wani abu ne, amma don Allah
kayi hakuri".
"Yayanta ta gani ta razana".
"Ba kwa yin zargin cewa ko shi ne ya yi
mata wannan aika-aikar? Domin ba karamin
razana tayi ba da ta ganshi wanda hakan yasa
(memory) dinta ya kusa dawowa yadda yake".
152
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri
Cikin zafin nama ya daki tcbirin gaban Dr.
Sa'id yana mai huci, ya cс.
"Kaga Doctor ka tsaya iya aikin ka,
wannan ai cin fuska kakc son yi min, kasan
yadda muke da uban yaron nan kuwa? Ubanmu
daya da shi, ZURI'A DAYA mukc, me zai kai
shi ya yi mana wannan illar? Sam kada na kara
jin wannan furucin a bakin ka gudun kada ka zo
ka jefa zumuncin mu cikin matsala".
"(Relax) Ranka ya dade, duk abin bai kai
ga daga hankali haka ba". Dr. Umar ya ce.
"Haba Doctor, maganar tashi ce bata yi
min dadi ba, me yasa zai sa zargi akan dan
dan'uwana? Allah Ya kiyaye hakan ma ya faru a
cikin mu".
"Amcen".
Dr. Sa'id ya fada, kana ya ci gaba da cewa,
"Mu ma bama fatan hakan a garc ku, abin
da aikin mu ya nuna mana shi ne yasa har muka
yi maka wannan tambayar, amma don Allah kayi
hakuri zamu yi abin da ya dacc akai, za muyi
wani gwaji don mu sake dubawa ko dai
kwakwalwar ta ne ya dan motsa yasa hakan ya
faru. Amma don Allah kayi hakuri don naga ka
153
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
fusata sosai, ni kuma na fadi haka ne ba don
wanzi abu ba".
"Shi kenan Doctor naji, ya wuce, Allah Ya
taimaka, da fatan zan iya tafiya ko?"
"Za ka iya tafiya, amma yanzu ba ma son
kowa ya shiga gurinta domin muna son gwada
wani abu a tare da ita na zahiri, don mu gane me
hakan yake nufi? Don haka klu jira mu".
"Babu laifi".
Ya fada a lokacin da yake kokarin tashi
daga inda yake zaune, shi ya fara fita sannan
suka tsaya suna dan tattaunawa.
Haka ya zo ya same mu tsaye bakin dakin
yanayin sa duk ya sauya, Alh. Jafar ne ya yi
saurin tare shi yana tambayar sa me suka ce da
shi?
Sakin fuska ya yi ya ce, "Cewa suka yi
suna son duba kwakwalwar ta su gani, domin
ihun da tayi ya yi yawa, don su gano ko wani
abu ya faru da ita".
Sakn ajiyar zuciya yayi, ya cc, "Mun gode
Allah, Allah dai Ya bata lafiya don girman
Manzon mu".
Duk gurin aka ce, "Amcen".
154
:
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Muna tsaye a gurin sai ga likitocn nan s'ın
dawo, wannan karon har da wasu samari su uku,
babu wanda suka yiwa magana, suna zuwa suka
tsaya sai suka tura wani daga cikin matasan nan
guda uku cikin dakin da Aziza take.
Yana shiga bai fi minti uku ba sai muka
jiyo Aziza na ihu kamar yadda tayi lokacin da ta
ga Hameed, jin haka sai suka sake tura mutum
biyun nan, nan ma dai wani ihun ta shiga saki
babu kakkautawa tana cewa.
"Ban son ganin ku, bana son ganin shi,
Abba! Abba!!".
Cikin gaggawa likitocin suka bude kofar
sai ga mata sannan sun fito, su kuma sai suka
shiga ciki, wannan karon har damu domin cewa
suka yi muma mu shiga.
Sai da muka shiga Aziza na ganin mu ta
fito daga inda take 6uya da sauri ta zo ta
rungumc Abbanta tana ccwa.
"Abba mc yasa ka bari suka shigo? Tsoron
su nakc ji, Abba don Allah kada ka tafi ka barni
su kara shigowa".
155
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Likitocin cikin hikima da dabara suka
samu suka yi mata allurar bacci, nan da nan
bacci ya dauke ta, nan suka nemi a basu guri.
Sun jima tarc da ita sannan suka fito gaba
daya iyayen mazan suka nema su biyo su, haka
suka je, Alh. Jafar da Mukhtar, sai Abban ku
duka suka dunguma.
"Alh. Mustapha ina me neman afuwar ka
dangane da furucin da nayi maka dazu". Cewar
Dr. Sa'id.
Ya cc, "Babu komai Doctor, na fuskanta
yanayin aiki ne, kuma komai ya wuce".
"Madallah na gode, sai magana ta gaba,
yadda muka bincika a zahiri da kuma na'ura mai
kwakwalwa ya nuna mana cewa Aziza a yanzu
tana tsoron dukkan wani da namiji matashi
wanda hakan ya nuna cewa su ne suka yi mata
wannan ta'asa.
Tun da hakan ya faru bata taba razana irin
na yau ba, domin ganin matasan da tayi hakan ne
ya razana ta har take son tuno wani abu da ya
faru da ita a baya. Don haka muddin zata na
ganinsu to zata ci gaba da zarana wanda cikin
biyu dole ayi daya, ko dai (memory) dinta ya
156
Zuri'a Daya-1 Saladatu Muhammad Waziri
dawo ko kuma wata matsala ta faru da
kwakwalwar ta, Allah Ya kiyaye don ba ma
fatan haka a gare ta".
Gaba daya suka ce, "Ameen".
Dr. Umar ya kara da cewa, "Don haka
dolc a kiyaye sanin su wane za su dinga zuwa
dubiya gurinta, domin gudun afkuwar wani
tashin hankali.
Tabbas tun da muke bamu taba samun
(patient) mai irin wnanan lalurar ba, sai dai mun
taba samun wata wadda ita kuma maza ne gaba
daya bata son gani daga babba har yaro, tana
ganin mun zo duba ta zata shiga ihu da razana,
dole muka hakura sai 'yan uwanta mata ne suka
shiga duba ta. Sai ita kuma wannan nata daban
ne, matasa take jin tsoro, kasan abin na Allah
kowa da irin nashi lalurar".
Alh. Jafar ya ce, "Gaskiya ne likita, mun
gode, kuma insha allah zamu kyaye mu saka ido,
kuma insha Allah ba zamu sake barin Hameed
ya zo nan asibitin ba har sai ta warke sosai".
"Shi kenan Alhaji, ba ma shi kadai ba duk
wani matashi da zai sa idan ta gashi zai razana ta
bama fata ya zo gurinta, domin hatsarin da yake
157
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
cikin al'amarin, nasara ce da kuma rashin ta,
kaga abin ya zamo (fifty-fifty)".
Mukhtar yа сс, "Hаkа ne likita, amma ni
ina da magana da Yaya zai yarda da an raba
yarinyar nan da cikin da ke jikinta, kaga sai taji
da daya, amma ace ga wannan ga wannan abin ai
ya yi mata yawa, yarinya karama da ita,
shakrunta fa sha hudu zuwa sha biyar har yaushe
zata iya jure rainon ciki?"
Mustapha ya dafa Mukhtar ya ce,
"Mukhtar ka saki ranka, ka dauka wannan duk
yana cikin jarrabawar rayuwar Aziza da mu
iyayenta baki daya, don haka Allah Yasan abin
da bamu sani ba, don haka bamu san dalilin
faruwar hakan ba, sai dai mu dauki yarda da
kaddarar Sa mu jira muga ikon Allah. Murnar
mu daya da ba ita ce taje yawon banza ba ta
dauko shi, karfi aka nuna mata".
Jikin Alh. Jafar ya yi matukar sanyi, ya
kasa cewa komai, banda idanu da kunne da ya
zuba babu abin da ya iya tofawa, sai fama cewa
Allah Ya kiyaye Ya bata lafiya dai.
Nan suka gama abin da ya kaisu, sannan
suka fito suka dawo gurinmu. Alh. Jafar bai jima
158
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
ba a gurin ya ce zai tafi, nan ya tambayi ina
Hameed? Nan muka ce tun dazu ya yi nan bai
dawo ba.
Sallama ya yi damu ya bi bayansa, haka
nan Abban ku suka sanar mana duk yadda suka
yi da likitocin, mu dai addu'a muka yi akan Allah
Ya fitar damu cikin wannan hali da muke.
Alh. Jafar zaune yake cikin motar sa shi
kadai yana faman sauke numfashi da ajiyаr
zuciya, domın dai yana cikin (tention) ba kin
Karawa, Allah Ne ya taimake shi Ya rufa masa
asiri, amma ba don haka ba yau d aya kwashi
borin kunyar sa. Tabbas yau ya so ya shiga cikin
tsaka mai wuta, amma sai gashi Allah Ya rufa
masa asiri, abin da yake tunanin zai faru Allah
Ya kiyaye.
Sai da ya dan samu nutsuwa sannan ya
fara tunann matar sa da Hameed, ina suka shiga?
Nan da nan ya fito cikin motar ya shiga dubсdube babu wanda ya gani cikin su, dolc ya
hakura ya dawo ya shiga motar sa ya koma gida.
A falo ya iske Haj. Asiya tayi shiru abinta,
daga ganin idanunta kasan ta sha kuka na kin
karawa.
159
Zuri'a Daya-l Sa'adatu Muhammad Waziri
"Ina Hameed yake?"
Ya jcfo mata wata tambaya cikin kaushin
murya, don a fusace yake.
Daga kai tayi ta kalle shi, cikin sanyin jiki
ta ce.
"Ban gane wacce irin tambaya kake min
ba, awa ta nawa da bairn ku tare zaka zo kana yi
min wnanas tambayar?"
"Ya baro ni a can nima, nayi tunanin ko ya
gamu da ke ne kun taho gida. Ina zaton tunda
motar haya ya biyo yanzu za ki ganshi ya shigo
cikin gidan".
Yana gama fadin haka ya cire babbar rigar
sa ya ajje gefe, ya samu guri ya zauna. Kallo
daya zaka yi masa kasan ba ya cikin nutsuwa.
"Daddy, yanzu wacce mafita ka aje mana
a cikin gidan nan game da wani sabon tashin
hankalin da ya same mu? Kasan dai yanzu dole
kayi wani abu akan wannan al'amarin, don abin
yanzu ya zarce dukkan tunanin mu".
Cikin kaushin murya ya ce, "Mc kikc so
nayi bayan wanda nayi tun farko? Ai magana ta
riga ta wuce, fatan mu Allah Ya yayewa yarinyar
nan abin da ba zata iya ba".
160
Zuri'a Daya-1 fa'adatu Muhammad Waziri
"Kai Alhaji ka ji tsoron Allah kuma ka
dinga tausayi da sa tsoron Allah a zuciyar ka, ai
kuwa duk mai tausayi da imani dole ne ya
tausayawa yarinyar nan irin halin da take ciki,
daga wannan sai wannan, bata fita daga wannan
halin ba sai gashi tana fadawa cikin wani.
Ni dai shawara ta dole nc mu sanar da
iyaycn yarinyar nan cewa ga wanda ya jefa
'yarsu cikin wannan gararin, tabbas idan muka yi
haka zamu samu saukin tsangwamar da zamu
fuskanta, amma muddin muka bar wannan
al'amarin ran da duk asiri ya tonu to zamu fi
kowa jin kunya a cikin ZURI'A, domin wasu sai
sunce mu ne muka sa shi yaje ya yi mata hakan.
Ina ganin gwara tun wuri mu yiwa tufkar hanci".
Cikin zafin rai da daga murya sama ya ce.
"Asiya ban san wanc irin gaddama da
taurin kan da ke gare ki ba, sau nawa zan fada
miki maganar nan da ki rufc ta amma sai kina
dawo da abin baya? Don haka ki sani baki isa ki
sa ni abin da ban yi niyya ba, ya kamata ki
saurara min. Wannan ita ce rana ta karshe da za
ki sake min irin wannan batun, kin dai ji na fada
miki'.
161
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Yana gama fadin haka yasa kai ya fice
daga falon cikin fushi da 6acin rai.
Binsa tayi da kallon takaici, nan take
hawayc ya zubo a cikin idanunta, a bayyanc ta
cc.
"Jafar ka cika marar tausayi da son zuciya,
kuma insha Allah sai Ya bayyana gaskiya komai
dafen dadewa, kuma matukar ni cc na haifi
Abdulhamced sai na sa shi yin abin da ranka
baya so, naga yadda zaka yi dani".
Tana gama fadin haka ta samu guri ta
zauna tayi tagumi abin yana matukar ta da mata
rai, domin har yanzu ta kasa samun dukkan farin
ciki a wannan ranar tun da ta samu labarin cewa
Aziza na dauke da ciki".
A can cikin daki Alh. Jafar ya kasa zaune
ya lkasa tsayc, haka ya dinga shiga da fice don
jiran dawowar Hameed amma yaji shiru, gashi
har misalin karfe goma na dare babu shi babu
labarin sa. Nan hankalin sa ya kara tashi,
wannan karon har kofar fakinsa yasa mai gadi
ya zo ya jijjige, tunanin sa yana ciki zai yi musu
irin na rannan, amma da aka cire kofar sai aka ga
162
Zuri'a Doya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
dakin wayam, babu kowa a ciki, baka ya kara
jcfa shi cikin damuwa.
Har gari ya wayc babu Ilameed babu
wanda aka samu ya zo da labarin ya ganshi,
kwana daya, kwana biyu babu Hamced babu
labarin sa, pan hankalin ZURI'A ya tashi saboda
da kansa ya shiga fada ma 'yan uwansa bai ga
Hameed ya dawo ba, yau kwana uku.
Kowa yaji abin sai kansa ya daure, domin
gakan bata taba faruwa da shi ba. Nan hankalin
kow aya tashi, haka aka shiga cikiyar sa har
gidan (radio) amma babu wani labari da aka
samu a wannan lokacin.
Kallo daya zaka yiwa Alh. Jafar kasan
yana cikin tashin hankali mara misaltuwa.
Ganin yadda yayi mugun tashin
hankalinsa akan rashin ganin dansa Haj. Asiya
tana kallon sa amma ita abin ko a jikinta don
abin da ta fada masa cewa tayi ita bata sin ta
sake ganin Hamced a gabanta domin tana
ganinsa jefa ta cikin tashin hankali da damuwa
yake yi, yaje can ya karata.
Tun da ta fada masa haka ya shiga fushi
da ita, hade da fada mata cewa duk abin da ya
163
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
facu da dansa ba zai taba yafe mata ba tun da
baki tayi masa. Hakan yasa ya dauke mata wuta,
sam ba ya sauraronta, haka duk ya bi ya
dugunzuma, ya hana ma kansa kwanciyar
hankali.
Tsananin damuwar da yake ciki yasa ko
aiki ya ki fitayana ta yawon neman labarin inda
dansa ya shiga, amma shiru babu labarin sa.
* *
Yadda al'amarin yake, tun sanda Hameed
ya fito daga cikin asibitin hankalin sa ya yi
mugun tashi jin labarin Azizan sa na dauke da
cikin sa, hankalin sa ya yi mugun tashi yaji gaba
daya duniyar tayi masa zafi, yaji sam baya
sha'awar son ci gaba da rayuwar duniyar gaba
daya. Haka ya dinga jin kamar bashi da kowa,
bashi da komai a duniya, haka ya dinga jin yaje
ya yi rayuwar sa shi kadai babu kowa a cikin
rayuwar sa.
Haka ya fito bai san inda zai jc ba, sai dai
ko kadan bai sa ma ransa ccwa zai koma gida ba,
domin bai ga wani amfani da zai sake a rayuwar
sa ba tunda har ya jefa Azizan sa cikin wannan
164
Zuri'a Daya-I sa'adatu Muhammad Waziri
bala'in na datse mata dukkan farin cikin rayuwar
ta da burinta, ya kuma illata rayuwarta gaba daya
don ya kassara ta baki daya.
KUNAR ZUCI da shi ya wuni a wannan
ranar, ayan ya bar cikin asibitin, haka yana lafiya
daga nan sai ya tafi can, don haka ya yanke ma
zuciyar sa cewa dole ne yaje ya nemi kotun
Musulunci ya gabatar da laifin sa don a hukunta
shi.
Bai san ina zai je ba domin bai san ina zai
samu kotun ba, don haka da yaga dare ya yi bai
yi nasarar abin da yake nema ba, wani masallaci
ya samu ya kwnata a gurin yayi barci a can
Hausawar Sabon titi, sa safe ne ya samu limamin
masallacin da bayan sallar asuba.
Bayani ya yi masa sosai, bai 6oye masa
komai ba, ya gaya masa irin halin taskun da yake
ciki, da kuma abin da yake so ayi masa na
hakkin Allah.
Jikin liman ya yi mkatukar sanyi, ya yi
matukar tausaya masa tare da jinjina irin karfin
imanin da yake da shi, nan ya kara tabbatarvva da
cewa yin hakan ba halinsa bane, iftila'i ne da
rudin zuciya da kuma sharrifn shaidan.
165
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Nan ya ce, "Yaro lallai kam kana cikin
tashin hankali da rudin rayuwa, hakika wannan
shi ne tsoron Allah na hakika, tabbas da za a
dinga samun mutane masu irin wannan laifin
suna bayyana kansu ana fitar musu hakkin Allah
akan su to da tuni duniyar tana nan zaune lafiya.
To amma ina! kullum abubuwan sai dada
tabarbarewa suke yi.
Dama dole ka shiga damuwa da rashin
samun nutsuwa cikin ranka, domin agbin da kayi
ba karami bane, sannan duk wanda yaji me ya
faru sai ya yi tsinuwa ko la'antar wand ayayi
mata wannan al'amarimka ga kuwa nutsuwa a
gurinka ba zata taba samuwa ba tunda baka
bayyana cewa kaine ba a yafe maka.
Amma tunda kayi nadama ka dage akan
kana so a fitar da hakkin Allah akan ka, idan
yaso daga baya zaka koma ka bayyana gaskiya,
to zan taimaka maka, kuma na tabbata idan an
fitar maka da hakkin Allah zaka samu nutsuwa
har cikin zuciyar ka. Kuma Allah Zai taimaka
maka ta sauran hanyoyin da zaka cira, amma ina
son ka kudura a ranka cewa ba zaka kuma
kusantar inda zina take ba.
166
Zuri'a Daya-I sa'adatu Muhammad Waziri
Ka duba ka ganka shekarun ka basu fi
ashirin ba zuwa da daya, amma ka jefa kanka
cikin tashin hankali haka".
Hawaye ne ya shiga zubowa a fuskar sa,
ya ce.
"Baba ina cikin wani irin rudu da
damuwar da ban taba tunanin wani cikin
rayuwar nan ya shiga irinta ba, wallahi Baba na
yi maka alkawari ba zan kuma yin zina ba har na
koma ga mahalicci na".
"Shi kenan Abdulhameed, insha Allahu
zan taimaka maka aa fitar da hakkin Allah akan
ka, tunda hakan ya faru, amma kasan dole sai
munje kotun tare sun yi maka tambayoyi sannan
su aiwatar maka".
Murna ce ta bayyana a fuskar Hameed, ya
tashi ya rungume Malam Liman yana kuka, nan
take tausayin Hameed da kaunar sa suka cika
ransa, nan ya tambaye shi akan ya fada masa
cewa ina iyayen sa suke da zama?
Ya kada harshe ya ce, "Baba kamar yadda
na fada maka cewa mahaifina baya goyon bayan
da a hukuta ni, don haka yasa na na gudo nan har
Allah Ya hada mu da kai, don haka ka wakilci
167
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
iyayc na ka zama cewa kai yayan Bababane ne
na zo maga da wannan labarin shi ne ka kawo ni
nan don ayi min bulalar".
Liman da kansa ya bashi masauki a a
gidan sa cikin dakin yaransa manya guda uku, ya
hada su guri daya shi kuma ya bashi daki daya
don ya samu ya sake sosai. Kwanan sa biyu a
gidan ranar nan sun dawo daga kotun