'yan bori Mustapha ya yi da ya
gama fahimtar bayanin da Hameed yake masa,
nan take wasu zafafan hawaye suka zubo a
cikin idanunsa ya ji komai na cikin duniyar nan
ya masa zafi, haka itama aisha sai yanzu ta
gane me yake nufi.
Da sauri ta zo ta cakumi Hameed tana
kuka tana cewa.
"Hameed ka cuce mu, ka ci amanar
yarda da kaunar da muka nuna maka. Ashe
193
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
dama kaine ka yi mata wannan aika-aikar? To
Allah Ya isa tsakani na da kaiba zan taba yafe
maka ba, kaje insha Allah zai ka dandana
kuncin da yafi wanda ka jefa mu".
Nan take ya fara kuka yana cewa dor
Allah ta yafe masa, haka ta ture shi taje ta
zauna tana kuka. Haka yaje gurin Mustapha ya
tsuguna gabansa yana kuka yana rokon zya
yafe masa.
Cikin kunar rai ya daga hannu ya wanke
shi da mari, ji kake tasss!
"Idan baka tashi ka bar gurin nan ba zan
yi kasa-kasa da kai naga uban da ya tsaya
maka, mara mutuncin banza, munafukin wofi".
Ya fada cikin daga murya.
Mikewa ya yi daga wurin da ya fadi
domin ya yi mutukar jin marin, nan ya saker
dawowa gabansa yana kuka, ya се.
"Abba duk abin da zaka yi min kayi min
matukar zaka huce daga facin ran da na saka,
wallahi sharrin zuciya ne da rudin shaidan, duk
su ne suka debe ni da aikata haka".
194
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
Wani mari ya sake kai masa a karo na
biyu nan ma ya kara samun sa, a karo na ukun
ne nayi sauri na saka hannu na tare, na сс.
"Mustapha barshi haka tunda abin da zai
faru ya riga da ya faru, kai kuma tashi ka tafi
abimka Allah Ya shirye ka, zalunci kuwa ka
riga da kayi mana shi, kai namu ne babu yadda
za muyi da kai, amma ba don haka ba ni da
kaina zan sa a rufe ka a gwada maka hankali ka
gane abin da ka yi mana".
Rarrafowa ya yi ya zo ya rike ni yana
kuka yana cewa.
"Granny wallahi na tuba, ku yafe min,
hakika na san abin da nayi ban kyauta ba,
Ammi kema ki yafe min".
Sauri tayi zta dauke kallonta gare shi zta
се.
"Kadfa ka kara kira na Ammi, ni ba
Ammin ka bace Hamecd, yanzu abin da zaka
saka mana da shi kenan? Kaje abinka insha
Allah sai Allah Ya yi mana sakayya da halin da
ka jefa mu ciki, domin Allah basya bacci, Yana
195
Zuri'a Daya-1 _Sa'adatu Muhammad Waziri
amsa addu'ar wanda aka zalunta cikin
gaggawa".
Cikin kuka ya cc, "Ammi ku yafe ni,
nasan ban kyauta ba, amma ku yi min duk abin
da zai fanshi bacin ran da na saka ku matukar
yin hakan zai sa ku huce".
"Hameed ka tashi ka bace min daga nan
domin bau son jin duriyar ka a gurin nan,
domin kana kara haifar ma da zuciya ta
damuwa. Ka cuce mu ka jefa mu cikin tashin
hankali, tsakanin mu da kai sai dai Allah Ya yi
mana sakayya, amma maganar yafiya tsakanin
mu babu, kaje can ka karata, ka jira ganin
sakayyar abin da kayi mana, domin Allah sai
ya biwa 'yar uwarka hakkin ta".
Cikin uka Aziza ta ce, "Ammi kada ki
kara kirana da cewar ni 'yar uwarsa ce, idan da
ni din 'yar uwarsa ce ba zai yi min haka ba. Bai
tausaya min ba, bai kuma duba zumuncin mu
ba sai da ya hakke min, to ya żan yi na yafe
masa?"
Nan kuka ya ci karfinta ta fado jikina
tana yinsa, tana cewa.
196
a
Zuri'a Daya-1 Sa'adalu Muhammad Waziri
"Ya Hamecd ba zan taba yafc maka ba".
Dukkanin mu kuka muka ci gaba da yi,
aka rasa wane zai iya rarrashin wani a cikin
mu.
Hameed ya matso gurina zai fara rokona
na daga masa hannu akan ya yi min shiru,
ganin yanayi na yasa bai iya furta ko da kalma daya ba dole ya ja bakin sa ya yi shiru.
Cikin fushi Mustapha muka ga ya damki
wuyan rigar sa ya ja shi sun yi waje ba tare da
ya ce da shi uffan ba, haka suka yi waje tare,
da har nayi tunanin naje na bisu na tambayi ina
za su? Sai na dawo na tsaya, nan muka zauna
muna. ta jimami da nuna alhinin faruwar
al'amarin, muna cikin wannan halin sai ga
Maryam nan ta zo.
Bayan mun sanar da ita abin da yake
faruwa hankalin ta ya yi mummunan tashi,
itama kukan tayi mai isar ta domin abin ya
daga mata hankali.
Tun da ya yi (parking) motar sa a cikin
(estate) din ya shiga kiran sunan duk wanda ya
197
Zuri'a Daya-1 Sa'adatu Muhammad Waziri
zo bakin sa, haka ya zamo kamar karamin
mahaukacі.
Kai tsaye kofar gidan Alh. Jafar ya nufa
rike da rigar Hameed, shi kuma binsa yake bai
ce da shi kala ba, domin ba shi da abin da zai
iya cewa da shi.
Alh. Hamża da Alh. Lukman su suka
fara fitowa suka hangi Mustapha ya nufi gidan
Alh. Jafar, sauri suka yi suka mara masa baya,
suna hango shi da Hameed sai farin ciki ya
kama su domin tunanin su ya gano Hameed
daga batan da yayi. Haka suka nufo gurin cikin
farin ciki tare da yi ma Allah godiya na
bayyanar yaron su, domin dama kullum suna
cikin zulumi.
Cikin daga murya ya shiga kiran Alh.
Jafar babu kakkautawa, a sukwane ya fito shi
da Asiya. Yana ganin su ya hankada Hamced
gabansu ya je taga-taga zai fadida sauri
zmahaifin sa ya tare shi amma duk da hakan
sai da ya fadi.
Dai-dai lokacin da su kuma suka karaso,
nan take suka yi turus cike da mamakin abin da
198
Zuri'a Daya-I Sa'ndatu Muhammad Waziri
suka ga yayan su yayi, take abir ya daure musu
kai hade da mamaki.
Cikin daga murya ya cc, "Jafar ka bani
mamaki kai da azzalumin yaron ka, ashc ku
dama maha'inta ne ban sani ba? To wallahi yau
babu mai raba ni da ku sai kotu tun da kai da
danka azzalumai ne marasa amana".
"Kai Mustapha, nutsu kasan wane furuci
kake yi da sanin wa kake jifa da wadannan
kalaman, domin ba zan iya jurc daukan su ba".
"Dole ka jure su kuwa domin babu yadda
zaka yi, ban san rashin imanin danka ya kai
haka ba, haka kuma kai ma ban yi tunanin zaka
yi min haka ba. To amma tunda Allah Ya
bayyana mana gaskiya to ai shi kenan, dole
gobe ku ga sammaci kai da danka a kotu,
domin babu abin da zai sa na hakura tun da ku
azzalumai ne".
сe.
Alh. Hamza ne ya matso kusa da shi, ya
"Subhanallahi! Yaya Mustapha mene ne
ya yi zafi haka kake wannan furucin? Don
Allah kayi hakuri ko ma meye ya faru a
199
Zuri'a Daya-I Sa'adatu Muhammad Waziri
tsakanin mu za mu iya maganta shi ba wai sai
mun tozarta kanmu ba duniya ta jimu, domir
wannan babban abin kunya ne a ce daya dag
cikin mu ya maka fan uwansa a kotu sabod
wani abu da ya faru tsakanin mu".
"Hamza ka rufe min bakin ka a gurin
nan, bari na gaya maka babu wanda ya isa ya
hana ni aiwatar da abin da nayi niyya turi da
abin ya shigo da munafurci da rashin imani. To
bari na fada maka, ko kasan cewa Hameed shi
ne ya yiwa Ammi na fyade har ciki ya shiga
wata ukи?"
Gaba dayan su rudewa suka yi, Alh.
Hamza da Lukman duk suka fito da idanun su
waje, tsananin mamaki da tashin hankali ne ya
bayyana a fuskar su. Nan take suka shiga raba
idanu da kallon juna.
Nan take ya zayyane musu duk abin da
ya faru, jikin su yayi sanyi, yana fada musu
hawaye na zuba a fuskar shi.
200
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels