yayi mishi Addarmu sosai, bugun semo Manga ya dauka, yana kallon yadda na rabe a
gefen.
"Ai wallahi kin more! Irin wannan mutumin idan ya aureki don Allah ki dauke ni, me miki aiki."
Tsaki nayi tare da share maganar shi.
"Nagode! Sosai! Bani da abinda zance maka!"
"Toh! Amma kinsan yanzun da can baya akwai banbanci, dan one Year challenges da kika
fuskanta ya ishe ki, and ban san me zaki dauki zuwa na ba, amma ki fahimci wani abu daya.".
Shiru yayi tare da sauke Lulu, ฦดace.
"Ina son ki koma Schl! A wayayyar mace! Me Class! Wacce zata iya kome dan kare kanta!
Sannan ire irin Aahil suna nan da kawaye bila adadin, me kika shirya?!"
"Ban shirya kome ba! Sai dai wani karamin Game! Wanda zamu buga idan na shigo,
Nagode da hidimar da kayi, sannan ban rike lissafin nawa na barnatan maka ba, amma zaka
iya dubawa sai ka gaya min akwai kudin da na ajiye domin ina tunanin shine wanda na taba
na."
Buษe motar yayi sannan ya ciro wasu takardun, ya mikawa Luluh yace.
"Tun kafin na tafi! Japan na maida sunanki kai, toh ban ganki ba, amna wannan Atm ya daina
aiki, ga naki nan."
Shiga motar yayi sannan ya kira Manga, Ina kallon su suka bar garin, bayan yayi mana hidima
sosai........
The Game....... Loading ๐บ
[7/2, 9:02 PM] BAHAUSHIYAH๐ฅฐ: BAHAUSHIYAH
๐๐ข๐ต๐ต๐ข๐ณ๐ข ๐ ๐ข๐ฏ ๐๐ข๐ต๐ข
Babi-sha-takwas
The Game..
Ina tsaye har na daina ganin su, ji nayi ance.
"Munafukai ina zai kai mana yaron mu!?"
A razane na juya ina kallon Baba Habu bakina na rawa. Na ma rasa me zance Mishi.
"Zaki bani amsa ko sai na falla miki mari!"
"Ni Ni Ni ma ban sani"
Kauuuu ya tsinka min mari, wanda ya gigitani. Har sai da hancina ya fashe.
Kuka na fasa tare da rike fuskana.
"Zaki min magana ko sai na takaki"
Wani irin shakurarren kuka nasaka mishi.
"H
Jar buhu me tsaba, me algarara, Hajiya Husnah gaya min me zanyiwa wannan tsohon kwanon"
Inji Manga,
Zaro Ido nayi, cike da mamaki, yaushe gayen nan ya sauya haฦa
Tsakani da Allah Manga yake shirin Baje Baba Habu.
Shan gabanshi nayi cikin tsoro nace.
"Don Allah ka rufa min asiri, kafata shaye shaye ne?!"
"Alqur'ani da kin barni na kaddamar mishi, Yasin ko tsohona ne tace zai tab'a inuwar Gidan
Baba HABIBU sai na samface mishi keya, Hajiya shiga abinki baki da damuwa da kowa, ki taka
Uban kowa ki kwana lafiya, Ni Manga sai na sare kan mutum da gariyo na"
Ikon Allah nace a raina, yaushe Manga ya koma haka?
"Dr mana! Shine yayi wannan aikin!"
Shigewa nayi cikin gida dan bazan iya jin haukar Manga ba, domin zantuttunkar shi yana
niman sani ciwon kai.
Ina shiga cikin gidan, na same yan uwana, ana ta labarin Dr.
Wani Jaka Meemah ta bani, cikin murmushi, tace.
"Ehhee! Our Addarmu! Hmmm! Nima Allah ya bani like your Handsome "
Duka na kai mata, Mubarak ya kwashe da dariya, Abdul yace.
"Addarmu! Wallahi gayen karshen ne! Shiga dakin mu Kiga har yanzu da kamshin perfumes din
shi, Gaskiya kin iya riko wuyar Gayu."
"Kuma Ya Muba! Sun dace da!"
Ina jin su, da suka isheni da yabon shi ban san lokacin da na buga musu tsawa ba da cewa..
"Dalla kuyi min shiru?! Kunga mutum duk hankalinku ya tashi, waye ya gaya muku soyayya
muke dashi, malamin na ne. Kuma yadda kuka zake nan ba musulmi bane! Arne ne!"
Na fada musu a raunane wanda ni kaina ban san nayi hakan ba, sai dai na san kiran shi arne
yayi tasiri a zuciyata sosai.
"Toh meye kuma na kuka? Tunda arne ne ai shikenan! Mu dai muna son shi haka." Inji
Meemah,
Tsaki nayi zan shige daki.
"Toh mukan muna yin shi kuma Allah yasa ya musulunta a sanadinki"
A fusace na juya ina kallon shi nace.
"Idan kace tausayi na yarda! Amma musulunci! Ga members Christian Association of Nigeria!
CAN! Kasan me kace! Toh ma taimakin shugaban CAN ne na kasa, shugaban matasan
Catholic na arewa baki daya, zan iya yarda idan Ankita shi me ruwan musulunci, amma ya
Musulunta is not easy! Domin zai ya zama fada tsakanin Musulmi da Christian."
Ina gama fad'ar haka na shige d'akin, ina kuka. Wanda ban san dalilin shi ba.
---
Shigowa Innarmu tayi ta ganni zaune da kayan da Meemah ta bani.
"Asma'u! Meye na kuka?!"
"Innah ban sani bani!"
"Toh ko dan anyi maganar malamin ku ne"
Gyad'a mata kaiai nayi,
"Toh baki son maganar shi ne?!"
Sunkuyar da kai nayi, naja hancina. Sannan nace,
"Inata musu bayani sunki su fahimce ni babu soyayya kamar yanda suke tsammani, shi ne ya
bani haushi."
"Shine abin kuka amma ai kanenki ne! Kuma dole suyi miki musu, lokacin da yazo naga
bakon yanayi a tare dake! Jikinki na rawa kika dawo dan ki karrama shi, idan na fahimta yana
da wata muhimmanci a tare sake. Sannan naji kina cewa shi din Ahlun kitabi ne Ko?! Toh tunda
babu soyayya don Allah ki tsare kimarki da addinin ki, koda akwai soyayyan dole ki kula da
kanki. Husnah muna bukatar nutsuwarki da kamalarki don Allah karki watsa mana kasa a ido."
Innarmu tayi min nasihar da tasani kuka, sannan tayi min addu'a sosai, sannan ta bani
shawara yadda zan kame kaina dan kar ya dauka abun hannun shi ne yasani nake bibiyar shi.
..... Bayan sallah isha muna zaune a tsakar gida.
Bayan mun gama cin abinci Baba ya kalle ni, sannan yace min.
"Dazun naji kuna shirme da kanenki shine har da kiran mutumin da yazo gurinki da arne!
Husnah me yasa baki da harshe! Kullum harshenki yana yawan kaifi sosai, kome sai kin aibanta
alkiblan shi.
Idan Arnen ne baki godewa Allah ba, mutum ya dibo tafiya tun daga kaduna ko nace zaria,
amma bayan tafiyar shi ki bishi da maganar arne. Bana son haka domin kar wata rana kiyi
kuskuren da bazaki iya gyarawa ba."
Haka baba yayi min fada sosai, sannan ya tashi ya koma dakin shi.
Nima dai Yau kukan dare ya kare tunda yanzun ina da tudun dafawa.
---
Karfe sha biyu ya isa zaria, kai tsaye gidan shi na staff ya wuce, yana shiga wanka yayi Sannan
ya kwanta.
Bai tashi ba, sai da kiran sallarsa asuba ya tadda shi, ban daki ya shiga yayi brush, sannan ya
dawo ya bude Bible, ya fara addu'o'in, har karfe shida, wanka ya shiga. A hankali yake jin wata
Irin nutsuwa, tana shigar shi.
Yana gamawa yazo ya shirya cikin normal haf jamfa, sai wando brown kaftani, ya gyara
gashin kan shi ya kwanta, kallon fuskarshi yayi sannan ya dauki kayan shi.
Yana fitowa kitchen ya shiga ya soya kwai da ruwan tea, ya had'a sannan ya, fito a nutse
yake ci wani irin dad'i yake ji. Musamman idan ya tuna babu abinda Aahil ya isa yayiwa Manga.
Yana gamawa ya tattara kayan sannan ya wuce ban daki ya kuma brush, sannan ya fita.
A hankali yake jan motar shi, yana juya abinda ya faru tsakanin mu.
Murmushi yayi sannan yace.
"Cried lady!"
Murmushi ya kuma saukewa yana zare ido shima yace.
"Haka ta fida golder eyes dinta. Sai cutie lip's dinta, Nan dark brown. Short strawberry noise
dinta nan!"
Shi ษaya sai dariya yake yana fada yana dariya.
"Kayi hakuri kaci wani abu sabida kai bakona ne! Addininmu tana girmama bako! Wowwww! Ga
mace nan Devanah! Wacce tasan kanta."
Haka yayita surutu shi daya har ya isa makarantar, yana parking Aahil Yana shigowa.
Kusan a tare suka fito, sannan suka rungume juna. Suna gaisawa.
Kowa wucewa yayi inda yake da zama.
Karfe ษaya sai ga Devanah, a fujajan, ganin shi yasata zuษewa akan kujerar dake kallon
shi tace.
"Bature! Mafarki nayi wai ka You Fall in Love! Da wata musulim lady, shine nazo gani ko
dagaske ce! Ashe mafarki nayi."
"Hatred is as blind as love!" Kura mishi Ido tayi kamar zata saka kuka tace.
"But! Ni da kai we are in love! Kuma bana jin tsanar, sai dai A Danger Foreseen Is Half Avoided"
"If you are prepared to face a problem or difficulty, it will be easier to deal with. Devanah ni na
gaya miki a gaban kowa Ni bana sonki, ni babu so a zuciyata, Please ki bar min Office. Kuma
kiyi hakuri ga ring din Engaged dinmu"
Mika mata yayi sannan ya tattara kayan shi, ya fita zai bar Ofishin sa.
"Bature! A bada excuse is better than none!"
Bai juyo ba, yace mata.
"Am always give you my excuse, even if it's a poor one! Please zoki fita!"
"Because God bless you with many miracles! Ba komai amma i promised you babu wata
macen da zata zauna da kai mark my words!"
Tana gama fad'ar haka tazo ta tsaya a gaban shi zata wuce, tace.
"You! Ka cutar da son da nake maka! Allah sai kayi danasanin Betrayed dina da kuka yi, bazan
tab'a barin ka kayi farin ciki ba, sai na zame maka fitina a rayuwar ka, muna nan da kai."
Goge kwallar dake sauka daga idanunta tayi, sannan tace..
"We shall see how you with get successful in your life"
Da kuka ta bar A.B.U tana me alkawarin sai ta rama abinda yayi mata, a can bakin get Suka
haษu da Aahil ya bata hakuri kamar shine Baturen da ya lalata mata rai.
Yayi mata alkawarin zai mishi magana.
....
Tunda ya rage saura kwanaki sha biyu na koma Zaria nake hada kayana, sai dai da na
duba sai naga duk sun sha ruwa, dan a salla munyi kala hudu, kowannen.
Duk da ban san kowa a bauchi ba, Amma nayi kasadar. Shiryawa nazo na sayi kayan irinsu
material, kananun atamfofi, sai na kai wunti, dan akwai wata da ta kaini shagon telanta da na
gaya mata ni bakuwa ca.
Aikuwa ya amshi kayan, ya bani kwananki da zan koma.
Sai takalma da bags da kuma veil da wasu abubuwan na amfani na. Nayi wasa da kudi
sosai. Sannan na dawo gida.
Anan kuma, cincin da dambun nama, tayiwa Dr sai soyayyar zabuwa da Baba yasa aka
mishi.
......
A can Zaria kuwa Dr Imran Shaikh Abdul, suketa shige da ficce domin a bude min file dina, da
wasu abubuwana.
Duk da hannun Dr ake kome amma yaki shiga dan baya so, Aahil ya fahimci abinda yake
aikatawa.
Yau jumma'a, suna zaune a baranda, dukkansu Malaman nan suke tattaunawa, suna cikin
haka sai ga Aahil ya iso, zama yayi suka gaisa dukkan su.
Sannan ya kalli Dr Bature cikin murmushi yace.
"BYC! Ko zaka rakani ne bauchi."
"Bauchi!!!" Duk yan gurin suka hada baฦi. Cikin izza yace.
"Eh! Wani abu ne?!"
"A'a! Allah ya dawo da kai lafiya.". Suka ce mishi.
Kallon Dr yayi sannan yace.
"Baka ce kome ba!"
"No friend! Gobe zan shiga Abuja" ya faษa a hankali.
"Ok bazaka rakani ba?!"
Kauda kai yayi cikin murmushi yace.
"Kusan haka!"
"Toh karka je, gurin Yarinyar nan zanje"
Murmushin mugunta da takaici Dr yayi yace..
"Kace ina gaida ita! Kace Aljuhun baya yana kewar tsiwarta"
Dake bai kira sunanta ba, babu wanda ya kawo Husnah ce.
D'aga kafada yayi sannan yace.
"Oho zan gaya maka kasan ta tsane ka, but idan muka shirya zan tuna mata kai. Yau ina jin
ฦishirwanta ne."
.
Girgiza kai Dr yayi bai ce mishi kome bai, sai sunkuyar da kan shi da yayi, kwana biyu nan
yana wasa da zuwa service, dan shi kanshi bai san dalilin shi naki zuwa Church ba, ya
danganta haka da, aikin da yasha kanshi. Mabiyan shi sai kiran shi suke ya dawo.
Bayan lafiyanta shi kau.
"HUSNAH!" Itace damuwar shi, domin kuwa bazai yi su cigaba da mu'amala yana Kirista tana
musulma mebin tafarkin ta ba, abinda zai yi tana dawowa, zai yakince damuwarta ya zuba a
kwando shara, sannan ya mai da goben shi da addinin shi sama da kome, dan idan yana
bibiyar ta zuciyarshi zata iya sanya shi sabon Yesu.
Wannan itace dogon nazarin da yake kwana da ita yake tashi.
......
Washi gari...
Asabar cikin shigar Alfarmar Aahil ya taso motar shi, sai bauchi.
Ya iso da tambaya, sai dai tun kafin ya iso cikin garin mu, Manga da Abokan shi suka mishi
rashin mutunci, na fitar hankali, kamar zasu kona shi da ranshi,
Labari yazo mana cewa su Manga sun hana wani mutum zuwa garin nan,
Allah sarki haka Aahil ya koma,(โน๏ธ๐ค Karka damu wannan sharrin wancan kafirin ne
zamu jone)
......
Ranar da zan tafi makarantar, Baba ya turani cikin gida, abin dariya. Sai gashi har da cewa.
"Muna jiran tukwaicin boko"
Inji Matar Baba Yawale, sai kuwa suka saka dariya.
Dariya nayi musu sannan nace.
"Allah ya tayani tsare kimata"
Wannan maganar ta sanya su shiru har na fita suna zaune sake da bakinsu.
Har mararaba suka rakoni, abin mamaki sai ga Dr, zuba kayan yayi. Muka koma cikin
gari.
Ya gaida baba, da yan uwansa. Sannan yayi musu wankan hannun cikin aljuhun.
Sosai ya kashe bakin mutane, sannan ya dawo dani gaban baba suka min fada sosai.
Sannan Baba ฦดace.
"Malam ga Amanar ta nan!"
"Nayi maka alqawarin da ruhin Yesu me tsarki zata dawo cikin amincin sa."
"Ni kuma na baka amanarta cikin amincin Allah"
Sosai iyayena suka yarda da Dr, sannan da zai tafi yace.
"Mubarak! Zaman gida bafa na maza bane! Ka bani takardarka mu nima maka aiki da SS."
Shafa kai Mubarak yayi sannan yace.
"Da ina son na cika federal Poly ne na nan Bauchi shekara biyu."
"Toh duk yadda kuka yi kayi min magana,, ina tare da kai"
Haka ya gama zai tafi ya kalle Abdul sannan yace.
"Malam Abdul! Kaki makaranta, zan dawo next week ka shirya Military school Jos!"
"Meemah kema Addarmu Zaki biyo ko school of nursing Zaki"
Tsalle tayi sannan tace.
"Yaya duk wanda ka zab'a min ina so"
"Toh shikenan! Zan zo Next!"
Ni dai ban ce kome ba, har muka gama, sannan muka yi sallama zamu bar garin, zuwan
manga Naga ya fita sunyi magana can ya koma cikin mota ya dauki abu, yana zuwa ya mika
mishi, key yace.
"An jima zasu kawo maka, amma kayi ฦoฦarin zama na gari"
Godiya har da ihu
Haka muka bar garin naga yana kallon gurare, tare da gyada kan shi.
Bai ce min kome ba, kaina na kallon tagar motar, ji nayi ya ajiye min abu akan cinyata na juya.
iPhone12 pro ce, ya daura min kwalinta, bai ce min cikanki ba, Nima ban damu na tambaya
ba, sai can naji kunya ta kamani nace.
"Na waye?!"
Banza ya bawa ajiyata, sai yanzun na tuna tun da yazo sannu bai hadani dashi ba.
"Kayi hakuri!"
"Me aka min?!"
Juyawa nayi na kalle shi, sannan na mai da kaina titi.
Daga haka bai kuma ce min kome ba.
Bamu tsaya ba gaskiya sai a kaduna, inda ya kaini Sadau beauty aka min gyaran fuskan da
zaba min man shafawa, sai kaya da yayita jida min, tare da takalma, kai duk wani abinda zan
saka nafito yar yayi ya saya min.
Gurin cin abinci muka je, na kasa ci sai da yayi mana takeaway.
Bamu iso Zariya ba sai karfe uku, ya kawo ni wani state. Sannan ya fito ya fara shiga da
kayana, ina bin gidan da kallo.
Muna shiga ciki naga an saka kome, har da kayan kallo karamin friji, duk abinda zan
bukata akwai a gidan.
"Gobe zaki shigo school, sabida kuna da Class. Akwai Driven da zai zo yana kai ki da dawo
dake. Wannan gidan ki zauna har ki gama sauran lokacin da ya rage! Bazan tuna miki kome ba,
sai dai kuyi kokarin kare kimarki, batun wancan gayen ki manta dashi, ga kome na bar miki."
Gyad'a kai nayi kawai dan wallahi bazan kyale Aahil ba, yana tafiya na rufe gidan na
cigaba dayi kimtsa gidan ina duba abinda zan ci.
Tunda nayi sallah, na kwanta. Ina tashi na tuna da kayan shi da zan bashi.
Ban kira shi ba dan bana son yayi tunanin wani abu.
......
Washi gari..
Karfe tara Driven yazo, doguwar rigar baki na saka wanda yake da ratsin Golder a jiki, na nad'e
kaina da gyalen golder, sannan na fito rike da jaka, na fito.
Zama nayi a cikin motar, ina duba waya na lokaci ya tafi.
A hankali muke tafiya, har muka isa makarantar, wata mota ne tayi ฦamar zata buje
mu, muka bari ta wuce, parking space muka je, na gama daukar kome na bude motar na fito.
Yayinda shima ya fito cikin motar shi, cikin wata kafiran shadda, ash color, sai gaban shi Dr
sanye da Canada suit.
Kamar Ance ya juyo Fuskar shi sai a kaina, bakin shi na rawa yana nuna ni da yatsa
yace......
So min tab'i ango ya dafa Amarya ๐คฉ๐
.08130269641.....
.na kudine
Saura page daya na gama free
[7/2, 9:03 PM] BAHAUSHIYAH๐ฅฐ: BAHAUSHIYAH
๐๐ข๐ต๐ต๐ข๐ณ๐ข ๐ ๐ข๐ฏ ๐๐ข๐ต๐ข
Impossible.
Babi-sha-tara
"Husnah HABIB Manga!!!"
Dafe goshinsa yayi tare da juya inda Dr yake yace.
"Ka ga abinda na gani!"
Cikin halin ko ina kula ya rab'a gefen shi Dr yayi ya bar gurin yayinda nima na wuce kamar
ban san halin shi ba.
Mamaki ne ya kama shi, kamar wanda aka dasa shi a gurin ya cigaba da tsayuwar, cike da
mamaki.
"Husnah HABIB Manga! Anya ba ita bace! Kai itace mana, taya haka, ina bazai yi ba."
Da sassarfa ya shigo cikin department din su, lokacin har nayi abinda ya kawo ni zan fita.
Tsare hanyar yayi cikin murmushin sa, na salon yaudara, yace..
"Kamar HUSNAH ko?!"
Juya idanuna nayi akan shi tare da girgiza kai nace.
"Excuse me!"
Matsa min yayi na fita, cikin ji da kai nake taku, dayawa daliban da suka sanni sai gasu suna
ta d'aga min hannu, haษuwa ta da Aahil ya fama min ciwon shekara daya!
Am just keep smile in my face! Deep inside my heart amma feel bada, domin sai gashi a
cikin makarantar ana nuna ni, tare da d'ago al'amarin ya kuma zama trending again.
Koda na shiga aji kowa kallona yake musamman da na kasance yar gaba dasu da aka
dawo dani baya.
Wata yarinya ce itama yar kwalisa, na zauna a kusada ita.
Kallona tayi tare da mika min hannu!
"Zahrah Almustapha Chinade"
"Daga Bauchi?!"
Na tambaye ta!
Murmushi tayi sannan tace.
"Eh! Amma mazauna kaduna!"
Murmushi nayi mata sannan nace.
"Asma'uh Muhammad Habib, from Toro, amma kauyen Narabi "
Zaro tayi sannan ta saka dariya, tace.
"Wowwww! Daga state daya muke"
Nan muka gaisa sama sama, muna cikin tattaunawa ne, Mutumin ya shigo, cikin isa da jin shi
wani ne!
Fito da jotty dina nayi, sannan na fidda birona.
"Barkan ku dalibai! Sabin zubi da tsofin hannu, toh gamu nan a wani tafiya i hope zaku yi
abinda iyayenku suka ka turo, ban da... Ok muyi abinda ya taramu"
.
Yana magana idanun shi na kaina, ban kula shi ba na cigaba da ษaukar abinda yake mana,
Sai da ya kwashi awa biyu curr tun 10 bai fito ba sai 12, tare da Zahrah muka fito, itama
tana murmushi tace.
"Muje mu can mu jira"
Karar wayata ce ta sani duba jaka.
Sako aka turo min, shaf na manta da Dr.
๐๐ฃ๐ ๐๐๐ฉ๐๐ฃ ๐๐๐๐ช ๐ฌ๐๐ฉ๐ ๐ข๐๐ฉ๐จ๐๐ก๐?
Tab'e baki nayi cikin gajiya na tura mishi.
๐๐๐ฃ๐! ๐๐๐๐ฃ ๐ ๐ ๐จ๐๐ข๐ ๐ก๐ค๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐ฌ๐๐ ๐๐๐ ๐๐ฃ๐ ๐ ๐ ๐๐ช๐ง๐๐ฃ๐!
Kashe wayar nayi, sannan muka zauna. Muna hira da Zahra.
Muna d'an hira sama sama! Aka zo daukarta.
"Asmy kizo mu ajiyeki mana!"
murmusa mata nayi sannan na nuna mata driven. Mikewa nayi sannan nace.
"Anzo dauka na, ma"
"Toh sai gobe kenan?!"
"Eh da Yardan Ubangiji!"
Na gaya mata,
Tana shiga motar su nima ina shiga.
Nima shiga nayi, kamar ance ina daga kai sai ga Dr ya zuba hannun shi a cikin
aljuhun.
Juyawa yayi abinshi ciki, ajiyar zuciya na sauke, sannan na jingina kaina, ina girmama
alamarin Dr Bature, ya zame min rumfar sha shirgi, ya shigo rayuwata a dai dai lokacin da ya
dace.
Lumshe idanuna nayi ina girmama rashin kunya da tsana ฦarara da na nuna mishi,
yau shine min wani tsanni rayuwata, ban dashi da bazan dawo nan ba, ban dashi da na zama
tarihi.
Ban dashi da nayi haukar gayawa iyayena korata akayi, haduwata dashi. Itace abu mafi
daraja da na tab'a samu a rayuwata.
Sai dai kash.....
Yarena Addini na ya min iyaka da shi, kasancewar shi bahago daga wata duniya na daban ni
kuma ba damiya daga wata dinuya dan haka fatan Alkhairi itace a tsakaninmu.
Ban san mu iso gida ba, dai da Driven yace.
"Madam mun iso!"
Fitowa nayi na shiga cikin gidan. Na bude d'akina na zuba kayana.
---
"BYC! Ina maka magana kana share ni, ko baka ga yarinyar bace"
D'ago kai yayi a fusace, amma bazaka fahimci hakan ba, sabida ya toshe idanun shi da wata
sun glass! Shi burin shi tunda ta bar cikin makarantar, ya ishe shi.
"Wacce yarinya kenan?!" Yayi mishi tambayar renin hankali.
Tsaki yayi sannan yace.
"Husnah mana!"
"Ai na manta da ita!"
Yarinyar da muka dan yi soyayyar shan minti" ya faษa a fusace.
"Haba easy! Mutumin! Wallahi na manta ne! Amma yanzun na tunata! Ince kwanaki kaje
gurinta?!".
Tsaki yayi sannan yace.
"Ina naje! Ai ina ganin ba yar garin bace! Domin naje wani mahaukaci ya kusan illatani shi yasa
ban gaya maka ba."
"Ai sabida kaje cutar da yar mutane ce shi yasa ta kare maka, Wallahi ka daina abinda kake
tun kafin lokaci ta kure maka"
Kyalkyalewa yayi da dariya sannan ya ce.
"Allah gafuru rahim ne! Dan halal har yanzun kofafin tuba abude suke ba a rufe su ba."
Baki sake Dr ke kallon Aahil, sabida don zuciya irin tashi ya rufe ido yana kiran Allah gafuru
rahim ne, shi yasa baya sha'awan musulinci, idan akwai abinda yake bashi mamaki yadda
musulmai ke aikata kuskure su nuna Allah nasu ne, su kadai.
Haka yayi ta hauka a cikin ofishin Dr bai ce mishi kome ba baya daga abinda ya faษa
mishi.
......
Tunda na shiga gida, na zube a falon, cikin Sa'a suka kawo wuta, har barci yayi gaba dani.
Karfe biyu daiยฒ na farka, miฦa nayi sannan na nufi cikin dakin nayi alola, nayi sallah ina
idarwa nazo na kwab'a garin dan wake, na fara jefawa. Dake nazo da garin yaji.
Zafi ya dame ni, na shiga daki na cire kayan jikina, zani na daura a kirjina sai dan hular
da na saka, na cigaba da aikina.
Ban gama ba sai uku Sara, mangyad'an kuli nazo da ita amma na samu ya kawo min Oky.
Zama nayi na zuba a filet, na koma gefe na yanka albasa, sannan na zauna na fara ci,
ina binshi da yaji.
Buga kofar aka yi, na mike ina tura baki dan nasan ba Lallai bane na kuma komawa akan
abincin.
Ji nake idan na buษe ba fallawa wanda ya daga ni a cikin abinci na mari, cikin yar hasala
na bude kofar.
Idanun mu ne, suka harde da juna, na wasu dakikai. Nayi maza na janye.
Da sauri na rufe kofar cike da mamaki, tare da wata muguwar kunya, ji nake kamar na bude
kasa na shige.
Daki na koma na saka kayana sannan na fito ina sunkuyar da kai na kasa,
Kamar babu abinda ya gani, dan da na buษe mishi kofar shigowa yayi yana, shakar kamshin
mangyad'a, sauke idanun shi yayi a filet din dan wake, janye idanun shi yayi sannan ya cigaba
da tsayuwa.
Fito da wayar shi yayi, yana ta danne danne, a raina nace.
Shi kuma haka Allah ya halicce shi bai gajiya da latse latse.
D'ago kai yayi tare da zuba min Ido, sannan ya mai da kan wayar.
Komawa daki nayi na dauki jakata, na ciro wayar sannan na kunnata.
Ina rike da ita, sako ta shigo.
๐๐ฎ๐ฟ๐ธ๐ถ ๐ธ๐๐บ๐ฎ ๐ถ๐ฟ๐ถ๐ป ๐๐ฎ๐ป๐ป๐ฎ๐ป ๐๐ต๐ถ๐ด๐ฎ๐ฟ ๐๐ฎ๐บ๐ฎ๐ป๐ถ๐ป ๐ฟ๐ฎ๐๐ต๐ถ๐ป ๐ถ๐น๐ถ๐บ๐ถ ๐ฎ๐ธ๐ฎ๐๐ถ, ๐ฝ๐น๐ ๐ธ๐ถ ๐๐ฎ๐๐ฎ๐ป๐ถ ๐ธ๐ฎ๐ฟ๐ฒ ๐ฎ๐บ๐ฎ๐ป๐ฎ๐ฟ ๐๐ฎ ๐ฎ๐ธ๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ป๐ถ|
Kallon shi nayi, sannan na tura mishi.
๐ฝ๐๐ฏ๐๐ฃ ๐ ๐ช๐ข๐ ๐๐!
....
Satar kallon juna muka yi, sannan ya turo min.
๐๐ฃ๐ ๐จ๐๐ ๐ค๐ฃ๐! ๐๐๐ช ๐ฃ๐๐ ๐ ๐จ๐ค๐ฃ ๐จ๐๐๐๐ ๐๐๐ช๐๐
Shi kan sa bai san dalilin gaya mata ba, ya dai tsinci kanshi da gaya mata inda zai je.
๐ค๐ !!
Shi ga dakin nayi na dauko mishi aikan shi, sannan nazo gabanshi na ajiye mishi.
Sannan na juya, zuwa inda Abincina yake na zuba mishi, zan saka yaji.
"Kad'an bani ci pepper"
Maggi na fasa mishi, sannan na ajiye mishi dan karamar kular.
"Da fatan babu matsala?!"
"Hmm," nace mishi.
Fita yayi bai kuma juyowa ba.
---
Washi gari....
Zaune yake a tsakiyar manyan Pastors da Bishop Yohana!
"Abraham! Muna jinka, meye Matsalar ka da baka son Aure?!" Inji babban su.
Shiru yayi. Can Baban Devanah yayi magana cikin b'acin rai yace.
"Ba yau ba! Devanah take haukar son shi, but yaron nan ido da ido ya gaya mata baya sonta.
Haka ma bai mishi ba, sai da taje inda yake ya wulakantata. Sabida kaf....."
"Ezra! Ka daina aibanta min Yarona! Nasan Abraham mai biyayya ne, kuma zai auri
Devanah shi kenan!"
"Doris dole nayi Magana, ban san meye Manufar ku akan shi ba, amma ai dole wata rana
ungulu zata koma gidanta na tsamiya, ko kunso ko kunki. Dole ya tsallake line of destiny din shi.
Abinda na sani, Y'ata tana son shi, about rayuwar shi kune kuka sani but bazamu iya changing
destiny din shi bane, zamu yi iya yi mu."
"Ezra! Domin yarinyar ka shine kake irin wannan maganar! Eyye don't forget ba ayiwa
namiji auren dole, idan yace yana. Kuma nace maka zai aureta me yasa kake mana haka ne?"
Sosai tashin hankali ne sosai ya bayyana a cikin Family din dakyar wasu manyan suka
dakatar da haka, sannan aka kuma baikon Devanah da Bature zai ayi bikin november.
Sai yamma likis ya dawo, ban ganshi ba tunda bai zo ba, sako ya turo min.
๐ฟ๐ ๐๐๐ฌ๐ค! ๐ฝ๐ช๐ฉ ๐๐๐ฏ๐๐ฃ ๐จ๐๐ข๐ ๐ฏ๐ช๐ฌ๐ ๐๐ฃ๐๐ ๐๐๐๐ช ๐ข๐๐ฉ๐จ๐๐ก๐?!
Ina karatu naji sakon shi, dubawa nayi, sannan na tabe baki nace.
๐ฝ๐๐ง๐ ๐ ๐๐ ๐๐๐ฃ๐ฎ๐/ ๐จ๐๐ฃ๐ฃ๐ช ๐๐ ๐๐๐๐๐ฎ๐.
.......
Bai kuma bin takaina ba, sai dai yana cike da damuwa sosai.
.....
Washegari.
Karfe biyu muka shiga ajin, Shi ya shigo mana aji, ya nutsu sosai yana mana bayani, cikin
gogewa da kwarewa.
Sab'anin Dr A A har ya gama yan mata ne, a gaban shi.
.......
Shigowa yayi ya kalli Dr yace.
"Friend! Excuse me. Idan kun gama ina son gani HUSNAH."
Dr bai ce mishi kome ba, na kauda kaina fuskata a daure nace.
"Bazan sami zuwa ba!"
Har ya juya zai fita na fadi haka.
Takowa yayi, har gabana ya kura min ido, yace.
"Idan nace ayi abu! Ina nufin