shi.
Yayi wani irin nisa a cikin tunani, wanda daga juya zuwa yau bai tab'a tsammani ba.
Karfe biyu saura ya isa abuja, inda aka zo daukar shi da wasu audi 2019, da tambarin
CAN..
(Idan aka ce CAN magana ya kare! Kungiyar kiristoci ne! Reshen naija, CAN suna da
wani irin haษin kai. Domin misali zaku duba rikicin Jos, har sojoji suke dashi, kuma kudaden
shigar su yana fitowa ne daga Kudin baiko da ake bayarwa nan a church)
Dr Bature Yohana Chibok, daya daga cikin matasan kungiyar ne, wanda suke matukar
alfahari dashi, Dr Bature yayi nisa a cikin addini shi, inda tsabar kar musulmi ya kalubalence shi
har wasu surori na Alqur'ani ya haddace ma'anar su.
......
Bishop Yohana Chibok POV.
A unguwar Asokoro estate, gidajen masu hannu da shuni ne, birjin a gurin, a hankali motar
da suka zo daukar shi suke ratsa unguwar.
Sai bin motar da ido ake, musamman masu zuwa daurin aure, dan unguwar su daya da Aahil,
asalima makotane tun daga Rome, Italy suke tare.
Tun Mommah nakin mu'amalar shi da Aahil har ta hakura, dan idan ta hana shi fita zai kwana
ya wuni bai ci komai ba, dan dole take barin shi yake zuwa gidansu Aahil, gashi Ummin Aahil
itama tana matuฦar son shi.
Wani katon get aka bude mishi wanda aka rubuta CAN a jiki suka shiga.
A hankali ya sauke kafar shi daya tare da shaฦar kamshin furannin gidan musamman Queen
of the day, a Sannu ya fito baki daya.
A hankali yayi tsaki, yace.
"I wish da tana nan yanzun Father cinye Ni zai yi Nama danye."
"God bless! If you finish that your thinks am always here"
Dariya yayi tare da shafa kanshi yace.
"Father! Da alamu you're really angry"
Jinjina kai yayi sannan yace.
"God bless you! and your dreams maybe come true"
"Amen! Father!"
"Not Amen! Kasan me yasa ba a baka matsayi ba har yanzun a Church, sabida kaki aure! Ga
Devanah she always worry, Kai baka da kishine. Look at you friend yau zai yi aure dukda am
sure ka girme shi, me yasa bazaka yi aure ba naga Jikokina before na koma fadar Yesuu me
ceto."
Tari Bishop ya fara Dr Bature ya rike shi, tare da shiga cikin gidan, suka zauna, wasu kartin
maza ne masu kama da irin mugayen arnan dajin nan suka mike.
"Oh! Fathar me yasa baka ji, kaje kana yadda ciwonka a banza!"
Daya daga cikin su ya harari Dr tare da jan tsaki.
"Joel ni kakewa tsaki!"
"No Father!"
"Toh who?!"
"Am sorry"
"Zauna Father, Daniel please bani bottle na ruwa mana"
"Mr Arrogant you came back, zaka dame ni da bani bani, idan an ce kayi aure kafata keep
wani deeply smile, kaman mace"
"Oh bro jeka mana, Kawar Devanah"
"Ahhh now!"
Da sauri ya kawo mishi ruwa ya bud'e a hankali ya sakawa Bishop a baki, yana sha ya ture
goran yace.
"Your name is God bless! Shi yasa ka zama me albarka a cikin duniyar nan,"
Kallon agogo yayi cikin sauri ya mike tare da cewa.
"Father bari naje daurin aure Abokina"
Cikin Tsokana Daniel yace.
"What's about you nd devanah"
Da sauri ya haura sama ya watsa ruwa sannan yayi yar abinda yayi ya saka babbar riga da
jamfa, sannan ya saka wata agogon shi wanda ita kadai ma ta ishe me karamin karfi rayuwa!
Wato sifa manyan Christian suna jin dadin rayuwarsu, domin kudi suke samu na fitar hankali.
Musamman kudin baikon nan,(๐๐คฃShegen kudi hatta dan dake cikin ana cire mishi nashi
hadayar)
Takalmin kafar shima kawai yaci a kalla, balle kudin shaddar jikin shi. Da sauri yake
saukowa yana gyara zaman hular shi akan shi.
"Father zan tafi dan an kusan daura auren!"
"God bless! Ina maka fatan albarka sannan ka dawo lafiya!"
"Amen! Father Ina mommah take"
Murmushi Father yayi sannan yace.
"Ai Mamarku akwai Ibada, sunje Yawon Bushara, can Chibok."
"Am why she didn't."
"Hey! Jeka idan ka dawo kayi mita, Mr Arrogant. Gaskiya I pity for Devanah domin kai sai me
hakuri zata zauna da kai a dawo lafiya, abokin Yaran musulmai"
Idan yabi na Daniel cika mishi kunne zai yi dan haka, yafita da sauri.
Drive da ya kawo shi shine ya kai shi babbar masallacin Abuja a inda za a daura auren.
Koda ya isa ya samu ana cikin shirin daurin auren ne, dan haka ya kutsa dakyar har
inda ya kusan samun Aahil.
Dafa shi aka yi, cike da mamaki ya juya yana kallon mutumin..
"Na kyale Moddibo Usman Abubakar ne sabida na aika ka gidan Kaso, ashe har ya shiga
ya fita. Dole ya saka hannu a wannan kwangilar ko kuma na saka a Yarona Aahdeel yayi
band'ashenta, idan bai saka ba, kuwa toh wannan katafaren Estate din da yake ciki shida
Moddibo Family ya bani sai na fita harkanku"
Murmushi yayi tare da ture hannun Mutumin, yace.
"Am sorry sir! I think bani bane, am Dr Bature Yohana Chibok."
Har ya juya zai tafi sai yaji ba zai iya barin wannan abin a ranshi ba.
Tsayawa yayi Sosai a gaban mutumin, ya juya idanun shi da suke dama daya a juye yake yace.
"Kalli cikin idanuna! Kasa ke mai-maita kalmar cin zarafi, ga wata mace, sai nasaka anyi
hanging dinka. Ko ya'ya kayiwa yarinyar kallon banza, sai na cika maka zuciyarka da firgici kalli
cikin idanuna."
Jikin Mutmin ne yayi mugun sanyi, sabida kallon cikin idanun Dr Bature ya sanya shi jin
marar shi ta cika da fitsari.
Da sauri ya bar gurin, wannan itace baiwar da Dr Bature yake da ita, sam shi yasa bai
shiga Shirgin kowa but da zaran ka jure shi karka yarda yace maka kalli cikin idanun shi, domin
idanun da zaran ranshi ya b'aci toh komawa kalar ta mage ko na zaki take juyewa.......
Guess who......
Karku manta Wannan book kuษi ne.
Idan ta bank ne=200
Idan kuma katin mtn=300
Gama su bukatar VIP=500 bank account
Kuma katin mtn ne=600
Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdul Rahman
Manga
Idan ka biya ka sanar dani ta wannan number08130269641๐๐ป
Thanks........
Idan kuma kana son Inuwar Gajimare! Kayi min magana ta wannan number! Shima.
Long page....
[7/2, 8:52 PM] BAHAUSHIYAH๐ฅฐ: BAHAUSHIYA
๐ญ๐๐ข๐ต๐ต๐ข๐ณ๐ข ๐ ๐ข๐ฏ ๐๐ข๐ต๐ข๐
๐๐๐๐ค๐ ๐๐ฃ ๐๐๐ฉ๐ฉ๐๐๐๐ฃ ๐๐๐๐๐ช๐ ๐๐ง๐ฌ๐ ๐๐!
๐๐๐๐ฃ๐๐ ๐ผ๐๐๐ช๐ก๐ก๐๐๐ ๐๐๐ฏ๐๐ง๐! ๐๐๐ข๐๐ฃ๐๐ฅฐ
๐๐๐๐๐๐๐๐ฎ๐๐ฉ๐ ๐ฉ๐ ๐ ๐๐๐ฃ๐! ๐๐ฃ๐ ๐ฉ๐จ๐๐ฎ๐ ๐ฃ๐ ๐จ๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐ง๐๐๐ฃ ๐ผ๐๐๐ช'๐๐ง ๐๐ ๐ ๐๐ ๐ ๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐ช๐ฃ๐๐ ๐ง๐๐ฃ๐๐ง ๐๐ ๐ ๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐ ๐ฃ๐
๐๐๐ง ๐๐ช๐ฌ๐ ๐๐๐ช๐๐ฅฐ๐, ๐ผ๐ก๐ก๐๐ ๐ฎ๐ ๐๐๐๐๐ง๐ฉ๐ ๐ข๐๐ ๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ข๐!๐ฅฐ๐
Black Monday.
Babi-takwas
Shiru yayi yana nazarin can ya tattara ya watsar sannan yayi wucewar shi inda angwaye
suke, yana isa gurin cikin fara'a Dr Aahil wanda ya sha manyan kaya, irin na Dr Bature, ya mika
mishi hannu suka gaisa.
Wasu tawagane suka zo wucewa, kan Dr Bature a sunkuye ji yayi ana busa algaita
lafiya Moddibo Usman Abubakar! Lafiya toron Giwa dan Abubakar. Na gaida Uban Abubakar.
Koda ya d'ago sun wuce, murmushi yayi sannan ya kalli Dr Aahil cikin raha yace.
"Gaskiya ina son culture dinku na Hausawa, kamar yadda akaiwa wancan mutumin ya burgeni."
Cikin jin dadi Dr Aahil ya bude baki zai magana akayi shelar an daura Auren Dr Aahil Aliyu
Maitama tare da A'isha Ahmad Sodangi...
Kura mishi Ido Dr yayi cikin tausayin Husnah. Ganin yadda A.A ke murna dama haka
Musulmai sukewa junar su, Amma me yasa?! selfish.
Tabbas son zuciya ya sanya Dr Aahil ya cutar da innocent lady, da bata ji ba, bata gani ba
yayi destroy rayuwarta into hell.
Ganin yadda kowa ke taya shi murna shima ya mik'a mishi hannu daga nan suka dunguma
zuwa liyyafa wanda aka shirya a Center hall.
Gurin yayi kyau, duk abinda ake yi, Dr Bature yana kallon su har suka gama.
Ranar bai koma gida ba sai ฦarfe biyar yana shiga gidan ya tadda ita, kauda kai yayi cikin
sauri ya nufi step yana hada bibiyu.
Dan haษu yarinyar ta haษu, matsalar shi baya yinta ne baki d'aya.
Kallon Daniel tayi, kamar zata yi kuka tace.
"Kana ganin ya share ni?!"
"Mr Arrogant! Ne fa, Devanah ga Joel da yake sonki me yasa ba zaki amince ba".
Murmushi tayi tana kallon Joel, akwai mabanbanta halayyar da ya raba Dr Bature da Joel, Dr
mutum ne me kamun kai, ko taba ba yasha, balle wine.
And secondly Dr baya niman mata amma shi yanayi. Sun isheka."
Mik'ewa tayi tabi bayan shi, tana zuwa yaji kofar a rufe, tsaki tayi ta cigaba da bugawa.
Kuma shima yasan da haka, zata iya shigo mishi, that's why ya rufe kofar.
Sai da ya shirya tsaf sannan ya zo ya bude sanin cewa zata ya rungume shi.
Shi yasa sai ya rungume kofar yayi Banga banga.
"Excuse Mr Arrogant!"
Murmushi yayi, sannan yace.
"Ok Miss Funny zan shirya tukun"
Ya rufe kofar, abin shi kwanciyarshi yayi cikin jin dadi ya manta da ita.
Tabbas yasan Devanah tana masifar son shi, amma Allah ya gani baya sonta, baki daya a
rayuwarsa. Bawai bata yi bane, tayi iya wuya shine dai bata mishi ba. Kuma da Babanta da
Mommah cikin su daya.
Sai da ya share barcina shi tukun kiran sallar magabri ya tashe shi.
"Wancan Ustadz din nan yana da katon voice!"
A hankali ya bude labule yaga yadda akayi ruwa sosai, yana son yanayin sanyi, sabida
tana sanya shi farin ciki, Infact ma yanayin sanyin damina tana kara mishi sanin cewa shi din
namijine cikakken mai lafiya.
A yanzun haka bai ki a ce yana da matar shi ba. Wacce da zaran anyi ruwa yazo kusa dashi.
Amma ina kallon mata yake marasa sanin fa'idar so, baya son macen da zata so shi ya fi
dacewa yace yana sonta.
Ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya shirya tsaf, cikin kananun kaya kafin lokacin
zuwa dinner yayi.
Yana fitowa yaga kowa a saman dinning table, share su yayi dan yasan Devanah ce tayi
girkin.
Diban Whiter rice tayi da vegetables sauce, sai coslow ta kawo mishi.
Kallonta yayi dake babu masu lura dasu kowa na cin abincin sa ne, ya fincikota zuwa kirjinshi
kasa kasa yace.
"Bana son Kona fix din gashin kanki da kuma nail dinki, shi yake sani jin kyamar cin abincin ki,
Kinga duk inda zanje zan dawo naci abincin Mommah, kina sona but ya kamata ki koye yadda
zaki kula da abinda zanci."
"Am so sorry! Ba zan kuma ba."
Jan abincin yayi ya fara ci, har ya koshi, zama suka yi ya janyota sosai dan ya lura yana
son haka, daura kanta yayi a cinyar shi yana bata labari, wanda dayawa akan ibadarsu ba
Wannan ba shine matsalar ba, ita kawai ya furta mata cewa.
Ina sonki. Shine damuwarta. Amma gayen nan ya shareta ya cigaba da bata labarin kanzon
kurege.
Mik'ewa tayi zaune tace.
"Baka da wani labari sai na Ibada da Addini, ni bashi ne damuwa na ba Bature ina matuฦar
sonka, wanda zai iya sanyani kashe duk wacce kace kana so, Bature AM ready to take ko wani
irin kalubale akanka, Matukar wata ta shigo rayuwarka zan kasheta kuma zan kashe banza.
Tunda
Baka fahimci how many years na d'auka ina jigila da sonka."
Juyawa tayi zuwa ga Father tace.
"Father! Na rantse da Yesu me tsarki bazan tab'a barin Bature ya hadani da wata mace na,
koda kuwa zata zame min ajalina Father ka gaya mishi na kai makura gurin son shi sai yaushe
zai furta min yana sona."
Mik'ewa yayi zai fita, Father ฦดace.
"Abraham! My Son!"
Tsayawa yayi cak, tare da kallon Bishop.
"Meye laifin ta?!"
Ya tambaye shi a sanyayye,
"Bata da matsala, kuma ni bawai bana sonta bane, ban san ya nake jinta bane a raina,
Father trying to love Devanah na kasa, Father bani ke son Devanah ba, Brother na shi yake
sonta, but am."
"Bature! Meye laifina?!"
"Ita soyayya abace da kana iya jin shi koda baka tare da masoyin ka, Devanah idan bana
tare dake Mantawa nake da duniyarki Devanah baki cikin ruhina, Kiyi hakuri ษan ruhin me tsarki
Yesu Almasihu."
Fasa ihu tayi tare da Fad'uwa a kasa tana birgima, tsaki Joel yayi cikin fada yace.
"So what dan yace baya sonki! But am still love you!"
"Hell you da love din banza da wofi!"
Haka Devanah ta hauka, har ya fito daga sanye da dark grey suit, sannan ya durkusa ya
d'agota.
Kura mishi ido tayi ta kuma sake wani Irin kuka, me ban tausayi.
"Kace baka sona?!"
Sosa goshinsa yayi sannan ya tsallake ta yayi tafiyar shi.
---
Husnah. POV
Innarmu ce ta koma gida ni na zauna a jikin Baba wanda bai da Alamar farfaษowa.
Kura mishi ido nayi kwalla na zuba daga idanuna, na ฦasa fahimtar kome dan gani
nake kamar nice silar fadawar shi wannan halin rayuwar, Baba yayi spendin all Rayuwar shi for
my Education but lokaci guda kome ya juya up side down. Duk sabida ni.
"Ya rabb." Na fada a sanyayye,
Zuwan Meemah ya rage min nauyin tunanin da nake, muna zaune har dare Before
Innarmu tazo muka koma gida.
Tunda muka dawo nayi sallah duba agogon nayi naga karfe tara saura, daukar kudi nayi na
fita.
Can wani unguwa naje akwai wani sabon asibiti me sunan Allah na kowa.
Bayani nayiwa Likitan, murmushi yayi sannan ya rubuta min test kala uku, da One scanner
naje aka yi min.
Dawowa nayi na zauna har sakamakon ya fito na kai mishi, tunda ba zauna nake share
kwalla, dan nasan na karanci abinda ya shi midwifery, amma Sam tunani na bai bani ina da ciki
ba.
Kallona Dr yayi cikin nutsuwa sannan yace.
"Yanzun idan na gaya miki wani magana bayan abinda kike tsammani ya zaki ji?!"
Hade hannuna nayi guri guda, kwalla na zuba nace.
"Alhamdulillah!"
Murmushi yayi sosai sannan yace.
"Congratulations! Baki da matsalar kome! Babu Aid Babu pregnant, Babu wani ciwo. Sai na
damuwa jininki ya haura sosai."
Gyad'a kai nayi, ya rubuta min magani sannan nayi mishi godiya na fita.
....... Nayi yar karamar barci, amma da zaran na tuna gobe Sunday sai naji bugun
zuciyata ya tsananta.
Kwana nayi ina juyi har kusan asuba, sannan na samu barci. Da asuba da Meemah ta
tashe ni da ciwon kai na tashi, sallah ma dakyar nayi.
Abin karyawa da aka kawo min ma ban iya ci ba, sai kusan azhar lokacin Innarmu
tazo, nayi wanka tare da cin abinci nasha magani.
Duk ranar na wuni ne a gida, sai dare nace Innarmu ta zauna Ni naje na kwana a jikin
Baba.
Dakyar ta yarda, naje na kwanan.
Karfe biyar da rabi yayi mata a cikin asibitin, nayi mata sallama.
Tsoron da firgici sun samu mazauni a zuciyata, tashin hankali da gigita sun tabbatar a
fuskana, a haka na shirya na wuce zaria. Tun daga bakin get ake nuna ni, tun daga nan na
fahimci am finish.
Kusan me yasa haka yayi muni, sabida Ni Bahaushiya ce! Kuma wacce tafito cikin al'ummar
musulmi, idan da Kirista ce baza a damu da ita ba. Sabida basu koyi da da'a kamar bahaushiya,
Ko dan ina talaka ce, kai tsaye hostel na wuce, cike da kunya da nadama mara amfani, yau
masu nuna min Dr na soma sune masu zagina, masu zagina dan naki amsar soyayyarshi sune
masu min dariya masu ganin cutatta zai yi sune masu sunkuyar da kai cikin takaici da bakin ciki.
Ina shiga suka kwashe da dariya, sai Teemah ce tazo da sauri.
Ta rike hannuna muka shiga daga cikin wani irin marayan kuka na sake, na shiga bata
labarin halin da nake ciki.
"Allah yana tare dake, meye na kuka, kece baki san me ya faru ba, bayan dukar da yayi miki,
shugaban dalibai da wasu dalibai sunyi zanga-zanga, tun ranar juma'a har jiya, kuma sunce a
miki adalci."
Girgiza kai nayi, muna zaune har lokacin zuwa aji yayi, kamar bazan fita ba na shirya. Amma
na fara da hada kaya na ne, sannan na shirya zuy aji.
Duk inda na wuce fatan Alkhairi kawai ake min, nasan bani shiga rayuwar kowa, amma
dayawa mutane suna yina ne sabida baiwar da Allah yayi min na dinbun ilimi,
Shi yasa da na zauna sai gashi ana kawo min gaisuwa.
Ni dai bana iya Magana, shigowar Dr Bature, fuskar shi a murtuke shi ya kuma hautsina
min lissafi, sai satar kallon shi nake.
Amma fir yaki kallona, shiru yayi yana latsa wayar shi.
D'ago kai yayi sannan yace.
"Husnah HABIB Manga.". Yana fad'ar haka ya juya ya fita.
Yana fita na kalle yan ajin, cikin murmushi sannan nace.
"Assalamu alaikum! Ina me niman yafiyar ku, ban sani ba ko na zalince ku, Ni baku min kome
ba. Nagode."
Ina gama faษar haka na juya na fita, tare da tattara komatsan na.
Ban san me ya bani kwarin gwiwa ba, amma ko kukan zuci da nake. Conference hall naje,
na sami malaman mu ne da wasu daga cikin staff.
Tunda na isa cikin gurin na tsaya, sai wasu daga cikin dalibai.
An karanto min abinda aka ce nayi. Wasu abubuwan dalibai ke kareni, wasu kuma
malaman mu, karshe aka ce dai abisa hukuncina kora ce, sabida nayiwa Dr. Aahil Sharri.
Kuma iyayen shi sun nuna abu mishi hakkin su kar a lalata mishi suna, toh bisa ga bincike da
Dr Bature Yohana Chibok yayi tare da Imran Shaikh Abdul Hakim, tare da wasu dalibai. Sun
tsaya tsayin daka inda suka nuna min adalci an dakatar dani har na shekara d'aya!
"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Nagode sosai!
Insha Allah a zaman shekara d'aya zan koma iyayena su daura tarbiyyan da aka rusa, but Zan
DAWO DR AAHIL ALIYU MAITAMA, Nagode da tsaya min da kuka yi,"
Daga haka na juya tare da barin Hall din, kowa sai da ya sha jinin jikin shi, sabida nayi
maganar a sanyayye but cikin zuciyata yana kamawa da wuta ne, na fitan hankali.
Ban bar makarantar ba naga kiran Muba! Dauka nayi yace.
"Jikin baba ya tashi, ki dawo gida."
Kashe kiran nayi sannan na koma hostel na tattara kayana na fito dashi tare da barin
Makarantar, juyawa nayi na kalli bakin get, Ina me fatan Allah ya dawo dani domin karasa
wasan da aka fara na tashi 0, Dr Aahil ya tashi da 2....
Karku manta Wannan book kuษi ne.
Idan ta bank ne=200
Idan kuma katin mtn=300
Gama su bukatar VIP=500 bank account
Kuma katin mtn ne=600
Acct: 0472282105
GTBNK Ramlat Abdul Rahman
Manga
Idan ka biya ka sanar dani ta wannan number08130269641๐๐ป
Thanks........
Idan kuma kana son Inuwar Gajimare! Kayi min magana ta wannan number! Shima.
[7/2, 8:53 PM] BAHAUSHIYAH๐ฅฐ: BAHAUSHIYA
๐๐ข๐ต๐ต๐ข๐ณ๐ข ๐ ๐ข๐ฏ ๐๐ข๐ต๐ข
First challenging...
Babi-tara
Haka na bar makarantar ina kukan zuci, har na isa tasha.
Babban damuwata me zan gayawa Innarmu? Ambaton Allah nake baji ba gani. Har na
iso Kaduna, na rasa inda zan kai kayana.
Kawai sai na dauka na wuce gidan wata Yar unguwarmu matar tsohuwa ce, bata gani. Na
ajiye zan zo na amsa.
Sannan na wuce Asibiti nan naga Halin da Baba yake ciki zafin ciwo ya tab'a mishi brain,
sam yaki a ya zauna ni kawai yake son gani, yana gani na ya rike hannuna sannan yace.
"Muje ki kaini Mahaifata kar na mutu anan dan basu da asara sai ke."
Duk yadda naso ya fahimci halin da yake ciki yaki, dan dole aka mishi Alluran barci. Muna
cikin jarabta, amma Alhamdulillah tunda Allah bai wulakantamu ba. Jikin Baba da sauki
matsalar shi yasa rai sai mun bar Kaduna, dan har zuciyar shi ta soma tabuwa. Abun tausayi
haka muka tsayar da shawara, tare da rubuta mana magani, sauran kudin da ya rage aka
bamu.
Ranar da muka dawo, jikin mu duk yayi sanyi dan a ranar muka tattara kayanmu tsaf, muka
yi bankwana da garin Kaduna.
Baya bata kad'an...
Tafiyar mu kadan Sai ga Dr Bature yazo nima na, kuma abin takaici ya manta sunan Garinmu,
sai dai Rabi yake cewa.
...... Tafiyar awa hudu ya kawo mu, garin Narabi. Abin bakin cikin shine anki bamu inda
zamu sauka, duk yadda muka roki arziki, amma suka k'i.
Sai da wani dattijo Abokin Malam Manga yayi musu fatafata, aka bamu wani karamin part me
dauke da dakuna biyu, nan ma, mutumin yace ba zai yu ba shine suka bamu shashin Innarmu
na dame dauke da dakuna hudu, dukda ginin jar kasa ce. Amma yayi, dan haka muka shiga da
baba cikin dakunar bayan mun gyara ko ina.
Abin tausayi sai gashi wai kyamarmu ake a cikin gidan, babu me zuwa gurin mu,
Mubarak da Abdullahi, da Ghaddafi idan suka je masallaci ba'a tsayuwa kusada su.
Tsagwama kuwa ba a cewa kome, daga ni har Meemah da lulu bamu fita ko ina. So
muna cikin wani halin rayuwa.
Godiyar Allah mun tanadi kayan abincin mu, shi ya taimake mu, kome muna dashi. Sannan
ga Atm din Dr B, na kasa amfani dashi.
Jinyar jikin Baba shine matsalar mu.
Satin mu biyu da dawowa, Baba Yawale da Baba Haruna suka zo har kofar shashinmu,
wai sun zo duba Baba.
Basu shiga ba suka tsaya daga bakin kofa. Suka gama abinda zasu yi sannan suka fita.
Alhamdulillah, dukda halin da muke ciki, cimmar mu me kyau ce, domin da masarar mu ta
kare, kudin Hannun mubarak ya tafi nabardo yayi mana siyayyar kayan abinci.
Haka zalika baba na cika wata guda muka kawo shi, bauchi kunsan sha'anin kudi kuma
zara bata kyale dami ba, dan haka na tafi bankin da naga ansaka sunan shi a jikin Atm din,
wato Ecowa, nan naje cire kudin abinda na fara duba balance din, dafe machine din nayi kwalla
na zubo min, sabida kudin da suke cikin account din ya wuce misali, asalima kamar account din
shine na CAN.
Dan haka cikin hankali irin nawa na cire naira dubu 50, sannan na bar gurin, na koma
asibitin nan na samu sun bashi gado, duk abinda aka rubuta sai da muka saya.
Idan naga halin da muke ciki, blime kaina nake sabida duk abinda ya faru laifina ne.
Bazan tab'a yafewa kaina ba, dan haka, na duba wayata na kira Mubarak, na gaya mishi ya
gayawa Innarmu an kwantar damu.
Wannan karon mun fada hannun da ya dace domin likitotin sun san me suke yi, kuma
suna kokari domin kusan team din su, su goma ne akan shi..
Ranar test kawai bakwai aka bamu, abubuwa sun min yawa, dan haka Mubarak ya tawo ya
bar Innarmu, mu biyu muka yita kaiwa da komowa, har Allah yasa muka gama.
Idan na tafi masalaci sai na zauna nayita kuka, sabida bani da wata karfin zuciya.
A ranar naji wa'azin malam tijani yusuf guruntu, akan Zina wato mazinaciya jakar
gayu, ranar kamar zuciyata zata fita, nayi kuka har sai da aka shiga tambaya na.
Ni Husnah ba fara bace ni baka ce, idan nace baka Yes I mean black din, amma ina da
madai-daicin fasali, a cikin halittana idanuna da hakorana sune farare, dan haka bani da
wannan kyau da za a fasaltani, but Alhamdulillah.
Sai dai ni din doguwa ce, ina da tsayi wanda na dauko Innarmu, dan duk dakin mu
Mubark ne dan gajerenmu.
Mun sami tarbiya sosai, dan muna girmama na gaba damu, sannan bamu da kwadayi
da hangen nesa. Uwa uba. Abin hannun mu bai rufe mana ido ba. Muna da dabi'ar hakuri da
zurifin ciki, amma akan ka wulakantamu bamu da hakuri.
Idan da zan zauna nayi maka magana dauka zakayi ni din yar wani ce, tsabar yanga da
sanyi dan ko fada nake yi dariya ake min, wai ban iya fada ba, maganar ma dariyarta ake wai
na cika sanyi da yawa.
Na kuma godewa Allah nace Alhamdulillah.
Ni kaina ina mamakin taya na bari A'a ya cuce ni, dukda wannan halin nawa.
Kwanan mu uku aka sallame mu, domin an samu maganin kuma yana fara sha numfashin
sa ya fara tsayawa dai-dai.
Muna isa naga Abdullahi a tsaye da wani katako, ana rabashi da wani, da sauri na sauka
a mashin din nace.
"Abdul!!"
"Wallahi na kuma ganinka a shashin mu, sai na sauke ma kafarka, kai ko Luluh ka rikewa
hannu, sai na maka tij...."
Kifa mishi mari nayi, cikin takaici, nace.
"are you out of your sense?! Kasan waye shi? Babban yayan su Baba ne?"
Wani irin zuciya yaja sannan ya sake katakon, ya juya.
Riko Baba Mubarak yayi, dan shi kam ya kasa dago kan shi.
"Ba dole ba! An haifi yara masu sak da ruwan shegu, dube gansamemmeyar budurwan da aka
ajiye. Ga wata a ciki, an gama yawon bariki an dawo mana da tsarabar jinya"
"Inji Baba Haruna?"
Murmushi Baba yayi sannan ya rike hannuna muka shiga gida, nayi kuka ranar har na tsani
kaina, na fara ganin laifina wai ban amshi auren Manga ba, amma lokaci ya kure min, muna
shiga muka tarada anoda tension din.
Rufe bakina nayi kuka ya kwace min, slowly. A hankali na zame ma fasa wata irin kuka me
cin zuciya da ruhi?!
WHY?! Our Mommy! Wani kato him try to rapunzel her.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun?! Allah mun tuna ka yafe mana our sins"
Rarrafawa nayi jikin Innarmu na kwanta, ina kuka. Dukkan mu kuka muke, hatta Baba i pity for
him, Biological brother din shi , da yake son ketare iyakar shi, Why?!
Kodan Innarmu Tana da jiki me kyau ne, oho. Dan haka ce ita ta haife mu ba, kuma ya
danganta da yadda kake tafiyar da matarka, basu fahimci haka ba, Baba yana ฦoฦarin tattalin
mu, daga abincin mu har suturan mu me kyau ne.
---
Zaune yake ya tsurawa wayar hannun shi Ido, wata guda kenan but kullum sai ya zubawa
wayar ido yana jiran ganin alert.
Kallon yanayin garin yayi anyi ruwa Marka marka, bazai ce bai da nutsuwa ba, but yana
cikin damuwa, shafa kan shi yayi dan yasan damuwar shi na dakatar da yarinyar nan
Bahaushiya nan ce. A yanzun yana son sanin halin da take ciki ne.
Daga tafiyar ta zuwa yanzun yaje KD Yafi sau goma sha biyar, kuma duk result ษin daya ne,
babu wanda yasan sunan kauyen su hatta makotar su babu wanda yasan sunan kauyen an dai
san daga Bauchi suke, amma babu wani shaidan a Bauchin suke.
Kara wayar tayi, tsaki yaja sannan ya duba, text message ne, budewa yayi yaga
daga bank din shi na Ecowa, wani ajiyar zuciya ya sauke, yana kallon wayar, da lokacin da aka
cire kuษin da bank din da streets din Muhammad Abdul kadir away bank road Bauchi.
Fauce wayar tayi ta zuba mishi ido, sannan ta juyar da kanta