iya
karatu da yaro, malama ance karatun likitanci kika yi meye zan sha cikin ya zube?"
Murmushi nayi sannan nace mata.
"Ke abin murna ne ya same ki? Ai ciki baya hana kome, haka ma D'a baya. Hana kome?!
Sannan ke abin murna ne a gare ki. Baki gan ni har yanzun babu mijin aure ba, kin san ciwon
da nake ji a haƙa toh ki godewa Allah da ni'imar da yayi miki."
Nan nayita mata nasiha, sannan na rakata har kofar gida......
Domin kasancewa a group bin Bahaushiyah kayi min magana ta nan
08130269641......
[7/2, 8:59 PM] BAHAUSHIYAH🥰: BAHAUSHIYAH
𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢
1 Year challenge..
Babi-sha-shida
A cikin shekara guda da muka yi mun mun amshi jarabawarmu hannu bibbiyu, na farko
dai kafewa da baba yayi akan sai nayi karatun boko, na biyu. Fushin mahaifa yana tare da
fushin Allah,
Na uku rashin addu'o'in akan kome da muke bukata, sai rashin niman zabin Allah.
Wadannan sune suka jagoranci wannan matsalar da muka fuskanta, amma Alhamdulillah ban
cika shekaran ba Baba ya faɗa da bakin shi. Duk abinda ya faru damu shine silah....
A cikin wannan yanayin Baba Yawale ya fara wani irin ciwo.
Sosai fa, gashi babu halin kai shi asibiti.
Dole suka sami Baba da maganar jikin shi, Baba na ganin shi yace.
"Wallahi ciwon bata zaman gida bane asibiti zamu kai shi."
Ai kuwa Baba Iro da Baba Habu da Baba Haruna suka ce basu kai shi ba.
"Amma da kun bari an jaraba, tunda." Cikin fada suka rufe Baba har da cewa.
"Bazamu kai shi ko ina ba, sabida mun san me ke samun shi, sharrin da kuka kulla mishi sai
ta koma kanku."
"Ni kuma?! Wallahi bani da wata manufa"
Ya gaya musu araunan. Amma suka rufe idanun su, suka mishi sharrin ai shi yawa Baba
Yawale Yasin me tafiyar rana.
Haka yaje shi da Allah, duk da halin hakuri na Baba sai da ya rike Abin a ranshi wanda
haka ya masifar d'aga mana hankali domin saka abin da yayi a ranshi yaso d'aga masa ciwon
shi.
Sai gashi ba akai Baba Yawale asibiti ba mu mun kai Baba Asibiti.
Dake a toro kwanan shi biyu muka dawo.
Saura wata wata biyu kacal na koma makarantar, wanda na tsananta addu'o'in sosai, har
Azumi muke da Innarmu, dan haka shiri nake sosai.
Domin kuwa na mikawa Allah alamarina, kuma na maida hankali na akan duk motsin yan
uwana da dangina, amma zuciyata tana cike da fansa abinda Aahil yayi min amma dole sai da
wanda zai min jagora zuwa makarantar.
---
Wata goma da yayi baya kasar bai hana shi jin kamar karya dawo ba, duk da kewar da yake
yi na wasu abubuwan, idan ya tuna da Devanah, sai yaji dama ya zauna, idan ya ɗebe
tsamanin da gani na sai yaji ran shi ya b'aci, kamar yayi ta zaman shi a tokyo, tunda ba zai
samu abinda yake da tsananin don gani.
Shigowa Samantha tayi suka gaisa, komawa gefe tayi tana matsar kwallar, ya tako har
gabanta, sannan ya rike hannunta yace.
"Kinga ni dake muna da banbanci, kuma ina da matar da zan aura har anyi mana baiko, don
Allah kiyi hakuri karki raba min hankali gida biyu., Zan yi alfahari idan kika zauna a duniyar ki."
Dan rungume ta yayi sannan ta sake mishi kuka.
Daga nan ya dauki jakar shi ya fito duk wanda suke gaisawa sai da suka ji babu dadi har
ya gama abinda ya kawo shi zai koma.
....... Daren juma'a ya sauka a garin abuja, Mommah da Father sai dai Devanah wacce take ji
kamar zata shige jikin shi dan murna.
Haka suka zo gida ananta hidima dashi...
---
Tabbas ya auri matar da yake so! Sai dai matsalar bai da kwanciyar hankali, domin kuwa
mugun zarginta yake dan tun sau daya da ya tab'a ganinta a kofar wani hotel a garin kaduna,
yaji zuciyarshi kamar zata fado.
Matar shi na aure, me tazo yi a hotel?!
Ko kafin ya same ta har ta shige cikin hotel din haka ya gama dubata, karshe ya gwada
kiranta sai gashi ta dauki kiran, yace.
"Kina ina gani a hanya ina dawowa!"
"Ok Allah ya dawo da kai lafiya.".
Sam Sai yaji bai yarda da ita, domin kuwa, taya gashi ya ganta zata ce, ita tana zaria.
Kamar mahaukaci ya kama hanyar Zaria, abin takaici yana hanyar da zai kai shi zaria road sai
gashi an hada wani husuma wanda taja dole ya hakuri sai da aka bawa damar wucewa.
Lokacin da ya iso ya sameta tana barci. Tun daga nan sai ya soma taka tsantsan da ita,
wanda haka yasa shi mata kule sosai.
Tana zuwa islamiyya, ya hanata zuwa. Duk inda take zuwa indai akwai Maza Aahil ya hanata.
Kamar tayi hauka ta gayawa Iyayen su, akayi ta zama amma fir yaki ya rage takurawar da
yake mata.
Kuma dan tsiya bawai ya daina mugun abinda yake yi bane, shi dai matar shi ce kar ayi da ita.
Haka yayi janyo musu rikici dan yace bazata bikin kawarta ba, aikuwa tsabar kishi kai
Aahil ki kasuwa baya barinta fita sabida kar wani ya ganta yayi mata magana.
Ana haka ta sami ciki, Amma dan wulakanci, sai da ya zubda mata da cikin. Karshe
ya dauketa ya kaita asibiti aka k'ak'aba mata implanin.
Kuma dake masifar bin mata tayi masa yawa, har yau burin shi Husnah, dan duk macen
da ya kwanta da ita yana tashi sai yayi magana yace.
"Dalla dubeta, da kofar shiga kamar rijiya"
Karku yi mamaki hatta matar shi haka yake zama yace mata.
"Zaki nunawa Husnah kyau ne amma dan dad'i kayi sex kamar ka haura gajimare ai Sai
Husnah. Ba irinki da ana tab'aki zaki fara hawaye duk lalaci ya cinye ku. Ita ko yaushe na
bukace ta zata zo, kuma kayi kome da ita bata damu ba sai ke, tur."..
Wannan Iskancin da yake yi mata ne, ya sanya ranar ta haukace mishi, shi kuwa ya rufe ta da
duka.
Wanda ya sanya aka kwantar da ita a asibiti.
---
Satin shi biyu da dawowa daga Tokyo, bai fita ko ina ba, iya kar shi abuja.
Dan haka yau ya hada kayan shi. Devanah tasaka shi a gaba sai kuka take mishi.
Bai kulata ba yana ta kokarin hada kayan shi, dan haka yadda ta mike kawai ta rungume
shi, juyawa yayi dan ya dakatar da ita, sai dai kafin yayi wani abu tasan mishi bakinta a cikin
nashi.
Dake shaidan ya sami mafakar siyasa, aikuwa ya amshi tayin ta. Suna daga tsaye har
sai da suka zube, a gado.
Zuciyarshi da kwakwalwar shi bata buƙatar abinda ke faruwa, amma gangan jikinshi
yana maraba da wannan yanayn, ganin yau Allah ya bata shi bata yi wasa da damar ta, dan
haka duk inda tasan zata iya tab'awa dan ya motsa nan take yi idanunta a rufe, jikin shi ya
amshi sakonta.
Duk yadda yaso tabuka kwatar kanshi, ya gagara, dan haka ya barta ta cigaba da juya
shi don ran ta.
Buɗe idanu yayi ya kalleta yadda take, niman tab'a mishi, Kamfanin sadarwan
shi(🤔🤣😂 Yanzu sai wata tace ikon Allah! Ita mai Dambu ko wani bu sai an sami sunan 🤐
muke tunda baka da burodi amma ai Kanada kamfanin sadarwa)
Caraf ya riko hannunta, yana girgiza mata kai.
"Baka da lafiya ne a Manhood dinka?!"
A shake yace.
"No Ni bana son haka!"
"Na rantse baka isa ba!"
Ta faɗa masa a fusace, tana ƙoƙarin saka hannun ta a cikin wandon shi.
Tureta yayi, ta fadi. Kallon mamaki tayi mishi idonta na kawo ruwa.
Tashi tai ta rufo kofar tare da ɗaukar keyn tasaka a cikin bra dinta.
Zaro Ido yayi cikin b'acin rai ya tashi yace.
"Bani key na, sannan ki fitan min a d'akina!"
.
"Ai na rantse bazan fita, sai ka gaya min baka da lafiya ne?!"
. "Kifita kafin raina ya ɓaci!" Ya buga mata tsawa.
"Na rantse bazan fita ba sai ka gaya min, meye matsalar ka akan mace."
Shiru yayi yana kallonta ran shi na kara fusata, kamar ya mata rashin mutunci, amma ba zai
iya ba. Kuma dan tsiya sai kwaɓe mishi kaya take a gaban shin.
Sunkuyar da kai yayi yana me jin bakin ciki da b'acin rai, ji yaƙe kamar ya kurma ihu, ko zai
samu sauƙin Iskancin da take mishi.
Kuma kan shi na sunkuye tazo, gaban shi. Tare da durkusawa.
Dafa shi tayi, bai san lokacin da idanun shi suka rufe ya tsinka mata mari.
"Dauki kayan ki! Kafin nayi miki abinda bazaki manta dani ba."
Mik'ewa tayi dan jin muryan shi take kamar zata fasa gidan, ta dauki kayan ta ta saka tare da
barin mishi daki, dake ran shi ya b'aci ko shirin bai karasa ba, ya kwanta jikin shi na rawa.
Shi yasa bai cika son ran shi na b'aci ba, domin idan ya fusata jikin shi har wani rawa yaƙe
ina dalili yarinya sai kace ba mace me kunya ba, tazo tana mishi Iskanci da rashin ta ido.
........ Har yamma bai fito ba, sai da Mommah tazo dakin ta zauna tana cewa.
"Don meye ya hadaka da Devanah, kuma ta fito tana kuka."
Shiru yayi mata haka ya tabbatar mata da tabbas bata kyauta mishi ba, dan haka
tashiga bashi hakuri har ya fara ajiyar zuciya, kafin wani lokaci zazzaɓi ya rufe shi.
Kwantar da shi tayi ta fito, zuwa d'akinta ta dauki magani taje ta bashi, sannan ta zauna a
gurin tana shafa kan shi.
Har barci ya dauke shi. Fita tayi daga dakin taro har dakin Devanah, tace.
"Me kika mishi?! Shin an taba so dole ne? Ko ance miki yana sonki ne?! Haka kawai kin hana
min Yaro sakat ayi magana kice ba a sonku. Ku ɗin kuma abin da ya dace ne, rabona da na gan
shi cikin wannan halin kusan shekaru talatin da takwas, yaro ne kunya da da'a, shine zaki zo ki
sanya shi cikin damuwa.
Toh ga zoben ki, dama sabida ni ya amshi tayin ki, idan yayi miki kike can ki kashe kanki, Shi
yasa kullum nake addu'o'in sabida karya ga yarona shaidanun mata irin ki, tabbas na yarda
kece shaidaniyar da zaki raba ni dashi. In ba haka ba me yasa zaki Wani zo kisan shi a cikin
mugun hali Muguwa me mugun nufin, ina ma turoki akayi toh zai koma kanku.
Aure ne ance ba ayi sai me? Kije akwai mazaje da yawa a duniya ki bar min yarona don Allah,
karki kuma samun shi kije ki nemi abokin rayuwarki.
Yarona yana da rayuwa me kyau. Dan haka kar na kuma ganinki anan gidan.."..
Tana gama fad'ar haka ta juya tabar dakin . Tana fita kuwa Devanah ta saka kuka me
matuƙar cin rai, domin bata tsammaci maganarta zai zafaffa haka ba. Meye laifinta.
Dan taso Bature sai tayi laifi, haka tayi ta kuka, har dare bata fita ba, dan tace bazata bar
gidan ba sai ya bar garin.
Mommah kuwa abinda yasa tayi fada gudun kar wani dalili ya b'allo musu tekune, shi
yasa tayi mata iyaka don bazata dauki wannan kasadar ba, yadda ya saba dashi nan awayi
gari wata tayi mata Wuff da d'anta...
....... Washi gari.
Da wuri ya bar Abuja bayan yasha addu'o'in da kariya kar Allah ya raba shi da sharrin
shaidaniyar mace.
Wacce zata iya ruguza mishi tunani.
Tunda ya isa kaduna dake jirgi yabi, Kungiyar su ta CAN ce ta turo aka dauke shi zuwa
Zaria..
Yana isa ya samu an gyra da mishi ofishin sa, inda ya sami karin matsayi zuwa senior
lacture, haka ya kara mishi daraja a idanun mutane dama ..
Sai dai matsalar yaki magana da kowa, sai da Dr Imran shima sabida case dina ne yayi mishi
magana.
Haka ya cinye satin bayi da lokacin kan shi sai na aiki da wasu abubuwan, ranar
asabar ba tare da yayi wata doguwar magana na ya kama hanyar bauchi.
....... Wannan karon ma ya gama yawon shi bamu hadu ba, haka kuma rabon a cire
mishi kudi a cikin account ya jima, jikin shi yayi masifar sanyi, domin ya fara zargin ko anyi
aurena ne, haka ya tattara ya dawo.
Bayan sati biyu yana son zuwa, ga Aahil da yazo mishi da zance, ya samu labarin inda
nake a bauchi.
"Ai abu yayi kyau?!" Ya ce mishi a takaice.
"Gaskiya abokina tun da na rabu da ita, ban kuma samun nutsuwa ba, zanje koda zanyi Sa'a
ta amince min, idan iyayen ta sun sa baki sai na watsa musu ita, kaga cikin sauki na maida ita
karuwa me lasisi!"
Bai d'ago ya kalle shi ba, amma yaji zafin maganar...
"Kuma Abokina wallahi har yau ina rena matan da nake mu'amala dasu, domin Husnah tafi so
kome, Insha Allah nan da Weekend zanje na ganta, na kuma nuna ina sonta, domin mu karasa
wasan"
"Allah ya bada sa'a?!" Dr yace mishi, dan bazai iya magana ba, idan ma yayi tabbas abinda
yake cikin ranshi zai fito. Sai yayi shiru ya cigaba da aikin shi Har Aahil zai fita yace.
"Tana bauchi, can local government din Bauchi wato toro, tana wani dan kauye wai narabi,
zanje a matsayin wakilin makaranta, idan iyayenta basu san da kome ba sai na rufa mata Asiri
mu cigaba daga inda muka tsaya..."
"Hmm" kawai yace mishi. Aahil na fita, yaja tsaki, cike da bakin cikin Iskancin da Aahil yake
kuma ana kallon shi ba atab'a dakatar dashi ba...."
---
Ina zaune, bayan na gama cin abinci wani yaro ya shigo da gudu yana haki yace.
"Malama mau! Wani mutum a waje yana kiranki! Kin ganshi ne yayi kyau Sosai......"
Toh Fa.....
An kusan gama Free pgs...
Gashi an kusan Fara Game?
Insha Allah.....
Page The Game yana zuwa.....
Domin shiga paid group....
08130269641......
[7/2, 9:00 PM] BAHAUSHIYAH🥰: BAHAUSHIYAH
𝘏𝘢𝘵𝘵𝘢𝘳𝘢 𝘠𝘢𝘯 𝘔𝘢𝘵𝘢
Manga!
Babi-sha-bakwai.
D'ago kaina nayi cike da mamaki, yo Allah na tuba tunda na shigo garin narabi, ko namijin
fara bai tab'a zuwa inda nake ba balle namijin mutum.
Kallon Yan uwana nayi naga suma mamaki suke, can sai ga yara a guje, har suna shirin
faduwa.
Sai ihu suke, Malama Kiga bakon da yazo ya bamu kudi mu raba.
"Waye??!"
Na tambaya a takaice,
"Wani me kama da mutanen cikin tv?!"
Dumm kirjina ya buga Dr Aahil?!
Cikina ne ya bada wani irin sauti, kululu. Kamar zan fasa kuka na dauki hijab Dina me hannu,
sannan na kalli Luluh da tayi tsuru tsuru.
Mika mata hannuna nayi ta mike tare da shiga daki ta dauko hijab ɗinta, kallon su Innarmu
nayi sai ga hawaye sharrrr.
Na rasa meke min dad'i.
"Toh kije mana!"
Innarmu tace min.
A hankali nake jan kafana, wata bakar audi 2018 na gani, ji nayi kamar zuciyata zata fito daga
cikin kirjina.
A hankali nake takawa, har na isa gefen motar, kaina a sunkuye.
Ga uban kwalla da yake zuba da mugun gudu, daga Idanuna.
Sauke glass din gefen shi da nake yayi bakin shi dauke da toothpick, yana sarrafa ta. A
bakin shi.
Juyowa yayi tare da zuba min ido.
Buɗe motar yayi sannan yace.
"Beautiful Girl! Zo Nan tunda Auntynki kuka ya zame mata, madubin dubawa ta."
A kagge na d'ago kaina, muka zubawa juna ido. Jikina ne ya dauki rawa, cikin tashin hankali
da firgici nace.
" Dr Bature!"
Rufe bakina nayi jikina yana keerrma, duk sai na diririce. Ƙamar na zura da gudu.
"Shigo mota!"
Yace min a takaice,
Kallon su Baba Haruna nayi , tare da girgiza mishi kai,
Bai kuma min magana ba ya kalle ni, na wani lokaci, sannan yace.
"Baki iya girmama bakon ki bane?!"
Da sauri na koma cikin gidan, na dauki kofin silve na cika mishi ruwa, ajiyewa nayi na tuna
muna da Faro a shago, na dauki. Kular abincin Baba wanda Innarmu tayi dambun Shinkafa.
Na saka a tire, tare da jerawa. Sannan na fito, kicibis nayi da Manga yasha gabana, fauce
tiren yayi sannan ya watsar dashi, sannan ya riko suma na da karfi, yana jana, abinda ya
fiddawa Dr Bature da sauri daga cikin motar shi tare da Luluh, wacce ta saka kuka itama.
"Manga sake Ni?! Manga ka bari idan na sallame shi sai kayi abinda ka saba na tijaranmu."
"Naga shegen da ya isa miki magana, tunda na fahimci ke din baki gane Yaren da nake
miki baki san ke din mallaki.."
Ban san meye ya gani ba, domin Dr ya iso, yana jijjiga, Luluh.
Sake ni yayi da sauri ya bar gurin, cikin wani irin kuka nace.
"Kayi hakuri! Abincin da zan kawo maka ne."
Kusan a tare dashi muka durkusa, yana kallona. Ina share kwallar dake bin idanuna.
Daukar cokali naje yi, muka dauka a tare, da sauri muka kalli juna. Nice na fara janye
idanuna da hannuna.
Sannan na kuma kai hannu zan dauki filet muka dauka a tare.
Kauda kai muka yi a lokaci guda, Luluh tace.
"Laaa! Addarmu yau sai kallon kuda kuke,"
"Ya labari?!"
D'ago jajjayen idanuna nayi, na dan kalle shi, kafe ni yayi da idanu. Sannan ya juyar da
kan shi.
"Ohhhh! Manga ko? Kuma."
"Husnah! Wannan shirmen fa?!" Kin tsaya shiririta." Inji Baba,
D'agowa Dr yayi cikin nutsuwa ya gaida Baba, sannan ya mike da Luluh a kafad'arshi, ya
koma gurin motar shi.
"Waye shi?!*?"
"Malamin mune?!" Na bashi amsa a takaice,
Shiru yayi ina bin bayan shi,
"Toh taya aka yi, abinci ya zube a hannunki."
"Baba Manga ne?!"
. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.
"Ki nima mishi, abinda zai ci"
Shago naje na dauki cus-cus, tare da wasu kayan aiki na shiga nayi mishi kunun cus-cus,
ɗin sannan na juye mishi a karamin bowl.
Ina zuwa na samu yana hira da luluh kuma kamar bankad'e mishi kome luluh,.
"Sauko ki wuce idan na shigo gidan sai fasa bakinki, tunda kin koyi gulma"
Zaro Ido tayi irinta yara idan sunji za a zane su ta kalle shi zata yi kuka tace.
"Bako nice na gaya maka Addarmu kullum sai tayi kuka?! Ince kai ne kake tambaya na, suwaye
a can. Ni kuma na gaya maka sun tsanemu"
Dariya ya saka tare da sumbatar goshina yarinyar, juyawa yayi Bayan motar shi ya dauko
wani katon kwali ya mika mata, yace.
"Daga yau ni ba bako bane! Ni Uncle Ba ne, kuma ki cigaba da min aikina ga chocolat, sannan
Allah ya kai mu zan zo miki, kawo kunnenki na gaya miki kin san muna da yan sa'ido."
. Magana suka yi tare da fashewa da dariya har da tafawa.
"Zoki wuce ko na sab'a miki"
"Ya Haka Malama! Ko kina kishi da kawata ce? "
Tsuke fuska nayi cikin alamun da gaske nake, da sauri ta fito daga motar na sami keyarta na
maketa.
"Sai nazo zaki gaya min yaushe kika zama haka, mara jin magana, ai sai."
Da gudu ta shiga gida tana dariya, dan sun manna min hauka shi da ita.
Saka mishi abincin nayi ina b'ata rai, ina ajiyewa. Meemah tana isowa gurin.
"Addarmu! Inji Baba wai ki shigo dashi dakin zaure."
"Toh! Zaka iya biyo ni."
"Inda baki yi tsammani ba, zan iya binki har can" kallon bakin shi da yayi maganar nayi, cire
saman suit din shi yayi sannan ya bar na ciki fari me dogon hannu.
Lokacin da muka shiga gidan, na buɗe mishi dakin su Mubarak, dan addu'a nake Allah
yasa a tsabtatace ne, muna shiga naji har da room fresh, suka saka,
Ajiye abincin nayi zan juya na ganshi jingine da kofa, ya hard'e hannunshi a kirjinshi.
Sunkuyar da kai nayi.
"Am sorry! Ban san yadda aka yi ba nayita kwasar kudin ka, and dashi nayi jinyar Babana sai
kuma"
Na fashe da kuka, na cigaba da bashi labarin abinda ya faru. Takowa yayi gabana.
Ya mika min hanky, sannan yace.
"Saura sati nawa ki koma school?! Wannan lokacin na abu biyu ne! First Class! Da kuma, zaki
iya ko kuma na juya abuna."
Kura mishi ido nayi ganin, shima kallona yake, amna ba abinda nake ganin ya faɗa bane,
domin idanunshi wani yare na daban yake gaya min, zare ido na nayi cikin nashi, sannan nace.
"Bani da wannan halin!"
"You can do! Because Aahil is susceptibility" ya faɗa min.
Girgiza kai nayi murna na rawa nace.
"Hmmm! Am not strong enough!"
"Inji waye? Zaki iya"
"Ok kaci abincinka nagode!"
Na koma gefen shi na tsaya, juye da fuskar shi yayi,. Ya zuba min ido,
Jin kai fin idanun shi nayi har cikin zuciyata, takurawa nayi a gefe, jikina na rawa.
"Relax! Ni bada mugun nufi nazo gare ki ba! Dan haka jikinki ya daina rawa."
Jin shi nake kawai, yana matsa min ina bud'e kofar, carak naji ya riko hannuna.
A firgice na kalle shi kamar zan sake mishi kuka nace.
"Dr Haramun ne! Tab'a macen da ba muharramin ka ba, and Idan kayi dubi muna cikin addinin
mabanbanta ne! Don Allah idan kana son na cigaba da ganin girman ka, stop."
A hankali ya janye hannunsa, a wuyar hannun na.
Sannan na fita, yadda na fitan haka na dawo na same shi da Littafin Ahlari a hannun shi,
ajiyewa yayi, zai dauki Alkur'an ni nayi maza na dauka ina me tsare shi da ido.
"Kur'an ba gama garin books bane irinsu, Attarura, Injila,Zabure, tare da sufi Ibrahim. Littafi
ne mai tsarki da daraja, dan haka Please karka nayi saurin tab'awa, tunda kai baka da tsarki."
Gyad'a min kai yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Toh am sorry for the!"
"No ni ba fushi nayi ba" na faɗa mishi a takaice, ina tattara duk wani littafi me daraja a gurin,
shima durkusawa yayi yana kallon yadda nake, cizon bakina sannan, kuma na lashe bakin,
murmushi yayi sannan yace.
"Ina son tafiya kuma kinki muyi magana"
D'ago kai nayi sannan na kalle inda na ajiye abinci da ruwa bai tab'a ba.
"Taya zan saurari bakon da bazai ci abu daga hannuna ba?!". Na tambaye shi ina kallon
fuskarshi,
Juyar da kan shi yayi zuwa gurin abincin sannan yace.
"Ban iya cin abincin ni daya bane!"
Kamar nace mishi toh ai sai ka zauna na baka, tunda haka ka zaɓa.
Sai na share shi nace..
"Hmm"
Zama yayi sannan ya koma kan abincin ya fara addu'o'in, juyawa nayi cikin jin haushi nace.
"Stop that praying, in ba zaka ci ba ka barshi dan na fara gajiya da abinda kake min, yau daya
ka addabe ni, ka hanani."
Ayya tashi yayi daga kan abinci.
"Ko zaki min magana da su baba da Mama zan wuce yau."
Mik'ewa nayi na isa gaban shi.
"But the food?!"
Girgiza min kai yayi, cikin murmushi.
"Am ok!"
Shiru nayi ina tsaye a gaban shi, na rasa gane kai na, me yasa nayi mishi magana ai da na
barshi yayi yadda yake so.
Cikin shashekar kuka nace.
"Kayi hakuri! Kaci koda one spoon ne"
Zuwa nayi gurin abincin na diba jikina na rawa na kawo mishi.
"Kayi hakuri, duk addu'o'in da yayi maka kayi, Domin addinin mu yana girmama bako."
Amsa yayi ya zauna a hankali, sannan ya fara ci. Kallona yayi sannan yace.
"Kece kika dafa ko Mama?!"
"Kaci abincin! Sunnar ce babba idan ana cin abinci ba ayi magana, gudun kar a kware." Na
gaya mishi,
Sai da yaci sosai, sannan ya ajiye cokalin, mik'ewa yayi.
"Ka zauna! Idan kasha ruwa sai ka mike".
Komawa yayi, tare da zama, yana kallon gefen da hisnul musulin yake ..
"Karba ka sha"
Garin karba hannun mu ya hadu, kallon juna muka yi, sannan na janye nawa, ya sha ruwan.
Tashi nayi sannan nace.
"Tashi muje ku gaisa, dan nasan yau zaka koma."
Na riga shi fita, dan haka na samu tsakar gidan a gyare tass, ce mishi nayi ya shigo.
A hankali ya shigo da cewa.
"Gafaranku mutanen gida."
Kallon Juna Maryam da Mubarak suka yi, Innarmu ce tace.
"Lalle maraba, Barka da zuwa."
Da Hausar shi wacce kana ji kasan kabila ne shi yace.
"Yawwa! Mama mun ishe ku lafiya"
. murmushi Innarmu tayi sannan tace.
"Lafiya lau! Ya mutanen gidan!"
"Sai godiyan me ceto!"
Da sauri Luluh ta fito tare da hayewa jikin shi tana cewa.
"Uncle b! Kaga Addarmu sai da ta ja min kunnena! Wai sai ta yanka ni tabawa Dog da pig nama
na Tunda bana ji"
Murmushi yayi sannan yace.
"Karki damu! Sai na mata bulala, nima"
Sannan ya juya ga Innarmu yace.
"Jikin Babanmu! Ubangiji ya kawo mishi Salama a cikin lafiyar shi"
"Amin! Jiki da sauki!"
Fitowa Baba yayi suka gaisa, sosai. Sannan yace.
"Nan da Sati biyu Husnah zata dawo makaranta, shine nazo naji ko zaku barta ta koma! Dan ni
na zata ko tayi aure ne!"
Gyara zama Baba yayi sannan ya fara da cewa.
"Nayi bakin cikin da tayi rashin jarabar ta na karshe, toh Amma kasan Al'amarin Ubangiji, gashi
mijin bai zo ba, amma muna nan muna mata addu'a, Allah ya kawo na gari! Toh badan kazo ba
bana jin zan iya barinta ta koma jami'a, sabida a cikin watan nan naji yadda yaran suke abinda
bai dace ba! Kuma kaga mace ce, su nake na kaita gidan mijinta cikin kwanciyar hankali. Amma
tunda kazo, tabbas zata koma. Amma don Allah ka tayani tsare kimarta. Mace ce dan
tsautsayin kadan zai iya jefa ta cikin damuwa, ba ita ba har mu iyayenta. Don Allah na baka
amanarta. Daga ganin ka Na yarda da kai don Allah karka zubda yardan da take zagaye da
zuciyata da idanuna!"
Jikin Dr ne yayi mugun sanyi, zufa na karyo mishi, tare da sunkuyar da kai yace.
"Baba! Nayi maka alkawarin ni da kaina zan dawo da ita idan aka yi hutu"
A gaban iyayena yayi musu alkawarin rike amanar da aka bashi, sannan da zai tafi muka taki
shi yana dauke da Luluh,.
Yana isa gurin Motar sai ga Manga.
"Kai Dan iskan kauye!"
Ya kira Manga, jikin shi na rawa ya isa gaban shi, buɗe boot yayi sannan ya ce mishi.
"Sauke min wannan kayan dukka, ka kai cikin gidan su Husnah, sannan kazo ina son ganinka!"
Da sauri ya shiga dauka yana kaiwa yana dawowa, bugun Shinkafar, rabin bugun wake,
manja galan da mangyad'a, kwalin kifi, kwalin taliya da makaroni, sai katan na manyan
gwangwanin peak na gari me guda shida, 7000g da na milo, sai kwalin sigar me iyali, sai
Indomitable.
Fitowa Baba yayi yace.
"Yaro meye kake haka?!"
"Baba! Albarka nake nima! Ka sanya min kawai."
"Allah yayi maka albarka, ya jibanci al'amuran ka duniya da lahira."
Baba