Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuwa ga wayar ganin cire kudi aka yi ta wurga mishi wayar. Sannan ta shiga balle botirin rigarta. "Karki soma?!" Yace mata, daukar wayar yayi, ya barta a gurin. Zata sanya shi damuwa. Ko waye ya gaya mata shi haka yake yau kwanan ta biyu da zuwa dan an kusan yi musu engagement dashi , shine aka turo ta su shirya kan su dan tace idan bashi ba sai rijiya. Ba tare da yaji komai ba, ya barta a gurin yazo inda zai samu nutsuwa, tabbas indai yau ta cire kuษ—in toh tana Bauchi! Toh taya zai sameta, shi babban damuwar shi ciwon mahaifinta, a wani hali suke ciki. Lumshe idanun shi yayi, yana kuma hango, ranar da zata bar makarantar ko waiwayar in yake bata yi ba, dukda kuwa taso ya kalleta lokacin da ya shigo ajin amma shima fir yaki, dukar iska yayi sannan yace. "Am sorry!" Zuba mishi hannu tayi a kafad'arshi tace mishi. "Hmm! Thanks Har kasan nazo gurinka ne" Ture hannun ta yayi cikin jin haushi yace. "Devanah! Bana gaya miki gaskiya ba, nifa bana sonki?!" Zaro ido tayi tana kallon bakin shi wanda yake kewaye da suma, sai dan kwata miliyan din da ya kamata fuskarshi, had'iye yawu tayi. Cikin damuwa tace.. "Wai meye na tsare maka ne da baka sona." Hade fuska yayi sannan yace. "Kawai bana jinki ne a raina!" Kallon shi tai, sannan ta mike tare da barin gurin shi, ta koma ciki tana hada kayanta. --- Sunkuyar da kai nayi, ina me cigaba da duba pose Dina, ganin Inuwar mutum nayi akaina, ya zuba min jajjayen idanun shi. D'agowa nayi cikin rashin tsoro nace.. "Akwai abinda kake bukata Manga?!" Jingina yayi da bango sannan yace. "Nazo ne, dan na gaya miki yau da dare zan zo ki bani abinda kike bawa yan jami'ar da kika yi aka koro ki?!" Murmushi nayi, sannan na kalle shi sama da kasa. Na dan lashe bakina, sannan nace. "Eh toh! Su din suna da aji da tsafta taya zan hada jikina da naka kazami irinka dubi hakoranka, kai dube ka ga?! A dauri nashi ko a b'ata igiya. Salin alin kafita kafin na baka mamaki" Tawowa kaina nayi dama ina cike da abinda aka wa Innarmu, ban san lokacin da na dauki tabarya na make dan banza ba ya dai fasa ihu tare da ficcewa da gudu yana ihu. Hmmm! Rayuwa kenan, amadadin aga laifin shi sai aka kuma ga laifina, wai na saba da karuwanci shine nazo na kama shi da karfin Bala'i, garin ya kwaci kanshi ya buge. An aka yita yamudidi dani, har da iyayena, abin dariya duk kuma danginmu ne ake wannan hayaniyar. ...... Kwana biyu zan mai da Bana Asibiti, kamar bazan tafi ba, nace Mubarak yaje yace a'a dole na shirya muka tafi da Innarmu, Aka bar Meemah da Luluh. Kafin mu isa asibitin muka biya banki na cire kuษ—in, anan ne naga kallon rashin yarda daga iyayena, amma basu min magana ba, har muka tafi asibitin nan na gama kome, amma nasamu sami ganin likitan ba, dole sai wata sati. Haka muka dawo bayan nayi mana cefane, yau ma mun dawo mun sami case. Abdullahi da Mubarak sun daki Manga, rikicin da aka rinkayi har muka dawo, mu dai bamu ce komai ba, har zamu shige Baba ya tsaya a gaban Yan uwan shi. Murmushi yayi sannan yace. "Ban san meye Iyalina suke fuskartan farmaki ba daga gareku, Ban san me yasa suka rasa kariya daga gare ku ba? Wallahi bazan tab'a cutar daku ba sabanin yadda kuke cutar dani karku manta Allah yana kallon ku, Haruna Matana Mai sunan Malam Husnah da Maryam! Allah zai bi min hakkina." Yana gama fad'ar haka ya juya muka shiga gida, a ranar Mubarak yaje ya nemo masu sanya kofa a Gumau, kuma aka zo aka saka, bayan mun cire wasu kudin aka shata inda za a kara mana tsayin katangar mu, tare da rufe kofar cikin gida. Hmmmm mutanen yau kabar su Yadda Allah yayi su, sabida bazasu fahimci kome ba, sai tarin jahilci, sabida rashin sanin hakkin Allah,...... Karku manta Wannan book kuษ—i ne. Idan ta bank ne=200 Idan kuma katin mtn=300 Gama su bukatar VIP=500 bank account Kuma katin mtn ne=600 Acct: 0472282105 GTBNK Ramlat Abdul Rahman Manga Idan ka biya ka sanar dani ta wannan number08130269641๐Ÿ‘ˆ๐Ÿป Thanks........ Idan kuma kana son Inuwar Gajimare! Kayi min magana ta wannan number! Shima. [7/2, 8:53 PM] BAHAUSHIYAH๐Ÿฅฐ: BAHAUSHIYA ๐˜๐˜ข๐˜ต๐˜ต๐˜ข๐˜ณ๐˜ข ๐˜ ๐˜ข๐˜ฏ ๐˜”๐˜ข๐˜ต๐˜ข patience. Babi-goma Patience is more precious than intelligence. Tabbas na fadi haka ne domin sanin cewa yan uwan Baba basu san me ake kira da Haka ba, a kalubalen mu, hakuri itace ta farko. Da muka fara yi, domin kuwa badan mun yi hakuri ba toh tabbas bakin ciki, ya ishemu riga da wando. Ban da dangin Innarmu bamu yin hulษ—a da kowa asalima kamar tsoron mu ake yi, idan naga halin da muke ciki, sai na godewa Allah, b'cos mun tsallake zaman jahilci. Kallon Atm ษ—in Dr Bature nake, ina shafa code din bayan, abinda ya fara zuwa raina shine ya isa haka cire mishi kudin da nake sabida domin. Poverty waits at the gates of idleness. Dole sai ka nima zaka samu, kuma shima ai nona yayi ya tara, dan haka muka zauna da Mubarak da Baba. Na shiga musu karya nace.. "Sauran kudin da muka dawo da shi daga asibiti, shine naje na bude account, ranar da muka fara zuwa asibitin bauchi da Baba, toh yanzun akwai sauran kudin. Shine nake tunanin ko zamu buษ—e injin nikar gari, toh sai an tafi." Kallona Baba yayi cikin murmushi, sannan yace. "Kina ganin zasu barmu, nufi so samu ne?!" "Baba hakuri yafi hankali daraja da tafiyar bazata, duk abinda zasu yi Allah yana tare damu, Ina tare da Addarmu!" Murmushi Baba yayi sannan yace.. "Allah yayi muku albarka," ya faษ—a a hankali. "Amin Baba" muka ce dukkan mu, Bayan kwana biyu muka je har Bauchi muka sayo injin, tare da Muba, a kofar Gombe. Sannan muka dauko wali tun daga Bauchi yazo Narabi ya haษ—a mana kome. Mun biya shi kudin shi, sannan muka saka aka kafa mana, rumfa a jikin gidanmu tare da yin dakin da injin din zai zauna, Kun san me yasa nakira hakuri a maganar farko! Sabida idan bakai hakuri ba zumunci zai iya lalacewa. The next day muna tashi sallar asuba, Baba dasu Muba zai su Masallaci suka samu an balle dakin injin din an sace, babu komai a cikin shagon, da sauri Ghaddafi ya juyo zai gaya mana, Abdullahi ya rike hannunsa, tare da nuna mishi Baba ya wuce, haka suka tafi sallah, bayan sun dawo ina wankewa Lu'lu'a idanu, suka shigo, na gaida Baba Su Muba suka gaida ni ba tare da sun kalle ni ba, amma naga so sad a fuskarsu. Murmushi Baba yayi sannan yace. "Nawa kika sayi injin nan?!" "Dubu dari da hamsin?! Dan na gasa ne, sai service da akayi dubu sha biyar, da kudin kawowa dubu biyar, kudin me aiki dube biyar. "Waye ya baki kudin?!" Take cikina ya hautsina bakina na rawa na kasa bashi amsa yayi murmushi yace. "Allah! Ko?" Na gyad'a kai na, "idan ya karb'a me zaki ce" "Alhamdulillah nagode mishi da ni'imar da yayi min" "Toh ki leka waje! Bayan haka kar naji kinyi wani magana Allah yana tare damu" Ban iya fita ba, Maryam da Innarmu suka leka, da kuka Maryam ta dawo, cikin gida. An cika a kofar gidan sai surutu akeyi, ni kam bance kome ba, na girgiza. Dan sai da nayi zazzaษ“i. Taya zan kuma zuwa na ciro kudin bayan nasan duk inda yake yana ganin alert. Kuma comfirm ina amfani da kuษ—in. Amma babu karya na kwana ina kuka, domin sai da Meemah ta zauna muka yi kukan tare sannan muka kwanta. Kirana Baba yayi sannan yace. "Kudin sun kare ko?!" Girgiza kai nayi alamun akwai, amma bazasu wuce na rufwa kai asiri ba. "Toh indai akwai ki kuma buษ—e shagon koda kuwa kayan masarufi ne!" Jinjina kai nayi, sannan nace. "Shikenan!" Kwana goma tsakani, muka gyara shagon, sannan muka tafi har bauchi muka kuma yin sayayyar kayan masarufi, duk abinda za a nima hatta katin waya, da abin canjin waya muka sayo babban generator, da wata karamar deep freeze. Wannan karon na cire kudi me mugun yawa, zuciyata har bugawa take, tare da Addu'ar Allah yasa daga wannan bazan kuma tab'a mishi dukiyar shi ba. Dama masu azancin magana sunce practice make Perfect. Doing something reapeadily is the Only way to be become good at it. Dan haka nasaka a raina, Allah zai bamu nasara. Dan kuwa shi ba Azzalumin sarki bane. Babban J5 aka kawo mu, inda muka samu masallacin kofar gidan mu, cike da maza baba yana tsaye. Kallon mu yayi lokacin da ake sauke kayan, sannan ya kuma lalle su. "Wallahi! Na rantse da Allah, idan aka kuma fasa min shago sai na bawa kowa Mamaki, anyi na farko. Kar a kuma." Yadda yayi maganar ya basu tsoro dan sun san shi mutum ne mai mugun hakuri, kuma idan aka kure shi toh. Barin su yayi yazo yana son taya mu sauke kayan Amma bai da lafiyan ko nace karfin hakan. Kallon mu Baba Yawale yayi cikin jin haushi yana kumfar baki yace. "Wallahi sai naga bayan shi tun." "Kafin kaga bayan shi ka fara duba Alamarin yaron nan Kamalu ashe mu, a nan muna tacewa yana yar sana'a a birnin ashe yaron nan karatun nasara yake yi, gashi mun dauki Kuluwa mun bashi." A zabure yayi kan Baba Iro, yana zare idanu. "Toh wallahi yau zai sako min Y'ata." Fuya- fuya, ya nufi gidan surukinsa, dan zubda kima yaje ya dauko yar shi, da tsohon ciki, muna gyara shagon bayan mun kai freezen ciki, muna saka kome a cikin mazaunin sa. Suka zo zasu wuce, abinka da mai ciki ta hango biscuit aikuwa ta tsaya ta ciro kudinta tace. "Addarmu, bani biskon nan?! Shi Kamalu yake sayo min idan zai zo daga birni " Na diba a bakin leda na saka mata, nace. "Tsohuwa da alamun nice zan amshi haihuwar." "Kan jakar, buhun kaniyarki me tsaba" Baba Yawale ya danna mata ashar, yazo ya fisge ledar ya wurga min, sannan ya shiga balbale ni da masifa. "Wallahi ni sai naci! Dan ji nake kaman zan mutu, kuma kasan Kamalu ba mutuncine da shi ba, domin ya ce min yana irin karatun masu kaki ne, wallahi idan ka bari muka mutu, toh kaf danginmu sai ya alburushe mu." Yazo ta amshi ledar tace . "Nagode sosai." Hmmmm. Su suka sani, mu kam damuwar mu ta ishe mu, bazamu ari damuwar kowa ba. A tsorace muka shirya kayan mu, amma da dare yayi muka kwashe aka mai da cikin gida. Wannan karon babu matsalar kome, amma sai dai babu ko kare da yake zuwa sanyan kome sakamakon ce musu da akayi ai Zina nake zuwa yi a birnin, da kudin muke wannan facakan, ranar da naji haka. Yankan jiki nayi na suma, bawai dan naji haushin kalmar bane, a'a sai dan tension yayi min yawa at my age, bani raba dayan biyu jini na ya haura sama da 360, A karon farko da nayi wani katob'ara nace. "Me yasa ma ban mutu ba?!" Buge min baฦ™i Innarmu tayi, tare da zuba min rankwashi tace. "Mu da aka abin sabida mu, muce me?! Ki godewa Allah da ya jarabce ki ta wannan hanyar, sai ki gode mishi." Nasiha tayi min sosai, sannan nace mata. "Innarmu kiyita mana addu'o'in, ina bukatar addu'o'in ki, ba iya Ni ba hatta yan uwana." Na fada cikin kuka da gajiyawar halin rayuwa. --- Bature (POV) Tsaye yake a cikin ofishin sa, ya zubawa window idanu, har yanzun dai yana nazarin makomar kwanakin da aka bashi, a gida akan Devanah! Allah ya gani bayi son Devanah. Amma karfi da yaji ta makalewa Rayuwar shi. Kara wayar shi tayi ya kalla sannan ya kauda kai, sake jin kara yayi, sai ya share. Jin kara na uku yasa shi dubawa. Dubu dari biyu da hamsin sau biyu, aka cire. "Miss Manga!" Ya ambata cikin cool Voice ษ—in shi, lumshe idanun shi yayi, yaga Balance din cikin account ษ—in ko girgiza basu yi ba, dan yasan each Sunday ana turo mishi 1.6m , kudin service din da yayi a ranar, wai ma dan bai da mata ne, da yana dashi tabbas da yafi haka samun kuษ—i. "Ina take a Bauchi?!" Wannan itace tambayar da bai da amsar ta. Tattaro kayan shi yayi sannan ya saka kai zai fita, a bakin kofa suka hadu da Dr Aahil, mika mishi hannu yayi suka gaisa. "Dr BYC! Kana biyu ina ka shiga ne?! Ko nazo bana samun ka?!" Murmushi yayi sannan yace. "Ina dab da barin kasar ne! Shi yasa bani zama sosai kuma ina son na gama da daliban master din nan!" Wucewar wata daliba yar sabon shekara ya sanya shi juyawa yana binta da kallo musamman yadda ta Cancare cikin riga da wando, ga earpie da key mota a hannunta. "Dr A'A! Har yau baka cire ranka akan yan mata ba, bayan kana da mata a gida." Cikin iya shege ya kwashe da dariya yace. "Ka san Allah ina son na kuma haษ—ewa da wancan Yarinyar, amma bana son mu same matsala irinta Miss Manga." Tab'e baki Dr Bature yayi sannan yace. "Ai yayi kyau!" Daga haka ya mika mishi hannu, suka kara gaisawa ya wuce, abin shi. --- Yana tsayawa da motar shi sai da zuciyar shi ta buga, nakine ya sanya shi haka ba, sai hango motar Devanah! Fitowa yayi a matuฦ™ar jin haushi, ya shiga gidan ganin key din kofar shi a kasa an fasa, turus yayi sakamakon ganin kowa da kowa har da yan church din shi. Mik'ewa suka yi, aka fara rabtab'o addu'o'in, yana tsakiyar su, sai addu'a suke mishi yana cewa. "Amin?! Suna gamawa Mommah ta mika mishi dan karamin a kwati me dauke da zobe, kallon su yayi sannan ya girgiza kai yace. "As i told do you! Nifa bani sonki! Kiyi hakuri kije ki auri Joel! Na rantse bana jin kome akanki bana jin kaunarki!" A gaban kowa ya gaya mata baya kaunar ta, bakinta na rawa take nuna akan ta, tare da kallon kowa na gurin hawaye na zuba mata da mugun gudu tace. "Gaya min! Meye na rasa da baka sona? Meye na rasa kyau, ilimi, waye, ko nasaba, dukiya ko me?!" Girgiza mata kai yayi cikin damuwa yace. "Kinga irinta ko?! Baki rasa kome ba, amma ni zuciyata babu sonki ne?!" "Amma ita Bahaushiyar fa?!" "Kinga karki kawo mana shirme mana. Ni babu wata yar Hausawar da nake kulawa zargin kine kawai." Kwace wayar shi tayi ta gama dube dube bata ga kome ba, sai shaidar ciran kuษ—i, kuka ta fasa me tsuma rai da ruhi. Riko hannun shi tayi cikin tashin hankali tace. "Da sonka na girma! Dashi na tashi a raina, na rantse maka da Yesu bani da mafarki sama da na same ka, Idan baka da lafiya ne, am agree zan zauna da kai haka! But don't reject my love, na rantse zan zauna na jiraka har ranar da zaka fara sona!" Ya zai fahimtar da Devanah! Ta gane so ba a mishi tilis, amma halin da take ciki ya karya masa zuciya. Fadawa jikinshi tayi, yana jin kukanta, na cika mishi kunne. Yaki yake da zuciyar shi. Mikawa Mommah hannu yayi, ta sanya mishi zobe ya riko hannun shi yace. "Zan zauna dake! But ku zama sheda duk ranar da na sami wacce nake so zan aureta ne ya zama dolenki you be patience, da abinda zan yi idan na sami wacce nake so." "All is fair in love nd War" Ta faษ—a a hankali. Shi kuma ya bata amsa da cewa. "Things that are done in love or war can often be excused." D'ago kai tayi tana kallon shi, bayan ta amshi zobenta zata da mishi tace. "Karka ga laifina! Loveless life is a living death. Dan haka dan na haukace akan son ka ko na mutu bani da kaico" Murmushi yayi bayan ya rungume ta, yana me jin zafi da ciwo a ranshi yace. "Without affection, life is difficult, karki zurfafa dayawa!" "Indai bazaka wulakanta ni ba, zan zauna da kai har karshen rayuwa ta." Abinda zuciyarshi yace mishi. ๐——๐—ฒ๐˜ƒ๐—ฎ๐—ป๐—ฎ ๐—ธ๐—ถ๐—ป๐—ฎ ๐—ฐ๐—ถ๐—ธ๐—ถ๐—ป ๐—น๐—ผ๐˜ƒ๐—ฒ ๐—ฏ๐—น๐—ถ๐—ป๐—ฑ, ๐˜€๐—ต๐—ถ ๐˜†๐—ฎ๐˜€๐—ฎ ๐—ฏ๐—ฎ๐—ธ๐—ถ ๐—ด๐—ฎ๐—ป๐—ถ๐—ป ๐—ฏ๐—ฎ๐—ธ๐—ถ๐—ป๐—ฎ ๐—ฑ๐—ฎ๐—ป ๐—ป๐—ฎ๐—ฐ๐—ฒ ๐—ฏ๐—ฎ๐—ป๐—ถ ๐˜€๐—ผ๐—ป๐—ธ๐—ถ! Nan aka rufa musu kai da addu'a bayan baikon su. --- Husnah (POV) Sam bana son fita ko ina koda shagon ne, duk da yanzun akan zo a sayi irin su klin may soap, sugar, da dai sauran su, amma ban tab'a ganin mugayen mutane irin dangin Babanmu ba, kome da gafara suke zuwa su dauka, kuma hakan bamu tsira ba. ....... Second Challenging.... Loading ๐ŸŒบ [7/2, 8:54 PM] BAHAUSHIYAH๐Ÿฅฐ: BAHAUSHIYA ๐˜๐˜ข๐˜ต๐˜ต๐˜ข๐˜ณ๐˜ข ๐˜ ๐˜ข๐˜ฏ ๐˜”๐˜ข๐˜ต๐˜ข Second Challenging. Babi-sha-daya Ban san me ya faru ba, kawai sai ga Mubarak ya shigo da Baba rike dashi, fitowa muka yi dukkan mu. Innarmu tace. "Lafiya Mubarak" Ganin Abdullahi muka yi ya zari wani itace ya fita da gudu, babu dan kwali na bi bayan shi, wallahi yaron nan baya ji. Yana zuwa ya sami kafadar Baba Haruna ya zabga mishi b'arin Itacen nan. Cak na tsaya ina kallon ikon Allah, haukacewa yayi baki daya yayi ta muka musu itace. Kusan shekarun shi nawa, sha takwas! Amma dake yana da tsayi ya mike zaka rantse yafi mu shekaru. Zuwa nayi na zabga mishi mari, cikin ciwon rai dan ban san me zan iya yi mishi after all, Yana huci yace. "kai Tsohon banza maza sake min kanwa! Saketa kafin na ci..." Jijjiga shi nayi cikin gigita nace. "What?!" "Wannan tsohon banzan wai dan ya renawa mutane hankali, wai auren meemah yazo yi, wallahi idan bai saketa ba, Allah sai na kashe banz...." Rufe mishi baki nayi. Ina kallon su, cikin nuna dagaske haka ne, dattijon yace. "Bashi na Haruna yaci. Na kusan dubu talatin, shine ya bani auren diyar wan shi." Akan 30k an wargaza future din kanwarmu. Juyawa nayi na koma cikin gida, birkita kayana nayi na ciro dubu talatin cif na kawo ishi, nace. "Bani? Sakinta!" Na mika mishi hannu, cikin duniyanci yace. "Ko kina da inda zaki kaini tsohuwar kilaki?!" "Abdul! Ji min da tsohon nan ba shi ba hatta wanda ya tsaya mishi ka karya min kafafuwan shi." Allah kenan, ganin yadda Abdul ya kinkimi itace zai kai mishi, aikuwa yace. "Toh mara kunya ko girman tsofa na baki gani ba, toh na saketa daya." "Ina ukun zaka yi tsohon banza!" A take dai sai da muka raba auren abinda babu kyau, Allah mun tuba. Baba Haruna kan ai shiga dashi cikin gida aka yi, tare da nima mishi maganin tsamin jiki. Koda muka shiga cikin gidan, rufe Abdul Innarmu tayi da duka, tana yi tana kuka. Ba shi daya ba, nima bata kyale ni ba. Mun zata case din ya kare washi gari sai ga, yan sanda. Ban san yadda zan fada muku halin da muke ciki ba, amma maganar gaskiya, muna cikin bakin ciki mara iyaka, muna ganin tasku da jarabta, bamu rasa kome ba, sai kwanciyar hankali da nutsuwa. An tafi da Abdul, wani abin bakin ciki, shine ba ajiye shi a Toro ko Magama gumau, ba sai aka kawo shi bauchi. Sannan aka ki gaya mana inda yake, tsabar zalinci. Koda muka zo bauchi mun fara bin kananun ofishin yan sanda. A ranar a cikin garin bauchi muka wuni. Har dare babu labarin inda yake, sai da muka gama yawo. Dakyar muka sami labarin inda yake, an kai shi can Dass. A daren muka dauki shatar mota har Dass, acan suka ce baya nan. An kai shi wani karamin kauyen dass, wato Zan. Abinda bamu sani ba, tsohon da ya auri Maryam ne ya biya kudi aka kawo Abdul gurin, mun same shi an mishi mugun duka, ko daga kai ba ya iya yi. Kuka rahama ce, dan haka basu bamu shi ba sai da muka yi Yaren hannu da aljuhu. Aikuwa suka sake mana shi, a daren muka wuce dashi asibitin bauchi, aka bashi magani. Muka kuma biyan kudin mota aka dawo damu gida, Muna isowa karfe biyar na asuba. Gida muka shiga dashi, Mubarak da Driven da ya kawo mu, suka wuce masallaci. Anan ma sai da Su Baba Yawale suka musu wani diban albarkan. Haka Driven ya tafi yana mamakin wasu dangin al'ajabi. Wato abinda na fahimta a rayuwar Bahaushe, shine idan yana bariki. Shi na kowa ne, kuma idan da zasu haษ—u da dan garin su, toh tabbas sun zama yan uwa, wannan bawai dan labarina nake fada ba, sai dai nasan cewa akwai yan arewa da suke kudancin Najeriya, sun san da haka. Amma a cikin garin shi toh fa, idan bai kai zuciya nisa ba. Bakin ciki ya ishe shi. Domin zaman mu a garin Kaduna, bamu san tashin hankali ba, haka ma a toro bamu san me ake kira hayaniya ba. Amma dawowar mu, mahaifar mu, yau ta kare mana. Domin ido da ido ake mana hassada, ga gaskiya jahilci da kauyanci ya rufewa mutane ido. Duk wata hanyar da aka san zamu karu toshe shi ake. Idan nace da Ciwo a rayuwata ban yi karya ba, dan na zata a Novel ko a film ake labarin destiny, sai yanzun na fahimci asalin destiny. Ina da magana a bakina, amma bani da wanda zan juyewa, sai na zabi nayi ta kallon kowa da ita. A yau ina raye ne, dan wata kaddarar, amma nasan gobe bakin ciki ya ishe ni riga da wando. Domin dan saurayin da yan mata ke yi, bani da shi. Asalima Manga ne ya hanani sukuni, tare da cewa idan ina son a cigaba da sayan kayan mu, toh na amince mishi mu raya wani dare, daya har gonar Baba zai dawo mana dashi. Kallon shi nayi tare da murmushi nace. "Toh Malam Manga, sai dai har ka mutu Hussy bazata tab'a baka abinda kake hari ba." Dariya yayi sannan ya taso zai yo kaina, na daga mishi hannu cikin b'acin rai nace. "Wallahi ka Kuskura ka tabani zan maka.." Takawa nayi har gaban shi, ina kallon cikin idanun shi nace.. "Wallahi zan maka kaciya!" Ganin yadda fararen idanuna suka dira a cikin nashi ne ya sanya shi firgita ya juya da sauri ya fita. ....... Ina ganin mun tsallake wannan matakin. Sai ga wani tashin hankali wai ana zargin Abdul da satar akuyar Baba Yawale. Dariya muka yi, Abdul yayi bakin ciki sosai, dan har zolayar shi muke. Tsaki yake kawai yana cira. Toh ya zamu yi, tunda muna cikin line of destiny, dole mu cigaba da tsallakawa, har Allah ya bamu ikon cinyewan. --- Aahil (POV) Kallon matar sa yayi wacce take ta sharan barci, ya zuba mata ido. Bawai ya rasa kome bane, domin kuwa yazo mishi yadda yake so, sai dai duk matan da yake mu'amala bai ji mace kamar Hussy ba. Ajiyar zuciya yayi, da ya tuna lokacin da yake, murjeta bata ko tari. Sannan duk yadda yayi da ita bata ce mishi ta gaji, sai dai idan sun gama ya nemi kari tace tana da Class. Duk yawon bin matan shi bai tab'a haduwa da irinta ba, kuma baya jin zai samu irinta, idan ya duba matar shi tafi hussy kyau amma. Tsarin halittar ba daya bane. A ina zai samu hussy dako lallabata zai yi ya cigaba da moreta idan yaso sai ya san yadda zai saka a dawo da ita schl. Tashi yayi ya shiga ban daki, kwara ruwa yayi sannan ya fito. Kwanciya yayi yana nazarin ta yadda zai sameta. "Teemah" Itace yake da yakinin zai samu number ta a gurinta. .... Washi gari ko karyawa bai yi ba, ya shirya dan matar shi ba aiki take ba, a bakin kofar fita ya hadu da Yarinyar da take musu aiki, kallonta yayi sannan ya bata hanya ta wuce, ba kome bane matsalar shi yaga tudun mazaunin ta. Aikuwa tana shiga yabita da ido, bai ga wani abin burgewa ba. Shifa burin shi ya hadu da me irin halittar hussy! (Amma kana ruwa) --- "Allah Dr idan akayi baiko zamu iya gwada kanmu, a gani ko muna da lafiya, dan haka nazo maka hutu tunda anyi rabin aure, sauran zamu karasa a gidanmu." Inji Devanah, Kamar ya fashe da kuka, haka ya kalleta, sannan yace.. "Yanzun ke ko kunyar fadar haka baki ji ba. Ai ni bana fatan na sumbaci matar da zan aura, sabida kar Shaidan makiyin Baban mu, Adam yayi sanadin da zanyi laifi wa Ubangiji me ceto." "Amma dai naga wannan zamanin na jin dadin rayuwa ne! Don Allah ka daina mai da kanka, mara wayewa." "Lal.." Jin sakon a wayar shi ya sashi dubawa, dan a yanzun baya jin kome a ranshi na damuwa matuฦ™ar zai duba wayar shi yaga an cire kudi, sai yaji ya kara jin tausayin yarinyar, domin yasan banda dole bazata tab'a karban kudin ba, kuma shima ko a yanzun yayi aikin lada saboda Ubangiji zai bashi wani shatin babban fili a cikin aljanna. Murmushi yayi sannan ya zubawa wayar ido. Fauce wayar tayi tana kallon shi, tace. "Yaushe tafiyar ka?!" Tsaki yayi sannan yace. "Wata sati, amma ina son zuwa bauchi, akwai taron da zanje nayi na addini." "Ok zan raka ka!" Ware idanu yayi akanta yace . "Baki da hankali, me zaki yi a can, kawai ki koma gida idan na gama zan zo kafin na wuce." . Gyad'a kai tayi tare da tura mishi baki. Ya kalli wayar yafi sau goma, badan kome ba sai dan tausayin Husnah, ko wani hali suke ciki?! Ya dangin Baban su suka karb'e su?! Banda ya hango ilmi ibada a cikin ฦ™wayar idanunta ba, ba makawa da sai ya shiga garin ya mai dasu kiristoci, tare da buษ—e musu makarantar primary da Secondry, tare da primary health care. Toh ba zai iya ba, domin fahimtar Husnah HABIB Manga, itama ba taya baya bace, a cikin dalibai Musulmai na cikin makarantar. Dan ko kwanati a cikin award da aka bada na World hijab day, sai da aka bata kyautar yarinyar da tafi kowacce daliba saka hijab, tare da mata fatan Alkhairi ta dawo cikin makarantar lafiya. A lokacin da yaga takardan gayyatar bai damu da yage ba, sai da yaji Dr Aahil yana zage zage, wai akan me za a karrama yar iska shine ya duba, aikuwa ranar da za ayi taron yaje cikin shigar jamfa na wata material na maza. Sai wando kaftani

Chapter 5 of 10