Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
siyo, E, to Anas gaskiya duk sai ka siyo don abin da muke da shi 49 kadan ne in kuma ta na cin rogo in sarrafa mata ya yi dariya ya ce cin rogo ai sai ke Anty ya fita yin siyayya maigidan ya shigo ya tsorata da ramar da tayi, wanka kawai ya yi ya ce su zo su ga Likita ita kuma ta ce babu wani Likita da zata gani dan ta warke, ganin ta yi kicin-kicin ya hakura ya samu falo ya zauna ya zubawa rigimammiya ido. Anas na shigowa ta mike ta shiga kicin ta shirya girki Anas din ne ya taimaka ma ta wajan shirya tebir ya na zaune ya na karatun Jaridar Leadership hankalin sa na kan su sai da su ka kammala ta shiga wanka kafin ta fito ya na zaune ya na hattamawa, wani gululun bakin ciki ya tsaya ma ta wuya ta karaso ta dafa kujerar da ya ke kai ta ce, Yayana abincin bakin Anas ne, ko ma waye mu kinsan ko ba ayi mana tayi ba ci muke, to Allah ya kyauta, ta bude taga kadan-kadan ya ci ta gyara ya ce kwalliyar ki ta birge ni zo ki raka ni Mr. Biggs, ta ce amma dai kasan hijab zan sa da nikaf, ya ce E, na sani ki zo ki raka ni ta ce bakin da za su zo masu mahummanci ne dan ni zasu zo dubawa, bai kamata ace ba na nan ba, yanzu fa zamu dawo, dole dai ta bishi su ka tafi, ashe wayo ya yi mata asibiti za su, Likitan da su ka gani ya yi mata tambayoyin daga karshe dai scarnning aka yi matga nan su ka tabbatar da ciki har na wata 50 biyar shi kansa Likitan ya yi mamakin sakarcin da tayi ba ta gane ba sai dai kuma da ya ke na fari ne kuma har yanzu da ta ke da cikin tana yin messes murnar da Nazir ya yi abin gwanin sha'awa don tun a gaban Likitan ya ringa nuna mata murnarsa daga nan sai Mr. Biggs sun suyo snack sannan ya shiga da ita wani store nan ma dai kudi ya kashe sannan su ka nufi gidca ta ci sa'a bakin nata sai da ta dawo su ka zo. Washe gari Nazir da kansa ya ringa fita da rogo a ranar aka zuba kayan abinci wannan cikin ya sa Nazir ya ringa tarairayarta ita abin har mamaki ya ke ba ta, saboda wani irin zazzafan so da ya ke nuna ma ta, ko da ya koma Dubai satinsa bi biyu da ya dawo kuwa babu abin da bai zo da shi ba na baby, ai kuwa aiki ma hana ta ya yi ya ce sai ta haihu kafin ta haihu ne ya ke fada mata zai soma ginin sa dan gidan da zai gina zuwansu London ta nuna sha'awarta da gidan shi kuma ya sa aka zana masa gidan cikin satin da ya fada mata aka soma gini. Cikin Shema'u ya isa haihuwa faf Laraba da asuba Allah ya sauke ta ta sarnu 'yarta mace mai kama da ubanta sak! Ranar da ta kainu komal kan idanun Nazir eka yi don duk korar da akayi masa kin tita ya yi da ya fita zai dawo, yarinyar 51 kuwa da an karfe ta sai ce kawo ta tun ya na bai wa Hajiya haushi har ta hakura. Ranar suna yarinya ta amsa sunanta Halima, sunan Hajiyarsa saboda haka muke ce mata Nur, a gaskiya sunan Nur dangin Hajiya sun zo da yawa akwai wata 'yar kanwar Hajiya wai ita Ummulkulthum wacce tazo suna tun da aka yi suna ba ta koma ba, ko da ya ked ba na ce mata yarinya ba don a haife ta girman ga ta dama ita irin mutanan nan ce ga girman jiki ga tsayi sannan kirjinta a shafe ya ke, uwa uba babu mazaune ko da ya ke ba za ka sa ta sahun farare ba haka ba za ka ce ma ta baka ba, amma sam ba ta da fasali, don ko ni mace ba ta yi min ba ba re kuma da namiji, Ummu irin 'yan gayun nan ce ma su iya yin fasi fa ga shi karatu ta ke dan medicen ta ke karanta, amma fa kwakwalwarta fanko ce don dai irin 'yan dumama kujera, turanci kuwa ko na minti biyar ba za ta iya ba, ga shi mahaifinta ya dauki burin ganin sai ta zama Likita, dan shi mahaifinta ba mazauniba ne hakan mahaifinta ya rabu da mahaifiyarta saboda mugun halinta Ummu tasha raba cahaifinta dda matarsa dan sam ba t ada hali ga shi mahaifiyarta na matukar sonta don ita kadai ce da ita ba ta san' 6acin ranta, duk dacewar mahaifinta na yin rawar gani wajan 52 tarbiyarta da karatunta don ita ko note ba ta yti sai inDady ta ya yo waya ya ce zai dawo zata yi saboda dole ya duba littattafan ta duk da in ya duba ba ya gamsuwa don mafi akasari in ya yi mata tambayoyi babu amsa, shi ne ya ce wai mr isa ba ta sa Date cikin note dinta shi ne yanzu in zata yi kwafin sai ta sa Date saboda ya kan bi date ne ya duba. Zuwan Ummu gidan ya kawo sabon canji saboda bala'in iyayanta duk samarin gidan babu mai sakar mata fuska da ma shi Nazir ba ya kasar sai Abubakar shima saboda ita ya daina hira falon Hajiya, tun kafin na haihu Alhaji Yusif baya nan sai dai an sanar masa ta waya don ya na Cairo to yau Allah ya dawo da shi har falona ya shigo abin da ban taba gani ba, kayan barka kuwa masha Allah har da dubu goma akai, da safe kamar yadda kowa ya saba zuwa gaishe shi nima sai da naje don jego bai hana ni zuwa ba, to hakan ce ta kasance Ummukulthum itama taje ya amsa gaisuwar ta ya ce bakuwa muka yi? Ta ce "Ba ka gane ta ba.?" Та се 'yar gidan Hajiya Hauwa ce Ummu ya ce au! Ita ce, i ai tun suna ba ta tafi ba ya ce bazawara cem haba Alhaji budurwa ce fa ya yi salati ya sanar da Ubangiji, ya ce yanzu shi mahaifinta ya zauna da wannan sangamemiyar a 53 matsayin budurwa, ba ya tsoron kar duniya ta zage shi yanzu in ya shiga gida zai iya gane wace uwar wace 'yar? Gaskiya ya yi mata aure, Hajiya ta hade girar sama da ta kasa saboda tana ganin kamar ya ba da ita cikin kishiyoyinta, Alhaji karatu fa ta ke Likita ce ya ce Allah isa ita ce ABCD in ban da shashanci ka zauna da ya yi wannan girman ba ka tsoron haduwar ka da Allah ko ko sai ya dauko abin kunya ka dora masa laifi? To wallahi aure zan mata ke daga nan ma wajen mahaifinta zanje, in karasa mai gaya maka gaskiya kayi asara yana cikin fadan sai ga Anas da Abubakar sun shigo. Ya kalli Anas ya ce kasan Ummu 'yar uwarka? Ya ce "E." Alhaji na santa wani abu ya faru? A'a na baka ita wata biyu masu zuwa biki, ya yi wata irin dariya ya ce Allah na gode na gode sai dai ni wallahi ina da wacce zan aura mun yi kuma alkawari kuma kai ka ke daďa tunasar damu kan mahimmancin alkawari, sai dai ga dan uwana nan Yaya Abubakar ko zai yi kari, Alhaji ya ba wa Abubakar shima ya yi godiya ya ce a'a amma bai sani ba ko Umar zai karba tunda dama wacce ya ke so ta yi auran ta, nan fa Hajiya ta yi ta fada wai an wulakanta 'yar kanwarta duk su ka zuge, saboda a gaskiya irin sigar Ummu ba ita maza ke 54 yayi a yanzu ba saboda ita ko saurayi ba ta taба yi ba a rayuwarta, daga ita har uwarta ba su da burin da ya fi ace yau an sami mai sonta, to gaba daya dai sun zuge wannan abu bai wa Hajiya dadi ba, Nazir ya da wo daga Dubai, gida ya dauki murna kamar yadda aka saba, ana ta shan alawoyi kalakala da bisket da dai sauran tarkace, tun da ya dawo idanun Ummu na kansa kamar tsohuwar mayya, yadda taga ya na tarairayar matarsa sai t ake ganin ina ma ita ta samu haka har ta kuduri niyyar fidda Shema'u ita ta zama madadinta. Nazir ya shiga falon Hajiyansa hannunsa dauke da Nur, ya na tafe ya na yi ma ta wasa kaı ka ce da wata me wayon ya ke, Hajiya ta kalle s} ta ce "Kai dai ba ka jin kunya diyar fari kake wa wasa, Hajiya kawo miki ita fa nayi, ina uwarta? Wanka ta ke ni kuma sai na ce bari in kawo ta gurin Hajiyarmu ta goyata a bayanta, kai raba ni da goyon 'ya'yan mutane ai ni yanzu na ce na daina goyon jika, subul ta sako baki Ummu kenan ta ce, kawo in goya ta mu iyaye bama gajiya da goya 'ya'yanmu. Hajiya ta ce E, ku yi ta goya su da ma naku ne, amma ni ba zan goya wannan katuwar ta karya ni ba, ba Husna da ke zaune tana jin su itama ta tofa tata ta ce kinga kuma Alhaji ya saba da ita dan naji ya na cewa gidanta da ban da 55 ba anan kasar za su zauna ba sai Saudiyya ba ki ji sunanta ba Nur, haske fa ake nufi ai wannan ta fi su ce, Ummu ta karbi Nur ta goyata ta juya ta fita daga falo Nazir ya ce Hajiya ina kika samu wannan zankalar ta ce ba ka gane Ummulkulthum din ba? Au! 'yar gidan Umma Hajiya ce ra ce i ya ce zaman me take a gidan nan ina gidan mijinta ta ce ai budurwa ce karatun Likita ta ke kai Hajiya gaskiya ya kamata ayi mata aure, ta ce ai kai muke jira kai ne mijin ya ce kai wallahi wannan ko a kafa aka daure min ita sai na kwance na gudu, ina zan kai wannan? Hajiya ta bata rai ta sake salon hirar ta su, ashe duk Ummu tana jin su. Da yamma ta shirya ta tafi gida in da ta fada wa mahaifiyarta ita fa Nazir shi ne choosing dinta saboda haka mahaifiyarta ta ce ka r ki ji komai kamar an yi an gama. Da safe Nazir shi da Shema'u su ka shiga gaida Alhaji anan shima aka yi masa tayin Ummu kamar yadda aka yi wa 'yan'uwansa amma ya ce me zai yi da ita, can dai ba ta da fasali har su ka dawo wajansu ya na ta mita wai shi an cuceshi hada shi ma kawai da aka yi. Kafin Nazir ya koma Dubai sai da ya je gidan Umma Hajiya don shi ba ya zuwa sai Sallah, amma sai ga shi can ne gurin cin abincinsa 56 kwata-kwata ya sallama na Shema'u abin zai ba ka mamaki kina ce Nazir ya rikice kan Umınu dan yanda ya ke musu barin kudi abin da mamaki, ana zaune tsakar gida Hajiya take ce da kishiyoyinta wai Nazir zai auri Ummu amma ita kwata-kwata ta fi sha'awar Anas ya aure ta saboda shi ne ba shi da aure haba Hajiya wannan wace irin magana ce kina ganin yadda matarsa ta sake sosai duk cikin yayanmu mata wa ya samu yadda Shema'u ta samu ki godewa Allah tunda da kansa ya dawo ya ce ya na sonta, ai da yanzu ki a garin wasu gara a garinku a garin ku ma a gidanku a gidanku ma a dakinku a dakinku na kuma a hannunka, duk ina za ki so Shema'u ya yi E, Ummu 'yar 'yar'uwarki ai wallahi gwanda ya aure ta itama ta ji dadi yo irin wannan 6arnar da kudi da ya ke ma ta, ai wallahi Hajiya kar ki sassauta sai an yi ayi nan da nan a gama, au ya ce sai ya gama gininsa, nan dai su ka zige Hajiya tas. Ta 6angaren Nazir kuwa yanzu soyayya ce mai karfi ta kullu shi da Ummu, in kuwa zai tafi Dubai dole ne iya adadin kwanakin da zai yi sai ya yi list dan kudin zancen kwanakin ya bayar in kuma ya na nan to ta na gaban motarsa su na zaga gari kwata-kwata Shema'u tun ta na girki da shi har ta hakura tun tana san jin dalili har ta zuba wa 57 sarau ar Allah ido kuma duk wannan zancen auran da ake kwata-kwata ba ta sani ba, dan babu wanda ya fada mata duk abin da ake na aure babu abin da ba akai ba wanda ya zama al'ada amma ba ta sani ba, ko ya fada ma ta ya gama gini bai yi ba illah yaje ya dauki Umma Hajiya da amaryarsa Ummu ya kai su gidan sun dimauce da ganin gidan ya се su zabi daki su ka ce to biki ya rage saura sati uku. Aysha matar Abubakar ta rasa yadda zata tari Shema'u da zancen da ya karshe ta shiga falonta ta zame ta a zaune ta yi shirin fita zuwa in da ta ke koyarwa su ka gaisa ta ce dama wata magana nake so muyi, ta ce ina jin ki Ukti dan haka ta ke ce mata, to abin da zan fada maki ba mai dadi ba ne, amma ina so ki nutsu ki kuma yi tawakkali don nasan dole ne ki sani yanzun ma abin da ya sa na fada miki dan ki yi wasu gyare-gyare, Ukti ina jinki don Allah ki fada min ko hankalina ya kwanta, ta ce to ba wani abu ba ne illa ina son in tambaye ki kinsan Nazir zai yi aure? Har yau saura sati uku tini ma anje an yi jeren amarya tun jiya jikin Shema'u ya hau tsuma ta ce Ukti fada min gaskiya Nazir dina Yayana shi ne zai min kishiya shi ne zai haďa ni da wata, don Allah Ukti kice min April full ki ked min dan zuciyata bazan 58 haska wasu Kona kanka ni da nake ganin ko uku zai yi kina da hikimar da za ki zauna da kowacce, nima abin da ya sa na fada miki don kiyi kyararrakin da mu kan yi a al'ada in za ayi mana kishiya, kiyi zamanki in da bai gaya miki ba kar ki nuna kin sani ke dai yi gyaranki nan dai ta zauna ta yi ta bata baki har ta yarda ta fasa tafiya yau aikin da bata fita ba. Nazir bai dawo ba sai ana i jibi daurin aurensa da Ummu ni duk a tunanina Jamila zai aura ashe wai Ummul kai namiji sai a barshi shi da ya ce ko a kafa aka dora masa ita zai kwance ya yar sai gashi an wayi gari ya na kiran ta da (Ta musamman) kai namiji dan kansa ne ana i gobe za a daura aure kuma washe gari kenan kai amarya а ranar ya zo mun da zance gobe daurin auransa zai auri Ummulkulthum, kanwarsa gobe za a kaita a yau dai ya ke so in kwashe kayana in koma sabon gida, ji nayi kamar in shake shi ya mutu don takaici na ce a'a Nazir ka barni a nan Allah ya baku zaman lafiya da na ji zai dame ni kawai na fice na yi 6angaran Ukti, ji na yi an ce in zo babana ya zo na fita na gaishe shi ya ce min maza hada kayanki ki koma sabon gidan ku Allah kuma ya baku zaman lafiya, haba yar albarka Shema'u ki sani duk in da kike albarka na tare da ke tunda 60 na aurar da ke ban taba samun matala ba, kullum sai na yi miki addu'a mai kishiya zata tsinta a wanda ke baki tsinta ba, nan fa ya ringa yi mata wa'azi ta tashi ta na kuka ta hada kayanta aka zuba a mota sai sabon gida ta yi sallama da mutan gidaduk anje rakata. Kuma sai maigida da ya gyare ya ke tas falo yasha gyara da wasu irin kujeru dun dum dum dum ga irin shegun kayan kalo dining table din ku abin a gani ne ga wata hadaddiyar show glass an jera wasu irin kirinset labulayan kawai sun ba wa dubu dari baya, Shema'u ta gigice da wannan shegen gyara master room shima wani Italian bed ne aka shimfida masa wani arnen bedshirt gidan all of then dinsa an cika shi da kayan kudi room da ya kawai aka bari babu komai a ciki kuma babu in da aka rufe ko ina a bude ya ke kicin ma abin gwanin sha'awa Nazir ne ya shigo ke Shema'u har dakin da babu kowa shi ne naki duk nan da kike gani kayan amarya ne ta kalle shi ta girgiza kai ta ce, to, ta kalli Aysha ta ce Ukti ku saka min gado dan nasan babu gurinsa sif a jeran akwati na ragowar kayan a saka min su a gareji, hakan kuma aka yi. Da daddare wanta ya kawo mahaifiyarta tazo ta yi mata nasiha mai ratsa zuciya, ta ce kiyi 61 hakuri duk wanda yaga take-taken auran nan tun farko to an san da wata manufa aka yi shi, to amma ki sani hakuri ba ya 6aci duk rintsi duk wuya kiyi biyayyar aure wataran sai labari nasan kina da ilimin Islama kin san tarihin manyan bayin Allah mata wadanda suka yi biyayyar aure da irin rabon da su ka samu kina da tarihin Rabi'atul Adawiyya, haka tarihin Nana Fadimatu, Bintu Muhammad da irin biyayyar da tayi, ku 'ya'yan yanzu ne ku ka dauki aure gurin holewa da jin dadi amma ai shima bautar Allah ne mahaifinki ya ce ya na yi miki fatan alheri, ya na kuma kara tausarki duk abin da za su yi miki ki mika lamarinki ga Allah don yanzu idanun kowa da kunnen jama'a ya na kanki duk wani yunkuri da zaki yi sai a ce kishi ne to kishi halal ne, ki san irin wanda za ki, wallahi Shema'u nasan kina da zafin kishi to kiyi hakuri tunda naji maganar auren mijinki nake miki addu'ar Allah ya rangwanta miki haka da ta yi tayi mata nasiha har ta ji zuciyarta ta lafa sannan ta tafi. Washe gari aka daura auran Ummu da Nazir ko yanki bai bani ba bare wasu kayan fadar kishiya. Bayan sallar Isha aka kawo amarya tunda 'yan kawo ta su ka zo suke yar da magana ice ko 62 ba ayi musu sata ba ko kuma a barbade musu kaya da magani don sun san aikina ne yau kwanan gidan amarya duk a nan aka kwana amma haka Ummu ta tsallake jama'ar da su ka kawo ra tayi master room a nan ta kwana ita da miji kun ji amaryar zamani, har sha daya ba su fito ba su na can ana zuba amarci nan kuwa tsofaffi duk an shanya su duk da uwar 'yan uwanta ne sai da su ka nuna ba su ji dadin yanda ta zake ba haka na danne kishina na kula da duk jama'ar da su ka zo sai da Suleman yazo muka gaisa ya ce ya na son ganin Ango na ce, to bara in je in kira shi na je n ayi nocking din kofar tun kan in shiga na jiyo mitarta wai shi kamar bai da mata ya fiye damu naji dariyarsa, nan da nan na ji wani abu ya soki kahon zuciyata, na ce Yayana Suleman na ji wai duk sun hadu ango bai fito ba, ya ce to bari muyi wanka sai mu fito na ce, to haka dai har aka gama budar kai kowa ya watse daga ni sai amarya sai maigidan da 'yar babynmu Nur. Ango Nazir dai bai shigo dakina ba sai da ya kwana tara dakin amarya wanda ni nasan addini da al'ada sati daya ya ba shi a matsayinta na budurwa ban nuna masa na ji haushi ba dan nasan shi ba jahili ba ne ya sani sarai, babban abin da ya takura min shi ne rashin sukuni a gidan, don ko 63 Yau tun da gari ya waye da ya ke muna jarabawar karshe ina sauri saboda yau muna da gasa karatu ga shi ina daga cikin daliban da jaharmu ta dauki nauyin mu zuwa Misira kowa ya na ta ya ni murna amma Ummu ko kallo. ban isheta ba, dama ita tunda ta debi kayan kicin dinta sai ya zama koda ta yi sha'awar yin girki sai ta yi a falo ko a jikina domin ban da tsinke cikin falon balle wani akasin ya faru a sha dani na yi shiri dan har na goya Nur zan tafi na samu Nazir da Ummu za su fita na ce Yayana don Allah in hanya daya zamu yi ku rage min hanya, ya kalli Ummu ya се Tamusamman kina jin abin da Shema ta fada, tana yatsina ta bude jakar ta ta dauko naira dari wai in shiga taxi, su sauri suke, takaici ya kama ni Nur ta sa kuka ta na mika wa mahaifinta hannu ya kalli Ummu ta ce ka dauke ta ta raka mu, yasa hannu zai fige ta a bayana na ce uh'um makaranta zani ka bar min yarinyata, ta kalle ni sannu me 'ya, ko kunyar fada ba ki ji ba ya fige yarinyar ya mika ba ta wani rungume ta kamar gaske, ta kalle ni ta ce awon kaninta zamu kinga kuwa ya kamata tayi mana rakiya, su ka ja mota su ka tafi nima ta tafi ni dai haka na kammala pepar nan amma bani da natsuwa ina kammalawa na dawo gida har na dawo ba su dawo ba, kwanciya nayi saboda a 65 gajiye nake. Sai La'asar na farka, ina tashi na fito falo, a falo na same ta tana wasa ita kadai na juya na shiga wanka ina fitowa na tada Sallah. Nur da ke wasa a falo ta nufi show glass din Ummu ta na wasa, daidai lokacin Ummu ta shigo falon, ke ke ta daka mata tsawa kaga shegiyar yarinya za ki cuce ni ki fasa min kaya 'yan uwa kar ku manta Nur fa a lokacin shekarar ta daya, iri ta soma tafiyar nan dan ko kwari bata yi ba ba ku ga fincikar da ta yi ma ta ba, taja ma ta kunne ki ka kara zuwa gaban show glass dina sai na ci ubanki ko kayan uwarki ne yarinyar ta kwalla kuka wanda ina Sallah ya gigita ni, duk da dai ban san yadda aka yi na sallame sallar ba na tsince ni ne a hanyar falo a daidai lokacin da ta ke wannan fadan shi kuma Nazir shi dá kaninsa Anas sun shigo falon nima na kawo falon da niyyar in zo in dauke 'yata ganin na taho da hanzarina ya sa ta dauke yarinyar da mari, kafin in kai in da su ke yarinyar ta kife akar ko motsi ba ta yi, kafin in je Nazir da gudu ya dauki yarinyar ya na fadin kina da hankali kuwa, shi kuwa Anas bai yi wata-wata ba ya dauke ta da mari ji kake tas! ya sake kifa mata ta wani 6arin, shi dai Nazir ko ta kanta bai biya ba ya na ta girgiza Nur amma ko motsi, ya rikice gaba daya sai mikawa Anas ya ke ya na 66 cewa kaga ni ta mutu ko Anas ya karbe ta ya saba a kafada ya fita shima ya bi bayansa na kasa komai sai kuka saboda nasan yarinyar ta mutu ne ko ni Ummu ta daka sai naji jikina balle 'yar shekara daya. Ba su su ka dawo ba sai bayan Sallar Isha. fuskar nan tata gaba daya ta kumbura aka dawo min da ita Anas sai ban hakuri ya ke shi kuwa uban gayyar ya kasa magana cikin dare jikin Nur ya yi tsananin zafi saboda zazzabi na jika tawul ina goga ma ta can yarinya ta ringa fisge-fisge na rása in da zan yi da raina na tashi na yi master room ina nocking din kofar kuma ina jin surutan su amma an ki a bani damar shiga, ganin halin da Nur ta ke ciki yasa ni danna kai cikin dakin na yi nadamar abin da na gani, kuma nasan a yau nice da girki koda ya ke ni kaina bazan iya tuna ranar da Nazir ya kwana a dakina ba ya na tashi ya zabgan mari wai ni wacce irin mahaukaciya ce na nuna masa Nur da ta ke a sume na ce ka gani Nazir ka gani zata mutu kuma in ta mutu matarka ta kashe min yarinya ya ce to ta mutu mana ina ruwana ko an ce miki na damu na dawo daki ina ta tofa mata addu'o'in da su ka sauwaka a gare ni. Gari na wayewa ko wanka ban yi ba salla kawai na yi na goye Nur a bayana ina fitowa a falo na same su na durkusa na gaishe shi na ce Nazir ga Nur fa ciwon 67 ta yayi zafi ka taimaka ka kaita asibiti ya ce na gaya miki ba damuwata ba ce, kije ki kaita mana in ta mutu Allah ya jikanta, hawaye yha biyo fuskata na mike jiki babu kwari yayin da Ummu ta rinka jifana da wani matsiyacin kallo takaici ya kama ni saboda yau da gobe sai Allah na duba ma'ajiyata ko ficika bani da ita, ga shi daga nan zuwa gidanmu tafiya ce mai yawa, haka na daure na fito, tafiya nake ba ta wasa ba saboda na gaji ai ni naji ana yi min hani na duba sai naga Anas ne ina zaki ne? Na je duba Nur aka ce ba kya nan, zan je gida ne a kasa kike nufin za ki tafi, na girgiza kai kasan safiya ce motoci suna wahala mai ya hana mijinki fita da ke na ce yau baya jin fita shigo in kaiki na shiga baya tun muna mota tana goye a bayana na ji tana wannan fisgefisge ya na tsaida mota tun kafin ya yi magana nayi fid na fice da gudu na shiga gida na kunto Nur tana fisge-fisge mahaifiyata tana tambaya ta lafiya? Ina kuka na ke fada ma ta abin da ya faru, ta juyo da niyyar zuwa gun mahaifina ashe ya na tsaye ya na jinmu ta ce Malam bari in shirya mu ta fi asibiti baba na cikin fushi ya ce ba zai yuwu ba ba hakkinmu ba ne mu kai ta asibiti tunda ya na da iyaye bani yarinyar in kai wa mahaifansa in suma sunga ba za su kaita ba

Chapter 9 of 10